Hausa novels

Ruwan Zuma Page 52 Hausa Novel

(52) Abul d’age k’afarshi yayi a hankali ya wuce Mas’ud junior yana cewa, “Mama ina wuni?” Bai jira amsarta ba ya bud’e d’akinshi ya shiga kana ya rufe k’ofar har da saka makulli. Mas’ud J kuka ya saka yana saka yatsunsa a baki idanunsa na tsiyayar hawaye yana kallon iyayensa. Haydar ne yayi saurin isa gurinshi ya d’aukeshi suka fita waje kamar yanda tun farko ya so a mishi. Laila bata ji dad’in hakan ba har ta taka zata je d’akin Abul sai ta tuna maganar Kaala Abdi da yake cewa kar ta yawaita mishi fad’a, wani lokacin ta barshi da kanshi ya gane abun da yayi bai dace ba. Abul yana shiga d’akinsa ya dafe kanshi wanda ya fara ciwo nan take dalilin kukan yaron da ya fara ji, sakanni kad’an da haka ya ji Haydar ya d’aukeshi yana rarrashinsa suka fita waje. Runtse idanunsa yayi yana tuna kwayar idanun yaron wanda suka tara ruwa a ciki da bai d’aukeshi a kan lokaci ba. Girgiza kanshi yayi ya daina wannan tunanin kana ya zauna a bakin gadonshi yana kallon yanda aka gyara mishi d’akinshi ko’ina na tashin k’amshi. Ya jima a haka sannan ya tu6e kayanshi ya shiga wanka. Yana fitowa ya samu sabbin k’ananan kaya har guda goma a kan gadon nashi, kamar ba zai saka ba amma ya za6i riga da wando three quarter ya saka kana ya fita falo. A falo ya samu Laila tana kallo ya zauna can nesa da ita shima ya fara kallon, juyowa tayi ta kalleshi tana jin kamar ta je ta rungumeshi tsabar kewarsa da tayi amma ta hana kanta gudun kar ta tunzurashi. Gyara zamanta ta yi ta dubeshi cikin nitsuwa ta fara magana cikin yaren Shuwa ta ce, “Ya kake ya ka baro mutanen Maiduguri?” “Suna lafiya. Ummii tace a gaisheki.” Ya bata amsa ba tare da ya kalleta ba. Laila idanunta ne ya tara hawaye wai Abul ne yake mata magana cikin nitsuwa haka? Yaushe rabon duniya da ayyiriri? Shiru suka sake yi na wasu sakanni sannan Laila ta lura da kayan jikinshi fara’arta ta k’aru ta ce, “Naga ka sanya kayan da Haydar ya sayo maka sun yi maka daidai duk da cewa bai san size d’inka ba. D’azu fitansu shi da Mas’ud J suka sayo maka.” “Waye Mas’ud J?” Yayi tambayar yana kallonta a karon farko tun shigowarsa falon. Da d’an mamaki Laila ta dubeshi ta ce, “D’ana, kaninka. Mas’ud ya yiwa takwara ai.” Shiru Abul yayi bai ce komai ba sannan ya tashi zai tafi Laila ta tsayar dashi tana tambayar ina zai je? “Zan je in cire kayan ne.” Marairaice fuska ta yi ta ce, “Don Allah kar ka cire Abul. Tun da har ya iya zuwa ya sayo maka alhali ko magana bata had’aku godiyar da zaka mishi shine ka sanya kayan. Please.” Ya kai seconds talatin a tsaye sannan ya juyo zai zauna Laila da farin ciki ya kamata tana godewa Allah ta ce, “Ga can abinci na maka your favorite.” “Sai anjima zan ci.” Ya bata amsa yana k’ara zama. Hira take janshi dashi yana amsawa sam-sama, wani lokacin ma sai yayi kamar bai ji ta ba amma bata hak’ura sai ta k’ara mishi wani maganan. In baza ta manta ba rabon da ta zauna da Abul haka a gida suna hira suna tad’i shekara guda kenan har da watanni biyu zuwa uku. Har yanzu bata daina mamakin wai Abul ne zaune a falonta suna hira ba. Ana kiran sallah Haydar ya fito daga falonshi tare da Mas’ud J wanda ke tsotsan strawberry yana yamutsa fuska. Laila tana ganinsu fara’arta ta k’aru ta kar6eshi yana saka mata a bakinta wai ta ci. Duk yawunshi ne a jiki amma haka ta saka baki ta gutsiri kad’an sannan ta had’iye tana kad’a kai ta ce, “Dad’i.” Bakinshi ya bud’e yana dariya kana ya k’ara turawa a bakinshi yana dannawa da dasorinshi har ya gutsiri kad’an ya kuma 6ata fuskarsa don