*ASM Bk2040*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
…………Washe gari Fatuu na gama sallar Asuba bata koma bacci ba kasantuwar ranar Monday ce ta hau yin shirin tafiya School, Misalin k’arfe bakwae saura tana cikin yin breakfast jikinta sanye da Uniform wayarta dake a gefenta ta fara ringing ta kai hannu ta d’auka sunan Ya Haisam ta gani a screen d’in har saida ta d’an yi mamaki kafin tay picking, gaishe da shi tayi bayan ta d’aga ya amsa yay mata ta tashi lpy tace lpy Lou tambayarta yay k’arfe nawa zata je School tace mashi yanzu tana yin Breakfast ne sai wurin kaman k’arfe 7:15 zata tafi yace Ok zai zo ya kai ta daga haka yay cutting kiran, bin wayar tay da kallo bayan ta cireta daga kunne tana kallo can kuma ta d’an ta6e baki ta ajeta taci gaba yin breakfast d’in ta, K’arfe bakwae da Minti goma ya kira yace in ta gama yana waje ta amsa mashi da to dama Hijab kawae zata saka sai jakar goyon ta ta nufi gaban dressing mirror ta dan k’ara gyara fuskarta ta saka glass d’inta daga haka ta fita, sai da ta lek’a d’akin gwaggo tay mata sallama ta bata kud’in abun hawa da Abinci tace ta barsu Ya Haisam ne yazo zai kaita kuma dama akwae wasu canji zata yi break d’in dasu tana murmushi ta d’aga mata kai kafin tay mata Allah ya tsare ya bada sa’a ta amsa da Amin tana nufar Kopar fita, bayan ta shiga Motar ta rufe ta juya ta kalle shi yana sanye da jallabiya ash mai gajeran hannu da d’an murmushi ta gaishe shi fuska a sake ya amsa yana kallonta kafin ya juya ya ja Motar suka tafi, shiru ba wanda ya k’ara tankawa sai itace ke ta d’an kallon shi sai kuma ta juya duk yana lura da ita ta mirror can ta k’ara juyowa shima ya juya karaf suka had’a ido ya d’age mata gira yace “What?” d’an motsa baki ta fara yi a marairaice tace “dama akan wayan da ka siya man jiya ne” idonshi akan hanya yace mi ya samu wayan tace “ba komae, d..dama Kawu Amadu ne ya fad’i mana kud’inta to shine muka ga tayi kud’i da yawa don har gwaggo ma tana cewa zata yi maka magana kud’in sun yi yawa sosae” d’an guntun murmushi yay kaman bazai ce komai ba yana ta driving ita kuma ta kafe shi da ido can yay sigh yace “yanzu ya za’ai da shi kenan?” Da sauri tace “a barta kayi wani abun da kud’in” d’age gira yay yace “to in ba abunda za’ai da kud’in fa?” Tura baki tay yana kallon ta ta mirror a shagwa6e tace “ya za’ai ace ba abunda za’ai da kud’i?” shiru yay yana cigaba da driving da d’an murmushi akan face d’in shi ita kuma sai faman k’unak’uni take tana yamutsa Fuska sai kace abun tsiya akai mata bana Arziki ba duk yana kallonta ta mirror can taji yay sigh yace shikenan akwai yadda za’ai to, da sauri tace to ta kai hannu k’asa ta d’aukko jakarta ta bud’e dama ta sako wayar don ta bashi, fiddota tay ta maida jakar ta mik’a mashi d’an kallon wayar yay ya maida idon kan hanya taji yace “ai ba nine zan yi ba kece” da d’an mamaki kan fuskarta tace “ni kuma, to ni zanje in maida masu ne?” girgiza mata kai yay kafin yace “I mean zaki iya bayar da shi in baki so” waro ido tay da alamun Al’ajabin jin abunda yace ya d’an kalleta ya d’age gira alamun tabbatar da abunda yace d’in ta cuno baki tana mashi wani kallo batare da ya kalleta ba taji yace shi take harara a shagwabe tace ita ba hararan shi take ba, tasan tunda ya fad’i hakan ba amsa zai yi ba dole ta maida ita cikin bag d’in, Lokacin da suka iso ya parker tay mashi godiya tana niyyar juyawa ta bud’e kopar yace mata wait ta dakata ya bud’e glove box tana ganin kud’i zai ciro ta tsuke