Hausa novels

Kanwar Maza Page 70 Complete Novel By Ayshercool

Page 70

 

A rikice Jamil ya kalli takawa ya ce “Kana nufin ni ne ke da alhakin yin garkuwa da aisha, kai ba a zargeka ba sai ni?”

 

Adam ya ce “Ni dama a can a cikin zargi nake, ban ce kai kayi garkuwa da aisha ba, amma abun da ka yi ya jefa ka cikin zargi, madalla da yarinya mai kaifin tunani kamar rumaisa” yana gama maganar ya fice daga office ɗin.

 

Wani irin gumi Jamil ya yakice, yana wani irin huci.

 

“Da ni ka ke zancen Adam, zaka gane ba ka da wayo, daga kai har wannan shegiyar yarinyar mai ƙulla mini jakar tsaba, saboda kaji su bini”.

 

A daren jiya kuwa, Mahmud yawonsa ya din ga yi da Sabir, har da zuwa yawon ciye-ciye, ya sayawa Sabir kaya ba kaɗan ba, soyayyar da  yakamata ya ji game da ɗan uwansa Adam, shi yake ji a Sabir, koma ya ce fiye .

 

Ammi tana nan tana dakon dawowarsu, Nusaiba da Iman ma, duk suna tare da ammi, suna jiran dawowar Mahmud.

 

Wajen ƙarfe tara da rabi, sai ga Mahmud, sidi ya biyo shi, da uban faggon kaya niƙi-niƙi, zuwa shashin Ammi, da da yake ji kamar wata baƙuwar duniya, amma yanzu the more yake shiga, the more yake zama familiar da wurin.

 

Mahmud ya nuna masa wuri ya ajiye kayan, ba tare da ya kula kowa ba, ya ƙarasa kan kujera, ya kwantar da Sabir da yake bacci, ya durƙusa a gabansa yana ta shafa gashinsa, kamar ya tafi da shi, ya kwana a wurinsa.

Ya miƙe a hankali ya juya zai fita, Ammi ta ce “Wannan kayan fa?”.

 

“Nasa ne” ya faɗa a taƙaice ya fice.

 

A sashin Mummy ya tarar da Mummy ta rako Samha, tana ta rarrashinta, idonta yayi jawur, alamar ta sha kuka, ya san ba zai wuce ta gaya mata saƙon Adam ne ba, shiyasa take wannan kukan.

 

Sai da Mummy ta rakata har mota, sannan ta koma sashinta.

 

“Ina ka je ne? Tun sallar magariba baka dawo ba, baka kirani ba kuma, na san baka yawo da daddare”.

 

“Na fita da Sabir ne”

 

A ɗan razane ta ce “Waye Sabir?”

 

“Ɗan mu da Adam ya haifa”

 

“Au yanzu dan rashin zuciya, har ɗan sa ka je ka ɗauka kana yawo da shi? Wurin giwar ka je kenan?”.

 

“Sirikarta na saka ta ɗaukko mini shi, ina ƙaunar yaron nan sosai da sosai”

 

Mummy a ranta ta ce “Lallai tsuguno ba ta ƙare mini ba, akwai sauran rina a kaba, aikin malam na kan dutse ya fara sanyi”

 

Ya ce “Mummy, ya dai na ganki wani iri, akwai damuwa ne?”.

 

“Damuwa akwaita Mahmud, ban gane maka bane kwana biyun nan, ka san dai a duniya bamu da maƙiya sama da giwa da Adam, yanzu kuma naga kamar alaƙa ce tsakanin ka da matarsa, ko ka san yarinyar nan cewa ta yi wai ina yi wa Adam asiri?”

 

A ransa ya ce “Tom, hasashena ya tabbata, matar nan ta faɗa tarkonmu”

 

“Na gaji da wannan rashin albarkar, nan ya zo ya gama yi mini rashin mutunci, a gabana ya ci mutuncin ƴaƴana, saboda wannan hatsabibibiyar yarinyar, kuma ta ce wai ina yi masa asiri, a gidan ubanta ta ga asirin, zai maimaita a gaban mai girma wambai, dole ayi mini iyaka da ita”.

