Uncategorized

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars za ta rika yin wasannin ta a Katsina

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars za ta rika yin wasannin ta a Katsina

Kamfanin da ke kula da gudanarwar gasar kwallon kafa ta Firimiya a Najeriya, (League Management Company) ya bayar da umurnin mayar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars garin Katsina.

Kamfanin ya bayyana cewa daga yanzu kungiyar ta Kano Pillars za ta rika yin wasannin ta ne a filin wasa na Muhammadu Dikko dake cikin birnin Katsina.

Wannan dai na zuwa ne bayan hatsaniya da aka yi a satin da ya gabata yayin wasan kungiyar ta Kano Pillars da Rivers United a garin Kaduna.

Kungiyar ta Kano Pillars dai ta shiga matsala ne tun bayan da aka mayar da filin wasan ta na Sani Abacha dake garin Kano asibitin ‘yan Korona.

Daga nan ne aka mayar da kungiyar a garin Kaduna taba wasa kafin wannan sabuwar dokar.

Back to top button