Ajiya A Duhu Book 1 Page 19 Complete Novel
🅿️➖1️⃣9️⃣…….Sosai ƙannen Yazeed sukai farin cikin dawowar mahaifiyarsu gidan. Gaba ɗaya sun zagayeta anata cakai-cakai kowa na bata labarin abinda ya faru da bata nan. Itako sai murmushin jin daɗi take yi musamman akan abinda suka dinga ma Ammie. Suna a hakan Aunty Sabuwa ta samesu. Tashi Hajiya Yaya tai suka shige ƙuryar ɗaki suka rufe kansu. Dama itace tai kiranta tunɗazun bayan wucewar su Babansu. Sai da Aunty Sabuwa tasha fresh milk ɗin data ɗakko daga falo sosai sannan ta dire tana sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Kai nafa kwaso rana da yawa. Kin ganni nan daga tudun wada nake. Kin san munata shirye-shiryen bikin ƴar ƙawata Sailuba. Ko sanda kika kirani muna tsaka da meeting ne ma dan tun sassafe na baro gida” “Kai kar dai kice min bikin yarinyar nan har yazo?”. “Wlhy kuwa yazo Yaya ai abin babu wuya…” “Gaskiya ba wuya kam. Abin mamaki wai Sailuba da aurar da ƴa”. “Hhh kai yaya da abin dariya kike. Yo ALLAH na tuba komu badan yaran nan sun tsaya ruwan ido ba ai da tuni jikoki sun cika mana ko’ina.” “Ai dan ubansu dole kam suzo su fito da mazajen aure dan na gaji da ganinsu ɗirka-ɗirka a gida sai yawo bikin wasu da taron birthday party. Ba maneman nan suka rasa ba amma narasa mi sukema hange-hangen”. “A’a to yadai kamata wlhy Yaya. Yanzu abin sha’awa bakiga yarinyar nan yanda mijin ya haɗo lefe na nunama sa’a da tsara ba. Jiya mukaje muka duba gida komai yaji gidansa kamar ka zauna kaita kallo. Kuma karki daɗa karki raga yaron shagone wlhy. Amma komai babu raini”. “To Sabuwa ai dama abin zuciya ce ba dukiya ba. Sai dai kuma kana gudun inda yaronka zai je ya ƙasƙanta ne. Ko ka saida akuya ta dawo tana ci maka danga.” “Da wannan kuma dan wannan. Yanzu dai zakije min baici ko?”. “A mizai hana, ranar yinin biki insha ALLAHU zan zo, ai Sailuba nada mutunci da girmamawa. Yarinyar nan ko sanda kike zaune a Kano indai tayo tanan anguwar dai ta shigo mun gaisa”. “Sailuba ai bata da damuwa Yaya. Damma ALLAH ya bata shegen miji ne kawai. Wai shi uztazu. Ko akan bikin nan sai da muka bisa ta ƙasa sannan fa ya amince da wannan shagulgulan amma da duk ya hana”. “Oh kice dai kuna nan da halin bin malam nan maƙaryata ko Sabuwa?”. “Ko ɗaya aunty kawai dai sai ta kama. Wani lokacin ne halin mazan nan sai ka haɗa da dabaru. Yanzu ko ke abinda Yaya ke miki a gidan nan da zaki bari ai masa ɗaurin huhun goro ai da kin wuce wajen. Ko su su Basariyyan haka nan suka zauna ne kike gani. Ai wlhy ba banza ba yake wannan rawar jikin akansu har shi ma Yazeed ɗin”. “Zan iya yadda dake wlhy Sabuwa, dan yau naga abu a gidan nan. Kai Basariyya makirar mata ce. Tabbas na tsani Asiya kuma bana sonta amma wani lokacin gara min ita sau dubu akan Basariyya……….” Tsaf Hajiya Yaya ta labartama Sabuwa yanda komai ya faru yau a zaman da akayi, har hukuncin da su Baba suka yanke. Sosai Aunty Sabuwa ta sauke ajiyar zuciya da har sai da Hajiya Yaya ta ce, “Lafiyarki kuwa irin wannan ajiyar zuciya haka?”. “Wlhy ƙalau Yaya. Naji kawai abubuwan duk sun zo da sauƙi ne. Koba komai ai mu munafuncin Basariyyan yaman rana yau, dan in dai an rigada anyi na Nazeefar Asiya kuma sai dai ta nema ma ƴarta wani mijin amma ba Yazeed ba”. “Nima haka nace ai, shiyyasa ma na ƙyalesu aje a hakan. Amma kuma kin san Basariyya maciji ce bata ramin kanta. Mi kika fahimta a wannan salon nata?”. “Hassada ce kawai wlhy Yaya. Tasan auren Yazeed sai ya zama na nunama tsara a gidan nan shiyyasa take so ta cusa na ƴarta ayi tare. Kuma tayi na banza dan babu abinda zamu fasa sai ma mu ƙara in sha ALLAHU. Ita waye ƴar nata zata aura ma shin?”