 

Cikin ko in kula Mahmud ya ce “Amma dai idan ki ka kai ƙarar wannan Yarinyar, za ace girma ya faɗi, raƙumi da shanye ruwan ƴan tsaki”.

 

“Ba ita zan kai ƙara ba, shi Adam ɗin ita a wa, ina ruwana da ita, amma dole ayi mini iyaka da su”.

 

***

Daf da la’asar, rumaisa ta shiga ɗakin takawa, tana dudduba abun da za ta gyara.

 

Daga toilet ta ji ya ce “Waye a nan?”

 

Ta amsa masa da “Ni ce nan”

 

“Rumaisa duba drowern mirror, ki bani shaver”.

 

Ta yamutsa fuska ta ce “Rumaisa kuma?”

 

Ya ce “Eh”

 

“Ba cewa ka yi mimi zaka din ga ce mini ba?”

 

“Anƙi ace mimin, miƙo mini da sauri”

 

Ta ɗaukko shaver ɗaya, ta tsaya a ƙofar banɗakin ta ce “To shigowa zan yi?”.

 

Ya ce “Eh miƙo mini”

 

“Au kai ba ka jin kunya, to ni ba zan shigo ba, zuro hannu ka karɓa”.

 

Ya ce “To ai ba tsirara nake ba, miƙo mini abu nake yi”

Ta tura ƙofar a hankali, ta ɗan leƙa, yana tsaye a gaban mudubin toilet ɗin, ya shafa wani cream a fuskarsa, da wata shaver a gabansa, ga wani towel ɗin a wuyansa.

 

Duk da haka sai ta ji wani iri, ta ƙarasa a hankali, ta tsaya tana kallonsa.

 

Ba tare da ya kalleta ba ya ce “Ya dai?”

 

“Bakomai, so nake naga me ake yi da shaver”

 

Ya ɗan waro ido ya ce “Baki san me ake yi da ita ba?”

 

Ta jinjina masa kai alamar eh.

 

“Ba kya aski kenan?”

 

Rumaisa ta ce “Ni namiji ce da zan yi aske kaina”

 

Ya girgiza kai ya kerɓi shavern ya ce “To tsaya ki ga me ake askewa da ita”.

 

Aikuwa ta tsaya, ta zuba masa ido.

 

Ya kammala gyaran fuskarsa da ita, sannan ya ɗebo cream a wata container, ya shafa a hammatarsa da ta fara fitar da gashi, ba sosai ba.

 

A hankali ya sanya shaver yana cire gashin. Ta ce “Innalillahi, dama abun da ake yi kenan, to ni ya aka yi bani da shi, sai yaushe zai fito mini?”

 

Ya ce “Da gaske baki da shi?”

 

Rumaisa ta ce “Bai fito mini ba, kuma ina so, in ga ya fito mini da yawa, idan na ɗaga hannuna a din ga gano shi”.

 

Adam ya ce “Saboda ƙazama ce ke? Waye yake ado da gashin hammata, ƙazanta ne to”

 

“Eh, amma dai ina son ya fito mini”

 

“Duk ranar da ya fito, ki ka bar shi, ni da ke ne, idan kin ga ya fara fitowa ya taru, ki yi mini magana in sake koya miki yadda zaki aske shi. Amma gashin hannta ba abun so bane, ba abun ado bane. I even wonder kin fara period but still a child”

 

Rumaisa ta ce “To ni dai Allah ya sa ya fito da wuri, sai ka sai mini shavern nima ko?”.

 

Ya ce “To, jeki zan aske ɗayan”

 

“Me?”.

 

“Gashin” ya bata amsa kai tsaye.

 

“A ina yake shi kuma, ko na ƙafarka, ga hannunka ma”

 

“A’a towel ɗin ƙuguna zan kwance, nan ma akwai wani, shima ba a barinsa cirewa ake yi, idan ba haka ba mutum ya din ga wari, idan ya fito shima ki gaya mini a sayo shavern, sai in koya miki”

 

Yatsunta ta saka, ta toshe kunnunwata ta bar toilet ɗin, saboda ta daina jin abun da yake faɗa, a tunaninta ai wannan abun kunya ne.

