Hausa novels

Kanwar Maza Page 79 Complete Novel By Ayshercool

Page 79

 

*TALLA! TALLA!! TALLA!!!

*ƊANƊANO DAGA LITTAFIN NAZEEFA SABO NASHE, MAI SUNA ƘUDURAR ALLAH*

 

Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab’a kusantar wata mace ba?” Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta “Tabbas Jaheed jininka don gwajin k’wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba’a yi gwajin ba.”

 

Shiru na tsawon lokaci d’akin ya d’auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k’wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab’a rik’ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d’ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab’a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD’i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi.  Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K’UDIRAR ALLAH….

 

(*Ina ma’abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaɗantar da ku, da ɗaɗan litatafan hausa masu ma’ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA ɗin sa ya kasance daidai da na yaron da bai taɓa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ƙuruciya har girmansa, bai taɓa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ƙudurar Allah. Masu buƙata kai tsaye za su iya tuntuɓar ta a kan lambar wayarta 08033748387*)

 

 

 

 

*Littafin kuɗi ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*

 

 

 

 

 

 

 

 

Buɗe ƙofar banɗakin yayi ya fito, ta ƙwala ihu ta rufe jikinta, ko kallonta bai yi ba, ya maze kamar bai ganta ba, ya wuce ya kashe fitila ya kwanta.

 

Ajiyar zuciya tayi, ta saka kayanta, ta nufo gadon, sai dai ya babbake gadon, kuma ya ajiye system a kan gadon.

 

“To ka matsa mini in kwanta”.

 

Ba tare da ya kalleta ba ya ce “Gado ɗaya zaki kwana da ƙaton?”.

 

“To a ina zan kwanta?”

 

Yayi mata shiru, ya cigaba da tattaɓa system ɗin.

 

Ta hau ta ja fulo ɗaya ta kwanta, ta ce “Papa ni fa buge-buge nake yi idan ina bacci, wurin nan yayi mini kaɗan”

 

“Saboda gaki giwa ko? Ki ka buge ni ƙasan gado zan hankaɗa ki”

 

“Dan Allah papa ka matsa, ga space can a bayanka fa”

 

Ganin ba zai kulata ba, ya sanya ta kwanta, shima kashe system ɗin yayi, ya kwantar da kansa a kan pillonta, jin numfashin sa a fuskarta ya sanya ta buɗe ido.

 

“Papa wai dan Allah idan baka takura mini ba baka jin daɗi”.

 

“Mmm” ya bata amsa.

 

“To dai ina yawun bacci, kan gari ya waye na jiƙa fulon nan, gara ma ka tashi” dariya yayi ya ce “Ba zan fa tashi ba”

 

Ta yinƙura zata juya masa baya, ya riƙeta.

 

A haka wani irin nannauyan bacci yayi awon gaba da su gaba ɗaya.

 

***

Iya ƙoƙari sosai mai sunan baba yana yi, a kan ya samu ya kammala ginin nan, duk da kusan abubakar ne yake ta aikin, gefe ga kayan lefe yana fama.

Sai dai a duk lokacin da ya tambayi iman, ko ta na da buƙata kalar abun da za a saka mata a kayan lefe, sai ta ce masa ita ba ta da zaɓi, duk abun da yayi mata shikenan.

 

Yadda laila ta tsaya a kan rumaisa, haka yanzu ma ta tsaya a kan Iman, take ta shan gyara, sai wani irin kyau take, ta ƙara ƙiba tayi fresh da ita, fatar nan ta ƙara sheƙi, saboda yadda ta kama sabayar maman Khadija, gefe kuma ga maganin maman ilham, wanda ya ƙara sawa ta cika ta yi fam da ita.

 

Abunka da farar mace, har wani ɗaukar ido take yi, mai sunan baba duk lokacin da ya zo wurinta, sai ya ga ta ƙara yi masa kyau fiye da da, sai dai ba zai iya fitowa ya ce mata tayi kyau ba. Sai ma ji da ya din ga yi, ina ma ta daina fita, saboda kishinta.

 

Mai sunan baba ya saki jiki da mahmud, dan har gidan da iman za ta zauna, sun je tare, ya din ga yabawa mai sunan baba sannan ya ce “Ni yakamata na ƙarasa aikin ginin nan fa”.

 

Mai sunan baba ya ce “Saboda me?”

 

“Saboda haka ya kamata”

 

“Ko kuma ka raina abun da nake yi ne?”

