Novel Document

Fil’azal Hausa Novel Pdf Free Download

Fil'azal Complete Novel By Sa'adatu Abdullahi

Description/Story:

Fil’azal! Complete Hausa Novel Document Written By Sa’adatu Abdullahi

 

Description

Kaduna state, Malali GRA Sani Sami Close.

A hankali yake sakkowa daga kerarriyar matattakalar benen, kafafuwannan nasa fari karr kmr a lashe kai bakace ya taba taka kasa bama da kafafuwan nasa,.

Yayinda lallausar hannunsa me kama da lambun farar Audiga yake rike da wayoyinsa guda biyu, daya kirar Samsung dayar kirar Iphone X. Yanada kudin daze rike wayar billions of naira , sbda shidin ba karamin me rufin asiri bane, ubangiji ya masa Arziki sosai fiye da tunanin me karatu, Arziki irin wanda ya gajesa a gun mahaifinsa Sarki jikan sarki. Kwata-kwata shi ba mutum bane da duniya ke gabansa, hasalima duniyar bata masa dadih, a kullum in zaka kalli fuskarsa Zakasan kawai rayuwa yake a duniya amma Sam bayajin dadinta, Daka kallesa dole Zakasan yana cikin Jarrabawar rayu. Sanye yake da wani danyen boil light ash color , irin ligt dinnan sosai. Boil din me sheki da tsantsi, dinkin riga da wando. anyi masa dinkinne irin na dattako, wato de dinkin manyan mutane, yayinda aka kewaye wuyar rikar jikin nasa da wani siririn aiki baki mara hayaniya, irin na manyan mutane. A yadda naga boil din nasa na sheki ya tabbatarmin da dolema zeyi tsananin tsada,.

Kansa sanye da black din huta wadda tasha zanen aiki irin na zamani, aikin hannu ce hular ammafa irin wadda turawa sukayi Aikin danni ban taba ganin hula me kyau irin ta kansa ba. Lallausar fararen kafafuwansa sanye da black shoe me kyau dagani shoe din bame nauyi bane, Sam shi bayasan abubuwa masu nauyi shiyasa yana tsananin san boil yard ba kasafai ya fiye mu’amala da shadda ba sbda tana masa nauyi , Sam besan harkar hayaniya, saboda shi mutum ne da bayasan abinda ze takurasa, sbda yanada tsananin Jin zafi, a bedroom dinsa kusan AC uku garesa, manya-manya, baya iyayin bacci in AC be ratsashi ba, duk inda yake shiga akwai AC a gidansa, hatta da corridor dinsa akwai AC, Kitchen AC, toilet AC, matansa sam basa iya jimawa in suka shigo part dinsa sbda tsananin sanyi kai kace a cikin frij kake, ko a cikin ruwan teku. seshi din daya saba zama yake iya zama. Kuma ba wani jiki bane dashi, bashi da kiba kuma shi ba siriri bane, irin mazannan ne masu cikar zati da cika ido amma Sam bashi da kiba, sede yanada kirar karfafa,. launin fatarsa irin launin ruwan fari ne, ga farar fata ga Hutu AC to AC, Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un! Wayyo Kyau!! , jikinnan luwai-luwai, kamar ataba jini ya bulbulo!, tako ina a jikinsa luf-luf yake da Gashi musammanma hannayensa da kafafuwansa yanada Gashi zara-zara tamkar akama a kitsa.. Yanada tsananin kyau, kyaun da harshena baze iya misaltasa ba, dogo neshi sambal ba gargad’a, yanada Dara-daran idanuwa, luhu-luhu, yayinda idanuwan nasa suka kansance a kullum sanye cikin farin siririn glass, medical glass, sometimes be cika gani kwarai ba inba glass a idonsa, musammanma in da daddare. Yanada dogon hanci yayinda yakeda madaidaicin baki, yanada kasumba, madaidaiciya, bakaramin kyau kasumbar ta kara masa ba Ainun, ya d’an manyanta amma hakan be girgiza tsananin zallar madarar kyaunsa ba, kyaune ya hadu da Hutu da kudi. , a kallah ze Kai 50yrs.

