Hausa novels

Fentin Zina Page 13 Hausa Novel

***Da dare bayan sallan isha suna zaune cikin dakin inna da Ameena da fateema inna bata ciki tana dakin baba malam.Hira sukeyi sosai suna dariya inna ta dago labulen tace Ameenatu babanku na kiran ki dauki mayafi kije maza.Dum gabanta ya bada sautin bugu cikin sanyin muryar data dirar mata yanzu tace toh inna.Sake labulen tayi ta koma Ameena ta bita a baya ta shiga da sallama lokacin har inna ta zauna.Yauwa karaso Ameenatu zo ki zauna nan kusa gare ni, baba malam ya fada yana nuna mata kasa kusa dashi.Furucin shi sai ya dan saukar mata da natsuwar firgicin data shiga ta tako a hankali ta zauna ta kara gaishe shi ya amsa yana shafa kanta domin haka ya sabar musu duk in zaiyi magana mai muhimmanci dasu.Ameenatu…..Baba malam ya kira sunan ta.Ta dago kai ta amsa da na’am.Baba Malam ya cigaba da fadin, inaso ki natsu ki saurari abunda zan fada miki da kunnen basira.Toh baba.Yauwa! Ina wannan yaron Ahmad dana bashi izini akan ki?.Tunda ya ambaci sunan Ahmad taji muguwar faduwar gaba cikin dan rawar murya tace yana nan baba.Toh kina jina?.Ta gyada kai.Na janye maganar shi wannan yaron sakamakon nayi bincike akan shi wanda tun farko ya kamata inyi sai banyi ba toh dai na gano dabi’unsa marasa kyau da bai dace in bari tarayyar ku ta cigaba a haka ba ina fatan kin gane?.Ameena tsabar rudani bata san duniyar da take ciki ba sai da ya kara kiran sunanta ta amsa tana dawowa cikin hankalinta.Kindai ji abunda na fada miki ko Ameenatu? Nasan ki da biyayya da kuma hakuri dan wannan abunda na nema daga gareki bazai gagare kiba Ameenatu.Kuka take son yi amma bata son karya wa baba malam zuciya sai ta gyada kai.Ya cigaba da cewa, a wata unguwa da suka zauna a yadda na same labari ya lalata wasu ‘yan mata guda biyu rikicin da sukayi da iyayen yaran ya sanya suka bar unguwar suka koma wata da yake suna da dan shi, nanma hakan ce ta kasance a kalla yaran daya bata basu kirguwa kinga ko ban zama nagartaccen uba ba muddin na barki kika ci gaba da kula wannan yaron don haka ina mai baki hakuri nasan abun zaizo miki bambarakwai kuma shigar sauri ki daure insha Allah zaki samu wanda ya fishi domin bada gaskiya yazo miki ba, yaudara ce kawai.Toh baba insha Allah zanyi yadda kace daga yau dinnan zan yanke alakata dashi ta har abada.Allah ya miki albarka tashi kije.Ta mike ta fita baba malam ya kalli inna yace naji tausayinta dana sani tun farko nayi bincike sosai kafin barin shi ya rabeta sai dai Allah ya fimu sanin abunda yake daidai.Hakane malam Ameenatu tana da sanyin hali ga tsananin hakuri da kawaici duk cikin yarannan ta fisu dabi’u masu kyau.Allah ya zaba mata mafi alkhairinsa.Ameen inna tace ta dan gyara kwanciyar ta.Ameena tana shiga daki ta fada kan gado ta saki kuka mai cin rai da ban tausayi, fateema ta taso tana tambayar ta Adda lafiya me ya faru? Me baba malam din ya miki kike kuka dan Allah ki bar kuka kada nima ki saka ni kin san aduk duniya babu abunda nafi tsana sama da in ga rashin walwalar ki.Tsagaitawa tayi da kukan ta mike zaune ta share hawayenta.Fateema ta zauna ta kamo hannunta tana shafawa alamar rarrashi tace kiyi hakuri dukda bansan me kikewa kuka ba amma ki sani komai yayi farko yana da karshe.Fateema ashe Ahmad mayaudari ne macuci? Ashe azzalumi ne mai lalata diyoyin mutane? Ashe Ahmad ba son aure yake mun ba? Ta kara fashewa da sabon kuka, wannan karon Fateema bata yi yunkurin hanata ba har saida ta gaji don