fuska bayan ya d’aukko 5k ya mik’a mata yace tay break tak’i amsa tana kallon shi yace ta amsa mana kawae sai ta fara jujjuya mashi kai tana mashi magiyar ya bassu gwaggo ta bata, bin ta da ido kawae yake yace tunda ya fiddo ta amsa sai ta k’ara kawae sai ta juya mashi k’eya still yay yanata kallonta irin abubuwan shagwabar nan da take yi ba k’aramin tafiya take dashi ba sai tai ta burge shi, jin yayi shiru yasa ta juyo ganin kallon da yake mata ne yasa itama ta kafe shi da nata idon suka cigaba da bin juna da wani irin kallo mai wuyar fassarawa dole Fatuu ta sare don bazata iya jurewa ba ba shiri ta sadda kanta jikinta duk yayi weak d’an guntun murmushin gefe yay ya kira sunanta ta amsa jin bai k’ara cewa komae ba yasa ta d’ago ta kalleshi alamar ta amshi kud’in Yay mata da kai sai ta kasa k’ara yi mashi gardama don duk ya kashe mata jiki a sanyaye ta mik’a hannun ya bata ta furta ta gode ta kai hannu ta d’aukko jakarta zata fita taji ya tambayi k’arfe nawa zasu tashi d’an kallon shi tay tace k’arfe biyu ya d’aga kai ta juya ta bud’e Motar ta fita, nufar class area tay tana yi tana waiwayen Motar yana kokarin juyawa har ya tafi, tunani iri iri a ranta har ta isa Class tana shiga Fauzy dake ta zuba idon ganinta ta mik’e da sauri ta nufo ta tana mata welcome ta d’an mata side hug Fatun na murmushi suka nufi seat d’in su, bayan sun zauna Fatuu tace da wuri ta taho kenan tace mata a’a ai tun jiya da daddare ta dawo suna haka malamin su ya shigo, basu k’ara samun daman yin hira ba har saida akayi break sannan Fauzy ta shiga tambayarta ya Haisam Fatuu tace mata shine ma ai ya kawo ta da d’an mamaki tace “kai haba, shi dae bai gajiya da yin hidima dake bawan Allah amman mudae ba wannan muka fi so ba kawae ya fito ya mana Wuff da ke don Allah” d’an ta6e baki Fatuu tay tace “Uhm ai ke Fauzy wannan ba komae bane hidima ai sai jiya da muka fita dashi” cike da k’aguwa tace “ya kai bani in sha” nan Fatuu ta kwashe komae na kayan da ya siya mata har zuwa wayar daya siya mata hannu Fauzy tasa ta rufe baki da tsananin mamaki ta maimaita sunan wayar Fatun tace wllh bari ma ta gani ta kai hannu ta d’aukko jakarta bayan ta bud’e ta zura hannu ta fiddo da kwalin wayar ta mik’a mata, zaro ido Fauzy tay baki bud’e da d’an k’arfi tace “Wllh iPhone 15 d’in ce da gaske” wannan Maganar da tay ta jawo hankalin yan seat d’in bayan su wata Aisha ta ja hijab d’in Fauzy ta waiga tace taji tana iPhone 15 su ganta ta mik’a masu kan kace mi sauran wad’anda suke cikin ajin basu fita break ba harda maza duk suka taso ganin wayar ana tambayar wake da ita Fauzy na nuna masu Fatuu wani harda cewa ashe dae ita big girl ce mai babbar harka haka, wata student ma tace ashe dae ita babbar Hajiya ce basu sani ba wani dake gefe ya tambayi wai nawa take ne 15 d’in na kusa dashi ya bashi amsa nan fa wasu suka zaro idanu wasu suka hau jinjina kai, lokacin da Fauzy ta amshi wayar ta juya don ta ba Fatuu ganin yanayin fuskar ta yasa ta tambaye ta lafiya miya faru ne kaman zatayi kuka tace “ni fa Fauzy ban so aka san da wayar nan ba wllh don ni tsoro nike ji ina zaman zamana in ja ma kaina bala’e” dafa Shoulder d’inta tay tace “in sha Allahu ba abunda zai same ki ki kwantar da hankalin ki” a sanyaye tace Allah yasa, don ta k’awar mata da damuwar tace “Amman fa gaskiya Zarah ina tunanin Ya Haisam son ki yake wllh” waro ido Fatuu tay tace “ke waya fad’a maki da har zaki rantse” tace”uhum haba Zarah kiyi tunani mana nasan ba yau ya fara