 

Ta fice daga ɗakin sa, ta sauka ƙasan bene.

 

Asiya da barira, suna ta yi mata sannu da gida, ta amsa musu tana gaishe su, sai dai ta lura da yadda baba Uwani ke ta wani kumbura fuska.

 

Ruma ta ce “Baba uwani, me nayi miki ne?”

 

Ta kalleta ta ce “Hmm tambayata ma ki ke yi?”

 

“Papa yayi mini faɗa, ya ce kar na sake ai, ranar ma dan raina a ɓace yake ne”.

 

Asiya ta ce “Ranki ya daɗe, wata jita-jita na jiyo, da na je karɓo miki saƙo a wurin Ammi”.

 

Ruma ta ce “Wace jita-jitar kuma?”.

 

“Wai saƙo ya iske cewa, kin ce hajiya jamila, babar Yallaɓai Mahmud, wai tana  yi wa maigida takawa asiri”

 

Rumaisa na jin haka, ta san mahmud ne ya bayar da wannan saƙon, yana nufin baba uwani ta kai tsegumin, kuma shi ya saka ta faɗa a gaban baba uwani.

 

Rumaisa ta waro ido ta ce “Ni ɗin, waye ya faɗa? Ni harkar wa ma na shiga balle na faɗi wannan maganar?” Ta ɗan yi shiru sannan ta ce “Anya babu munafuki a sashin ammi? Idan ma na faɗa, ai ba a gaban wasu bare na faɗa ba, balle ma ban faɗa ba. Amma ai ba ƙarya nayi ba, idan ma na faɗa, idan ta san ba ta yi, ai ba zata tsargu ba, idan kuma yin take, A’uzu bi kalaimatillahi tammat.

 

Tsuru-tsuru baba uwani tayi, tana ta yaƙe baki ta ce “Ai uwar ɗakina, asirin ma ba za a rasa yi ba, saboda abu ne na gidan sarauta, kowa kansa kawai ya sani, galibi ba Allah a ransu”

 

Ruma ta ce “Yauwwa, Aisya kin ji ko, barira ma kin ji, ga baba uwani ma ta faɗa, mummy na yi wa takawa asiri, ashe bani kaɗai na fuskanci hakan ba”.

A rikice baba uwani ta ce “Ba haka nake nufi ba, ki yi wa Allah da ma’aiki kar ki ƙulla mini sharri”.

 

“Ba sharri bane, ai ke ki ka faɗa”

 

Rumaisa ta nufi hanyar satairs, cikin tashin hankali, da mamakin yadda jikar cikinta, take yi mata wayo, ta bi bayan rumaisa. Ruma ta tsaya ta waiwayo ta ce “Idan ki ka biyoni sai na gaya masa” ta juya ta cigaba da hawa.

 

Ta koma a sukwane kitchen, ta ce “Aisya, da ku za a haɗu a ƙulla mini sharri ko?”

 

Barira ta ce “Ba wani sharri baba uwani, mu ba butulu ne irinki ba, idan baki yi wasa ba, an ƙulla miki kyakykyawan tarko kema, kamar yadda ake haɗa baki da ke, ake cin dudduniyar giwa”.

 

“In ji uban wa? Waye ya haɗa bakin da ni?”.

 

Asiya ta ce “Oho, a juri zuwa rafi da tulu…”.

 

Barira ta ce “Wataran zai fashe”.

 

Ruma kuwa daɗi take ji, ta san tana daf da tonawa baba Uwani asiri. Ta shiga kitchen ta duba fridge, taga takawa ya kawo kaji, amma bai gaya mata ba. Ga kayan miya duk ya ajiye bai gaya mata ba, balle ta yi aikin su.

 

Tana aikin tana mita, ya zo ya tarar da ita a kitchen.

 

“To uwar ƙorafi, menene kuma?”.

 

“To ba kaine ka kawo aiki ba, kuma ba ka gaya mini ba”.

