Hausa novels

Matar Damisa Book 1 Chapter 37 Complete Novel

Matar Damisa Book 1 Complete Novel Document

*typing📲*

🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)

*written* *and* *story* *by*
*Asma’u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)

*WhatsApp me 09065443871*

*BOOK ONE*⬇️
*99 to 100*

*👉 END 👉 END 👉 ENDED OF BOOK ONE*

*DOMIN SAMUN LITTAFI NA BIYU KU HANZARTA BIYAN KUƊIN KU A FARASHI MAI SAUƘI…*

*MATAR DAMUSAA BOOK 2 PAY ONLY 200👌👇👇👇*

*ASMA’U MUHAMMAD AUWAL,*
*9065443871, OPAY BANK.*

*OR*

*ASMA’U MUHAMMAD AUWAL,*
*2267236949, ZENITH BANK*

*SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER*
👇👇👇
*09065443871*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

 

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

𝐔𝐩! 𝐔𝐩!! 𝐔𝐩!!! 𝐇𝐮𝐫𝐫𝐲💃💃💃

𝐒𝐀𝐅𝐍𝐀 𝐆𝐑𝐀𝐏𝐇𝐈𝐂𝐒 𝐃𝐄𝐒𝐈𝐆𝐍.
ᴴᴼᴹᴱ ᴼᶠ ᴳᴿᴬᴾᴴᴵᶜ ᴰᴱˢᴵᴳᴺ
ᵂᴱ ᴰᴱˢᴵᴳᴺ ᴬᴸᴸ ᴷᴵᴺᴰ ᴼᶠ ᴰᴱˢᴵᴳᴺ ˢᵁᶜᴴ ᴬˢ:
𝐿𝑂𝐺𝑂* 𝑃𝑂𝑆𝑇𝐸𝑅* 𝐵𝐴𝑁𝑁𝐸𝑅* 3𝐷 𝑀𝑂𝐶𝐾 𝑈𝑃 𝐿𝑂𝐺𝑂* 𝐹𝐿𝑌𝐸𝑅* 𝑆𝑇𝐼𝐶𝐾𝐸𝑅* 𝑃𝑅𝑂𝐷𝑈𝐶𝑇 𝑆𝑇𝐼𝐶𝐾𝐸𝑅* 𝐼.𝑉 𝐶𝐴𝑅𝐷* 𝐼.𝑉 𝑉𝐼𝐷𝐸𝑂* 𝐵𝐼𝑅𝑇𝐻𝐷𝐴𝑌 𝑉𝐼𝐷𝐸𝑂 𝐹𝐿𝑌𝐸𝑅* 𝑃𝐻𝑂𝑇𝑂 𝐹𝑅𝐴𝑀𝐸* 𝑅𝐸𝑀𝑂𝑉𝐸 𝐵𝐴𝐶𝐾𝐺𝑅𝑂𝑈𝑁𝐷* 𝑃𝑅𝑂𝐹𝐸𝑆𝑆𝐼𝑂𝑁𝐴𝐿 𝐼.𝑉 𝐶𝐴𝑅𝐷* 𝑆𝐴𝑉𝐸 𝑇𝐻𝐸 𝐷𝐴𝑇𝐸* 𝐸𝑋𝑃𝐿𝐴𝐼𝑁𝐸𝑅 𝑉𝐼𝐷𝐸𝑂* 𝐿𝑌𝑅𝐼𝐶𝑆 𝑉𝐼𝐷𝐸𝑂 𝐴𝑁𝐷 𝑀𝑂𝑅𝐸…
𝗣𝗟𝗘𝗔𝗦𝗘 𝗖𝗔𝗡𝗧𝗔𝗖𝗧 👉 08148318396 𝗦𝗔𝗙𝗡𝗔 𝗚𝗥𝗔𝗣𝗛𝗜𝗖𝗦.

🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀

Adity ganin yanda Junaid ya rungumi ƴan mata a jikinsa yasa ta fusata cikin zafin nama ta tashi sama ta dirƙo a gaban Junaid, hannu ta kai musu zata cabki wuyan su Angel da Ayush kenam Junaid yayi saurin riƙe hannayenta biyu ya ɗago da dara-daran idanuwansa yana kallonta cikin fushi, girgiza mata kai yayi sannan ya tureta gefe,
tana huci tace “waɗannan karuwanka ne suma ko? toh ka fito fili ka zaɓi wacce kake so a cikin mu, bazan yadda da irin cin amanar nan ba da kuma yaudara, kayi mun alƙawarin zaka aure ni yanzu kuma sai ganin ƴanmata kala-kala nake kuma duk naka, yau ba wacce zan bari da lafiyarta…”
haka ta gama surutan ta da yaren china,
Mommy kuwa kallonta kawai take ita kallon mahaukaciya take mata, ga maganar ta sauri-sauri..

Duk maganganun da Adity tayi Junaid yana sauraronta,
Angel ce ta ɗago tana kallonsa kafin ta maida idonta kan Adity tana faɗin “my man baka so zaman lafiya ba tinda acikin ƴanmatanka har da china, mezakayi da china kuwa?…”
kafin Angel ta rufe baki Adity ta tafo da gudu ta girbe mata ƙafa sai yaraff ta faɗi ƙasi,
cize leɓɓenta tayi da shirin yin mugunta wani irin murɗewa Angel tayi ta miƙe tsaye tareda cankin Adity a cikinta har sai data faɗi ƙasi,

Junaid tsabar baƙin ciki bai tanka musu ba sai ma ɗaukar Ayush da yayi ya haura upstairs da ita, zaije ya kwantar da ita saboda firgicin da ta shiga yasa tayi bacci a tsaye..

