Labarai

Fatalwar Delu Part 13

Fatalwar Delu Part 13

 

🤡 FATALWAR DELU 🤡

Part 13

Kingboy Isah 👑

Short story

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION

 

Cikin karaji na bude murya hade da cewa, “Uban waye ne wai da ba zaiyi magana ba”. Ai kuwa sai ji nayi an fara jijiga dan kyauren na karfe, ana neman balle kofar a shigo. Nan take wani sabon tsoron ya sake ziyartar zuciyata, na tabbata idan Surayyah ta shigo kashina ya bushe. Jiya na yaudareta da kalaman soyayya na kwaci kaina yau na tabbata in na shiga hannunta ba zata saurareni ba. Ai bansan lokacin da na fara karanto ayyatul qursiyyu ba, ai kuwa da fara karantawa muka ji mace ta kwalla kara a kofar dakin, daga bisani kuma kamar daukewar ruwan sama sai mukaji an daina jijigawa da buga kyauren shagon. Ni dai har lokacin ban daina karatun ba, sai da aka dauki lokaci da naji ba’a kara kwankwasa kofar ba na daina karatun hade da ajiyar zuciya. Na juyo na kalli Bukar wanda har lokacin yana rike da kafata na ce, “To sarkin tsoro sakar min kafa, in ma Aljanar ce ai gashi na koreta”. Sakin kafar tawa yayi ni kuwa ina ganin haka na ce, “Bari na leka in ga ko tana nan”. Ai ba shiri Bukar yayi wani tsalle ya tashi ya rikoni, kamar zaiyi kuka yake fadin, “Nura dan Allah ka rufa mana asiri, karka jawo mana mutuwa tun lokacinmu baiyi ba”.

Kadan ya rage inyi dariya da gaske na so in bude in duba amma Bukar ya hanani dole na dawo na kwanta ina fadin, “Ai shikenan sai ku dawo mu kwanta tunda ko waye mai dukan dakin ya gaji ya tafi”. Ina jin Bukar da Mati suna magana a hankali yayin da Bukar yake kara bashi labarin yadda na daukko jariri da tsakar dare a ranar da na zo gari. Shi kanshi Mati ya tsorata da labarin da Bukar ke bashi game da ni, sun dade a zaune sun kasa bacci ni kuwa tun ina sauraron hirar tasu har bacci yayi gaba da ni. Ban farka ba sai asuba lokacin da muka tashi yin sallah. Ko wajen bude dakin su Bukar a bayana suka labe sai da suka tabbatar na bude na leka babu kowa sannan suka fito suna sanda kamar munafukai. Da safe wajejen karfe goma ina kwance a dakin Bukar ina latsa waya sai ga Bukar ya fado dakin kamar wanda aka jefo shi, dan har sai da ya dan tsorata ni, na dago ina tsaki hade da cewa, “Haba Bukar wannan gudu haka kamar wanda mutuwa ta biyo”. Bukar yana huci ya ce, “Nura akwai matsala fa, yanzun nan daga gidan Mai Gari nake Hamsa’u ce ba lafiya tana can sai ririketa ake sai kace mahaukaciya”.

Da jin haka na mike tsaye ina fadin, “Subhanallah me ya sameta haka ta so muje”. Bukar ya riko hannuna yana fadin, “Tsaya kaji mana, zare-zaren da take babu abinda take fada face sunanka tana fadin wallahi in dai Nura ne ta hakura kar a kasheta, ta daina son Nuran”. Na tsaya kuri ina kallonsa, kana ya cigaba da cewa, “Abinda na fahimta in dai labarin da ka bani a kan Fatalwa Surayyah gaskiya ne tana sonka to wannan ba aikin kowa bane face ita”. Na danyi jim kadan kana na koma na zauna ina fadin, “Zancenka gaskiya ne, babu ko shakka ma Surayyah ce ta aikata haka domin jiya naje munyi hira da Hamsa’u bayan kuwa shekaran jiya ta gargadeni a kan karna sake kula wata ‘ya mace”. Bukar ya watsa hannu sama yana magana kamar zaiyi kuka, “Wallahi Nura ni dai zuwanka garin nan banji dadinsa ba ko kadan, gashinan sai bala’i kake jawo mana kala-kala”. Na danyi murmushi hade da cewa, “Idan kayi zuciya ka nemo min abun hawa mana yanzu kaga in ban bar muku garin ba. Ai nima ba son raina nake zaune ba”.

