*ASM Bk2005*
_Destiny may be delayed but cannot be changed……_
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
……..gidansu Haulat ta nufa tana zuwa bakin lungun ta hangota ta taho jikinta sanye da Uniform d’in islamiyya hakan yasa taja ta tsaya suna kallon juna har ta k’araso gabanta tana kallonta ganin yanayin fuskar Fatun yasa da yar damuwa tace “kawata ya jikin har yanzu?” gyad’a mata kai tay idanunta sun cicciko da kwalla tace “kiyi hakuri don Allah in sha Allahu komae zai wuce ki dawo kaman da wllh Allah ne shaidata bana jin dad’in halin da kike ciki Fatuu, dake nike kwana nike tashi kullum Addu’ata Allah ubangiji ya yaye maki abunda yake damunki” ta k’arasa itama idanunta sun ciko, shiru Fatun tay kaman bazata ce komae ba sai kuma Haulat taji tace “Yanzu Haulat ki fad’i man ya zanyi in daina jin son Ya Handsome” a sanyaye tay Maganar, ajiyar zuciya Haulat ta sauke kafin ta dafa shoulder d’inta tace “shi so matsalarshi kaman ciwo ne farat d’aya yake shiga amman sauki sai a hankali ba kaman yadda yay maki mugun kamu,amman ba ina nufin bazai barki ba saidae a halin da kike ciki yanzu son Ya Haisam bazai iya barinki farat d’aya ba ba kaman da yake kina ganinshi, dole sai kinyi yak’i da zuciyarki sosae duk yadda zata rink’a azalzalarki kan sonshi ki daure ki cije kar ki biye mata in akwae abunda Ya Haisam d’in ya ta6a maki wanda ya 6ata maki rai ki rinka tunano shi duk in ta ayyana maki wani abu game da sonshi……..” katseta Fatun tayi tace “ni bai ta6a man komae ba na 6acin rai, kawae dai abu d’aya ne banji dadinshi ba shine yadda ya 6oye man tsakaninshi da Aunty Fanan ni nayi zaton soyayyar yan’uwantaka ce kawae tsakaninsu kinga dana sani koda ke baki sani ba lokacin da mukayi Maganar yana sona da zan fad’i maki yana da wadda yake so” shiru Haulat tayi yayin da cikin zuciyarta take ayyana cewa koda ma ya ta6a yi maki abunda ya 6ata maki rai a halin da kike ciki bazaki ji haushin shi ba, a fili tace “to ki daure kiyi kaman yadda nace maki da farko sannan ki dage da Addu’a don ba abunda yafi karfinta in sha Allahu zaki ga komae ya wuce kaman ba ayi ba” jinjina mata kai kawae Fatun tayi, da d’an Murmushi Haulat tace “kinyi kyau sosae” godiya tayi mata tana son tayi mata Murmushin itama amman ta kasa ta kama hannunta tace suje kada ta makara, akan hanyarsu ne Haulat ke tambayarta sai yaushe zata dawo islamiyyar tace mata ta kusa, a daidai kopar gidansu suka rabu Fatun ta wuce ita kuma Haulat tay tsaye har saida taga shigewarta sannan ta girgiza kai,ba k’aramin tausayi take bata ba duk tayi sanyi sai kace ba Fatuu ba daka kalli fuskarta zaka fahimci she’s in serious grief, juyawa tay saida ta gaishe da kawu Amadu kafin ta wuce. Lokacin data shiga gidan bata ga gwaggo ba har Parlor da d’akinta ta duba bata ganta ba hakan yasa ta wuce d’akinta ta haye gado ta fad’a duniyar tunani,tana son ta daina jin son Ya Handsome saidae son nashi ya rinjayi hakan acikin zuciyarta, dama don ta tabbatar ma kanta da baisonta ne yasa take jin gara ta daina son nashi ta huta amman a yanzu bata da burin