Adity da Angel faɗane ya kaure a tsakaninsu suna naushin juna kamar wasu maza,
har zuwa yanzu ba wacce taci galaba akan ɗaya, haka sukayi kaca-kaca da parlour, da sauri Adity ta ɗauki glass bottle ta wurga wa Angel! cikin salo da ƙwarewa wajen iya faɗa, Angel ganin glass bottle yana tafo wa saitin goshinta da sauri ta durƙusa ƙasi ya wuce ta saman kayinta cikin rashin sa’a kuwa bottle ya daki tsakiyar plasman nan take film ɗin da ake showing ya ɗauke gaba ɗaya..

Mommy ce tazo tana rabasu tareda faɗin “meyasa kuke hakane kamar wasu dabbobi kuna faɗa…”
wani irin juyi Adity tayi ta kaiwa Angel naushi cikin zafin nama nan ma Angel ta sake kaucewa gefe sai hannun Adaty ya sauƙa akan leɓɓen bakin Mommy,
daiden lokacin da Junaid yake sauƙowa down ƙwayar idonsa akan su….

Mommy da sauri ta dafe bakinta da hannu tana faɗin “innalillahi wa inna’ilahi raju’un, sun cire mun haƙwara nashiga uku..”
kafin a ankara kuwa jini har ya ɓata hannun mommy, da sauri Angel ta riƙe mommy tana cewa “mommy dan Allah kiyi haƙuri, mun shiga uku! kinga kin fasa mata baki ko? ke a dole ƴar china tsinanniya kawai..”
Jin zagin da Angel tayi mata ne ya ƙara fusata ta zata yo kan Angel, Junaid ya cabki kunkumin ta da hannu ɗaya ya ɗagata sannan ya nufi ɗakinta da ita,

Angel binsu tayi da kallo cikin ɓacin rai kafin ta zauna kusa da mommy wacce har zuwa yanzu tana kame da bakinta, lips ɗinta ne ya fashe, Angel tace “mom please am really sorry, muje na wanke miki bakin..”
riƙo hannun mom tayi sannan suka nufi ɗakin mommy, ita dai mom tayi tsumu ta kasa cewa komai,

(daman ance ɗan kuka mai jawa uwarsa zagi, to wannan kam mai jawa uwarsa duka ne🤣🤣🤣)..

Bayan Junaid ya shige da Adity ɗaki dirar da ita yayi a saman gado, daman ya fito da dorinarsa mai baki uku,
cikin ɓacin rai kafin Adity ta ankara har ya soma zabga mata dorina a jiki,
tana mutsil-mutsil zata tashi ya hankaɗata ƙasi yana wara mata dorina ta ko ina,
ƙin kuka tayi saboda kar mutanen gidan su jiyo ta saboda kar su raina ta,
ganin Junaid yana shirin faffasa mata jiki yasa ta fara ihu ihu take na gaske tana neman agaji,
a gigice ta tashi ta buɗe ƙofar ɗakin ta nufi parlour tana ihu tana sossosa jikinta, nan ma biyota yayi shima yana faɗin “tinda kin raina ni toh yau zan fitar da wannan raini..”
girbe mata ƙafa yayi ta faɗi yaraf a ƙasi ya cigaba da zabga mata wannan dorinar,

kafin kace mai Rumana ta fito da gudu tsayawa tayi tana kwashewa da dariya,
saiga mommy da Angel suma sun fito har bakin mommy ya kumbura suntum,
daga can saman upstairs kuma Ayush ce itama ta sauƙo a gigice jin ihun da ake a cikin gidan domin ihun ne ya tasheta daga baccin da take,

Mommy ce tayo kan Junaid ta riƙe hannunsa tana faɗin “ya isa haka Junaid kar kaji mata rauni, ai duk abunda ya faru laifin ka ne kai ka jawo wa kanka, meyasa zaka zo kana dukanta..”

Junaid cikin fushi ya kai mata canka da ƙafarsa yana cewa “i will teach you a lesson, useless girl..”
ita kuwa tana daga kwance sai ihu take ta zabgawa duk da yabar dukan natan,

ita kuma Rumana dariya take sosai taƙi dakatar wa, a fusace Junaid ya kalli gurin da take a tsaye ya ciro wayarsa daga aljihu saida ya saita goshinta kafin ya wurga mata wayarsa akan goshi, kamar wacce aka zare mata rai tayi tsitt tareda dafe goshinta kamar zatayi kuka tsabar taji zafin bugun da ya yi mata a goshi, abunka da farar fata wato baturiya har gurin yayi jawurr kamar jini zai fita,
wayarsa kuwa mai ƙirar iphone 15 pro faɗuwa tayi a ƙasi ta dagargaje…

ransa a ɓace yake nuna ta da ɗan yatsarsa yana faɗin “zan kashe ki idan na sake jin dariyarki…”

Juyowa yayi yana kallon Angel a fusace, ai kuwa bata jira wani-wani ba da gudun gaske ta koma ɗakin mommy ta danna sakata, saboda gudun kar ya yo kanta…

kawar da kansa yayi yana kallon Ayush tana tsaye a tsakiyar benin bata ƙarasa sauƙowa ba,
ganin irin kallon da yake mata ne yasa ta kawar da kanta gefe, itama da gudu ta koma ɗakinta…

Adity ce ta tashi da gudun gaske ta nufi ɗakinta tana faɗin “tiger bai warke ba wallahi, mahaukaci ne..” ta danna sakata a ɗakinta..
da sauri zai bita ɗakin mommy tayi saurin riƙe hannunsa tana girgiza masa kai, ga kuma kumburarren baki😹,
itama Rumana ɗakinta ta wuce da ɓacin rai tana riƙe da goshinta,
mommy tace “toh daga yanzu zaka fara ganin alamar Auren mata uku ba wasa bane, gashi suna son saka maka hawan jini…”
kafin mommy ta ƙarasa maganar ya katseta da cewa “impossible ba macen da zata ɗora mun jinya, kuma wallahi a yau zasu tafi..”