Da rana muna zaune karkashin bishiya nida Bukar bayan mun gama shan kunu, sai ji mukayi anyi sallama hade da cewa, “Kaine Nura ko?”. Na dago kai ina kallonsu, wasu gardawa ne su hudu a cikinsu na gane mutum daya shine saurayin da yaje wajen Hamsa’u taki kulashi jiya. “Eh nine Nura”. Na fada ina sauraren jin me zasu fadi. “Oya yanzun nan ka taso muje gidan mai gari ana nemanka, idan kayi gardama an bamu umarnin mu daukeka ta karfi da yaji mu kaika”. Wani gardi ya fada yana hura hanci. Bukar ya mike tsaye yana fadin, “Saifullahi lafiya kuwa? Me Nura yayi da yasa mai gari yake nemansa?”. “Idan anje can zakuji”. Wanda aka kira Saifu ya fada, ina jin haka na mike hade da cewa muje, duk da ina fargabar abinda ka iya faruwa idan naje amma haka na shiga gaba suka rufa min baya Bukar shima ya biyomu baya. Ko da mukaje gidan mai gari a kofar gidan na hangi wani dan guntun mutum baki wul da shi, duk ya daura fata da layoyi a jikinsa, ba sai an fadi ba na gano Boka ne ko kuma dan bori. Tsaye suke a kofar gidan shida mai gari da mutanensa. Suna ganina suka fara fadin yauwa ga shegen nan an kamo shi.

 

Nan take gabana ya fara dukan tara-tara domin kuwa bansan wace badakalar aka shirya mini ba, muna karasowa mai gari ya ce, “Ranka shi dade Boka Girgije ga yaron nan an kawo”. Nan take boka ya juyo yana kallona muka zubawa juna ido, ni kallon mamaki nake yi masa, tsabar muni a wajensa sai kace gwaggwan biri, ga shi gajera. A zuciya na ce ga shegen muni ga karya kuma ga sabo. Boka girgije yayi yar dariya kana yace, “Mugu a haka kun ganshi kamar na kirki, maye ne ya so ya cinye kurwarta ba karamar daba kukayi ba da kuka nemo ni da wuri da yanzu Hamsa’u ta bakunci lahira”. Ina jin maganar da Bokan ya fadi hankalina ya tashi, banyi aune ba sai ji nayi wannan matasan sun fara kai mun duka, ai kuwa nima na juya ina ramawa tare da kare dukan wasu, don kuwa ba zan tsaya ina kallo su lahantani ba. Rama dukan da nake shine ya fusata mutanen wajen, sukayi ca a kaina, na tabbata sunyi niyar illatani ne amma mai gari ya dakatar da su bisa umarnin boka na cewa kar a kasheni sai na saki kurwar Hamsa’u wai mu shiga gidan in saketa kafin a yanke min hukunci.

 

Ina huci na bi bayansu, zuwa cikin gidan mai gari yayinda suma matasa da sauran mutanen gari suka rufa mana baya, tun daga nesa na fara jiyo kukan Hamsa’u tana ihu tana fadin in dai Nura ne bata sonshi ta hakura da shi a barta kar a kasheta. A haka har muka shiga dakin da take ciki, wasu mata ne ke rike da ita yayin da kaskon turare da boka ya hayaka yake a gefe, Hamsa’u na daga kai ta hango ni nan take ta saka ihu ta rungume daya daga cikin matan da suke rike da ita da karfi tana fadin, “ku ce ya fita bana sonshi bana son ganinsa. Idan ta gammu tare zata dawo ta kasheni”. Boka yayi murmushi irin na yan iska hade da cewa, “Kwantar da hankalinki yar baba yanzun nan zamu rabaki da shi. Ku kwantar da ita ya tsallakata mayen banza da wofi”. Jin hakan yasa na ce, “Mai gari ina da magana wallahi ni ba maye bane, ko na tsallakata ba abinda zai faru amma…”. Kafin na karasa magana mai gari ya daka min tsawa hade da cewa, “Maza ka aikata abinda boka ya umarceka”. Ba muso na ce “To”. Duk kuwa da nasan ko tsallakawa dubu zanyi mata ba shine maganin ciwonta ba. Nan take na tsallakata sau uku kamar yadda bokan ya ce, amma a banza don haka boka yace sai na kara tsallakata. Haka kuwa akayi wajen sau uku ina maimaita tsallakata amma ihu da kukan da take bata daina ba.