 

Mahmud ya yi murmushi ya ce “Ni na isa? Kawai akwai buƙatar yin hakan ne, iman da mahaifiyata, da kuma rumaisa suna bina nannauyan bashin da yakamata na sauke”.

 

Mai sunan baba cikin rashin fahimta ya ce “Wane irin bashi kenan?”

 

Mahmud ya ɗan yi shiru ya ce “Ban san a yaya zaka ɗauki abun ba? Na san zaka ji shi hagu a dama. Kamar yadda kowace uwa da ɗa, yake akwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakaninsu, to ni saɓanin haka ne, ba wata soyayya ko shaƙuwa tsakanina da tawa uwar, hasali ma a gabana ake cutar da ita, bana iya cewa komai. A lokacin da iman ke kan ganiyar kwasar baƙin ciki na fasa aurenta a jejjere, a lokacin ammi ta nemi alfarmar na auri iman, amma na ƙeƙashe ƙasa na ce ba zan ba.

Ni kaina bana gane yadda wasu abubuwan suke gudana, har sai da rumaisa ta shigo rayuwarmu, take ta ƙoƙarin haska mini hanya, da farko da ni daga nannauyan baccin da nake yi. Tana ta ƙoƙarin gyara tsakanina da mahaifiyata. Na san zaka ji labarin a wani iri ba lallai ka fahimta ba, amma ka bar shi a haka, ni dai fatana, ka bani dama ko yaya nayi wani abu a kan rayuwar iman, ko dan farantawa ammi da kuma rumaisa”.

 

Ya share hawayen da ke ƙoƙarin zubo masa, ya fita daga gidan, tabbas kamar yadda ya faɗa, umar bai gane kan wannan rikirkitaccen zancen ba, tayaya zaka rayu a cutar da mahaifiyarka a gabanka, ba tare da ka ɗauki wani mataki ba?.

 

***

Baccinsa yayi nisa sosai, har alarm ɗin wayarsa ya dinga bugawa na sallar dare, amma bai tashi ba, sai da rumaisa tayi masa wani duka da ƙafarta a ciki, ya tashi a razane.

Har ya tashi zaune, bacci kawai take yi, kuma kaɗan ya rage ba ta faɗa daga kan gadon ba, duk ta baje kamar baccin jarirai.

 

Janyota yayi ya gyara mata kwanciyarta, ya rufeta da bargo..

Yayi shiru yana kallonta, tare da mamakin yadda Allah ya yassare mata baiwa kala-kala, a haka dai gata ba ta ji sam, amma tana da baiwa ba ƙarama ba, shi kansa yana mamakin yadda yake lallaɓata, yake bin duk abun da ta ce masa.

Maybe hakan ba ya rasa nasaba da yadda yake ganin girma, da kuma darajar abun da tayi masa, wanda ko duniya zai bata ba zai biyata ba.

 

Ya durƙusa yayi kissing ɗin goshinta, sannan ya sauka ya shiga banɗaki.

 

Da safe kuwa yana banɗaki yana wanka, tana tsaye a gaban dressing mirror, tana kallon kanta a mudubi, tunani take maiyasa ba ta zo da sabayarta ba, dan ba ƙaramin missing ɗin kunun take yi ba. Kar fa ta je su koma yadda suke a da, gaskiya gara ayi a koma gida, ta cigaba da amfani da kayan maman Khadija da na maman ilham.

 

Knocking aka yi a ƙofa, ta nufi ƙofar ta buɗe, ta ga wata mata a tsaye, cikin broken English matar ta ce mata abincin da aka yi order ta kawo.

 

Rumaisa ta ce “Wannan wane irin turanci ne babata, wannan kalar turancin kamar na ƴan lagos, kenan turancin kano daban, na anty laila ƴan canada daban, na abuja da Lagos iri ɗaya?”

 

Matar ta ce “Ban gane me ki ke faɗa ba?”

 

Rumaisa ganin matar ba ta jin hausa, ya sanya ta samu abun yi, ta riƙe ƙugu ta ce “Na ce, wane irin turanci ki ke yi, ke baki iya hausa ba? Kuma dai papa bai fita ba, kuma bai yi waya ba, ya aka yi ki ka kawo abinci, ko na sadaka ne?” Kamar shashasha matar take kallon ruma, dan ba ta fuskanci komai ba.

 

Takawa ya ƙaraso ya karɓi kayan hannun matar, ya yi signing ya ce mata ya gode.

