Hausa novels

Ruwan Zuma Page 10 Hausa Novel

(10) “You take it too far Mas’ud! Meyasa zaka yi wani DNA test?” Ta tambayeshi tana mai tashi zaune cikin mamakin maganar daya gama fad’a. “Saboda irin wannan ranar da zaki kawo zance irin haka. I did the right thing.” Ya kare kansa cikin sauri don bai ga illar abunda yayi ba. “Yayi kyau.” Shine abunda ta k’ara fad’a kana suka yi shiru dukkaninsu.   Ana kiraye-kirayen sallah su Abul suka shigo gidan, ganin ba fara’a a fuskar mamansu yasa duk suka zauna suna tambayarta dalili. “Babu komai, kawai na gaji ne.” Ta basu amsa tana mai tashi tsaye ta shige d’akinta. “Uncle Mas’ud nasan ta fad’a maka, don Allah me yake damunta?” Abul ya tambaya. Mas’ud ya d’age kafad’arsa alamar bai san komai ba kana shima ya tashi ya tafi yana cewa, “Ka sameni a masallaci.” Sai da ya fita sannan Sabrin ta kalli d’an uwan nata tace, “Watakila magana aka mata akan aure, ban san meyasa Mama tak’i yin aure har wannan lokacin ba.” Ta dafe kanta kana taci gaba da magana. “Ina jin zancen mutane a waje cewa ni ‘yar mace ce ban samu tarbiyyar uba ba. Akwai wani abokin Salman da ya ta6a cewa wai bai ga abunda Salman ya gani a jikina da zai aureni ba, alhali ana zargin mahaifiyata da fasik’anci. Wallahi Mama bata wannan halin, kullum tare muke yini da ita a Laila Beauty kuma tare muke dawowa. Mutane basa yiwa zawarawan wannan zamanin adalci, kowacce mace ta jima bata yi aure ba sai kaga ana mata kallon ‘yar iska mara kamun kai.” “Meyasa baki fad’a mini ba?” Fad’in Abul cikin tsananin 6acin rai. Sabrin ta kalleshi cikin mamaki. “Menene ban fad’a maka ba?” “Na abokin saurayinki.” Cikinta ne ya kad’a sanin halinshi na zuciya shiyasa bata fad’a masa ba, yau ma su6utar baki tayi har ya ji. “Ohh, Salman ya nuna masa kurensa.” Ta mik’e da niyyar tafiya taji ya fara magana, “Baza tayi auren ba, idan akwai wanda take hanashi numfashi don ta k’i yin aure to ya mutu. Bana fatan tayi aure, zamanta a haka ya fiye mini komai akan in bud’i ido in ganta da wani namiji ba ubana ba.” Yana fad’an hakan ya fice daga falon tamkar zai tashi sama. “Wannan banzan zuciya da akidar taka Allah ya yaye maka Ya Abul.” Fad’in Sabrin a sanyaye tana shigewa d’akinta. Sati biyu da haka Laila na zaman gida bata fita ko’ina, hakan ba k’aramin damun ‘yan gidan yayi ba. Mas’ud, Abul da Sabrin babu wanda bai mata magana ba amma tana zaune ko shagonta tak’i lek’awa sai Sabrin ce mai zuwa. “In fad’a miki wani abu? Zamanki a gida bashi zai hana mutane magana a kanki ba, wani a hakan zai samu abunda zai fad’a na 6atanci a kanki. Zai ce me kike yi? Ko ciki kika yi shiyasa bakya son fitowa? Ko kuma cuta kika samu kika zauna a gida? Da maganganu da dama. Kenan ko ki fita, ko kar ki fita zasu yi magana! So, kinga kenan gwara kiyi abunda kike so suyi magana, a kan ki takura kanki wanda bashi zai hanasu yin magana ba. Shi d’an Adam haka yake, duk yanda kayi baza ka ta6a masa daidai ba kuma bazai fasa magana ba. Live your life the fullest.” Wannan maganan da Mas’ud ya fad’a mata yasa