Na kalli mai gari hade da cewa, “Mai gari dan Allah ka saurari bayani na, wallahi zan fadama asalin abinda na sani game da cutar Hamsa’u, nasan a dalilina abin ya shafeta amma wallahi bani na sa mata cuta ba kuma ni ba maye bane”. Boka ya daka min tsawa hade da cewa “Karya yake mayen banza da wofi, zaka saki kurwarta ko sai jikinka yayi tsami”. Ya fada yana zare min jajayen idanunsa. Da jin hakan matasa suka yo kaina da nufin fara dukana musamman saurayin Hamsa’u da taki kulawa domin shi har ya dau kulki. Mai gari ne ya dakatar da su hade da cewa, “Muna sauraronka yanzu ka fada mana minene dalili, bama wannan ba kuma taya za’ayi ta samu lafiya”. Na gyara tsayuwata hade da cewa, “Matsalar fatalwa ne watakil jiya ta zo ta firgita Hamsa’u shiyasa take cikin rudani har yanzu, amma bari na tofa mata addu’a watakil ta dan ji sassauci. Na nufi wajen Hamsa’u da nufin na danyi mata addu’a amma boka ya dakatar da ni yana fadin, aka kuskura aka barni nayi mata wani abu zata iya rasa ranta. Jin hakan yasa Mai gari ya daka min tsawa ya dakatar da ni. Na juya a fusace na kalli boka ina fadin, “Kai dai makaryaci ne, babu abinda ka sani to wannan yarinya ba wani mayu ko aljannu dake damunta, Surayyah ce yar Fatalwar Delu ta sa mata razani da tsoro ni ko sau dubu zan tsallakata ba zata warke ba domin bani da nasaba da cutarta”.

Mai gari ya dube ni hade da cewa, “Kai yaro miye hadin ‘yata Hamsa’u da Surayyah diyar Fatalwar Delu kuma?”. Nan fa na kwashe labarin fara soyayyarmu da Hamsa’u da kuma yadda muka hadu da Surayyah duk na fada musu, har haduwa ta biyu da kuma kashedi da tayi mun a kan cewa karna kara kula Hamsa’u amma tsautsayi yasa na kulata. Na kara da cewa, na tabbata wannan shine dalilin da yasa Fatalwa Surayyah ta kawowa Hamsa’u farmaki. Ko da jin duk labarin da na bayar Boka girgije ya kurma uba ihu hade da cewa, “Kai yaro karya kake, baka isa ka raina mana wayo ba, fatalwar Delu ni kadai ne nake iya fafatawa da ita kuma in tsira da raina, amma bayan ni duk wanda ya hadu da fatalwar Delu to fa kwanansa ya kare, don haka wannan labarin naka karyace zallah a cikinta”. Na girgiza kai kana na dubi mai gari na ce, “Yallabai wallahi duk abinda na fada gaskiya ne, kuma ga Bukar nan shine shaidata, tun a ranar da na fara kwana garin nan na fita daji tsakar dare kuma na dawo a raye”. Mai gari ya kalli Bukar dake gefe a tsaye. Tun kafin mai gari yayi magana Bukar yace, “Kwarai zancensa gaskiya ne, domin Nura baya jin maganata tun a daren da ya zo na gargadeshi amma baiji maganata ba haka ya fita, daga karshe ya kwaso mana bala’i na wani dan jaririn aljani cikin shagon da safe da muka tashi muka nemi jaririn muka rasa. Ni tun daga ranar ma ban kara kwana a shagona ba na koma shagon Mati da kwana, kuma ko jiya muna kwance munji ana ta kwankwasa mana daki tsakar dare. Kuma na tabbata wanda yake kwankwasa dakin ba mutum bane, domin Nura yana fara yin addu’a sai gashi an daina kwankwasawa. Hakan ya tabbatar min da cewa aljannun da ya kwaso ne suka biyo shi nan”.