 

“Wai ni ya aka yi ka saka aka kawo abinci, naga ba wanda ka kira a waya”

 

Ya ce “Ai na so matar nan ta zane ki, kawai kin saka mata a gaba, kina ta mata surutun banza da hausa, bayan ba ganewa take yi ba”.

 

Ta ce “Mhmm, nima fa kamar da a makarantar mu, bana gane komai, kamar dai ni da matar nan, ni babban abun da nake ganewa, a bani kuɗin makaranta na sai goriba, ko manɗo na yi tsokana da surutu na dawo gida”.

 

“Yanzu fa?”

 

“Ina ganewa, anty laila ke koya mini sosai, kuma zaka ga result ɗina”

 

Suka karya, yana yi mata mitar, dukan da tayi masa cikin dare. Dariya ta din ga yi masa, ta ce “Ai dama na gaya maka, Innalillahi ni fa sai da aka yi mini aure na daina fitsarin kwance, musamman idan ana sanyi, in ji fitsarin ya matseni, sai in yi mafarkin gani ina fitsari a banɗaki, wallahi ina tashi zan ga nayi a kwance”

 

“Yanzun ma waye ya sani ko kuna abun ki?”

 

Ta ce “Haba papa, lokacin fa ina yarinya ne fa nake baka labari”

 

“To yanzun girma ki ka yi, ko da yake an fara girma fa, mantawa nake yi” Saboda kar ya zauna ya fara tsokanar ta, ya sanya ta tashi ta tafi window tana leƙawa.

 

Can ya ji ta ce “Innalillahi”

Ya ɗago ya ce “Lafiya?”

 

“Papa ina ka kawo mu nan? Nan ai duk ƴan iska ne leƙo ka ga fa”

 

Ya ƙarasa ya tsaya a bayanta, wasu mata take nuna masa, sun sha matsatsun kaya, marabarsu da tsirara kaɗan ne, sai kaiwa suke suna komowa.

 

Ya ce “Sun yi kyau tubarkallah” ba shiri ta kalle shi ta ce “Me ka ce?”.

 

“Na ce sun yi kyau”

 

Haɗe rai ta yi ta ce “Amma dai ka san haram ne ko?”.

 

Adam ya ce “Ke fa ki ka nuna mini” janyo window tayi ta rufe tana huci.

 

Ya fara ƙoƙarin ture ta ya sake buɗewa ya ce “Matsa ban gama gani ba”

 

Rumaisa ta haɗe rai ta ce “Wallahi ba zan matsa ba”

 

Yayi murmushi dama abun da yake so kenan, ya ce “Yanzu da cewa na yi, ki saka irin kayan, cewa zaki yi ke ba ƴar iska ba ce,  tunda na ga na bati, ai sai ki barni na kalla ko?”

 

Tayi shiru tana kallon sa. “Ko zaki saka?” Yayi maganar yana tsareta da ido, sai dai tayi shiru bata bashi amsa ba.

 

Ya ce “Ke ba ƴar iska ba ce ko? Laila ba ta gaya miki babu kunya tsakanina da ke ba?”

 

Shiru tayi tana tunani, tabbas laila ta gaya mata, kuma usy ma ya gaya mata, kenan da gaske suke mata?.

 

A hankali ya ce “Shikenan, laifina ne” ya juya ya bar wurin.

 

“Zan saka” ta furta kamar tayi zunubi.

 

Ya tsaya ya waiwayo ya ce “Are you serious?” Ta jinjina masa kai alamar eh, dan har ga Allah saboda kar ya cigaba da kallon waɗancan matan ya sanya ta ce zata saka, kuma bata son kishiya.

 

Ya ce “To mu je in anjima mu sayo, zaki saka?”

 

“Eh amma zaka daina kallonsu?”.

 

“To me zai saka na kallesu? Ai na san ba kyau, in dai zaki saka ba zan sake ba”

 

Murmushi yayi yana kallon baby face ɗin ta, ta faɗa ne kawai saboda kishi.

 

Ya ce “To shikenan, in anjima zamu je, saura sai mun dawo ki ce baki san zance ba”

 

Wuni suka yi tare, ya bata damar yin surutunta son ranta, ba tare da nuna mata ya gaji, ko ya ƙosa ba, suka sha dariyarsu tare ta bashi labaran ta lokacin tana gida, salla ce kawai ta din ga fitar da shi.

