Uncategorized

Macijine Shi Page 35-36 Hausa Novel

Na mammy kabeer

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 35/36

_______________Kallon- kallo naga matan nan nayi atsakaninsu, ko wacce tana jifar Æ´ar uwarta da mugun kallo, yayi  da zuciyoyinsu ke buga cike da mamaki .

” Habeebee ina kashiga? Me yasami rayuwarka? Na shiga damu matuÆ™a lokacin da muka wayi gari an nemeka anrasa ba Æ™asashen da bamu zagaye ba wajen nemanka, na sanya Æ™udede, kadarori,dama  kanfanunuwa na ga duk wanda ya kawo min koda labarin in da kake ne,amma bamu sami komai da ya shafeka ba,meke faruwa habeebee?”dattijon nan ya faÉ—a yana mai shafa fuskar Adeeb  hawaye na zuba daga idanunsa.

Ahankali Adeeb ya kamo hannun mahaifin nashi ,tare da sumbatar hannunsa ,sannan yace ” abie wasu abubuwan basu buÆ™atar afadesu,saidai kawai mubarsu cikin zuciyarmu, sannan muyi ta kallon azzaluman dake  neman ganin bayanmu  da bakin halinsu.” Adeeb ya faÉ—a yana mai kallon daya daga cikin matan dake tsaye aÉ—akin.

Kallone irin na duk abinda kike aikatawa akaina, na  sani kuma ki kiyaye ranar haduwarmu.

Ahankali naga matar cikin ruÉ—ewa da irin kallon da Adeeb ke mata,ta sanya gefen  mayafin dake kanta tana goge zufa daga goshinta ,kanta a Æ™asa.

Ita kuwa É—ayar mata cikin sassarfa ta karaso gaban Adeeb ,hannu tasa akan kumatunsa tana shafawa, hawaye ya gama wanke mata fuska.

“Hayatee nayi kewarka  fiye da yadda zan fadamaka, naji daÉ—i da Allah ya kuÉ“utar dakai daga sharrin mahassada” matar ta faÉ—a cikin kuka tana mai rungume Adeeb.

” Ammina” Adeeb ya faÉ—a cikin wata irin murya mai cike da kewa ,yana mai rungume matar daya kira da amminsa.

Matashinnan kuwa gaba daya ya haÉ—e fuska ,ba alamun fara’a ko murnar dawowar Adeeb gida atare dashi.zamu iya cewa ma bakin ciki yake da ganin Adeeb É—in.

Zama sukayi abakin gadon ,shida mahaifin nashi,fuskokinsu dauke da mafificin farin ciki da É—auki ganin juna.

” Habeebee ka bani labarin abinda ya faru” mahaifinsa ya faÉ—a yana mai kwantar da kan Adeeb É—in akan cinyarsa.

Kwanciya Adeeb yayi tare da kamo hannun mahaifin nashi kafin yace ” abie ,zan baka labarin komai daya sameni ,amma yanzu baka da lafiya ka huta kayi barci abie na” Adeeb ya faÉ—a yana sumbatar hannun mahaifin nashi.

Karanta Littafin >>> Macizai Ne Complete Novel

Dariyar farin ciki abie yayi tare da shafa kan Adeeb yace ” ai naji sauki yanzu kam ,wanda yayi silar kamuwa da cutar yazo ya bani magani,bana jin ciwon komai habeebee likita ,zaka iya tafiya” abie ya faÉ—a yana mai kallon likitan cikin fara’a .

Godiya likitan yayi cikin garmamawa ,yana mai taya sarki murnar dawowar Adeeb É—in gida,dan kowa yasan da batun bacewar Adeeb É—in.

Dubawa nayi cikin dakin naga ya rage daga sarki sai Adeeb da ammi,amma  É—ayar matar da saurayin nan tuni sun bar É—akin.

Fattu kuwa tana nan zaune afalon wannan matar ta sauko daga saman sarki cikin wani irin yanayi ,dan ko lura da fattu batayi ba, sai ƙoƙarin kiran waya take .

Ba jimawa kuma,saiga wannan kyakyakywan saurayin shima ya fito cikin fushi da bacin rai,kallonsa fattu keyi taba dan hango yanayin kama da sukayi da Adeeb,saidai ko kama ƙafar kyan Adeeb baiyi ba.

Harya gota inda fattu ke zaune ,sai kuma ya dawo da sauri ya tsaya akanta.

Fattu kuwa da sauri ta mike tsaye tana kallonsa.ganin irin yadda ya tsaya mata akai ƙerere.

Shikuwa saurayin nan mai suna,Rashad ,wani irin. Shegen kallo yake bin fattu dashi,tunda ga sama har kasa,wow wannan kayan fa  ?daga ina haka?ya faÉ—a cikin zuciyarsa yana mai kashewa fattu idanu.

HaÉ—e fuska fattu tayi tana mai turo baki tare da kawar da kanta gefe.

