Page 61
Adam yayi ta maza ya ce “Au dama kina nan? Mun wuce su mama a falo ban ganki ba ai”.
Cikin matsanancin takaici ta ce “Meye na borin kunya kuma? Ai ba ka so ka ganni ɗin ba ne? Tun da har ka shiga ta falo, ka biyo ta nan za ka tafi”.
Rumaisa ba ta kula Samha ba, dan ba zata manta fuskar ta ba, ta mayar da hankali wurin tsinkar furanni da ke wurin, sai dai tana jin duk abun da suke faɗa.
“Yanzu da ma adam a kan wannan abar ka wulaƙanta ni, ka ƙi ka aureni? Yanzu wannan abar wani abu ta fi ni da shi, yarinyar da ba ta kai a kirata mace ba ma, an ya ka yi mini adalci kenan? Soyayyar da na nuna maka tsawon shekaru shikenan ba ni da wata makoma?”
“To ni idan ba mace ba mace ba ce, namiji ce ni?” Rumaisa ta yi maganar tana riƙe ƙugunta.
Adam ya kalli rumaisa ya ce “Wuce ki je mota ki jirani”
“To saman motar zan hau ko ƙarƙashin tayoyi? Tun da a rufe take”.
“Duk in da ya yi miki” kallon banza ta yi wa samha ta wuce.
Samha tana ta tunanin a ina ta san fuskar rumaisa ma, ta kasa tunawa, ta ma fi cika ido a hotunan bikinsu, a zahiri kuwa ƙwaila ce ta gaske.
“Yanzu abun da ki ka yi kin kyauta Samha? Da auren wuri aka yi miki, ko baki haifeta ba kin kusa, wannan ai salon ki janyo wa kanki raini ne”.
“Ban damu ba adam, ba raini ne a gabana ko akasin haka ba, ni batun soyayyaya ta ce a gabana, wallahi ka cutar da ni Adam”.
Adam ya ɗan yi shiru, sannan ya ce “Ban cutar da ke ba Samha, abun da nake son ki gane shi ne, komai muƙadarri ne na Allah. Daga haɗuwata da rumaisa, zuwa lokacin da na aureta, da zan gaya miki zaki gane aurena da ita ƙaddarar Allah ce”.
“Ba ka son ta kenan?”
“Ba zan ce eh ba, kuma ba zan ce a’a ba, ki yi haƙuri ki cigaba da addu’a, idan da rabo sai in aureki, idan kuma babu ko yi haƙuri, ki auri wani, kar ki ce zaki cigaba da zaman jirana samha”.
Rumaisa kuwa ranta a ɓace, ta ƙarasa in da motarsu take, tana zuwa ta ga Jamil da Jabir a tsaye a wurin suna magana, ba ta kula su ba ta tsaya, tana hura hanci.
Jamil ya ƙarewa rumaisa kallo ya ce “Lallai, Adam sai ka ce makaho, dan Allah ina mamora a tare da wannan yarinyar? Me wanna za ta tsinana masa a zaman aure? Yanzu wannan ya zaɓa ya bar Samha? Saboda wannan abar?”.
Jabir ya ce “Kai ba ka san komai ba ai, ba ta da kunya ne yarinyar nake gaya maka, kai ka ga wahalar da ta din ga bashi, ka san ita ta dawo da jaririn fulani, kan ta faɗi fulanin ma ta rasu, sai da aka kai ruwa rana, ba ta da kunya”
Zabura Jamil ya yi ya ce “Kana nufin da gaske wannan yarinyar ce, ta dawo da yaron wurin aisha?”.
Jabir ya ce “Tambayeta ka ji”
Juya musu ƙeya rumaisa ta yi, tana wasa da ƙasa da ƙafarta.
“Ke, da gaske kin ga fulani, kin ganta a hannun ƴan bindiga, suwaye? Ya aka yi suka kasheta?” Yayi maganar cikin rikicewa yana kallon rumaisa,ya na jin tamkar yanzu A’isha ta rasu.