yau Laila ta fita tana jin zuciyarta cikin farin ciki. Sanye take da laffaya sanfurin Sudan kalar baki mai adon jan furanni, fuskarta da ba’a rabashi da kwalliya yau ma ta tsara mai kyau da sauk’i. Har yau Laila bata k’ara tsayi ba wanda yasa hatta Sabrin a yanzu ta fita tsayi. Sannan gyaran da jikinta ke samu yasa ko kad’an baza ka bata yawan shekarunta ba, sai dai kayi ta canki-canka tsakanin talatin ko talatin da d’aya. Kai tsaye Laila Beauty ta nufa wanda ke bakin Zoo road domin duba me aka yi bata nan, duk da cewa Sabrin na kawo mata rahoto kullum. Ganinta ba k’aramin dad’i ya yiwa ma’aikatanta ba wanda halinta na barkwanci da sauk’in kai yasa suke girmamata da kuma yi mata aiki cikin aminci duk da cewa ba’a rasa bara gurbi. “Welcome back Madam, we missed you.” Cewar Elizabeth mai kula da Spa. Da haka sauran suka gaisheta tana amsawa ciki fara’a har bakinta ya fara ciwo. Laila Beauty shine sunan da ta sakawa sabon shagon da ta k’auro ciki, wanda ake gyaran jiki da kai, zana lalle da kuma sayar da turaren wuta, humra wanda dama shine sana’arta tun farko. Da yamma bayan an rufe shago ta kamo hanyar dawowa gida ita d’aya dalilin Mas’ud ya biyo ya tafi da Sabrin gida. Tana tuk’i tana jin wak’ar Hamisu breaker na Gimbiyar Hausa tana bi a hankali. Har ta wuce ta k’ara dawowa ta shiga Donutfairy super market. In bata manta ba yau sati biyu kenan ciff rabonta da gurin kuma basu da wasu kayan buk’ata a gida. Tana tafiya tana tsintar abunda basu dashi, can kuma ta d’auki waya ta kira Sabrin, “Ehh, menene babu a gida?” Sabrin ta fara fad’a mata Laila na duba kwandon take hannunta. “Shikenan sai na dawo.” Da haka ta kashe wayan ta juya baya. “Innalillahi.” Ta furta da k’arfi ganin mutum a bayanta yana murmushi. “Me haka mallam?” Ta daka mishi tsawa zuciyarta na bugawa don ba k’aramin tsoro ya bata ba. Haydar da tun tana waya yake tsaye a bayanta yana jira ta gama ya gaisheta yaji babu dad’i a ransa, alherin data masa kwanaki yasa bai mance fuskarta ba. Lokaci guda fuskarsa ta kwaye ga kuma kunya da yaji dalilin Nasir na kallonshi yana mishi dariya a kanta na gefen damarsu. “Kiyi hakuri Hajiya. Dama zuwa nayi na gaisheki sai na samu kina waya, dalilin da yasa na tsaya kenan a bayanki. Don Allah kiyi hak’uri amma ba niyyata in tsoritar dake ba.” Ya bata hak’uri da tsantsar nadama a fuskarsa. A zuciyarshi kuma zagin kanshi yake yi da har ya tunkareta alhali yasan masu kud’i sun fiye wulak’anci. Tsaki ta ja mai sauti kana tabi ta gefenshi ta wuce. Nasir da ke gefe ya k’ara tuntsirewa da dariya wanda hakan yasa Laila ta juyo tana kallon abunda yake yiwa dariyar. Ganin bada ita yake yi ba yasa ta maida kallonta kan wanda yake yiwa dariyar yana nunashi da yatsa, yaron da ya tsoritata yake yiwa dariya, wanda shi kuma ya had’e fuska har kwalla na taruwa a idanunsa. Tasan ba babba bane don a kalla zata bashi shekaru goma koma fiye da haka. Ganinshi da tayi a haka sai ya bata tausayi domin tasan rad’ad’in da ake ji idan an gwatsale mutum, Madu yana mata haka muddin