daya wuce taga ta aureshi wani irin son shi zuciyarta ke azabta mata dashi, a hankali ta kai hannu ta goge kwallan dake zubo mata, mik’ewa tay ta zauna tsakiyan gadon ta d’aga hannu idonta na kallon sama a fili tace “Ya Ubangijina Allah ka yaye man damuwata ka cire man abunda nake ji acikin zuciyata na son Ya Handsome tunda bai sona….” fashewa tay da kuka ta shafa kafin ta koma ta kwanta tana sheshsheka a haka bacci ya kwasheta, sai gab da sallar Magrib gwaggo ta shigo gidan dama makwabta ta shiga dubiya ganin takalman Fatuu a bakin kopa yasa ta gane ta dawo ta nufi d’akin ta d’age labule, ganinta kwance tana bacci yasa ta shiga ta tasheta tayi salla,bayan Sallar isha saiga Fanan lokacin sun dawo daga Gym yau ma Abubuwan ci ta kawo mata kamar rannan ta sanar da ita gobe around 12 ta shirya zasu fita gari kaman tace bata zuwa amman kuma a gaban gwaggo ne hakan yasa ta amsa da to kawae, tare da gwaggo suka ci abubuwan da ta kawo masu ba don tana jin dad’insu ba sai don gwaggon ta matsa mata, bayan sun gama ta bata wanda aka d’ibar ma Amadu ta fita ta kai mashi bayan ta dawo saida ta watsa ruwa ta canja kaya zuwa na bacci sannan ta kwanta sai faman sak’e sak’e take aranta kaman ko yaushe don sam bata jin bacci saboda tayi na yamma koda gwaggo ta shigo yi mata Addu’a isketa tay idonta biyu tace to in ta tashi yin baccin ta tabbatar tayi ta amsa mata da toh.
Washe gari tun bayan data yi breakfast ta tattara kayan wanke wanke tayi tana niyyar yin shara gwaggo tace ta barshi zatayi hakan yasa ta koma tay kwanciyarta, wuraren karfe sha d’aya da wasu mintuna gwaggo ta lek’a dakinta ganinta kwance yasa tace mata ba zasu fita bane tay kwance ta daure ta tashi ta shirya ta amsa mata da to, bayan ta tafi ta yunkura ta mik’e zaune ta zuro kafafunta k’asa har cikin ranta bata son fitan don tasan dole taga Ya Handsome kuma duk inta ganshi ita kad’ai tasan mi take ji, wani dan Murmushin takaici tay wai yau itace ke gudun ganin Ya Handsome, da k’yar ta mik’e ta nufi wardrobe d’inta ta cire kayan jikinta d’aura towel tay ta wuce Toilet, bayan ta fito mai kawae ta shafa tasa undies ta zumbula doguwar riga ta koma gado tay kwance, K’arfe sha biyu saura mintuna kad’an Fanan ta rafka sallama har saida Fatuu ta runtse idanunta jin muryartata, Ma sha Allah abunda na fad’a kenan ganin shigar da tayi ta kwankwatsetsen leshi Coffee brown yana da touches din light brown an mata wasu matsiyatan riga da skirt da suka bi shape d’inta skirt d’in daga k’asa ya bud’e sosae haka hannun rigar ma ya d’an kumburo k’afafunta sanye da takalma masu tsini sosae brown haka hannunta tana rike da yar madaidaiciyar jaka louis vuitton brown colour, tun daga kunnuwanta da wuyanta da hannayenta duk zinari ne harda zobban yatsun hannunta ta kifa daurin kallabi zarah buhari da alama tana son irin d’aurin gashin kanta ta lankwasashi ya tsaya k’asan shoulder d’inta ta d’aura d’an veil brown color a kafadarta d’aya da bata ma sa gyalen ba saida Haisam yay mata Magana sannan ta d’aukko tasa, tsayawa tay bakin Kitchen suna gaisawa da