strawberryn akwai tsami kad’an. “Abul ya gajiyan hanya?” Haydar ya mishi tambayar yana zama a wani kujeran daban. “Lafiya.” Ya amsa kamar wanda aka mishi dole kana ya tashi yana cewa, “Mama na tafi masallaci.” “Mu je tare.” Fad’in Haydar yana mik’ewa tsaye ya bi bayan Abul wanda ya k’ara sauri baya son su had’a hanya. Abul na gaba Haydar na baya haka suka tafi masallacin suka yi sallah amma Abul ya rigashi dawowa gida ya je kan dinning table ya zuba abinci yana ci, a haka Haydar ya shigo ya sameshi ya ce, “Ina ta nemanka ashe kai ka dawo gida.” “Eh.” Kawai yace kana yaci gaba da cin abincinsa ba tare da ya kalleshi ba. Ganin haka yasa Haydar ya wuce sashensa yana jin babu dad’i a zuciyarsa domin yana iya bakin k’ok’arinshi wajen ganin ya zauna da yaron lafiya amma shi baya ko ganinshi da daraja balle maganar arzik’i ta shiga tsakaninsu. Yana cin abinci Laila ta fito daga d’akinta da alama sallah ta yi hannunta d’auke da Mas’ud J yana kad’a abun wasanshi hankalinshi a kwance. Itama Laila zama ta yi a kan kujeran dinning kusa dashi tana cewa, “Har kun dawo? Ina Haydar d’in?” “Yana can.” Ya nuna mata hanyar sashensa. Kad’a kai ta yi ta fara d’iban abincin tana tambayarshi yanda makarantarshi zata kasance tun da an mishi step down. “Ni fa bazan koma makaranta ba, sana’a zan fara yi.” “Ikon Allah. Wace sana’a kenan? Ka fasa zama Computer scientist d’in kenan?” “Tun lokacin dana rasa computer ta na ji abun ya fita a kaina saboda komai nawa yana ciki. All a had.” Ya fad’i maganar kamar zai yi kuka yana ajiye spoon d’insa cikin plate d’in. “Tatatataatata.” Suka jiyo muryar Mas’ud J yana mik’awa Abul abun wasanshi yana murmushi. Zura mishi ido Abul yayi fuskarsa babu yabo babu fallasa ya ce, “Me yake yi hakan kenan?” Laila da dad’i ya cikata kamar ta mutu ganin Abul ya fara kula d’anta ta ce, “Yana son bawa mutane abunsa musamman idan ya ga basa dariya. Yanzu ma ina ganin ya ga ka 6ata rai ne shine ya mik’o maka abun wasansa don kaima kayi wasa ka daina fushi.” Abul mik’a hannunshi yayi ba tare da ya shawarci zuciyarsa ba Mas’ud J ya dangwala mishi abun wasan yana cigaba da 6angala mishi dariya. “To nagode.” Ya fad’a yana murmushi kad’an wanda bai ma san yayi ba sai Laila ce ta lura da hakan ta kuma ji dad’i bana wasa ba. Mas’ud J d’aga hannayensa duka biyu yayi yana neman barin cinyar Laila wai Abul ya d’aukeshi. “Not so fast young man.” Fad’in Abul yana ja da baya amma bai ankara ba Laila ta ajiye mishi yaron a cinyarsa. Ganin Mas’ud junior zai fad’i k’asa Abul yasa hannayensa ya tareshi yana kallon abu d’an k’arami a hannunsa yana mishi dariya, sai tafa hannayensa yake yi yana rocking jikinsa. “Kun yi kyau tare.” Fad’in Laila tana murmushi har hakwaranta na bayyana. Abul har zai mik’a mata Mas’ud yaji yaron ya kama gemunshi yana wasa dashi, hakan yasa ya dakata yana kallonshi yana jin wani iri a zuciyarsa wanda ya kasa gane menene, amma abunda ya sani shine ba zai k’ara saka yaron kuka kamar yanda ya sakashi d’azu ba. Mas’ud junior ya dad’e a jikin Abul yana wasa Laila kuma na cin abinci suna hira wanda yawanci a kan Ummii ce da ta kafe baza ta dawo Kano ba, can ya fara mik’a hannu zai koma gurin mamanshi, hakan yasa Laila ta gane me yake so ta ce, “Yunwa yake ji bari in had’a mishi kunu a kitchen.” Ta fad’i hakan tana tashi tsaye. Yana ganin mamanshi ta tashi ya saka kuka Abul ya ce, “Mama ki kar6eshi yana kuka.” “Wallahi ko na tafi dashi ba zai barni in had’a kunun cikin kwanciyar hankali ba. Ka rarrasheshi zuwa nan da minti biyu ka dawo mini dashi.” Ta fad’i hakan