Mommy tace “a’a ba yanda zasu je a yau har sai an kammala hidimar nan, kuma muje mu ɗakinka inaso yin magana da kai mai muhimmanci, kafin baƙi su fara hallaruwa zuwa anjuma kaɗan…”

Mommy jan hannun Junaid tayi suka nufi upstairs acan ɗakin Junaid zasu tattauna….

bayan sun shiga mommy zaunar dashi tayi a bakin gado itama ta zauna tana fuskantarsa, tace “Junaid dan Allah inaso ka nutsu kabar duk wannan haukar ka hangi abunda zai biyo baya, nasan kasan ciwon kanka kuma ka mallaki hankalin kan ka, kasan mai yake maka ciwo, waɗannan ƴanmatan daka tarasu ba wayewa bane sai tarin tashin hankali, kai kan ka hankalinka ba’a kwance yake ba nima kuma haka, dan Allah na roƙe ƙa Junaid kamun wata alfarma ɗaya…”

juyowa Junaid yayi yana kallon mommy sannan yace “ina jinki mom..”

tace “na tsara wani abu ne, inason wannan walimar da za’ayi anjuma ya tafi tareda baikon ka, ka zaɓi mace ɗaya acikin ƴanmatan ka ayi muku baiko da ita, sauran kuma duk ka watsar amma banda Ayush tinda ita ta rigada ta zamo naka, idan kuma ita ka zaɓa a matsayin matarka zanfi kowa jin daɗin hakan sosai amma bazanyi maka dole ba, ka zaɓa da kanka tin yanzu saboda a gaban mutanen za’ayi muku baikon…”

Junaid dogon numfashi yaja yana karkaɗa ƙafafunsa ya tsayar da eyes ɗinsa a guri guda kamar mai yin tunanin wani abu, yace “Mom ki ban lokaci zanyi tunani akai…”

Girgiza kai mommy tayi tana faɗin “babu wani lokacin da muke dashi a halin yanzu, ka duba fa yanzu ƙarfe 12 rana tayi kafin kuyi shirye-shiryen ku har lokaci zai ƙure, kuma dole sai anyi zaman shirya wacce za’ayi baikon da ita, bamu da lokaci kai ai kasan wacce tafi kwanciya maka a rai….”

Mommy dai har cikin zuciyarta tana so taji ya ambaci sunan Ayush, haka take binshi da kallo tana son jin sunan da zai furta..

yana motsa baki a hankali ya furta cewa “nifa mace biyu zan zaɓa, Adity da Yushert inaso ayi mun baikonsu a tare….”

turɓune fuska Mommy tayi sannan tace “Adity wacce ka gama dukanta yanzu?..”

yace “eah mom saboda a rayuwata inaso na ringa dukan mutum da zaran yamun laifi, toh kinga Adity a koda yaushe zan iya mata dukan fitar rai ita kuma Yushert bazan iya dukanta ba saboda tanada rauni kuma ina tausayinta sosai…”

Mommy jijjiga kai tayi tana faɗin “a’a wallahi baka tausayin Ayush, inda kana tausayinta da bazaka haɗata da wannan ƴar china ba, kawai dai kace kuna son zaluntarta ne..”

yamutsa fuska yayi sannan yace “to mom ya kike so nayi, ai ba’a guri ɗaya zan ajiyesu ba…”
Mommy ta katse shi da cewa “nidai ban yadda da wannan haɗin ba, idan Ayush ka zaɓa toh ita kadai ce, idan kuma Adity ce to kaje can ka Aureta ita kaɗai amma bazaiyu ka haɗa mun Ayush da wata ba…”

juyowa yayi yana kallon Mommy da dara-daran eyes ɗinsa yace “to kuwa idan na Auri Yushert zata sha duka ne a gurina, domin bazan juri raini ba, tana mun laifi zan ɗau hukunci yanda nayi wa Adity dukan na toh haka itama saina farfasa mata jiki, tinda nace zan haɗa ta da wacce ta saba da dukana kin ƙi yadda toh shikenam idan kin yarda da abunda nace zan Auri Yushert idan kuma baki yarda ba, zan haɗasu duk su biyun na Aura domin bazan taɓa barin wani ya Auri Yushert ba saboda ita ce first kis…..” bai ƙarasa maganar ba ya dakatar tareda juyar da kansa gefe, saboda baya son furta wani abu domin yana matuƙar jin kunyar mom ɗinsa..

Mommy ce ta ƙarasa masa da cewa “itace mace ta farko daka sumbata? bazaka iya barin ta a wani ba? hmmm! nasan haka kake son cewa…”

dasauri Junaid ya juyo yana kallonta cike da mamaki, sosa sumar kansa yayi yace “mom baki ce kin amince da batuna ba, shin zaki Aura mun Yushert ita kaɗai da zarar tamun laifi na hukuntata da duka ko kuma zan haɗata da Adity inyaso koda tayi mun laifi zanje na hukunta Adity a madadinta ne kodai mekika ce?….”

Mommy kallonsa tayi tareda jan numfashi tace “na amince ka Auri Ayush ita kaɗai inyaso idan tayi maka laifi saika hukuntata, gwara kaiɗin ka zalunce ta akan Adity, nasan wata rana Allah zai saka mata kuma zakayi danasani…”

“please mom kefa kika ce babu lokaci, tinda kin yarda da yarjejeniyar mu shikenam aje a fara shiryata kafin lokacin da za’ayi mana baikon ya gabato, ni yanzu zan fara shiri ne…”
ya miƙe tsaye zai nufi toilet, ya kuma cewa “mom a ƙira masu girke-girke da kuma waɗanda zasu gyara parlour nan saboda naga duk sunyi kaca kaca da wajen,
Sannan kuma ƴan uwanki suna kan hanya ɗazu nayi waya dasu,
my phone yana can parlour kije ki zare mun sim ɗin na sannan kisa a kawo mun wata wayar na 5.5million….”

