Zakuna Biyar Page 34 By Princess Teema
WS-HOSPITAL.Kai tsaye room ɗinsa Dr James ya wuce da ita, bai direta a ko’ina ba sai a saman bed ɗinsa. Toilet ya wuce, sai da ya yi wanka saboda wajen jini da suka je, ya tsabtace jikinsa fes, sannan ya dawo cikin ɗakin, jikinsa sanye da bathrobe ya haye saman bed ɗin, jawota jikinsa ya yi, ya fara sarrafata cikin salon kwarewa. Can cikin barci ta ji ana taɓa mata jiki, a hankali ta waro idanunta, kai tsaye sai saman face ɗinta, dik da cewa dim light ne a kunne, amma tana iya ganin fuskansa sosai. Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa. “Sir”……… Ɗan kwantowa kanta kaɗan ya yi. “Da sir yakamata ki dinga kiran mijinki ne?”. Ya faɗa yana shafe cikinta. Kai ta girgiza mashi, fuska ɗaure da kyakkyawan murmushin nan nata da bana fatan in daina ganinsa a kan fuskanta ta ce. “Sorry oga”.Dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali, yana jin wani irin azababben sonta na ƙara shigarsa matuƙa, shi kaɗai yasan irin matsayin da take da shi a cikin zuciyarsa, ita ma ita kaɗai tasan irin son da take yi mashi. “My oga please ka kaini in ga darling ka ji?”. Ta faɗa cikin raunin murya, da alama da yaron nan a ranta ta yi barci, sun gagara mancewa da shi ko na second ɗaya ne……. Ɗan rintse idanu ya yi, ya ji haushi, tana neman ɓata mashi darensa mai daɗi. Can ƙasa ya ce. “Zuwa da gobe idan muka tashi aiki zan kaiki ki gansa”. Ya faɗi hakan ne kawai cikin tsananin mayen sonta da yanayin da yake ciki, amma batu na gaskiya ba zai iya kaita in da darling yake ba, dan izuwa yanzu cutar ta gama yawace gangar jikinsa, dik wanda ya kusancesa zai kamu ne, suma 3D sai sun yi using care overall da oxygen dan kada su shaƙi iskar numfashinsa a ɗakin da yake a ciki, suna shaƙa zasu kamu a cutar ne suma.Jin cewa zai kaita wajensa gobe ne yasa ta fara murna tana farinciki, nan ta saki jiki, ta bashi haɗin kai, sosai ya yi romancing ɗinta, ya gigitata ya sanya ta har da kuka, amma kamar ɗazun ne, bai tare da ita ba, iya wasa ya yi har ya yi realizing abin dake damunsa, ya samu natsu sosai. Ɗaukarta ya yi suka shiga toilet, kun sansu da kunya sosai, sai faman ɓoye fuska take yi, shi kuma shugaban marasa kunya na duniya, wai ta mashi wanka, ta ce a’a ita kam ba zata iya ba.Suna shiga cikin jaccuzi ya jawota jikinsa, daga shi sai shorts, ya so cire shorts ɗin ma ta dinga mashi magiya kada ya cire, saboda son da yake yi mata ya hakura ya shiga cikin ruwan da shi. Mara kunya dik ya cire mata kaya, yasa dik ta takure waje guda, tana ta faman dukunkunewa, ya jawota jikinsa, haka ya dinga wasa da ita a cikin ruwan nan, sai da ya sake realizing round 2, sannan ya ce su yi wanka, dare ma ya yi. A natse suka gudanar da komai, ya bata bathrobe ɗinsa ta sanya, yau tana jin tamkar wacce akaiwa kyautar duniya da abin dake ciki, sai murna take yi. Ɗaukarta ya yi, sai kan gado ya direra, tana ce mashi zata sanya kaya a jikinta, ai ina, jawota jikinsa ya sake yi, ya ja masu bargo. Can ƙasan maƙoshi ya ce ta yi barci sai da safe in zata koma wajen babies ta sanya kayanta, yanzu taka tare da mijinta ne, ya hutar da ita sanya wani sleeping dress.Soyayya, soyayya shegiyar aba ce, sai ta kwanta luff a jikinsa, yana ɗan shafa bayanta har barci tai awon gaba da ita, shi ma ba jimawa barci ta ɗaukesa. ASUBA TA GARI.—————————🔥Washegari da su sister Zinta suka zo basu fahimci an ɗauki jarirai guda biyar ba, saboda in baku manta ba Dr Mark ya cire gadan babys ɗin ai. Kamar kullum, shirye-shiryen yi wa dikka jariran wanka suka fara yi. Zama sister Zinta ta yi a gefen gado tana ɗan dafe mararta dake murɗa mata a hankali. A kusa da ita sister Maya ta zauna tana faɗin. “Sis lafiya kika zauna?”….. Tana ɗan dafe ciki ta amsa da. “Cikina na ciwo, ina ganin menstruation ɗina ne, dama tin daren jiya nike expecting ɗinsa”….. Siririn murmushi sister Maya ta yi kafin ta ce. “Na ƙosa nima in fara wannan period ɗin dan in ji me kike ji da kullum kike kukan ciwon ciki idan zaki yi”…….. “Uhm da kin fara zai isheki ne, ga ciwo ga wahala”. Ta kai karshe tana ɗan kwanciyar rigingine ko zata ji sauƙin ciwon da cikin nata yake yi mata.Nasan yanzu tambayoyi sun gama cika maku kai kan cewa ya aka yi sister Maya bata fara period ba kuma bayan shekarunsu ɗaya da sister Zinta ko? Kuma ace 18 years old bata fara ba, abin da mamaki ko? To haka ne, yadda kuka ji ne, Maya bata period, bata taɓa yi ba, bata san ya yake ba. Kun tina cewa Dr James ya ce zai auri sister Zinta, ita kuma sister Maya zai mai da ita PA ɗinsa? Kun tina wannan magana?.To ba Maya kawai ba, dikka nurses dake cikin wannan hospital ɗin basa period! Zinta ce kawai take yi! Amma saura nurses ɗin dikka shiru ne, ga shi dai shekarunsu ɗaya watau 18 years, amma basa yi. To dikkansu 3D sun cire masu mahaifa ne, babu mahaifa kuma ai kunga babu zancen period ko? Su dama dan su yi aiki 3D suka kyankyashesu ba dan su haihu ba, shiyasa 3D ɗin suka cire mahaifansu gabaɗaya, to sister Maya na daga cikin waɗan da aka cirewa Mahaifan.Ita kuma sister Zinta ya bar mata mahaifanta ne dalilin abu ɗaya, in baku manta ba ya ce zai haɗa eggs ɗinta da sperm na Haiza’an watau daddynta, yai mata dashen cikin dan ta haifa mashi yara masu kwakwalwa irin na daddynsu Lion ko? To saboda wannan dalili yasa ya barta da mahaifarta tsinanne, kuma karin wani abin takaici bafa sperm ɗinsa zai dasa mata ba, shi da yake matsayin mijinta ai yakamata da nasa zai yi dashen, a’a, dana ubanta zai yi mata saboda tsinanne ne shi! Annoba! Ya ci alwashin sake haifo Muhammad Haiza’an bayan sun kashe na asali! Yana da hanyar da zai yi dashen sperm ɗin Haiza’an ya kyankyashe ƴaƴan da yake ikirarin nasa wanda zasu gajesa ɗin ba sai a jikin sister Zinta ba, amma saboda kudurinsa na son ya ga ya haifi magaji wanda ya fi Haiza’an kaifin ƙwaƙwalwa shi ne zai dasawa ƴar cikinsa, kai wannan abu da bakinciki yake.Sister Maya ta fi sister Zinta tsananin son yara, shiyasa ta sanyawa wannan ƙanin nasu suna darling, saboda tsananin son babys, ga shi kuma ita ce ba zata taɓa haihuwa ba har abada, dan har ovaries ɗinta basu bari ba, ba halin ai mata dashen wani mahaifan, kun tina na faɗa maku dik karshen wata akwai drugs da 3D suke basu suna sha? Ai saboda cire masu mahaifa da suka yi ne.ALLAH