kanta tayi shiru.Kiyi hakuri adda nasan abunda ciwo dukda bazan ce ga yadda kike ji ba amma zan kiyasta, yanda yazo da nufin yaudarar ki mun godewa Allah da har manufar shi ta bayyana mana da wuri ba tare da ya kai ga ci ba, Allah ya saka miki cin amanar ki da yayi.Insha Allah yanzuma zan tura mishi massage na rabuwa ta har abada.Gaskiya ne bai kamata ya cigaba da kallon ki a matsayin wacce ma ya sani ba gara yasan cewar kin gano manufarsa.Ahmad ya ci amanata ya karya yardata akan kowani da namiji bazan sake aminta da kowani saurayi ba don dukkansu suna suka tara, miko mun wayata in rubuta masa sakon don banaso har saina huce.Dauko wayar fateema tayi ta mika mata ta zauna a gefen ta.Shiga bangaren tura sakonni tayi ta soma rubuta sako kamar haka.””Assalamu alaikum bayan gaisuw da fatan alkhairi ina fatan zakayi hakuri da abunda zaka ji daga gareni, mahaifina ya gudanar da bincikensa akan ka kuma sakamako ya fito ka fadi jarabawar shiyasa na zabi sanar da kai da wuri domin babu bukatar mu ci gaba da bata ma juna lokaci, a karshe ina yi maka fatan samun wacce ta fini, na barka lafiya, daga Ameena!””Bata jira ta kara karantawa ba ta tura sakon kai tsaye..Ba’a fi mintuna biyu ba sai gashi ya kirata bata dauka ba ya sake kira bata dauka ba a kira na ukunne fateema tace adda gara ki dauka ai ku karkare.Bata musaba ta danna receive, a nashi bangaren yana jin ta daga ya fara da cewa, sweetheart dan Allah kada ki kashe mun waya na rokeki ki tsaya ki saurare ni wallahi kage aka mun duk abunda kika ji wanda yayi sanadiyyar kika yanke wannan danyen hukuncin ba gaskiya bane sai dai idan makiya ne suke son shiga tsakanin mu amma na rantse miki ni babu abunda nayi.Ba cewa akayi kayi wani abunba kawai yafi dacewa mu yanke alakar dake tsakaninmu cikin dadin rai ba tare da dayan mu ya cutu ba.Haba sweetheart cuta kam dai? Wace cuta ce za’a mun ni Ahmad wacce tafi rabani dake babu ita duk duniya.Sauke numfashi tayi cikin huci domin har karkashin zuciyarta take jin ta tsane shi kuma iya gaskiyar ta take fada baza ta ci gaba da rayuwa dashi a cikin zuciyarta ba, ta budi baki tace kaga Ahmad Allah ya baka wacce ta fini kuma dan Allah kada ka sake nema na.Daga haka ta kashe wayar bata saurari magiyar da yake mata ba.Kwanciya tayi tana fadin ya Allah kasa hakan shine mafi alkhairi a rayuwata.Ameen fateema ta amsa mata.An dauki akalla watanni lokacin harta kammala waec and neco dinta, i zuwa yanzu ta manta da babin Ahmad ta share shi daga cikin rayuwarta tana ci gaba da samun natsuwa da farin ciki ita a gareta hakan ma yafi mata kwanciyar hankali.Yau tunda ta tashi take jin faduwar gaba ga rashin natsuwa, inna da fateema aun fita zuwa layin gabansu dubiyar mara lafiya sai ita kadai ce a gida baba malam ma baya nan dama yayansu kam ba mazauni bane.Tana zaune a tsakar gida tana wankin kayanta taji an kwankwasa kofa bata maida hankali ga kofar ba saboda babu mai musu wannan dabi’ar sai ta bari ko iskane ya dan taba kofar ta share ta ci gaba da wankinta, kwankwasawa aka kuma yi a karo na biyu sai ta mike dama da karamin hijabi a jikinta sai ta wuce zauren tana cewa waye?.Shiru ba amsa ba ta kara fadin waye?Nan ma babu amsa har zata koma cikin gida sai wata zuciyar ta raya mata ta bude taga ko waye hakanan tasa hannu ta bude kofar.Komawa da baya tayi ta jingina jikin gini sakamakon bugawar da zuciyarta tayi data yi tozali da Ahmad dake tsaye yana kallon ta.Kallon cikin ido sukayi wa