Fatalwar Delu Part 14
🤡 FATALWAR DELU 🤡
Part 14
Kingboy Isah 👑
Short story
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
Yinin ranar mun yi shi ne a nan gidan Mai Gari don a cewarsu idan aka bar mu muka tafi, ba ko shakka Bukar zai iya gudu wa ya bar gari. Nima na amince da hakan dan ko ba komai ya kamata yau dai a kawo karshen rigimar nan da Fatalwa Delu muje Bukar bata hakuri kowa ya huta, shi kuwa boka tuni ya tafi gida a cewar sa zai je ya shirya. Idan dare yayi mu biya ta gidan shi idan ya gama shirin sai mu fita dajin tare. A lokacin da labari ya kai wajen iyayen Bukar, nan take suka nufi gidan mai gari cike da tashin hankali, domin mahaifiyarsa sai kuka take a cewar ta za’a kashe mata yaro ne kawai. Ko da suka zo gidan mai gari babu irin roko da magayi da bata yiwa Mai Gari ba a kan ya kyale mata yaro amma Mai Gari yay ta lallashinsu yana nuna musu fa’idar rabuwa da wannan Annoba ta Fatalwa Delu. A cewarsa idan Bukar yayi sanadiyar rabuwar garin da annobar Fatalwa Delu tabbas ya zama abin alfahari ga dukkan mutanen kauyen, kuma sunanshi dole ne ya shiga cikin tarihin garin, wanda za’a rika tunawa nan da daruruwan shekaru masu zuwa.
Ganin Mai Gari yaki sauraren su ne yasa suka juyo gare ni, mahaifin Bukar ya ce, “Nura sanin kanka ne abokinka Bukar shi kadai muke da shi da namiji Babba, sauran yan uwansa duk mata ne. Rokona a gareka shine dan Allah karka yarda wani abu ya sameshi, ni dai yanzu na damka amanarsa a gareka”. Yana fadar haka naji zuciyata ta karaya, amma sai na jure na ce, “Ba komai Baba na maka alkawarin insha Allah yadda mukaje lafiya haka zamu dawo lafiya”. Sun dade a nan kafin suka wuce gida. Da dare bayan munyi sallar isha’i mun ci abinci, mai gari da wasu jama’ar fadar mai garin sune suka raka mu har gidan boka dake bayan gari sannan suka jiyo a cewarsu kar karfe 9 ta samesu a hanya gwara suyi gaggawar komawa. Nan take na fara haska gidan na boka Girgije wanda muke tsaye a tsakar gida da alamu shi yana cikin daki, gidan zana ne sai bukka daya, a can gefe akwai wajen da aka zagaye da zana ina kyautata zaton nan ne bandakinsa.
Babu komai a gidan sai tarkacen hauka, kwarangwal ne kala-kala na dabobi, sai wasu fatocin dabbobi suma da aka rarrataye a gefen bukkar tashi. A saman murfin bukkar kuwa duk ya daura wasu matattun abubuwa da suka fi kama da beraye da su gafiya. Ganin mun dade tsaye boka bai fito ba na dubi Bukar hade da cewa, “Bukar kayi wa bokan nan magana mana, ya fito mu san abin yi”. Shiru na ji yayi bai ko tanka ba, da na haskashi sai na ga yana hararata, kadan ta hana inyi dariya, na tabbata Bukar ba karamin haushi na yake ji ba. Dakin Bokan na nufa ina fadin, “Sallamu Alaikum Boka-Boka Girgije”. Daga can naji ya kwala ihu hade da cewa, “Kai ba’a mana sallama a nan, idan bakayi wasa ba yanzu zan saka aljani yayi ma aski da kwalba, ba’a mana wargi a nan, ku zauna a nan idan na gama shiri zan fito”.
Tsaki na ja yayin da na haska wani dan kututuren icce na nufeshi domin in zauna, a zuciya ina tunanin raini irin na bokan nan, wai har ni zaiyiwa barazana da aljani, lalai baisan ko ni waye ba. Bukar ma ganin tsayuwar ta isheshi yasa ya zo ta inda nake ya zauna, har lokacin yaki yi min magana sai dai yayi kwafa yaja tsaki, fitilar hannunsa kuwa ya hasketa fayau yaki kashewa, sai kace idan ya kashe wani abu zai zo ya kamashi. Fitilun sabbi ne masu shegen haske mai gari ya bani daya ya ba Bukar daya duk a cikin guzurin tafiya. Muna nan zaune dai Bukar duk a tsorace yake ganin dare yayi, gashi gidan bokan baya da maraba da waje, domin zanan da ya zagaye gidan baya hana na waje hango na ciki, haka zalika wanda ke ciki yana ganin mutanen waje. Da Bukar yaji motsi ko yaya ne sai in ga yayi saurin haska wajen, ganin Boka ya shanyamu a wajen yaki fitowa yasa na daga murya hade da cewa, “Boka ka fito mu tafi dare yana kara yi”. Shiru baiyi magana ba.