 

Da zai fita sallar magariba ya ce mata “Mimi, ki zauna karki fita ko ina, idan na idar da salla zan je meeting ba daɗewa zan yi ba, zan dawo in sha Allah”

 

“Wai ni zaka bari a ɗakin nan nikaɗai?”

 

“Eh, ba daɗewa zan yi ba”

 

“Wallahi tsoro nake ji, haka kurum a yankani, idan ka tafi sai dai ka tarar da ni a bakin titi, ko na ɗaukko rigima da sai an koromu daga wurin nan. Ko kuma in jiraka a wurin shigowar nan, kuma ka bani system ɗin ka da wayarka ɗaya nayi game har ka dawo”.

 

“Salon ki goge mini wani abun, idan ki ka goge mini abubuwana, sai na kai ki prison, zan baki amma a ɗaki zaki zauna”.

 

Rumaisa ta basar ta ce “Prison ai sai marasa gaskiya, dan Allah kar ka barni a nan papa, da gaske tsoro nake ji fa” tayi maganar cikin shagwaɓa.

 

Yayi ajiyar zuciya ya ce “Bari na je nayi sallar sai mu tafi”.

 

Da misalin ƙarfe takwas da mintuna biyar na dare, takawa yayi parking a gaban harabar wata plaza, ya sanya rumaisa a gaba, suka shiga.

 

Wani irin katafaren office ne, ƙato mai kyan gaske.

 

A can suka tarar da bashir ma, ruma ta ce “Yaya bashir, ya aka yi ka zo nan?”

 

Ya ce “Ɗazu na shigo ni, ai ya ce mini tun jiya ku ka zo”

 

Suka gaggaisa da mutanen wurin, sai dai ruma ta raɓe a kusa da adam, saboda duk sai ta takura, ita kaɗai ce mace a cikinsu.

 

“Adam wannan kuma fa?” Cewar ɗaya daga cikin su, da ya tsare rumaisa da ido.

 

Barrister sa’ad ya ce “Madam ɗin sa ce”.

 

Ya ce “Masha Allah, amma me zata yi a nan, harkar aiki ce fa”

 

Adam ya ce “Ba zata hanamu aikinmu ba, mu fara kawai barrister meye a ƙasa?”

 

Barrister sa’ad ya ce “Eh to, harƙallar fasa bututun man fetur, da kullum ake yi wa ƴan ƙasa ƙarya da ita, Dss sun kama mutum uku shekaranjiya a delta, bayan sanarwar da hukumar matatar mai ta fitar cewa, man da ake samarwa a Nigeria yayi ƙarancin da kuɗin da yake kawowa ƙasa ba zai wadaceta ba, sai an ciyo bashi, sai dai mutanen sun ce SMOKE suke yi wa aiki, an sake su ba tare da kowa ya san an yi bama, Salim ne yake gaya mini”

 

Takawa ya ce “SMOKE again?”

 

Bashir ya ce “Adam, shirye-shirye fa sun yi nisa, wakili zai tsayar da ɗan sa Khalifa takarar ɗan majalisa, kuma ka san jam’iyyar tana da ƙarfin da ko da ƙarfin tuwo zasu ƙwata su bashi, mecece makomar al’ummar da mutumin banza zai jagoranta?”

 

“Ba wannan ba, cire sunanka da ga jerin jami’an da za a ƙarawa matsayi bayan dawowa daga ƙaro karatu, yafi ɓata mini rai”.

 

Takawa ya ce “Ba matsayin nake buƙata ba, goyon baya ta yadda zamu yi ƙarfin da zamu iya ƙalubalantar kowa. Akwai buƙatar lawyoyin cikinmu, ƴan siyasa da sauran hukumomi masu son yin aiki domin ƙasarmu ta gyaru, ace sun ƙara yawa”.

 

“Adadin mutanen ka adadin matsalarka, adadin yadda sirrinka zai din ga fita, aikin yana tarwatsewa, ayi ta haɗaku rigima da zargin juna”

 

Tsit suka yi suna kallonta, shi takawa a wurinsa ba abun mamaki bane ba, jin kalaman hangen nesa a bakin ruma idan ta ga dama, dan na shirirtarta sun fi yawa.

 

Ya ce “Silent mimi, meeting fa nake yi”.

 

“Daga bayar da shawara?”