. “Yo waya sanan musu bata faɗa ba. Ai kin santa ita komai nata ƙunshe-ƙunshe saboda munafunci bata so a sani. Amma nidai tunda nake a gidan nan ban taɓa ganin wani fitaccen baƙon mutunci da za’a kirashi mijin aure yazo wajen Huznah ba. Sai dai idan ba’anan gida ake taɗin ba”. “Eh ai munafuka ce zata iya tsara komai. Shiyyasa wlhy Yaya ki zagargari yaran nan suma su fiddo mazan aure, in ba hakaba zataita kutsawa ne dan taga ta gama aurar da nata yaran duk ɗan abin arziƙin su wawashe a barsu su da saura. Kina dai gidan nan agololi biyu sukai aure Yaya ya dinga ɓarin kuɗi kamar babu gobe. Badan mun daƙile wannan ba ma dana uku kenan. To shi dama aurar da yara haka yake na farko-farkon nan sunfi morewa, dan anfi kashe musu dukiya”. Sosai zancen Aunty Sabuwa ya shigi Hajiya Yaya. Cikin juyayi ta ce, “Oh dama haka abin yake Sabuwa? Amma shine baki fargar dani ba tuntuni”. “Ba fargar dake ne banyi ba Yaya. Kin san auren agololin can munafuntarmu akai akaita komai kamar talakawa zasu aura shiyyasa bamu bama abin muhimmanci ba. Sai daga bayan nan muke ganin ashe lulluɓin biri akai mana da fatar kura. Kuma ko rantsuwa nayi banyin kaffara Yaya ne ya samawa yaran nan mazansu. Shegu da yake suma burin su kenan gasu nan har da ƴaƴa bibbiyu”. “Humm ai Daddyn Yazeed ya jima yana zaluntata a gidan nan ban farga ba. Kiga fa Asiya ta bayan bayana wai itace da waɗan nan nasarorin. Babu komai zamu ɗauki mataki”. “Babban ɗaukar mataki ALLAH Yaya kuɗi zaki fiddo ko ki shirya ma dake muje ayo miki aiki ɗan gaske. Mufa ba bokaye muke bi ba. Malamai ne na zaure, kin ga ko kaje wajen malami ba bokaba ai babu batun rasa sallar da ake cewa ta kwana arba’in ko?”. “Hakane kuma. Inaga dai wannan karon zanje ɗin”. “Haba koke fa yaya”. (Humm ALLAH ai ba’a masa wayo ko dabara Sabuwa. Idan abu ya dameka ka miƙa lamarinka ga UBANGIJI shi baya barci kuma baya mantuwa. Fafi yawan wasu abubuwan da muke ɗaukarsu damuwa a rayuwarmu hassada ke mana jagora akansu. Amma mu sani rabonkafa rabonka ne. Sannan wani baya canja maka ƙaddararka. Duniyar nan cike take da arziƙi, ka tsarkake zuciyarka ka nema naka kaima in dai nakan ne wani bai isa tare maka wannan samun ba ko ya ƙarama kansa. Shima iya nasa kawai zai ci. Ya rabbi ka yafe mana kurakuranmu😭🙏 ka gafartama iyayenmu 🙏).____________★ “Tabbas da manufa kam ta ƙarfafa maganar taki Asiya. Amma kada ki wani damu. Mu ALLAH yasa haka shine mafi alkairi. Dan nima ta bakinki zuwa yanzu auren Maanal da yaron nan ya fita a raina. Duk kuwa da shi ɗin mutumin kirki ne. Amma halin uwarsa da ƴan uwansa bazai bar Maanal zama lafiya ba. Gata ita mai rauni. Ni yanzu abinda nake gani kawai mu lallaɓa Maanalu ta bama yaron nan Rafeeq dama ya shigo sosai, shi kansa Yazeed ɗin ba lallai idan sun aura masa tasu ba su barshi haka ai”. Tabbas hakanne Nene, ni kaina wlhy yaron nan Rafeeq yamin. Yaron a haka dai kamar baida wata damuwa. Gashi kuma ɗan uwan Majdiya uwa ɗaya uba ɗaya. Majdiya mutuniyar kirkice ga addini. Dan hatta yaranta tarbiyyarsu ta banbanta da sauran ƴaƴan gidansu. To dan dai yaran yanzu ne kai kana hango musu alkairi su suna wani hange daban. Amma dai yanzu zanyi duk yanda zanyi ta cigaba da zama can Abujan dan bana sha’awar dawowar Maanal gidan nan a yanzu kuma sam Nene wlhy”. “Wannan ma tunani ne mai ƙyau. Gara ta zauna a can ɗin kusa da ƴar uwarta. Tunda shima can yake Rafeeq ɗin sun ma fi samun shaƙuwa. To amma shi maigidan naki bazaiga an masa ba daidai ba?. Kinga dai yanda yake matuƙar ƙaunar yaran nan da musu hidima. Tunda kuka dawo hannunsa bai taɓa bambanta al’amarin su dana ƴaƴansa ba”. “Tabbas hakane Nene. Nima idan na tuna hakan jikina yana sanyi. Dan ya musu abinda mahaifinsu da ƴan uwansa suka gagara musu. To amma yaya zamuyi, matar nan wlhy ta wuce duk yanda kike tunani. Nata ma mai sauƙi