Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 15 Complete Novel

 

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

    FIFTEEN📍

      “Nace ki fadamin abinda kika gani pls”…. 

Jamila ta fada tanajin kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a Nigeria…….

      “Hmmm wannan maganar bata waya bace!,just come and see for yourself!”…. 

Numfashi ta sauke daga daya barin tana fadin

    “Just tell me,I promise you I’m on my way today,koda hint ne ki bani,har kinsa zuciyata tinani iri iri wallahi”…..

      “No sis,just calm down,trust me ina da dalilin kin fadamiki a waya,gwara dai in kinzo din we’ll figure it out together okay?”….

      “Shikenan,toh ya jikinsu Deen?”….. 

      “Alhamdulillah zaace,dan shi ya farka ma,itadai tananan a kwance”…

     “Allah sarki,Allah ya tashi kafadunta ya basu lfy duka”……. 

     “Ameen ya Allah”…….

        Sosai Deen yake kallonta kamar tsohon maye,ayanda yake karewa fuskarta kallo yasan tsap aka basa abun zane ze zanata,kyakkyawa ce ajin farko,irin kyawunnan me shegen daukan ido da kallo daya zaka yiwa mutum kasan yanada kyau,fara ce amma ba chanchan ba,color dinta kamar dai half cast,kallonta ya karayi tindaga goshinta harya karaso habarta,goshinta na dauke da dot din sallah kasancewarta ma’abociyar ibada sosai,hakan sai ya kawata kyawun fuskarta,gashin girarta baki wulik ne da saika dauka tayi brow tint,gashi da curve shaped me kyau,tsabar cika har hadewa girar keyi,it’s just a perfect curved brows!…. Murmushi yayi yana kallon dogon hancinta me kyau kamar ka cireshi ka gudu,ana cewa yana da dogon hanci yau sai yaga na wacce yafi nashi kyau?…. 

    “Fatabarakallahu ahsanul khaliqeen”… 

Ya fada beneath his breath a yayinda ya kara dora idonsa akan idanunta dake a rufe,ko a haka mutum na gani yasan manyan idanu ne da ita,toh inaga inta budesu?… Dafe kai yayi jin mere thought of bude idanunta is driving him crazy….. 

     “Hasbunallahu wa ni’imal wakeel”….

Ya fada yana sauke idonsa akan pouted cute lips dinta,ze iya cewa tinda yake be taba ganin cute attractive lips irin nata ba,infact shi be taba karewa mace kallo irin haka ba sai akanta,sai kuma ya fara tambayar kansa anya shi psychopath ne kuwa kamar yanda ake fada? Cuz what he’s feeling is a raw feeling,bawai sonta yake ba dan ba wannan a dictionary dinshi,but he’s actually feeling something unusual,kamar magic haka yaji abu na fizgarsa zuwa gareta especially her lips,he just want to know how they feel,a yanda yake kallonsu daga gani zasuyi laushi so he wants to confirm,ba wai kissing dinta zeyi ba,he just want to screen them with maybe his fingers,yasan idan ya shafasu ze gane,karasawa dab da ita yayi yana cigaba da kallonta……..

   “She’s dangerously beautiful!”….. 

   Ya fada yana kokarin dora hannunshi akan lips dinta……… Sallamarta ce ta katseshi,yayi saurin janye hannunsa…..

Karasowa tayi fuskarta ba yabo ba fallasa tace 

     “WACECE ITA?!”……

   A razane yace

      “ban wacece ita ba”….

     “Bakasan wacece itaba? Har kukayi accident tare?, don’t forget you’re talking to a judge! My friend explain yourself!”…..

    “Trust me,mami wallahi bansan wacece ita ba,she only helped me,unfortunately sai mukayi accident”

Deen ya fada obediently,ba itaba har shi kansa saida yayi mamakin yanda ya mata magana with respect yau…

Dan shiru ne ya biyo baya kafin tayi breaking silence din da fadin

    “Ka fadamin gsky tin yanzu dan wallahi idan nayi bincike nayi finding out abunda ka fada karyane,I’ll deal with you,kasanni sarai!”…. 

    “Yes,bansan taba but I want to know who is she too”…. 

