Zamantakewar Aure

Kada Ka Sake Kayi Wadannan Abubuwan Bayan Ka Gama Saduwa Da Matarka

KADA KA SAKE KAYI WADANNAN ABUBUWAN BAYAN KA GAMA SADUWA DA MATARKA:

Da akwai wasu munanan dabi’un da akasarin maza suke yi da zaran sun gama biyan bukatansu da matansu. Wasu mazan matansu basa iya musu magana saboda kunya. Wasu kuwa ana musu amma sunki gyarawa. Wasu mazan dama matan musamman sabbin ma’aurata basu ma san abinda suke yi bama ba daidai bane.

Karanta>>> Dalillai 4 Da Suke Sawa Nonon Mace Zuwa Ba Tare Da Ta Tsufa Ba.

Ga wasu dabi’un da akasarin maza suna aikatasu da zaran sun gama jin dadin matansu da ya kamata masu yi su daina kamar haka:

1: Bingirewa Da Bacci
Akasarin maza da zaran sun kammala saduwa da matansu babu abinda suke son yi sai bacci. Gaskiya wannan dabi’ar yana cutar da mata.
Duk da yake bincike ya tabbatar da wasu dalilai dake sa maza Bingirewa bacci da zaran sun kammala Jima’i su kuwa mata idanuwansu su dawo garau. Hakan ba yana nufin bane namiji bazai yi yar hira da matarsa ba, ya yaba mata kafin ya yi bacci ba.
Wasu mazan kamin mace ta sake gyara jikinta har sun soma minshari. Wannan mummunar dabi’a ce a Jima’ince.

Karanta>>> Sirrin Gyaran Nono Ga Budurwa Da Matar Aure Kashi Na Uku

2: Wasa Da Waya:


Wasu mazan ba bacci suke komawa ba, amma suna kammala saduwa da matansu zasu dauko wayarsu ko su kunna TV su soma danne danne ko kallo, kiran waya ko kuma wasan game sun manta da matansu kamar basu ne suke ta ihu da sumbatun dadi ba, mintuna kalilan baya ba?
A gaskiya hakan bai dace ba. Koda namiji yana da wani uzurin yin waya ya tabbatar a wannan lokacin da yake wayan matarsa na jikinsa suna hira ko wasanni domin nuna mata mahimmancin ta.

Karanta>>> Sirrin Gyaran Nono Ga Budurwa Da Matar Aure Kashi Na Daya

 

3: Juya Mata Baya:


Akwai kuma wasu mazan da suna kammala saduwa da matansu kawai sai su juya masu baya. Tana kallon gabas yana kallon yamma.Wannan ba dabi’ar miji na kwarai bane.
Duk mace tana so mijinta na samun gamsuwa da ita sai ya rumgumeta har bacci ya sace su yana mata hira.

Karanta>>> Abubuwa 9 Dake Da Tasiri A Yayin Kwanciyar Aure.

4: Saurin Shiga Wanka Ko Maida Kaya A Jiki:
Wadannan dabi’un guda biyu da zaran namiji ya gama saduwa da matarsa tamkar yana nuna mata ne ya gamsu da ita ba tare da neman bayani daga bakinta ko tana bukatan kari ba.
Shi wanka musamman da ruwan sanyi yana kara kwantarwa namiji sha’awa ne. Shi yasa masana suka bada shawara duk namijin da yake son zuwa zango na biyu to kada yayi tsarki da ruwan sanyi sai na dumi.
Haka shima saurin maida kayanka a jikinka zai sa sha’awar da matarka take da shi na a sake tushi ya kau saboda ganinka cikin mayafi babu kaya yakan sata azama.
Don haka duk mazan da suke saurin shiga wanka, ko maida kaya a jikinsu ba tare da neman Izzinin matansu ba su daina.

Karanta>>>Yadda Ake Hadin Tsumi Mai Motsa Sha’awa Da Karin Ni’ima.

5: Korarta:
Musamman ma’auratan da ba daki guda suke kwana ba. Inda namiji yana gamsuwa kawai zai cewa matarsa ta tashi ta koma dakinta ta kwanta. Gaskiya wannan ba dabi’a mai kyau bane wajen magidanci na kwarai.

Karanta>>> Nau’in Abinci Da Ba’a So A Ci Lokacin Da Za’a Yi Jima’i

6: Shan Taba:
Musamman ‘yan sigari ko wiwi. Suna kammala saduwa da matansu suke banka musu wuta. Wannan bayan cutar da matarka da kake yi wacce a wannan lokacin tana so ta ci gaba da shan bakinka. Haka kuma zai kwantar maka da sha’awa koda matarka na son kuje Karaye baza ka iya ba

Karanta>>>  Ingantaccen Matsi Da Bashi Da Illa, Kuma Da Kanki Zaki Hadashi.

7: Hattararta:
Kila a lokacinda kuke tsaka da jin dadi ta yi wani abu ko tace wani abu da bai yi maka dadi ba, don haka kuna gama Jima’i sai ka hau hattaranta. Wannan ba dai-dai bane. Idan ba tsoro ba mai yasa a lokacin baka yi fushi ka fasa Jima’i ba sai da kuka gama zaka ce zaka mata masifa.

Karanta>>> Abubuwa 9 Dake Da Tasiri A Yayin Kwanciyar Aure.

8: Dauko Zancen Da Zai Bata Mata Rai-:
Wasu mazan suna dawowa gida ne da wata kullelliya a zuciyarsu. Amma domin kada su soma da maganan hakan ya jawo a hanasu Bado. Sai su bari sai sun gama gamsuwa sai su taso da zancen domin batawa matansu rai tunda yanzu bukata ta biya.
Hakan ba daidai bane. Shi wannan lokacin na nishadi ne da soyaya bana batawa juna rai bane.

KARANTA>>> CIKAKKEN BAYANI DANGANE DA SAURIN INZALIN

 

9: Kada Ka Nuna Mata Gazawar Ta:


Ana samun wasu mazan da zaran mace ta gaza a wani yanayi na saduwa ko ta yiwa miji wani abu da bai ji dadi ba, sai ya bijiro da zancen nan take.
Kada ka gwasale matarka nan take idan ta gaza a wani yanayi ko aikata kuskure a yayin da kuke Jima’i.
Irin wadannan zantukan ana yinsu ne kamin a gudanar da Jima’i na gaba sai a tattauna Jima’in da aka gudanar a baya domin kiyayewa

Karanta>>> Amfanin Kubewa Musamman Ga Ma’aurata

10: Neman Abinci Nan Take:
Tabbas ana iya jin yinwa bayan an gudanar da Jima’i. Don haka ana iya sake bukatan cin wani abincin. Amma dai ba anan take ba.
Yana da kyau maigida ya bari sai sun gama jin dumin juna. Sun gama yabon juna. Sun yiwa juna godiya sannan daga bisani a nemi abinci amma ba haka kawai kana gama CIN MATARKA sai kawai ka nemi cin abinci ba😒

Wadannan sune wasu daga cikin abubuwan kiyayewa da zaran maza sun kammala saduwa da matansu.
Da fatan maza zasu daure su gyara wadannan mugayen dabi’un da suke aikatasu bayan Jima’i da basu dace ba kuma hakan na kuntatawa matayensu.
✍️

Karanta>>> Maganin Kowacce Irin Cuta Da Izinin Allah.

Back to top button