tana shigewa kitchen ganin Junior da gaske kukan yake yi. Abul jijjigashi ya fara yi yana cewa, “Yi shiru, bari ta gama ta kawo maka. Ka ji?” Amma ina! Yaron bai ma san me yake cewa ba domin shi in yana jin yunwa to babu zaman lafiya, akwai wani lokaci da Haydar ya ta6a cewa ‘Allah kar Ya nuna mini ranar da zaka ji yunwa talauci ya hanani saka abinci a bakinka Mas’ud’. Ana rarrashin a falo har aka fita waje bai daina kuka ba, Abul kuwa tuni kanshi ya fara ciwo yana jin haushin kanshi don a tunaninsa ko abun da ya yiwa yaron d’azu ya tuna yake son barin gurinshi. Haydar ne ya fito falonshi da ya ji kukan yayi yawa ya samesu a waje Abul na cewa, “I’m sorry, please ka yi shiru.” “Meya sameshi ne?” Haydar ya tambayeshi yana kar6an Mas’ud J wanda ya rage kukan ganin babanshi da yayi. “Ta je had’a mishi kunu ne shine yake ta kuka.” “Ai haka yake idan yana jin yunwa ba’a gane kanshi. Bari in je in duba ko ta gama had’awa.” A kitchen Haydar ya samu Laila ta gama dama kunun tana shirin fitowa suka had’u a bakin k’ofa yana murmushi ya ce, “Ya aka yi ya d’aukeshi?” “Long story, bari in bawa wannan angon Ammin abinci kar ya fasa mana gida da ihu.” Da haka ta yi gaba zuwa falo ta zauna Haydar ya ajiye mata Junior a cinyarta ta fara bashi kunun. Kiran sallah da aka fara yasa Haydar ya shafa kan d’an nashi yana cewa, “Bari in je sallah in dawo Bundle of scream d’ina.” A masallaci Haydar ya had’u da Abul yana alwala amma babu wanda ya kula wani har suka shiga masallacin aka tada sallah, ana idarwa suka kama hanyar gida wannan karon Abul bai yi saurin wuce Haydar ba, ganin haka yasa Haydar ya fara mishi magana yana cewa, “Yaushe zaka shiga school kayi registration? Na ga Sabrin har sun fara karatu kar lokaci ya k’ure maka.” “Sana’a zan fara.” Ya bashi amsa bayan ya d’auki dogon lokaci bai amsa ba. “Why?” Haydar ya samu kanshi da fad’i sanin irin yanda Abul ya kwallafa ranshi a kan Computer har ana kiranshi da Computer Geek. “Babu.” Da haka suka shigo cikin gida Haydar dai bai daina mamakin canjawar ra’ayin Abul ba. Haydar sashensa ya nufa yayin da Abul kuma ya shiga nasu ya samu Laila na goye da Mas’ud junior yana gyangyad’i alamar bacci zai yi. Waya take yi wanda a take Abul ya gane da Sabrin ce ya nemi ta bashi wayar su gaisa in ta gama maganar. “Sabrin.” Ya kira sunanta yana murmusawa bayan ya juyawa Laila baya. Daga d’ayan gefen Sabrin ta kwala ihu ta ce, “Yaya Abul? Kai ne? Yaushe ka dawo?” “Hey calm down mana, wani tambaya d’aya zan amsa miki?” “Yaushe ka dawo Yaya Abul?” Ya jiyo muryarta na karkarwa alamar kuka take yi. “D’azu da yamma, Mama bata fad’a miki bane?” “Bata fad’a mini ba wallahi, ina ce kana gida? Bari in zo yanzun nan ka jirani don Allah.” “No, kiyi zamanki a gidanki gobe zan zo Insha Allah.” “A’a Yaya Abul ka bari in zo don na dad’e ban ganka ba.” “Yaushe kika koyi musu dani ne Sabrin? Dare yayi bai kyautu ki taso daga gidanki cikin daren nan ki zo gida ba. Gobe Insha Allah zan zo har gidanki ki ganni, kin ji?” Gyad’a kai tayi tamkar tana ganinshi sannan ta share hawayen fuskarta ta ce, “Allah ya kaimu goben ina nan ina jiranka. Yaya Abul…” Ta kira sunanshi. “Na’am, ya aka yi?” “Don Allah kar ka sake tafiya ka barmu.” Shiru yayi na wasu sakanni sannan ya ce, “Ina nan.” Basu jima a wayan ba ya mik’awa Laila wacce ta yi sallama da Sabrin bayan ta fad’a mata dalilin da yasa ta k’i sanar da ita dawowanshi, domin Kaala Abdi ne yace kar a fad’awa kowa ya dawo kar a zo a cika gidan ya kasa samun hutu, domin a yanzu so ake yi ya samu nitsuwarshi ya kuma saba