ta kaiwa Ummii abu. Kuma in ta tuna da kyau cewa yayi yazo ne ya gaisheta, kenan ya santa har yaga dacewar zuwa ya gaisheta. Bata kyauta masa ba, don har lokacin abokin aikinsa na masa dariya bai daina ba. “Kai d’an samari.” Ta samu kanta da fad’i ba tare da tayi shawara da zuciyarta kan me hakan zai jawo mata ba. Haydar da yake shanye kwallarsa domin ya tsani wulakanci ya juyo da mamaki yana duba wa take kira. “Yes, da kai nake. Zo.” Ta yafitoshi da hannu tana mai sakewa fuskarta fara’a. Da mamaki Haydar ya tako zuwa gurinta yana mai bada rata tsakaninsu domin gujewa laifin da ya aikata d’azu. Kanshi a sunkuye, hannayensa dunk’ule a bayanshi ya russuna yace, “Hajiya gani.” “I’m Sorry na maka tsawa. Ban tsammaci ganin mutum a bayana ba and kasan mata da tsoro.” Tayi ‘yar k’aramar dariya wanda saurayin bai tayata ba. “Kace kazo gaisheni ko? I bet ka sanni a wani guri ko kayi makaranta da ‘yayana ko?” Ta fad’i hakan tana mai k’arewa fuskarsa kallo wacce take ganin tamkar ta ta6a gani a wani guri. “Ina wuni?” Yace da ita fuska ba yabo ba fallasa. Laila ta d’aga gira d’aya cikin mamaki, kenan duk abunda ta fad’a bai ji bane ko dai ya za6i ya share ne? “Lafiya, Alhamdulillah.” Ta bashi amsa tana mai juyawa domin bata ga amfanin tsayawa dashi ba. Har tayi taku uku ta k’ara juyowa a karo na biyu dalilin tuno inda suka had’u da kuma meya faru a ranar. Ita tun a ranar ta manta dashi domin ko minti ashirin ba’a yi da had’uwarsu ba Madu ya kunsa mata bak’in ciki, hakan yasa ta mance da mai tsayuwa irin na Aliyunta. “D’an samari.” Ta k’ara kiranshi wannan karon murmushi ne a fuskarta na hak’ik’a ba na dole ba. Haydar da dama bai tafi ba ya juyo yana kallonta. “Kaine saurayin da ka sakamin kaya a cikin mota last two weeks ko? Sai yanzu na ganeka. Me sunanka?” Ta tambayeshi tana mai cigaba da murmusawa domin tuno da halinsa na kirki da tayi. ‘He’s innocent and cute kamar Abul’ ta fad’a a zuciyarta tana jiran amsarsa. “Sunana Aliyu, Aliyu Haydar.” Ya bata amsa wacce tasa lokaci guda fuskarta ta canja, fara’arta ya d’auke. “Amma an fi kirana da Haydar.” Ya k’ara fad’i yana mai mamakin canjawar yanayinta kamar wata hawainiya. “Sorry, sunanka triggered some memory. So Haydar it is. Ya kake?” Ta fad’a tana mai juyawa gurin da zata biya kud’i. Hakan yasa Haydar ya gane so take ya bita, ai kuwa ya kar6i kwandon hannunta yana washe baki domin bai yi zaton tana da sauk’in kai haka ba. Juyawa yayi ya yiwa Nasir gwalo wanda ya sake baki yana kallon ikon Rabbis Samawati. Ya rasa ya akayi Haydar yake da farinjinin mutane mata ko maza, duk in da ya shiga da wuya ya fito bai yi aboki ba saboda iya shiga ran jama’a da yake dashi. Shi ya kai mata kayan data saya har cikin mota suna magana jefi-jefi wanda Laila take ganin ba komai bane domin a matsayin k’ani ko d’a ta d’aukeshi. “Hajiya muna yin home delivery, idan kina buk’atar abu zaki iya kiran numbers d’inmu dake jikin ledojin nan sai ki fad’i abunda kike so a kawo miki har gida.” Fad’in Haydar yana bud’ewa Laila mota. “Hakan yayi, duk ranar da nake da buk’atan hakan zan kiraku Insha Allah.” Tace dashi bakinta d’auke da murmushi. Da haka ta ciro wasu kud’in ta mik’a mishi amma yak’i kar6a. Daga baya ma juyawa yayi ya koma cikin kantin bayan ya mata sallama. Hakan ba k’aramin burge Laila ya k’ara yi game da yaron ba, tana son mutum mai nitsuwa da kuma son mutane da sanin yakamata. Bakinta d’auke da murmushi ta bar farfajiyar kantin ta kama hanyar gidanta.  