sarki su bama su san ana yi ba, bama su san ana haɗa eggs da sperm a kyankyashe jarirai a hospital ɗin ba, su dai suna aiki kawai, kuma tsabar 3D azzalumai ne basu barsu sun yi karatu ɓangaren lafiya kai tsaye ba, sai suka turasu suka yi ilimi ɓangaren chemicals, sun san da cewa jinin Muhammad Haiza’an ne su, muddin suka koyar dasu ilimin lafiya to sai sun ci ubansu ne, dan dik wata badaƙala da suke yi zasu ganosu, shiyasa suka haɗasu da tace chemicals da banbantasu, sannan su zubasu cikin kwalabe su shirya, kunga wannan Dr James ɗin ba zai ga Annabi ba tsinanne…………😭A irin brain na baiwar da suka gado kuna ganin alluran da Dr James yai wa darling na wancan cuta har sun gano ba magani bane cuta ce dik da basu da ilimi kan ɓangaren 3D, me kuke tinani zai faru da ace ilimin lafiya aka koyar dasu ba ilimin sanin chemicals ba? Kuna tinanin izuwa yanzu da basu gano abin dake binne ba ne? Da sun gano cewa kowani shekara sai an kyankyashi jarirai sama da 500, kuma a fitar dasu izuwa black market! Wlh da zasu gano dik abin da ake yi, har SECTION E da sai sun gano balai da fitinar game da tashin hankalin dake ciki, amma an barsu da aiki a SECTION C na hidimtawa chemicals ɗin da bama su san me ake yi da shi ba. A zuƙo sinadaran dabbobi kawai a haɗasu da tacesa da gyarawa……….😭”Ni nasan ba wani wahala, kawai ragonta ne irin naki”. Sister Maya ta faɗa tana ɗan murmusawa. Already saura nurses ɗin har sun fara yi wa jariran wanka……. “Ina ganin abin da my oga ya mun daren jiya nema ya hana period ɗina zuwa”. Cewar sister Zinta. Zazzare fararen idanunta a kanta sister Maya ta yi, tana ɗan sakin murmushi ta ce. “Bani labari”. Da yake shaƙuwarsu ya zarce misali sai sister Zinta ta bata labarin komai. Ƙara faɗaɗa murmushinta sister Maya ta yi, ta dinga tayata farinciki tare da ce mata ta kula sosai, ta zage ta kame zuciyar Dr James sosai, saboda taga kowa son shi yake yi, kada ta bari ya kubce mata, cike da farinciki ta amsa da zata yi hakan. (Kada ku ga wani lokaci ina rubutu kan waɗan da basu a addinin Musulunci kuma ina saka In Sha ALLAH, ko wani abin da ya danganci sunan ALLAH ku ga laifina, bakinmu mu musulmai ya rigada ya saba da ambaton ALLAH subhanahu wata’ala, shiyasa nike mancewa in saka waɗan da basu san ALLAH ba kuma suna kama sunansa, nasan ba zan iya gyara wannan matsala ba shiyasa nai magana, ko yaya sai na ambaci sunan ALLAH, yanzu haka a karshen maganar sister Zinta har na rubuta ta ce In Sha ALLAH sai na tina na goge, dan haka in kunga irin haka ku wuce kawai, saboda da kiran ALLAH ɗin ne!.)Cikin zolaya sister Maya ta ce. “Amma abin da ogan yai maki is it sweet?”. Shiru sister Zinta bata tankata ba, ta dai dafe ciki, ganin haka yasa sister Maya sake cewa. “Da gaske cikin yake maki ciwo sosai ne?”. Kai ta gyaɗa mata alamar e, ɗan rungumota sister Maya ta yi, ta fara yi mata sannu, tana shafa kanta on a serious note, sai kuma ta ce. “Ko dai in je in karɓo maki drugs a drugs side ne?”….. Kai kawai ta gyaɗa mata alamar e tana rintse idaunta saboda azaban zafin da take ji.A hankali sister Maya ta kwantar mata da kanta a saman pillow, ta miƙe game da nufar waje tana kallon babys dake ta faman kuka, suna son shan madara. Dab zata fita Dr Kamal na sako kai, karo suka ci, baya ta ɗan ja tana ƙoƙarin ɗago da kallonta taga wanene, sai kuma ta risinar da kai, dan kamshin perfume na 3D ya bata amsar su waye ne. “Good morning sir”. Ta faɗa tana duƙawa. Tsayuwa Dr Kamal ya yi a dab gabanta, ya baiwa Dr James and Dr Mark hanya suka wuce ciki. “Morning babydoll, ina zaki je kike sauri haka?”. Dr Kamal ya faɗa yana kallon hannayenta da ta haɗe waje guda, suna ɗan kerma.”Dama sister Zinta ce cikinta yake ciwo, zan je sashen drugs in karɓo mata magani”……… Kai kallonsa a kan Zinta yai, sai kuma ya kalli Dr James dake tsaye gaban wani baby dake ta faman kuka…….. “Meyake damunta?”. Ya tambaya a natse. Haka kawai sai ta ji ta tsinci kanta da tsananin jin kunyar faɗin abin dake damun ƴar uwar tata.Ganin haka yasa ya ce. “Jammy kana da patient”. Ya faɗa yana kallon Dr James. Ɗago dara-daran eyes ɗinsa Dr James yai a kansa, yai mashi kallon wace patient kuma amma bai yi magana ba.Da hannu Dr Kamal ya nuna mashi Zinta dake kwance saman gado, idanunta a rufe ruf. Kallon ƙasan ido Dr James yai mata kafin ya ɗan jinjina kai alamar okey, ya cigaba da abin da yake yi, shi kuwa Dr Mark ɗan air, shi fa ba ruwansa da soyayya, in kunji Dr Mark na magana to sabga ce ta cigaban aikinsu, bai san wani abu wai shi soyayya ba.”Mu je office ki haɗa mun green tea”. Dr Kamal ya faɗa, ba tare da jiran amsarta ba ya wuce gaba, bayansa ta bi tana waigo sister Zinta, ba dan 3D ne ya kirata ba da ba zata iya tafiya ta bar ƴar uwarta cikin ciwo ba.Sai da Dr James ya kammala duba jariran tsab, ya tabbatar da suna cikin ƙoshin lafiya, sannan ya nufi gadon da Zinta ke kwance, shi kuma Dr Mark da suka gama duba jariran sai ya wuce office ɗinsa kawai, dan bashi da lokacin ɓatawa a nan.A kanta ya ɗan sunkuyo tare da dafa forehead ɗinta da tafin hannunsa ɗaya, can ƙasan maƙoshi ya ce. “Menene yake damunki?”…….. Slowly ta waro idanunta a kan face ɗinsa, idanun nata sun yi jajir saboda azaban ciwo. Muryanta na ɗan rawa ta ce. “It’s time for my menstruation, cikina ne yake ciwo”.Shiru ya ɗan yi, can kuma ya ce. “Kin shirya mashi ne?”…… Kai ta gyaɗa mashi alamar ta shirya. Hannunta ya riƙo tare da cewa. “Mu je office ki sha drugs a can, hope kin yi breakfast?”