Girgiza kai mami kawai tayi,a ranta tana fadin ‘anzo gurin’, as a judge tasan koyaya there’s something,sannan one thing she loves about Saifuddeen shine baya karya,very straightforward mutum ne shi,tin farko ta yarda besan yarinyar ba amma tasan akwai wata a kasa shiyasa tace mishi zatayi bincike,shikuma yasan tinda tace zatayi bincike zata gano komai shiyasa kawai ya fada mata abinda ke ransa,yasan kuma she’s a very smart person kusan a gurinta ma ya dauko smartness dinsa……..

 Ganin batace komai ba ya kalleta kamar me tsoron yin magana yace

     “Mami don’t judge me,amma dan Allah what do you notice about this girl?”…

Kallon fatima zainab mami tayi,tadanyi smiling sannan tace….

     “She’s very beautiful,nasan abinda ke ranka kenan?”….

Girgiza kai yayi yace

     “I know she’s so gorgeous but there’s something in between that beauty,ki kalleta sosai”….

Girgiza kai mami tayi tace…

    “I can only see a young pretty lady sleeping peacefully,no in between!”……

     “I know,but she looks dangerous”…. 

Zaro ido mami tayi tana fadin……

     “Dangerous kuma?,what do you mean by that?,how can a person look dangerous Saifuddeen?”…

     “Dangerous might not be the right word,but trust me akwai wani abu a tattare da yarinyar nan,bansani ba ko nikadai ke gani,but I’m assuring you she’s not okay”…… 

      “Saidai idan you’re mistaken,but this lady is perfectly alright,bansan wannan halin naka Saifuddeen, hakanan sai kaga mutum kace he’s not ok,da alamu kai kanka you’re not ok”…..

Murmushi sosai Deen yayi  yace…

     “Ai ni koda yaushe I’m not ok a idonki mami,amma yarinyarnan hmmm let me just keep quiet,well zakiga abunda nake cewa wataran”……..

Mami zatayi magana kenan sukaji sallamar mutane…..

Bude ido mami tayi ganin yan sanda sun zagaye dakin,kafin tace wani abu daya daga cikinsu ya nufi gurin Deen da handcuff a hannu,yana fadin

    “You’re under arrest sir!,silently follow us to the station”…..

     “Arrest?, For what?”….

Mami ta fada tana wondering mai Deen ya aikata?

    “Yes ma,ganinki a gurinnan ne yasa bamu sa masa handcuffs ba duk da bamusan alakarku ba,so tell him to follow us quietly”…..

Ajiyar zuciya mami ta sauke sannan tace 

    “He’s my son!, I’ll get him to the station my self,ku muje!”…. 

Sai a lokacin Deen ya dago,ya kalli doctor yaname nuni da fatima zainab yace

    “Pls take very good care of her for me,I’ll definitely come back soon for her!”……

Murmushi Doctor yayi yana nodding kansa,mami ko binshi da wani mugun kallo tayi,ace anzo kamaka amma ko a jikinka saima bada wani sako da kakeyi,wani kalan mutum ne Deen?….

       Kuka takeyi sosai tana ganin abun kamar almara,ace wai ita alhaji zesa a kama?, a lokacin daya fita daga part dinta dariya tayitayi dan tasan asirin data masa bai isa ace ya sakesa ba wallahi,sai kawai ta cigaba da harkokin gabanta kamar komai bai faru ba,tuno da alwashin fatima zainab yasa cikinta ya kada,mikewa tayi da sauri ta nufi toilet,sai kuma ta dawo ta zauna tana bawa kanta assurance din ba abinda fatima zainab zata iyayi tinda tasan ta gama da alhaji,zama tayi ta dora kafa daya kan daya sannan ta kunna tv……

Tana nan a kishingide kamar daga sama taji an daki kofar part dinta,kafin ma ta motsa wasu kattin mata suka baibayeta alhaji na biye dasu,a take ya basu umarnin suyi arresting dinta, ba bata lokaci  suka aiwatar da umarninsa……..

Su husnah najin alamun yan sanda suka fito da sauri,turus sukayi ganin daddy ne da kansa yasa a kama mamansu,hakuri suka shiga bashi amma ko kulasu beyiba dan sam baya cikin nitsuwarsa, shikadai yasan mutuwar Fatima Zainab abinda ze haifar masa…..