Ɗaga kai Rumaisa ta yi ta kalleshi, ta yi guntun tsaki.
“Magana nake yi miki, aisha ƙanwata ce, jami’in tsaro ne ni, ki gaya mini abun da ya faru, ko kuma ƙarya ne kawai haɗin baki ne?” Yayi maganar kamar zai kaiwa rumaisa duka.
Sheƙeƙe rumaisa ta ce “To mijinta ma shi Adam ɗin ban gaya masa komai ba, balle wani kai, ba ruwanka da ni kuma, wallahi ka sake ce mini wannan abar, sai na yi maka rashin mutunci, mai na yi muku, ni na ce kar ya auretan? Wannan masifaffiyar matar na na ɗauka ma babar wasu ce”.
Daga nesa da ya tunkaro su, ya hangi rumaisa tana zazzaga masifa, Jabir ya riƙe hannun Jamil, ya ce kar ya yi magana.
Adam ya ƙaraso ya ce “Lafiya kuwa?”
Rumaisa ta ce “Ce mini yayi wai wannan abar, ni na ce kar ka auri waccan matar, da za su din ga ce mini wai wannan abar, shi kuma wannan har da ce mini mara kunya, me na yi masa na rashin kunya”.
Adam ya buɗe motar, ya ce wa rumaisa “Shiga ki jirani”
Buɗe motar ta yi ta shiga ta zauna, tana cigaba da tura baki.
Adam ya kalli Jamil ya ce “Sannu Jamil, kirkin ka har ya yi yawa, shikenan ita rayuwa ba za a karɓi ƙaddara ba, ka ƙi halartar ɗaurin aurena, kuma ka ƙi yi mini Allah ya sanya alkhairi”.
“Allah sanya alkhairi saboda ka auri wannan abar?” Yayi maganar yana nuna motar adam.
Adam ya sauke hannun Jamil ya ce “Ko dan albarkacina, yakamata ka tausasa harshe a kan ta, matata ce, kuma bana son zumuncinmu ya samu matsala saboda son zukatanmu”.
Jamil ya ce “Adam ka na da ƙwarin gwiwar yin wannan maganar? Dama yarinyar nan ita ce ta zo da jaririn aisha, ka ce aisha a hannun ‘yan bindiga ta mutu, ya aka yi ita ta kuɓuta, wani mataki ka ɗauka, na san dole ba za a rasa wani information daga bakinta ba, menene dalilinka na ɓoye mana?”.
Nan da nan Adam ya hasala ya ce “Kai ma kana zargin ni na kashe fulani na yi tsafi da gawarta ko? To na yi, idan wani bayani ka ke da buƙatar ji daga bakinta, ka je ka tambayi mai girma turaki”.
Cikin sauri Jabir ya ce “Jamil, bai kamata ka faɗi irin wannan maganganun ba, da na san haka abun zai zama, da ban gaya maka ba, takawa dan Allah ka yi haƙuri”
Bai ko tsaya ba, ya wuce mota, ya buɗe ya shiga, zuciyarsa na yi masa wani irin zafi.
Sai da suka ɗan yi nisa sannan ya cewa rumaisa me suka ce miki?.
“Su wa?” Kallonta yayi, ta ga alamar babu wasa a idonsa, ta ce “Tambayata yayi, wai ya aka yi na san anty aisha, ni kuma na ce ban sani ba”
Jinjina kai kawai ya yi, ya cigaba da tuƙinsa.
Wani store yayi parking, ya ce ta fito su shiga. Ta fita ta bishi tana kallon wurin.
Suka je ɓangaren jakunkuna ya ce ta zaɓi jakar makaranta.
Haushi ne ya kamata, dan ko zancen makaranta ba ta so.
Ya sai mata kayan karatu da rubutu, da takalma, jakar ma uku ya saya mata, sannan ya sakata a mota suka tafi.