gwaggo data lek’o tana washe baki ta shiga kod’a kwalliyarta tana Fad’in “Tubarkallah ma sha Allahu d’iyata kin matuk’ar yin kyau, d’ana ya barki kikai kwalliya haka karfa a kwace mashi ke” dariya sosae Fanan ke yi jin Maganar gwaggon tace “ni tashi ne ai ba wanda zai iya mashi snatching” gwaggo tace “tabbas wannan haka yake” tambayarta tay Fatuu tace “tana d’aki tun da tay wanka ta shige nasan zuwa yanzu ta shirya bari in kirata” tana niyyar fitowa Fanan tace ta barshi bari tay mata Magana ta nufi d’akin, tana d’aga labule suka had’a ido da Fatuu data tashi zaune jin ta zata shigo, nufar ta tay ta zauna gefen gadon ta kamo hannunta tace “Zarah are u ok?” kai ta d’aga mata alamar eh, kallon jikinta ta d’anyi tace ” ya baki shirya ba?” a hankali tace mata ta shirya,
“But u doesn’t look gud in dis” tay Maganar ta d’an kamo rigar jikinta ita dae shiru tay mata hakan yasa ta tambayeta a ina kayanta suke ta nuna mata bangaren da kayanta suke a wardrobe da hannu ta mik’e ta nufi wardrobe d’in idon Fatuu a kanta ita kanta tayi mata kyau sosae, dudduba kayan ta shiga yi can ta fiddo wasu riga da skirt na Red lace a sallar data wuce Haisam ya yi mata su, lokacin data juyo da kayan har saida gabanta ya buga, aje mata su tayi gabanta tace ta sasu zasu fi yi mata kyau akan wannan rigar, ba yadda ta iya dole ta saukko daga gadon ta d’auki kayan ta fita, bayan wani lokaci ta dawo ta saka su Fanan na ganinta ta saki Murmushi ta hau yaba kyaun da kayan suka yi mata don itama sun kamata sun fito mata da k’irarta saboda yanzu sun saba da Kb mai d’inki yasan irin d’inkin da take so duk da gwaggo bata son ana mata matsattsun kaya saidae bata ma sanin an kai d’inkin saidae ta gansu an kawo taita fad’a, kama hannunta tay ta kaita gaban Dressing Mirror yar light makeup tay mata ta tambayi inda jewellery d’inta suke ta nuna mata drawer chest tana jawowa tay arba da sark’a mahad’in kayan silver ce mai adon red stones harda d’an hannu da zobe ta d’aukko su ta saka mata ta sake d’aukko agogo zata saka mata Fatun tace ta barshi d’an hannun ya isa ta amsa mata Ok, d’aurin kallabi mai kyau tayi mata bayan ta gyara mata gashinta ta d’aure tun kafin ta tambayi takalma Fatun ta curo daga kan shoe rag dake gefen mirror d’in ta saka, d’agowa tay tana kallon kanta a madubi yaushe rabon data yi gayu haka,had’a ido sukai da Fanan ta cikin mirror d’in ta sakar mata Murmushi itama ta d’anyi mata suna cikin haka gwaggo ta d’aga labule ganinsu tsaye yasa tace “kar dai 6ata maki lokaci tay bata shirya ba tun d’azun” tana Murmushi tace “No ta shirya granny na sa ta canja kaya ne” kai gwaggon ta jinjina kafin ta saki labule, bayan ta yafa gyalen kayan da takalma bata d’auki jaka ba suka fito, gwaggo ta fito daga cikin kitchen sukai mata sallama kafin suka wuce idanunta akan Fatuu sosae taji dad’in ganinta tayi gayu haka, Wata rantsattsiyar Mota ce brown fake a kopar gidan bata ma ta6a ganinta ba suka nufeta Fanan ta bud’e mata baya ta shiga ta rufe itama ta bud’e gaba ta shige,wani masifaffen kamshine ke tashi cikin motar hadi