Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 22 Complete Novel

 

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

                           TWENTY-TWO📍

         Juyowar da Deen zeyi sukayi ido hudu da mami da Umm da sukayi mutuwar tsaye a gurin suna bin parlourn da kallo da sakekken baki…..

Ba karamin tashin hankali Deen ya shiga ba da ganinsu saidai bazaka gane hakan a fuskarsa ba, sai a lokacin ya fara dana sanin kawota gidan bayan ya san mami tasan gidan, shi a plan dinsa ze mayar da ita a yau ya samu ya koma kafin su mami su gane ya fita ashe mahaukaciya ya dauko be sani ba, gashi yanzu har sun gane bayanan sun biyoshi, abun kunyar kuma sunganshi rungume da ita, shikuma ya kasa sakinta kamar wanda aka yiwa baki….

Har bayan minti biyar anrasa me magana tsakanin Umm da Mami, kowannensu was just speechless with lots of questions, kada ma Umm taji labari that was more than disappointed, koda yaushe ita take kare Deen idan mami na complain akansa, koda tana masa fada bata wani ganin stubbornness dinsa da mami ke fada sai gashi yau idanta ya mata kyakkyawan gani da batasan a mazaunin da zatasa saba, wai Deen ne rungume da wata haka? Yana ganinsu kuma ya kasa sakinta?…….. 

Itako mami rasa abinda zata kama tayi, gadai gida kamar anyi barin mahaukaciya ko film din dakin amarya albarka, toh wayayi wannan danyen aikin? Sannan kuma wacece haka da yake rungume da ita kamar zaa kwace masa ita?……. 

Haka kawai zuciyarta ta bata suzo gidan dukda tasan bayanan dan baze zauna inda yasan zaayi saurin ganesa ba, but to her greatest surprise sai gashi sun samesa a gidan, a’a bama shikadai suka samu a gidan ba sun samu abubuwa dayawa, sannan ko ina is messed up bata inda zasu bi su karasa ciki ma, toh ya bazasu shiga shock ba?…….

Guilty conscious ne ya kamasa sosai ganin sunki cewa wani abu, sai binsu da kallo kawai sukeyi, shikuma tsoron sakinta yake karta karayin wani hauka a gabansu, nan ko tini allurar daya mata ya sumar da ita besani ba sai kara kankameta yake….. 

Ganin shirun ba shine mafita ba yasashi tattaro sauran kwarin gwiwar daya ragemasa yace;

       “I’m sorry Mami, I’m sorry Umm, It’s not what you’re thinking wallahi, don’t judge me pls, I can explain!”…….

      “Are you for real? Har kanada gout din da zakace we shouldn’t judge you? after everything we’re seeing? Meka mayar damune? Shashashun da basu san me sukeyi ba? I am seriously disappointed in you! Wallahi Saif ka bani mamaki”…….

Cewar Umm da maganar Deen ba karamin kara bata mata rai yayi ba, saboda rainin hankali wai they shouldn’t judge him bayan duk abinda suka gani”…..

         “Umm please, Taimakonta kawai nayi, infact budurwar sameer ce ma, ni ban santa ba”….

Deen ya fada a rikice batareda yasan ya fadi haka ba……..

Wata muguwar harara ta zabga masa tace;

       “Taimakonta? I see! Budurwar sameer ce haka kamar wacce aka shafa muku fatiha, wa zaka renawa hankali, wawa kawai mara tinani!”….

Sosai hankalin Deen ya tashi ganin yanda Umm ta zuciya, yasan da yana kusa da ita ma da Allah kadai yasan mari nawa yasha yanzu, sannan kaji Umm tayi zagi to akwai matsala dan ta tsani zagi komin kankantarsa….

Cikin kokarin kare kai still yana rungume da ita yace;

       “Trust me it’s not intentional Umm, idan na saketa komai ze iya faruwa, she has mental illness kamar harda aljanu a lamarinta, dan Allah ku yarda dani”….. 