. Girgiza mashi kai ta yi alamar a’a bata yi breakfast ba, dan daga sashen 3D ɗin da ta fito wanka kawai ta je ta yi ta a nasu sashen, bata tsaya tafa masu abinci ba, a wannan hospital ɗin kowacce nurse tana da nata kayan abinci, su suke girkawa da kansu, kullum karshen wata ana kawo masu kayan abinci da komai da komai, kamar dai boarding school, so dayawan lokuta dama sister Zinta ɗin ke masu girki, ita da Maya komai nasu a haɗe yake, tare suke komai. Hannunta ya riƙo ya taimaka mata ta miƙe, tana miƙewa ta koma ta zauna tana faɗin. “Wash, too much of pain”……. Nisawa ya ɗan yi, baya son wannan ragonta nata sam, amma ya zai yi? Haka take, ya so ace jaruma take tamkar sister Lazy, sai dai ita takasance mai rauni da taushin zuciya ba kamar Lazy ba!. Rage tsawonsa yai, cak ya ɗauketa suka fito waje, ya saɓata a saman shoulder ɗinsa, haka ya keta gabaɗaya cikin hospital ɗin har ya isa ga sashen 3D, ya zo ya wuce sister Lazy dake zaune tana ƴan cike-ciken wasu takarsdu.Bakaramin tashin hankali ta shiga ba ganinsa ɗauke da ita, amma ta daure game da cizewa, a ranta ta ce zamu haɗu ne, sai na maki abin da sai kin tsani kanki kin kuma tsani duniya bakiɗaya.Shi kuwa bai dire Zinta a ko’ina ba sai saman doguwar sofar dake cikin office ɗin, yana sauketa ya ɗan shafa kanta game da ce mata sorry. Tana kallon fine face ɗinsa ta amsa da thank you. Gaban heater dake cikin office ɗin ya tsaya. Kunnata yai bayan ya duba akwai ruwa a ciki.Daga nan ya nufi show glass dake gefe, cup ya fitar tare da ganyen green tea, sugar da dik wani abin da zai buƙata, gaban heater ɗin ya sake komawa, da kansa ya haɗa mata tea mai zafi, ya ɗan barshi ya huce, sannan ya ɗauko ya dawo in da take a zaune.A gefenta ya zauna tare da miƙa mata cup ɗin, ta karɓa tana yi mashi godiya. “Make sure you take it all”. Ya faɗa yana miƙewa tsaye, kai ta jinjina alamar to, watau kula yana da daɗi, wlh dik zafin ciwon nan da take ji da ya nuna mata kula sai ta fara mantawa da ciwon, hankalinta gabaɗaya ya karkata a kansa da soyayyarsa a gareta. A saman chair ɗinsa ya koma ya zauna, ya ɗauki table phone, sister Lazy ya kira, bugu ɗaya ta ɗaga, cike da bada umarni da izza ya ce ta je sashen drugs ta ɗauko mashi naproxen yanzu ta kawo mashi. Ba tare da ya jira amsarta ba ya katse kiran. Tamkar zata fashe, tana wani irin huci ta miƙe, badan bata da tabbacin ba zai zuba maganin ba idan ta kawo da wlh wani maganin daban zata kawo, dan dai tasan zai duba ne, in kuma ya ga ba wanda ya ce ba to da matsala ta sani, ga shi bai iya hukunci ba, sai yasa ka gwammaci mutuwa a kan rayuwa!.A fusace ta miƙe ta nufi wajen tana huci, shi kuma ya jawo laptop ɗinsa ya fara duba ayyukan da suka yi jiya, wanda yakamata ya sanya hannu ya fara sanyawa, wanda yakamata yai cancel ya yi.A can ɓangaren kuwa, Sister Maya ce tsaye gaban table na Dr Kamal tana miƙa mashi cup da ta haɗa mashi tea, karɓa ya yi, ta ɗan risina alamar girmamawa, sannan ta juya zata tafi, hannunta ya riko da sauri, cikin sanyin murya ya ce. “Ina zaki je?”. Ras ta ji gabanta ya faɗi, ɗan zazzare eyesball ɗinta a kansa ta fara yi kafin ta ce. “Zan je wajen babies ɗinmu ne, lokacin yi masu wanka yana ta ƙurewa, ga shi ba’a basu madara ba”. Tana ɗan sunkuyar da kai ta faɗa. Cikin wani irin karuwan salo ya ɗan jawota ta faɗa jikinsa, ya zaunar da ita a saman laps ɗinsa, ai gabaɗaya ɗan ɗauke wuta ya yi, ita kam sai ji ta yi tamkar bata duniya, ta zaci mafarki take yi.Haɓarta ya ɗago suna fuskantar juna, cikin sanyin murya ya ce. “Kina ganin ba kamata ya yi ace yanzu naki babys ɗin kike kula da su ba? Ko ke baki son yaran kanki ne?”…….. Ai muryanta na rawa, da sauri ta ce. “Ina son babys sosai, ina son nawa ma, kuma ina son waɗan can ma sosai”. Ɗan rankwafowa kanta kaɗan ya yi, tamkar mai raɗa ya ce. “Kin shirya karɓar baby in baki? Zaki haifa mun yara kyawawa irinki?”…….. Da sauri ta shiga gyaɗa mashi kai alamar e. Sumbatar cheek ɗinta ya yi kafin ya ce. “Na jima ina fatan naga kin haifa mun magada, ga shi yanzu lokaci ya iso”….…. Shiru ta yi, ta gagara yin magana. Hannunsa ya ɗaura a saman cikinta, yana ɗan shafawa ya ce. “Wannan ɗan karamin cikin anya zai ɗauki twins kuwa?”…… Watau shi Dr Kamal yadda kuka ga Maya haka yake, akwai jarabar son yaran kansa fa amma, kuma shi a tsarinsa idan ya tashi dasa mata cikin zai yi, dashe zai yi mata, dan twins, triplets and quadruplets yake so, baya son ɗaya, shiyasa zai dasa mata.Me kuke tinanin zai faru idan yasan Maya ba zata taɓa haihuwa ba? Dan shi bai san Dr James ya cire har da mahaifarta ba, ya saka burin haifar yara kyawawa kamarta da ita. Watau akwai wani gagarumin yaki a hospital ɗin nan dik ranar da Dr Kamal ya gano bata da mahaifa, shikenan ba zai samu magada ba, har na hango kalar guguwar da zata tashi!.Ɓoye fuska ta fara yi a jikinsa, ta sunkuya tana ɗan murmushi, irin maganar tai mata nauyi. Haɓatar ya ɗago da hannu ɗaya, ɗayan hannun nasa kuma yana shafa bayanta izuwa kan mazaunanta, ya ɗan kwanto da gefen fuskansa a kan hair ɗinta. Shiru ne ya ɗan biyo baya kafin daga bisani ya ce. “Jeki kula da babys ɗinki, anjuma in mun tashi aiki ki zo mu tattauna”. Ai da sauri ta miƙe tamkar wacce ke kan ƙaya, dan dama ya sakata wani hali, bata taɓa zatan zata jita a jikinsa ba. Waje ta nufa tana ɗan kame jikinta, binta da kallo ya yi yana jin wani irin sonta na ƙara ratsa shi. Dab zata fita ta ɗan waigo dan ta saci kallonsa, karaf suka haɗa ido, kashe mata ido ɗaya yi, hakan yasa ta juya, da sauri ta fice tana murmushi, dimple ɗinta irin na Leo yana lotsawa gwanin burgewa.Tana zuwa ta isko wasu babys biyu suna kuka, an masu wanka an shiryasu tsab. Ɗaukansu dikka biyu ta yi, ta ɗaura ɗaya a shoulder ɗinta, ɗaya a cinyarta, ta fara jijjiga babys ɗin, da kyar wanda yake kan cinyarta yai barci, a hankali ta kwantar da wanda yake hannunta yana ɗan kuka, ta miƙe ta mai da wanda yake saman laps ɗinta saman gadonsa, ta dawo ta ɗauki ɗayan, tana jijigasa tana zarya a cikin ɗakin, sai take jin tamkar darling ɗinta ne, da yake kunga shi ne rigimammen yaro, so wannan mai kuka na yau ta ji kamar an dawo da darling ne.A can kuwa, sister Lazy ta kawo drugs ɗin, har ƙasa ta tsugunna ta miƙo mashi, karɓa ya yi tare fitarwa ya duba. Ganin wanda ya buƙata ne ya ce mata. “You can go”. Ya faɗa yana miƙewa, ya nufi gaban sofar da Zinta take bayan ya ɗauko mata robar ruwa daga freezer ɗinsa.Tamkar sister Lazy zata haɗiyi zuciya ta mutu tsabar taƙaici, tana gani sai faman cewa Zinta sorry yake yi, yanzu ya kara sakar mata zuciyansa, tin da ya yi wasa da jikinta, ya ji ɗuminta, ya ji sa a duniyar Jupiter, daga nan ya sake narke mata.Da kansa ya ɓalle drugs ɗin, sannan ya ɗagota ya zaunar, ya sanya mata drugs ɗin a baki, ya ɓalle bakin robar ruwan, ya bata. Tana ɗan shagwaɓe fuska ta karɓa, sai ce mata sorry yake yi. Bayan ta sha ya rufe ruwan, sai ya ce ta kwanta ta yi barci sai zuwa yamma, yau ba zata yi aikin komai ba. Sai da ya tabbatar ya kwantar da ita, sannan ya miƙe zai koma chair ɗinsa kenan sanyayyar muryarta ta katse shi da cewa.”My oga, please our darling, jiya har mafarkinsa na yi, na yi mafarkin yana ta kuka yana son shan madara, please ka kaini wajensa ka ji?”