da ni’imtaccen kamshin ac, yana zaune jikinshi sanye da jugunannar brown shadda da akai ma fav dinkinshi wato Sen style kanshi ba hula sumar nan tasha gyara sai salk’i take, tana shigowa ta kai hannu ta kama hannunshi guda tace “Sorry babe we kept u waiting” jinjina mata kai yay lokacin suka had’a ido da Fatuu ta cikin Mirror ta gaidashi a sanyaye ya amsa daga haka yaja Motar suka tafi, tunda suka hau hanya bata ce uffan ba sai Fanan ce keta mashi hira hannunta guda ruk’e da nashi hannun yana driving da d’aya wani lokacin kuma ya kan janye hannun kaman in zai sha round, sai Fanan d’in ta sakota sannan take bud’e baki tay Magana, kopar Marusa lowcost ya nufa dasu gidansu Nana suna tsayawa bakin gate d’in gidan Nanar ta fito dama tana ta dakon zuwan nasu don Haisam ya sanar da ita game da zuwan nasu, rungume juna sukai ita da Fanan cike da farinciki take mata sannu da zuwa bayan sun saki juna ta kai idonta kan Fatuu dake tsaye gefe da Murmushi ta kamo hannunta tana mata sannu da zuwa, nufar Motar tay Haisam ya bud’e kopar suka gaisa tace “lallai zakee wannan too match haka kaida Amarya kaman dae an d’aura” yana Murmushi yace mata miya rage ne, ce mashi tay yini zasuyi ko yace zaije dae ya dawo After zuhr akwae wuraren da zasu je, lokacin data shiga dasu gidan gaba d’aya yan gidan na a Falo don a k’agare suke da suga wadda Zakee zai aura don ba k’aramin zuzuta ta Nana tay a wurinsu ba,suna shiga duk suka mik’e suka tarbesu da fara’a suna masu sannu da zuwa kowa idonshi na akan Fanan dake ta masu dariya, bayan sun zauna duk suka shiga gaishe da ita tana amsa masu Fatuu ma ta gaidasu duk suka kira sunanta suka ce tana lafiya da yake sun santa yanzu sosae don duk salla gidan Haisam ke kawota kunshi harda kitso in tana so, wani lokacin ma hakanan in ya fito da ita kaman da yamma in ba islamiyya sai ya kawota gidan idan ya dawo sai yaje ya dauketa yanzu Nana ta san tsakaninta da haisam d’in don akwae lokacin data je gaida Hajiya lokacin taje gidansu Fatun suka gaisa da gwaggo, abubuwan ci da sha aka shiga jera masu kafin a gama Abinci,Fanan ce ta fara ci ita Fatuu cewa tay ta koshi Nana tace wai ko bata lafiya ne ita fa ta lura duk tayi sukuku ba kaman yadda ta santa ba tana rufe baki sauranma sukace duk sun lura da hakan harda mommy d’insu, Fanan ce ta gaya masu bata lafiya ne bata dad’e ma data fara samun sauki ba duk suka hau yi mata ya jiki tana amsa masu suka ce Allah ya sawake,saida Nana ta matsa mata sannan ta d’an ci wani abu, fira sosae suka shiga yi da Fanan dama ita bata da bak’unta ita dae Fatuu baka jin bakinta saida aka kira sallar Azahar Nana ta jasu d’akinta suka yi salla Fatuu na gamawa ta kwanta kan abun sallar su kuma suka ci gaba da yin fira a tsakaninsu har Fanan nace mata za dai tazo bikinsu ko Nanar tace ai ko a India akeyi sai taje balle Lagos Fanan d’in tace ai a Abuja ma take tunanin za’ayi just bai wuce ay wasu programmes a Lagos sannan a dawo Abuja a nan za’a daura aure, duk hirar da suke Fatuu na jinsu jin Maganar aurensu da Fanan ke yi yasa ta runtse idonta sosae