maki hidima ba amman fa hidiman ta canza salo ke baki fahimta ba tunda yake dake ya ta6a maki hidima irin wannan ya d’auki abun har million kacukam ya baki, je ki asa ma shi mai yawan Alkhairi ne mizai sa bazai siya maki wata irin waya ba tunda gasu nan iri iri in ma masu uban kud’i ne duk akwae su amman sai ya za6i wannan da fitowarta kenan kuma ba kowa ne zai iya riketa ba ke in ba don kina da wani matsayi a wurin shi ba da yafi wanda kika sani taya zai maki hakan?” bin ta da ido kawae Fatun take dama kanta duk a d’aure yake game da sabbin abubuwan da yake mata Fauzy ta ci gaba “ba fa wani abun mamaki bane don ya kamu da son ki kema da ai yadda ya d’auke ki kika d’auke shi ko ta zo ta canza zani to shima d’in zai yuwu hakan ce ta faru dashi ni wllh in hakan ta kasance sai nafi kowa farinciki ko ba komae Allah ya amshi Addu’ar mu zuciyarki kuma ta samu abunda take muradi” sai lokacin Fatuu tay d’an murmushi had’i da yar ajiyar zuciya,
“Yanzu ace sai ya bayyana maki yana son ki kuma yana son kuyi aure zaki hak’ura da karatun ki bi shi?”Fauzy ta tambaye ta had’i da d’age gira wani kallo Fatuu ta jefa mata kafin tace “har ma sai na baki amsa ai kema kinsani” dariya Fauzy ta sa tace “baki tsoron matar shi kawae sai ta ganki da mijinta matsayin Matar shi?” Fatun tace “to ai cewa kikae in yace yana sona kuma ya aure ni kinga tunda shi ya 6allo ruwa ai shi zai san yadda zai da ita ko” duk suka sa dariya Fauzy na fad’in uwar wayo wato shi yace yana so sai kace ita irin bata so d’in nan Fatun na dariya tace to ai irin hakan saida basaja suka ci gaba da dariya har Fauzy na Addu’ar Allah ya nuna mata ranar da zaice yana son ta a kur kusa Fatun tace shida ma zai tafi yau tace ai duk inda yake zai iya furta mata hakan ba wata matsala bace, daga baya Fatun tace suje suyi break lokaci nata tafiya kar a dawo suka tafi, k’arfe biyu daidai Haisam ya kirata yace yana inda ya ajeta da safe, tare da Fauzy suka taho suka zagaya d’ayan side d’in Fatuu ta bud’e gaban ta shiga Fauzy ta leka tana murmushi ta gaishe da shi fuska a sake ya amsa mata tace Zarah ta fad’a mata yau zai tafi Allah ya kiyaye a gaida Aunty Fanan ya amsa da Ok zata ji daga haka tace ma Fatuu sai sun had’u Gobe tace to, tun bayan da ta shiga cikin Motar ta gaishe da shi ya amsa bata k’ara cewa komae ba har suka hau hanya can ta kalleshi tace “sai k’arfe nawa zaka tafi?” Fuska sake yana kallon hanya taji yace ta k’osa ya tafi ne da sauri tace a’a ta dae tambaya ne kawae gyad’a kai yay suka d’an yi shiru sai kuma taji yace “ko za ki ne?” da sauri ta kalleshi tace ina yace “U.s” d’an bud’a ido tay tace “ni da nike karatu” shiru ya d’anyi still bai kalleta ba can yace “da ba karatun za ki je kenan?” itama shirun ta d’an yi har saida ya d’an juyo ya ce mata bata ji bane cike da jin kunya a hankali ta d’aga mashi kai alamar eh kawae sai gani tay yay d’an murmushi ya maida idon shi kan hanya saida ya d’an d’auki lokaci sannan ya sake cewa “kin daina tsoron matana kenan” tsuke fuska tay ta d’an tura baki tace “ai ni dama ba tsoron ta nike ba kawae dae ina ganin in naje bazata ji dad’i ba taga bamu had’a komai ba na bika har can karshe ma ta koro ni” d’an murmushi yay kafin yace “to yanzu da kika ce da ba karatun zaki kin daina tunanin zata ji ba dad’in ne?” d’an watsa hannu tay tace “to ai kaine ka tafi dani ko bani nace ba in ma taji ba dad’i kai kasan yadda zaka yi” wani kallo ya juyo yay mata duk sai tasha jinin jikinta ta fara sussuna kai