Uncategorized

An Kamo Wata Matashiya Data Fara Tattaki Daga Bauchi Zuwa Abuja Domin Nuna Goyon Baya Ga Dan Takarar Gwamna.

 

Rahoton Daily News Hausa

An kamo Amira Ahmad mai shekaru 22 da fara tattaki daga Bauchi zuwa Abuja domin nuna goyon bayanta ga dan takarar gwamnan jihar Bauchi a jam’iyyar APC Farouq Mustapha da kuma karrama ‘yar dan takarar kan shiga cikin talakawa da yafi a taron da jam’iyyar APC ta gurdanar a Abuja.

Dan takarar gwamnan Farouq Mustapha, ya bada umurnin a dakatar da ita, ta koma gida zai biya mata kudin jirgi ko na mota domin taje Abuja ta sameshi duba da halin rashin tsaron da ake ciki.

Yanzu dan takarar ya bayyana a shafin sa na Facebook da cewa an samo nasarar kamo ta a garin Jos.

Related Articles

Ga abunda ya rubuta kamar haka; “A safiyar yau na samu labarin wannan baiwar Allah Amira Ahmad Bauchi ta fara tattaki zuwa Abuja domin karrama ni da iyalina. Cikin gaggawa na sanya Daraktan Kamfen dina ya bita, inda ya sameta a Jos. Ya dauketa cikin koshin lafiya kuma ya maidata gida wajen iyalinta”.

“Ina godiya ga Amira kuma zan gayyaceta zuwa zama na musamman tare da iyalina anan Bauchi”.

“Kamar yanda muke fadi tashi wajen inganta rayuwar iyalanmu, nauyi ne akan mu mu inganta rayuwar magoya bayanmu”.

Back to top button