Gidajen ƴan uwansu ya din ga zagayawa da ita, suna gaishe su, sai dai rumaisa ta ƙule da yadda wasu suke karɓarta, tare da nuna ita yarinya ce, ta yi masa ƙarama da aure.
Babu wanda ya sake ƙona mata rai, kamar hajiya Lubabatu, wato mahaifiyar Jabir, matar Galadima mai ci a yanzu.
Ban da tana ganin girman matar, ta yi sa’ar mama, da babu abun da zai hana ta zageta, dan ma Adam yana ta kareta, amma matar ta ci zarafinta, duk da bakomai take fahimta ba.
“Ragowar ƴan bindiga aka kawo mini kenan, lallai takawa, ka yi jihadi sai fatan Allah ya biya ka”.
Adam ya ce “Ba ragowa ba ce ba, kuma aurenta ba ni na yi jihadi ba, ita ta yi, tun da kun san waye ɗanku, amma ta amince da aurensa”.
Hajiya Lubabatu ta yi dariya ta ce “Yo ba dole ba, ai ko a turu kake ɗan mu yana da arziki da sarautar da za a aure shi domin sa, kuma a zauna da shi, kwaɗayin abun duniya ne kawai”.
Ba dan Ammi ta matsa, lallai ya zagaya da rumaisa, ya nuna mata familynsa ba, ya kuma yi musu bangajiya ba, da babu abun da zai sanya ya zo gidansu Jabir, wurin mahaifiyarsa.
Adam ya ce “To Hajiya, ina ga bari mu koma, akwai in da zamu je”.
“Ahh haba dai, na saka a ɗora muku girki ai”.
“A’a Alhamdilillah, a ƙoshe muke”.
Hajiya Lubabatu ta ce “Gaskiya ban ji daɗin wannan zuwan ba, yakamata a kawo mana ita ta wuni, da haka tana shiga cikinmu, za ta san yadda matan sarakai suke rayuwa, dan na san ba sani ta yi ba”.
Adam ya ce “Bakomai ana koya mata”
Wata hadimar Hajiya Lubabatu ta ƙaraso, ta bawa hajiyar wata leda. Ta karɓa ta miƙawa rumaisa ta ce “Amarya ga wannan ba yawa, kya sai tsintsiya, sai na sake kawo ziyara, tun da rabona da gidan, tun washegarin kai ki, mun ce a bamu ƙyalle mu tabattar da abun da aka auro mana, an yi mana wala wala”.
Rumaisa ta sha kunu, ta ƙi karɓar ledar.
“Ki karɓa mana” rumaisa ta girgiza kai ta ce “A’a”
Hajiya Lubabatu ta ce “Takawa, ba ka gaya mata, masarauta ba ma kyauta ace a’a ba, rayuwar masarauta, ba kamar ta sauran gama garin mutane ba ce”.
Ya kalli rumaisa da ke kusa da shi ya ce “Ki karɓa, ba a mayar da kyautar matan sarakai”.
“Bana so” ta faɗa yadda shi kawai zai ji.
Ya saka hannu ya karɓi ledar ya ce “Godiya take, kin san amaryat ta wa akwai jan aji, da gudun raini, kyauta ko da ga ni take, sai ta tantance, gaku sarakai, amma ta fi ku sarauta” yayi maganar a baibai, cike da mayarwa da Hajiya Lubabatu martani.
“Ikon Allah, da alama auren haɗi zai koma na soyayya, ai labarin zuciya a tambayi fuska takawa”.
Adam ya ce “Eh to, ba zan musa miki ba, amma hausawa suka ce ɗan hakin da ka raina..”
Murmushi kawai hajiya Lubabatu ta yi, tana yi musu su gaida gida. Rumaisa tuni ta yi waje, dan idan ta cigaba da tsayuwa, matar nan tana washe baki, tana gaya mata magana, ba abun da zai hana ta zageta.