kamar daga sama taji yace “yanzu in tafi dake d’in kenan?” Da sauri ta kalleshi suka had’a ido ya d’age mata gira alamar ta bashi amsa da sauri ta girgiza mashi kai tace “ni fa ba so nike in bika ba tun farko na tambaye ka lokacin da zaka tafi ne don in raka ka Airport” murmushi kawae yay yaci gaba da driving d’in shi itama ta juyar da kanta taci gaba da kallon hanya har suka iso gida ba wanda ya k’ara tankawa tay mashi godiya ta d’auki jakarta tana kokarin bud’e kopar ta ji yace mata before 4:30 zai tafi ta d’aga mashi kai ta fita yaja Motar ya wuce gida. Tana shiga gidan ta wuce d’akin gwaggo tay mata sannu da gida anan ta sanar mata zancen tafiyar Haisam gwaggon tace bari ta tashi to taje tay mashi sallama, d’aki Fatuu ta nufa ta aje jakarta kafin ta wuce kitchen ta zubo Abinci ba wani mai yawa ta ci ba don sunci abubuwa sosae da break ita da Fauzy tana gamawa ta wuce toilet don yin wanka, Misalin karfe hud’u da yan mintuna lokacin angama sallar la’asar Fatuu ta isa part d’in Haisam tana sanye da riga da skirt na atampa mai jajayen flowers had’i da mayafi mahad’in su tayi d’aurin kallabi mai kyau ga glasses d’inta manne a idanun ta, a hankali ta tura kopar parlon ta shiga da yar sallama idanun ta suka sauka kan Abbas dake zaune kan L-shape yana sanye cikin k’ananun kaya kasumbar shi tasha gyara gashin sai kyalli yake suna had’a ido suka sakar ma juna murmushi yace mata ta shigo mana tayi tsaye a bakin kopa ta nufi armchair ta zauna ta gaida Abbas d’in da murmushi ya amsa mata ta tambayi Abdul yace yana school bai dawo ba da yake yana yin lesson ta jinjina kai shiru suka d’an yi ta juyar da kanta can taji yace tazo raka mutumin nata ne d’an murmushi tay kawai bata ce komae ba shima yar dariya yay bai k’ara cewa komae ba can kuma sai ya mik’e yace yana zuwa in Haisam ya fito tace mashi yana Mota ta d’aga mashi kay ya nufi hanyar fita, after few seconds sai gashi ya fito yana janye da d’an trolley da kuma jakar laptop yana sanye da kananun kaya kai idonta tay kan shi har ya k’araso cikin parlon ya tsaya gefenta yana kallonta ganin hakan yasa ta mik’e tana cigaba da kallon shi da d’an murmushi ta gaida shi ya amsa ta fad’a mashi Ya Abbas yace yana Mota yana dai ta kallon ta tana Maganar kawae sai ji tay slowly yace “baki tsawo ne?” bud’a ido tay alamar mamaki sai kuma ta d’an tura baki tace “duk tsawon da nayi, dafa a iya nan d’in ka nike yanzu kuma kad’an ya rage in kawo shoulder d’in ka” tay Maganar tana nuna mashi inda ada tsawonta yake a jikin shi daga inda take, shiru bai ce komae ba yana cigaba da kallonta fuska a sake ganin bai ce komae ba yasa a d’an shagwa6e tace “to tunda baka ganin tsawona kai sai ka samman naka tunda kana dashi kai sosae” shirun dai yay sai kuma ya d’age gira yace tana so ta d’an k’ank’ance ido ta d’aga kai alamar eh, aje jakar laptop d’in dake a d’ayan hannun shi yay kan d’ayar armchair d’in dama ya saki trolley d’in tunda ya tsaya kawae sai gani tay ya kai hannu d’aya ya jawota jikin shi a razane ta zaro ido tana kallon shi shima haka still holding onto her motsa baki ta fara amman ta kasa cewa komae bata ankara ba sai ji tay ya ida yin hugging nata sosae ta yarda har ya d’aura Ha6arshi a saman kanta, zaro ido Fatuu tay ta d’an bud’e baki alamar Al’ajabi k’amshin turaren shi ne ya cika mata hanci har bata san lokacin da slowly ta lumshe idanunta ba zuciyarta ta fara melting sun d’an d’auki lokaci a haka can wata zuciyar ta fara raya mata hakan fa da sukae ba