 

Ya ce “No, su Aisya na ce idan sun gama aiki, su zo su gyara miki, sai ki ɗibi naki, ki basu na gida”.

 

Rumaisa ta ce “Saboda ni ban iya aiki ba ko? To Wallahi ina ƴar ƙaramata, na iya gyara nama, ko kaza ko kofi, ni fa tun ina shekara uku mama ta ce nake kuka, a bani ɓare maggi, da daka, na iya aiki sosai da kake ganina”.

 

“To Allah ya baki haƙuri, idan kin gama, ki dafawa mama wani abun, ko mu saya a waje, mu je ki gaishe ta, dan ni ina zuwa mu gaisa”.

 

Tsalle tayi a kitchen ɗin “Yeeee, zan ga mama, amma shine ka yi mini wayo, ka ke zauwa kai kaɗai?”.

 

“Eh, ai da yake maman tawa ce, ba taki ba, kuma a kyauta zan kai ki ba, da sharaɗi”.

 

Cikin mamaki ta ce “Sharaɗi kuma?”

 

“Eh sharaɗi mana.

 

Ta ce “Na me?”

 

“Kiss zamu yi”

 

Ta kwaɓe fuska ta ce “Kiss, iskanci fa kenan”.

 

Ko a jikinsa ya ce “Eh, shi zamu yi”.

 

“Taɓ wallahi a’a, ƙazantar?”

 

Matsawa ya yi kusa da ita, ya sunkuyar da fuskarsa dai-dai tata, ta rintse ido ta kame jikinta.

 

Ya ce “Wai ke haryanzu kamar robot ki ke, ba kya jin komai ne?”

 

Ta sake kawar da kanta gefe, tana rintse ido.

 

Ya rungumota a jikinsa, ya kai fuskarsa tata.

 

“Wallahi idan ka yi mini zan yi ihu, kuma ma ba kullum nake yin brush ba, bakina wari yake” ba ƙaramar dariya ta bashi ba, gaba ɗaya ta tsorata sosai.

 

Ya girgiza kai ya ce “Ki yi girki mu tafi da shi, idan an yi sallar magariba zamu tafi” yana fita, tayi ajiyar zuciya, tana ta sauke numfashi.

Kanwar Maza Complete Novel Document Txt

***

 

Iman ce zaune a gaban Ammi, ta tattara mata hankalinta, jin ta ce mata, akwai maganar da take son su yi mai muhimmancin.

 

Ammi ta ce “Iman, Jabir ne yazo mini da wata magana, wai yana sonki, kuma nan kusa yake son ayi komai a gama, baki ji daɗin da na ji ba, kin ga shi na gida ne, kuma ya san duk halin da ake ciki”

 

Ras! Gaban Iman ya faɗi, mussaman ganin yadda ammi ke murna da al’amarin.

 

“Ya ki ka yi shiru, ba ki ce komai ba?”

 

Iman ta ce “Ammi tsoro nake ji, kin san mamansa ba za ta amince ba”

 

Ammi ta ce “Iman addu’a zamu yi, Allah ya sa ta amince ya shige mana gaba, na san babu yadda za ayi”

 

Jiki a sanyaye Iman ta ce “To Ammi” daga haka ta tashi ta tafi ɗakinta, ammi ta nuna goyon bayanta a kan lamarin, gashi ita ko kaɗan, ba ta ra’ayin Jabir, hasali ma zuciyarta na tare da wani daban, da bai san tana yi ba.

 

Mai sunan baba yana ɗakinsu yana cin abinci, yana jiyo tsalle-tsallen ruma a tsakar gida, takawa kuma yana tare da mama suna hira.

Haka kurum ya ji gabansa ya faɗi, har sai da ya ji tamkar abincin da ya haɗiya ba zai wuce ba.

A take tunaninsa ya kai kan iman, ya janyo wayarsa, ya shiga What’s app ɗin sa, sai dai ba ta online, to idan tana online ma me zai ce mata?.

 

Ya taso ya fito tsakar gida, rumaisa ta zauna ta saka Yasir a gaba, suna magana ƙasa-ƙasa.

