Hausa novels

Innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un Allah Ya Yiwa Sheikh Dahiru Usman Bauchi Rasuwa Yana Da Shekaru 101 A Duniya

An haifi Sheikh Dahiru Usman Bauchi a Gabashin Gombe a shekarar 1927 (1346 Hijriya) kuma ya soma karatunsa na addini a hannun mahaifinsa, Alhaji Usman.

Ya kuma karbi izinin yin karatun Kur’ani gaba daya kuma ya haddace shi kafin ya cika shekaru ashirin.Baya ga mahaifinsa, ya yi karatun addini a wurin wasu malamai da yawa, ciki har da Shehu Ibrahim Inyass.

Malamai da dama sun girmama shi saboda iliminsa, kuma an ba shi shaidar Gangaran a fannin Tafsirin Alkur’ani, wanda ke nufin shi babban masanin Tafsiri ne kuma ana iya cewa ya kai matsayin farfesa a wannan fannin.

A 1950, ya fara bayar da karatun Tafsiri, wanda aka fara saka shi a gidan rediyon jihar Bauchi a 1976. Daga baya, a 1980, ya yi karatun Tafsiri a gidan rediyon tarayya da ke Kaduna, wanda kuma aka fara sa shi a rediyon a wannan shekarar.

Ya na da yaya mahaddata Alkur’ani da yawa Bayanai sun nuna mashahurin malamain yana da ’ya’ya 95 da jikoki 406 da tattaba-kunne 100. Daga cikin wannan adadin, ’ya’yansa 77 da jikoki 199 da kuma tattaba-kunne 12 ne suka haddace Alkur’aninSheikh Darihu Bauchi ne daga cikin halifofin Shehu Ibrahim Inyass, Halifan Darikar Tijjaniyya, bayan wanda ya assasa ta, wato Sheikh Ahmadu Tijjani.

Yana daga cikin manyan malaman Musulunci a Najeriya, shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Koli da ke bayar da Fatawar Musulunci a Najeriya sannan babban jigo ne a Darikar Tijjaniya a Najeriya da ma Afirka.

Back to top button