Hausa novels

NIHAAD Chapter 74 By Khaleesat Haiydar Complete Novel

74

Tun da suka shigo parlon Mami ke kallon Hajiya Safeenah da mamaki, ko ba Hajiya Safeenah bace take gani, ita ko Hajiya Safeenah bata ma lura da Mami ba har ta zauna a parlon, Aunty Suwaiba ta fita dauko mata ruwa da abinci, Mami tayi karfin halin cewa “Safeenah??” Hajiya Safeenah ta juya da sauri zuwa direction din da aka kirata, buda baki tayi ita ma da mugun mamaki tana kallon Mami, Aunty Jamila tace “Lahh ashe kun ma san juna” Mami tace “Wai dama nan gidan ne za ki zo gaisuwa?” Hajiya Safeenah ta kasa cewa komai tsabar yanda mamaki ya cikata, Mami tayi er dariya tace “Ikon Allah, what a coincidence…” Hajiya Safeenah tace “Lallai kam ikon Allah” a hankali Mumy da ta zauna parlon tana kallonsu tace “Ashe kun san juna kenan” Mami tace “Kawata ce sosai Safeenah” Mumy tace “Allah sarki, To maa sha Allah” Babu wanda ya kara cewa komai a cikinsu, ko wacce da tunanin da take a zuciya, can Mami ta kalli Mumy warce ita ma tayi nisa tunanin da ta fada tace “Hajiya an kai maki kayan shayi daki, da kin daure kin je kin sha ko ba yawa, ki daina zama ba cin abinci” cikin sanyin murya Mumy tace “Toh” Daga haka ta mike ta wuce bedroom dinta, Aunty Jamila ta mike ta bi bayanta don hada mata Shayin, Mami ta kalli Hajiya Safeenah tace “Toh ya hanya Hajiya?” Hajiya Safeenah ta sauke ajiyar zuciya tace “Alhamdulillah, sai gashi mun hadu gidan rasuwar” Mami tace “Wallahi kuwa, amma marigayin kika sani ko uwar gidan tasa?” Hajiya Safeenah tace “Ita warce ta shiga ciki yanzu ita na zo ma gaisuwa” Cike da confusion Mami tace “Warce ta shiga ciki? To ai ita ce uwar Nihad, amma kuma i don’t understand, a ina kika santa? And kin saba zuwa gidan nan kenan kuma baki san Nihad ba?” Hajiya Safeenah ta kalli Mami ta kasa cewa komai da farko, can ta jinjina kai a hankali tace “My late father and her late father have the same parent amma kuma bamu taɓa sanin juna ba sai yau ta dalilin rasuwan mai gidanta na zo mata gaisuwa, ni dai kinga tun bayan rasuwar mahaifina mahaifiyata ta koma kasar Yemen da ni, a can na girma nayi karatu har nayi aure a can, i never had the privilege of knowing my paternal relatives gaba dayansu sai babban yayansu wanda muka zo yanzu tare da shi, shine ma ya kirani ya sanar min rasuwan nan yace min tunda ina Nigeria lallai in shirya in je gaisuwa don er uwata ce ta kusa amma bamu san juna ba” Mami ta rike haɓa cike da mamaki tana kallon Hajiya Safeenah, can a hankali tace “You mean Nihad’s mother is ur cousin??” Hajiya Safeenah dai sai kallon Mami take bata ce komai ba, Mami tace “Ikon Allah” Throughout zaman nasu a parlor babu me cewa komai cikinsu, Hajiya Safeenah ruwa kawai ta dauka ta sha a abincin da Aunty Suwaiba ta kawo mata… Mumy ta daure ta sha shayin da Aunty Jamila ta hada mata shi ma don Aunty Jamila ta tsareta ne a dakin, Nihad na zaune gefen gado ta tashi daga baccin da take, Mumy ta juya ta kalleta, sai kuma ta hada mata shayin a cup din da ta sha ta dauka ta mika mata tace “Ki sha, ki tafi parlor ku gaisa da bakuwa…” Nihad ta amshi shayin ta ajiye kan bedside drawer, a hankali ta sauko daga saman gadon ta nufi bandaki don wanke bakinta, Aunty Jamila tace “Ga abinci nan Maman Khalil ta kawo maki, sai ki hada da shayin” To kawai Nihad tace ta shiga bandakin. Bata tadda su Mumy da Aunty Jamila a dakin ba bayan ta fito, ta dau shayin amma ta kasa don bata da appetite gaba daya, it’s now completely dawning on her cewar da gaske ta rasa beloved