 

“Yasir, kai ka san ta kan waya, na san kai gwani ne, hacker ne kai, hacking nake so ka yi mini”

 

Ya harareta ya ce “Ni ne hacker?”

 

“Yi haƙuri, wani abu zaka yi mini, wayarka zaka ara mini, zan haɗaka da wanda zaku yi aikin tare, sirri muke so”.

 

“Ke, bana son iskancin banza, haka kurum ki ja mini masifa, ke idan kin nemo magana mijinki zai fitar da ke, ni kuwa fa?”

 

Ruma ta ce “Ba irin wannan aikin bane, yaya usy ya san komai, tare muke shawara ma, papa zaku tayani mu taimakawa, amma bana son ya san halin da ake ciki, bari ya usy ya dawo, zan baka lambar Mahmud ɗin, ƙanin mijina ne” gyaran murya suka ji a bayansu. Ruma ta waiwaya taga mai sunan baba a tsaye.

 

Da sauri ta tashi ta ce “Laa mai sunan baba ina wuni, ban san kana nan ba ai”

 

Alama yayi mata da ta je, ta ƙarasa zuwa cikin ɗakinsu, ya kalleta ya ce “Ina yarinyar nan, ta warke?”

 

Cikin rashin fahimta ta ce “Wace yarinyar?”

 

“Ƙanwar mijinki?”

 

Ruma ta ce “Auu, Anty Iman, dama ba ta da lafiya ne?”.

 

Ya ce “Never mind, je ki kawai”.

 

“Tana lafiya ƙalau, shekaranjiya ma mun je gidan, kusan kullum idan muka je, sai ta ce mini ina yaya Umar, ko ta bani wayarta ta ce….

 

“Fita ki bani wuri” ya katseta, saboda yadda ta fara zuba.

 

Sum-sum ta fice, ya nemi wuri ya zauna, yana tuhumar kansa meye ma na tambayar rumaisa.

 

Tamkar mata, haka suka din ga shewa da Usman ya dawo, ta baje musu abincin da ta zo da shi, ta haɗu a cikinsu, suna ci.

Idan da sabo, takawa ya riga ya saba, dan haka ba ya damuwa ma yanzu, ya riga ya fuskanci irin alaƙar da ke tsakanin su, shiyasa a rashin su, take sauke masa duk wani kwandon rashin ji da take yi musu.

 

Sai ƙarfe goma suka bar gidan, suka tafi gida.

 

***

“Jamila ina cikin damuwa, wai ni Jabir zai tunkara, ba tsoro ba kunya wai yana so in bashi dama ya auri ƴar da giwa ta tsinto iman?”

 

Mummy ta ce “Ni na san wannan maganar tuni, ba wannan ne ya dameni ba, lamari ya fara jagulewa, na fuskanci kamar aikin malam na kan dutse ya fara sanyi”

 

Cikin mamaki ta kalli Mummy ta ce “Kin sani fa ki ka ce? Amma baki gaya mini ba”

 

“Ban zaci abun har zai kai haka ba, ban ɗauka da gaske zai yi maganar aure ba, amma na san ba wata matsala ba ce ba, zaki iya jajircewa a kan hana faruwar hakan”.

 

“Lallai ma jamila, ke kin fi kowa sanin, ba zan haɗa alaƙa da giwa ba, ya auri ƴar ta idan Allah ya sa ya samu sarauta, su mallake mini ɗa?”

 

“Lubabatu naki fa mai sauƙi ne, nifa abubuwa sun fara sakwarkwacewa, dole a nemo sabon boka, duk da na bayar da aikin da aka bani na ƙarshen nan, amma dole na nemi abun yi, akwai matsala”.

 

Hajiya Lubabatu ta ce “Kin ga ni yanzu bana gane komai, sai anjima ma yi magana daga baya kawai”

 

Mummy ta ce “Dole in motsa in sauya taku, ban taɓa samun matsala a abubuwan da nake ba sai a wannan karon, saboda zuwan wannan matsiyaciyar yarinyar, ƴar wannan abar daga zuwanta za ta hargitsa komai, Allah ya sa uwani ta yi abun da na sakata, yadda yakamata”.

