Fatalwar Delu Part 15
🤡 FATALWAR DELU 🤡
Part 15
Kingboy Isah 👑
Short story
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
Ni kaina sai da na zabura, amma da na haska na ga bera ne kuma na juya naga halin da su Bukar suke ciki sai na kyalkyale da dariya. Ina dariya nake fada musu bera ne fa, Bukar da Boka babu wanda jikinsa baya karkarwa saboda tsoro. Boka ya janye Bukar daga jikinsa ya ci magani yana fadin, “Kai dai Bukar tsoronka yayi yawa, gashi garin ihun da kake ka firgita jaririn aljana Kundusa yana shirin guduwa, ihun da nayi magana ce nake yi masa a kan ya dawo”. Wata dariya na sake kyalkyalewa da ita, zuciyata ta fara bani lalai za’a sha drama a wannan daren, fatana dai yadda muka taho lafiya Allah yasa mu koma gida lafiya. Gaba mukayi a wannan lokacin Bukar yana biye dani kafata-kafarsa ya rike min riga daga baya kamar wanda zai gudu ya barsa. A dai-dai inda muka tsaya da Surayyah a waccan ranar na dakata hade da cewa, “Mun karaso, a dai-dai nan ta ce mu sameta”. Nan take na fara haske-hasken fitila domin ganin ta inda Fatalwa Surayya zata bullo. Su ma su Bukar haske-hasken suke cike da tsoro, yayin da boka ke furta wasu kalamai da ba’a fahimtar me yake fada.
Jin shiru bata bullo ba yasa na fara kwalla kira, “Surayyah, Surayyah, masoyiya Surayyah kina ina ne”. Kamar daga sama muka fara jin dariya wacce ta cika gaba daya dajin, murya na fita uku-uku. Abin tsoron ma shine ba zaka iya bambance muryar macece ko ta namiji ba, ta yaro ce ko ta babban mutum ba. nan take muka cure waje guda bayanmu ya hadu da na juna kowa yana haska ta bangarensa. An dan jima ana dariya zuwa can mukaji Bukar ya ce, “Ga… ga.. ga su nan sun fito”. Ya fada yana i’ina murya cike da tsoro, nan take muka juya da sauri ni da Boka muna haska saitin da suke. Su uku ne dukkansu cikin fararen kaya masu kama da likkafani, Surayyah sai kaninta da kuma wata dattijuwar fatalwa ga dukkan alamu itace mahaifiyar Surayyah kuma Fatalwa Delu. A dan nesa damu suka dakata har a lokacin dariya suke babu wanda ya tsayar da dariyar da yake a cikinsu. Ganin dariyar taki karewa yasa na dan matsa wajensu a tsorace ina fadin, “Yauwa masoyiya Surayyah kamar yadda nayi miki alkawari ga Bukar nan na kawo domin ya baku hakuri ku yafe masa, ina fata kamar yadda mukayi alkawari kema zaki cika ba zaku cutar da mu ba”.
Har na gama magana basu daina dariyar da suke ba kuma babu alamar zasu dakata, ganin hakan yasa da sauri na juya ga Bukar dake makale a bayan Boka Girgije yana karkarwa hade da lekenmu. “Bukar me kake a nan ne, maza ka tawo ka nemi yafiyarsu mana bisa laifin da ka musu”. Karkarwa kawai yake yaÆ™i motsawa daga inda yake, nasan cewa hakan zata iya faruwa, don bai taba yin ido da ido da fatalwa kamar haka ba, gwara ma ni nasha haduwa da ita musamman Surayyah da kaninta. Abinda dai ya ban mamaki shine ganin tsoro karara a fuskar boka, da na haskashi da kyau sai naga kamar kafufunsa ma kyarma suke. Ganin Bukar yaki tahowa yasa naje na jawo shi gaba, nan take na umarce shi ya durkusa domin basu hakuri, hade hannuwa yayi bayan ya tsugunna kan gwiwoyinsa murya na rawa ya fara fadin, “Dan Allah dan annabi ba dan halina ba ina rokonku ku yafe mini, wallahi na dade da yin nadama akan abinda na aikata muku. Kullum da shi nake kwana a raina ku yafe mini dan Allah”. Ya fada yayin da hawaye ke gangarowa a bisa kuncinsa, ni dai ban sani ba na tsoron ne ko kuwa na nadama.
