Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 42 Complete Novel

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

                            FORTY-TWO📍

        “Dan Allah abby dagaske?”…..

Khaleel ya fada yana ji kamar ya taka rawa…..

Gyada kai abby yayi yana murmushi yace;

     “Yaushe kace zaa daura auren?”…….

Cikin zumudi khaleel yace;

    “Anjima kadan Abby”…..

A nitse cikin tausasawa Abby ya sake fadin;

     “Amma kuma haka zaa daura auren tana kwance ba lafiya? Son meyasa bazaka bari in taji sauki ba? Kaga sai ayi abinnan cikin farin ciki da kwanciyar hankali”………

Shiru khaleel yayi yana jimamin abin aransa, tabbas maganar Abby gskyne amma zeso a daura ko tana kwancen ne saidai kuma baze iya yiwa Abby musu ba…… Cikin sanyin murya da mutuwar jiki yace;

      “Toh Abby Allah ya bata lafiya”….,

Murmushin jindadi Abby yayi ganin khaleel ya fahimce shi ya dafa kafadarsa yace;

      “Karka damu my son, zata samu lafiya very soon Insha Allah kuma ina tare daku, sannan shawarar da zan baka ka barta a asibiti taji sauki sosai akan kuna zuwa kuna dawowa”………

      “Hakane Abby, Insha Allah haka zaayi, nagode sosai”…..

Nan suka cigaba da hirar duniya…………

        Cikin dare jirgin su Deen ya sauka a Dubai, ba bata lokaci ya tari cab ya kaishi gidansa da daddy ya siya masa lokacin da yazo wani course 5 years back, yana zuwa ya tarar da gidan a gyare kamar yanda ya bari dan kullum sai anzo an gyare gidan ga kuma mai gadi da komai, shiga cikin gidan yayi ya nufi bedroom dinsa direct, wanka yayi sannan yayi sallah yasha coffee, shi gabadaya ya manta wani abu waishi abinci dan rabonsa da cin abinci tin ranar data bata, haka yake fama da tea da coffee, shida kowa ya san shi da cin abinci sosai sai gashi ko shaawar abinci bayayi akan yarinyar da batasan me ke mata yawo a ka ba…..

Tracker dinshi ya fito dashi ya gwada tracking wayar offline saidai kash an kashe abinda ze bawa tracker din access to wayar, abinda kuma be sani ba shine Umm ce ta kashe ko kuma ita fatima zainab dince?…

Inko fatima zainab ce lallai she’s too smart, sai kawai ya yanke shawarar nemansu da kansa har ya gansu tinda an tabbatar masa suna dubai….. 

Yaso ya bari zuwa gobe ya fita ya fara nemansu sai zuciyarsa ta kasa daurewa, haka ya fito a daren ya fara yawan nemansu, kamar zararre haka ya dinga zuwa layi layi, shago shago a kafa yana nemansu, babu lungu da sakon daya gani dabe shiga nemansu ba, yayi tafiya yafi na hour uku amma babu kome kama da su, haka ya daure ya cigaba da bawa zuciyarsa kwarin gwiwa akan lallai ze nemosu duk inda suke, yana tafe har aka kira sallar asuba, a Grand Bur Dubai Masjid daya kasance nearest mosque a lokacin ya shiga yayi sallah, haka ya zauna yayita kwararo addu’a Allah yasa ya gansu yaci ubansu, kamar zararre haka ya dora daga inda ya tsaya bayan ya fito daga masallacin, ya shiga abun hawa kuma yaki dan gani yake sai yafi ganinsu a kafa, haka yayita shawagi a garin dubai yana nemansu, kawai sai tsintar kansa yayi a ‘Opera Gallery Dubai’, zaro ido yayi yana mamakin yaushe ya kai nan, gurinda sai kayi tafiyar 400km daga gidansa sai gashi yayi wannan uban tafiya be sani ba…… 