 

Wayar Mummy ta fara ringing, ta duba taga baba Uwani ce, ta ɗaga ta ce “Ya aka yi?”.

 

Cikin kuka baba uwani ta ce “Ina cikin bala’i ranki ya daɗe, yarinyar nan wai ashe tana sane ta ce kina yi wa takawa asiri, dan ta gane idan ina kai miki maganar giwa, wallahi a sashinki ma akwai munafukinta, wallahi yarinyar nan ba yarinya ba ce aljana ce ranki ya daɗe, dan Allah kiyi wani abu a kai”.

 

A fusace Mummy ta ce ‘Kuma ki ka samu ƙwarin gwiwar kirana ki gaya mini wannan shirmen? Yayi miki kyau, ki mayar da hankali ki yi mini aikin da na saka ki, na san matakin da zan ɗauka a kanki”

 

“Na shiga uku, hajiya wani irin mataki?” Katse wayar Mummy ta yi, ta jefar a kan gado ta ce “Aikin banza”

 

**

Kamar kullum takawa ya je gaida ammi, ya tarar da kaya a ɗakinta, har da ƙaramin keke na yara.

 

Ya ce “Ammi, wannan kayan fa?”

 

“Mahmud ne ya saya wa takwaransa”

 

Har zai yi magana, da ya kalli fuskar ammi sai ya fasa.

 

Ammi ta ce “Yauwwa, ban gaya maka wani abun arziki ba”.

 

“Wane abun arzikin?”.

 

“Ina ranar da jabir ya zo, muka fita ka ke tambayata fara’ar me nake yi?”

 

Ya jinjina kai alamar ya tuna.

 

“Wata magana ya zo mini da ita, da ta faranta mini rai”

 

“Maganar me kenan?”

 

“Cewa yayi ya na son Iman, kuma aurenta zai yi”

 

Adam ya yi Jimmmm sannan ya ce “Yaushe kuma ya fara sonta?”

 

Ammi ta ce “Ban sani ba, ya ce mini dai zai je ya lallaɓa hajiya Lubabatu, ba ka ji daɗin da na ji ba, idan ta amince ai na ji daɗi, tun da ɗan gida ne, kuma na yaba da shi, jabir ɗa ne a wurina”

 

Adam jinjina kai kawai yayi, ya tashi ya ce “Bari na je wurin aiki, ina da idan na taso zan biyo, sai na dawo”

 

Ammi ta ce “Allah ya tsare”.

 

Abun ya din ga damun Adam, baya son tonawa Jabir asiri, amma sam bai dace da auren Iman ba, salihar yarinya kamar wannan, duk da kashedi da gargaɗin da yayi masa, bai ji ba, bai kuma janye maganar son auren Iman ba.

 

Ga wanccan batu da rumaisa ta ɗaukko masa a kan Jamil, gaba ɗaya sai abubuwan suka ƙara rikice masa. Sosai yake son saka pressure a kan Jamil, dan har yayi maganar da Bashir ma, sai dai gefe ɗaya yana tunanin anya haka zai yiwu kuwa? Kar ya ɓata zumuncinsu, tayaya Jamil zai saka hannu a ɓatan aisha, bayan babu wanda ya san ma ta zo ƙasar sai shi, kar ya biyewa shirirtar rumaisa ta rufta shi, amma duk da haka akwai ƙamshin gaskiya a maganganunta.

 

Ƙarfe sha biyu ya kira sidi a waya, ya ce ya je ya ɗauki rumaisa, ya mayar da ita gida.

 

Ƙarfe biyu ya tashi, daga wurin aiki, ya tafi wurin aikin su Jabir.

 

Fuskar Jabir babu yabo babu fallasa, suka gaisa.

 

“Jabir, zuwa na yi na ji dalilin da ya sanya ka je ka samu ammi, ka ce mata kana son iman, baya ka san yadda muka yi da kai?”.