Mommy ce itama ta miƙe tsaye ta kama kunkumi tace “Ashe Babana dole nayi maka biyayya akan abunda kace mana, saboda kana sakaye da sunan mahaifina shine zaka wani bani order?..”
ta ƙarasa maganar tana harararsa..

juyowa yayi yana murmushi yazo gabanta ya haɗe tafukan hannayensa biyu sannan yace “please my lovely mom banida time ne yanzu abokai na zasu fara zuwa, help me mom…”

Mommy dariya ne ya kuɓuce mata ganin yanda yayi kalar tausayi tace “shikenam my son je kayi wankan ka, zansa a kawo wedding gown wa Ayush..”

Junaid hannu yakai saitin lips d’in mom yana fad’in “mom kinji rauni da yawa fa, gashi har ya kumbura waje, kije Kisha magani saboda wajen ya sa6e…”

Murmushi tayi sannan tace “bazan sha magani yanzu ba saboda yau na tashi da Azumi..”

Zaro eyes yayi waje tareda fad’in “Azumin na meye ne?..”

tace “zan godewa ubangiji na akan samun lafiyarka mana, amma inadai ba kid’e² zakuyi ba? domin banason harkar shaiɗanci…”

yamutsa fuska yayi sannan yace “mom kin dai san manya² mutane ne zasu halacci taron nan ko? kuma har da abokan mahaifina da kuma shuwagabanin mu na sojoji, yaushe za’ayi party kuma, just iya walima ne aci asha a godewa ubangiji, toh tinda kin kawo maganar baiko sai a haɗa ayi awajen taron…”

Mommy murmushi tayi tareda jan kuncin Junaid tace “Masha Allah my son, Allah ya maka albarka..”

shigewa cikin toilet yayi tareda faɗin “thanks nima kisa a kawo mun suit yanzun nan kafin na fito a wanka, na manta ban tanadar dashi ba, ni kuma bazan iya saka old ba…”
yana cikin toilet ya ƙarasa maganar,
Mommy da murmushi a fuskarta tabar ɗakin…

☆☆☆☆☆

Misalin ƙarfe 2 Doctor Hasheem yana zaune a ɗaya daga cikin kujerun falonsu yanata danna wayarsa, sai ga Laylah ta fito sanye da doguwar riga maroon colour na kanti har jan ƙasa take, mai dogon hannu,
rigar ya ɗameta ta sama breast cup ɗinnan ya zaunu ga daman dirarriya ce gaba ɗaya ta cike rigar, daga kunkuminta kuwa rigar ta baje sosai, taci ɗaurin ɗan ƙwalinta ta fitar da gashin ta tsakiyar ƙwalin, ta ɗauko gyale ɗan ƙarami kalan kayan mai tsantsi ta yafa a kafaɗarta, ɗan kunnen da sarƙar wuya tareda warwaron hannunta duk sunyi colour da kayan jikinta,
ga ta hau takalmi mai tudu sosai shima kalar kayan, ta lanƙayo ɗan ƙaramin handbag ɗinta, ɗayan hannun kuma tana riƙe da ƙatuwar infinix ɗinta, tana taku a hankali ta shugo falon tana ƙamshin turare gata sha makeup domin zuwa tayi akayi mata na kuɗi…

Doctor Hasheem kallonta yayi tareda miƙewa tsaye yana faɗin “wow my little sister kinsha kyau sosai, fashion girl ƴar wanka…”

murmushi tayi sannan tace “my bros ka tayani da Addu’a Allah yasa idan munje walimar nan Ogah Junaid ya faɗa cikin soyayyata, tinda har ya warke nasan zan burgeshi..”

shima Doctor Hasheem murmushi yayi sannan yace “toh Allah yasa..”
in short answer ya bata, ya kuma cewa “toh mu tafi ko kar lokaci ya ƙure mana, ina kina tareda gate pass ɗinki..”

ɗan turo baki tayi tace “Ina dai a kai ɗaya aka bawa, sai dai na maƙale a bayanka..”

yace “ok shikenam muje mu koh..”
har sun ɗan fara tafiya Laylah ta tsaya tana faɗin “Big bros Maimoon fa? yakamata kaje ka dubo ta kafin mu tafi karta ji mu shuru..”

jim yayi kaɗan kafin yace “ok wait for me..”
ya nufi can cikin gidan wanda yakeda rata sosai da compound ɗinsu, key yasa ya buɗe ya danna kansa ciki yana sallama,
Maimoon tana zaune akan katifa ganin shugowar Doctor Hasheem yasa ta kawar da kanta gefe, kwata-kwata ma bata son ganinsa,
zama yayi a bakin katifar tareda cewa “Maimoon har yanzu fushi kike dani? daman soyayya zata iya juyewa ƙiyayya? daman ba ƙaunata kike ba ashe….”

kafin ya ƙarasa maganar ta katse shi da cewa “please malam inason ganin mahaifiyata, na fahimce ka kai baka san ciwon rashin iyaye a kusa ba, shiyasa ka rabani dasu ka kawo ni nan saboda rashin imani irin taka…”

Ajiyar zuciya Hasheem yayi sannan ya ɗago yana kallon Maimoon cike da mamaki yana maganar zuci “wai yaushe yarinyar nan ta canza haka ne? duk irin son da take mun amma yau itace take gaya mun maganganu har da zagi?…”

katse masa tunani tayi da cewa “malam Hasheem kaban wayata na ƙira iyaye na su zo su fidda ni daga cikin wannan akurkin ɗakin kajin ku….”