da ganin Haydar da Laila a matsayin mata da miji ba tare da hakan ya bashi haushi ba. Though bata fad’a mata duk wannan bayanan ba. Suna gama waya Abul ya mata sai da safe ya shige d’akinsa ya kulle domin bacci yake ji dalilin gajiyar da ya kwaso a hanya, ai kuwa yana kwanciya ko minti biyar bai yi ba bacci yayi awon gaba dashi. Laila wanka ta shiga bayan ta kwantar da Mas’ud junior, tana fitowa ta yi shirin bacci ta mulke jikinta da humra kamar yanda kullum take yi kana ta d’auki d’anta suka tafi sashen maigida d’awisu ko ba tsuntsaye namanka sai sarki. Abinci ta samu yake ci, suna had’a ido suka sakarwa junansu murmushi ta isa can in da gadon Mas’ud yake ta shigar dashi ciki ta kwantar dashi. “Sarkin rigima yana recharging na gobe.” Fad’in Haydar yana d’aukan plate d’in da ya gama cin abincin ya fitar zuwa falo ya ajiye a kan dinning. “In baka daina cin abinci a cikin d’akinka ba zaka jawo mana 6era fa.” Fad’in Laila tana zaune a bakin gado tana shafa cream a k’afarta wanda ke sawa yayi laushi. “Na saba da hakan ne, a d’akin Ammi nake cin abinci kullum. Baki bani labarin Abul da Mas’ud J ba.” Ya canja maganar yana hawa kan gadon bayan ya tu6e singlet d’insa. A nan Laila ta bashi labarin duk yanda aka yi ta k’arishe da cewa, “Yanzu damuwata shine ya fara maka magana yana darajaka, ko kai ba mijina bane ai ka girmeshi.” “Baby step Laila, baby step. Komai a hankali zaki bi sai kiga ya tafi yanda ya kamata. D’azu a sallahn magrib bai tsaya muka dawo tare ba, amma a sallan isha tare muka dawo har yake fad’a mini ba zai koma makaranta ba shi sana’a zai yi.” Cikin mamaki da kuma farin ciki Laila ta dubeshi ta ce, “Shi d’in ya fad’a maka haka? Ya yarda yana maka magana? Ya Allah nagode maka.” Haydar dubanta yayi yaga tsantsan farin cikin da take ciki sai yayi shiru bai fad’a mata ainihin abun da ya faru ba, ai hakan ma shima ya ji dad’i tun da Abul ya iya amsa mishi. Gyara zamanta ta yi ta dubeshi sosai ta ce, “Ya fad’a mini wai ya rasa Laptop d’insa da duk abun da yake ciki wanda hakan ne yasa ya ji ya fasa cigaba da karatun da yake yi. Ina ganin idan na saya mishi sabo zai fasa sana’ar ya koma makaranta.” “Anya kuwa? Ya san zai iya samun sabon Laptop amma na shi yake so wanda abubuwanshi suke ciki. Watak’ila sayarwa yayi, amma dai zan gwada mishi magana ko za’a iya tracking d’inta.” “Zai yi wuya Abul ya sayar da Laptop d’inshi ko da kuwa ya rasa abun sakawa a bakinshi ne, ina tunanin sace mishi aka yi ko kuma ya sha kayan maye ne ya mance in da ya jefar.” “Hakan ma zai iya yiwuwa amma dai zan gwada trying, watak’ila hakan ma zai sa ya k’ara sake jiki dani.” “To Allah yasa amma ni nafi son yaci gaba da karatunshi wallahi.” Fad’in Laila tana kwanciya a kan k’irjin Haydar. “Kiyi addu’a Allah ya za6a mishi mafi alkhairi kawai. Mutane nawa ne suka yi bokon amma babu aiki sun ajiye kwalin suna sana’a? Duk shawarar da ya yanke in har mai kyau ce kiyi supporting d’insa ko a gaba zai iya yin karatun Insha Allah.” “Allah ya za6a mana mafi alkhari to.” “Amin Amin.” Ya amsa yana k’ara jawota jikinshi. “Haydar.” Ta kira sunanshi a hankali. “Na’am Matar Haydar.” “Kamar ciki nake dashi fa.” Ta fad’a tana d’ago kanta suna kallon cikin idanun juna. “Meyasa kika ce haka?” Ya tambayeta amma nan zuciyarsa sai da ta buga da k’arfin gaske yana addu’an Allah yasa akwai cikin. “Kawai haka nake jin changes a jikina kamar lokacin da nake da cikin Junior.” “To Allah ya kawo mai albarka amma gobe ki gwada mu gani.” Gyad’a kai ta yi ta k’ara kwantar da kanta a k’irjinshi tana sauraran bugun