kyau miyasa zata bari ya rungume ta haka bacin tasan ba matar shi bace ita ko har ta manta da labarin yaudarar da aka ma Fauzy ne da sauri ta bud’e idonta jin tana kokarin d’ago da kanta yasa shi cire beard d’in nashi daga saman kanta ta d’ago ta kalle shi sam bazata iya karantar yanayin fuskar shi ba, ganin baida niyyar sakinta yasa ta kira sunan shi cikin disasshiyar murya ya d’an bud’a ido alamar amsawa da ido tay mashi nuni da rok’on da yay mata alamar ya saketa ya kafeta da ido kamar bai gane mi take nufi ba hakan yasa ta d’an 6ata fuska sigh yay slowly ya saketa had’i da furta “am sorry” shiru tay ta sadda kanta ya kai hannu zai kama trolley d’in ta d’ago tace mashi bari ta rike bai ce komae ba ya d’auki jakar laptop d’in yay gaba ita kuma taja trolley d’in tabi bayan shi, saida suka je part d’in Hajiya harda Abbas ta rako su har bakin Mota tana ma Haisam Allah yasa a sauka Lafiya ya gaida su Farha da yake Lagos zai sauka daga can gobe zai wuce Us, Abbas ne ya shiga driver seat sai Haisam na gefen shi ita kuma Fatuu ta shiga baya ya tashi Motar Hajiya nata d’aga masu hannu har suka fuce, bayan sun hau hanya sama sama Abbas da Haisam d’in ke yin hira can Abbas ya kalli Fatuu ta cikin mirror yace “Mom Zarah yau ba kuka kenan Ya Handsome zai tafi” dariya tay mashi bata ce komae ba Haisam ya d’an juyo ya kalleta ta rufe Fuskar ta da gyalen ta Abbas duk yana kallon ta ta cikin mirror yana dariya yace “yakamata yau ma a d’an rera mana gaskiya” d’an tura baki tay tace “ai ko wanccan lokacin ma don ina tunanin ya tafi kenan ko zai zo sai an dad’e” Abbas yace “Hajiya na raye ai dole zai rink’a zuwa ko don ita yanzu ma ai in ya tafi baza’a dad’e ba sosae zai dawo don akwai bikin wani Friend d’in mu da za’a yi bayan babban salla kuma shine best friend d’in shi a cikin musulmai” waro ido Fatuu tay tace shi kenan ba musulmi bane yace eh Christian ne d’an sarkin inyamurai ne sun d’an zauna anan amman yanzu ba’a nan suke da zama ba amman shi wanda zai auren shi ke kula da wasu wurare na mahaifin shi kamar Hotels da wasu kamfuna tare sukae Secondary da shi, jinjina kai Fatun tay kawae shi dai Haisam bai tanka masu ba, bayan sun iso Airport d’in gaba d’aya suka fito Haisam ya zagaya wurin Abbas ya bashi hannu yay mashi godiya shima yay mashi fatan sauka lpy ya juya ya kalli Fatuu dake d’ayan side d’in tana kallon shi da d’an murmushi shima yay mata daga haka ya juya ya tafi har ya d’an yi nisa Fatun ta k’wala mashi kira ya tsaya ya juyo ya kalleta da faffadan murmushi ta d’aga hannu tana yi mashi bye bye yana murmushi ya jinjina mata kai kafin ya juya Abbas dake dariya ya kalleta suka had’a ido ganin dariyar da yake mata yasa ta d’an cuno mashi baki yace shidae ai bai ce komae ba ta shige cikin Motar shima ya bud’e ya shiga ya ja suka tafi. Sati biyu da tafiyar Haisam aka fara Azumi saida ya turo mata kud’i masu yawa na siyan kayan Azumi tuni ta kai kayan da ya siya mata wurin Kb don a d’inka da aka fara Azumin har tana zolayar gwaggo wai ya taga bata da niyyar yi mata d’inkin salla tana dariya tace ai ita Haisam ya d’auke mata nauyin wannan kuma, a cikin kayan da ya siya mata taba gwaggon atampa da lace amman sai ta amshi lace d’in kawae tace ta bar atampar ta k’ara ba yadda bata yi da ita ba amman tak’i karba sai taba Fauzy ita kawai dama tana da wani material da bata d’inka ba ta had’a mata sosae Fauzy taji dad’in kayan tay ta godiya a tare suka kai d’inkin bayan Fauzy tasa Fatuu ta rakata itama