“Hi babe !” Rashad ya faÉ—a yana mai Æ™oÆ™arin kamo hannun fattu.

Da sauri fattu tayi baya tana mai turo baki tare da biye hannunta abayanta.

Murmushin gefen baki yayi tare da shafa gefen  fuskar fattu yace ” yanzu ina cikin hanzari amma zan nemeki,dan kin kwanta araina kuma yawuna ya tsinke” ya faÉ—a yana mai wucewa bayan ya sunbaci hannun daya taÉ“a fuskar fattu dashi.

Duk zancen da yake da larabci yake yinsa,dan haka ba abinda fattu ta fahimta cikin zancen nasa.taÉ“e baki tayi tare da binsa da harara , tana faÉ—in” Allah ya isa taÉ“a min fuska da kayi” ta faÉ—a afili tana mai murguda baki,sannan ta koma ta zauna.

Tana nan zaune shiru -shiru agurin nan ,tunanin take ko ina Hamma ya shiga ya barta anan?karfa taje tana zaune kawai taji anfara yankan naman jikinta,ga shegen sanyin falon duk ya isheta.

Wani irin ƙamshine ya doki hancin fattu,cikin sauri ta lumshe idanunta tare da budewa tana mai kallon ta inda tajiyo ƙamshin,

Masha Allah,wata kyakyakywar budurwace mai tsananin kyau da gayu,taci ado da wata doguwar riga baÆ™a ,mai tsayin  gaske ,dan saida wasu yammata kusa su shida dake Binta abaya suka riÆ™e kasan rigar,gaba daya wuyanta da hannunta hatta gashin kanta anyi masa ado ne da kwal,tayi kyau matukar gaske,kallo daya zakayi mata kasan tana cikin farin ciki,dan kuwa sai murmushi take,tana tafiya É—as-É—as cikin salo da yanga.

Kallonta kawai fattu keyi cike da tunanin wannan ɗin ko wacece?amma gaskiya ƴar gayuce ta gaske,nima nan gaba irin wannan kwalliyar zan riƙayi inji ta yanga abina.fattu ta faɗa cike da murmushi tana kallon budurwar.

Download >>> Ana Dara Ga… Complete Novel Document

Ita kuwa budurwa tana karasowa tsakiyar falon ,idonta ya sauÆ™a akan fattu,dammmm !taji  gabanta ya faÉ—i, wannan É—in kuma wacece?daga ina haka?me takeyi acikin babban falo?budurwar ta faÉ—a cikin zuciyarta ,tana mai jin wani irin tsabar fattu cikin zuciyarta,dan saitaga duk yadda take taÆ™ama da kyau wannan yarinyar tafita,saidai kawai tafi wannan wayewa da sanin duniya.

Kallon -kallo aka fara tsakanin fattu da wannan budurwa,ba abinda ya Æ™ara batawa  budurwar nan rai irin yadda fattu ta tsareta da ido,wato ko shakkar ta ma batayi.

Cikin takunta na isa da rangwada ta ƙarasa gurin da Fattun ke zaune,

Kallon wulaƙanci take yiwa fattu tana wani yamutse fuska.

” Wacece ke?

Budurwar ta faÉ—a cikin harshen larabci.

Kallonta fattu tayi ba tare da tace komai ba,dan bata san me take cewa ba.

Ran budurwar ne ya É“aci sosai,hannu tasa tare da fizgo fattu ta kama kwalar rigarta, cikin isa da gadara take faÉ—in” ke kinsan komi wacece ina miki magana kika shareni?ke Æ´ar uban waye marar kunya?”budurwar ta sake faÉ—a cikin fushi,

Fattu kuwa cikin jin zafin abinda budurwar tayi mata ta ballawa budurwar harara tare da ture hannun budurwar  daga wuyanta,tana mai murguda baki.

Gaba daya hadiman da suka taki budurwar nan zato ido sukayi,cikin tsoro da tausaya wa fattu ,dan ta tabka babban kuskure.

Zato ido budurwar tayi itama tana mai kallon fattu ,” kee!!! Ni kika turewa hannu?lallai minti babban kuskure.budurwar ta faÉ—a tana mai É—auke fattu da wani lafiyayyen mari, kafin fattu da gama dawowa cikin hayyacinta ta sake jin wani zazzafan marin a dayan kumatunta.

Wani irin azabar raÉ—aÉ—ine ya ziyarci fuskar fattu,cikin hanzari ta dafe duka kumatunta tana kallon  budurwar nan,nan da nan zuciyar Æ´aÆ´an Fulani ta motsowa fattu, ai batasan lokacin data É—aga hannu itama ta shararawa budurwar nan matuka har biyu ba…….

Download>>> Macijine Shi Complete Novel

Manage please my fans,

Wllh am seek.

Mrs babi ce💘💘💘

Back to top button