Ko da gama fadin haka sai ji mukayi an daka mai wata irin tsawa wacce tasa dukkanmu muka zabura mukayi baya, cikin bacin rai da masifa ta fara fadin, “Karya kake yaro tsakaninmu da kai babu afuwa ko yafiya, dole ne na kasheka, bayan na kasheka kuma mutanen garinku ma ba zan barsu ba, su da zaman lafiya har abada”. Lokacin da na dago naga ba kowa ke maganar ba face Fatalwa Delu, tana gama fadin haka ta sake kyalkyalewa da dariya, daga bisani kuma sai gani mukayi ta mika hannunta nan take wani irin haske ya taho da gudu ya nufi Bukar, ai ina ganin haka banyi wani dogon nazari ba nayi tsalle na shiga gaban Bukar na tare hasken. Hasken yana zuwa ya shiga makogorona, nan take naji wani irin azaba lumfashina ya fara kokarin daukewa, ana cikin haka na dago kai da kyar na kalli Surayyah hade da cewa, “Masoyiya Surayyah ba haka mukayi dake ba, banyi zaton zaku karya alkawari ba, cewa kikayi idan Bukar ya baku hakuri shikenan rigima ta kare, amma me yasa? Meyasa zakuyi yunkurin kasheshi”. Tsawa naji Surayyah ta daka mini hade da cewa, “Rufe min baki makaryaci kawai, idan karya alkawari ne ai kai ka fara, waccan ranar kayi alkawarin ba zaka sake kula ko wace mace ba sai ni. Amma sai gashi na kamaka kana magana da waccan banzar yarinya, don haka yanzu ba karamin tsanarka nayi ba tunda kai mayaudari ne”.
Ina jinta yayin da nake ta kokowar fitar da lumfashi, idanuna sunyi ja saboda matsar da nake ji a wuya. A hankali na juya ga Bukar na fara fadin, “Bukar ka gudu ba zasu kyale ka ba, kayi gaggawar barin wajen nan. Nayiwa mahaifinka alkawarin babu abinda zai sameka don haka dan Allah ka gudu ka bar wajen nan”. Bukar banda kuka babu abinda yake ganin halin da nake ciki, nan take ya juya ga Boka Girgije yana fadin, “Boka ka ceceshi mana, dan Allah karka bari ta kasheshi Boka”. Jin haka yasa Boka kauda tsoro hade da matsowa gab da ni ya zarewa Delu ido yana fadin, “Ke karamar alhaki, ina umartarki da kiyi gaggawar sakin yaron nan. In ba haka ba kuwa yanzun nan zan kawo karshenki”. Kyalkyalewa tayi da dariya sosai kana ta tsuke fuska hade da cewa “Kai kuma wanene kai?”. Duk da ya tsorata amma ya daure ya gyara tsayuwarsa hade da cewa, “Nine nan Bako Girgije mai girgije bakaken aljannu irinku, maza ki saki wuyan yaron nan”. Yana fadar haka nan take y fiddo wata laya katuwa daga cikin jakarsa, tana rike a hannunsa ya fara nunata saitin Fatalwa Delu yana wasu surutai da ba’a fahimtar me yake cewa, zuwa dan lokaci kuma sai ya daddage ya jefi Fatalwa Delu da wannan laya. Tsutsayi sai ga layar ta sami Fatalwa Delu a goshi da karfi.
Nan take tayi wani kara cike da bacin rai ta sa hannu ta dafe goshi inda layar ta sameta, a dai-dai wannan lokacin ne na ji an sakar min wuya daga shakar da akayi man. Nan take na tashi zaune ina lumfashi da sauri-da-sauri, ana cikin haka sai ji mukayi Fatalwa Delu ta kurma wani uban ihu kana daga bisani ta ce, “Ni ka jefa? Lalai yau ka tarowa kanka masifar da tafi karfinka, dole nayi ma hukunci mai tsauri kafin na hallaka ka”. Tana fadar haka ta kalli Surayyah da kaninta dan karamin yaro fatalwa ta ce, “Ku kuma ina so kafin na gama da wannan tsohon kuyi gaggawa kashe wancan marar kunyar yaron”. Ta fada tana nuna Bukar da hannu, ko da ta gama magana nan take na ga wannan yaro kanin Surayyah ya rikide ya koma wani narkeken bakin kare mai matukar muni da ban tsoro. Ban manta ba shine karen da mukayi artabo da shi waccan ranar, ita kuwa Surayyah nan take ta bata rai fuskarta ta kara zama abun tsoro. Ina ganin haka na juya ga Bukar wanda yake tsaye a matukar tsorace na ce, “Uban me ka tsaya jira ne ka gudu, karka yarda ka tsaya a ko ina”. Ai kuwa yana jin haka ya juya da gudun bala’i ya nufi hanyar da zata kaishi cikin gari.