Shi kansa adam mood ɗin rumaisa ya gani, ya san a ƙule take kamar ta fashe dan takaici, la’asar ta riga ta yi sosai, ya ga idan suka koma gida, shi ficewa zai yi, ya san zama za ta yi, tayi ta ƙunci a gidan, dan haka ya wuce da ita da ita gida.
Ammi ba ta nan, sai Nusaiba da Iman, da kuma Sabir, ganin Sabir ya sanya ya manta wani ɓangare, na fushin da take yi.
Ba ta fiye shiri da Nusaiba ba, ta fi yi da Iman, dan haka da ita suke ta hirarasu.
Iman ta saka aka kawo musu abinci, nan iman take bata labarin, bayan ta dawo gida mai sunan baba ya kirata, ya ga missed calls ɗin ta, a lokacin take gaya mata, yadda suka yi da shi, da ta kira shi tana tambayar sa, ina take.
Ruma ta din ga dariya ya ce “Baban mama, sa ba ka dariya sai hamma, kirarin da mama ke yi masa kenan, shi dai kar a raina shi”.
Iman ta ce “Anty rumaisa gara haka fa, ina son in ga namiji mai aji, rashin kintsi ko ga namiji bai yi ba ai”. Suka cigaba da dariya, iman na nunawa rumaisa hotunan biki.
Nusaiba kuwa kallon iman take, yadda fuskarta take nuna jin daɗin hirar mai sunan baba da suke yi.
Nusaiba a ranta ta ce “Iman, wannan ba irin mutumin da ya dace ki so bane, ya fiye zafi, larurarki kuma tausasawa take buƙata, kuma wataƙila ba zai amince da ke ba, idan ya san ke wacece, uncle J ɗin dai, shi ya san k wacece, shi zai iya zama da ke, wannan wahalar sarrafawa zai yi miki’.
Ana idar da sallar magariba, Adam ya dawo, ya ce rumaisa ta tashi su tafi, ta ce ya bari ta ga ammi, ya ce a’a so yake ya je je ya huta, haka ta tashi ta bishi, sai dai suna barin gidan, ta tuna abun da ya faru yau, ta ji ɓacin ran ya dawo mata.
Ko da suka je gida, baba uwani ce ta fito tana yi musu maraba, sauran hadiman sam ba sa abun da take yi, rumaisa har mamaki take yi, kawai yau sai ta din ga ganin dariyar baba uwani, kamar dariyar hajiya Lubabatu da ta din ga yi musu ɗazu, tana yi musu dariya, kuma tana ci mata mutunci.
A ƙasan benen ta bar shi, shi da baba uwani, ta hau saman benen ta wuce ɗakinta, ta shiga banɗaki, ta duba pad ɗin jikinta, tana fatan ta ga babu komai, dan ta gaji da zubar da jinin yake yi, amma ta ga ɗan kaɗan, kuma adam ya ce mata, idan ba ta saka, ta ga babu abun da ya zuba a kai ba, kar ta kuskura ta ce za ta yi salla, dan kamata yayi tana salla washegarin da period ɗin ya zo mata.
Ta yi wanka, ta canza wata, ta saka kayan barcinta ƴar rigarta sai wando, ta hau kan gado ta baje, dan ta gaji.
Ba ta yi tsammani ba, bacci ya yi awon gaba da ita.
Washegari da safe, rumaisa da kanta ta sauka kitchen ɗin ƙasa, ta tarar da barira da Asiya, suna aikace-aikace.
Suka hau gaida rumaisa ta ce “Ni fa ku daina gaishe ni dan Allah, kunya ku ke bani, doya zan ɗauka”.
Asiya ta ce “Wani abun za a girka miki ranki ya daɗe”.
Ta ce “A’a, ni zan yi da kaina.
Ta ɗauki abun da take so, ta koma.
Ta yi ta gyare-gyaren ta, sai dai abubuwan da suka faru jiya, suka cigaba da damunta.