Wata kyakkyawar shawara zuciyarsa ta yanke masa, ba bata lokaci ya shiga cikin opera gallery, guri ne me dauke da zane kala kala na gani na fada da akeji dashi a kasar dubai, drawing session ya shiga yace a bashi materials, sunata mamaki me zeyi dashi, haka aka kawo masa duk wani necessary abu na standard drawing, ba bata lokaci ya nitsu ya shiga zana duk wani features na fuskarta kamar yanda yake haddace akansa koda yaushe….. Ya kai one hour yana zanen kafin ya gama amma it was so perfect kamar ba artificial ba, kallon zanen ya shigayi with so much adoration kamar ita yake gani a zahiri, murmushi ne ya subuce masa kamar tana wajan yace;

      “Ashe haka kike da kyau? Can I say you’re the most beautiful girl I’ve ever seen? Naaah don’t feel yourself bana kallon mata bare in sani”……..

      “Where are you? Meyasa zakibi namiji ku gudu? Why? Why baby girl!! Allah idan an daura aurennan saina kashe shi, I don’t mind you being karamar bazawara! Barema I have a strong feeling that baa daura ba!!”…..

Ya sake fada yana jin yanda ransa ke baci, daga drawing din yayi ya cigaba da kallo yanata masifa kamar da ita yake……

Tafi yaji anayi daga gefensa ya dakatar da masifar da yake ya dago yaga su waye, ganinsu yayi a tsaye sai kallon drawing din da yayi suke kamar su kwace daga hannunsa, tafi suka sakeyi cikin turanci wani ya mika hannu ze karbi zanen yana fadin;

      “This is so perfect habeebee! Like beyond perfect! Can we pls have a copy of this?”……

     “No!”….

Deen ya fada cikin hada rai…..

     “Ok can we just capture it habeebee?”….

      “Impossible!”…..

     “Why?”….

   “Because she’s my soul mate and I can’t afford sharing her with anyone!”….

Ya basu amsa kai tsaye…..

Wani ne ya kalli Deen yace;

      “Wow she’s so beautiful, I mean flawless”….

Wani kallon banza Deen ya masa ya rungume hoton yanda bazasu gani ba yace;

     “I didn’t ask for your compliment! I know she’s beautiful!”……

      “Wow such a jealous fellow!”….

Harararsa Deen yayi ya tashi ya mika musu atm card dinsa still kirjinsa rungume da hoton yace su cire kudin materials dinsu da yayi using, cewa sukayi ya barshi for the sake of the beautiful design, ai sai suka kara kunnashi yayita bala’i wai mutane basa gani suyi shiru, ya karbi card dinsa ya watsa musu cash din dake aljihunsa kamar ze dake su sannan ya fita, kallon mamaki suka bisa dashi suna tunanin sunyi abun arziki sai gashi abu ya juye musu……….

Tafiya ya cigaba dayi yana rungume da zanen kamar zaa kwace masa, plan dinsa a da shine ya zanata ya dinga nunawa mutane hoton yanda zeyi saurin ganosu, amma yanda yaji wa’enchan suna koda zanen ko sama da kasa zasu hade baze iya kara nunawa kowa ba, haka ya cigaba da yawo yana nemansu da description kamar yanda ya fara, yana cikin wannan hali yaga call din sameer ya shigo wayarsa da number Nigeria dinsa, dake akwai wani clone application da zaka iya cloning number Nigeria dinka data wata kasar sai a kiraka da number Nigeria normal ya shigo, dauka yayi da sauri jikinsa na rawa yace;

      “Sameer ya ake ciki? Ya gaya maka inda suke a dubai din?”…..

Daga daya barin sameer yayi wani murmushin mugunta ganin yanda Deen ya wani damu sosai dan shi fa haryanzu be yadda Deen ba, in ba hakaba meye hadinsa da khaleel? Sannan takaicin kin daga wayarsa da khaleel beyiba ya sashi kiran Deen ya shirgasa dan baze zama shi kadai yake suffering ma wulakancin da khaleel ya masa ba bayan yaci burin zuwa ya bata aure…….