ƙayataccen murmushi yayi yana kallon kyakykyawar fuskarta sannan yace “baza ki bar gidan nan ba har saikin warke gaba ɗaya…”

a fusace ta jefa masa pillow tana faɗin “ƙarya kake wallahi mungu kawai Azzalumi, ai ɓoyeni dakayi bashi zai sa asirinka ya rufu ba, wallahi saina bazawa duniya cewa kai ɗan ta’adda ne mai yiwa mata fyaɗe…” ta ƙarasa maganar tareda fashewa da matsanancin kuka.

shi kuwa girgiza kai yayi sannan ya tashi yabar ɗakin tareda murɗa key ya rufeta, daman already an kawo mata abinci da kuma ruwan sha..

bazai iya juran kalaman Maimoon ba, tabbas yasan yanzu ta tsane shi shi kuwa har yanzu tana cikin zuciyarsa, yana son maimoon sosai abunda ya faru kawai tsautsayi ne da ƙaddara, kuma tausayinta yake ji..

yana zuwa harabar gidan ya tarar da Laylah tana tsaye a jikin motar,
shigewa sukayi ya tada motar suka tafi….
(to sai mun haɗu a gidansu Junaidu…)

shima Doctor Hasheem ba ƙaramin kyau yayi ba, yasha gizna sky blue da hularsa shima sky blue, ga kuma takalminsa mai sawu ciki shima kalar kayan, sai ƙamshin turare yake ga kuma ƙamshin gizna shima yana bada nashi ƙamshin, domin sabin kayane bai taɓa saka su ba..

☆☆☆☆☆☆

mutane har sun fara hallaruwa, sai shugowa ake da wasu manya-manyan motoci maka-maka, zafafan mutane ne suke fitowa daga cikin motocin masu kuɗin gaske, da ƴanmata kala-kala,
ƴan uwa daga wasu garuruwa har sun ƙaraso wasu daga ƙasar waje,
abun baƙin ciki shine babu ƴan uwan mahaifin Junaid ko ɗaya, abun yana masa ciwo sosai a ransa, hakan yasa bai damu da ƴan uwan Mommy ba, saboda kullum mitarsu akan ba’a san asalin mahaifin Junaid ba,
kuma ba’a son ransu Alhaji Junaidu ya haɗa Auren ɗiyarsa Doctor Fatima da kuma mahaifin Junaid ba…

Junaid yana tsaye a gaban madubi yana sanye da gajeran wando da farar singlet ya gama kimtsa jikinsa tsab sai ƙamshin turare yake, ya gyara sumar kayinsa ya kwanta luf-luf har waran kafaɗarsa..
yanzu iya kaya kawai zai saka shima an kawo masa yana ajiye akan gado,

yana tsaye yaji an zagayo da hannaye ta gabansa, ta cikin madubi ya ga Angel ce ta kwantar da kanta a bayansa tana kuka,
riƙo hannunta yayi ya zagayo da ita ta gabansa ya riƙe haɓarta sannan ya ɗago da fuskarta sama suna kallon juna yace “meyasa kike kuka?..”

murya na rawa tace “Mommy ta sanar mun baikon da za’a maka kai da Ayushert, ta gaya mun komai..”

rungumarta yayi sosai a jikinsa yace “sorry my Angel, nasan zakiji wani abu a ranki koh?..”

ɗagowa tayi tana kallonsa tace “Mommy ta fahimtar dani komai, saboda haka ba abunda naji a raina saima ƙarin farin ciki, Ayushert tana masifar ƙaunarka kuma kaima nasan kana sonta, ni daman bansa a raina cewa zan Aureka ba, ni dai abunda na sani shine ina sonka…”

murmushi yayi sannan yace “ina ji da ke my Angel, and i will never forget you in my life, we will stay together forever…”

Kuka ne yake shirin kuɓuce mata ta ƙwantar da kanta saman ƙirjinsa,
yace “abun kunya ne naga soja tana kuka…”

kwashewa tayi da dariya tana dukan faffaɗar ƙirjinsa tareda faɗin “ai ɓangaren aiki da ban, ɓangaren soyayya ma daban,
my man! ina tayaka murna sosai, Mommy ta ce da zarar anyi baiko za’a yanke ranar bikinku, amma shawarar da zan baka shine ka daina hurting heart ɗin Ayushert saboda naga macece mai haƙuri da hankali, kuma she is a younger lady tayi dai dai da rayuwarka kuma kunyi matuƙar dace wa da juna, amma kaje ka ƙwaso waɗancan tsofin ina zaka kaisu marasa ɗa’a da tarbiya, daman ni babu maganar Aure a bookless ɗina….”

ɗago haɓarta yayi yana faɗin “daman yaudarata kike yi?..”
tana dariya tace “see this man wai yaudara…”
suka haɗe goshinsu guri ɗaya suna dariya,

Angel ta ture shi tana faɗin “lokaci fa zai ƙure naga mutane har sun taru, ta nufi gaban gadonsa ta ɗauko kayansa,

daman ita ta kammala shirin ta, tana sanye da doguwar riga Abaya milk mai duwatsu a jere daga sama har ƙasa ta gaban rigar, tayi rolling gyalen rigar a kayinta sai tudun sumar gashinta da ya fito kamar wacce tayi acuci maza sakamakon tuƙeshi data yi,
ƙafarta tana sanye da farin thorns mai ɗan tudu, Angel ta fito tayi kyau sosai tayi shigarta na musulmai, kamar balarabiya haka ta fito ga ta farinta ɗan dai dai ruwan tarwaɗa domin bata kai sauran haske ba, ko rabin Ayush bata kai haske ba balle su Aunty baturiya da Aunty china, daman Angel asalinta ƴar misrah ce amma kuma iyayenta ba musulmai bane, aikin soja ya kaita ƙasar California, yanda iyayen Ayush suke, kuma Angel ta tafo da tarin bayanai akan su…

a gurguje Angel ta taya Junaid ya saka kayansa, suit ne masu kyan gaske baƙaƙe da kuma farar riga ta ciki mai dogon hannu, ta ɗaura masa wannan abun wuyan nan na ado (na dai manta sunansa🙄).