. Idanunta na ciccikowa da kwallah ta faɗa. Bata san darling yana can cikin mawuyacin hali ba, yana faɗa tsakanin rayuwa ko mutuwa, ALLAH ne kaɗai yasan kalar azaban da bawan ALLAHN nan yake ciki, cutar ta huda jikinsa sosai, wani lokaci har bleeding hancinsa yake yi, sun sanya shi cikin wani glass transparent haka, wanda suna iya ganinsa, ta nan suke bashi madara, dik wannan rikici nasa da kukan ya daina, ko motsin kirki baya yi, a iya kwana ɗaya kawai fa kenan.Ya ALLAH me kuke tinani zai faru bayan kwanaki 5! Ya kuke tinanin wannan cuta zata yi wa al’ummar duniya? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun…….. Ayi hakuri da abin da zan rubuta daga yanzu har gaba, ta yiwu yai maku daɗi ko akasin haka, amma dole zan rubuta! Dan labari ne kan halin da duniya take ciki! Burina in wayarwa da mutane kai, in farkar da kowa yasan halin da ake ciki, dan haka ku yi hakuri da abin da zaku ji kuma zaku ga na rubuta, nasan akwai tashin hankali da jefa zuƙata cikin damuwa har ma da kuka, saboda waɗan nan jarirai, jariri da bai san komai ba, dole nasan hankula zasu tashi, amma ba yadda zan yi ne! Dole ku san me ake ciki, ku daure ku cigaba da karatu, zaku ci ribar karatun ko ba’a kanku ba, ko a kan ƴan uwa, kunga yanzu idan kun ji za’a cirewa wata mahaifa ai ko shawara ce zaku bata, idan yazamana dole za’a cire mata sai ku ce mata in an cire ta ɗauke kayanta ta koma da shi gida ta je ta binne. Wlh tashin hankalin dake cikin wannan duniya ta zarce bakin ɗan adam ya zayyano shi, wani fitinan idan kuka ji sai ku zaci ba gaskiya bane! Amma wlh abin da ya fi ɓarnar da su 3D suke yi yana iya faruwa a duniyar yau, fatanmu dai ALLAH ya karemu daga dikkan azzaluman nan, ya kawo mana karshen zalunci, ya bamu kwanciyar hankali da zaman lafiya, daga karshe ya bamu dacewa da lahira game da cikawa ta hanyar shahada. Jikin mace gabaɗaya kadara ce, mu mata muna ganin rayuwa a yanzu, tin da aka gano jikinmu kadarori ne shikenan, kowacce ta dage da addu’a, babu abin da ya fi karfin ALLAH, idan kika riki ALLAH dole a ganki a barki……. Magana ta karshe kuma shi ne ƙasar AVARIS ƙasa ce ta kirkira, babu ƙasar a zahiri, na kirkiri ƙasar ce saboda bana son in ɗaurawa wata ƙasa wani abin da ba shi ba, kunga yanzu ƙasa ta ce Avaris, dik ɓarnar da na ɗaura mata babu wani shugaban da ya isa ya fito ya ce na ɗaurawa ƙasarsa wani abin, sannan a bisa dokar ƙasa kuskure ne ka yi ɗaurawa wata ƙasa irin wannan abin kai tsaye, shiyasa na kirkiri tawa ƙasar, dan haka Avaris ƙasar kirkirace! Fatan kun gane kun kuma ɗauki haske?.”My oga, please our darling, jiya har mafarkinsa na yi, na yi mafarkin yana ta kuka yana son shan madara, please ka kaini wajensa ka ji?”….. Jinjina mata kai ya ɗan yi. “Ki yi barci zuwa dare zan kaiki”. Ba tare da ya jira amsarta ba ya wuce ya koma wajen chair ɗinsa, lumshe idanunta ta yi, tana jin ciwon cikin na raguwa, har barci yai awon gaba da ita. Ita kuwa sister Maya tana can tana fama da jijjiga wani baby da yaki yin shiru, amma zuciyarta na can wajen tinanin Dr Kamal da abin da yai mata ɗazun, yadda ya jawota jikinsa, ya ALLAH, abin ya tsaya mata a zuciya, sai take jin tamkar ta sake komawa wajensa, dan bata gaji da kallonsa ba.Wasa-wasa sonsa na shiga zuciyarta, watau 3D tantirai ne, sun iya sanyawa mutum soyayyarsu a rai cikin ƙanƙanin lokacin. A haka suka wuni yau, sister Maya ta yi ta fama da babys ɗin, hankalinta ya rabu kashi uku, tana fama da babys, tana tinanin Dr Kamal, tana kuma tinanin sister Zinta dake fama da ciwon ciki, bata san a wani hali take ciki ba, ta damu sosai tana son sani, ga shi ba damar ta je 3D side idan ba su suka nemeta ba. Haka ya wuni sukuku, ta ɗauki wannan baby ta dire ta sake ɗaukar wani, kewan darling tamkar ya kasheta, har yamma around 5 daidai 3D suka sake dawowa dan duba lafiyar yaran, kun san basa amfani da ɓargon yaron da ya raunata ko bashi da lafiya, lafiyayyun yara suke amfani da su, shiyasa kuka ga suke yawan zuwa duba lafiyarsu, sau uku a rana suke zuwa dubasu, ko ɗan zazzaɓi yaro ya yi a take zasu ɗauki mataki, basa wasa da lafiyar jariran, dan su samu sinadaran da suke so kada su yi asara. Kewaye suka dinga yi a cikin yaran, suka auna kowanne, suka tabbatar da suna lafiya, sannan suka nufi waje. Zasu fita ne Dr Kamal ya tsaya, sai ya dawo ciki, a kusa da ita ya tsaya, can ƙasa kamar mai raɗa ya ce. “Akwai aikin da zamu yi yanzu, zuwa dare zan ganki”. Ba tare da ya jira amsarta ba, ya juya ya bi bayansu Dr James.Suna fita kai tsaye SECTION E suka nufa, zasu fara sarrafa ɓargon ƙashi da sinadaran jariran can dan yin magungunar da suke da buƙata. A tinaninku me dame suke yi da ɓargo da jinin jaririn? Magungunar me dame suke haɗawa? Wasu sinadaran suke haɗawa? Ina suke kai magungunan? Shin suna fitar da maganin ne ko kuwa ya suke yi da shi?. Alƙalamina zai warware maku komai tsab, ba zan rage komai ba, mu je zuwa.3D na fita sai ga sister Zinta ta shigo babys safe room ɗin. BABIES SAFE ROOM (BSR) na taƙaita maku dan rage wahalar ƙira, ku ce BSR kawai.Ta warke garau, ta sha barci a office na Dr James har ta gode ALLAH, dama jiya bata samu damar yin wani barcin kirki ba, saboda murzanta da ya dinga yi, yau dai ta more, sai yanzu da zai fita ya tada ita, ya ce ta je ta yi wanka zata wastsake. Kafin ta fito wanka ta samu haɗaɗɗen mandi rice ya ajiye mata a wajen sofar da ta tashi, ga crispy chicken da lemun abarba mai mugun sanyi, ta yi mamakin ganin irin abinci, bata taɓa cin irinsa ba, ai ce mashi ta yi zata je ta ci da sister Maya, bai hanata ba, dan bashi da matsala da ƙawancensu, sai ya ce mata ta kula da kanta, anjuma zai zo ya ɗauketa su kwana a ɗakinsa. Tana murmushi ta ce okey. Zata ɗauki kayan abinci ta ji an rungumota ta baya, ajiyar zuciya ta sauke tare da juyowa a hankali, ta faɗa jikinsa. Shafa lallausan gashin kanta ya fara yi izuwa gadon bayanta, ya ɗan sumbaci cheek ɗinta kafin ya saketa, ta ɗauki kayan abincin, ta nufi kofa tana waigosa, yana tsaye ya rungumo hannaye a kirji yana kallonta, har zata fita ta sake waigosa, da alama ita ma bata son rabuwa da shi.Kashe mata ido ɗaya ya yi, hakan yasa