Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 59 Complete Novel

*ASM Bk2059*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

………….Fauzy na zuwa ba 6ata lokaci suka tafi don itama Fatun ta gama shiryawa, sai Magrib ta dawo Fauzy an sauketa a School, daka kalli fuskarta ma zaka gane tasha gyara ga wani k’amshi da jikinta ke fitarwa, lokacin data shiga gidan d’akin gwaggo ta nufa ta isketa ta dawo tana yin salla hakan yasa ta juya ta nufi d’akin ta, a gaban dressing mirror ta tsaya bayan ta cire veil d’in da tayi rolling ta fara k’are ma kanta kallo tana sakin murmushi, hannu ta kai tana shafa kumatun ta da har wani glowing suke, skin d’in ta ta k’ara yin sumul gwanin taushi dama a mulke take Saboda tsadaddun mayukan da take amfani dasu, bayan wani lokaci ta d’auki gyalen ta da ta ajiye a gefen mirror ta fita, d’akin gwaggo ta koma ta iske ta gama Sallar tana zaune kan darduma tana tasbihi, gefen ta Fatuu ta nufa ta zauna suka had’a ido ta sakar mata murmushi saida ta shafa sannan itama ta mayar mata da murmushin tace “Auta ta ta fara fitowa sak Amarya” murmushi kawae Fatun ke yi ta gaishe da ita bayan ta amsa ta tambaye ta Fauzy tace mata an aje ta a Makaranta ta d’aga kai, d’an shiru su kai suna ta yi ma juna murmushi daga baya Fatuu tay mata Maganar kud’in d’azu da aka turo da wanccan da tay mata Maganar su gwaggon ta tambaye ta ta tura ma Aunty Mareeya tace mata eh, tace to ai nata ne ba zatay amfani dasu bane, d’an shiru Fatun tay kafin tace “ni ba abunda zan yi dasu kawae dae ina tunanin zuwa shagon Aunty Zee in siyo wasu kaya” gwaggo dake kallonta ta tambaye ta wane irin kaya ko na sawa tace mata eh, tace “Yanzu duk kayan da ke gare ki sai kin k’ara,wasu ma fa baki ta6a sakawa ba sai aita tara kaya don ma ana bayarwa, duka yaushe Chairman ya baki akwati biyu na kaya ga shima Yayan naki da zai tafi yay maki akwatunan kaya ga wad’anda kike siya duk basu isa ba ki tattara abun ki ki tafi dasu sai kin k’ara wasu” da d’an alamun kunya Fatun tace “d…dama wai ko wanda zan sa ranar Juma’a d’in ne da yan underwear” da k’yar ta k’arasa Maganar had’i da sunkuyar da kai gwaggon tace “ni ina ganin tunda lokaci ya riga ya k’ure kawae ki bar shi yanzu yaushe har aka d’inka ma tunda kina da sababbin kayan da baki ta6a sawa ba ko cikin su ne ki za6i d’aya sai ki saka, nasan ma ko daga bayane zai maki suturar tunda hakanan ma yayi bare kuma yanzu, kawae don lokaci ya k’ure ne amman su underwear d’in zaki iya siyowa” kai ta d’aga mata alamar to, “to wai ma kin had’a kayan naki ko kuwa baki had’a ba?” a hankali ta girgiza mata kai alamar a’a, tace “to har sai yaushe ko sai lokaci ya k’ure kizo Kita faman duminiya” d’an yamutsa fuska Fatuu tayi kaman zatai kuka tace “ni wllh gani nike kaman wasa ba gaske ba wai zan bar gidan nan” yar dariya gwaggo tay tace “ki bari sai ranar zaki shaida in wasa ne ko gaske, in Allah ya kaimu ranar Juma’a kaman yanzu ai ina sa ran kin ma bar gidan nan” cike da shagwaba tace “Wayyo Allah, wllh gwaggo ban jin dad’i zan rabu daku zan koma wani wuri” tana rufe baki k’walla suka zubo mata sharr gwaggo dake ta dariya tace “ni