      “Sun bar dubai saboda dad dinsa ya gano suna chan!”……

Da sauri Deen yace;

      “Ina suka koma pls?”…..

     “Iran!”……

    “Ok ok thank you, but where in Iran?”….

        “Wlh bansani ba, be fadamin ba”….

      “Alright no problem”…..

  “Chan zaka tafi kenan?”….

Sameer ya tambaya yana dariya kasa kasa….

Cike da damuwa Deen yace;

     “Yes chan zani, just call me if there’s anything, ko zaka bani number khaleel pls?”….

     “Babu waya a hannunsa, wayar different mutane yake ara yake kira na”……

     “Okay”….

Deen ya fada yana kashe wayar, ya kunna data ya hau duba available flight to Iran.. Allah ya taimakesa ko ya samu na nan da thirty minutes dake Iran babu wani nisa da dubai…… 

A Iran azahar ta masa ya shiga Nasir al-Mulk Mosque yayi sallah, kamar a dubai haka ya zauna ya kwararo addu’a akan Allah yasa ya gansu anan, saidai kash haka ya karaci yawansa kamar yanda yayi a dubai ko alamunsu babu, yanajin yanda kafafuwansa suke masa nauyi amma baze iya hutawa ba, gani yake lokacin daze huta kila lokacin ze gansu, haka yayita zagaye Iran duk sanda yaji kiran sallah ya Parker yayi sallah yayi addu’oi ya cigaba da tafiya kamar me hijira…….. 

A haka har wata washe garin tayi, wani supermarket yagani kusa da wani hotel ya shiga ya siye kayan da ze chanza sannan ya shiga hotel din yayi wanka ya shirya, shayi kawai yasa aka kawo masa yasha ya dora daga inda ya tsaya ko tinanin bacci bayayi…..

Bayan ya idar da sallah asuba kiran sameer ya sake shigo masa, ya dauka da sauri as usual……

     “Boss kana Iran din ne?”…..

Sameer ya tambaya kamar gaske…..

      “Eh ina chan, kaga haryanzu bangansu ba wlh”….

Deen ya basa amsa yana jin wani daci a ransa……

       “Ai dama bazaka gansu ba, ashe sun sake barin Iran!”…..

Cewar sameer kai kace haka abin yake…..

Cikin hargowa Deen yace;

     “Shit! Ina suka koma kuma? Wallahi if I get hold of them na lahira sai ya fisu jindadi”….

 Tabe baki sameer yayi aransa yace kai kasan munafurcin da kake shiryawa, a zahiri kuma sai yace;

     “Sorry dude! China suka koma!”…..

     “What? China kuma?!”…..

    “Yes china!”….

   “It’s okay ko gaba da china sukaje saina nemosu wallahi!”……..

   “Kaidai bari bansan me yake damun brain din khaleel na guduwa ba, gashi be gayamin ina suke a china ba”……

     “Karka damu, ko ina suke zan nemosu!!”…..

Deen ya fada cike da karfin gwiwa…..

Suna gama wayar ya fara laluben flight da zaije china yanzu yanzu, be samu ba saina anjima haka ya hakura ya samu guri ya zauna a airport din…….

Yana zama wata iranian babe tazo ta mishi hi, ko kallonta beyi ba bare ya san tanayi, shafa fuskar shi tayi tace;

     “Hello handsome!”…..

Dagowa yayi ya dauketa da wani wawan mari dama neman inda ze sauke fushinsa yake abu ya cika da ita, a take yaga securities sun yo kansa, zabgawa wanda ya fara zuwa kusa dashi mari yayi ya naushi na daya gefen, yarinyar ce tayi saurin dakatar da securities din dan ita bataji zafin mari ba sam, ta kalli Deen da yake wuci kamar ze tashi sama tace;

      “I’m sorry handsome”…..