kirjinta yay mata wani irin nauyi, suna cikin firar kanwar Nana tazo tace ga abinci can an shirya Fanan tace a kawo masu shi nan kawae tace to ta juya, bayan an kawo kayan Abincin Nana tay serving nasu Fanan tace ta zuba masu gaba d’aya su ci tare tana dariya tace “an gama Amaryarmu” kiran Fatuu ta fara yi ta tashi su ci abincin tana ji tay mata shiru har saida ta d’an bubbuga kafafunta sannan ta amsa mata koda tace mata ta tashi suci Abinci cewa tay ta koshi zuciyarta tashi take zata iya yin amai jin hakan yasa ta kyaleta suka fara ci su biyu har Nana na cewa gaskiya tana jin jiki Zarah mai Magana ka ganta haka Fanan tace ai da sauk’i ma yanzu, Bayan sallar Azahar Haisam yazo ya d’aukesu Nana da kannenta sukae masu rakiya har Mota don basu gaji da kallon Fanan d’in ba gaba d’aya ta tafi da hankalinsu, lokacin da suka isa bakin Motar bayan sun gaida Haisam har ce mata sukae amman dai Aunty zaki dawo ki mana wuni ko Nana tace ma Haisam ai gaskia wannan ba zuwa bane dole ya maido masu ita wuni shi dae murmushi kawae yake Fanan d’ince tace masu zata dawo kafin ta tafi in sha Allah Fatuu dai na tsaye gefe ta jingina da Motar duk ta k’agara su tafi ita in son samu nema su maidata gida kawae, sallama sukai masu harda Fatun suka shige mota suna d’aga masu hannu suka tafi sannan suka koma cikin gidan suka hau yabon Fanan. Daga nan Gra suka wuce gidansu khairat wanda tangamemen gidane had’addan gaske don babanta dan Majalisa ne a Abuja basu cika ma zama anan Katsina ba sunfi zama a Abuja yanzu ma don ana hutu ne,tayi murna sosae da zuwan Fanan haka Fatuu ma hannu biyu ta kar6eta tare da sauran yan gidan har tana tambayar Fanan sis d’insu ce tace mata eh don ranar da ta kai Fanan gidan Hajiya itama bata lura da sadda Fatun ta fito daga Mota ba ta shige gida lokacin idonta na akan Fanan da Masoyinta, lafiyayyan Abinci da abubuwan ci da sha aka jere masu akan c-table da khairat tace a shirya table Fanan tace ba wani ci zasuyi sosae ba don sun ci Abinci ita Fatuu ma cewa tay ta koshi saida khairat tace ya za’ai tazo gidansu first time tace kuma bazata ci komae ba, dole ta d’an tsakuri wasu abubuwan itama Fanan ba wani mai yawa taci ba suna cikin fira Haisam ya kirata su fito su tafi khairat d’in tace ita gaskiya bata yarda ba cewa tay zatai spending whole day shine daga zuwa zasu tafi saida tace mata ai zata dawo kafin ta tafi sannan ta yarda ta rakosu har waje bayan sunyi sallama da yan gidan harda kyautar undies da turare guda ukku masu kyau da tsada taba Fatuu tay mata godiya, suna baro gidansu khairat zagayawa yay dasu gari sai gabda la’asar suka wuce gidan Abbas suna yin parking Abbas da dama jiransu yake ya nufi Haisam yana dariya suka gaisa ya kalli Fanan data fito yace “Our bride u’r highly welcome” amsa mashi tayi da “thank u Abbas” tana dariya ya kai idanunshi kan Fatuu ta d’an yi mashi Murmushi yace “Mom Zarah kwana biyu” ita dae murmushin yak’e kawae take mashi kafin suka nufi ciki suna shiga entry din Falon Feenah ta tar6esu da fara’a tana sanye da doguwar rigar lace hannunta ruk’e