         “Deen meka yiwa yar mutane, what are you hiding?!!!”…

Sai a lokacin mami ta fada strictly ganin rainin hankalin daya keso ya kara musu, suna kallon yarinya kamar bata numfashi amma zece inya saketa komai ze iya faruwa, it means he’s hiding something kenan….

Cikin rashin sanin abunyi yace;

      “Mom believe me I’m not hiding anything and…. Be karasaba idonsa ya sauka akan hannunta da jini keta zuba, a rude yace;

      “Innalillahi her hand is bleeding, kinga abinda kika jawo ko? gashi kinjiwa hannunki ciwo yanzu ya zanyi? Will you even allow me to treat you?”…..

Sai kuma ya dorata a kan three sitter ya tafi bedroom dinsa da sauri dan dauko first aid box, Mami da Umm na tsaye suna kallon ikon Allah…..

Fitowa yayi da sauri ya nufi inda take hankali tashe har lokacin begane a sume take ba, hannunta ya kama yana kokarin tsaida jinin yace;

     “Just stay still bazan miki da zafi ba, kar kimin kuka irin na dazu”….. 

Shifa harga Allah ya manta da wasu mami dake tsaye a gurin, burinsa kawai kar wani abu ya sameta dan ya tsorata da ganin yanda hannunta ke fitar da jini…..

         “Na tambayeka mekayiwa yarinyar mutane kaki cewa komai sai fadin we should believe you , what nonsense?”……

Muryar mami ta dawo dashi senses dinsa bayan ya samu ya tsaida jinin dake zuba daga tafin hannunta …..

Cikin murya me rauni kamar ba Deen the stubborn brat ba yace;

      “Wallahi ba abinda na mata”….

  “And meya sumar da ita, second why is she bleeding?, I just hope it’s not what I’m thinking that happened”….

Umm ta fada cike da takaici….

         “No no no, plsssss, it’s just her hand that is bleeding, and she’s not unconscious”…..

Hade rai tayi sosai tana fadin;

      “Hala idonka na maka ciwo ne, ko duk salon fooling dinmu ne? Baka ganin jini na zuba down her legs?  And wani kalan nonsense Doctor ne kai da baka gane mutum ya suma? Well kana sane ai”…. 

        “Rabu da dan rainin hankali yagani ai, wai mu ze renewa hankali, wallahi rufe ido zanyi na makaka a kotu, she deserves Justice!!!”

Sai a lokacin Deen ya kalleta sosai yaga da gasken bata numfashi ga jini nan facha facha down her legs, toh garin yaya? Ya akayi be kulaba? Gashi yanzu suna masa wata fassarar da ban thinking he raped her?!!…. “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” 

Ya fada yana shaking head, yanzu ta ina ze fara bata treatment? What causes the bleed down? Shidai ya shiga uku bejiba be ganiba daga taimako………

Ganin she’s bleeding more gashi baze iya treating dinta a gabansu ba yasa ya kalli Umm pleadingly yace;

      “Doctor please, dan Allah kiyi treating dinta, karta mutu, kinga she’s bleeding profusely, I have all materials here”…..

Dauke kai tayi dukda ba karamin tausayi yarinyar ta bata ba dan Umm akwai tausayi sosai, tace;

      “Even if I want to treat her flying zanyi in sameku a gurin? Ko cikin messed area dinnan zan bi inzo, besides bazan tabata ba saika gayamin gaskiyar abunda ya faru!”….. 

      “Ok ok bedroom din dake kusa daku is clean bari in kawota nan, Just treat her for me Doctor, I promise you zan fadi duk abinda ya faru please”……

Ya fada yana kokarin daukar fatima zainab….