Ko kallonta beyi ba ya tashi ya bar gurin………

Dawo da kallonta tayi akan securities din tace;

      “I need to know everything about him before today runs down!”……

     “Yes ma!”…..

Suka hada baki wajan fada……

Saida asuba ya isa china saboda tafiyar kusan awa shida sukayi, hotel din dake kusa da airport ya shiga yayi wanka yayi sallah sannan ya fito ya hau nemansu kamar yanda ya saba, duk inda zashi yana rungume da hotonta a kirji amma ya kasa nunawa kowa, ya gwammace yayita nemansu akan ya nunawa wani hotonta…….

Haka yayita yawo har gari ya waye……

Kwanansu uku a asibiti sannan ta dan dawo normal amma har lokacin baa sallamesu ba….. 

Tana zaune khaleel ya shigo bayan yaje sun gaisa da Abby, a lokacin ta dade da sanin Abby dan kullum sai ya shigo ya dubata saidai haka kawai taji mutumin be kwanta mata ba shiyasa ta kasa sakin jiki dashi, zama yayi a kusa da ita, ya kalleta cike da so da kauna da tausayi yace;

     “Ya jiki my love?”…..

     “Alhamdulillah”….

Ta bashi amsa cikin muryar marasa lafiya….. 

     “Abby yana gaishe ki”….

Yi tayi kamar bataji ba tace;

     “I need you to get my codeine for me khal, banajin dadin jikina wallahi”….

A sanyaye ya mike da fadin;

      “Okay, let me go get it for you, amma kamar yau zasu sallamemu bazaki jira mu koma ba?”……

Girgiza kai tayi tace;

     “I can’t wait, ka dauko min yanzu”….

     “Okay love”…

Ya fada yana fita daga dakin, straight hotel din da suka sauka ya tari cab ya kaishi, yana zuwa ya dauko two bottles kamar yanda yaga tana sha ya saka a cikin hand bag dinta da suka siya sanda suka zo…..

      Tana kishingide ya dawo hannunsa dauke da jakarta, mika mata yayi ta karba ta zuge jakar, ciro kwalaben tayi ta ajyesu a gefe, har zata zuge jaka ta hango wani abu, fito dashi tayi taga wayar Umm ce data dauka, jujjuya wayar ta shigayi a hannunta tanajin wani guilty conscious na kamata na daukarwa mata waya datayi, sai kuma oga ya fado mata arai, ko ina yake yanzu? Murguda baki tayi tace ‘masifaffe’, kallonta khaleel yayi yace;

      “Ke kuma dawa?”…..

Tsaki tayi tace;

     “Wani banza ne!”…… 

Sai kuma ta hau kunna wayar………

KARANTA ZAFAFA 2023

*IDON NERA By Mamuh ghee*

       Deen daya keta yawan nemansu har lokacin ya kasa giving up kawai yaji tracker dinshi ya fara alarming din din din, da sauri ya duba wayarsa inda yayi connecting yaga processing address, ko kafin ya gama tantance ko mafarki yake yaga address din ‘American Hospital Dubai’, hakan kuma yana nufin an kunna wayar a chan ne, zabura yayi ya sake gyara tsayuwarsa yana kallon wayar da har lokacin address din beyi disconnecting ba, nan yagane wayo khaleel yayiwa sameer yake cemasa baya dubai, toh kodai sungane yana nemansu ne? Koma menene Allah ya tonu asirinsu, a yau dinnan basai gobe ba zeje ya samesu, cije dan yatsa yayi tuno da distance din dake tsakanin china da dubai, amma be gaza ba haka ya siye ticket a take ya bar china da short short dan baze iya jiran direct flight ba……. 

        Sai yamma aka sallamesu daga asibitin, sallama sukayi da Abby suka tafi da niyar gobe Abby ze jagorancesu a daura auren tinda ta samu lafiya sosai,  sai a lokacin kuma ta kashe wayar……. 