 

“Tambayar da ka zo ka yi mini kenan Adam? Ka watsa komai kana neman ka ɓata zumunci, saboda kana auren wannan ƴar yarinyar, gaba ɗaya kanka ya juye, abun da ta ce kawai shi kake yi babu bincike? Ka je ka cewa Jamil yana da saka hannu a ɓatan matarka, ta yaya ƴar uwassa ce fa, ta yaya zai yi hakan? Ta ce Mummy tana yi maka asiri, magana ta koma kunnenta, ka je ka yi wa ƙannenka wulaƙanci dan su je gidanka duba ka, dan rashin ta ido, a gaban Mummy, yanzu kuma ka zo kana maganganu dan na ce zan auri Iman, kai ka san aurena da iman shine rufin asirinta, kuma ka sani Mummy sun kai ƙararka wurin mai girma wambai, dan yau da safe ya kira Ammi a waya, lallai yana nemanka, kuma zama za ayi na mussaman a kanka da matarka, dan da yiwuwar har gaban mai martaba, ba zai yiwu dan ka yi aure, ka hargitsa mana family ba.

 

Duk da gaban takawa ya faɗi, amma cikin jarumta ya ce “Jabir, gaban mai martaba ba gaban Ubangiji bane ba, daga nan a kaini duk in da aka ga dama, shi ciki da gaskiya, wuƙa ba ta taɓa huda shi” ya fita ya bar office ɗin.

 

Yanayin yadda ya zo ya wuceta a falo, ya sanya ta gane, akwai damuwa, har zata basar da shi, sai ta ji ba zata iya ba, ta bi bayansa.

 

“Papa, yau ba cin abinci, ba magana, iya sanina ban yi wani laifi ba”

 

Ya ɗan lumshe ido ya ce “Bakomai, ki je bacci zan yi”.

 

“Ba bacci ka ke ji ba, wani abu ne yake damunka”,  ta yi maganar tana murza zoben hannunsa. A hankali ya buɗe idonsa ya kalleta.

 

Ta zauna a kusa da shi, ta ce “Bari na yi maka ta Yaya usy, ya ce gist me masoyiya ya ake ciki, to gist me aboki ya ake ciki?”

 

Ita duk tsananin situation, ba ka rabata da wasa.

 

Sai ya samu kansa da gaya mata halin da ake ciki.

 

Ta kwashe da dariya ta ce “Ohh, ni ƴa su, yaro bai san wuta ba sai ya taka, to kar a fasa kaini wurin mai martaban mana, idan ban warware kowa a gabansa ba me nake, ni fa bana tsoron kowa sai Allah, kuma wallahi duk abun da na faɗa gaskiya na faɗa. Sai in faɗi komai a gaban mai martaban”.

 

Cikin rashin fahimta ya ce “Me zaki faɗa?”

 

“Ba zan gaya maka ba, daga gaya maka abu a kan Jamil ka je ka gaya masa, dama na san zuciyarka ba zata bari ka danne ba, shiyasa bana gaya maka wasu abubuwan, sai ka ɓata mini aiki, ni bana ƙwaina sai da zakara, ka san wanda ya gaya wa Mummy na ce tana yi maka asiri?”

 

Ya ce “A’a”

 

“To baba uwani ce, kuma ina sane na faɗa, dan daga ita sai ammi da iman a wurin na faɗa, baba uwani na kwasar sirrin ammi, ta je ta gaya wa Mummy. Saura kuma ka faɗa so muke mu kama ta red handed, Daddy ya tabbatar mini da ya ganta sau biyu a sashin Mummy cikin dare”.

 

A sukwane ya tashi zaune, yana kallon rumaisa kamar ya ga abun tsoro, ya fara tsorata da lamarin rumaisa, kamar wata mai rauhanai.

 

Ta tura baki ta ce “Meye kuma? Saura ka gayawa wani, idan ka faɗa ba zan sake gaya maka abu ba, yanzu in anjima mu je gida, ina son in ga Mummy, na tabattar maka da babu wanda zai wani kira ka ya tuhume ka”.

 

“Kin fara bani tsoro ne, don’t make things complicated, tayaya za ki ce baba uwani tana cin amanar mu?”