 

Takawa ya ce “Idan ki ka kuma magana ba zan sake fita da ke ba”

 

Barrister sa’ad ya ce “Adam, allow her please, gaskiya fa ta faɗa”

 

Takawa ya ce “Rabu da ita, yanzu dai sa’ad, zan yi magana da salim, ya sake bin diddigin samo mana hujja da tabattar da abun da ya faɗa, zamu sanar wa da mutane.

Sannan ɓangaren media, su musbahu, dole su cigaba da tattaunawa da masana tare da fahimtar da mutane illar ciyo wannan bashi, dan ba ƙasa ake ginawa ba, kansu suke azurtawa, na rasa wani asarraren ne ya zauna ya samar da dokar yi wa ƴan majalisa da tsofaffin gwamnoni hidima da kuɗin al’umma, wace irin ƙasa ce haka, a mulke ka a gasa ka, kuma a ranto kuɗi a bawa wanda ya zalunce ka ace ka biya, abubuwan nan sun fara isata, muna tufka ta gaba ta baya na warwarewa”.

 

“Wannan faɗar fa da ka ce ayi ta gayawa mutane, ƙara musu takaici ku ke yi, maganin abun yakamata ku yi musu, tayaya za a zo ace mini wane ya ɗauki kayana, mutane na kallonsa babu wanda yayi yinƙurin hana shi, balle a karɓa mini kayana, kuma azo ana bani labari, kamar haka ne fa papa”

 

Bashir ne ya tafawa rumaisa, ya ce “Kai, rumaisa kina da brain irin sosai ɗin nan, takawa yakamata kayi mata special adviser a tafiyar nan. Amma rumaisa mun koma maganar mu ta farko, domin iya kama ɓarawon da yayi miki sata, dole wataƙila mutane na buƙatar ƙarfi da yawa, dan wataƙila ɓarawon ba ɗaya bane ba, sun ɓuya da yawa da muggan makamai”

 

“Sai ku yi musu dabara, ta hanyar yi musu tarko, ku kama wakilin nasu, idan kuka cigaba da zuba ido ana yi mini sata, idan nawa kayan suka ƙare kan naku zasu dawo, kuma bayan sun gama idan suka rasa abun sata, ku zasu fara kamawa suna sayarwa, ana ciniki ku kamar dai yadda ake fataucin dabbobi, ayi ta ciniki kamar an kama bayi, kamar dai yadda aka sace ni, da ni da anty aisha”.

 

Maganganu rumaisa ta saƙa musu cikin hikima, da sai da ta sanya su cikin nazari, adam ya ce “Ina ga mu tashi haka, zamu biya wani wurin ne da ita, zamu haɗu gobe in Allah ya kaimu ”

 

Barrister sa’ad ya ce “Allah ya kaimu, amma lallai muna buƙatar ƙwaƙwalwa irin t madam a tafiyar nan”.

 

A ransa ya ce ‘Baku san butsancinta ba, sai tayi muku wani shirmen zaku gane baku da wayo’.

 

Adam kansa har wani ciwo yake, yana ta tunanin maganganun ta, ita kuwa ko a jikinta, har suka isa masaukinsu.

 

Kamar yayi mata magana a kan maganganun da tayi, amma ya shareta, dan da yayi zata fara wahalar da shi.

 

Kwanansu uku a Abuja, ya kaita yayi mata sayayya, ya kashe kuɗ sosai, banda tsarabar da ya yi mata da zai dawo, banda uban kayan lefenta da haryanzu wani abun ma bata taɓa ba, ga shirin bikin iman nan ma yana ta hidima.

 

Suna tafe a hanya tana kallonsa, ba ƙaramin tausayinsa take ji ba yanzu, gaba ɗaya yadda ta tsammaci halinsa ba haka yake ba, duk da dai mafaɗaci ne mai zuciya, amma a zamansu ta tanƙwara shi ta ƙarfin tsiya ya tanƙwaru, dan shi kansa ya san ko bai durƙusa mata a kan gwiwoyinsa a zahiri ba, a baɗini yayi.

 

Tana ta ɗaɗɗaga kayan da ya saya mata tana murna, wasu kayan tana tunanin anya zata iya sawa kuwa, duk da anty laila ta koya mata saka ƙanan kaya, amma wasu kayan sun yi watsewa da yawa.

 

Yana zaune a kan gado yayi shiru, yana zancen zuci, rumaisa ta buɗe akwatinsu, ta fito da pencils ɗin ta na zane, ta ɗaukko cardboard paper, ta zube su a kan ƙaramin Centre table, da cleaner da duk abun da take buƙata.