shagon Zee ta siyo kayan sallanta har Fatuu ta k’ara siya mata wasu abubuwan Zee taji dad’in kawo mata Customer da Fatun tay har tay adding nasu a groups d’inta da take business koda zasu ga abu suna so, Alhamdulillah angama Azumi lpy ranar salla tare da Hajiyar Sanata harda Fauzy suka je Masallaci ko k’unshi ma tare suka je gidan su Nanah kamar kowacce Salla, da Fauzy gida zata tafi yin salla amman Saboda tana son su yi yawo tare da Fatuu ta fasa sai bayan sallan zasu tafi tare da Aunty Mareeya, su Fatuu an zama yan mata sun dai sha kyau da sallar abun ba’a Magana Tk ne ya kaisu wurare kamar yadda Haisam ya bashi umarni ko ina tare da Fauzy take zuwa har gidan Abbas suka je da sauran wurare sun sha zafafan hotuna da iPhone d’in Fatuu harda Vedios suka daddaura a status anan Haisam ya gani har ya yaba sosae taji dad’in yabon da yayi har saida ta kasa hak’uri ta ma Fauzy forwarding sai ga Voice note d’inta harda su shewa tana fad’in “Zarah da alamu mutumin nan fa ya kamu wllh kawae miskilanci ne ke d’awainiya da shi amman muje zuwa gab yake da ya shigo hannu” ita dae Fatuu dariya kawae take, har gida Aunty Mareeya tazo tayi ma gwaggo an sha ruwa lpy bayan salla haka ma Abbas ya kawo Feenah da suka zo gidan Hajiya, ana gama salla Fauzy ta tafi Funtua Fatuu taso ta bita amman gwaggo ta hana satin ta d’aya ta dawo suka koma Makaranta sun ci gaba da karatu ba tare da wasa ba a haka har babbar salla tazo wannan lokacin Yola gwaggo tace zasu je yin salla Fatuu taji dad’i sosae ana saura kwana biyu suka tafi Hajiya ma wannan karon saida babbar salla taje Abuja don da k’arama cewa tay bazata je ba ai bata dad’e da dawowa ba Fauzy a Katsina tay salla cike da kad’aici saida suka gama aikin naman layya sannan suka tafi Funtua, su Yadikko sun matuk’ar yin murna da zuwan su kar ma Mino taji ta kasa boye murnarta harda d’inki gwaggo tayi masu su duka harda baffan Fatun da shima yay farin cikin ganin su, kud’i masu yawa da zasu siya lafiyayyun raguna biyu Haisam ya turo ma Fatuu yace suyi layya harda kud’in da zatayi hidiman salla lokacin da ta kira don yi mashi godiya yake sanar da ita sun zo suna Abuja har tana ce mashi zai je katsina ne yace ai Hajiya bata nan kuma suma basu nan wurin wa zai je tace ai da an gama salla zasu koma yace suma bazasu dad’e bane amman yana nan zuwa bikin abokin shi da Abbas ya fad’a mata tace Allah ya kaimu, ana gama salla da kwana biyu suka dawo don ba wani Hutu suka samu ba just salla break ne, washe garin da suka dawo Fauzy ma ta dawo suka cigaba da karatun su.
A bangaren mutanen Us ma tuni sun koma lokacin Auren su ya cika shekara harda kusan wata a lokacin Fanan ta matsa lamba kan lalle sai suje a duba lafiyar su ta bangaren haihuwa don tun auren su bata ta6a yin 6atan wata ba koda kuwa sau d’aya gashi tana period lpy lau, wannan karon ma dai kaman sauran lokutta Haisam d’in cewa yay basu bukatan hakan yanzu ta bari a k’ara lokaci in bata samu ba sai su je amman shi a wurin shi still yayi wuri amman tak’i gaba d’aya ta burkice mashi wai dole tasan wani cikin su bai rasa matsala tunda har sun shekara amman har yanzu batai conceiving ba, sosae ta hana mashi zaman lafiya harda su koke koke to shi mutum ne mara son yaga wani cikin damuwa balle ma ace shine sila hakan yasa yace tayi duk abunda ya kamata sai su je d’in, sosae taji dad’i ba 6ata lokaci tay making appointment da Doctor d’in da zasu gani a Asibitin da take aiki washe gari suka je aka fara masu diagnosis daga