zuciyarsa hankalinta a kwance domin murmushi ne ma a fuskarta, kuma tana fatan Allah yasa cikin ne a jikinta saboda bayan ta haihu Haydar ya nemi ta yi planning tun da bata son d’aukan ciki amma ta tuna mishi alk’awarin da ta d’auka a lokacin da ya dawo, wanda take cewa zata cigaba da haihuwa har lokacin da ta isa menopause d’inta. Farin cikin da Haydar yayi a ranar har sai da ya sakata ta yi hawaye saboda shima hawayen yake yi ya rungumeta yana mata godiya tare da saka mata albarka babu k’akk’autawa. Yanzu watan Mas’ud J shida kenan amma bata samu ciki ba bayan duk hiran da suke yi kusan kullum sai dai in ita ce ta nuna ta gaji yake d’aga mata k’afa. “Yau ma akwai hiran ne?” Ta tambayeshi tana kai hannunta jikinshi in da yafi buk’atarta. “Kullum, sai dai in ke kika ce a’a.” Ya fad’a yana kashe wutan d’akin. “Make less noise don yanzu yaran biyu muke da su.” Ta furta a hankali cikin kunnenshi. “An gama Matar Haydar.” Washe gari da asuba Haydar ya bugawa Abul k’ofa suka tafi masallaci tare, suna dawowa Abul ya sake komawa bacci shine bai tashi ba har k’arfe goma na safe. Wanka yayi sannan ya fito ya samu babu kowa a falon sai mai aiki da take shara ta gaisheshi ya tambayeta ina mamanshi ta fad’a mishi tana d’akinta. A cikin d’aki ya samu Laila na yiwa Mas’ud junior wanka wanda shima bai jima da tashi daga baccin ba, yana ganin Abul ya fara buga ruwan ciki bahon yana dariya irin ya ganeshi d’in nan. “Morning to you too young man.” Abul ya fad’a yana isa cikin d’akin ya zauna a bakin gado yana murmushi. “Ka tashi?” Laila ta tambayeshi tana jin zuciyarta kamar zata fashe tsabar murna da farin ciki. “Na tashi. Ina kwana Mama?” “Lafiya kalau. Ya gajiyan hanya.” “Alhamdulillah.” Ya amsa yana kallon Junior da yake k’ok’arin barin cikin bahon wai zai zo gurinshi. “Ka tsaya in d’auraye maka jikinka sai ya d’aukeka mana.” Ta fad’a tana rik’eshi yana neman yin kuka. Cikin sauri ta gama mishi wankan ta mik’ashi ga Abul ko towel babu a jikinshi, sannan daga baya ta bawa Abul towel d’in ya lullu6eshi yana goge mishi kanshi suna yiwa juna dariya babu gaira babu dalili. “Mama meyasa baku mishi kaciya ba har yanzu?” “Babanshi yace sai ya cika shekara biyar ko shida.” Ta tashi tana shigar da bahon cikin band’aki sannan ta dawo tana goge gurin da mop. Bayan ta mayar da mop d’in ta dawo ta samu Abul na shafa mishi man shafawa bayan ya bashi abun wasa yana kad’awa. Tsayawa ta yi a kansu tana jin hawaye na taruwa a idanunta domin har yanzu bata gama yarda wai Abul ne zaune kusa da ita yana ta6a d’anta da Haydar ba. A zatonta zai tsani d’an har yayi k’ok’arin yi mishi mugunta amma sai gashi cikin k’ank’anin lokaci har sun saba da juna, wato jini ba abun wasa bane. Sai da ta gama shirya Mas’ud J sannan suka dawo falo Abul ya zuba abinci yana ci ita kuma tana bawa Mas’ud J nono. Har Abul ya gama cin abinci ya dawo falo shi bai daina shan nonon ba, zama yayi a kujera ya ce, “Baya k’oshi ne?” “Waye? Ohh Mas’ud? Haka yake, amma idan ya k’oshi shi da kanshi zai juyar da kai.” Ta fad’a tana murmusawa. “Mama are you happy? A hakan?” Laila ta jiyo tambayar a bazata wanda hakan yasa ta sunkuya ta dubi yaron dake kan cinyarta yana ci daga jikinta yana mata murmushi ta d’ago kai ta kalli Abul ta ce, “Ina cikin farin ciki Abul saboda a yanzu ina jin kaina complete ba tare da na ji kamar na rasa wani 6angare na jikina ba. I am happy because I found love again bayan na cire rai da samun hakan. I’m happy saboda a yanzu babu mai kirana da sunan karuwa sai dai ace na auri yaro wanda baya damuna