 

Ta tashi ta nufi takawa, ta riƙo hannunsa ta ce “Taso muyi zane papa”

 

Ya ƙwace hannunsa ya ce “Leave me, am not in mood”

 

Ta ce “Gaskiya ni ba zaka zauna kayi mini shiru ba, ka taso”.

 

Ya ɗaukko wayarsa ya ajiye mata, ya ce “Gata nan je ki kiyi hirar da ita”.

 

“I want de encrypted the portrait i gave you 6months ago”.

 

A hankali ya juyo yana kallonta, ta jinjina masa kai ta ce “Taso”

 

Tashi yayi a hankali ya biyo ta, suka zauna a tsakiyar ɗakin.

 

Ta fara da zana farin wata, irin a daren goma sha huɗu.

 

Yayi shiru ya nutsu yana kallon ikon Allah, sannu a hankali ta yi zane iri ɗaya sak da wanda ta bashi, sai dai a wannan karon da alamomi da bayanai yadda zai gane.

 

Ta zana kanta a zaune a cikin daren a daji, ga masu garkuwa da su riƙe da bindigogi, sai ta zana wata hanya, ta rubuta unknown distance. Tayi alamar yadda sautin ababen hawa ke kaiwa suna komowa a nesa da wurin, duk da yanayin wurin babu alamar abun hawa zai iya bi.

 

Ta kalleshi ta ce “Papa meye ma’adanai?”

 

Ya ce “Resources, albarkatun da Allah ya ajiye a cikin ƙasa, da ƙasa ke amfani da su, a sayar ko a sarrafa dan al’ummar ƙasa su mora”

 

Ta ce “Ok”

 

Sai ta koma kan zanen ƴan ta’addan, ta nuna ɗaya yayi magana ya ce “Ga mutanen SMOKE can suna aiki”

 

Ɗaya kuma ta yi alamar ya ce “Ƴan wahala, coustom sun gama gyara musu hanya, da sun je za su wuce”

 

Ta koma wajen da tayi alamar sauti na tasowa ta ce “Unknown resources”

 

Ta ce  “zasu iya kasancewa ma’adanai ne kawai? Ko kuma akwai wani abu bayan ma’adanan da suke ɗauka. Ka tambayi uncle bashir, a ina ya tsinto ni, ba zan ce takamaimai in da ya ganmu nan ne  aka sace mu ba, amma daga nan zuwa in da aka ɗaukemu, kwana uku nayi ina tafiya, sannan duk wanda aka kama a wurin da ma’adanan nan suke, sun san suwaye SMOKE!”

 

Jiki a sanyaye ya ɗauki zanen yana dubawa, rumaisa ta sake cewa “Nayi maka wannan bayanin ne, saboda naga you are curious about it. Amma still SMOKE ɗin na da nasaba da sace anty aisha, dan ita ba dan a karɓi kuɗin fansa aka kawota ba, dan a koyawa mijinta darasin da har abada ba zai manta ba aka kawota, ku kula sosai wannan aikin SMOKE ne. Shi ne abun da aka ce lokacin da aka kawota.

Papa idan har babu wanda ya san anty aisha ta dawo daga kai sai ita, dole-dole akwai na kusa da ita da ya sani, aka haɗa baki da shi, ko ta gayawa wani kai baka sani ba, ko kuma ka ƙara tsananta bincike a kan yaronka da aka kashe wanda shi ya tafi kai ta garin nasu”

 

Tamkar rumaisa ta zare masa lakar jikinsa, gaba ɗaya in da ya dasa hasashen binciken sa daban, abun da rumaisa kuma ta gaya masa dabanz to meye manufar ƙin yi masa wannan bayanan tun da wuri?.

 

“Mimi meyasa duk baki yi mini wannan bayanin ba tuntuni, ki ka bari nake ta wahala?”.

 

“Saboda baka buƙatarsa a lokacin da ka neme shi, yanzu ka mayar da hankali ka san suwaye SMOKE ɗin dai. Saura kuma ka je ka gayawa wannan abokan aikin naka, dan ka fiye yadda da mutane da yawa, yaya bashir kawai zaka gayawa, idan ba haka ba zan sake gaya maka komai ba”

 

Daga haka ta tashi ta bar shi da tufka da warwara.

 

Gaba ɗaya ya rasa nutsuwarsa da walwala, kwanyar rumaisa ba duk kai ba, rashin jin ta kawai mutane ke iya gani, amma ba kowa ke iya ganin baiwar da Allah ya yi mata ba.