da babynta data sake haifa kusan shekara d’aya data wuce, hannu Fanan ta mik’a mata ta amshi babyn da fara’a tace “What’s her name?” tace “Nasreen” Abbas ne yace su shiga ciki mana, jin an fara kiran salla yace bari suje suyi salla su dawo suka juya da Haisam, cikin falon suka nufa bayan sun zauna suka gaisa da juna Fatuu ma ta gaishe da ita ta amsa tana ce mata kwana biyu itama Murmushin tay mata kawae ta mik’e taje ta kawo masu ruwa da lemu da d’an abun ta6awa ta koma ta zauna bayan ta zuba masu lemun a cups, hira sosae suka shiga yi da Fanan dama sun san juna ta waya badai su ta6a ganin juna ba a zahiri ita Feenah ta ta6a ganin pic d’in Fanan wanda suka yi tare da Haisam a wayan Abbas, bada jimawa ba su Abbas suka dawo akan 3 seater suka zauna Feenah ta gaida Haisam ya amsa mata fuskarshi a sake Abbas yana Murmushi yace ma Fanan “Amaryarmu zuwa ba sanarwa mu shirya maki sosae” tana dariya tace “it was a suprise” jinjina kai yay yace mata anzo lafiya ya karatu ta amsa mashi da Alhamdulillah, kallon Fatuu yay da tay shiru gefen Fanan da yake kan sofa 2 seater suka zauna yace “Mom Zarah ya karatu?” a sanyaye tace mashi lpy lou yace “an kusa graduation ko?” kai ta d’aga mashi alamar eh yace to Allah ya bada sa’a ta amsa da Amin ta tambayeshi ina Abdul yace yana tahfiz daga haka ya juya kan Fanan suka cigaba da hirar india ita kuma ta d’an kwantar da kanta tay shiru sai kace bata a falon can Abbas yace “Wai Mom Zarah kodae baki Lafiya ne?” d’ago kanta tay ta kalleshi kafin ta bashi amsa Feenah ta rigata cewa”Wllh Dear nima am about to ask her shirun nata yay yawa” shiru tay tana binsu da ido ta rasa mi zata ce Fanan tace masu ai bata lafiya ne almost a week yanzu ne ta d’an samu sauk’i har suka fito tare, jinjina kai sukae gaba d’aya sukai mata Allah ya sawake ta amsa masu da Amin suka cigaba da firarsu ita kuma ta koma ta jingina da kujera tana binsu da ido, tun bayan da Abbas yay Maganar jefi jefi yake juyawa ya kalleta duk in ya kalleta kuma sai su had’a ido hakan yasa tasha jinin jikinta sai yan kame kame take, wani d’an guntun Murmushi yay bayan sun k’ara had’a ido da ita yace “Mom Zarah ko ki shiga ciki ki kwanta” kafin ta bashi amsa Feenah tace “amman dear yamma yayi fa kuma ba’ason bacci irin wannan time en ba kaman ita da bata lafiya,
“ai dama ba ina nufin tay bacci ba ta d’an hutu looks like she isn’t comfortable here” kai Feenah ta d’aga tace “amman fa bata ci komae ba just drink tasha, kallon Fatuu yay still da Murmushi a fuskarshi yace ” Mom Zarah ana ciwo ba cin abinci ai baza’a warke da wuri ba kuwa, ki daure kici Abinci” shiru tay tana kallonshi kafin ta kai kallon kan Haisam da tunda Abbas ya fara mata Magana yake kallonta, a hankali ta sunkuyar da kanta jin bugun da kirjinta ya fara ga kwalla dake neman zubo mata Abbas yace in bata son ci taje kawae aikuwa da sauri ta mik’e ba tare data yadda sun had’a ido da kowa ba ta nufi Bedroom d’in Abdul ta shige, Abbas da ya bita da ido ya juyo ya kalli Haisam yace “miyake damunta ne?” yana daga kishingid’en da yake ya fad’i