saboda nasan hakanne babu k’arya a ciki kuma ba sa6awa Allah nayi ba illa kwaikwayo da nayi da Manzon Allah SAW, amma ka ga kwanaki da ake mini k’azafin zina? Na shiga damuwa sannan na ji bak’in ciki mara misaltuwa. I’m happy Abul, and Ina son in mutu cikin wannan farin cikin.” “Then nima I’m happy for you Mama. Wannan rayuwarki ce wanda ke kike da ikon tsarashi yanda kike so, I’m sorry I couse you pain da kuma bak’in ciki. Everyday fucking day ina regretting yanda na 6ata tawa rayuwar akan abu da kika tsarawa taki rayuwar, I don’t know what got in to me da har nayi tunanin hakan zai sa ki rabu da mijinki ki yi rayuwa kamar yanda nake so. Kaala Abdi said I’m selfish and I agreed, everything I did is about me not about you or Sabrin, nine ya kamata in kula daku amma sai ya kasance ku kuke kula dani I failed as a man. Babana ba zai ta6a yin farin ciki dani ba idan yau ya samu labarin halin da na jefa kaina a ciki don kin nemi farin ciki a karo na biyu. Kaala Abdi said all that and I believed him, I’m so sorry Mama don Allah ki yafe mini bak’in cikin dana sakaku a ciki. I promise to support you duk da cewa I hate your husband amma I will like to see you happy ko da kuwa dashi ne. I’m sorry Mama.” Laila kuka ne ya kwace mata wanda hakan yasa Mas’ud J ya sake nonon yana dubanta shima fuskarsa a kwaye alamar zai yi kuka. Ganin haka yasa ta yi saurin share hawayen fuskarta tana juyar da kan yaron ga barin kallonta, sai dai shima Abul d’in hawaye yake yi kanshi a gefe kamar wanda baya son a ga me yake yi. “After all that happened Abul, na koyi yafiya ga mutane ko da kuwa sun mini cuta mafi muni kuma na koyi zama da su da suka canja halayensu. Kullum idan na zo bacci sai na furta yafiya a gareka saboda bana fatan Allah ya kamaka da alhakina a ranar gobe balle har ace a dalilina ka shiga wuta. Komai ya wuce Abul, ka manta da komai kamar ba’a yi ba. Na yafe maka duniya da lahira, da abun da ka mini a baya da wanda zaka mini a gaba duk na yafe maka, sai ka nemi yafiyar Allah domin shi ka fi sa6awa da ka kauce hanya da hankalinka da kuma iliminka. Allah ya yafemu gaba d’aya.” “Nagode Mama.” Ya fad’a yana share hawayen fuskarsa. Itama hawayen nata ta share kana ta mik’e tsaye ta ce, “Ka je kaci abinci sai ka tafi gidan Sabrin d’in domin tun da safe ta kira na fad’a mata kana bacci.” “Ki bar abincin kawai domin nasan ta mini a can.” Ya fad’i hakan yana komawa d’akinsa ya d’auko abu ya dawo falon ya mik’a mata. Laila k’ar6a ta yi tana dubawa cikin farin ciki domin laffaya ce a cikin ledarta mai kyau, ya ce, “Tsarabarki ce, ga nan ta Sabrin.” Ya nuna mata na hannunshi wanda ke cikin leda. “Ka kyauta sosai nagode, a ina ka samu kud’i haka?” Ta fad’a cikin d’oki tana warware laffayar ta fara d’aurawa bayan ta mik’a mishi Mas’ud J. “Sauran kud’in da kike ajiye mini a gurin Kaala Abdi ne.” “Masha Allah gashi kalar ta mini kyau, shukran habibi.” Tana gama nad’awa ta shiga d’aki ta d’auko jakarta da kuma baby bag d’in Mas’ud J ta fito tana cewa, “Mu tafi.” “Ina zaki je?” Ya tambayeta. “Shago zan je, ai tun lokacin da Sabrin ta fara zuwa school ni kuma ya zama kullum sai na je.” “Ohh!” Da haka suka fita zuwa tsakar gida Laila ta rufe gidan kana ta mik’a mishi key d’in motar tana cewa, “Mu je ka ajiyemu a shago sai ka tafi gidan Sabrin d’in. Idan na tashi zan kira Haydar ya dawo dani gida.” Bai yi musu ba ya kar6i key d’in ya shiga itama ta shiga gaba sannan ta kar6i Mas’ud J daga hannunsa ya kunna motar suka fita daga gidan suna hira gwanin ban sha’awa. A bakin shagon yayi parking