kuma kinga dad’i nike ji…” Katse ta tay da fad’in “kai gwaggo dama ashe kin gaji dani” tace “ai abun farinciki ne yanzu ka ga naka yayi aure ba kamar da auren yay wuya yan mata da dama nata neman mijin aure babu, gashi ke kin samu d’aya tamkar da miliyan don wannan wuce dubu, in na ce banji dad’i ba ai na zama butulu ban gode ma Allah ba daya amsa man Addu’ar da nike maki koda yaushe ta ya baki miji na gari” d’an murmushi Fatun tay ta sunkuyar da kai can ta d’ago tace “nama ji dad’i daba nesa bane zan rink’a zuwa koda yaushe….” Da sauri gwaggo ta tari numfashin ta “ki rink’a zuwa ina? aikuwa dana sa6a maki wllh mi kika d’auki aure ne, abun wasa ko mi to a hir d’in ki kika ce zaki rink’a yin sunturi kina zuwa sai na sa6a maki kuwa, Mutuncin mace ta zauna a d’akinta sai ta kama ta fito” tana ta yamutsa fuska tace “kaman ma ke bazaki missing d’ina ba” tana yar dariya tace “ba kuwa zan yi ba tunda na samu madadin ki, Mino zan d’aukko ta dawo nan dama nayi mata alk’awarin zata dawo” d’an waro ido Fatuu tay ta fara sakin murmushi cike da farinciki tace “Yanzu Mino nan zata dawo kenan?” Kai ta d’aga mata, “amman kuma ai bata gama Secondary d’in ba” gwaggo tace “Eh aji biyar ta shiga in ta dawo nan sai ta k’arasa ai” sosae Fatuu taji dad’i sai faman washe baki take, tana matuk’ar son yan’uwan ta don kuwa mahaifiyar su itama tana son ta suma kuma haka don in ba ka sani bama baka cewa ba uwar su d’aya uban su d’aya ba ba kamar dae Mino d’in bala’en kama take da Fatuu, tana zaune a d’akin akai sallar isha gwaggo ta tashi tayi ita kuma ta koma d’akin ta, bayan gwaggo ta gama d’akin Fatun ta nufa tana shiga ta iske ta a kan gado tana latsa wayarta tace mata ta tashi ta taya ta su had’a kayan nata tace to, saukko da akwatunan ta sukai daga saman wardrobe gwaggo ta bud’e wardrobe d’in ta fara za6o mata wanda zata tafi dasu ita kuma tana jerawa, suna cikin haka taci karo da k’umshin ledar magungunan da Aunty Mareeya ta fara aiko mata ta fiddo tana fad’in miye aciki, d’an zaro ido Fatuu tay ganin gwaggon na kokarin kwancewa yasa gabanta ya hau fad’uwa ta sadda kanta k’asa, bayan ta bud’e k’ura ma abunda ke ciki ido gwaggo tay ta kai hannu ta fiddo da yar kwalbar ciki ta d’aga tana duba takardar jiki lokacin Fatuu ta d’an d’ago gwaggon ta jefa mata wani mugun kallo ba shiri murya na rawa tun ma kafin ta tambaye ta ta hau yi mata bayanin wadda ta bata, har saida gwaggo taji d’an sanyi don da hankalin ta har ya tashi ta maida kwalbar ciki kafin ta kalleta sai yan kame kame take ta tambayeta ta yi amfani dasu ne tace mata a’a gwaggon tace to Saboda mi ba bata akai don tayi amfani da su ba, cikin yar in ina ta ce mata na kwalbar dole sai jinin ya d’auke su kuma sauran wani da nama ake cin shi wani kuma da peak milk tana Maganar tana sussune kai, yar ajiyar zuciya gwaggon tay tace mata taje wurin Amadu ta amso Madarar da sauri tace to ta juya gwaggon ta bita da ido har ta fita, bayan ta amso tasa ta d’aukko Kofi da cokali a Kitchen ta tambayeta yadda aka ce a had’a ta fad’i mata da kanta ta shiga had’a mata bayan ta gama ta bata ta shanye daga baya suka cigaba da abunda suke.