mashi matsalar Aljanu ne da mamaki Abbas yace “Aljanu kuma, dama Mom Zarah nada Aljanu?” kai ya d’aga mashi kafin yace mashi shima bai san tana dasu ba sai yanzu, shiru Abbas yay kaman mai nazarin wani abu cikin ranshi ya ayyana dis is more like a heartbreak ba Aljanu ba,can ya tambayi Haisam waye yace tana da Aljanun, farko shiru ya d’an yi mashi sai kuma yace mashi a wurin Hajiya yaji daga haka bai k’ara cewa komai ba shima Abbas d’in bai k’ara tambayarshi wani abun ba, misalin karfe shidda mai d’aukko Abdul ya kawo shi cike da farinciki ya ruga ya haye Haisam yana fad’in “Baba Zakee ashe kazo” kai Haisam ya d’aga mashi yace “My Boy ka girma fa yanzu kana haye babanka haka zaka karya shi” kyalkyacewa yay da dariya Fanan ta bisu da kallo tana murmushi don tana son yara ba kamar yadda ta gansu haka yanzu sun burgeta shiyasa burinta suyi aure itama ta haihu, Abbas ne yace mashi ga Momy d’inshi nan tazo yaje ya gaishe da ita da sauri yace “Aunty Zarah?” girgiza mashi kai yay ya nuna mashi Fanan dake mashi dariya ya k’ura mata ido yana kallonta can ya juya ya kalli Abbas yace “ba Aunty Zarah ce Mommy na ba?” Abbas dake Murmushi yace “yeah ita Mom d’in Zakee ce ita kuma wannan Mom d’inka ce kai kadae kaman yadda Zakee yake babanka” da mamaki yace “to Matarshi ce?” Abbas yace “eh itace zai aura” bin ta yay da kallo ganin haka yasa Abbas yace yaje ya gaidata ya saukko daga jikin Haisam ya nufi wurinta yana zuwa ta rungume shi tana tambayarshi ya Makaranta yace mata lpy lou tace yana dai kokari ko yace mata eh duk bai wani saki jiki ba, can ya janye jikinshi ya koma wurin Abbas yace “Dad ina Mom Zarah ba’a zo da ita ba?”
Yace “Tana d’akin ka bata jin dad’i ne” zaro ido yay yace “bata lafiya” kai Abbas ya d’aga mashi aikuwa da gudu ya nufi d’akin nashi suka bishi da ido da d’an Murmushi kan fuskokinsu, tun a bakin kopa ya fara kiran sunanta yana shiga ya ganta ta dukunkune saman gado baiwar Allah da k’yar ta samu bacci ya dauketa,hayewa yay saman gadon gefenta ya fara bubbuga jikinta yana kiran sunanta, a hankali ta bud’e idonta da sukai ja ta kalleshi tana ganin shine ta yunk’ura ta tashi zaune da d’an Murmushin da iyakarshi lips d’inta tace mashi ya dawo bai bata amsa ba ya kama hannuwanta da yar damuwa yace “Aunty Zarah wai baki Lafiya” shiru ta d’anyi tana kallonshi shima kallonta yake ba komae take tunawa ba sai farkon kawota gidan lokacin da sukai game dashi cike da nishadi da kuma sauran lokutta, ita yanzu shikenan haka zatai ta zama da damuwa ta ayyana a ranta kawae sai ta fashe da kuka, waro ido Abdul yay a rud’e yace “Aunty Zarah kuka kike” shiru bata ce mashi komae ba ta rufe bakinta da tafin hannunta, kokarin sauka daga kan gadon ya fara yi yana fad’in “bari inje in gayo ma su Dad baki lafiya kina kuka azo akai ki Hospital” da sauri ta kamo hannunshi tana girgiza mashi kai yace “kar naje na fad’i masu?” d’aga mashi kai tay alamar eh yace “to ki daina kukan don Allah” yadda yay Maganar kaman shima zai sa kukan, a hankali tace to ta daina ya kai hannu yana goge mata hawayen, da