Fatalwar Delu Part 7

Mai gari ya sauke ajiyar zuciya, shi kuwa Boka Girgija tsaki yaja hade da cewa, “Karyar banza wannan labari duk tatsuniya ce ba gaskiya ba, bincikena ya tabbatar min da cewa kai maye ne kuma kaine ka kama kurwar Hamsa’u, aljana Laiyyana ba zata mun karya ba”. Mai gari ya ce, “Saurara boka yaran fa kamar da gaskiyarsu, domin gashi ya tsallaka yar baba amma babu wani sauki, ya kamata mu sauraresu”. Ya maido hankali gareni hade da cewa, “Yaro yanzu ya za’ayi kasa ita Fatalwa Surayyah ta saki Hamsa’u ka taimaka ka fiddata daga cikin rikicinku kai da ita”. Na sauke ajiyar zuciya kana na gyara tsayuwata na ce, “Hakika wannan abu ne mai sauki, kuma bama Hamsa’u ba, akwai hanyar da za’a bi garin nan ya dawo dai-dai za’a rabu da fitinar Fatalwa Delu. Kuma ni nasan hanyar da za’a bi domin a rabu da ita”. Ina gama fadar haka naga mutane ciki harda mai gari sun cika da farin ciki, sabanin Bukar da na kalla naga ya tsura min ido a tsorace ga dukkan alamu ya gano nufina, saura kadan nayi dariya ganin yadda duk ya tsorace, amma na dake na cigaba da zancena ina cewa, “Hanyar kuwa daya itace, dole Bukar ya biyoni muje ya ba Fatalwar Delu hakuri da tsakar dare. Fatalwa Surayyah ta tabbatar min idan har Bukar ya je ya basu hakuri to zasu yafewa yan garin nan kuma zasu daina kashe mutane zaman lafiya zai samu garin nan, to kaga idan har mukaje a wajen zan saka maganar Hamsa’u itama zata warke ta daina firgita”.

Cikin shashekar kuka Bukar ya fara fadin, “Na rantse da Allah ba zan fita daji tsakar dare ba, ba ubanda zai sa in fita in kai kaina mahallaka wallahi, ba’a isa ba”. Yana fadin haka ya juya zai fita, nan take Mai Gari ya umarci wasu matasa suka rikeshi, mai gari ya dubeni hade da cewa, “Ka tabbata idan har Bukar yaje ya bata hakuri zata janye daga garin nan kamar yadda ka fada”. Na ce, “Kwarai yallaba, da haka tace sai ta kashe Bukar saboda shi kadai yayi saura a cikin wadanda suka kashe ita Delu din, amma da na rokar masa afuwa ta ce idan har yaje ya bada hakuri zasu yafe masa. Sannan domin tabbatar da tsaro ina rokon za’a hadamu da Boka Girgije yau da dare muje Bukar ya ba Fatalwar Delu hakuri, in akayi haka kaga ko da mun fuskanci wata matsala daga garesu sai Boka Girgije ya yaki ita fatalwar Delu”.

Boka yayi wani uban ihu hade da cewa, “Kai yaro karya kake, Fatalwar Delu hatsabibiya ce, ni kaina da kyar nake iya kare kaina daga sharrinta, don haka ina mai baku shawara karkuyi gangancin fita da dare, ga dukkan alamu tarko ne ta nada muku dan ku fada ta kasheku ku duka”. Mai gari na jin haka yace, “Haba Boka kowa a garin nan ya yarda da kwarewarka, karka sa mu fara tantama a kan kwarewar aikinka mana, rakiya fa kawai zakayi musu saboda gudun matsala. Ka sani idan fa tafiyar nan tayi nasara to fa dukkan kauyen nan namu ne zai sama lafiya”. Nan take Boka ya fara hura hanci ga dukkan alamu ranshi yayi matukar baci, musamman yadda naga yana watso min wata iriyar harara. Boka ya ce, “Na amince zan rakasu amma dukkan abinda ya faru karku zargeni domin tun farko na gargadeku”. Bukar kuma sai hawaye yake, ina kallonsa yana fadin, “Nura kar muyi haka da kai dan Allah, karka jani inda za’a hallakani”. Tausayinsa ya kamani amma bani da wata mafita a yanzu haka sai wannan, dole ne mu jaraba, domin hausawa na cewa da jarabawa jirgin sama ya tashi.

😅 Lalai kunsha jira, ba laifina bane.

 

Back to top button