An fito daga sallar isha’i Deen ya karaso ‘American Hospital Dubai’, sake duba tracker dinsa yayi yaga an kashe wayar dazu, hakan ya basa tabbacin dole suna asibitin inma basa nan toh suna kusa, reception din asibitin ya nufa da niyar ya nemi appointment da me asibitin a matsayinsa na likita yanda zeyi saurin gano patients din dake asibitin…….

Kamar a mafarki yaji an dafa kafadarsa, juyowa yayi da sauri duk a tinaninsa wata yar rainin hankalin ce yaci ubanta itama, sai kawai yaga mutumin da be taba tinani ze kara gani ga a rayuwarsa……. 

Baki na rawa ciki da mamaki yace;

       “Abby?????”….

     “Na’am Saifuddeen”….

Ya basa amsa idonsa na cikowa da waye…..

Sai kuma ya rungume Deen yana fashewa da kuka…

Ruko hannunsa Deen yayi suka fita daga harabar asibitin yana fadin;

     “Dan Allah ka dena kuka abby, where have you been all this while?”…….

Cikin rauni Abby yace;

      “Bani da lafiya Saifuddeen, ina kwance a asibiti fiye da shekara biyar sai yanzu Allah ya tashi kafaduna”……

Cikin tausayawa Deen yace;

     “Subhanallah! Allah ya kara lafiya abby”…..

A hankali yace;

     “Ameen, ina boddi na?

    “Tana nan!”….

Kamar zeyi kuka yace;

     “A ina?”….

     “Gida!”…..

Deen ya bashi amsa……

     “Dan Allah Saifuddeen ka taimaka ka kaini in ganta dan Allah”…..

Abby ya fada yana ruko hannun Deen….

     “Karka damu zan kaika amma akwai wani urgent abu daya kawoni idan na gama sai mu tafi tare”……

Sake fashewa yayi da kuka yace;

      “Dan Allah ka kaini yanzu Saifuddeen sai insa a dawo da kai a yau, dan Allah ka kaini kafin na mutu”…….

Tausayi ya bawa Deen sosai dukda yanaji bazai iya komawa Nigeria batareda ya gansu, cikin tausayawa yace;

       “Bazaka mutu ba Abby, na maka alkawarin zan kaika amma ba yau ba”…..

Sai ya nemi ya duka kasa akan dan Allah Deen ya kaisa…….

Hanashi kaiwa kasa Deen yayi yanajin yanda jikinshi ya sanyi ganin yanda babban mutum kamar Abby ke neman tsuguna masa, a take ya yanke decision din daya kejin tinda yazo duniya be taba takurarren decision irinsa ba…….

     “Naji zan kaika, amma dare yayi yanzu ka bari gobe da safe sai mu tafi”….

Cikin farin ciki Abby ya sake rungume Deen yana fadin;

     “Nagode nagode sosai son, babu matsala mu bari goben toh”…..

     “Yauwa, bani number wayarka zan kiraka da asuba”……

Cikin wani irin yanayi Abby yace;

     “Ka kwana tare dani mana”….

Murmushi Deen yayi yace;

     “Don’t worry zanzo da safe ai ina kusa, akwai report din daya kamata inyi ne kafin mu tafi”….

      “Toh a hakanma nagode sosai Saifuddeen, Allah ya kaimu gobe da safen”….

    “Ameen ameen Abby, saida safe”…..

        “Allah ya bamu alkhairi….

Abby ya fada yanajin kamar yayi tsuntsuwa yagansa a Nigeria gobe……

Abby na komawa ciki su khaleel suka fadomasa, rudani ya shiga akan yanda zeyi da lamarinsu, tabbas yanaso yaga sunyi aure kamar yanda suke so amma ba irin wannan auren ba, ya fiso suyi aure na gaske da amincewar iyayensu….. Wani dabara ne yazo masa yayi dialing number khaleel……

Suna zaune yana matsa mata kafafunta yana mata tausa sunayi suna zubawa juna kalaman soyayya yaga kiran ‘waliyyi’ kamar yanda yayi wa Abby saving, ba bata lokaci ya dauka ya fara gaisheshi cike da ladabi…….