Batace komai ba dan gaskiya yarinyar ta bata tausayi itama, and rayuwarta ya kamata a fara cetowa before anythin, ganin batace komai ba ya samu kwarin gwiwar nufarsu, yanajin kwalba na chakar kafarsa yana masa zafi, ga yanda jinin da take zubarwa yake bata gurin amma yaki tsayawa har saida ya sadata da gadon dakin…. Yana ajyeta ya fita da sauri dan ya dauko duk wani needful abubuwa dukda yasan beyi mata komai ba haka dai ya kwaso harda surgical suture if it happens da dinki dukda besan garin yaya ba…… 

Yana tsaye akanta harsuka shiga dakin, tausayi yarinyar ta basu sosai har Umm ta kasa bashi dirty slap din datayi niyar basa ta fara kokarin treating yarinyar … Bin yarinyar da kallo mami tayi tace;

      “Wannan ba ita bace kukayi accident tare ba?”…

Ajiyar zuciya me karfi ya sauke sannan ya gyada mata kai yace;

       “Itace mami, she was kidnapped! I only intended helping, shine na kawota nan na boyeta dan nemanta sukeyi haryanzu….…”

Be karasa ba sukajiyo muryar Umm na fadin;

      “Ya akayi ka bari ta taka kwalba haka sosai?”….. 

Bashi ba hatta mami da ita Umm din dake treatment din saida suka sauke ajiyar zuciya gane cewa it’s not what they’re thinking…. Shiko Deen ji yayi kamar anzuba masa ruwan sanyi da jin hakan dan harga Allah ya tsorata dukda yasan ba abinda ya faru, wani kalan rudewa yayi ne da har ya kasa gane abinda ya sameta kamar ba Doctor ba?…..

           Awan daddy biyu kenan yakasa zaune ya kasa tsaye, sai kai da kawowa yake cikin rashin sanin abinyi, ba karamin tashin hankali ya shiga ba a kwana biyunnan, neman duniya yayiwa fatima zainab ya rasata, ya kirata so ba adadi amma amsar dayane  ‘switch off’, gashi so yake a daura auran gobe cuz he can’t wait till seven days anymore, ga khaleel yana kwance a asibiti ba lafiya, kowa kuma yasan abinda yake damunsa saidai this time around dole khaleel yayi hakuri dan baze iya taimaka masa ba, shi yanzu damuwarsa daya yanda khaleel zeji idan ya auri fatima zainab?……

Ya rasa meyasa yakejin kamar wani abu na shirin faruwa, bashi kadai ba hatta tawagarsa gabadaya kowa a tsorace yake shiyasa suka yanke kawai a daura auren gobe kosa samu nitsuwa….. 

Daurewa yayi ya shirya dan zuwa dubo khaleel a hospital….

Kwance khaleel yake kansa a sama yana kallon ceiling….. Shikenan mutum baya mistake kenan a rayuwa? Meyasa bazata basa second chance ba?…  Wannan maganganun yaketa maimaitawa a brain dinsa….. Ya rasa ya zeyi da ita tagane he’s so sorry kuma he doesn’t mean abinda ya faru kawai sharrin shaidan ne, and he had learnt his lesson in the hard way, ba karamin dauriya ya dingayi ba a yan kwana kinnan datake bashi attitude sosai, daga karshe ma sai ya nemeta ya rasa gabadaya, idan ya kira wayarta kuma a kashe, yana cikin wannan halin aka mishi text da wata number wai “I’m sorry I’m getting married to the love of your life, forgive me!”….

At first kin yarda yayi, yayi disregarding din maganar dan yana ganin hakan is impossible not until meshi ya turo masa evidence da dole ya yarda da gasken aure zatayi, and that’s what shattered him completely da har saida aka danganasa da hospital, a yanzu ma yana kan strict medication ne dan heart dinshi is giving up, at first he was suffering from Tachycardia (a medical term for medical term for a heart rate over 100 beats a minute) sai ya koma extreme Bradycardia ( a medical term for a slow heart rate below 60 beats a minute) which is more risky….  Yanzu haka da sun san ya farka da yanzu anmasa Evolocumab injection ( an injection is used to reduce the risk of a stroke or heart attack or the need for coronary artery bypass (CABG) surgery in people with cardiovascular disease(heart diseases)) da suke mishi koda yaushe shiyasa zaka samesa kusan koda yaushe yana bacci, anayin hakanne kuma dan a ragewa mutum tinani…..