ya saka takalminsa baƙi na kayan, ga kayan yanda suka kama jikinsa ya fito yayi kyau sosai, sumar kansa har wani sheƙi yake ya yi laushi yanda kasan gashin jarirai har kafaɗarsa,
fuskar nan yayi fari sol,
Angel ce ta sanya masa agogon hannu sannan ta ƙara feshe shi da turare..
(ku hasasho yanda Junaid yake domin bazan iya tsara irin kyan da yayi ba, nadai tsara shi kaɗan😹😹)..

Bayan sun kammala Angel ta miƙa masa new phone ɗinsa tace “ga saƙon Mommy tace na baka, sim ɗinka yana ciki..” da murmushi a fuskarta ta kuma cewa “my man kayi kyau sosai saika fito kamar ɗan indian..”
hannu ya kai ya kamo lips ɗinsa yace “zan cire bakin maganar fa…” suna dariya da haka suka bar ɗakin, tace masa “kai na gama shirya ka, kaje abokanka suna jiranka, sauran ita Ayushert zanje itama na shirya ta…”

murmushi yasau mata ba tareda yace komai ba ya sauƙa downstairs, ita kuma ta wuce ɗakin Ayush…

Angel tana shiga ɗakin Ayush ta tarar da abun mamaki, baki ta sake tana kallon Ayush wacce take ta shan baccin ta ko wanka batayi ba, gashi har an taru,
sai kuma ta tuno da maganar Mommy yanda take cewa Ayush bata san da maganar baiko ba amma kar a sanar mata anaso ayi mata bazata ne!!!

rufe ƙofar ɗakin Angel tayi sannan ta nufi yanda Ayush take kwance saman gadonta, zama tayi a bakin gado tana bubbugar sawayen Ayush a hankali,
a gigice Ayush ta tashi tana faɗin “dan Allah kayi hakuri Yaya Junaid wallahi bazan sake ba, wayyo Allah nah…..”

zaro ido waje Angel tayi tana kallon ta cike da mamaki tace “sorry ki kwantar da hankalinki babu abunda zai faru da ke..”
Ayush tashi tayi zaune tana kallon Angel har ta haɗa gumi,
ta kwanta ne da tunanin yanda taga Junaid yana dukan Adity kamar bazai barta da rai ba, tayi tsammanin yayo ta kanta ne yanzun,

da murmushi a fuskar Angel tace “daman mommy ce ta turo ni akan nazo na shirya ki, kinji hayaniyar mutane har sun taru a guest house….”

Ayush tsaya wa tayi tana kallonta cikin rashin sanin ko ita wacece,
batayi tunanin Angel bace saboda tasan su ɗin ba musulmai bane ita kuma wannan da shigarta na musulmai,
Angel ce ta katseta da cewa “ki hanzarta ki shiga wanka yanzun nan, please..”
tayi hakan ne domin tasan dole za’a nemeta a wajen taron kuma yanzu kowa ya shirya ita kaɗai ta rage,
Ayush tana shirin tashi saiga mommy ta shugo tana riƙe da doguwar riga wedding gown da takalmanta da sarƙoƙin wuya, ganin Ayush a haka yasa mommy ta tsaya cak tana kallon Ayush tace “subhanallahi Ayush daman bakiyi wanka ba? dan Allah ki hanzarta yanzu kowa fa ya hallaru acan guest house, shima Junaid an ƙira shi sun tafi da abokansa, nima yanzu can zan tafi saboda akwai gabatarwar da za’ayi,
Angel yanzu zan turo muku wata inyaso saiku shiryata ku biyun zakufi sauri….”
Mommy tana kaiwa nan ta ajiye ledar kayan sannan ta juya da sauri ta fita,
itama mommy ba ƙaramin kyau tayi ba a cikin wata danƙararriyar gizna water fruit mai tsadar bala’i tasha ɗinkin doguwar riga ya baje sosai har jan ƙasi yake, ta hau takalmi mai tudu yanda tsayin rigar zai ɗan ɗage,
ga anyi mata zigzar wuta a giznar mai style, ta ɗauko gyale water fruit shima mai duwatsu, tasha makeup sosai tayi matuƙar kyau, ga sarƙar ya zauna mata a wuya kamar wanda aka ƙeroshi dan ita, ga ba ƙashin wuya ko ɗaya,
sai ƙamshin turaren da yake tashi a jikinta,
(nifah mommy tafi burgeni yaciin😘)…

Ayush jin mommy ta ambaci sunan Angel yasa ta tsaya tana kallonta,
Angel kamar zatayi kuka tace “kiyi sauri mana Ayushert, muma fa munaso a buɗe taron damu, please too pass…”

haka ta tashi da sassanyar jikinta ta nufi toilet, ita har cikin zuciyarta bata kawo komai a ranta ba,
bata san da maganar baiko ba..

♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎

Anan fa ake taro na manyan mutane, kowa yana zazzaune a kujerarsa da lemuka kala-kala a gaban kowa,
ta can saman hall kuma tsararrun kujeru ne a jere na mutane namusamman, Mommy tana zaune akan ɗaya daga cikin kujerun sama, sai ta gefe kuma Rumana ce tasha rigar kanti wato riga mai haɗe da dogon wando, kayan roba ne amma jikinsa duk gashi-gashine mai colour purple, hannun rigar kuma ɗaya mai dogon hannune ɗaya kuma gajeran hannu ne, amma kuma wandon ta ƙasi a baje yake, rigar tayi kyau sosai kuma itama mai rigar tayi matuƙar kyau ga farin gashintan nan ta kwantar dashi har gadon bayanta, ga goshinta kuwa ta 6angare guda yayi jaa yanda Junaid ya wurga mata wayarsa, ƙafarta kuwa tana sanye da takalmi thorns mai tsinin gaske, dan dai sun iya tafiya da takalmin amma idan mu mukasa kam ai sai dai mu karya ƙafarmu…

ta ɓangare guda kuma Adity ce take zaune itama tayi kyau a cikin wata baƙar riga dogo har zuwa gwiwarta mai ɗinkin bubaa da dogon wandonta mai fela ya ɗan baje ta ƙasi, ta toshe da baƙin glass a idonta, sumar gashinta kuma ta kwanto wani ta gaba, itama takalmi mai tudu ta saka,
can jikinta kuma a farfashe da zaku cire rigar 🤣,

sai kuma wasu manya-manyan ogannin sojoji,
ta tsakiyan kuma doguwar kujera ne yasha kwalliya an tanadar wa Junaid da Ayush ɗinsa…
warai ya cika da zafafan mutane duk kuma sunada pass a hannunsu,
wani irin ganga ake bugawa mai ratsa zuciya da kuma sojoji masu hura sarewa, abokanan Junaid ne suka rinƙa tashi ɗaya bayan ɗaya suna gafatar da kansu tareda jawabai na musamman da kuma murnar samun lafiyarsa..

Mommy ce ta taso itama ta bada cikakken tarihin Junaid da irin gwagwarmayar da suka sha kafin ya samu sauƙi,
wasu har da kukan su tsabar tausayi,
Rumana da Adity duk ba wacce bata zubda hawaye ba, sannan Mommy ta sanar wa al’umma cewa yau ne ranar Baikon Junaid tareda wacce yake so kuma zai Aura nan da wasu ɗan kwanaki kaɗan…

dake da turanci mommy take magana duk ba wacce bata razana ba acikin ƴanmatansa su biyu wato Rumana da Adity,
Laylah itama tana zaune a kusa da Yayanta Doctor Hasheem tsabar rikicewa da sauri ta miƙe tsaye daga zaune,
Doctor ne ya riƙo hannunta tareda zaunar da ita yana girgiza mata kai,
tinin ƙwalla har ya soma gangaro wa Laylah..

mutanen waran ne suka fara tafa hannayensu cikin farin ciki da jin daɗin lamarin,
tare da buga ganga mai bada sauti, komawa mommy tayi ta zauna cikin jin daɗi, duk a cikin manya-manya mutanen nan ba wanda bai tashi ya sanyawa Junaid albarka ba da kuma nuna masa farin ciki..

saida aka gama gabatar da kowa kafin aka buƙaci ganin Amarya domin su sanyawa junansu zoben ƙauna,
(magana ake ta rayuwar turawa to meya hwaru🤔😜)..

Ana tambayar Amarya daide lokacin aka shugo da ita,
Angel tana riƙe da hannunta na dama sai wata mata mai sanye da hijabi har ƙasi tana rufe da fuskarta da liƙab itama tana riƙe da Ayush ta ɓangaren hagun,

Ayush tayi matuƙar kyau bana wasa ba,
ta saka wedding gown fari na campany irin mai kama jikin nan, daga saitin gwiwarta kuma rafar ta baje sosai, ta bayan yana jan ƙasi, dirin jikinta ya fito bana wasa ba, ga hips ɗin nan kamar kamar dai….

a hankali take taka takalmin ta fari mai duwatsu ta sama ga tsini domin daƙer take taka takalmin a hankali gudun karta faɗi,
ga anyi mata gyaran gashi gaban goshin nan anyi style da gashin wajen ya kwanta, aka naɗa mata gwaggwaro da net ɗin kayan jikinta, sannan aka rufa mata ɗan ƙaramin gyalen net ɗin akan ta da fuskarta gaba ɗaya, ga an zuba mata makeup, Ayush bata ƙwalliya ma ya kuka ga kyanta balle yanzu da akayi mata makeup na amare, kyau iya kyau kam ba’a magana…

tinda suka shugo har aka zaunar da Ayush idon Junaid yana kanta, har maganar zuci yake “anya kuwa wannan itace Yushert ɗita? wannan kam aljanar kyau aka samo mun…” yana maganar zucin idonsa na kanta wacce take zaune ata gefensa,

photuna kawai aketa musu da masu wayoyi da camera man duk suna ɗauka ne a photo har da video domin ba ƙaramin dacewa sukayi ba, sunyi matuƙar kyau sosai…

ita dai Ayush har yanzu ta kasa gane mai hakan yake nufi ne, a tunaninta duk karramawa ne haka, an nuna an damu da ita tinda gashi har ɗaukota akayi aka zaunar da ita,
abunda yake cikin ranta kenam..

mata mai liƙab kuwa itama zama tayi tana bin kowa da kallo, itadai mommy ta turata ne akan taje su taho da Ayush ba tareda tasan ko wacece ita ba, domin tin zuwanta bata cire liƙab ɗin ba,
Ayush ce kawai taso ta ganeta amma itama bata gama wayeta ba, ita kaɗai sai murmushi take a cikin liƙab ɗin, tana cikin farin ciki matuƙa….