Ta saba Adam da wuri yake tashi ya fita, ta samu ta gyara ɗakin, amma ta ji shi shiru. Dan haka kai tsaye ta nufi ɗakinsa ta shiga babu ko sallama.
Sai dai tozali ta yi da shi a tsaye, daga shi sai gajeren wando, ya ajiye towel a gefen gado alama wanka zai shiga.
Ta kawar da kanta gefe ta ce “Ka saka kayanka, zan yi gyaran ɗaki, ko ka fito waje, idan kuma ka yafe shikenan”.
Girgiza kai kawai ya yi, ya ce “Zo ki gyara”.
Kanta a ƙasa ta shiga, ta fara kwashe kayan duk da ya barbaza tana mita. “Wai sai ka ce wani Sabir, komai sai ka watsar da shi” bai ce mata uffan ba, ta cigaba da mita.
“Ga kuɗinki nan a kan mudubi, 100k ne, hajiya Lubabatu ta baki jiya”.
“Allah ya kiyaye, ba abun da zan yi da su, ka ɗauke ni ka kaini, ana ci mini mutunci, amma nayi-nayi ka ƙi ka kaini gidanmu na ga mama. Wallahi matar nan ba dan ta kusa zama tsohuwa ba, babba ce da sai na yi mata rashin mutunci, ina fa gane baƙar magana, shi ma wannan Jabiru yake da wannan ɗayan, suka din ga ce mini wannan abar. Ni na tsani wannan jabir ɗin, shi kuma ɗayan mai kama da mugwaye. Ita kuma wannan matar har da ce wa, wai ni ba mace ba ce, Hansai take ko Hasana, duk kana ji ana ci mini mutunci.
Ta manta ai ni dama ƙanwar maza ce, a namiji aka haifeni, sai da ga baya da na fara girma aka lura ashe ni mace ce, ni na ce kar ka aureta da za a din ga zagina? to wallahi ba ruwana da wata masarauta, duk wanda ya yi mini, sai na rama, a wayance matar nan ita ma tana nufin, ni ƴar talakawa ce na aureka saboda kana da kuɗi fa take nufi, ba ta san taimaka wa na yi na aureka, saboda ammi ba da kuma Sabir” sosai take masifa, domin dama, dama take son ta samu ta amayar da abun da yake ranta.
Takowa ya yi zuwa gabanta, tana tsaye a gaban mudubi, sai iya shege take yi, tana masifa.
Sai kuma tsoro yakamata,ba yau ta saba ganin namiji ba riga ba, idan da sabo ta saba a gida, amma ganin adam a haka, ya sanya take jin, tamkar ta aikata wani jibgegen saɓo.
“Ke dama mace ce nan a haka?” Ai ba ta san lokacin da ta ɗago ta kalleshi ba.
Ya janyota gaban mudubin sosai ya, ya cire hular kanta, gashin nan na ta baƙi wuluk, ta yi parking ɗin sa. ya ce “Wannan ɗan gashin naki ne kawai zai sa a san ne ba namiji ba ce ba, kamar namijin haka ki ke ai, taimakawa na yi na aureki, dan ba yadda zan iya, amma kalleki fa sosai a mudubi” yayi maganar yana nunata a cikin mudubi.
Ɗaga kai ta yi tana kallonsa.
Ya ce “Eh mana, ke ba kwalliya ba, ke dai gaki nan, behaviors ɗinki ma na mazan ya rinjayi na matan. Wasiƙar da ki ka rubuta mini, ki ka ce na taɓa miki nono ni ban gansu ba ai.
Kawai da ma sharrinki ne, abun bai fi girman wake ba, wata ƙwaila da ke, ai ba ƙarya aka yi ba, dole kowa ya tausaya mini, look at you.
Da ma na ce nawa sun fi naki baki yadda ba, look at me, bai fi naki ba?” Yayi maganar yana shafa ƙirjinsa.