Shirye-shiryen kawo kayan auren Sabrin ake yi wanda hakan yasa Laila ta kasa zama. Ana washegarin za’a kawo ta kira wayar kantin Donutfairy. “Ina neman Haydar yaron da yake aiki a nan gurinku.” Fad’in Laila tana mai nunawa Sabrin drinks d’in data rubuta wanda za’a sayawa bak’i. “Yayi Mama.” Kana ta juya ta tafi inda Aunty Ajidde ke kiranta. Laila na tsaye akan layin har aka bata Haydar suka gaisa sannan ta fara k’irga masa abubuwan da take so yana rubutawa a wani memo. “Za’a kawo gida ko?” Ya tambayeta yana murmushi duk da cewa bata ganinshi. “Eh, gida zaka kawo. Ka mini lissafi sai in turo maka kud’in ka basu kamar kullum.” “To Hajiya. Mun gode.” Da haka ya kashe wayar yana murna domin yasan baza ta barshi haka ba, kusan wata guda kenan yana kai mata kaya gida. Kafin ya kai kuma zata tura masa kud’i ta account d’insa wanda shi kuma zai d’auki na kantin ya tura musu sauran kuma ya rik’e, wanda dama tace masa idan yaga extra ya d’auka ta bashi.  Yana gama lissafi ya tura mata, nan take kuwa yaji k’arar shigowar kud’i a wayarsa.  Wani tsalle yayi yana ihu domin wannan karon har dubu goma ta k’ara masa. Nasir da shi ya d’auki wayar tun farko yace, “Yau kuma nawa ka samu?” “Goma ciff mutumina. Yanzu ma zan je gurin telana in biyashi kud’in d’inki.” Haydar ya bashi amsa yana mai barin gurin cikin sauri don ya saka kayan da zai kai mata a mota. Nasir ne ya tayashi d’aukan kayan sannan ya aika kud’in ta bankin ogansu bayan Eke ya lissafa komai. Motar kantinsu k’irar pick up ita ya kunna kana ya wuce kasuwa cikin sauri. A gurguje ya kar6i d’inkinsa kana ya koma gidansu.  Yana shiga ko sallama babu ya nufi inda randarsu ke ajiye yana tu6e kayan jikinshi. “Yau na shiga uku ni Suwaiba. Kai Ali me zan gani haka? Tu6e kaya kake yi a tsakar gidana?” Wannan fad’in mahaifiyarsa kenan wacce ke tashi tsaye daga rumfarta. “Kai Ammi. Nasan dai ke d’aya ce a gidan kuma kin saba ganina a haka, kuma gashi nan zan bar gajeran wando.” Ya bata amsa ba tare daya kalleta ba ya fara zuba ruwa a bokiti.  Da haka ya d’auki bokitin wacce ko hannu bata dashi ya shige bayi yana mai rufewa da langa-langa wanda shine k’ofar.  Wacce ya kira Ammin ta tako zuwa inda ya zubar da kayansa ta fara tsincewa tana fad’a, “Ban san ranar da zaka yi hankali ba Ali, ji yanda ka zubar da kayanka a k’asa kamar wani k’aramin yaro bayan ka shigo gidan nan da gudu. Tukunna ma ina zaka je kake sauri haka?” “Ammi bani sabulu da soso.” Yace da ita daga band’akin. Tana masifa taje ta d’auko ta mik’a masa wanda sai da ta make hannunsa kafin ta bashi. “Ohh dariya na baka ko? Zaka fito ka sameni.” Da haka ta koma ta zauna a inda take taci gaba da sak’an hulan sanyin da take yi.  