Basu nufi ko ina da mama ba sai police station,abu kamar almara sai gashi an saka mama a cell ana jibgarta akan ta amsa lefin ita ta kona fatima zainab harta mutu sannan ta fito musu da gawarta…

Ba karamin fita hayyaci mama tayi ba,har takai ta kawo bata gani sosai,ganin suna neman hallakata yasa tayi accepting ita ta kona ta amma batasan inda gawar fatima zainab yake ba,jibgarta suka cigaba dayi wai saita amince zata nuna musu gawar…….. 

          Babu irin neman dabe yiwa fatima zainab a gidannan ba amma shiru kamar wacce ta bace,gajiya yayi ya hakura ya dawo part dinsa ransa fess ko banza ya san ya kullawa mama kullalliya,shiyasa akace idan zaka gina ramin mugunta ka ginashi karami saboda wataran kai zaka rufta ciki,ita yanzu tanaji tana gani tasan fatima zainab bata kone ba amma shedu duk sun nuna ta kone kuma ba yanda ta iya…….

Shigowarsa part dinsa yaji karar motar yan sanda,ko dar be jiba dan yasan mama akazo kamawa and she deserves it,saima zaman tinanin inda fatima zainab taje yakeyi, yasan dai da kafafuwanta ta fita kuma zata dawo….. 

Sameer ne ya fito daga bedroom din khaleel da sauri yace

     “Khal ba karar motar yan sanda nakeji a gidannan ba? I hope all is well?”….

Daga kai kawai khaleel yayi sannan yace

     “Yes,karka damu,it’s nothing serious”…..

     “Bangane it’s nothing serious ba? Kasan dai nima kamar family nake, ko haryanzu kanajin haushina ne da bazaka fadamin ba?”…….

Sameer ya fada da fuskar rashin jindadi 

     “Nop sam,you’re a family of course,kuma duk abunda ya faru ya wuce,nasan you don’t mean it,kawai long story ne!”…..

Khaleel ya fada dan harga Allah har cikin zuciyarsa ya yadda da sameer……. 

    “Toh ka fadamin meyake faruwa pls,wa kuma sukazo kamawa?”……

     “Well mama aka kama for an attempted murder that only me knows it’s attempted,but everyone thought it’s committed already,can you believe wifey taso konawa?”…….

Zaro ido sameer yayi ya dafe kirji jin wani mugun abu daya taso masa da khaleel yace wifey,da sauri ya maze yace 

     “Kaiii,is she insane?, saboda me zata kona fiancé dinka?, I hope your wifey is safe dai?”…..

      “Yes she is!”….

       “But why did you lie bayan kasan ba abinda ya sami wifey din?”…..

       “I want mama to learn her lesson,zan fadi gaskiya amma sai naga tasha wahala sosai yanda bazata kara attempting kashemin mahadin rayuwata ba”…..

     “Gsky ka kyauta,abunda tayi attempting is so disgusting,amma meyasa ta tsaneta haka? Don’t you think there’s something behind it?”….. 

    “Well I can’t really say actually amma nafi tinanin ta tsaneta ne saboda gatan da daddy yake nuna mata,wanda ya samo asali ne saboda ni”….

Murmushi sameer yayi a zuciyarsa yana ‘anzo wajen’ dan da alamu dai ze san wacece ita nan kusa ganin yanda khaleel ya saki baki yana bashi labari,yace

     “Can I know yanda relationship dinku yasamo asali,dan wallahi ba karamin birgeni soyayyarku takeyi ba”…..

Wani dadi khaleel yaji jin an yabi soyayyarsu dayake tarairaya,zuciyarsa fes yace

      “Yau zan fadamaka the little I know about wifey”….

    “Am all ears”…..