ta fice tana murmushi……… Sister Maya na ganinta ta miƙe ta rungumeta tana tambayar lafiyarta. Tana murmushi ta fara bata labarin abin da ya faru bayan sun zauna a gefen gado, sosai Maya ta ji daɗi, sannan ta karɓi kayan abincin ta fito da shi.Suka zuba a plate, sauran kuma suka baiwa sauran nurses dake faman baiwa babys madarar yamma. Sosai suka ci abincin, sai santi suke yi, haƙiƙa sun yabawa girkin, basu taɓa cin abu mai daɗinsa ba, har da lashe plate sister Maya ta yi, bai isheta ba, amma already sun baiwa sauran nurses sauran abincin, da zata ƙara.Lemun abarba dake cikin botle suka ɗauko, haba daɗinsa da sanyinsa da ya ratsa masu wuya sister Maya har da rufe idanu, ta dinga santi sister Zinta na yi mata dariya, basu baiwa sauran nurses wannan lemun ba, dan ƙaramin bottle ɗaya ne daidai shan mutum ɗaya, dan haka suka shanye tas, kafin sister Maya ta tattare komai, kunsan malaman asibiti da tsabta, ta tsabtace ko’ina tsab kafin ta dawo suka zauna da sister Zinta a kan gado suna hira, sun bar crispy chicken ɗinsu, dan cikinsu kamar zai fashe saboda ƙoshi, sun sha bottle water, sai sister Maya ta ce su bar shi sai anjuma su ci, na’am da hakan suka yi.Sister Maya ta bata labarin abin da Dr Kamal ya ce mata, sosai sister Zinta ta tayata murna, suka hau tsara yadda zasu kula da 3D har su samu soyayyarsu sosai!. —————————-🔥CRYSTAL PALACE.Da wani irin gudu ya shararo da motarsa kan titin dake cikin school ɗin izuwa parking lot, tin daga nesa ya hango Seraphina, Rimsha and Faryan suna tsaye suna magana, Seraphina ta ce ita ba zata shiga motarsu ba yau, bata jin daɗi, ta tsani ma ai mata mata magana, shi kuwa Faryan, lover boy, sai rarrashinta yake yi, ta kafe ita da kafa zata tafi, kuma karya take yi, yarinya har ta fara koyan karya.Uncle ne ya hure mata kunne, ya ce idan an tashi ta jira da kansa zai kaita gida, ya kasheta da kalaman kauna game da gift na chocolate har da heart design na pillow mai kyau da aka rubuta i love you blossom, ta sanya kyautar a cikin school back ɗinta, shi ne yake cewa da kafa zata tafi, da karfi da ya ji tana son koyar wasu ɗabi’u da ba nata ba. Ai tin Aryan bai gama karisawa wajensu ba ya ɗauko wani face ya sanya a fuskansa, face ɗin da Seraphina ta fara saninsa da shi, dama suna da shi a cikin motocinsu saboda gudun ko ta kwana. Winter jacket ya ɗauko, ya sanya a saman kayansa tare da kashe motar ya fito.Gabaɗaya kishi ta rufe mashi ido, ya manta Faryan ƙaninsa ne, yana zuwa ya damke mashi da karfi, yana son tambayarsa me ya haɗa shi da ita, amma yasan in dai ya yi magana sai Faryan ya gane, dan haka ya yi shiru bai yi magana ba. Ƙoƙarin kwace kansa Faryan ya yi, amma ya gagara, dan damkar IRON FIST ba wasa ba, abu kuma ya haɗu da kishi, ai ba’a magana. Ihu Seraphina da Rimsha suka kurma a tare, hakan ya yi silar dawowansa hayyacinsa, da sauri ya saki Faryan, idanunsa sun yi jajir, Seraphina har ta fara ruwan hawaye, muryanta na rawa ta ce. “Daddy please ka kyalesa”…… Da yake ta ganesa tin da fuskan ta fara saninsa.Wani irin damƙa yai wa hannunta, da karfi yaja sai wajen motarsa, ya buɗe marfin ya jefata ciki, bai sake bi ta kan kowa ba ya shiga gidan gaba, yana ganin Rimsha ta zo da gudu ta rike Faryan tana bashi hakuri. Tada motarsa ya yi, da gudun gaske ya bar school ɗin. Ni kam na ce ALLAH ya taƙaita basu haɗu da uncle bama, da abin zata fi munana!. Tana kuka jikinta na kerma, wani irin gigitaccen tsawa ya daka mata, da karfi ya ce. “Will you shut up! I’m coming for you, bari mu koma gida, sai kin faɗa mun wanda ya baki izinin kula Faryan!”.Cak ta tsaya da kukan, ta tsai da idanunta a kansa, mamaki ne yakamata na yadda aka yi yasan sunan uncle Faryan ɗin Rimsha, to ai ita bata faɗa mashi ba, hasalima tin da ta haɗu da Faryan basu zauna sun yi hira ba, ko a ina ya san sunansa? Ta gefi kanta da tambayar da babu mai amsa mata, ya ALLAH watau jinin IRON FIST akwai barin, har ta gano ya kira sunan Faryan dik da damuwar da take ciki.Ai yana parking a garage ɗinsu ta ɓalle door na motar, da gudu ta fita, kafin ya fito ta haye elevator zuwa hawansu, dole ya tsaya jiran elevator ɗin ya dawo ya ɗaukesa. Tana shiga parlonsu ta gudu bayan Madam ta ɓuya, tana kuka ta ce. “Mom kada ki bar daddy ya dakeni, na shiga ukuna”.Madam ma ƙoƙarin yin magana sai ga shi ya shigo, har lokacin huci yake yi tamkar zai kama da wuta. A tsakiyar parlon ya tsaya, babu wasa tattare da kan fuskansa ya ce. “Come here!”. Jikinta na kerma sosai, hawaye sun gama wanke fuskarta, ta ƙanƙame Madam tana faɗin. “Mom please help me, don’t let him go in with me”…… Madam ta gagara yin magana, dan ita kanta tsoron Aryan take ji, yana cikin kwanciyar hankali ma tsoro yake bata bare ace yana cikin fushi.Daidai lokacin Aunty Safiyya da Suhana suka fito jin hayaniya a parlon. Ganin abin dake faruwa yasa suka yi saurin ƙarisowa…….. Ran Aryan ya ƙara ɓaci, a fusace ya tako ya nufosu tamkar wani mayunwacin zaki. Ai yana ganin ya nufosu kuma Madam bata ce komai ba, sai ta saki Madam, da gudu ta diro ƙasa, tana ƙoƙarin watsawa da gudu ya damƙo gashin kan nan nata.Sama ya ɗagata sai saman shoulder ɗinsa, su Aunty Safiyya sai kallonsu suke yi. Bai direta a ko’ina ba sai cikin room ɗinta, a tsakiya ya direta tare da fara ƙoƙarin yi mata magana. Haba ganin bata da mafita ne, babu mai iya kwatarta a hannunsa ne yasa ta tuna abin da ta karanta a littafan can, yadda ake controlling fushin namiji, dan haka dole ta yi amfani da wannan dabara, dan wlh tana balain tsoron dukan Aryan, ta j kamshin lahira ranar, bata son ko a mafarki ta ƙara jin even one slap from him.Da sauri ta datse idanu, ta faɗo jikinsa, hot hug ta bashi game da saka mashi kukan shagwaɓa, tana goggoga kanta a saman lion chest ɗinsa….. Jimmmmm haka ya ji duniya ta tsaya mashi, omg, this kukan shagwaɓa melted his heart over, ga goga kanta a kirjinsa da take yi, ga shi she hugged him tightly, ai ɗauke wuta ya yi, zuciyansa na wani irin spark na shauƙin ƙaunarta……. 