Uncategorized

Yan Kannywood sun fara yin blue fim

 Wani abin mamaki yana shirin faruwa a arewacin kasar Nigeria a masana’antar shirya fina finan Hausa wato Kannywood, A karon farko an samu wani mashiryin wasan kwaikwayo ya shirya wani film mai suna Makaranta Hausa Film wanda gaba daya acikin shirin ana koyar da yadda ake Jima’i ne wato kwanciyar aure.

A tallan shirin Makaranta da aka nuna akan Youtube anga yadda wasan kwaikwayon yake nuna wata makaranta da ‘yan mata da samari suna karatu akan sanin Kwanciyar Aure, Acikin tallan, zakaga da kuma jin kalamai na batsa wanda ba a saba ji ba a fina finan Hausa.

         KARANTA WASU LABARAN

 An tsinci gawar wata Ɗalibar Jami’a Yar 300 Level an kwakule mata Idanun a wani Otal

 Scholarship Ƙarƙashin Ma’aikatar Ilimi Ta Ƙasa Da Kuma Hukumar Samar Da Lamunin Karatu Ta Ƙasa. 

  Gwamnatin Tarayya zata dauki karin Matasa 400,000 aikin N-Power

 Jaruma Nafisat Abdullahi Wadda aka fi sani da Sumayya ta bayyana ficewarta daga cikin shirin Labarina.

Sai dai wannan shirin tun kafin fitowar sa yagamu da kalubale da kuma suka daga wajen mutane dadama musamman masu bibiyar shafukan sada zumunta, shugaban hukumar tace fina finai ta jahar Kano wato Isma’il Na’abba Afakallahu yasha alwashin bin duk wata hanya da doka tabasu dama don suga ba a nuna shirin Makaranta Hausa Film ba, kamar yadda yafada shirin babbar barazana ce ga tarbiyyar al’ummar arewacin Najeriya.

Akwai dai fina finan Hausa da ake yawan zargin suna da tasiri wajen lalacewar tarbiyyar matasa wanda kuma ‘yan fina finan Hausa sunsha musawa cewa shirya shiryen nasu basa bata tarbiyya, asalima su suna koyar da tarbiyyar ne.

Sai dai idan za a fadi gaskiya shirin Makaranta wanda yake kusa da fitowa zai kawo babbar gudummawa wajen lalacewar tarbiyyar mutane a arewacin kasar Nigeria musamman matasa, yanzu dai mutane sun zuba ido domin suga za a fitar da Makaranta Hausa Film ko kuwa Isma’il Na’abba Afakallahu zai samu nasarar hanawa.

Kalli cikakken Bidiyon a ƙasa ta hanyar taɓa hoton.

Back to top button