 

Ita dai hankalinta kwance ta kwanta baccinta, amma adam bacci ya gagare shi, ya kasa zaune ya kasa tsaye ya kasa kwanciya yayi bacci, yama rasa me zai yi.

 

Yayi alwala, ya tayar da salla, yayi ta addu’a.

 

Har ya hau kan gadon zai kwanta, ya buɗe ya shiga kallon hotunan aisha.

 

Ya kashe system ɗin ya kwanta, rumaisa duk tana kallonsa.

 

“Papa”

 

“Mimi”.

 

“Ka kwantar da hankalinka dan Allah, zaka yi nasara, sai dai kar ka sanya ran ko komai ya bayyana zaka samu adalci yadda ka ke tsammani”

 

Bai ce komai ba, ya juya ya rungumeta sosai a jikinsa, yana ta jejjera numfashi.

 

“You are brave papa”.

 

“Yanzu kin yadda ba sakaci ne ya sanya ina jami’in tsaro na kasa karɓo Aisha ba?”.

 

Ta ce “Faɗa fa nake dan na baka haushi kawai, anty aisha ta gaya mini kai mutum ne mai yi wa iyalinsa hidima sosai”

 

Riƙe kunneta yayi ya ce “Daɗin me ki ke ji, idan kin ɓata mini rai ne?”

 

“Daɗin da ka ke ji idan kana tsokanata” ta bashi amsa.

 

Ya ce “Yauwwa kin tuna mini ma, bari in ɗora daga in da na tsaya, my mimi ƴan mata, budurwata ta kaina”.

 

Ƙoƙarin ƙwacewa take daga jikinsa, sai dai abu kamar wasa, Adam ya mayar da rumaisa cikakkiyar matarsa.

 

Wanda shi kansa abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba, kenan matsalar ta sa a cikin gidansa take kenan?.

 

Bayan gama jero sunayen ƴan gidansu, har da kiran ƙawayenta, banda cizonsa da ta din ga yi, kamar ƴar damusa.

 

Bayan shuɗewar wani lokaci, ya laluba ya ɗau wayarsa, ya kunna fitila ya haska fuskar rumaisa, da ta haɗa yawu da majina, da hawaye sai jan majina take yi tana kuka.

 

“Amarsu ta ango, finally budurwata ta zama matata, wannan cizo kamar damusa mimi” ɓare baki tayi, ta cigaba da kuka, tana wallahi sai na faɗa.

 

“Wa zaki gayawa? Ammi ko mama?”.

 

“Kowa na duniyar nan, kuma sai na rubuta kowa ya gani, kamar yadda na taɓa yi maka”

 

Ya yi dariya mai isar sa, kashe murya yana kwaikwayon ta ya ce “Yaya usy, mai sunan baba. Ai ko shi mai sunan baban, bai isa hana ni karɓar sadakina ba. Inyee ni dakata ma, nawa na baki sadaki? Ciko zan yi ko wani abu zaki rago mini?”

 

Ta ɗora hannu a ka, tana cigaba da kuka har da ta shiga uku ta lalace, shi kuma ya sakata a gaba, yana ta tuntsira dariya, bai taɓa ganin karaya ƙarara da miƙa wuya a wurin rumaisa ba sai yau.

 

Ya ce “Dan Allah ki goge wannan majinar mana, ƙazama, kin bayar da mata gaskiya” ya janyo ta yana goge mata hawayen fuskarta.

 

Buge hannunsa tayi ta ce “Wallahi yaya usy ne ya janyo mini, ya ce duk abun da ka yi mini ba haram ba ne, idan ban yadda ba zaka yi mini kishiya da shi da anty laila, suka ɗorani a hanyar da bata kamata ba”.

 

“Au zuwa ki ka yi ki ka gaya masa nayi miki wani abu?”.

 

Ta ce “Eh, duk abun da ka yi mini faɗa nake yi, wallahi Allah ya…..” Sai kuma tayi shiru.

 

“Allah ya isa, Usman ɗin ki ke yi wa Allah ya isa”

 

Ta girgiza kai. Ya ce “Ni?”

 

“Ni ban maka Allah ya isa ba”

 

Ya sake juyo da ita ya ce “Oyaa say thank you”.

 

“Thank you for what?” Tayi maganar tana mamakin rainin hankalin da yake mata.

