🤡 FATALWAR DELU 🤡
Part 3
Kingboy Isah 👑
Short story
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
Mamaki ne ya isheni wato yar iskar yarinyar nan biyoni tayi baya da jaririn kenan. A zuciya nake tunani shin wai ma me yarinyar nan take nufi da ni ne? A ganina kamata yayi ta tafi da kaninta gida wajen sakarar uwarta wacce nasan yanzu haka tana can ta saki baki tana sharara bacci ba ta san an daukko mata jariri ana yawo da shi ba. To ai ni banma ga dalilin da zai sa in dau jaririn nan ba, fitowa nayi daga shagon na dauki jaririn na haska hagu da dama amma banga shakiyiyar yarinyar nan ba. Don haka na je karkashin itaciyar bedi na ajiyeshi na juya ina tsaki, har na kusa shiga shagon na daga murya da dan karfi na ce, “Wallahi idan kika sake zuwa kika buga mana daki zan nuna miki na fiki wulakanci”. Na fada hade da shigewa shago na kulle, bansan ko yarinyar taji ba ni dai na fada.
A karo na biyu bacci na fara daukata na sake jin bugon kofa, wannan karon ma na tashi da sauri na haska fitila na nufi kofar shagon, ina kokarin budewa naji karan gudu a waje. Haka ya tabbatar min irin na dazu ne, wato an ajiye min jariri a kofa an gudu. Haka ne kuwa ina bude shagon na leka wayam babu kowa amma ga jaririn nan an maido shi an ajiye, ja’irin ya daina kuka ya rufe ido da alama bacci yake yi. Don haka a wannan karon banma fito daga shagon ba na ja tsaki na kulle kofar na bar yaron a wajen. Ina ciza harshe saboda haushi da takaici a zuciyata tunanin irin hukuncin da zanyiwa yarinyar nan nake idan na kamata. A haka dai na sake kwanciya a karo na uku, nan ma bacci ya fara kwasata naji bugun kofar. Amma a wannan karon sai nayi shiru kamar banji ba, da naji karan kwankwasawar ma yana yawa sai na sa hannu na toshe kunnuwana.
Don na sha alwashin ba zan sake fita ba, ina nan a kwance an fi minti biyar ba’a daina bugawa ba ni kuma naki tashi in bude, gashi ina jin bacci amma buga kofa ya hanani baccin. Tashi zaune nayi na haska fuskar Bukar nayi mamaki da na ganta a rufe da alamu bacci yake, amma ai in ba baccin mutuwa mutum yake ba ya kamata ace dukan kofar nan da ake mutum ya tashi. Na dan jima a zaune ina gyan-gyadi jarababbiyar yarinyar kuma bata daina dukan kofar ba, don haka na tashi a fusace baya na yanke shawarar daukko jaririn in shigo da shi. Ko ba komai dai bacci nake so inyi watakil idan na dau jaririn ta sarara da buga kofar, in ya so da safe sai in ba Bukar labarin abinda ya faru a yi cigiya a nemi uwar jaririn. Ai kuwa ina sake budewa naji karan gudu, a wannan karon ma sai da na fito na haska amma banga kowa ba, don haka na dan daga murya ina masifa don haushi harda zage-zage.
Sannan na dau jaririn na shiga daki na kulle, kai tsaye na tsallake Bukar dake kan katifa a kwance zuwa dayan bangaren, dake nine a bangaren jikin bango, na kwantar da jaririn a tsakaninmu. Fatana daya ma kar garin bacci cikinmu wani ya latse shi ni ko Bukar. Ina kokarin kwantawa kenan na ji Bukar ya tashi tsaye da sauri ya bar kan gadon, ina kokarin kunna fitilar wayata na ga ya kunna fitilar shi yana haska jaririn yana dan ja da baya kamar wanda yake a tsorace. Na ce “Kai Bukar kar dai ka ce min ba bacci kake yi ba, tun farko kana jin buga kofar da ake kaki tashi”. Ido ya tsare ni da shi, ni banma fahimci ko kallon me yake yi mun ba. Sai kawai na tsinto muryarshi yana cewa, “Amma wallahi Nura bansan kai mahaukaci ne baka da hankali ba sai yau”. Shiru dai nayi ina saurarenshi, domin jin hauka da rashin hankalin da nayi.
Ai ko sai ji nayi ya ce, “Yanzu duk yadda nayi maka gargadi karka fita daga shagon nan kenan sai da ka fita? Wato ka dauka abinda nake fada maka duk karya nake kenan ko?”. Yar dariya nayi hade da cewa, “Dallah gafara yanzu da na fita na dawo din ba gani a raye ba? Haska jikina ka ga babu jini ko kadan balle a fara tunanin rasa rai”. Shiru dai yayi baice komai ba, amma daga yanayin kallon da yake min yana kallon jaririn na san cewa akwai abinda yake son fada amma bansan me ya hanashi fadi ba. Nan na dan kara bude fuskar jaririn hade da cewa, “Yauwa Bukar duba wannan jaririn ka ga ko kasan uwarshi a garin nan, wallahi wata sakarar yarinya ce ta daukko shi a daji na ganta shine ta biyo ni ta kawo shi saboda hauka da kauyanci irin nata. Ko kuwa dai yarinta ne ke damunta oho”. Na karashe maganar ina kara nuna masa fuskar jaririn da ta sha farar hoda, ni dai a hasashena watakil hodar kurajen zafi ne ma.