👀Cikin kukan shagwaɓa ta ce. “I’m so so sorryyyyyyyyyy daddy, ba zan sake ba, for give me my gentle chaos”…… Oh God, this gal ta gama da daddy yau, wannan suna da ta kirasa my gentle chaos ya gama narka mashi fushin da ya ɗebo, fushin ya narke ya koma so da kaunarta sabo!. Bai san time da ya rungumeta tightly ba, wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke, fushi ta gudu.Da jin ya rungumeta ba karamar daɗi ta ji ba, ta ƙara shigewa jikinsa sosai. Shiru suka yi, shessheƙar kukan shagwaɓarta na tashi a hankali-hankali, yasa hannu yana ɗan shafa kanta izuwa kan bayanta. Gabaɗaya ya shige love mood, har ya manta cewa Campaion na IRON FIST yake!.Sun ɗauki 10 mins a haka, slowly ya saketa, ya raba jikinsu, saman sofa ya koma ya zauna, ya jingina kansa shiru tamkar mai tinanin wani abin, ya ɗan lumshe idanunsa soyayyarta na kara ratsa shi sosai. Ganin haka yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da zuwa ta zauna a kusa da shi saman bed, tana kallon kyakkyawan face ɗinsa.Ni kam na ce daddy fa ya yi mugun nisa a soyayyar Cherry bloom ɗin nan nasa, sai abin da muka gani, yanzu ita ke rike da ragamar zuciyansa, amma yarinta yasa ba zata gane cewa zata iya juya shi ba, ko Abba ba zai iya juya shi cikin sauƙi ba, amma ita zata iya a sauƙaƙe cikin kwanciyar hankali ma kuwa, amma ba zata gane hakan ba. To me kuke tinanin zai biyo baya? Ga su dai zaune shiru Cherry ta zuba mashi ido, idan ya wastsake ya dawo daga duniyar da ta jefasa me kuke tinani zai faru? Ƴar yarinya da ita tana son fin karfinmu, tasan komai, to thank god dai da bata fara aikata komai ɗin ba daddy ya farga!.Tin da sun zauna shiru bari mu leƙa wani ɓangare, watakila kafin mu dawo shi ma daddy ya dawo daidai ya wastsake. ————————–Zaune Abba yake a main parlo, yana rike da littafin The Franklin Scandal yana karantawa, hannunsa rike da gold scepter ɗinsa, ya miƙe kafafunsa saman lallausan throw pillow ɗin dake a gabansa, hankalinsa ya karkata kan littafin.Cikin natsuwa Ammie ta sauƙo ƙasa, tana tafiya tana wuwwurga idanu in da zata gano Rimsha ya jikin Abba, dan tasan lokacin dawowarta daga school ya yi. A gefen Abba ta zauna tare da cewa. “Barka da hutawa ranka ya dade”. Abba gwani a izza da isa, kai tattijon nan akwai taƙama da nuna karfin iko game da fadanci, anya Abba ba jinin sarauta bane ba kuwa?……. Sai da ya ɗauki mintuna kafin ya rufe littafin hannunsa, a natse ya ce da Ammie. “Yauwa sannu da fitowa”. “Ban ga Rimsha ba”. Ammie ta faɗa tana miƙa hannu ta karɓi sandar hannunsa, ta kwantar a ƙasa…… “Basu shigo ba ai”…. Shiru Ammie ta ɗan yi, can kuma ta ce. “Nasan dik abin da ka yanke abu ne mai kyau, baka yanke abin da bai dace ba, kuma dik abin da ka yanke muna biyayya da kuma mubaya’a a garesa, amma a wannan karon ina neman alfarma dan ALLAH! ALLAH ya kara maka nisan kwana da lafiya”. Bai amsa ba, ya dai zuba mata idanu yana kallonta, tasan halinsa sarai, shirunsa ma magana ce, dan haka sai ta cigaba da cewa. “Dan ALLAH ka bar batun haɗa wannan aure na su Aryan da waɗan can yaran…..”. Gagara karisawa ta yi saboda ɗan waro idanunsa a kanta da ya yi, mamaki ne ya kamasa jin yau karo na farko a gidansa ya yanke hukunci ake neman yi mashi katsalandan, abin da ba’a taɓa yi ba kenan. “ALLAH ya baka hakuri, tuba nike”. Ammie mace mai biyayya ta faɗa, sam ita bata son ai wa ɗanta auren dolen nan ne, dan ya ce mata baya so, sun yi waya jiya, ya faɗa mata muddin Abba yai wannan aure to ta sani kome ya biyo baya su suka ja, shi ya gama magana, baya son auren kuma ba zai yi ba! Idan aka matsa mashi ran kowa ba zai yi daɗi bane. Ammie tasan waye Aryan fiye da yadda Abba ya sanshi, tasan baya magana biyu, lallai dik wacce aka aura mashi sai ta gwammaci da bata zo duniya bama, dan billahil lazi mancewa da cewa ita macece zai yi, dama can maza suke yi wa kallon mata, aikuwa yarinya zata ji a jikinta ne!.Nisawa Abba ya yi, zai yi magana kenan sai suka ji ana knocking na parlo door ɗinsu. Wayansa dake gefensa Abba ya ɗauko, app na door ɗin ya shiga, akwai camera a jikin kofar ta baya, so idan kuka shiga cikin app ɗin zaku iya shiga Camera ku ga wanene yake knocking kuna daga zaune!…… Uhm duniya ta cigaba, ALLAH ka wadatamu da ire-iren waɗan nan cigaban a ƙasarmu.Yana dubawa ya ga Aunty Luna tsaye a bakin door. Ai da sauri ya danna door control, options suka bayyana, sannan ya danna open. Take dik wasu locks na kofar ta buɗe, ta ɗan motsa ta buɗe kaɗan. Turowa Aunty Luna ta yi ta shigo. Tana shirye cikin shiga ta alfarma, tana shirye cikin black jean, white top and winter jacket wanda ya zo mata har gwiwa a saman kayan, ta yi matuƙar kyau sosai, tana da natsuwa da hankali. Gaban Abba ta kariso, har ƙasa da durkutsa ta gaida shi cikin girmamawa, sannan ta ɗagawa Ammie ma gaisuwa. Dik da cewa Abba baya dariya, kai face ɗinsa ba zaku taɓa zatan yasan me murmushi ba, amma har cikin ransa ya ji matuƙar daɗin ganin Aunty Luna, a mutunce ya amsa gaisuwarta tare da ce mata ta zauna, ya nuna mata ƙasa saman carpet, dan shi Abba akwai izzar balai, idan yana saman kujera ba’a zama a sama kai tsaye.Zama ta yi. Shiru ne ya ɗan biyo baya, sai kuma can ta ce. “Dama na zo ne in baka hakuri kan abin da ya faru, daddyna ma ya ce in baka hakuri, abin bai yi mana daɗi ba, bamu ji daɗin abin da grandpa ya yi ba”……… Still dai fuskan Abba babu fara’a ya amsa da. “Kada ki damu surukata, in kin je gida ki sanar da daddyn naki gobe da kaina ina kawo mashi sadaki”. Murmushi ne ya kubce mata, dan ita dai har ga ALLAH tana matuƙar son Harleen, tin da ta kyalla idanu ta ga haɗuwarsa, gabaɗaya ta rasa kanta, kai jinin Abba ba dai haɗuwa ba, ga iya ɗaukar wanka, kai Masha ALLAH kawai zamu ce.Ta ɗan yi ƙasa da kai bata ce komai ba, ganin haka yasa Abba ya ce mata. “Ki je sama Harleen yana ɗakinsa, ku gaisa kafin ki koma ko?”. Tamkar Abba yasan abin dake ranta, tana son ganinsa ne dama, amma ta rasa yadda zata faɗawa Abba, bata san meyasa dik rashin kunya irin nasu na European amma take matukar shakkar Abba, yai mata mugun kwarjini, ganin cikin idanunsa wannan ta gagara yi, to haka Aryan yake, wlh ba kowa yake iya ganin cikin idanunsa ba, bare Lion da Vir, kai IRIN FIST dikka zaku zaci jinin Abba ne su ɗin, akwai su da balain kwarjini, cika ido, sanyawa mutum zarra, izza, isa da taƙama, yadda kuka ga Abba da karfin halin aurar da yara ko ubansu bai so ba, haka IRON FIST suke da shegen nuna iko a koma inane!. Miƙewa ta yi, ba kunya ta dinga zubawa Abba godiya, sai ta nufi sama. Ammie kam ta saki ido tana kallonsu, watau Ammie bata waye sosai bane, da sauran hijabin kunyarta in faɗa maku, amma Abba, ba dan wani abin ba, ba dan ina tsoron daddy Champion ba, da na ce Abba taƙadarin ɗan duniya ne! Amma ina tsoron Aryan, na yi shiru!.Har ta haye sai kuma ta tsaya game da juyowa, bata iya kallon face ɗin Abba kai tsaye ba, tana facing Ammie ta ce. “Daddy ina ne room ɗinsa?”