 

“Thank you for everything i did, faɗi”

 

“Wallahi ba zan faɗa ba”

 

“Ok, naga alamar bakin ki bai mutu ba, am equal to you”.

 

“Na shiga uku, na gode Allah ya saka da alkhairi ya biya buƙata”

 

Yayi murmushi ya ce “Kowa ya tuba dan wuya ba lada, ya cikata” ya sauka ya nufi toilet.

 

Har ya fito tana zaune a takure, jikinta sai tsuma yake yi, tana ta tunanin ya ma za ta yi ne.

Abun gaba ɗaya ta rasa a wani muhallin za ta saka shi, anty laila dama tuntuni tayi mata bayani, usman ma duk da ba kai tsaye ya gaya mata ba, amma yayi mata bayani, amma ita dai sam abun ya zarce tunaninta.

 

Kamar zai tsayar da taxi ya ce “Sss” ta ɗago ta kalleshi.

 

“Zo”

 

Tayi shiru tana kallon sa.

 

“Magana fa nake” a hankali ta tashi tana raɓe-raɓe.

 

“Auren kenan mimi, ki daina hararata kamar zaki kai mini duka, ki shiga toilet ki yi wanka, kamar yadda ki ke na period, sai dai wannan akwai banbancin niyya”.

 

Karatun ajin su yasir ne ya faɗo mata, sai yanzu ta gane ina karatun ya dosa, a wancan lokacin kanta a doɗe yake. To idan haramun ne ai ba za a koyar a makaranta ba, duk da haka ai mama ba ta ce mini haka ba. Wata zuciyar ta tunatar da ita.

 

A haka ta gama abun da za ta yi ta fito, sai dai still ba ta daina kuka ba.

 

“Haba mimi, hawayen zai ƙare fa, is ok ya isa haka, zo in canza miki kayan sai ki kwanata ki yi bacci”.

 

Ta girgiza kai ta ce “Ni ba na so”

 

Ta canza kayanta, ta kwanta a ƙasa, wai ba zata sake kwana a kan gadon ba.

 

Ya tayar da salla, sai da tayi bacci, sannan ya ɗauke ta ya mayar kan gadon.

 

“Allah kai ka san dalilin da ya sanya ka ɗauki Aisha, ina tsaka da ƙaunarta, ka bani rumaisa, kuma ita ma ka sanya mini son ta, Ubangiji Allah ka jagorance ni a al’amarin nan, ya sanya ta zame mini sanyin idaniya, kuma ka bani ikon kula da ita” yayi Addu’a murya ƙasa ƙasa, ya shfa kanta yayi murmushi ya ce “Ni na cancanci in ƙara sadaki mimi”

 

Su da zasu yi kwanaki biyar, abu kamar wasa adam yayi burus da komawarsu, ya addabi rumaisa da sai da tayi dana sanin biyo shi, kuma ya hanata waya da kowa, ammi tana mita ta ce tana son ganin rumaisa suna shirin biki, ga sabir yana ta rigima  shi mimi.

Adam yayi mursisi ya ce aiki ne ya riƙe shi zasu dawo.

 

Tayi kukan, tayi rashin kunyar, tayi tsiwar amma babu wadda tayi tasiri, adam yayi burus da ita.

 

Yau suna kwance da safe, tana jin yana waya da laila, laila tana tambayarsa rumaisa, ya ce bacci take.

 

“Wai takawa ba zaka dawo da yarinyar nan ba?”

 

“Honeymoon muke” ya bata amsa.

 

“Ni ka ke gayawa haka, lallai baka da kunya, dan Allah a dawo mana da ita, wallahi we are missing her”.

 

Wata shida na barku tare da ita, dan haka a ƙyaleni.

 

“Anty laila”  rumaisa ta yi maganar kamar za ta yi kuka.

 

“Na’am mimi, ya kike?”

 

“Dan Allah ki saka baki ya dawo da ni gida, na gaji” tayi maganar tana kuka.

 

Katse kiran yayi, ya harareta ya ce “Da gaske faɗa musun zaki yi abun da nake miki? Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya hana, kuma Allah ya tsinewa mai tona asirin aurensa, sirri ne mimi ba a faɗa”.

 

“Ni wallahi a gida ba a ce mini haka ba”

 

“Amma laila ta gaya miki ai, kuma Usman ma haka, amma tun da haka ne shikenan, ina ga kawai wani auren zan yi”

 

READ ƘANWAR MAZA PAGE 80 HERE


Proceed with your download by clicking the below button

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button