Hakan ce ta fusata ni na tashi na nufi dakin ina fadin, “Bari na ga abinda yake a cikin wannan tsukakkiyar bukkar”. Kai tsaye na kutsa kai cikin yar bukkar, ai kuwa Bukar yana ganin an barshi shi kadai ya saka kara hade da tashi ya bini dakin a guje. Muna shiga muka tarar da Boka Girgije zaune tsakar dakin babu riga a jikinsa sai wani jan wando dogo, kanshi ya daura jan kyalle, yayinda a fuska kuma yayi wani kwale da farin alli. Ya saka kaskon wuta gaba idanunsa a rufe amma bakinsa yana motsi jefi-jefi yana daukar wani gari a cikin bakar leda yana zubawa a cikin wutar. Kare masa kallo nayi daga sama har kasa sannan na shiga kallon yar bukkar tashi wacce babu komai sai tarkacen layoyi da itatuwan magunguna, sai gefe shimfidaddiyar katifa da aka ajiye kan tabarma saman katifar akwai zanan gado da bargo da filo. “Ranka shi dade Boka Girgije kai muke jira fa dare yana yi gwara mu gaggauta mu tafi”.
Na fada ina kallonsa, amma shiru bai ko bude ido ba balle in sa ran zaiyi magana, mun dade a tsaye ganin baya shirin yin magana na nufi wajen katifarsa ina fadin, “Kai wallahi na gaji da tsayuwar nan, Bukar zo mu dan zauna a katifar nan kafin ya gama”. Ina gaf da zama yayin da shi kuma Bukar ya yunkura zai taho sai ji mukayi Boka Girgije yace, “Karka kuskura ka danna jaririn aljana yar baka, yanzun nan ka jawa kanka bala’i”. Ya fadi yana nunani da yatsa, ni kuwa lokacin ina gaf da zama don haka ban ja birki ba na idasa zama, shi kuwa Bukar jin an ambaci aljana ya sa shi juyawa baya da sauri ya nufi kofar fita. Boka ya ce, “Maza ka tashi karka danne mata jariri Aljana Yar Baka bata da mutunci”. Juyawa nayi ina kallon saman katifar wayam ba komai, don haka na ce, “Gaskiya boka zaman nan da nayi idan ka ga na tashi to ka gama shirinka zamu tafi ne, saboda na gaji da tsuwa”. “Kai yaro baka jin magana ko? Kai fitsararre ne marar jin magana ko? Tabbas aljannu zasuyi maganinka”. Ya fada hade da juyawa ya cigaba da abinda yake, Bukar kuwa cike da tsoro ya ce, “Nura wai kai me yasa ka cika taurin kai ne? A nan ma so kake ka ja mana wasu aljannun kuma”. Boka Girgije ya dubi Bukar ya daga masa hannu hade da cewa, “Rabu da shi yaro da ni yake zancen”. Ni dai ban ce musu kala ba na gyara zama a katifar na cigaba da dube-duben dakin.
Muna nan wasa-wasa har na fara jin bacci boka baya da niyar kammala abinda yake balle muyi shirin tafiya, Bukar ma har ya gaji da tsayuwa ya zauna ya fara gyangyadi. A hankali na sulale a kan katifar Boka ina danna waya daga bisani kuma bacci yayi awon gaba da ni. Can tsakar dare na farka, na haska fitila saboda na ga duhu a dakin, Boka na gani kwance tsakar daki ya ja bargo yayi filo da shi, kanskon wutar da yake zuba magani tuni ya mutu, Bukar ma ya jingina da bango sai sharar bacci yake. Wayata na lalibo na kalli agogo karfe biyu da rabi, don haka na shiga tafa hannu ina tashin su Boka, da kyar suka tashi Boka na hararata yana murguda baki. “Ranka ya dade Boka ai na zata idan ka gama shirin zaka tayar dani shiyasa ma na fara bacci, gashi na farka naga kaima kana bacci ko dai ka fasa rakamu wajen nan ne?”. Boka ya nuna ni da yatsa yana fadin, “Kai dai wannan yaron ba karamin taurin kai gareka ba, tun zuwanku gidan nan nake muku hannunka mai sanda a kan zuwa wajen nan, Fatalwa Delu bata da imani bana so ku kai kanku mahallaka amma kai kaki fahimta”.