 

Washe gari wurin Misalin k’arfe sha d’aya saura na safe aka kira Aunty Mareeya daga tasha cewa ga sak’o an kawo mata daga Kano tace to suka fad’i mata tashar da suke, kiran Daddyn su Hanif tay ta sanar dashi zata je ta dawo, ba 6ata lokaci dama tana ta dakon isowar kayan ta tafi, bayan ta amshi sak’on magungunan direct gidan su Fatuu ta nufa lokacin tana Makaranta sai gwaggo ta tarbeta tana ta fara’a suka shiga Parlor, gaisawa suka shiga yi daga baya Aunty Mareeya ta warware kwalin da aka sako sak’on ciki ta shiga firfito dasu tana yi tana ma gwaggo bayanin kowanne ta shiga yabawa tana sa Albarka ita kanta taga sauk’in kayan gasu da yawa, bayan ta gama fiddo su ta nuna mata wanda yakamata a fara ba Fatun zuwa ranar tarewar sauran kuma sai ta tafi dasu taci gaba da amfani dasu a can gwaggon tace to da ta dawo sai a fara batan, sosae tay ma Aunty Mareeya godiya tana Allah ya bar zumunci daga baya ta tambaye ta ko akwae wani abu gwaggon tace ehh kayan k’amshi take so an mata kwatancen in da zata samu to ita kuma ba sanin kan su tay ba Aunty Mareeya tace wannan ba matsala bane akwae inda za’a same su masu kyau jera mata kawai za’ai don already a kwalaben su masu kyau suke nan ma godiya gwaggon tay mata ta tambayi kaman nawa zasu isa ta fad’i mata, bayan sun gama Maganar kayan k’amshin suka shiga Maganar Abinci da za’ai ranar Juma’ar, saida suka gama tsara komae Gwaggon ta bata kud’in abubuwan da zata siyo sannan ta tafi. Tun Aunty Mareeya na kan hanya ta kira Fauzy ta sanar mata zancen isowar sak’on Magungunan taji dad’i sosae ta sanar ma Fatuu ita dae d’an guntun murmushi kawai tay, bayan an tashi Hostel suka wuce Fauzy ta had’a kayanta a cikin d’an trolley zata bi Fatun kaman yadda suka tsara a aji ita da dawowa cikin Makaranta sai bayan ta tare daga baya Haisam yazo d’aukar su, tun bayan da suka shiga Motar suka gaida shi ba wanda ya k’ara cewa uffan har suka isa gida, suna shiga d’akin gwaggo suka wuce tana ta fara’a tay masu sannu da dawowa suka gaishe da ita tace in sun kimtsa su zuba Abinci yana Kitchen suka ce to suka nufi d’akin Fatuu, suna cikin cin Abincin gwaggo ta k’wala ma Fatun kira bayan taje ta bata wasu daga cikin Magungunan da aka kawo kaza da cicci6i da kuma zabuwa duk ta d’ibar mata tace taje ta cinye su duka harda romon su tace mata to ta koma d’aki Fauzy na zaune tana cin Abincin ta shigo ta koma inda ta tashi ta zauna, koda Fauzy taga abunda ta shigo dashi nan take ta gane na maganin ne tunda taga hotunan su jiya ta hau yin murmushi Fatuu ta aje tace su ci Fauzy ta zaro ido tace ta rufa mata Asiri wannan yafi k’arfin ta saidae itan tay d’an murmushi kawae ta kai hannu ta yago naman kazar ta kai baki koda taji taste d’in ta ba Arziki ta d’an yamutsa baki da k’yar ta had’iye na bakinta a tunanin ta ko kazar ce kad’ai haka sai ta d’ibi cicci6i shima tana kaiwa baki taji shi salaf sai kaifin magani bayan ta had’iye ta kalli Fauzy tace don Allah ta ci da dad’i sosae jin haka yasa ta cewa tunda ta matsa mata bari ta d’an ci ta kai hannu ta yagi kazar Fatuu nata gumtse dariya gaba d’aya ta kai naman baki ba Arziki itama ta tsaya cak ta kasa taunawa ta d’an zaro ido Fatuu kau mi zata yi in ba dariya ba, da k’yar Fauzy ta had’iye tana d’an yamutsa fuska ta kai hannu ta d’auki ruwa ta kwankwad’a bayan ta aje tace “tabb, ni fa koda na ganta na zata Normal farfesun kaza ne ashe ashe duk farfesun magani ne wannan dole ma tay aiki a jiki kam” koda Fatuu tace mata ta k’ara don Allah cewa tay wllh in ta ganta a lahira kaita akai hakanan taja ma kanta bala’e ta kasa zaman lafiya ita dae daya zamar ma dole taci Fatuu tay ta mata dariya, daurewa tay taci gaba da ci daga baya ma lafiya lau ta rink’a ci har ta cinye ta shanye romon kaman yadda gwaggon tace, bayan sun gama suka hau shirin tafiya gyaran jiki da wankin kai don gwaggo tace kitso za’a yi mata, da daddare bayan sun dawo sun ci Abinci gwaggo ta kara kiran Fatuu ta bata tsumi kusan kala ukku ta sha harda na magarya mai wanko mara yay maganin sanyi aikuwa sosae yay ma Fatuu aiki don duk wani sauran jini daya rage saida ya fito a daren,

 