Abbanta har duniya ta nade, ta goge hawayen da ya taru idonta ta tashi daga kan gadon ta dau Hijab dinta ta saka sannan ta fito parlon Mumy, a kan Hajiya Safeenah ta fara sauke ido a parlon, ta sunkuyar da kanta ta karasa ta durkusa saman Carpet tace “Ina wuni?” Cikin sanyin murya Hajiya Safeenah tace “Lafiya lau, ya hakuri??” Nihad tace “Alhamdulillah” Hajiya Safeenah tace “Toh Allah ya ji kansa ya gafarta masa” Nihad tace “Ameen” Mami dai sai kallon Nihad take, kamar yanda Hajiya Safeenah ma ke kallonta, Aunty Jamila da Aunty Suwaiba sai wata frnd din Mumy kadai ne a parlon, Mami tace “Kin ci abinci?” Nihad tace “Yanzu zan ci” Mami tace “To tashi ki je ki ci” Ta shi tayi ta koma dakin ta kwanta gefen gado, bata san sanda wani baccin ya sake dauketa ba alamar alluran bai gama sakinta ba. Karfe biyu saura Mami ta bar gidan bayan an mayar da flight dinsu zuwa karfe uku, Hajiya Safeenah kuwa dama sai gobe zata koma Abuja, Mami bata samu yin sallama da Nihad ba don har ta bar gidan bacci take. Wajen karfe biyar Nihad ta fito kofar gida ta dalilin kiranta da Khalil yayi ta wayar Aunty Jamila, tun da ta fito gate din yake kallonta, tana tafiya a hankali ta karaso gun motarsa, ya bude mata front seat ta shiga ta kulle motar, A hankali yace “When did u wake up?” Ba tare da ta kallesa ba tace “30 minutes ago” Ya juyo da ita yana kallonta ita ma tana kallonsa, ya kama hannunta murya can kasa yace “Nasan baki ci abinci ba ko?” Bata son yaga hawayen idonta saboda alkawarin da tayi masa, ya tada motar ya bar layin, wani tsadadden eatry ya kai ta, ya dau menu din wajen dake saman table bayan sun zauna ya mika mata yace “Zabar mana abinda za mu ci, kiyi mana order” Ta ɗan kallesa, sai kuma tace “Sai wa zai biya?” A hankali yace “Hajiyata” Murmushi kawai tayi, ya kira mata server din wajen, ta nuna masa abubuwan da zai kawo masu, Khalil dai sai kallonta yake har server din ya bar wajen, ta daga kai ta kallesa, ya kashe mata ido yace “Naga abinci me tsada kika yi ordering hope aljihunki da nauyi?” Tace “Idan ma ba nauyi u can wash dishes….” Murmurshi kawai yake bai ce mata komai ba, aka kawo masu abincin cikin some minutes, haka ya dinga distracting dinta da zance suna cin abincin, and he love the way she ate much, suna nan zaune Mami ta kirasa don tun dazu ya kira yaji ko sun isa gida lafiya, bayan sun gaisa tace “Don Allah ka ɗan dinga sa mata ido ta dinga cin abinci” Yace “Alright in sha Allah, ga ta nan ku gaisa” Ya mika ma Nihad wayar, bayan ta gaida Mami tace “Kun isa gida lafiya” Mami tace “Alhamdulillah, ki daure ki dinga cin abinci kin ji” Nihad tace “In sha Allah zan ci Mami” Sallama suka yi ta mika masa wayar. Sai dab da magrib suka bar wajen bayan ya biya bills din, yana parking dai dai kofar gida yace “Bari in shiga Masallaci” Tace “Toh” Ta bude motar ta sauka ya dau ledan takeaway da suka yi ya mika mata, ta amsa tace “Thank you” Ya sakar mata murmushi yace “You are welcome love” Sauke idonta tayi ta juya ta nufi cikin gate, ya kashe motar ya sauka. Mamaki ya cika Nihad ganin Hajiya Safeenah a parlon Mumy tare da Inna, ta gaishesu ta shiga cikin daki tana kallon Mumy dake zaune tare da Aunty Jamila, sa mamaki tace “Mumy bakuwar Mami bata tafi ba? Naga Mami ta tafi ita ai” A hankali Mumy tace “Ba bakuwa bace, gwaggwonki ce, she is my sister….” Nihad ta dinga kallon Mumy cike da confusion tace “I don’t understand ur sister, frnd din Mami ce fa, she is also staying in Abuja, and ta zo nan saboda Mami ne” Mumy bata sake cewa