ne, dan babbar matsalarta itace ƙanwar nan tata. Saboda mashawarta ne bata moreba kawai, amma duk masifarta ta wani fannin tafi Basariyya sauƙi”. “To mu cigaba da addu’a, ALLAH ai bai manta da kowa ba. In sha ALLAHU komai zai kasance da sauƙi. Yanzu dai sai kisan dabarar da zaki masa akan zamanta ɗin can dan a rabu lafiya har su gama wannan bikin nasu. Saboda yanzu kam kema fa sai kinyi haƙuri, zakiga abubuwa da yawa wanda za’a dinga miki su da gayyane.” “Hakane Nene. In sha ALLAHU babu damuwa. Dama dai matsalar tawa Maanal ce. Dan su wannan samarin babu ruwansu. Itace dai dama ina tsoron a jangwalo ciwon nan nata. Amma idan bata gidan koma mi suke shirin yi suyita yi”. Nene ta gamsu sosai. Dan haka suka cigaba da tattauna batun Maanal ɗin dai. Nene bata bar gidan ba sai bayan magrib. Ammie ta rakota sukaci karo da Hajiya Yaya itama ta rako Sabuwa. Kallon banza suka dinga musu. Dan Nene ma na gaishesu amma ko kulata basuyi ba sai ma tsaki da Sabuwa taja musu mai ƙarfi. Abin ya ɓatama Ammie rai amma sai ta danne. Itama Nenen duk da nata ran ya ɓaci sai ta danne dan bata son ƙarama Ammien damuwa… _________★ Damuwa da ɓacin rai da tashin hankalin hukuncin da aka yanke yasa a ranar Yazeed ya koma Abuja batare da sanin kowa ba. Ita kanta Hajiya Yayan sai da dare ta aika Basira kiransa ta dawo ta sanar mata ɗakinsa ma a kulle yake. Waya ta ɗaga tai kiransa. Batare da amsa sallamarsa da gaisuwarsa ba tace yazo tana nemansa. Haƙuri ya bata akan shi fa ya koma Abuja. Dan ya samu kira na gaggawa. Ranta ya matuƙar ɓaci amma sai ta danne bisa shawarar da Sabuwa ta bata na a dinga lallaɓashi yanzu har ayi a gama lafiya. Cikin sauƙaƙa murya tace shike nan idan ya dawo sayi magana. ALLAH ya bada sa’a. Ya amsa mata da Amin, dan ko yaya ya ɗan ji sauƙi a ransa na jin bata fushi da shi. Yazeed mutum ne mai kiyaye fushin iyaye, sannan yana da takatsantsan akan al’amarinsu. Ko wannan maganar Manaal ɗin da ace babu goyon bayan Daddy duk son da yake mata da tuni ya haƙura saboda mutuntasu…. ________★ A Abuja dai kam RK ya riƙema Maanal wuta. Dan kullum sai yazo gidan Shahidah sai ya fake da dubata yazo yi kasancewar dama sun sanar dasu hakan. Sai dai abinda basu sani ba duk tsarin RK ne dama akan batun zuwa gida dubatan kullum. Ya cigaba da kwaɗaita mata zancen aiki. Tun tana dojewa harta sanarma Shahidah. A mamakinta sai Shahidah ta bata goyon bayan mizai hana ta amshi tayinsa. Ai abune mai ƙyau neman nakanka musamman a wannan zamanin. Cikin damuwa Maanal ta ce, “Amma Didi kin san Ammie bazata yarda ba. Hakama Daddy zaiga kamar mun nuna gazawarsa ne musamman idan mukai dubi da duk yaransa mata babu wadda ya bari tayi aiki, ko ku sai da kukai aurene yace idan mazanku sun yarda kuyi aikinku. Idan ni kuma nazo masa da sabon tsari sai yaga kodan bai haifemu bane ba”. “Hakane Maanal. Amma idan aka duba naki al’amarin ke ai yana buƙatar uziri. Bazamu yanke hukunci ba yanzu ki bari zan sanarma Ammie to. Itama Amal zanyi magana da ita. Amma ko nan Daddyn su Barru shi goyon baya ya bada ɗari bisa ɗari, ya kuma ce in dai dan Daddy ne shi a barsa zaiyi magana da shi. Kinga an samu sauƙi kenan ai”. “Shike nan ALLAH ya zaɓa mana abinda yafi alkairi.” “Amin ya rabbi, wannan dama itace addu’ar daya kamata kiyi tun farko. Sannan dan ALLAH idan yazo ki daina ɗaɗɗaure masa fuskar nan taki, hakama idan ya kiraki kina ɗauka Auta. Wulaƙanci sam bashi da ƙyau”. “Didi ba wulaƙantasa nake ba nima. Bana son ya saki jiki akan abinda bazai samu bane kawai”. “Hummm Maanal kenan. ALLAH dai ya zaɓa mana abinda yafi alkairi”. Maimakon ta amsa da Amin sai Maanal ɗin kawai ta koma ta kwanta dama tana a ɗakinta ne tana karatun novel ɗin nata na fama Shahidahn ta sameta……..✍️