Washe gari Alhamis da safe bayan sun yi breakfast suka hau shirin tafiya Makaranta Haisam ne yazo ya d’auke su, Bayan an tashi ya d’aukko su suna dawowa Abinci kawae suka ci suka hau shirin tafiya k’unshi lokacin da Fatuu ta shiga toilet yin wanka har saida ta d’an yi mamaki ganin Pad d’in data sa da safe Kandas ba jini alamar dae ya d’auke hakan yasa bayan ta gama wanka ta had’a dana tsarki tayi sannan ta fito, tana komawa d’aki ta zura doguwar riga don yin salla Fauzy na ganin haka tay yar shewa ta hau tsokanar ta tana fad’in an yi a daidai abun ya mata dad’i wllh, ita dai d’an murmushi kawai tay ta girgiza kai, bayan duk sun shirya suka tafi, Ana gama sallar la’asar sai ga Saude tare da Tk rike da wasu jakunkuna masu shegen kyau guda ukku Gwaggo ta tarbe su suka shiga cikin parlor, bayan sun gaisa Saude tace mata gashi in ji Hajiya tace Fateema ta fara amfani da kayan ciki gwaggo ta hau godiya Saude ta k’ara cewa da Mota suka zo tace a kwaso kayan kitchen da sauri gwaggo tace to ta mik’e suma suka mik’e gaba d’aya suka fita, saida ta lek’a waje ta kira Amadu ya shigo aka fara kwashe na cikin d’akin shi ana kaiwa cikin Hilux d’in da suka zo da ita daga baya aka kwashe na cikin d’akin Fatuu, sai bayan da suka tafi ne gwaggo ta koma parlor ta bud’e jakunkunan ta fara dubawa, kaya ne ciki dinkakku lace kala biyu atampa kala ukku sai shadda data sha uban aiki itama kala biyu sai lifaya da dogayen riguna suma kala bibbiyu a cikin d’ayar jakar mahad’in sune wato takalma da mayafai harda hijab da jakunkuna sai cikin ta k’arshen underwear ne harda rigunan bacci dasu sark’ok’i da kuma kayan shafa duk da kayan basu da yawa amman fa da ka gani kasan masu kud’ine ba k’ananun kaya bane, bayan gwaggon ta gama dubawa ta hau jinjina kai cikin ranta take raya ita dama ranta ya bata da wuya ba’ai ma Fatun kaya ba, maida komai tay ta mik’e ta fita, d’akin ta ta koma tana zuwa ta kira Hajiyar a waya tay mata godiya ta tambayeta ba wata matsala tace mata eh ta k’ara yin godiya sosae da Addu’oi. Bayan su Tk sun kai kayan ta k’aramar kopa suka rink’a shiga dasu shida Amadu da gwaggo tasa ya bisu Saude ma ta fara d’auka Officer ya taso yace ta barshi ya kama aka rink’a shigar dasu tare da shi ita kuma ta nufi cikin part d’in don ta fara jerawa kaman yadda Hajiya ta bada umarni har aka shigar da komae. Yau ma sai bayan Magrib suka dawo har Fauzy ma anyi mata k’unshi gwaggo na gani ta hau yabawa don ba k’aramin kyau yay ba ya zanu rad’am abun ka da farare kuma gashi ja da bak’i ne yay gwanin burgewa gwaggo ta nuna masu kayan da aka kawo suka fara dubawa Fauzy nata santi ita dae Fatuu murmushi kawai take.

 

JUMA’AT BABBAN RANA

 

