Hausa novels

Ribar Uwa Complete Novel Document

Ribar Uwa Complete Novel Document By Azizat

Description/Story:

Ribar Uwa Complete Novel Document

Written By Azizat Hamza

 

Description

Shimfiɗa

Friday 8:12pm in Boston, Massachusetts, USA.

Haka kawai jikinta yai sanyi, lokaci guda ta ji komai ya fita a ranta. Hatta littafin da ke hannunta sai da ya faɗi ƙasa saboda yadda hankalinta ya kauce daga karatun. Wani sanyi ne ya shigeta lokaci guda, zuciyarta ya ma ta wani nauyi. Ta dafe ƙirjinta tana maimaita kalmar Hasbunallahu wa ni’imal Wakeel. A hankali ta fara jin sauƙi bayan ta shafe kusan minti biyu tana maimaitawa, duk da haka ba ta dena maimata waɗannan kalmomi ma su ɗimbin lada ba.

“Excuse me, are you ok?”  muryan wanda ke gefenta ya ankarar da ita daga halin da ta ke ciki. Ta juyar da kanta a hankali zuwa gefen sa tana mai gyaɗa ma sa kai domin ta tabbatar ma sa da lafiyarta ƙalau. Ya miƙa ma ta littafin ta da ya faɗi yana mai nuna littafin yana da daɗi shima ya taɓa karantawa. Ta ƙarɓi littafin tareda furta ma sa kalmar Thanks.  Matashin Baturen da ke zaune a gefenta wanda ba zai wuce shekaru talatin da biyar zuwa da takwas ba yai ma ta murmushi sannan ya cigaba da kallon window.

Ta maida littafin cikin jakarta domin ba ta ganin za ta iya cigaba da karanta shi a wannan baƙon yanayi da ta tsinci kanta a ciki lokaci guda. Littafin mai suna The catcher in the rye da ta ke karantawa tun kwana huɗu da su ka wuce ba ƙaramin jin daɗin karatun sa ta ke ba, ta yi nisa da karatun dan lokacin da ta shiga motar bus da zai kai ta anguwar ta su ta Mission Hill daga Roxbury ta kusa ƙarisa karanta shi bai fi shafuka shida zuwa biyar ya rage ba amma lokaci guda komai ya chanja ma ta. Baƙon yanayin da ta tsinci kanta a ciki ya sa ta yi kewar gida musamman mahaifiyarta wanda ta ke matuƙar so a rayuwarta. Har aka isa anguwar na su ba ta dena addu’a cikin zuciyarta ba. Ta sauko daga bus ɗin ta dinga takawa a hankali har ta kai gida.

Alwala ta yi ta yi sallah sannan ta hau kan gado ta kwanta saboda yadda takejin yanayin jikinta ba daɗi. A hankali bacci mai daɗi yai gaba da ita bayan ta shafa addu’ar bacci…

Daddaɗan mafarkin da ta yi a daren na jiya ya sa har kusan makara ta yi da asuba. Lokacin da ta yi sallah ta jima tana yiwa iyayenta addu’a tareda sauran al’ummar musulmi. Ta shirya a gurguje cikin doguwar rigan atamfa wanda ke da kalar blue da fari, ta ɗauki babban mayafi fari ta yane jikinta da shi. Chocolate cornflakes kawai ta haɗa da madara na ruwa ta zauna ta sha kafin ta ɗau jakarta ta wuce makaranta.

Ba ƙaramin jin daɗin jikinta ta yi yau ba tana tafiya tana murmushi, duk wani damuwa da ta ke ji jiya da dare ya warware. Haka nan takeji ajikinta yau ranan za ta zo ma ta da alkhairi. Idan ta gama ɗaukan darasin yau tabbas dole ta kira gida ta ji lafiyar mahaifiyarta sannan ta sanar da ita labarin mafarkin da ta yi mai daɗi. Ta kan yi mafarki da mahaifiyar ta lokaci zuwa lokaci amma mafarkin jiya daban ne dana koyaushe mafarkin Aljannah ta yi…

Su Ishirin da ɗaya ne a ajin na su kuma su biyu ne kaɗai musulmai, daga ita sai wani ɗan ƙasar Pakistan mai suna Azhar Ali Durrani. A gaba ɗaya ajin kuma su huɗu ne ba ‘yan ƙasar na America ba. Ita da ta zo daga Nigeria sai Azhar sannan Audrey mutuniyar Philliphine sai Lee Jung Bo ɗan ƙasar Korea ta Kudu.