juna na ‘yan dakiku yayinda Ameena taji duk wata lakka ta jikinta tana karyewa a lokacinda soyayya da duk wata kaunar da da take mai tana dawowa sabuwa harma ta ninja wacce take mai da, tanaji a ranta wannan karon babu mai rabata dashi babu wanda zai shiga tsakaninsu yasa su nesanta da juna, bata ce dashi komai ba hakan yasa ya shigo zauren ya tsugunna a kan kafafun shi yana kallonta ya hade hannayensa duka biyu waje daya alamar roko yace na azabtu da rashin ki da taayin lokutan da muka dauka bama tare dan Allah kada ki barni wallahi ban aikata komai ba ban san wani irin laifine mahaifinki yaji ance nayi ba ki yarda dani tsakani da Allah nike sonki ba da wata manufa ba.Tsugunawa itama tayi kamar yadda yayi tace kayi hakuri abun kauna bisa rashin fahimtata, kayi hakuri bisa yanke maka hukunci da nayi ban saurari naka hujjojin ba, ina sonka ina kaunar ka daga rana irin ta yau bazan kara rabuwa da kai ba, zan kasance tare da kai a ko wani irin yanayi nayi alkawari amma inaso ka rike mun alkawari da amana idan kayi haka ka gama mun komai.Ko wanda zai rushe walwala daga fuskar ki bana bukatar hada hanya dashi balle ni da kaina in aikata hakan! Har cikin zuciyata bargon jikina da duk wata jijiya ta jikina sonki ne a mamaye cikin su, babu bukatar baki ya furta domin koda zamu kwana mu yini mu sake kwana bazan iya gama karanto miki yadda nike kaunar kiba.Daidai zata yi magana kenan sai inna da fateema sukayi sallama, fateema ce a gaba sai inna a baya, dukkansu kusan suman tsaye sukayi na wucin gadi da ganin abunda ke wakana a gaban su kamar a mafarki.Fateema ce tayi karfin halin cewa meye haka kai kuma, ta nuna Ahmad da yatsa me kake yi a gidan mu ba ance ka rabu da ita ba ko ana so dole ne?.Mikewa sukayi a razane suna kame kame.Inna bata ce komai ba ta wuce cikin gida, fateema ta aika mai harara tace yaudarar naka har cikin gidan mu? Toh tun wuri ka canja sheka don nan ba wurin zaman ka bane, daga haka ta shige ciki ko kallon Ameena bata yi ba.Ahmad Cikin nuna fuskar damuwa yace basa sona baza su yadda su bani auren kiba kaico na ya zanyi da raina.Kada ka damu zanyi kokarin fahimtar dasu kuma nasan komai zai daidaita ka kwantar da hankalinka, ta fada amma kasan zuciyarta itama tashin hankalin take ciki yama zarce nashi don bata tsammanin baba malam zai saurara mata ko kadan.Sallama sukayi akan gobe zai shigo kafin ya wuce.Da sanyin jiki ta shiga gida jikinta ya soma mutuwa ne tun daga kallon da taga inna tana jifanta dashi tasan ta kaita makura yau dai.Ya miki kyau Ameenatu ya ana yabonki sallah sai kuma ki kasa alwala? Yaronda bashi da kyakkyawar tarihi kuma an sanar dake kin nuna amincewar ki sai yanzu rana tsaka zai bijiro.Karasowa tayi ta duka kusa da innan tace inna wallahi ba haka bane banma san da zuwan shiba ina wanki ne naji an kwankwasa kofa dana bude sai na ganshi.Da kika ganshi sai ya tsaya yana tsara miki magana tunda ya mayar dake sakarya wacce bata san me takeyi ba? Kuma kika biye shi tunda baki san ciwon kanki ba?.Shiru Ameena tayi idanunta na tsiyayar da hawaye.Magana daya zan fada miki itace ban yadda wata alaka ta kara shiga tsakaninki da yaron nan ba idan na isa dake.A razane ta dago tana kallon inna ta mike ta shigeta daki da gudu tana kuka kamar an aiko mata da sakon mutuwa.Inna ta Kali fateema, itama fateeman kallon inna take yi cikin mamakin da Addanta ta shayar dasu.Matar majeedadi✍️🙅‍♀️FENTIN ZINA🙆‍♀️🙅‍♀️EESHERT ADAMU

Back to top button