Sam ya fada giving khaleel full attention……

       It was on a Sunday evening,a gajiye khaleel ya shigo gidan 1am na dare,dawowanshi  kenan daga UK,ya kawo musu surprise visit,yanda kawai kowa saidai ya ganshi da safe,murda kofar main parlor yayi,by luck sai ya samu kofar a bude duk da beyi expecting ba,karar shara yaji daga far end din parlour,bin ko ina ya farayi da kallo harya hango ta…… “Hasbunallahu wa ni’imal wakeel,fata barakallahu ahsanul khaliqin,tsarki ya tabbata ga ubangijin daya tsara wannan halitta!”ya fada yana binta da kallo,kamar yanda take binsa da kallo……Wayam kuma sai yaga ba kowa,kamar wacce ta bace,kalle kalle ya farayi yana neman inda tabi amma bega ko alamun giftawar mutum ba,sai kawai yaji wani tsoro ya kamashi,yace kodai gamo yayi ne sbd shidai yaga halittar da duk wani lafiyayyan namiji bazai mata kallo daya ya dauke kai ba,sai ya fara karanto duk adduar da tazo bakinsa……Ya dade yana addu’oin kafin ya daure ya karasa cikin bedroom dinsa yana rokon Allah ya daukemasa abinda yagani daga idonsa,saidai me? Jiyayi kamar a lokacin yake ganinta,zai iya rantsewa tinda yake bai taba ganin macen da tayi capturing attention dinshi haka ba kasancewarsa playboy me wasa da zuciyoyin yan mata saboda kyawun da Allah ya masa,sai gashi yayi gamo da wacce ta gama dashi despite looking unkept,abun mamakin ma she looks so young a fuska bcoz ze iya cewa batafi 15 ba,sai dai a yanayin cikar halitta saika dauka tafi haka sosai,height dinta is medium saidai tafi kusanci dame tsayi,shiyasa saika kasa ganewa siririya ce ko me kiba? Dan daya fara kallonta daga sama ya dauka bata da wani jiki saidai yana kaiwa kasa yasan ba karamin halitta Allah yayi a wajan ba shiyasa ya kasa tantance stature dinta,addu’arsa daya Allah ya kara hadasu yanda ze fayyace komai nata sosai….  ‘Toh kodai aljana ce?’…..

Wata zuciyar ta fadamasa haka ganin tana shara karfe dayan dare,dole da alamar tambaya kuwa….“Kai saidai hurul’ayn”…. Ya fada kamar wani shashasha yana bawa kansa assurance din mutum ce… Zama a kasa yayi ya cigaba da siffanta surarta dayin sake sake kala kala a kanta idan har mutum ce… Sai da yaga yana neman wuce gona da iri sannan ya hakura ya fara istigfari da rokon Allah ya sake hadasu……

Koda ya kwanta still ita yake gani har bacci barawo ya daukesa,ko a barcinma bata barsa haka ba saida ta kawo masa ziyara,haka dai yayi baccinnan a hargitse…….. Koda ya tashi sallar asuba da ita ya tashi a ransa,haka dai ya daure yayi sallah a daki dan yanda bashida nitsuwarnan baze iya shiga mutane ba….. Wani baccin ne ya sake kwasheshi,saidai baije ko ina ba ya sake farkawa a birgice,burinsa kawai ya sake ganinta ko yaji sanyi a ransa,jallabiya ya zira ya fita da sauri ya nufi part din mamansa(momma)…..

Da farinciki ta taresa tana rungumeshi,baki har kunne tace

     “Welcome son,irin wannan surprise haka,yaushe kazo?”……

     “Who is she?”… khaleel ya fada batareda ya bata amsar tambayarta ba….

      “Bangane wakake magana akai ba?” 

      “Yarinyar da take shara da daddare!”

      “Bangane yarinyar da take shara da daddare ba?,oh wai waccan shegiyar?,toh ka fita sabgarta tun wuri banaso,kar inji kar in gani wallahi kaji dai na fadamaka!”……

      “Ina take?, I just want to see her”…. Ya fada kamar ba dashi tagama magana yanzu ba….. 

Haderai momma tayi tana fadin

    “Kaji dai abunda na fadamaka,kafita sabgar yarinyarnan,nima bansan inda take ba!”…..

     “Momma dan Allah ki fadamin indai harkinsan inda take idan baso kike zuciyata ta buga ba!”

   “Nace maka batanan,ka duba part din hafsah nasan tanachan”….. 

Momma ta fada kamar gaske,nan ko so take yana fita taje ta kulle fatima zainab yanda baze taba ganinta ba harya bar gidan kafin tasan yanda zatabar gidan gabadaya…… 

Fita khaleel yayi da sauri ya tafi part din hafsah(mama),itako momma da sauri ta fita daga bedroom dinta tayi kitchen inda fatima zainab ke tsaye tana wanke wanke,janta ta farayi har takaita wani abandoned room dake parlourn,turata ciki tayi sannan ta kulle dakin da mukulli ta kuma boye key din inda tasan ba wanda ze gani…

           Ko sallama beyiba yashiga part din, su husna ya tarar a parlourn suna kallo,da sauri suka shiga gaishesa da ladabi,be kulasu ba yace

    “Where is she?”….