ta fita daga motar amma Mas’ud J na ganin shago za’a shigar dashi sannan ga wani a mota zai tafi yawo sai ya fara kuka yana mik’a hannun zai tafi gurin Abul. “Mas’ud hoo, kai kenan kullum a dinga yawo da kai baka son zama guri d’aya? Ya Salam!” Ta fad’i hakan tana gyara gyalenta da yaron yake k’ok’arin yaye mata shi. “Kawo shi mu tafi tare, I hope akwai kununshi a cikin jakar nan?” Ya nuna baby bag dake bayan seat. “Are you sure? Ko da yake sometimes ana kaishi gidan Sabrin yayi awanni ma.” Da haka Laila ta sakashi cikin car seat d’inshi ta saka mishi belt kana ta rufe marfin motar tana cewa, “Ku gaisheta.” Murna fal fuskarta. Bata ma shiga cikin shagon ba ta kira Haydar ta sanar dashi abun da ya faru sannan ta kira Mas’ud shima ta sanar dashi wannan abun farin cikin wai Abul d’inta ne ya shiryu yake kuma huld’a da ita kamar da. Abul yini yayi a gidan Sabrin tare da Mas’ud J wanda da yaji yunwa zasu bashi kunu ya sha ya k’oshi, da ya gaji da kunun ne ya fara neman nono hakan yasa Abul ya yiwa Sabrin sallama suka dawo gida da yamma bayan la’asar. A falo suka tarar da Laila da Haydar suna zaune amma Abul bai kula Haydar ba, yana mik’a mata Mas’ud J kuwa ya shige d’akinsa ya barsu a nan. Da daddare Mas’ud da matarsa Naana da ‘yar su Sultana mai wata d’aya a duniya suka zo yiwa Abul Sannu da dawowa, Abul ya gaishesu cikin mutunci ya k’ar6i snacks d’in da Naana ta mishi ya shige d’akinsa ya barsu a falo suna hira da Mamanshi da Haydar. Bayan kwana biyu da haka, a weekend da safe Haydar ya tarar da Abul zaune a falo yana danna sabuwar wayar da Laila ta saya mishi. Zama yayi a gefenshi sannan yace, “Ka fad’a mini cewa baza ka koma school ba, sai daga baya Mamanka ta fad’a mini cewa saboda ka rasa Laptop d’inka ne shiyasa ka ji karatun ya fita a ranka. Idan sacewa aka yi let’s try tracking it ko za’a samu, I know zaka iya hakan. In kuma 6aci yayi let’s get you a new one ko da kuwa sana’ar zaka yi.” Shiru Abul yayi yana tunani domin shima yana son ya samu laptop d’in amma idan ya tuna cewa a gidan Sadistic Faruk ya bari sai ya ji gwuiwowinsa sun yi sanyi don ya tabbata Faruk zai lalata ko kuma ya k’ona. Amma an ce ‘A man can dream’, deep down yana ji a ransa Faruk bai lalata laptop d’in ba, sai dai ta yaya za’a iya zuwa a ce ya basu? Basu da wannan connection d’in yanzu, sannan ba zai yarda su sake had’uwa ba saboda har yau bai manta irin wasa da rayuwarsa da yayi ba. “Yana Abuja gidan Senator Gambo Umar.” Haydar da bai yi tsammanin zai samu amsar Abul ba ya gyara zamanshi ya ce, “A gurin waye yake? Sannan meya faru har ka bari a can?” “It’s a long story, but a gurin d’anshi Faruk yake. Sannan mun yi rabuwar babu dad’i saboda shi ya mini wannan lahanin a k’afata wanda har yanzu da d’ingishi kad’an nake tafiya.” “Banney told me yanda aka kawo musu kai, but he never tell me abun da ya faru a gidan ba. Ya ce labarinka ne idan ka ga dama zaka iya fad’a mini.” Duk abun da Haydar ya fad’a Abul sunan Banney kad’ai ya rik’e ya juyo cikin sauri ya ce, “Kana tare da Banney har yanzu? Don Allah ina yake?” Yanda yayi maganar with desperation in his voice yasa Haydar ya ciro wayarsa daga aljihunsa ya bashi numbern Banney wanda a yanzu shima ya shiryu har ya koma makaranta bayan an sha daga, domin da kyar aka d’aukeshi a fannin Medicine bayan sun samu labarin ya ta6a shaye-shaye. Sai dai ilimin da yake da shi yasa suka d’aukeshi a kan duk ranar da aka kamashi da kayan maye ya daina medicine kenan har abada ko da kuwa zai canja k’asa ne. Abul yana jin Banney ya d’auki wayar ya tashi