Nihad komai ba don ko magana me tsayi bata so, Aunty Jamila tayi murmushi tace “She is our cousin sister Nihad, ke may be kin santa a Abuja saboda Maman Khalil, mu kuma er uwarmu ce ta kusa ma kuwa” Nihad ta karasa kusa da su kana ganinta kasan ta rikice sosai tace “Ban gane ba Aunty” Aunty Jamila tace “Zauna ki ji yanda mu ke da ita” Nihad ta zauna gefen gadon tana kallonta, nan Aunty Jamila tayi mata bayanin relationship dinsu da Hajiya Safeenah, Nihad dinga kallonta babu ko kiftawa zuciyarta na bugawa, What?? Does it mean Nadeeyah second Cousin dinta ce kenan?? Duk a zuciyarta take wannan tunanin, Da yake su Mumy basu san komai kan auren da Khalil zai yi ba shi yasa basu fahimci abinda yasa Nihad ta daburce haka ba, Aunty Jamila tace “Ita ma Maman khalil din yanda kika yi mamakin ganinta a gidan nan haka tayi, ke a tunaninki saboda Maman Khalil ta zo gidan nan ko?” Nihad ta gyada mata kai a hankali amma ta kasa cewa komai don she is speechless, Aunty Jamila tace “Toh ba saboda ita bace, er uwarmu ce ta kusa sosai, kasancewar uwarta er yemen yasa bamu taɓa saninta ba, don a can suke da zama bana jin sun jima da dawowa kasar nan” Nihad dai ta ma rasa abinda zata ce masu, gaba daya jikinta yayi mugun sanyi, Aunty Jamila tace “She said tana da yarinya kuma tare suke a Abuja, kin san yarinyar ko?” Nihad ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, Aunty Jamila tayi kasa da murya ganin reaction din Nihad is weird tace “Ko dai wani abu ya taɓa hadaki da ita a Abujan ne?” Nihad ta girgiza kai da sauri tace “Aa, kawai nayi mamaki ne” Mumy dai kallonsu kawai take bata cewa komai don abinda ya dameta daban, Nihad ta mike ta fita daga dakin still in shock, tana fitowa parlor suka hada ido da Hajiya Safeenah warce ita ma tunani iri iri sun addabeta a zuciya tun bayan da ta san irin alaqarta da Nihad, Nihad ta sunkuyar da kanta ta nufi kofa tana tafiya a hankali ta fita, dakin Nihal ta shiga ta sameta tana bacci, zaunawa tayi gefen gadon dakin ta jinginar da kanta a hankali jikin gadon. Washegari karfe goma Hajiya Safeenah ta bar gidansu Nihad zuwa Abuja don ta kagu ta koma don ta hadu da Mami, kuma tun da ta zo har ta koma bata hadu da khalil a gidan ba, infact bai ma san ta zo ba don ba a gidan yake kwana ba. A kwana a tashi har Abba ya cika kwana ashirin da tara da rasuwa, zuwa lokacin kuma duk Allah ya sa ma family dinsa wani dangana na daban, sun amshi kaddaran rasa shi hannu bibbiyu, yan uwa da suka zo daga garurruka daban daban duk sun koma garinsu, gidan ya rage daga su sai su kawai, sai Inna da har sannan taki komawa gidan babban ɗan ta wanda kullum da daddare shi ma zai zo gidan shi ma, Aunty Jamila ma dai bata koma ba tana wajen yayarta sauran kannin Mumy ne suka koma gidajensu, Har a lokacin Umma na gidan amma zaman daki kawai take, ko nan da parlonta bata lekowa, a ko da yaushe ka shiga dakin nata zaka ganta zaune at the very far end a kan darduma da carbi a hannunta, Kamila kuwa kamar kar Abba ya rasu ta dawo hankalinta duk sabbin halayen da ta tsiro ta daina tunda dama ba bin jikinta yayi ba, Nihal ce kadai har yanzu bata daina kukan Abbanta ba safe, rana, da dare, ita kadai ce taki hakura, kullum zaka ganta babu walwala sai kuka, gwara Nihad ita cikin dare take nata kukan, duk don Nihal ta kwantar da hankalinta Mumy har cewa tayi Abba ya bar mata wasiyyan ya yafe mata duniya da lahira kawai Allah bai yi za su gana bane, amma Nihal taki yarda da hakan, ga Umma ko magana bata son mata a gidan, su ya farooq ma