k’yar ta samu hawayen suka tsaya cikin muryar wanda yay kuka tace mashi ya Makarantar yace lafiya lou tace yana dae kokari ko yace eh sosae,shiru sukai na d’an lokaci can yace “Aunty Zarah yau bazamuyi game ba tunda baki lafiya ko?” kai ta daga mashi alamar eh yace “Allah ya baki lafiya sai mu yi” a hankali tace Amin suna cikin haka sai ga Abbas ya shigo d’akin Abdul na jin sallamarshi ya sauka daga gadon da sauri ya nufe shi yana fad’in “Daddy Aunty Zarah tayi kuka a kaita Asibiti” jinjina mashi kai yay ya nufi cikin d’akin ya tsaya gabanta yana kallonta kanta na kasa tunda taji Abdul yace tayi kuka, slowly Abbas ya kira sunanta ta amsa ba tare data d’ago ba hakan yasa yace ta kalleshi kaman bazata d’ago ba can ta d’ago da jajayen idanunta ta kalleshi duk ta kame kanta,
“In akwae abunda ke damunki banda ciwon da akace kar kiji komae ki fad’a man” da sauri ta girgiza mashi kai tama kasa yi mashi Magana, d’an Murmushi yay yace “to miyasa kike kuka?” murya na rawa tace “d…da dama jikin nawane bana jin dad’inshi…” shiru ya d’anyi kafin yace “an kai ki Asibiti ne?”
“A’a, amman Aunty Fanan tayi man Allurar zazza6i ta kwana ukku nama samu sauki sosae yanzu”
“Ko mu kaiki Asibiti to tunda kince jikin naki har yanzu bai maki dad’i” taji ya fad’a, da sauri ta girgiza mashi kai tace “a…ai gwaggo tace ciwon bana Asibiti bane tasa anyo man Addu’a a ruwan zam zam ina sha” shiru yay yana cigaba da kallonta hakan yasa ta sunkuyar da kanta don gabanta wani irin bugu yake mata ita tsoronta wai kar ya gano mike damunta ya fita ya fad’i masu, sigh yay yace mata Allah ya bata lafiya ta amsa da Amin ya kalli Abdul yace ya cire Uniform d’in jikinshi yasa kaya yazo zasu je Masallaci ya amsa da to, wani sanyi taji bayan Abbas d’in ya fita Abdul ya nufi wardrobe d’in kayanshi don ya canja kaya bayan ya d’aukko wanda zai sa ya juya yace ma Fatuu wai ta juya zaisa kaya bata san lokacin data saki dariyar da rabon da tayi irinta ta manta, kifa fuskarta tay jikin pillow tace bata ganinshi yasa ya amsa da to, bayan ya fita saiga Feenah ta shigo da Murmushi ta nufi Fatun tana tambayarta ya karfin jikin tace mata da sauk’i tace to ta tashi tayi salla ta amsa da to ta mik’e ta nufi toilet itama ta fice dama Fanan ta kai d’akinta tayi salla shine tazo wurin Fatun, suna dawowa daga sallar Haisam yace ma Abdul yaje ya kira Zarah zasu tafi, tare suka fito dashi ya ruk’o hannunta idonsu akanta hakan yasa duk ta dabarbarce ta sadda kanta k’asa har ta k’arasa cikin Falon ta zauna kusa da Fanan, Abbas ne yace ko zasu tafi sai taci Abinci sannan, ba yadda ta iya dole ta d’an ci Abincin da Feenah ta zuba mata, har bakin Mota suka yo masu rakiya Feenah tace ma Fanan in sha Allahu kafin ta tafi tana nan zuwa dan da suna hira tace mata upper Monday zata tafi tace to tana jiranta, sallama suka yi masu suka k’ara yi ma Fatuu Allah ya sawak’e Abdul ya d’aga mata hannu yana mata bye bye itama ta d’an mashi kafin ta bud’e Mota ta shige suma duk suka shiga yaja suka bar gidan………..
.
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.