     “Wakake nufi yaya?”… Imaan ta fada ganin sai kalle kalle yake

    “The pretty girl,bansan sunanta ba, momma tacemin tananan”……

A take suka gane wa yake nufi dan ita kadaice a gidan wacce be sani ba tinda bayanan tazo,kuma ita kadai zaa iya kira da pretty a gidan,dan su kam uwarsu suka kwaso,kuma dai mama sai a hankali…

    “Tana part din momma yaya,ai anan take”…

Girgiza kai yayi yana tinanin meyasa momma zata mai karya, sai wata zuciyar ta basa shawarar tambayarsu ko WACECE ITA?…

      “WACECE ITA?”…..

     “Wallahi yaya muma bamu santa ba, daddy ne ya kawota, kuma be gayawa kowa wacece ita ba”…..

     “It’s ok”… Ya fada yana barin parlourn

 

   “Momma dan Allah dan annabi ki fadamin inda yarinyarnan take,an tabbatar min tana part dinnan” khaleel da yafi minti ashirin yana tambayar momma ya sake fada pleadingly 

    “Kasan Allah khaleel ka kiyayeni, dan naga taketakenka akan yarinyarnan, fisabilillahi daga ganin sarkin pawa sai miya tayi zaki? Bakasan mutum ba lokaci daya ka haukace akansa kana nemansa? Toh wallahi bazaka kara ganinta ba gwara ka shafawa kanka lafiya ka rabu dani!”…..

Momma ta fada a zafaffe……

Marairaicewa khaleel yayi kamar zeyi kuka yace

     “Momma dan Allah ki taimakeni ki fadamin inda take, I don’t care who she is kawai burina na kara tozali da ita”……

Haderai tayi sosai ganin kamar baya gane warning din datake bashi tace

      “Allah ya kiyaye, bakai  ba wannan shegiyar wallahi! Get out of my room, stupid kawai!”…..

Kin tashi yayi saima tsugunawa dayayi yacigaba da bata hakuri yanajin kamar ya fashe da kuka,zuciyarsa ko harta fara masa suya dan yanada heart problem tin yana karami,shiyasa in be samu abinda yakeso ba nanda nan yake fita hayyacinsa…

Ganin yaki fita kuma yana neman karyar mata da zuciya yasa ta fita ta bar masa dakin, parlour ta nufa ta kunna tv hankali kwance…… 

Biyota yayi da sauri ya cigaba da rokonta ta fadamishi inda yarinyar take…..

     “What’s your problem ne da zaka dunga  bina anywhere?”….

     “Tell me where the girl is, I love her, kuma aurenta zanyi!”…..

Sai da gaban momma ya fadi, abinda take gudu gashi ya fada tin kan aje ko ina,to wallahi bazai yiwu ba, Allah yaso ta tayiwa tufkar hanci tintini…. 

    “Bari gaji wallahi ko zanyi yawo tsirara bazaka aure shegiyar yarinyarnan mara asali ba!”…..

Fashewa da kuka khaleel yayi dan zuciyarsa is very weak, sam baya iya daukan abubuwa,he never knew this is what love felt like, he can’t believe he love someone at first sight?, Allah yasa ba alhakin ya’yan mutane bane ke neman kamashi,komadai menene Allah ya sassauta masa yasa ya ganta,magiya yashiga yima momma har saida ta mareshi tsabar bacin rai..

Wai duk matan duniya ya rasa wa zai so sai yarinyar da bata da asali?….. Ta kuma cewa

      “In kaga ka auri yarinyarnan toh bayan raina ne,in baso kake in tsine maka ba kafita ka bani guri”…

Wani irin jiri ne ya kama khaleel, a hankali yaji kamar numfashinsa na daukewa,daganan bai kara sanin abinda ya biyo ba!!!!

    

Alhamdulillah!! Finally back after a successful short ride…..

Thank you all for the prayers,calls,texts and all….

You all mean alot to me❤️

Saimu cigaba da gashi ko😂…..

Unique Barakancy ce😁

Back to top button