Yana cikin wannan hali daddy ya shigo, be juyo ba amma yasan shine dan shikadai aka bawa damar ganinsa dan baa san hayaniya a inda yake…….

      “Son”……

Daddy ya fada yana kamo hannunsa

       “Ashe you’re awake! How’re you feeling now?”…

Kai kawai khaleel ya daga masa batareda yace komai ba…….

Cikin tausayawa daddy ya kuma fadin;

      “Don’t worry son, ina nan ina nemota, Insha Allah fatima zainab bata da wani miji sai kai, so ka kwantar da hankalinka kasamu lafiya sosai, ko kanaso tazo ta ganka duk a ramene?”……

Da sauri khaleel ya girgiza kai kamar wani karamin yaro abundai gwanin tausayi…..

Haka daddy ya cigaba da kwantar masa da hankali yana basa assurance akan lallai sai fatima zainab ta zama matarsa har akazo aka mishi injection yayi bacci sannan daddy ya tafi………

     Hira sukeyi isu isu yan dakin sunata shafta abunsu, eesha ce ta kalli spot din fatima zainab tace;

       “Wannan unknown girl din anya lafiya take kuwa? Tun kafin a fara tests fa tabar hostel gashi har zaa fara exam next week, nidai na fara jin tsoro”……

Bilkisu ce ta karbeta da fadin;

       “Gsky dai lamarin akwai question mark, kodai bata da lafiya ne bamu sani ba?”….. 

         “Zatayiwu wallahi, gashi bamusan ta ina zamu fara nemanta ba”…..

Cewar eesha fuska dauke da damuwa…..

Bata rai umaima da bata wani sa musu baki a hirar ba tayi tace;

      “Toh ku ina ruwanku da wanda be damu da ku ba? Haka ta zabarma kanta sai kuyi minding business dinku mtssssssss”…….

Harararta eesha tayi taja tsaki itama tace;

      “Muma bamu sako ki a hirar mu ba, ai ko makiyinka ne  kaga baka ganshi ba ana shirin exam ai ka jajanta”…..

       “Sai kuyi kuma, kila ma tanachan tana zuwa lectures abunta kunanan kuna damun kanku”…… 

Umaima na fadin haka tasa ear piece….. 

Basu damuba suka cigaba da jajanta lamarin fatima zainab…..

      Duk minti minti yake duba agogo yana expecting dawowan Deen anytime soon, tun yana a kishingide har bacci barawo ya kwashesa be sani ba…..

 Wani mummunan mafarki ne ya tadasa daga baccin gajeran lokacin daya daukesa , wai Deen ya tafi da yarinyar gurin daurin auren, yana zuwa kuma yace a daura dashi, sai gashi ya dawo da yarinyar yana fadamasa yayi hakuri anriga andaura dashi…..

Wani mugun gumi ne yashiga keto masa, yana gogewa yana fadin ‘Allah ya kiyaye, Allah ya kiyaye’…. Shiyasa fa akace mafarki ba gaskiya bane, to in banda karyan mafarki ta ina Deen ze auri wacce ya fara gani a yau dinnan yanda yake babu soyayya a tsarin rayuwarsa, aiko auren zeyi sai wacce ta dage ta chusa kanta har Allah ya taimaketa ya sota sannan….Ballema yasan Deen baze iya stooping so low yaso yarinyar da shida khaleel suke fama akai ba…… 

Zaman gidan ne yaji ya ishesa kawai ya fita waje domin yasha iska ya kuma jira zuwan Deen dan yasan duk abinda ake yanzu yaci ace anshafa fatiha an tawo masa da amaryarsa…..