sama sama suke kulata, sai tayi kwana da kwanaki bata ga yayyin nata ba tunda yanzu dakin Mumy ta dawo gaba daya take Rayuwarta, result din su na final exams ma da ya fito sai da ta samu spill a almost duk courses din da ta dauka a semester din, ita da ko carry over bata taɓa samu ba a makarantar, wajen Mumy da Aunty Jamila kadai take samun relief a gidan, sae Nihad dake jan ta jiki ynzu, Aunty Maryam ta kira Mumy tun sanda aka yi rasuwan yayi sau hudu yanzu, kuma duk sanda ta kira zata sa Mumy ta ba Nihad su gaisa. Mumy ce zaune kan darduma da Hijab dinta har kasa hannunta rike da carbi, Aunty Jamila da Nihad ma suna dakin sai Nihal dake kwance idonta a rufe amma ba bacci take ba, Mumy ta kalli Aunty Jamila cikin sanyin murya tace “Ya kamata kuma ta tattara haka ta bi mijinta su tafi gida ko Jamila?” Nihad ta daga kai ta kalli Mumy da sauri sanin da ita take, Aunty Jamila tace “Gaskiya kam, tunda anyi sati hudu har da kwana biyu yau, kuma nasan saboda ita ne ma bai bar garin nan ba har yanzu, kar rashin hankalin namu yayi yawa” Nihad ta marairaice tace “Mumy ba sai anyi 40 days ba?” Mumy ta ɗan kalleta tace “Me za kiyi har 40 days a nan din?” Aunty Jamila tace “A duk inda kike kika ma Abbanki addu’a zai samesa ba sai lallai gidan nan ba Nihad, kinga Allah ya baki miji wanda ba ko wace mace ke samun irinsa ba a rayuwar nan, uwa uba ga danginsa mutanen kirki mutanen arziki, duk da matsayinsu amma kowa nasu ne babu girman kai ba komai, to kada mu zama kananun mutane mu yi ta ajiyeki a nan, gashi yau har sati hudu, don haka ki shirya gobe ya daukeki ku koma…” Nihad ta dinga kallonsu har hawaye ya cika idonta, tsoronta kar ta koma Abuja damuwar rasuwan Abbanta ya dawo mata sabo, don idan tana ganin Mumy da yan uwanta tana jin relieve sosai, Ta goge hawayen idonta cikin sanyin murya tace “Then can i go together with Nihal?” Aunty Jamila tace “Sai abinda mijinki yace” Nihal ta buda ido tana kallonta, a hankali tace “I will come but not now” Nihad bata sake cewa komai ba, haka Aunty Jamila ta sata gaba ta fara hada kayanta a akwati, Usman yayi sallama kofar dakin, Mumy da Aunty Jamila suka amsa masa ya shiga, bayan ya gaishesu yace “Mumy dama na shigo in gaya maki Abban Khalil ya samar min aiki a Nnpc na garin kaduna” Mumy da Aunty Jamila suka hada baki wajen cewa “Alhamdulillah” sosai suka taya sa murna, Mumy tayi masa addu’a sosai tayi masa fatan alkhairi, Yace “Nagode Mumy, Allah ya kara girma” Mumy tace “Yaushe zaka yi resuming aikin kenan?” Yace “Gobe lahadi za mu tafi kadunan tare da Farooq don shi ma zai koma aiki, on monday in sha Allah zan fara aikin” Mumy tace “Toh Allah ya bada sa’a, Allah ya tsare” yace “Ameen” Daga haka ya mike ya fita daga dakin, Aunty Jamila tace “Allah sarki, na taya sa murna sosai, Allah ya saka ma General da alkhairi” Tun da aka tura ma Usman offer din yaje ya nuna ma Umma a dakinta, ko gani bata yi ba bayan ta masa addu’a ta tasa ya je ya nuna ma Mumy a bangarenta. Aunty Jamila da Nihal na zaune parlon Mumy suna kallon wani movie Khalil ya kirata, ta daga wayar bayan ya gaisheta yace “Aunty dama zan zo da wani bako ne yanzu zai ma Mumy gaisuwa” Aunty Jamila tace “Toh sai kun zo” Nihad na can daki tare da Mumy da tun yanzu har ta fara mata nasiha ta yi hkuri ta zauna lafiya da mijinta kar ta basu kunya, gaba daya sun sa ta hada kayanta duk da dai basu ce ma khalil din gobe ya dauketa su tafi ba, tana son gaya ma Mumy auren da zai yi amma ta kasa don that’s her only nightmare ynzu, Aunty Jamila