Ayush tana zaune sai ji tayi ance Amarya da Ango ku tashi tsaye,
zaro manya-manyan eyes ɗinta tayi tana faɗin “su waye Amaren kuma?..” tayi maganar acikin ranta, bata ankara ba taji an riƙota a tsayar da ita, Angel ce take kusa da ita daman ita ta tasar da ita..

Junaid ne ya riƙo hannayenta biyu suna fuskantar juna, cikin rashin fahimta Ayush take kallon Junaid, shi kuma sai faman sake mata murmushi yake..

wannan tsari ne za’ayi shi idan duk suka amince suna son junansu toh zasu sanyawa juna zobe koda bayan nan ne babu halin rabuwa dole daga baya za’ayi aure ba fasawa ba janyewa..

Mai gabatarwa ne yazo gabansu ya tsaya sannan yace “Captain Junaid shin ka amince kana son Ayushert?”
Junaid idonsa akan Ayush yace “na amince ina son Yushert…”

mai gabatarwa ya ƙara da cewa “ka amince komin daɗewa zaka Auri Ayushert babu janyewa?..”
yana murmushi yace “na amince, bana fatan na rabu da Yushert koda wasa…”

kafin kace mai mutanen wajen sun haɗe wajen da tafi da ihun farin ciki especially abokansa, harda su buga ganga lokaci guda, kafin wajen yayi tsitt..

zoben zinare aka bawa Junaid ya sanyawa Ayush, ya karɓa sannan ya zura mata a dogin yatsunta..

mai gabatarwa ya komo kan Ayush itama ya tambayeta,
“Malama Ayushert shin kin amince da soyayyar Junaid?…”
sai a lokacin Ayush ta fahimci wani abu, ita a tunaninta Aure ake ɗaura musu a hakan,
jin tayi shuru ne yasa aka sake tambayarta
“Malama Ayushert kin amince da soyayyar Junaid? kuma zaki Aure shi?…”

wajen yayi tsit ana sauraronta,
hannu tasa ta yaye gyalen kan natan tana kallon Junaid tace “Ban Amince ba, kuma bazan taɓa Auransa ba! dukan mata yake yi, yau ma saida yayi wa wata budurwarsa duka kamar zai kasheta, a haka zan aure shi? to gwara na mutu banyi Aure ba, idan na Aure shi zai iya murɗe mun wuya ya kashe ni, ga ƴanmatan ka nan ka zaɓi ɗaya ka Aura amma banda ni……”

tana kaiwa ƙarshen maganarta ta juya da gudu zata tafi, ta gurmuɗe da takalmin ƙafarta zata faɗo ƙasan floor da aka ɗanyi tudun beni a gurin da sauri Junaid ya cafko kunkuminta ya rungumota jikinsa har idonsa ya cicciko da ƙwalla yana kallon yawan mutanen da suke wajen mata da maza gasu nan, yana rungume da ita jikinsa na kakkarwa tsabar takaici da baƙin ciki tinda yake ba’a taɓa basar dashi a cikin mutane ba sai yau, gaba ɗaya ya rasa ya zaiyi kamar ya nitse cikin ƙasa haka yake jii,
hajijiya ne yake shirin ɗibarsa, ƙafarsa tayi masa nauyi yana shirin faɗuwa da Ayush da yake rungume da ita, abokinsa commander yusuf yasa hannu ya ɓanɓare Ayush a jikinsa ya zaunar dashi yana bubbugar kafaɗarsa alamar rarrashi,
Ayush zame jikinta tayi tana tattara rigarta ta bar wajen kwata-kwata…

idan aka ware Laylah da Rumana da kuma Adity duk wajen ba wanda zuciyarsa bai sosu ba, musamman abokansa tsabar takaici kasa cewa komai sukayi suna zazzaune kamar wanda ruwa ya cinyesu,

Mommy kam haɗa kanta tayi da gwiwowinta bansani ba ko kuka take yi…

Angel itama kamar ta rausa ihu tsabar takaici, domin duk abunda zai taɓa Junaid haka take jinsa a ranta,
babban tashin hankalinta shine ganin hawayensa, tinda take dashi bata taɓa ganin hawayensa ba sai yau…

suna zaune babu wanda ya motsa sai matar nan mai liƙab itace ta tashi da sauri tabi bayan Ayush,
tana shiga parlour kai tsaye upstairs ta wuce saboda taga daga nan aka fito da ita,
tana buɗe ɗakin Ayush ta tarar da ita kwance sai faman rera kuka take,
ta rufe ƙofar sannan ta ambaci sunata “Ayushh..” cikin ɓacin rai ta ƙira sunan..

Ayush ɗagowa tayi da manya-manyan idanuwanta waɗanda sukayi jaa, har yanzu ta kasa gane ko wacece,
matar hannu tasa ta ɗage liƙab ɗinta sama,
a razane Ayush tana kallon matar ta tashi zaune tareda faɗin “Umaa! Uma kece daman kika zo..”

Ayush tashi tayi da gudu ta nufi yanda Uman natan take zata rungumeta, ta riƙo Ayush ta zabga mata mari, tana ɗagowa kuma du ta ƙara zabga mata wani marin ta ɗayan ɓangaren ta saketa ta faɗi ƙasi tana kuka ta riƙe fuskar ta da hannu biyu…….

 

*ALHAMDULILLAHI ANAN NA KAWO ƘARSHEN LITTAFINA NA ƊAYA..*

 

Domin sauke CikakkenLittafin Sai Ku Danna bulun Rubutun dake kasa 👇👇

Matar Damisa Book 1 Complete Novel Document 

 

*YA ALLAH KAMAR YANDA KA BANI IKON KAMMALA LITTAFINA NA FARKO ALLAH KA BANI IKON GAMA NA BIYUN*

 

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

Back to top button