Amma Inba an gaya maka ba baka isa ka gano hakanba, shekarun nasa sun buya a cikin kyaunsa da hutun dake tattare dashi, kai inka gansa ka rantse da Allah cikakken balarabe ne, saboda kyaun nasa ya wuce shahara, kyaun nasa yayi ratsa-ratsa da imanina, bantaba ganin tsarin halitta irin nasa ba, lafiyayyen namiji azahiri ga cikar zati kai dagani dole zakasan inside zeyi girman jarumar. (BURA)

A hnkli ya gama sakkowa daga upstairs din. , yayin da cikin sassarfa yake tafiya amma inka kallesa zakasha a hankali yake tafiya yanada tsananin sauri, wato yanada zafin nama, ba kasafai ake iya binsa a jere ba in suna tafiya da mutane, sbda yanada sauri, abunka da dogon Namiji. Se zuba kamshi yakeyi, na perfumes dinsa masu tsananin tsada, yanasan kamshi, yana kashe kudi kwarai a kan turaruka sekace mace, in takaice muku yafi wata macenma San kamshi shifa Sam baya mu’amala da datti ko kazanta, yanada tsananin tsafta ta fitar hankali. A hankali ya sauke idanuwansa kasa ya kalli dankareren watch din dake manne a tsintsiyar lallausar tubus din hannunsa wanda ke cike da suma. dai-dai watch din hannun nasa ya buga karfe goma da minti asirin na safe,Adai-dai lokacin kuma wayarsa kirar samsung ta dau rurin bukatar agaji, Ya duba yaga lambar Dreva dinsa ne kuma babban Amininsa tin Tala-Tala Malam Abdullahi wanzan. Dagawa yayi ya kara a kunnensa, ba tare da yace komi ba.

Daga cikin wayar aka fara magana “Ranka ya dade JAROOD har yanzu baka fito ba,,,Gashi Giwar sarki nata kirana..” (mahaifiyar Jarood kenan ita ake kira da giwar sarki) dan guntun numfashi yaja hadi da langwabar da Kai ya danyi jim for some seconds kana yace “Ganinan fitowa insha Allahu…” malam Abdullahi Dreva wato wanzan Yace cikin girmamawa “Allah fiddoka lafiya ranka ya dade, fari me farar Aniya dogo tsayuwarka tafi tsayuwar gajeru dubu, Allah ya ja ranka dan tsarki jikan sarki, yarima me jiran gado, tureka se Allah yayi, kai kainuwa ne ba a shukakaba sede akaga fitowarka…”

Wani guntun murmushi yayi , me dauke da siririn sauti, yayinda kirarin Wanzan ya bashi nishadi, ya jinjina kai kana Ya amsa da Amin daga bisani ya katse wayar. Direct ya nufa kofar dazata kaisa part din Hajiya Zulaihat wato uwar gidansa kenan ta Auren saurayi da budurwa Yana tafe yana bin ko ina da kallo a gidan, gidan ya tsaru iya tsaruwa, babu abinda babu a ciki na morewa rayuwa, komi na duniya ubangiji ya basa, sede yanaji a ransa Ina ma za a kwace komi na more rayuwa a bashi abu daya Rakk daya rasa a rayuwarsa, Wato martabarsa da kimarda ta d’ana miji, lokuta da dama shida kansa yanajin ya tsani kansa, Amma yazeyi da jarrabawa,.

 

File Name  Fil’azal… Hausa Novel Doc.
Title      Fil’azal 
Author  Sa’adatu Abdullahi
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Romantic Story
Published Date    22/06/2024
File Size    210Kb
Format Size    TXT
Phone No
Download Fil’azal Complete Novel Document By Sa’adatu Abdullahi

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 


 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button