Ko da ganin haka sai Surayyah ta bishi itama a guje, nima da na ga haka sai na bita baya duk da a galabaice nake amma haka na ware na bita a guje. Ina cikin gudu sai ji nayi ana bina baya a guje, ko da na juya na haska fitila sai naga ba kowa bane face wannan bakin karen yake biye dani. Nan fa aka kasa tsere, Surayyah na biye da Bukar ni kuma ina binta baya yayin da karen ke biye da ni. Ba ayi wani nisa ba Surayyah ta tarar da Bukar nan take ta sa kafafu ta kwalfeshi ai kuwa yayi sama ya fado kasa a galabaice hancinsa ya fashe. Dake ba nisa garemu da su ba ko da na haske na ga abinda ke faruwa nan take na kwalla ihu hade da cewa, “Surayyah aa dan Allah karki kashe shi”. Na kara kaimi wajen gudu domin na tarar da su, amma kafin na yi wani yunkuri sai ji nayi wannan kare yayi tsalle ya kamo rigata ta baya. Nan take na fara kai mishi naushi da dukkan karfina ina kokarin yakice shi daga jikina amma ina ya rikeni gam yana wani irin gurnani mai sauti abun tsoro. Daga can na hangi Surayyah ta sa kafa tayi kwallo da Bukar tana dariya, nan take ya mirgina da kyar yana kokarin tashi amma sai ta kara zuwa da sauri ta shureshi da kafa.
Hakan ne ya fusata ni tunowa da alkawarin da nayi ga mahaifinsa, a nan naji cewa tabbas da in bari Bukar ya rasa rayuwarsa gwara ni na rasa tawa. Ko ba komai dai dama baiyi niyar tahowa ba gudun hakan, nine na nace na sa ya taho ba dan ya so ba. Da wani irin karfi na kama kan karen nan banji nauyinsa ba haka na fara juyawa ina wulwulawa da shi, daga karshe na makasa a jikin wata bishiyar goruba da na gani a kusa da mu. Nan take naji ya saki wata irin kara, ga dukkan alamu ya bugu amma kafin na juya in nufi wajen su Bukar sai ji nayi ya sake yunkurowa domin kawo mun hari. Nan fa muka hau dauki ba dadi da shi, yana kawo min cizo ni kuwa ina sa kafa ina harbinsa, a haka Allah ya bani sa’a nayi masa wani harbi a wuya, nan take ya sake sakin kara ya ja baya yana kallona yana haki. Ko da ganin haka ban bi ta kanshi ba na juya na dauki fitilar da na yar a kasa na nufi wajensu Bukar. Tun kafin na karasa nake jiyo dariyar Surayyah, ina haskawa na hangeta ta daga Bukar da hannu daya ta shake masa wuya tana dariya, shi kuma sai harbe-harbe yake da kafa, da alamu lumfashinsa ne ke barazanar barin jikinsa. Ko da naga haka sai na falfala a guje nayi tsalle hade da bangazar Surayyah, nan take muka baje a kasa mu duka.
Na mike ina haska Bukar tare da fadin sunansa ganin ko motsin kirki bayayi. Na kalli Surayyah da itama ta mike tana kallona cikin matukar bacin rai, ta fara fadin, “Nura karka shiga abinda ba ruwanka, ina umartarka da ka matsa gefe in ba haka ba zan hada da kai in kasheku”. Ko da jin haka nima sai na cika da bacin rai na ce, “Karya kike wallahi baki isa ki kashemu ba idan har Allah bai nufi karewar kwanakinmu a duniya ba. Nayi kuskuren yarda dake har na aminta na kawo Bukar gareku, amma ki sani idan kika ga kinyi nasarar kashe Bukar to tabbas bana lumfashi ne, amma idan ina lumfashi sai inda karfina ya kare”. Ina gama fadin haka sai ji nayi Surayyah ta kyalkyale da dariya, ta dade tana yi kafin daga bisani ta murteke mummunar fuskarta ta ce, “Bari na ga ta yadda zaka hana in kasheshi”. Tana gama fadin haka ta mika hannu saitina, nan take na ga wata irin igiya ta bayyana ta nannade kafafu da hannayena. Da faruwar haka na fadi kasa, nayi iya kokarina in tashi zaune ma abu ya gagara. Ina kallo ta karasa wajen Bukar dake fidda lumfashi daya-daya, ta sake daga shi sama da hannu daya ta shake masa wuya.
Ina daga kwance a fusace na ce, “Muguwa kawai azzaluma na rantse da Allah idan kika kashe Bukar sai na ga bayanki kema, sai na kawo karshenki”. Ko da jin haka sai gani nayi ta bushe da dariya ta saki Bukar daga tsayen da take nan take ya fadi kasa ta tako ta nufo inda nake tana dariya. Tana zuwa ta durkusa a dai-dai saitin fuskata tana kallona ta ce, “Wai kai din ne zaka ga bayana? To tayaya me kake takama da shi, karfi ko tsafi? Maza ina sauraronka fada mun”. Nazari na shiga yi a cikin zuciyata, kwarai da gaskiyarta shin taya zan iya yin nasarar ganin bayanta bayan ta fini karfi nesa ba kusa ba, haka zalika ita fatalwa ce tana da baiwa irin na aljannu. Tabbas tayi mun nisa nesa ba kusa ba.
https://aihausanovels.com.ng/labarai/fatalwar-delu-part-15