Washe gari da wani irin yanayi Fatuu ta tashi ta kasa gane farinciki take ko damuwa gaba d’aya kasala ta baibaiye ta har Fauzy ta fahimci hakan ta tambayi Mike damunta tace ita dae gatanan ta rasa Mike mata dad’i ma yar dariya Fauzy tay tace zullumin barin gida ne, Bayan sun yi breakfast suka yi shirin tafiya Makaranta, koda Fatuu taje yima gwaggo sallama cewa tay ai tayi zaton zasu hak’ura da zuwa yau Fatun da tay sukuku tace ai ko sun zauna ba abunda zasu yi gara su tafi gwaggon tace shikenan itama ta lura da yanayin ta har saida ta tambayeta wani abu ke damunta ne tace mata ba Komai ta juya zata fita gwaggon ta bita da kallo tana d’an murmushi, tana komawa d’aki ta jiyo horn d’in Haisam suka fito, Bayan tafiyar su makwabta suka fara shigowa don gwaggo duk ta sanar dasu zancen auren da tarewar kowa yaji sai ya taya ta murna har innar su Haulat ma tazo nan aka fara shirin d’aura girki duk da ba wani abu za’ai ba miyar waina ce da sinasar da ta bada ayo mata sai Fried rice itama Aunty Mareeya ta amsa zata bada ayo harda su coleslaw, bayan an d’aura miyar aka fara had’a kunun Aya da zobo lokacin wasu daga cikin Abokan aikin gwaggon suka zo har an taho da su dublan d’in data bada aikin su nan aka cigaba da hidima, lokacin da su Fatuu suka dawo wurin k’arfe d’aya saura mutane sun d’an taru a gidan ba laifi harda Zaliha d’iyar kishiyar gwaggon da iyalanta da kuma iyalan baba shehu suna shigowa aka hau ce ma Fatuu Amarya Amarya ita dae d’an murmushi kawae take tana gaishe dasu suka wuce d’aki, suna shiga Fatuu ta nufi gado ta zauna dabar Fauzy dake k’ok’arin cire Hijab tace ba zama yakamata tay ba ta tashi taje tay wanka ta shirya kar aita ganin Amarya kamar an koro ta kallo kawae ta bita dashi bata da niyyar mik’ewa, suna haka gwaggo ta shigo ruk’e da plate d’in Abinci da kuma na sobo da kunun aya ta aje masu akan Carpet tace gashi nan su ci in sun gama taje tay wanka ta d’aga mata kai, bayan sun fara ci bata ci wani mai yawa ba ta cire hannunta Fauzy na tambayar ta badae har ta k’oshi ba tace eh rarrashin ta ta shiga yi kan ta k’ara tace mata bata jin dad’in bakin ta ne dole ta rabu da ita tace to taje tayo wankan, bayan tayo wankan itama Fauzy taje tayi suka fara shiryawa doguwar rigar shadda ta fiddo mata a cikin kayan da Hajiya ta aiko ta taimaka mata ta d’an yi make up ta koma saman gado ta zauna Fauzy ma ta hau shiryawa lokacin Haulat ma tazo bayan ta gaisa da gwaggo ta bata gudunmawar data kawo tana ta godiya ta koma d’akin Fatuu, a bakin gado ta zauna ganin yanayin ta yasa ta hau tambayarta lafiya ita da za’a gani tana farinciki Fauzy na yar dariya tace fargaba ce itama Haulat dariyar tayi.

 

Ana gama sallar Juma’a su Feenah suka iso sun ci gayu Abdul harda babbar riga tunda bai sa yaje daurin aure ba yasa yazo tarewa, harda katan katan d’in lemu da ruwa suka kawo da kwalin Warmers masu kyau harda na had’addan glass jug ga kuma kud’i gwaggo tay murna sosae sai godiya take, daga baya ta koma d’akin Fatuu tana zaune saman gado ta rungume Abdul da tunda suka shigo gidan ya nufi d’akin, bakin gadon Feenah ta zauna ta kalli Fatun da murmushi tace “Amaryar mu kin sha kyau” d’an murmushi kawai tay ta gaishe da ita aka kawo masu Abinci, su Feenah basu dad’e da zuwa ba Aunty Mareeya ta iso tare da k’atuwar kular Fried rice da trays d’in coleslaw anyi sealing, su Amadu ne suka shigo da su tare da Tk da wani abokin su ita kuma suka kamo k’aton kwalin kayan k’amshi ita da Maman taufiq makwabciyar ta da suka taho tare, gwaggo tay farinciki sosae har ta kasa rufe baki sai faman godiya take tana shi Albarka daga baya wasu daga cikin k’awayen su na makaranta da Fauzy ta gayyata suka zo ciki harda Zainab Muhammadu da wadda zatayi ma Fatuu make up dama sana’ar ta ce ba 6ata lokaci aka fara yi mata, lokacin da aka gama baka jin komai sai Tubarkallah da kowa ke fad’a don ba k’aramin kyau kwalliyar tay mata ba ba kamar da yake ba’a ta6a yi mata irin ta ba,nan fa aka shiga yi mata hotuna daga baya aka sa ta canza kaya tasa lace shima akai mata hotunan, haka aka ci gaba da hidima aka ci aka sha abun sai godiyar Allah, Bayan sallar la’asar Haisam na Zaune a Bedroom d’in shi na G.r.a tare da Abbas da Saleem da yasan da zancen auren daga baya Najeeb dae bai sani ba don bai K’asar yana Canada, basu dad’e da gama cin Abinci ba da Abbas ya kawo daga gidan Hajiya don anan ya iske su bayan ya kai su Feenah, gaba d’ayan su kowa na ruk’e da wayar shi yana latsawa jefi jefi suke yin Magana, can Abbas ya mik’e daga kan kujerar da yake ya nufi Haisam dake kishingid’e jikin shi sanye da ash d’in shadda ya zauna daga gefen shi yana fad’in “gafa Amaryar ka ta fito ma sha Allah” d’aga ido yay ya kalli wayar, Abbas yaci gaba da bud’e mashi sauran dama Feenah ce ta d’aura su a status