baya kuma yay referring nasu wani Asibitin suga Fertility specialist anan aka cigaba da yin binciken tun daga Family history nasu ko akwae wanda bai haihuwa zuwa su awon jini da hotuna sosae akai investigations saidae an fi yi ma Fanan don ita yake ganin kaman in ma matsala ce to daga ita ne sakamakon wasu tambayoyi da yay mata sai washe gari suka gama likita ya fara masu bayanin result na binciken da akayi masu anan yake fad’i masu Fanan ce mai matsalar don tana da Polycystic ovary syndrome (PCOS) Wato matsala ce data shafi kwan da take saki har saida Fanan ta firgita jin wannan Maganar a razane tace how comes ita da take having regular periods! Shima Doctor d’in yayi mamakin hakan daya kasance bata ga wani symptoms ba don yawanci indai mace nada matsalar to zata rink’a samun irregular periods ne bazata rink’a yin period very often ba saidae kuma a tambayoyin da yayi mata farko ta tabbatar mashi wani lokacin periods d’in yana d’an dad’e mata in yazo amman bata maida kai kan hakan matsala bane don tun kafin tay aure ma tana hakan wanda hakan ma na daga cikin alamomin matsalar tata sai kuma a Family history nan ma ta tabbatar mashi da Kakarta wato Hajiyar Sanata tana da Matsalar yawan miscarriage lokacin tana haihuwa hakan yasa iya yara biyu ta Haifa a rayuwarta daga Mahaifin Haisam d’in sai kuma Mahaifiyarta hakan ma ya k’ara tabbatar da yuwuwar tayi gadon matsalan ne daga wurinta, tuni hawaye suka wanke mata fuska don tasan tabbas indae tanada wannan matsalar to zata iya hana ta samun ciki balle harta haihu rarrashinta suka fara yi suna bata hak’uri Doctor yace bai kamata ta tashi hankalinta ba tunda is treatable za’a iya dacewa ta samu cikin nan ya shiga bata shawarwari da abunda yakamata ayi, tun bayan da suka baro Asibitin take ta cizgar kuka tana fad’in “Ya Haisam am barren! I cannot give birth I can’t give u child!!!” Duk ta firgice abunka da fara jijiyoyin kanta duk sun firfito fuskarta ta yi jajir ya kai hannu ya ruk’o nata yana d’an murza shi alamar rarrashi sai faman kuka take tana fad’in ta bani bazata iya haihuwa ba shikenan bazata bashi d’a ba har shakewa take wurin yin Maganar Saboda kuka shi kam sai faman rarrashinta yake a nutse yake fad’in ta kwantar da hankalinta hakan ai ba yana nufin kwata kwata bazata haihu bane Allah na iya nuna ikon shi a kowane lokaci a haka har suka iso gida still yana ruk’e da hannunta suka shiga Parlor a saman 3 seater suka zauna ya rungumeta yana cigaba da rarrashinta sai faman fad’in tasan da wuya ta haihu tunda tayi gadone kuma gara ita Hajiya ma tana yin miscarriage amman itafa ko sau d’aya bata taba samun cikin ba balle ma tayi 6arin, suna cikin hakan can ya ji ta tayi tsit kamar ba ita ke rizgar kuka ba da sauri ya d’ago fuskarta da tay jage jage yaga idanunta a rufe alamar ta suma a razane ya mik’e ya kwantar da ita akan kujerar ya nufi fridge ya d’aukko bottle water ya dawo bayan ya cire murfin ya d’an zuba a cikin hannun shi ya yayyafa mata a fuska sai gashi ta ja wata irin doguwar ajiyar zuciya da sauri ya rufe robar ya aje gefe ya duk’a a gabanta ya kai hannu yana d’an bubbuga face d’inta had’i da kiran sunanta slowly ta bud’e idanun suka k’ura ma juna ido can kawae sai ta k’ara fashewa da wani Sabon kukan daga kwancen tana girgiza kai hannu yasa yana shafa gefen fuskarta a hankali yaci gaba da rarrashinta can ta yunk’ura ta mik’e da gudu ta nufi d’aki ya mik’e ya bi bayanta……..
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.