Rumaisa ji ta yi tamakar ƙasa ta tsage ta nutse, sai ta nemi duk wasu kalaman rashin kunya, da fitsararta, ta rasa, ta rasa me ma za ta yi, ta saka hannu ɗaya ta rufe ƙirjinta, ɗaya kuma ta rufe fuskarta.
“Meye a wurin da ki ke rufewa, abu fayau kamar filin ball, ni aure zan yi nan gaba kaɗan, dan da gaskiyarsu, ba mace ba ce ke, haryanzu dai namijin ce, ba a gama tantancewa ba, macen ce ko namiji, ga rashin kunya, ga fitsara da faɗan tsiya, duk ke kaɗai, ba zan iya ɗauka ba da wanne zan ji?”.
Dummmm haka rumaisa ta ji maganar, jin ya ce wai zai ƙara aure, saboda ba ta da nono, idan ba batsa ba, meye haɗin sa da wannan abu?.
Gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, ta ma rasaa wani muhallin, yakamata ta ajiye wannan maganganun da adam yake yi mata, ba tare da kunya ko tsoro ba.
Ya kuma haɗe rai ya ce “Wuce toilet ki haɗa mini ruwan wanka”
“Ruwan wanka kuma sai ka ce wata baiwa?”.
“Ba zaki wuce ba kenan?”
Kamar ta saka ihu, haka ta tafi tana ƙunƙuni, ya bi bayanta, ta shiga banɗakin, sai dai ba ta san yana ƙofa a tsaye ba.
A Tsakiya banɗakin ta tsaya, ta riƙe ƙugu, cikin ƙwalla ta ce “Lallai ma, wai ni rumaisa ake yi wa wannan abubuwan, wallahi da sake”. Idonta ya sauka a kan toothpaste ɗin da adam yake amfani da shi, a wani tube mai kyan gaske.
Ta ɗauka ta buɗe, ta lakata ta saka a bakinta. “Dan mugunta ni ya bani mai yaji, shi kuma nasa mai zaƙi, saboda ga wadda dauɗa ta kashewa haƙora, ban yafe ba duk abun da yake mini”.
Da maganganun da take, da toothpaste ɗin da take sha, duk yana kallonta, ta ajiye ta nufi bath ɗin.
Nan ma wata mitar take yi “Wato ma kawai an kawo masa baiwa, na yi gyaran ɗaki, ya ci abinci na yi wanke-wanke, kuma wai ni zan haɗa masa ruwan wanka, ga shower ya kunna ya yi wankan, amma ba zai iya ba, ko da waye yake haɗa masa ruwan oho? Zai ga tsiya, wallahi ruwan zafi zan haɗa, idan ya ƙone gobe ba zai kuma sakani ba. Saboda tsabar wulaƙanci, mutumin nan ma bashi da kunya, kuma ammi ba ta san yana yin maganganun batsa ba, a haka kamar na Allah, kuma da alama ba ya yi wa kowa sai ni, to wallahi ni ina da tarbiyya “.
Ta din ga surutu a banɗaki, kuma ko da wasa ba ta waiwaya ba, balle ta ganshi, ta kunna ruwan zafi, fiye da rabin bath ɗin nan, sannan ta kunna na sanyi, ruwan sai tururi yake yi, ta ce “Allah ya sa yana zuwa kawai ya shiga, gobe ba ya kuma sakani aiki ba, bayan ya gama ci mini mutunci”.
Ji ta yi an rufe ƙofar banɗakin, da sauri ta tashi ta waiwaya tana kallonsa.
Ya shigo kamar zai wuce ta, ya shammaceta, ya danƙota, ya shiga cikin bath ɗin da ita.
Ihu ta kurma, jin zafin ruwan, ga kayan jikinta nylon ne, ya sanya yatsansa a kan leɓensa ya ce “Shhhhh, ai gara mu ƙone tare”.
Kiciniyar tashi ta hau yi, amma ya riƙe ta sosai a jikinsa, ya din ga ɗibar ruwan, yana zuba mata a kanta.
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.