Kamfanin shafin Facebook na fuskantar matsala mafi tsanani a tarihinsa, inda ake cin karo da matsaloli wajen aiki da wasu daga cikin manhajojinsa na intanet a fadin duniya.
Sai dai kamfanin ya ce yana kokarin shawo kan matsalar.
Baya ga ainahin shafin na Facebook shi kansa, manhajar Messenger da Instagram su ma sun gamu da cikas.
Ba a dai gano abin da ke haddasa matsalar ba, wadda ta fara tun kusan karfe Uku na yamma agogon GMT, wato Hudu na yammacin jiya a gogon Najeriya da Nijar.
Masu amfani da shafin Facebook sam basa iya bude shi.
Manhajar Messenger ta waya tana aiki ga wasu amma kuma wasu ba ta yi musu aiki, amma kuma manhajar ta Kwamfutar tebur ba ma a samunta.
Matsalar dai ba ta shafi WhatsApp ba amman ance akwai barazana matsalar ka iya shafar whatsapp din da kuma Instagram.