Uncategorized

Kura-kurai 4 Da Aka Yi A Cikin Shirin Labarina Season 5 Episode 4

 LABARINA (Zango na biyar, kashi na huɗu)

Sabon shiri, sabon salo, sabuwar fikira.


Shirin ya yi gamon katar tare da afkawa hannun gwanaye ta fuskar rubutu. Wato irin abin nan da ake ce wa komai na babba , daban ne.

Marubuta 1: Nasir S. GwanGwangwazo/Yakubu M. Kumo

Marubuta 2: Siddika Habib, da Sidiya Sidiya.

Labari: Aminu Saira

Ɗaukar nauyi- Sarkin waka

Ba da umarni– Aminu Saira

Kamfani- Saira Movies.

1. Son ma so wani… Soyayyar Ummi da Lukman ke nan!

2. Tawagar juyin juya hali ta kankama a gidan Yari ƙarƙashin Baba Ɗan’audu domin kafa sabuwar gwamnati.

3. Makauniyar soyayyar Lukman ta rufe ma shi idanu, yana ta tafka kura-kurai a zamantakewarsa da ahalinsa da masoya sa, da abokansa..

4. Kai tsaye mun ga illar zaɓen shugaba ko damƙa ragama a hannun mutumin da bai da cikakkiyar lafiya.

5. Majaujawar soyayya ta ɗibi Umar da Rukayya.

6. Rabiu ya iya taka rawa sosai, yana kara wa Shirin karsashi.

7. Alhaji Dan gaske uba ne yake da dattako, da kowa zai zama kamar shi.

Real Also:

Application Mai Matukar Ban Mamaki

Yadda Zaka Magance Matsalar Wayarka Cikin Sauki

KURA-KURAI:

1. Matakai da kalaman Aliyu duk da rashin lafiyar da ke damunsa sun yi tsuarin da babu abin koyo na gari a ciki. Daga ƙarshe mun ga illar zaɓen shugaba ko damƙa ragama a hannun mutumin da ba shi da cikakkiyar lafiya.

2. Zuciya da riƙo irin na Maimuna game da Rabiu sun yi tsauri da yawa, duk da cewa ya yi mata laifi. Ya kamata a samu zuciyar musulunci, “Matar na tuba…

3. Ummi fa matsayin baliga kuma musulma, yanayin shige wa Lukman da take yi gaba-gaɗi ba zai haifar da ɗa mai ido ba, duk dai shi ba ta ita yake yi ba.

4. Ban san irin surukin da za a riƙa yi wa cin kashi irin Baba Rabiu ba, kuma da hankalinsa ya ɗauki auren ‘yar sa ya baka.

 Labarina wata katafariyar makaranta mai ɗauke da manyan darussan rayuwa ababen koyi. Gefe guda kuma akwai raha da barkwanci da kalamai masu sanyawa a dara ko ba a shirya ba. Labarina na cikin manyan shirye-shirye masu dogon zango da ake yayi kuma yake ɗaukar hankalin masu kallo.

Mubarak Abubakar Saulawa

23-9-2022.

Domin Sauke Fim ɗin Labarina Season 5 Episode 4 Original HD Video cikin wayoyinku Sai ku danna inda aka saka Download Now! 

Domin sauke shi cikin wayoyinku sai ku danna nan 👇👇👇

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

Copyright 

If you are the right owner of this novel and you want us to remove it from our site please mail Us at aihausanovels@gmail.com

Back to top button