Ko minti daya beyi ba a bakin gate wani  kyakkyawan mutum yazo ya masa sallama yana mika masa hannu, gaisawa sukayi cikin mutunci, sannan sameer yace;

      “Saidai bangane waye ba, kodai sabon makoci mukayi ne?”….

Dariya yayi yace;

     “Eh kusan haka dai, dama wani abu nazo in fadamaka dukda bansani ba koshi kake nema”..

       “Ina jinka bawan Allah”….

    “Abokinka kake jira ko?”…

Zaro ido sameer yayi cikin rashin fahimta yace;

     “Bangane ba?”….

   “Deen kuke ce masa ko wa? Ina nufin shi!”…

   “Eh shi nake jira koya baka sako ka bani ne?”…

Dan dariya yayi sai kuma ya gimtse yace;

     “Niko ya bawa babban sako in baka!”…

          “Ina jinka bawan Allah meyace ka fadamin”…

    “Yace kayi hakuri dan shima yana sonta baze iya taimaka maka ka aureta ba, yanzu haka maganar da nake maka yana chan ya boye ta a gidansa!”……

Ba karamin shock sameer ya shiga da jin wannan mummunan labarin gashi dama yayi mugun mafarki akan hakan…. Daurewa yayi cikin yarda da Deen yace;

      “Karyane ni nasan Deen bazeyi haka ba, kuma Deen bashi da gida a abuja, dacemin kayi yana chan ana dauramin aure sai na yarda, tukunna ma kai waye da kasan duk wannan?”…..

        “Sanin ni waye baze maka amfani ba, abu daya nakeso shine ka yarda da abinda na fada ni kuma zan taimaka maka ka samu yarinyar dan tafi dace wa da kai akan shi”….

       “Toh meyasa kake magana kana dariya, sannan kuma tayaya zaka tabbatarmin da abinda kake fada?”….

     “Karka damu da dariyar dana keyi haka yanayi na yake, ko yanzu kace in kaika inda ya kaita zan kaika ka tabbatar ma idonka abinda na fada maka”…..

       “Naji, muje!”…..

          Dan dakatarwa  Umm tayi da taba kafar tana kallon wani black dot a tafin kafar fatima zainab, dagowa tayi ta kalli Mami tace;

      “Itace kikeson nagani da sukayi accident da Saif?”….

        “Eh itace fah”…..

Cewar mami tana kallon dot din itama…..

Ajiyar zuciya Umm ta sauke ta dago tana kallon fuskar fatima zainab tace;

       “Me kikeson nagani a tattare da ita a lokacin?”…

   “Wallahi gani nayi tamin kama dake sosai, ashe I was mistaken, sai yanzu dana kara kallonta naga bakwa kama sam”…..

      “Yeah gaskiya we have nothing in common, between she’s beautiful!”…..

      “Inaga shiyasa danki ya makale mata”…

Kallon Deen Umm tayi murmushi dauke a fuskarta kamar ba ita tagama masifa ba tace;

     “Fadamin gaskiya are you in love with her?”….

Da sauri ya girgiza kai, ya hadarai yace;

      “Ni? Allah ya kiyaye, kina kallonta haka silent killer ce Umm, can you believe ita tayi duka wannan fasha fashen? Saida namata allurar bacci shine fa ta suma, yanzu inta tashi Allah kadai yasan mezata kara fasawa a gidannan, now I have to renovate!”….

Zaro ido tayi tace;

      “Really? Amma kuma ya kamata a mata uzuri ba kace she’s mentally unstable ba, and renovation shouldn’t shake a billionaire like my son”….

      “Yes she is, tin a wanchan lokacin da mukayi accident na fadawa mami she’s not alright taki yarda”….

    “Ah toh ta ina zata yarda? Ni ma yanzu ai kalau nake ganinta!”…..