Tun daga shekarar farko zuwa yanzu da ya saura ƙiris su ƙarisa shekara ta biyu suna tare a ajin tamkar ‘yan uwan juna, kowa da ka gani a wajen karatu ne a gaban sa sannan karatun bai hana suna taimakawa junan su ba idan akwai wanda ya ke da rauni wajen fahimtar wani darasi. Daga sun kammala wannan sashi to saura mu su shekara biyu suna zuwa asibiti dan koyon aiki kafin su tafi residency na su…

Yau ma tana cikin wanda su ka zo ajin da wurwuri, kaman kullum a gaba ta zauna bayan ta gaisa da sauran mutane bakwai da ta samu a ajin. Ta buɗe littafi tana ɗan dududdubawa kafin malamin ya shigo, yau su na da darasin Professor Umar Audu Bamalli wanda ta san halin shi na yawan tambaya idan yana darasi. Tana jin daɗin darasin sa saboda gaskiya Allah ya bashi baiwar koyarwa gashi kuma ba ƙaramin jin daɗi ta ke yi ba idan ta ga baƙin fata na nuna zarra a ƙasar da ba tashi ba. Prof Bamalli ya yi ƙaurin suna a makarantar na su kuma kasancewar sa baƙin fata kuma ɗan Nigeria ya sa ya ke burgeta sosai kuma ta ƙe ƙara jinjina ma sa.

Makarantar su na Harvard Medical school ba ƙaramin ƙaurin suna yai ba a ɓangaren ilimi a duniya baki ɗaya. Idan za ka irga Jami’o’i da su ka yi fice da suna kuma su ka yi zarra a duniya idan ba ka saka Harvard ba kamar lissafin ka bai cika bane. A duk lokacin da aka yi ƙididdiga aka ware Jami’o’i fitattu goma ko fitattu biyar da su ka fi kowanne a duniya sai ka ga sunan Harvard yana zaune ƙyam acikin su. Taimakon Allah da addu’ar Uwa shi ya kawota wannan babbar makaranta da ba kowa ke samun daman shigan sa ba…

Ajin na su yai tsit saboda shigowar Prof Bamalli. Kamar yadda ya saba sai da ya gaisa da ‘yan ajin kafin ya fara gudanar da darasin. Kusan rabin awa da fara darasin na su ya jefo wata tambaya wanda Jack Stafford yai saurin ɗaga hannu ya amsa ta sai dai kuma amsar ta shi ba dai-dai bane. A maimakon ya gwaleshi ko ya nuna ba dai-dai ba ne sai ya ce “great, but we need something better”

Wata baturiya mai suna Emilia ta ɗaga hannu ta sake amsa wannan tambaya sai dai ita ma ɗin ba dai-dai ba ne. Prof yai murmushi ya ce “nice try Miss Stevenson”

Ya kalli budurwar da ke gefen Emilia wacce ya sani ‘yar ƙasar sa ce kuma ya san ta da ƙoƙari sosai. Hankalinta na kan wayar ta shiyasa ya ɗan kira sunan ta da ɗan ƙarfi. “Pakkari”

Budurwar ta yi saurin ɗago idon ta tana ƙoƙarin ba da nitsuwarta ga malamin na su.

Ya sake maimaita ma ta tambayar sa ko za ta iya amsawa sai kuwa ta bashi mamaki domin amsar da ta bayar ɗin shi ne dai dai. “Good” ya faɗa sannan ya cigaba da bayanin darasin da ya ke yi.

Wata baƙuwar number ne ke kiranta daga Nigeria shi ya ɗauke ma ta hankali ma daga ajin na su. Yadda numban ke kira akan kira ya sa ta yi tunanin ko akwai matsala ne. Ta dai daure ta ba da nitsuwarta a ajin da zimmar ana gamawa za ta kira numbar domin ta ji wanene ke kiran, cikin zuciyarta tana ayyana wa ranta ƙila mahaifiyarta ne ke son gaisawa da ita.