…… Abba dake kallonta ne ya amsa da. “Abba zaki kirani, room ɗinsa na side two daga parlon sama”…… Da okey ta amsa game da cewa thank you Abba tana murmusawan dake kara fito da kyanta.Ta juya ta karisa cikin second parlo. Kai tsaye ta nufi room ɗinsa. Yana kwance saman bed, daga shi sai shorts and singlet, hannunsa rike da waya yana dannawa, ya rungumo pillow a kirji, while ya ɗaura kafafunsa a kan wasu pillows ɗin, da alama yana jin daɗin yanayin da yake a ciki.A natse ta turo kofar ta shigo, sarai ya ji an turo kofa, amma ya zaci Faryan ne sai bai ɗago kai ba, dan yasan kofar ɗakinsu ai sai su kaɗai zasu iya buɗewa, dan haka bai zaci wata ce daga waje ba. Ita kuwa Abba ne ya buɗe mata kofar daga in da yake zaune a parlo, tin kan ta karisa ya danna open na side two doors, tana zuwa ta ga kofar a ɗan ture.Karisowa ciki ta yi, ko kaɗan bai ɗaga ido ba, abin da ya kara burgeta da shi kenan, wannan miskilanci da izzar tasu! Ga ɗan banzan girman kai wai sun fi karfin cewa sorry, zaku shiga hannun nisau ne dan ubanku Abba Khaiza’an, mu zaku gwadawa iskanci? Yanzu lokacinku ne, ku gama shan kamshinku zamu damƙeku ne, Aunty Luna kada ki kyale ɗan air, ki gyara mashi zama, ki ganar da shi mu fa nisa’u ba’a mana wannan shirmen!. Har ta iso gaban bed ɗin bai ɗago kai ba, sai da ta zauna a dab da shi, tasa hannu cike da yanga irin namu na mata, ga natsuwa ta karɓi wayan hannun nasa ne ya wani irin ɗawo dara-daran eyes ɗinsa a slow motion. Ai yana sauke idanu kan face ɗin mace bai san time da ya zarosu waje sosai ba, sai ya ɗan miƙe daga kishingiɗar da ya yi, ya zauna da kyau yana kallonta babu ko kyaftawa.Haɗaɗɗen murmushi ta sakar mashi kafin ta ce. “Good afternoon oga sir”………. Shiru bai amsa ba, sai ma juya idanu da ya yi, ya kalli door ɗin shigowa, kafin a natse ya dawo da kallonsa a kanta. Ɗan ɗaure fuska ya yi, a dake ya ce. “What brought you here?”..Nisawa ta ɗan yi kafin in a cool way sosai ta ce. “Coming to see your beautiful face, tin ranar baka sake dawowa ba, ka barni da tinaninka a cikin rai, shin ban maka bane? Baka son haɗin Abbanmu ne? Ko akwai abin da baka so a tattare dani ne?”. Ta faɗa tana ɗan jujjuya wayansa dake hannunta.Slowly ya ɗan fara yin ƙasa da idanunsa daga kan face ɗinta, ya fara bin sassan jikinta da kallo. Hakika idan ya ce bata haɗu ba ma ya yi karya, yaudarar kansa zai iya idan ya ce ba haɗaɗɗiya bace, kuma wlh idan kuka ganta ba zaku zaci ta kai 20 years bama, ai kun san yadda jikinsu yake da mugun kyau, gata ƴar kwalisa.Ganin ya yi shiru yana bin jikinta da kallo ne yasa ta kai hannu saman soft cheek ɗinsa, ta shafi wajen sajensa dake kwance luff kafin cikin salo mai ɗaukar hankali ta ce. “I love this”. Tana shafa sajen ta faɗa, sai kuma ta sake cewa. “Ka zo har gida, ka barni for more then 20 mins a tsaye, kana tinanin ka ci banza ko? You most pay it as soon as possible”. Ta dakata da maganar tana kallon face ɗinsa da kyau. Slowly ta mayar da hannunta izuwa kan kyakkyawan wuyansa, ta gangaro zuwa kirjinsa. “Everything of yours is so special”……. Yunkurawa yai zai yi magana kenan ta yi gaggawar mai da yatsanta saman soft lips ɗinsa, ta ɗaura yatsan nata game da cewa. “Shiiiiiiiii”. Ta faɗa tana matso da face ɗinta dab shi.”Now is my time, ka gama naka time da ka je gidanmu”. Ta faɗa cikin wani irin romantic way, shi kansa maganar nata cikin wani irin yanayi ya fita, wanda sai da ya sanya gabaɗaya jikinsa ya amsa, to shi tin da ba dutse ba ai dole ƙararrawarsa ta buga! Sai ga malam Harleen ya shiga natsuwarsa, wasu malam shiru ne suka shigesa, tsit kake ji. Kara matso da face ɗinta dan shi ta yi, ta zame yatsan nata daga bakinsa, suna iya shaƙar numfashin juna, can ƙasa ta ce. “Meyasa ban yi maka a matsayin mata ba? Faɗa mun in ji”…… Ba sai ga malam Harleen da rarraba idanunsa a cikin nata ba, ya gagara yin magana. Haɗe fuskokinsu waje guda ta yi, ta sanya ɗayan hannunta ta zagayo da shi ta bayansa, ɗayan hannunta kuma ta saƙalo wuyansa, kafin ya farga ta haɗe bakinsu waje guda………. 👀Hot kiss ta bashi na just 5 second, slowly ta fara zame bakinta daga nasa, sai dai ga dikkan alamu munahiki bai so ta cire bakin nata ba, dan har ɗan wani kama lips ɗinta yake yi, ta jisa sarai, amma ta basar ta zame bakinta, dan dama burinta ta kwaɗaita mashi, ta kuma rikita shi sai ta gudu ta barshi ta yadda dole ne ma yai tinaninta har ya biyota gida.Tana zame bakinta ta kalli cikin kwayar idanunsa da suka fara rikiɗewa izuwa ja. “Sai kazo gida”…… Ta faɗa tare da sakesa, ta miƙe tsaye, ai tamkar wawa haka ya zama, sai ya bita da idanu kawai yana kallon yadda take taku tamkar wahainiya, gabaɗaya ya jisa a duniyar sama jannaty. Sai da ta fice ya ja dogon numfashi tare da saukewa a hankali, ɗan lumshe idanu ya yi yana tariyo daɗin soft lips ɗinta, ya ALLAH, shi kaɗai yasan me ya ji, a ƙasan zuciyansa ya ce zuma, a fili kuma da miskilancin ta motsa sai ya yi gaggawar kawar da tinaninta, har da sa hannu ya fara goge bakinsa yana jan dogon tsaki, shi a dole zai yi avoiding ɗin abin, bayan kuma ƙasan zuciya ta kyatsa har da lashe baki, munahiki bai so ma ta dakatar da kiss ɗin iya haka ba.Ita kuwa tana fitowa ƙasa ta sauƙo, a cikin ranta taka faɗin ta kunnasa kenan, da kansa zai kawo kansa ne ma, tana sonshi so na tsakani da ALLAH, ga shi bata da matsala, wayayyiya ce kuma sosai, bata bari kanta ya kulle. Yadda ta bar su Abba haka ta iskosu, ƙasa ta ɗan duƙa tana yi masu sallama kenan suka ji knocking. Abba dake rike da waya ne ya duba wanene? Can ya gano grandpa ɗinsu Noor ne. Buɗe masu kofa ya yi. Cikin faɗa dattijon ya afko ciki, yana wani muzurai tamkar zai saka duka, cike da sababi ya fara zazzaga masifar ina jikarsa? Ai Aunty Lusi ta faɗa mashi nan ta yo, ya sha alwashin ba zai rabu da Khaiza’an ba, zai sace mashi ɗiya ya lalata.Tin da ya shigo yake wannan balai har ya kariso tsakiyar parlon. Daidai lokacin Faryan da Rimsha suka shigo. A natse Harleen ya sauƙo ƙasa jin banbamin dattijon. Shi kuwa daddyn Noor yana office bai san wani waina ake toyawa ba, shi dai kawai ya ce Aunty Luna ta zo ta bawa Abba hakuri a madadinsa tin da Aryan ya hana shi shiga.Da sauri dattijon ya zo ya rike Aunty Luna yana faɗin. “Basu yi maki komai ba ko?”