Amina wacce tayiwa kanta lak’abi da Minat ita ta shigo gidan hannunta d’auke da kwano bakinta kuma d’auke da sallama. Budurwa ce ‘yar makwabtansu, tun ba yau ba take nunawa Haydar so amma sanin ba aure bane a gabanshi yasa baya ko kulata. “Wa’alaikis salam. Minat kece?” Ammi ta saki fara’a a fuskarta. “Wallahi nice Ammi. Ina wuni?” Ta fad’a a kunyace tana mai sunkuyar da kanta k’asa. “Lafiya ‘yar nan, yasu Innar taki? Kowa lafiya ko? Ni na kwana biyu ban shiga na gaishesu ba wallahi. Kai ya kamata gobe in lek’asu.” Ammi ta k’ara fad’ad’a fara’arta. “Umm, dama Ammi naji kwanaki kince Ya Haydar na son d’anwake shiyasa yau nayi na kawo masa.” Ta k’ara saukar da kanta k’asa cikin kunya. “Kai amma kin kyauta Minat, to mun gode. Dama yanzu dawowanshi daga aiki ya shige wanka.” “Ai naga motar gurin aikin nasu a k’ofar gida.” “Da alama wani gurin zai je shiyasa yake sauri haka.” Fad’in Ammi tana kallon k’ofar band’akin in da Haydar ya fito daga shi sai boxer babu ko kunya. “Kai Haydar baka ji munyi bak’i bane?” Fad’in Ammi cikin kunya ganin yanda Minat ta zuba masa ido tana kallonshi.  Shi kuma ko a jikinshi in banda gimtse fuska da yayi da yaga Minat d’in. “To Ammi zama zanyi tayi a cikin band’akin har lokacin da taga dama ta fita?” Yayi shigewarshi d’akinsa wanda ke jingina da na Ammi. Dama gidane d’an k’arami wanda d’akuna biyun kenan kad’ai a ciki sai band’aki guda d’aya.  Tsaki Ammi ta ja kana ta girgiza kai tana mai duban Minat wacce ta sunkuyar da kai k’asa wai ita mai kunya alhali nan jikin Haydar take haskowa a idanunta.   Ai yau tayi farin zuwa, da wannan hoton zata yi bacci yau kai har kullum ma. Ina ma zai yarda ya tsaya ta d’aukeshi a hoto ai da hakan zai fi mata dad’i. “Minat kina jina kuwa?” Fad’in Ammi tana kallon yarinyar wacce da alama sam bata ji me take fad’a ba. “Um ina jinki Ammi.” “Nace yayarki Hajja ta haihu kuwa?”   Da haka suka cigaba da hira har Haydar ya gama shiri ya fito yana zuba k’amshi cikin sabon d’inkinsa, shadda ce fara kal ‘yar dubu biyar da aka yiwa d’inkin half jumfa daidai jikinsa. Sosai yayi kyau kamar balarabe saboda hasken fatarshi da kuma sajenshi da ya fara fitowa. Takalminsa ya duba yaga ta kod’e ya koma ya saka ta sallanshi wacce yake adanawa domin zuwa neman aiki.  Ammi dai bata kulashi ba domin fushi tayi dalilin ya fito tsirara bayan yasan sun yi bak’uwa a gidan. D’akinta ya shiga ya d’auko madubi kana ya k’ara fitowa yana duba fuskarsa yana kwantar da gashin kansa wanda tun a d’akinsa ya taje. “Ammi zan tafi, zan kai kayane gidan uward’akina da nake baki labari, yau karki d’aura girkin dare zan sayo miki duk abunda zaki ci.” Yana fad’in hakan ya koma d’akinta ya mayar mata da madubinta sannan ya fito yana kakkad’e jikinsa. “Ga d’anwake Minat ta kawo maka.” Fad’in Ammi tana mik’a mishi kwanon. “Ni bana cin d’an wake.” Shine amsar da ya bata yasa kai ya fice daga gidan ba tare da ya k’ara kallon inda