Na ce, “Boka nake ga tunda muna tare da kai ai babu abinda zai samesu. Na tabbata ko da tayi niyar cutar da mu aljannunka ba zasu bari haka ta faru ba”. Wata iriyar harara Boka Girgije ya watso min kafin ya gyada kai hade da cewa, “Yaro bai san wuta ba sai ya taka”. Na yi saurin cewa, “Boka idan tsoro kake ji ai ina ga sai mu bar tafiyar nan, in ya so gobe inje in cewa mai gari kace ba zaka iya zuwa ba tsoro kake ji”. A fusace boka ya juyo gareni hade da mun dakuwa ya ce, “Ka ci uwaka, kaji dan iskan yaro, ni zaka kalli idanuna ka ce ina jin tsoro? Mu da muke hulda da aljannu da ifiritai fatalwar banza fatalwar wufi da zanji tsoronta”. Nayi saurin cewa “Allah huci zuciyar boka ai na zata ko tsoron fita kake ne”. Mikewa naga yayi yana ta faman masifa wai ai shi babu abinda yake tsoro a duniya. Nan take ya fara shiri, na ga ya dauki wata hular gashi ya dora a kai, hade da rataya layoyi a wuya, wasu kuma ya daure a kafa da hannu. Kana ya dauki jakarsa ta fata dake rataye ya dau wata sanda dake kofar dakin itama duk layoyi ne a jikinta. Yana mazurai ya ce, “Maza ku tashi mu tafi”.
Ina jin haka na mike na kalli Bukar dake zaune yana binmu da idanu na ce, “Bukar ta shi mana”. Duk a tsorace yake kamar zaiyi kuka ya ce, “Na rantse da Allah tsoro nake ji”. Na ja tsaki hade da cewa, “Haba Bukar baka ga irin shirin da Boka Girgije yayi ba? Ai wannan shiri ba su uku ba na tabbata ko su dubu ne yau sai Boka ya ga bayansu”. Ko da gama fadin haka sai ji nayi boka ya cewa Bukar, “Yaro ta shi mu tafi babu abinda zai sameka, kai dai da zarar kaga abinda baka yarda dashi ba ka boye a bayana”. Yana fadar haka yayi waje nima na take masa baya, Bukar ba dan ranshi ya so ba ya biyo mu yana haska fitila. Tafe muke a jere mu uku kowa da dalleliyar fitilarsa a hannu sai kace masu patrol, nine gaba Bukar a tsakiya sai boka dake biye da mu a baya hannunsa rike da sanda ko fatalwar zai daka oho.
Hanyar da muka bi da Surayyah ranar nan na nufa domin ban mance wajen ba, a tafiyar da mukeyi ko dan motsi kadan mu ka ji sai kaga gaba-dayanamu mun haska wajen da fitila. Muna cikin tafiya Bukar ya ja birki ya tsaya jin haka yasa na juyo ina kallonsa domin jin abinda zai fada, kamar zaiyi kuka ya fara magana, “Nura dan girman Allah idan bakinku daya da fatalwar nan ka fada mini, nan fa hanyar makabarta muke dosa. Ni dai in wani laifi nayi maka ban sani ba da yasa kake kokarin kaini mahallaka don girman Allah ina roko ka yafe mini”. Ya bani dariya sosai amma sai na hadiye dariya hade da cewa, “Haba Bukar sanin kanka ne ba yadda za’ayi a hada baki dani a cutar da kai. Asalima duk abin nan da kaga anayi inayi ne domin in kubutar da kai daga garesu dan wannan ita kadai ce mafita idan ka basu hakuri suka yafema shikenan ka sama lafiya garin ma ya sama lafiya”. Wani bera ne ya fito daga cikin kaba dake gefen hanya inda muke tsaye ya zo ya tsallaka a guje zuwa raminshi dake dayan bangaren. Ai kuwa a tare Bukar da Boka suka fasa ihu, nan take Bukar yayi wani irin tsalle ya makalkale boka suna neman faduwa.
🤥 Na zuciya fa sai na gama labarin nan gobe da safe akwai post in sha Allah