a gurin ya wuce d’akinsa yana kiran sunan Banney kamar bai gaskata dashi yake waya ba. “Stepdad d’inka ne ya baka number na ko? Yaushe ka dawo gida ko har yanzu kana Maiduguri ne?” “Shine ya bani kuma na dawo gida. Meyasa baka nemeni ba all this while Banney? Where are you?” “Bana son in yi waya da kai in ji kana cikin wannan halin da na bari ne Abul, ina garinmu har na koma school na fara daga farko. Guess duk shekarun da nayi ina karatun sun zube a yanzu. How are you? Don’t tell me you are fine, ka fad’a mini halin da kake ciki nake so.” “Na dawo gida, na rok’i mamana gafara and my fucking stepdad ya bani adorable stepbrother. I will send you his pictures together with me. What about you.” “First of all, I’m who I am today saboda wannan fucking stepdad d’in naka, shi ya tsaya mini har na samu makaranta ya kuma d’auki nauyin duk expenses d’ina ba tare da ya gaji ba. After every two months yana zuwa dubani a school in da nake zama saboda ban koma gidan mahaifana ba and he understands why bayan na sanar dashi duk labarina. Abul har yanzu iyayena basu canja ba, they are still dogs.” Abul runtse idanunsa yayi domin labarin Banney ko shi baya son ji bare wani, sannan shi bai ga bak’in cikin da Banney ya gani ba a rayuwarsa dalilin k’azamar rayuwar da iyayensa suke ciki. Amma a hakan Banney ya gyara rayuwarsa sannan yaci gaba da karatunsa don ceto wanda yake da niyyar cetowa tun farko. Shi kuma me aka masa ma? Don uwarsa ta auri yaro shine har yake da guts d’in lalata rayuwarsa? Ya aka yi ma ya bari maganar mutane ta yi tasiri a zuciyarsa har ya za6i wannan jakar hanyar a matsayin mai 6ullewa. “I’m sorry dude.” “Ka tayani yi musu addu’a, ka kuma tayani yiwa Uncle Haydar godiya saboda shi ya taimaki rayuwata ya cironi daga gagari. Na kusa samun hutu na sati biyu, kuma I promised him a gidanku zan yi. Be nice to him or I will kill you with doctor’s scissors.” Dariya suka yi dukkansu Abul ya ce, “I missed you man.” “You sound gay mallam. I mean it, be nice to that man. Yana son mamanka tsakani da Allah kuma yana kareta daga shiga depression ta hanyar halal saboda tsawon shekarun da ta d’auka bata da auren nan zai iya messing da brain d’inta.” “Fuck off man, this is my mother we are talking about.” “Call it Doctors intuition but your mother sound happy idan nayi waya da ita, idan zan samu ni tawa mahaifiyar ta zama haka I will literally worship that man. I respect your stepdad, so idan kayi disrespecting d’insa a gabana I swear zan manta duk abotanmu in ci…..” “Kar ka zagi uwata.” Abul yayi saurin warning d’insa yana murmushi saboda yayi missing d’in Banney ba kad’an ba. “I will never! Nima uwata ce kuma ta fi daraja akan wacce ta haifeni.” Sanyi Abul ya ji a zuciyarsa domin zai iya cewa Banney shine abokinsa da yake jin sonshi har cikin zuciyarsa, jin yana cikin farin ciki a dalilin Haydar kuwa yasa yaji sassauci game da tsanar da yake yiwa mijin uwar tashi. Sun dad’e suna waya wanda Abul har yana mamakin yanda Banney ya san komai na gidansu, domin har fad’a mishi yayi cewa shi zai tura mishi pictures d’in Mas’ud J tun yana jariri har zuwa yanzu. Wannan abu yasa Abul yaji kishi kad’an domin wani bare ya fi shi sanin k’aninshi. Suna gama waya ya koma falo don yiwa Haydar godiya amma sai ya samu baya nan, komawa d’akinsa yayi ya bari a kan cewa zasu had’u a masallaci sallan magrib. Haydar kuwa yana ganin Abul ya shiga d’akinsa ya tashi ya fita daga gidan yana danna wayarsa. Ana d’auka yayi sallama yace, “Brother I need your help.”

Mum Fateey 👌

Back to top button