Minat d’in take ba. “Kai Ali, Ali.” Haka Ammi take ta kiransa amma bai ji ba domin kuwa hankalinshi yayi kan gidan Laila. “Kiji mini iyeyi na Ali, Ina ga kulaku yake yi shiyasa ya fad’i haka. Karki damu zan ajiye masa idan ya dawo zai ci.” Ammi ta bawa Minat baki tana d’an dariya kad’an domin kar ranta ya 6aci. “Ba komai Ammi, ni zan tafi gida.” “To mungode d’iyar arziki, ki gaishe da mamanki.” Da haka suka yi sallama ta fita daga gidan. Ammi ta bud’e kwanon tayi arba da had’ediyar d’anwake wacce taji latas, tumatir da kuma kwai dafaffe kwalli d’aya tak a sama. “To yanzu zan jira yaron nan ya dawo sannan muci tare ne, ko dai zan d’ebi rabona?” K’arshe dai Ammi tashi tayi ta d’auko kwano a d’akinta ta raba musu abincin har da kwai d’in wanda kashinta yafi yawa. “Ni na d’aukeshi tsawon wata tara a cikina.” Ta fad’i hakan tana mai d’auke kason kwanshi don nata bai isheta ba. “In ya dawo sai ya sayi wani in dafa masa.” Haydar kuma kai tsaye ya wuce gidan Laila cikin sauri kafin ogansu ya kirashi yaji inda ya kai masa mota. Yana isa maigadi ya bud’e masa gate ya shiga da yake ya saba zuwa.  Tare da maigadin suka sauk’e kayan suka saka a cikin store d’in da yake waje kamar yanda Laila ta buk’ata, saboda In bak’in sun zo ba sai ansha wahalar d’aukowa daga cikin gida ba. “Ina Hajiyar?” Haydar ya tambaya yana mai duba bakin k’ofar gidan.  Ya so ace ya had’u da ita ya mata godiya kuma ta ga kwalliyarshi. Haka kawai yaji yau yana son ya burgeta ta ganshi a cikin sabon kaya ba kod’add’un da yake zuwa dasu ba. “Hajiya tana can tana shirye-shirye.” Maigadin ya bashi amsa yana mai komawa bakin aikinshi.  Haydar dake tsaye a jikin motar da yazo da ita yaji ranshi yayi babu dad’i. Jiki a sanyaye ya shige motarshi ya kunna ya fara juyawa zai fita. A bakin k’ofar mashigan falonta ya ganta tsaye da wasu mata biyu wanda daga kallonsu ya gane ‘yan uwanta ne.   Hannu ta masa ya tsaya murna fal a cikinshi, ai abunda yake nema ne ya samu. Ya fito ya gaisheta tare da matan da suke tsaye tare. “Kalti Ajidde duba kiga wannan drinks d’in yayi wanda za’a bawa bak’i su tafi dashi?” Laila ta tambayi addarta tana bud’e store d’in. “Wannan ai har yayi yawa.” Fad’in Marwa wacce itama tayi aure a cikin Kano yayinda Safa ke aure a Maiduguri kuma baza ta samu zuwa kar6an kaya ba sai aure zata zo. “Yayi, kinyi k’ok’ari. Ai tuwon girma miyarshi nama.” Ajidde ta bata amsa kana suka shiga motar da Marwa tazo dashi suka fita daga gidan.  A nan hankalin Laila ya dawo kaf kan Haydar wanda sai a lokacin ta ga shigar da yayi na manyan kaya, wanda kullum cikin k’ananan kaya take ganinshi dasu. “Haydar.” Ta kira sunanshi tana murmusawa. “Na’am Hajiya, na sameku lafiya?” Ya k’ara gaisheta a karo na biyu yana russunawa. “Lafiya kalau, sannu da k’ok’ari. Kayi kyau fa, yau zaka je hira kenan?” Ta yabeshi tare da tsokanarshi domin ta sake dashi tun ba yau ba.  