har saida suka k’are sannan Haisam d’in ya janye idon shi ba tare da yace komai ba, Abbas ya mik’e ya nufi Saleem dake sanye da farar shadda yana latsa waya shima ya shiga nuna mashi d’an guntun murmushi yay cikin cool voice d’in shi tamkar Haisam yace wai yarinyar nan ce har ta girma Abbas na dariya yace mashi eh mana gashi ma har ta d’auke nauyin H,zakee Haisam din na jin shi bai ko kalle su ba Saleem d’in ya k’ara yin d’an guntun murmushi kawai, suna nan har aka yi sallar Magrib suka tafi Masallaci suna can har akai isha ana gamawa Hajiya ta kira Abbas tace mashi ya taho suje su d’aukko Fateema yace to bayan sun gama ya kira Feenah ya tambaye ta akwae Mutane ne da yawa tace mashi ba laifi, Saleem yay ma Magana da yake da Jeep ya zo kan suje su d’aukke su yace ok, kallon Haisam Abbas yayy yana murmushi yace ya taso suje ya d’an girgiza mashi kai alamar ba zai je ba ya juya yace ma Saleem su je ya mik’e har zasu tafi Haisam ya dakatar dasu Abbas ya juyo yana kallon shi ya mik’e yace yana zuwa, dressing mirror ya nufa ya jawo drawer chest ta tsakiya ya fiddo wani makulli, bayan ya rufe ya dawo wurin su ya mik’a ma Abbas yace yay amfani da Motar duba makullin yay ya d’ago da d’an bud’a ido yace “Lalle kana ji da Amaryar nan a Jeep d’in Dad d’in za’a d’auketa” shiru yay mashi ya nufi komawa kan kujera yace ma Saleem suje suka nufi hanyar fita daga Bedroom d’in, Bayan Hajiya ta kira Abbas tay mashi Magana ta kira gwaggo tace mata a shirya Fateema za’a zo a d’auketa tace to, d’akin ta ta nufa su Aunty Mareeya da Feenah da sauran k’awayenta duk suna ciki anata hira Aunty Mareeya sai basu dariya take gwaggo ta shiga ta sanar dasu, wani irin bugu k’irjin Fatuu yay gabanta yaci gaba da Fad’uwa Aunty Mareeya kau harda gud’a ta rafka ta mik’e tana fad’in Fatuu ta tashi ta canza kaya, Wani farin dankareren lace mai adon golden cikin kayan da aka kawo mata ta fiddo mata da gyalen shi golden da takalman shi half cover masu tsini suma golden harda purse d’in su dama barin su akai sai za’a kaita ta saka su, ba 6ata lokaci aka gama shiryata abun saidae ace Tubarkallah tayi kyau har ta gaji sai yi mata hotuna ake ba’a dad’e da gama shiryata ba Hajiya da Saude suka zo Hajiya na fadin gasu sun zo biko tana sanye da lifaya Saude ma tasha doguwar rigar lace da mayafi, nan aka shiga gaishe gaishe Gwaggo tace ma Hajiyar su shiga tace a’a basai sun shiga ba dare nayi a fiddo ta su tafi tace to ta nufi d’akin, tunda taji zancen an zo tafiya da ita ta saka kuka da duk ganin abun take kaman wasa sai yanzu ta tabbatar gaske ne, nan aka shiga rarrashin ta Aunty Mareeya data ruk’ota cike da zolaya take ce mata waya fad’i mata amare na kuka yanzu k’auyanci ne, bayan sun fito aka kaita gaban Hajiya dake tsaye tana jira tace akaita Mota duk aka firfita ta kalli gwaggo dake tsaye jikinta duk yayi sanyi tace itama tazo aje da ita ta rakata d’akinta tace to ta juya don d’aukko Hijab bayan ta dawo suka fita tare da Hajiya………….

 

 

 

 

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 da 3 Naira 400 ne za’a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za’a turo shedar biya ta wad’annan nos din 09013804524 ko 08169856268

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button