………. Faryan da ya shigo yanzu ne ya ce. “Ammie ina son yin magana dake”. Daidai lokacin grandpa ya nuna family da sandar hannunsa, cike da masifa ya ce. “Ba zan kyaleku ba! Dole hukuma ta ɗauki mataki a kanku, dole a shiga tsakanina da ku! Sai na gwada maku karfin dukiya! Sai na ɗaure dikka zuriarku, mutanen banza kawai”. Aunty Luna na kokarin dakatar da shi amma ina, ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba.Wucewa Harleen ya yi, ya zauna a saman carpet kusa da Abba tare da miƙe kafafunsa, tamkar bai ga grandpa ba, while ita kuma Rimsha ta nufi sama tana faɗin. “Ammie bari in cire uniform ɗina ina zuwa in baki labarin Seraphinata yau ma”. Ammie dai bata da aiki kullum sai sauraren labarin Seraph, dik Rimsha ta addaba masu. Faryan da ya zauna kusa da Ammie tare da kwanto da jikinsa a jikin Ammie ɗin ne ya ce. “Ammie na gaji, zo mu je in baki wani labari”………. Abba ya ce. “Gulma zaka kai mata ko?”. Yana ɗan murmushi ya ce. “Kai Abbanmu, ai mu bama gulma, wani labari zan bata fa, ina wannan kawar Rimsha Seraphina ɗin?”. Jinjina kai su Abba suka yi, dan dik wanda yake tare da Rimsha yasan labarin Seraphina. “To yarinyar yau saura kaɗan daddynta ya mun duka, wai dan kawai Rimsha ta ce mu yi dropping ɗinta a gida, zamu ɗauketa sai ga daddynta, labarin nike son baiwa Ammie fa Abba”……. Abba na ƙara tsare gida ya amsa da. “Waye shi da har ya isa ya taɓaka? Waye shi? Dame yake taƙama? Autan nawa zai taɓa? Waye ubansa a faɗin US!”. On a serious note Abba ya yi magana……… Ni kam da nike laɓe a gefe na ce waye ubansa kuma ya wuce Muhammad Khaiza’an dake wannan magana! Ko ya kuka ce ƴan amana?. Watau Khaiza’ans family muggan ƴan mannin hauka ne, sun baiwa banza ajiyar grandpa, tamkar basu san yana wajen ba, sai zazzaga masifa yake yi, ya gama kuri da nuna isansa, ya ce zai kira hukuma tai masu iyaka, dik babu wanda ya kulashi, ya nunasu da sanda, ya kirasu da mutanen banza, amma tamkar basu jisa ba.One thing about Abba, ko in ce Khaiza’ans family, su fa suna kula waɗan da suke ganin sun kai ne, waɗan dake da ilimi, ko musayar yawu zasu yi a cewarsu basa yi da dakiku waɗanda kansu baya ja basa fahimta! Sun raina isar grandpa ne, sun raina izza da taƙamansa, basa son harkar ƙaranta, shiyasa suka baiwa banza ajiyansa, basu da lokacinsa. Dama dai daddyn Noor ɗin da kansa ne to da sai Abba ya tanka, dan daddyn Noor akwai ilimi da sanin yakamata, amma grandpa, gargajiya kawai ya sani sai masifar tsiya da kullatar mutane a zuciya!.Yanzu me laifin auren nan? Banda hajilci irin na grandpa me laifin dan baku addini ɗaya kun yi aure? Musulunci bai haramta ba, dan haka ba zamu haramtawa kanmu ba, idan aka yi auren ma ai in su Aunty Luna na da rabo sai su musulunta.Ganin basu kulasa bane, suna ta sabbagar gabansu ne yasa grandpa jan hannun Aunty Luna, suka nufi hanyar fita yana faɗin. “Talakawa kawai, sai na gwada maku karfin kuɗi, sai na ƙasƙantar daku na walaƙanta rayuwarku, in ja ku a titi, ku jirayi dawowata, har ni zaku ɗaukawa jika ku kawo gidanku? Ku jirani”. Suna jinsa, amma babu wanda ya tankasa, suka baiwa iska ajiyansa, har ya fice yana sababi. Yana fita Harleen ya miƙe ya koma sama, Faryan ma ya nufi wajen Rimsha dan ya faɗa mata cewa shi fa ko zai rasa ransa ba zai fasa son Seraphina! Abba da Ammie suka cigaba da tattaunawa kan yadda za’ayi biki, Abba ya ce baya son taro, a sirrance za’a ɗaura aure, a cikin masallacin dake nan CRYSTAL PALACE ɗin, Ammie dai da ta ga da gaske babu gudu babu ja da baya a lamarin Abba kan batun auren nan, kuma tasan halinsa in yai magana ɗaya ko duniya zasu haɗe ba zai canza ba, sai kawai ta bada kai, ta hakura ta biye mashi suka hau tsara yadda komai zai wakana.DEATH OR LIFE! 🔥(DOL🔥)Tsaye Leo yake a gaban wani tapkeken tekun da ka kar iya kallonka ba zaka iya ganin karshen tekun nan ba, ga wasu manyan jiragen ruwan dake shawagi a tsakiyar tekun, bodace ta arewacin AVARIS, teku ce da ta haɗa manyan ƙasashe da dama ana kasuwanci ta cikinta, ana shigo da kaya a sake fitarwa, tana da girma matuƙa, to su suna kusa da ita ne ta cikin Avaris, a nan ɗan nesa kaɗan da ita Leo ya ce su kafa tantuna, saboda wani tinani nasa da ya barwa kansa sani! A cikin ransa yana jin yana mugun zargin wannan ɓangare da dajin da suke ciki, sannan yana zargin wannan tekun, yana da yaƙinin dik wani fitina dake shigowa Avaris daga nan yake farawa, ya yi imanin wannan dajin ita ce matattalar dik wasu manyan ƴan iskan ɓatagarin cikin Avaris, shiyasa ya zaɓa masu wannan waje.Sun kafa tantunansu yadda suka saba, ya yi matuƙar kyau, sun kuma rungumi rayuwar dajin nan tamkar gidansu, basu wasa da aikinsu ko kaɗan, musamman waɗan nan team na room 1 da kuma Arya, basa wasa ko kaɗan.Yana sanye da tactical tshirt da tactical trouser, ya rungume hannayensa a saman buɗaɗɗiyar kirjinsa, ya ɗaure kitson kansa a tsakiya, while pistol gun ɗinsa na waist ɗinsa a mazauninsa. Ya kurawa jiragen ruwan dake shawagi can nesa tsakiyar tekun idanu.A hankali ruwan sama yaf-yaf-yaf ya fara sauƙa a kansa, iska mai ɗan sanyi ya fara kaɗawa, alamar an yi babban ruwa a nesa da su. Lokaci guda hadari ta taso gadan-gadan, iska mai karfi da guguwa suka turnuƙe dajin, tsawa da walkiya ya fara yi. Hakan yasa dikka sojojin suka koma kusa da tantunansu except Leo dake tsaye bai motsa ba. A cikin ransa yana saƙa yadda za’a wayi gari ace sun gyara duniyar nan, sun tsabtacesa daga dik wasu gurɓatattu.Noor ne ya fito daga cikin tantinsu sanye da army trouser da tactical tshirts a jikinsa. Yana fitowa dik sojojin dake wajen suka ƙame tare da fara sara mashi…….. “Ina Leo?”. Ya faɗa a dake. Arya dake cikin tantinsu ne ta fito da sauri jin ya ambaci sunan Leo, tana fitowa ta ƙame game da sara mashi. Jinjina mata kai ya yi……. Ɗaya daga cikin sojojinsu ya ce. “Sir Leo yana bakin ruwa”. Nan ma kai ya jinjina alamar to.Sai ya nufi hanyar bakin ruwan, har ya ɗan yi step 2 sai kuma ya juyo, kai tsaye ya nufi cikin…………