“Innalillahi wa’inna illahir raji’un”. Naji Bukar ya fada, ni dai na bishi da ido, na ga ba mutuwa na fadi masa ba da yake fadar innalillahi. Sai ji nayi ya fara magana kamar mai shirin kuka yana cewa, “Wallahi Nura nayi dana sanin barinka ka kwana a garin nan, da na sani muna gaisawa zan nemo mashin ko a ina ne ya kaika can bakin titi ka tafi gida. Wannan wane irin bala’i ne? Ina hankalinka ya tafi ne, da zaka ga yarinya da jariri yanzu tsakar dare wai har ma ka tsaya kulata maimakon ka fara gudun ceton ranka”. Har zuwa lokacin da ya kai aya a zancensa ban fahimci me yake nufi ba, amma dai nasan baya wuce batun shegen tsoron nan da ya sa a ranshi, don haka na ce, “Ka ga Bukar wannan jaririn da ita yarinyar da na gani mutane ne ba aljannu ba, nasan yanzu zaka fara batun fatalwa ko aljani bayan kai da kanka ka tabbatar mini baka taba ganin daya a cikinsu ba”.
Ina gama fadar haka Bukar ya ce, “Ni dai wallahi ba dani ba, barin dakin nan zanyi wa ya sani ko wannan jaririn fatalwar ne, kai ga ka mai tausayi ko? uban marayu wai har da daukko shi ka shigo da shi shago. To wallahi bari kaji tun kwankwasawar farko da akayi na farka, amma tsoro ya hanani tashi balle na tsayar da kai, nayi tunanin kana da hankali shiyasa na kyaleka, ashe baka da shi yanzu gashi ka je ka daukko mana jaririn da baka san mutum ne ko aljan ko fatalwa ba, ni wallahi da nasan haka ne tun farko ba zan barka ka fita ba ko da kunce ne da sai na rikeka ba zaka bude kofar ba”. Bayan jin dogon jawabinsa nayi murmushi nasan a tsorace yake kawai, watakil da ya kalli fuskar jaririn ma yana iya gano da macen da suke kama a garin nasu. Na tallafi jaririn da hannu biyu na mika saitinshi a tsayen da yake, hade da cewa, “Ka ga fa mutum ne to ba aljani ba, ni bana son shigen tsoron nan naka. Ba ka ganin jaririn bacci ma yake?”.
Maimakon ya karba sai gani nayi ya juya yana shirin guduwa, na daiji ya ce, “Wallahi ba zan karasa kwana a dakin nan ba kaji da shi”. Da gama fadin haka ya fara kokarin bude kofa, yana budewa na ga ya tsaya daga bakin kofa yana leka waje tamkar wani munafiki ko marar gaskiya, nan da nan kuma sai gani nayi ya banka kofar da karfi ya makala sakata, nan take na fara tambayar me ya hanashi fita, ko wani abu ya gani amma yayi shiru ya kyale ni. Nasan ba komai ya hanashi fita ba sai tsoron jita-jitar Fatalwar Delu mai kashe mutane. Tsaki naja na koma na kwanta, ina jinsa shima ya dan dade a tsaye tukun ya zauna, amma bai kashe fitilar ba ya dalle fuskar jaririn da ita. Ko me yake nufi oho, ina kallo ya fara gyangyadi da alama shima bacci yake ji, don haka nima na rufe idanu da nufin yin bacci. Cikin sa’a kuwa lokaci kadan bacci yayi gaba dani, amma me ina cikin bacci naji an dalla min mari, wanda yasa na farka daga baccin, zafin marin yasa na dafe kumatuna.
Idanu na fara rabawa, ina karewa dakin kallo domin gano mahalukin da ya mareni. Bukar dai yana can zaune a inda yake ya jingina da bango da alamu ya gaji da gyangyadin har bacci ya daukeshi bai ankara ba, amma yana rike da fitilarsa a haske. Don haka na san cewa ba shine ya maran ba, don ba ta yadda za’ayi a dan kankanin lokacin nan ya mareni kuma ya koma inda yake ba tare da naji motsin komawarsa ba. Idanuna suka sauka a kan dan jariri wanda har a lokacin bacci yake, raina ne ya baci ina shafa inda nasha mari a fuska. Tunanin rama marin nake a jikinsa amma kuma bani da tabbacin ko shine ya mareni. Dan kuwa na tabbata idan zargin da Bukar yake na cewa wannan jaririn aljani ne ko fatalwa zai iya marina dan daukar alhaki…………..
Abokan hira sai mun hadu gobe, zan cigaba.