    “She’s not alright wallahi, kamar harda jinn a lamarinta kuma, kamar ma aurenta sukayi”…

Dariya sosai Umm tayi dan dama bawai tayi wani fushi dashi sosai bane, lesson kawai take son koya masa, sai kuma Allah yasa abinda suke zata ba hakan bane, duk saitaji hankalinta ya kwanta, tace;

       “Allah bazesa ba, wannan wani kalan mugun fata ne haka? Dan baka sonta sai kace aljani ya aureta, ni wallahi taban tausayi, I’m in love with her already, a ina iyayenta suke?”…..

Ta fada tana shafa fuskar fatima zainab dan ita haka Allah yayita da son mutane, kowa tagani ya mata tana sonsa, shiyasa she’s every body’s fav ba kamar mami ba that is kinda bossy….

       “Hmmm shikenan tinda baki yarda ba, karma ki wani sota dan wallahi da kanki zaki tsaneta inta fara haukarta, nifa bansan……”

Be karasaba mami ta daka masa tsawa tace;

      “Shut up my friend! Koda yake lefin ki ne, yanzu harkin manta da tarin laifuffukansa kina masa dariya, toh wallahi zakaci gidanku, now tell me what’s the essence of the face mask da har kasa wani a hatsari?”…..

Shiru yayi bece komai ba yana sauraranta, ta cigaba da fadin;

      “Ashe you’re this heartless bansani ba? Yanzu imagine an turo wani yazo ya kasheka, haka zaa kashe wanda bejiba be ganiba saboda yana talaka? Shikenan kun maida talakawa wa’yenda busan abinda sukeyi ba? Haryanzu kaki dena wannan I don’t care attitude din naka ko?”….

      “Mami ba haka bane, I was just….”

Wasu lafiyayyun maruka ta sauke masa guda biyu masu rai da lafiya, tace;

       “Ba haka bane a ina? Well I don’t blame you barewa bazatayi gudu danta yayi rarrafe ba, a gurin ubanka ka kwaso duk wannan banzan halin aka renamin hankali wai you have empathy issue medically, I’ll make sure I deal with you regardless of your so called issue, yanzu kuma zamuje ka karbi position dinka ayi freeing bawan Allah”…

       “Mami please, ki barni koda na yau ne, I promise you gobe zan koma, idan ta tashi bananan you can’t handle her wallahi”….

Deen ya fada yana kokarin controlling kansa dan jijiyoyin kansa har sun fara fitowa alamun ze iya birkice musu anything soon, shi kuma bayasan hakan ya faru amidst wannan critcal situation din”…

      “Kaji na rantse wallahi Deen sai ka koma a yau dinnan, shima kuma sameer zezo ya sameni, bani kuka hada baki kukayi fooling ba?”….

     “Mami kona koma saina dawo, she’s in danger koyaya na matsa kusa da ita zasu cutar da ita?”

      “A matsayinka na ubanwa a gurinta? Uba ko miji? Kasan Allah ka fita idona in rufe Deen, bansan yaushe ka zama fitsararre haka ba, imagine!”…

Mami ta fada tana dafe kai, mamaki take wai Deen ne yake gaya mata magana kai tsaye akan wacce yayi claiming bayaso, yes tasan shi da rashin ji amma duk wani abu daya danganci mace bayaso shiyasa take mamaki sosai yanda ya nuna damuwa akan wannan…..

        “A muslim brother, mami kefa kike gayamin musulmi dan uwan musulmi, ina taimakon mutane, so please let me be with her”…

 Mami zatayi magana kenan sujaji karar horn din mota da mugun karfi, wanda ko tantama basayi a bakin get din gidan ne!!!!!

Domin karanta cikakken littafin sai ku danna bulun Rubutun dake ƙasa 👇👇👇

https://www.aihausanovels.com.ng/2022/12/wace-ce-ita-chapter-11-complete-novel.html

Uniquebarakancy🌹

Back to top button