Prof Bamalli ya gama darasin sa inda ya ke tsaye domin amsa tambayoyin ɗaliban na sa kamar yadda ya saba a kowani lokaci.

Tana son tambayar Prof Bamalli amma kuma ƙaran shigowar text zuwa wayarta ya sa ta maida hankalin ta ga wayan domin ta ga wani irin saƙo ne…

Saƙon da ta karanta ne ya sanya numfashinta ya ɗauke na ‘yan daƙiƙu. Ta miƙe zumɓur tana faɗin “Ƙarya ne, ƙarya ne” hannunta na rawa ta shiga dialing numbar da ta turo saƙon. Mancewa ta yi da inda ta ke burinta kawai shine ta ji gaskiyan abinda aka turo. Wani bagidajen ne zai tura ma ta saƙon baƙin ciki irin haka, mahaukacin ne ya ke tura saƙon mutuwa haka.

Innayi ta rasu shi ne abinda aka turo. Ta ɗara wayan a kunne tana girgiza kai hawaye na zubo ma ta.

Wanda ta amsa wayar ne ta sanar da ita abinda ya faru a tsanake. Hakan yai sanadiyar suɓutuwar wayar da ga hannunta ya faɗi ƙasa gamida yin ƙara wanda ya sa hankalin duka ‘yan ajin ya tashi domin tunda Raudha Abubakar Pakkari ta miƙe tsaye tana kuka su ka san ba lafiya ba. Tambayarta su ka farayi randomly akan mi ya ke faruwa amma kwata-kwata ba ta jin su balle ta iya ba su amsa.

A hankali ta fara takawa tana tafiya  hannunta ɗaya a miƙe kaman zata taɓa wani abu. Hawayen da ke ziranya a idon ta ne ya ƙara ingiza yadda ƙwaƙwalwarta ke tuno ma ta lokuta na farin ciki da su ke tare da Innayi…

A mafi yawancin lokuta idan ka ji saƙon mutuwar wani na kusa da kai to abu na farko da ka ke tunowa shine kyawawan halayen sa. Za ka dinga tuno su a ranka kamar yau ne abin ya faru, abin zai shiga jikin ka sosai har ka ji duniyar nan fa ba madogara ba ce kuma kaima ɗin lokaci ka ke jira. Amma daga zaran wannan jimami ya huce sai mutum ya shagala da duniya ya manta cewa wannan nakusa da shi da ya mutu yana chan yana cin sakamakon abin da ya yi a duniya haka nan kuma shima ɗin ko ba daɗe ko ba jimawa zai je chan ɗin.

Ku biyoni domin jin labarin wata uwa da ‘ya’yanta, labari ne mai shiga rai da taɓa zuciya. Labarin da ban rubutashi dan komai ba sai dan ya zama kaman wani hanya na tunasarwa garemu ba ki ɗaya. Burina shine a ƙarshen labarin nan a samu mutum ɗaya ko biyu da su ka gyara zamantakewar su da kuma yadda su ke da iyayen su musamman iyaye mata.

Saboda darasin da na ke so na isar ta sigar labari ya sa na ke so  dan Allah idan ka karanta ka yaɗa shi saboda wani ma ya samu ko zai ƙaru ko kuma ka baiwa wani labarin a taƙaice ko za a samu wani da zai faɗakantu  da wannan labari.

Labarin daga farkonsa har ƙarshen sa kyauta ne ga duk wata Uwa da ke doron ƙasa. Its all about motherhood.

Allah ka jiƙan iyayen mu ka gafarta mu su amin

Wanda na su ke raye a daure a kyautata mu su wanda na su suka rasu a cigaba da mu su addu’a…

Ribar Uwa Complete Novel Document Txt

File Name Ribar Uwa… Hausa Novel Doc
Title Ribar Uwa Complete Novel Document 
Author    Azizat Hamza
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    27/11/2024
File Size    1.5MB
Format Size    TXT
Book Price    Free
Phone No     NIL
Download Ribar Uwa Complete Novel Document By Azizat 

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button