ta shigo dakin tace “Yaya ki fito za a maki gaisuwa” Mumy tace “Toh” daga haka ta mike ta nufi kofa, Nihad ta bi ta da kallo, lokaci daya hawaye ya cika Idonta, Mumy na shigowa parlon ta zauna tana kallon balaraben dake zaune, ya gaisheta da turanci ta amsa da fara’a, nan yayi mata gaisuwa, ya kuma yi ma Abba addu’a sosai, cikin sanyin murya tace “Ameen, thank you very much” Khalil ya gaida Mumy don duk ranan bai shigo gidan ba, Aunty Jamila ta tafi main parlor dauko ma baƙon ruwa don in dai Nihal ce ba tashi zata yi ba in ka bibiya ma hankalinta baya tare da ita, don a ko da yaushe zaka sameta absentminded barin idan ana kallo, Baƙon ya daga kai yana kallonta yace “Hi Nihad, i am so sorry for ur lost, may Allah SWT grant him aljannatul firdauss” Khalil ya ɗan yi murmushi ya kallesa da turanci yace masa ba Nihad bace sister dinta ce, Mumy ta tabo Nihal da bata ma san ana mata magana ba, Da sauri ta dawo duniyar tunanin da ta tafi, Khalil yace “Yana maki gaisuwa….” Ta kallesa duk da bata san abinda yace ba tace “Ameen nagode” Nihad ta fito daki don sarai ta dau muryarsa, ya daga kai yana kallonta bayan ta fito, tana Murmushi tace “Hi Ayman” Da Fara’a ya amsa mata, ta karaso ta zauna a parlon, nan suka gaisa yayi mata gaisuwa ta amsa ta masa godiya, yana nuna mata Nihal da mamaki yace “The resemblance is obvious, just complexion difference” Tana Murmushi tace “Yeah, she is my blood, her name is Nihal” Ya sake kallon Nihal yace “Nihal” Nihal ta kirkiri murmushi bata ce komai ba Yace “It’s nyc meeting with you Nihal” Ta gyada masa kai kawai, don bata son magana yanzu, Ayman bai wani dade a parlon ba, bayan ya sha ruwan da Aunty Jamila ta ajiye masa, yayi ma Mumy sallama ya ajiye mata dollar dari biyar, Mumy da Aunty Jamila suka yi masa godiya sosai, ya fita parlon tare da Khalil, Mumy na kallon Nihad da mamaki ganin yawan kudin da ya ajiye mata tace “Who is he?” Nihad tayi murmurshi tace “Sister din Mami namesake dinki ce ta hadani da shi farkon zuwana Abuja” Aunty Jamila ta buda baki tace “Lokacin basu san da aurenki da khalil ba?” Dariya kawai Nihad tayi bata ce komai ba, Aunty Jamila tace “Ikon Allah, to dama yasan khalil din ne?” Ta girgiza kai tace “Kilan sai daga baya, nasan Aunty Maryam ce zata gaya masa Abbana ya rasu shine zai ce zai zo gaisuwa, dama dai yana shigowa Nigeria but a Uk yake zama” Mumy tace “Allah sarki, Allah ya saka da Alkhairi, Allah ya bashi lada” Khalil bai dawo gidan ba sai dare, nan Aunty Jamila ta sanar masa gobe ya dau Nihad su tafi gida, ya dai yi shiru bai ce komai ba, komawa daki tayi wajen er uwarta, Khalil ya kalli Nihal dake juya abincin gabanta a parlon, yace “Ina wayarki Nihal?” Ta daga kai ta kallesa, sai kuma tace “Yana dakina” Yace “A kunne yake?” Ta girgiza masa kai don for more than a month now bata kunna wayarta ba, Yace “Ki kunna za a kiraki…..” Ta dai yi shiru tana kallonsa, yace “Kin ji?” Ta gyada masa kai kawai, Nihad ta shigo parlon rike da abinci ta kawo masa, ta ajiye gabansa ta zauna tana facing dinsa sannan ta dau plate tana debar masa abincin, shi dai kallonta kawai yake babu ko kiftawa, Nihal ta mike ta dau abincinta ta shiga dakin Mumy, a hankali Nihad tace “Should i add more?” Yayi kasa da murya yace “I want to feed on u, not rice and stew”

 

Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

 

Ur evidence via 07087865788

Download NIHAAD Complete Novel Document By Khaleesat Haiydar

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

Back to top button