 

Rumaisa ta ce “Ai ban ce ka yarda ba dama, amma zan tabattar maka da hakan, yanzu dai zo mu ci abinci, mu yi wasan gudu a backyard, in anjima in je wurin Mummy”.

 

Ya ce “Am not in mood, je ki yi wasanki”

 

“To buɗe mini wayarka na yi game” shiru yayi mata, ya tsunduma kogin tunani.

 

Ta ɗau wayar, ta kama yatsansa ta buɗe, ta jingina da jikinsa tana dannawa.

 

Shi muma ya bita da ido, kamar mai kallon abun al’ajabi.

 

Ta gama danne-danne wayarta, ya ajiye masa ta tafi nata shagali.

 

Sai dai da ta sauka ƙasa, ta tarar baba uwani bata nan, ta tambayi su Asiya, suka ce mata tun safe ta fita ba ta dawo ba.

 

Ta tafi backyard, ta samu ball ta yi tayi, kamar ba matar ba sarake ba, ta window takawa yake hangota, yadda take sarrafa ball ɗin a ƙafarta ka san ƙanwar maza ce.

 

Da la’asar bisa kasada, takawa ya ɗau ruma suka tafi gida, suna tafe yana sake tambayar ta, me za ta cewa Mummy, ita kuma taƙi faɗa masa.

 

Ko da suka je, ya ce sai dai su shiga tare, ita kuma ta ce idan tare suka shiga, abun ba zai yiwu ba.

 

A falo ta tarar da ruƙayya tana danna remote.

 

Rumaisa cikin fara’a ta ce “Mummy tana nan ne?”.

 

Ruƙayya tayi tsaki ta ce “Wace Mummy?”.

 

“Jamila babarku”

 

“Sunan Mummyn ki ke faɗa haka?”

 

“Kin ji abun da na ji, ranar da ki ka faɗi sunan Ammi gatsal”.

 

Mummyn ce ta fito tana waya, tana ganin rumaisa ta yi turus.

 

Ruma ta gaisheta, cike da duniyanci, ta yi murmushi ta ce “Amarya ba kya laifi, yau ke ce a sashina?”

 

Ruma ta ce “Eh Mummy wurinki na zo”.

 

“To gani”

 

Ruma ta ce “Sirri zamu yi”

 

“Ba damuwa Bismillah” suka shiga wani ɗakin na daban.

 

Ruma ta ce “Mummy, na ji kin kai ƙarar papa ne, shi ne na zo na baki haƙuri, dan Allah ki janye, kar ki saka ayi taron nan, ni nayi laifin ba shi ba”.

 

Mummy ta yi murmushi ta ce “Turo ki aka yi kenan? Gara na kai ƙararku ai, dan ban san laifin da na yi muku ba, kuma taro babu fashi, dole ku je ku wanke ni”.

 

“Mummy, tayaya zan san kina yi wa papa asiri, sharri aka yi mini, baba uwani ce fa ta gaya mini, kina yi wa papa asiri”

 

A firgice ta ce “Baba uwani kuma?”.

 

“Ita, kuma ba ƙarya take yi ba, tun da na kamata da wannan ɗazu da safe” rumaisa ta yi maganar tana ɗagawa Mummy, wasu layoyi, da wasu irin abu a cikin leda.

 

“Yanzu ko dai ki janye maganganun ki, ko kuma idan aka je gaban mai martabar, zan gaya masa komai, kuma mu ma muna da CID a sashinki, wadda take kawo mana rahoto. Abun da baku sani ba shi ne, na sanku tun kan na shigo cikinku, ina kuma sake maimaita muku, tunanin maza bakwai ne a cikin kaina, da kuma nawa na takwas.

Mummy ina roƙonki, da ki jingine makaman nan, ki sassautawa mijina haka, wallahi a dalilinsa nima bani da kwanciyar hankali, muraran nake ganin abun da mutane ba sa gani a kansa, dan Allah ki bari ya huta haka.

 

READ ƘANWAR MAZA PAGE 71 HERE


Proceed with your download by clicking the below button

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button