Kunya da dad’i ne ya lullu6eshi ya sunkuyar da kanshi k’asa yana dariya yana sosa k’eya yace, “Wallahi babu in da zanje. Daga nan ma gida na nufa.” “Oh, ya mamanka?” Ta tambayeshi tana mai jingina da motar tashi. “Lafiyanta kalau, tace in miki godiya yanda kike mini alheri bakya gajiya.” “Laa, babu komai.” Ta fad’a tana mai d’aukar wayarta wacce aka kiranta.  Sai da ta gama wayar ta k’ara juyowa ta kalleshi sama da k’asa tace, “Nikam shekararka nawa? Sannan a ina ka tsaya a karatu?” “Am… ashirin da tara nake amma na kusa cika talatin Hajiya. Sannan na karanci Sociology a BUK, last year na gama service.” “Wani offer na samu idan takardunka sun yi kyau watak’ila zaka iya samu.” Tace dashi tana dariya yanda taga lokaci guda ya rufe bakinsa cikin mamakin maganarta. “Hajiya ni d’in? Don Allah me zan miki na nuna miki godiyata? Me kuma nake miki da kike taimakona haka?” “Babu, zan iya cewa had’uwar jini ce and kana da hankali da nitsuwa.” Ta bashi amsa tana mai kallon kwayar idanunshi wacce ke cike da farinciki har ya rasa yanda zai yi. Godiya ya fara zuba mata tana dariya tana cewa ya isa amma ba don ta gaji da hakan ba, nishad’i take ciki na sosai domin sai yanzu ta tabbatar bayan su Abul akwai wani mutum da take jinshi a ranta tamkar 6arin jikinta.  Suna tsaka da haka Abul ya shigo cikin gidan, sai gani yayi mahaifiyarshi tsaye da wani, wanin ma kuma saurayi suna dariya tamkar mata da miji. Zai iya cewa bai ta6a ganin mamanshi tsaye da wani namiji tana dariya yana dariya ba sai wannan.  Kalmomin ‘mata da mijin’ ne ya maimaita a ranshi wanda hakan yasa lokaci d’aya yaji ya tsani mutumin har k’ok’on ranshi.   A zuciye ya isa gurinsu yana aikawa Haydar harara na ban mamaki kamar zai shak’eshi. Yana lura da yanda yake kallonta ba kallo ne na sauk’i ba, kallo yake mata irin wanda saurayi yake yiwa budurwarshi, kuma ba zai ta6a bari hakan ya faru ba.  Haydar ne ya fara arba dashi ya juyo yana cewa, “Ga Abul ya dawo.””Mama waye wannan?” Shine abunda ya fara tambaya fuskarsa a had’e kamar hadari.A ranshi kuma yaji ya tsani saurayin, tsana mafi muni.Zallar tsagawaron soyayya na gaba tare da nishad’i da kuma bankad’uwar wasu sirruka masu nauyi.A yau aka gama free pages wanda za’a cigaba da turowa ranar monday 21 december a paid group d’inmu na whatsapp.  RUWAN ZUMA littafin kud’i ne amma a Naira Dari N100 kacal. Na rage kud’inshi ne domin kowacce ta iya saya domin bana son wannan tafiya ta rayuwar Laila ya wuce kowannenku, mace ko namiji. Domin kuwa na ta6o wani al’amari ne da al’ummarmu na yanzu muke kushewa wanda hakan ba k’aramin 6ata muke aikatawa ba. Ku turo kud’inku N100 ta 5139579011 FCMB Suwaiba Babagana ko katin Zain/Airtel ta 09023713064.  Zaku yi amfani da wannan lambar wayar domin nuna shaidarku ta biyan kud’i kafin a sakaku a group d’in wanda suka biya. Ga maza masu son biya, kuma zaku tura kud’inku sai ku yiwa wannan lambar 0903 662 1442 magana a sakaku a group na maza zalla wanda d’an uwana zai kula dashi. Ina kuma wanda basa son hayaniyar group basa son a had’asu cikin mutane? Naku kud’in daban ne, zaku turo N300 sai a dinga turo muku ta private kullum.

Mum Fateey 👌

Back to top button