Saida suka gama gaisawa sannan Abby ya masa bayanin yar tafiyar data taso masa urgently zeje Nigeria, sosai hankalin khaleel ya tashi da jin wannan maganar saidai be gama jimami ba Abby ya fara masa wani bayanin daya faranta masa at the same time yasa masa shakku, cewa yayi indai ya daukesa a mahaifi kamar yanda ya fada yanaso su bishi Nigeria ya daura musu aure a goben kamar yanda yayi musu alkawari, shiru khaleel yayi dan ya rasa me zece, haka abby ya cigaba da basa baki da kara kwantar masa da hankali akan in suka bishi ba abinda ze hana a daura musu aure, in fact in zaman dubai din sukeso zesa a dawo dasu ana daura auren, nan ko so yake ya tafi dasu Nigeria yaje ya bawa mahaifin khaleel hakuri akan ya aura masa ita, yasan kuma Insha Allahu in yaje da kansa zasu amince, irin gamsassun bayanin dayayi ne yasa khaleel kallon fatima zainab dake sauraren komai itama kasancewar wayar a speaker take ya mata signal da ido akan me tagani, daga masa kai tayi dukda ba wani san Abby take ba amma maganganunsa sun gamsar da ita……..

Sai kawai khaleel ya fadamasa sun amince, sosai Abby ya nuna musu jindadinsa yayita shi musu albarka sannan yace ze aiko a daukesu gobe da safe kawai su zama cikin shiri…….

Deen yaso yaga manager asibitin a ranar amma abun ya gagara saboda baya kasar, haka ya kwana yana zagaye asibitin amma be gansu ba, sai gabannin asuba sannan ya fita ya samu wani hotel dake kusa yayi lodging, wanka yayi yayi alwala ya shirya sannan ya tafi sallar asuba, a masallaci suka hadu da Abby da ba karamin jindadin ganin Deen yayi ba, dan tattaunawa sukayi akan yanda tafiyar ze kasance sannan suka sake rabuwa……

 

8:00am dot Abby ya aiko da mota aka dauki su khaleel, ba bata lokaci suka fito suka shiga dama a shirye suke, sunyi balakin kyau cikin matching outfit kamar yanda sukeyi kwanannan, fitted abaya tasa daya fitar da kirar jikinta sai mayafin abayar data yane kanta dashi…..

Har cikin landing area aka kaisu, aka kuma saukesu daidai inda jet din yake, sai a lokacin suka gane private jet ne, mamaki ne ya kama khaleel dan be taba tinanin mutumin yanada arziki haka ba ganin yanda yake da balakin saukin kai…….

Demarcation biyu ne a cikin plane din sai aka kaisu na ciki bayan sun gaisa da Abby dake cikin na farko….. 

Suna shigewa Deen ya karaso, nuna masa kusa dashi abby yayi sannan ya zauna, addu’a akayi plane din yayi taking off……..

Sun danyi tafiya me nisa Deen ya mike tsaye, kallonsa Abby yayi yace;

      “Where to?”….

     “I want to use the rest room”…..

Ya bashi amsa…….

Suna zaune suna shan soyayyarsu kamar yanda suka saba a yan kwanakinnan, kullum ji suke kamar su chinye juna, sai kawai fatima zainab taji gabanta yayi wani mugun faduwa, ruko hannun khaleel tayi tace;

     “Taba kirjina kaji, my heart is beating fast”….

Be taba ba dan bayaso ya tadawa kansa hankali yace;

      “I can feel it, what’s the problem?”…..

Kankameshi tayi kamar zata shige jikinsa tace;

     “Bansani ba, tsoro nakeji wallahi”….

Zeyi magana kenan sukaji ana taba labilen dayayi demarcating dinsu dasu abby”…….

~Uniquebarakancy~

Back to top button