Zafafa 2023

Tsutsar Nama Book 2 Complete Novel Document Pdf

Tsutsar Nama Book 2 Complete By Billyn Abdull

Description/Story:

Tsutsar Nama Book 2 ! Complete Hausa Novel Document Written By Billyn Abdull

 

Description

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒐𝒏𝒆_

_Assalamu alaikum masoya. Fatan alkairi a gareku tare da barka da salla. Ya rabbi ka amshi ibadunmu ka yafe mana kurakuran mu. Ka gafartama iyayenmu. Kafin komai dole na fara da tarin godiya a gareku musamman wanda suka sayi kayan salla a wajena. ALLAH yabar zuminci. Nagode sosai da yanda kuka nuna ƙarfafawa a gareni akan wannan kasuwanci. Ina sake albishir a gareku da in sha ALLAHU wasu kayanmu na gab da sauka musamman abayoyi da handbags na yara dana manya. Sai kowa ya ƙara zuba kuɗi a asusu 😂. Gamu mun dawo filin daga. ALLAH ya bamu ikon sauke nauyin juna mu daku, ALLAH ya haneku cin hakkinmu, muma ALLAH ya hanemu tauye hakkinku 🙏. Godiya ta musamman gareku baki ɗaya 😘😘😘🙏_.

…….Kuka nayi sosai a wajen. Dan har sai da kaina ya dinga sara min tamkar zai rabe gida biyu sannan na miƙe. Cikin layi irin na rashin ƙarfin jiki na koma ɗakin dana kwana. Handbag ɗina na ɗauka tare da hijjabin danai sallar asuba. Gudun haɗuwa da shegen karensa ya sakani bi ta kitchen duk da ban san takan gidan ba. Ta bayan na bi, hakan yasa har na zagayo inda gate yake banga karen ba. Zaram maigadi dake zaune yana jin waƙa ya miƙe. Bakinsa har rawa yake wajen gaidani. Ban amsa masa ba. Face cemasa “Buɗe min!” cikin kakkausar murya da tsawa.
Cikin daburcewa da wuru-wuru ya ce, “Amma Hajiya oga baice….”
“Wlhy idan baka buɗe min ba zan haɗa kai da ogan na danna muku zagi.” nai maganar ina fisgo sandarsa dake ajiye saman bench. “Zaka buɗe min ko sai na ɗora maka ita a saman kanka”.
“ALLAH ya huci zuciyarki Hajiya bara na buɗe”. Ya faɗa cikin rawar jiki yana nufar ƙaramar ƙofar. Key yasa ya buɗe, na watsa masa harara sannan na fice. Sai da na tabbatar na fita sannan na jefa masa sandarsa nai gaba. Dogon street ɗin nabi da kallo, mai ɗauke da lafiyayyen titi. Sam ban gane a wace anguwa bane ba. Dan haka hankalina ya tashi. Amma sam banji na sare ba na cigaba da tafiya sauri-sauri duk da rashin ƙarfin jiki da nake ji. Addu’a kawai nake ALLAH ya kawo mai napep. Kai koda mota ce zan nema taimako. Na ɗan yi nisa a tafiyar inayi ina waigen bayana dan ji nake kamar makirin zai iya biyoni. Jiri ne ke ɗibata sosai, dan kaina har yafara harmutsawa. Na ɗan tsaya ina mai dafe shi da ambaton sunan UBANGIJI. Dai-dai nan wata farar mota da har ta gittani ta dawo da baya.
“Baiwar ALLAH lafiya kuwa?”.
Muryar matashiyar mace ta daki kunnuwana. Hannuna na janye daga saman kaina. Cikin kallonta dishi-dishi a wahalce na furta, “Bakomai hajiya.”
“A ya zakice ba komai. Gashi kinayi kamar ma zaki faɗi”. Tai maganar tana fitowa a motar. Riƙoni tai dan jirin ne ya ɗeban zai zubar. Muryarta da damuwa sosai ta ce, “Kinga bara na sakaki a mota. Sai ki faɗamin ina zaki na kaiki”.
Ganin mace ce, kuma dama abinda nake buƙata kenan sai banyi musu ba. Da taimakonta na shiga motar. Ina zama na lumshe idanuna kaina na ƙara ƙarfin sarawa matuƙa. Koda ta shigo ta zauna tana tambayata ina zata kaini kasa bata amsa nayi, hakan yasa tai shiru ta bani ɗan lokaci da take tunanin na samu nutsuwa sannan ta sake tambayata. Da ƙyar na iya furta mata. “Yakasai”.
“Okay ba damuwa. Amma ina ganin mu fara zuwa clinic sannan. Dan kina cikin halin buƙatar taimako. Ni likitace”.
“Karki damu ki kaini gida kawai na gode”. Na faɗa a matuƙar wahale.
“Bazai yiwu ba, kiyi haƙuri na taimakeki dan ALLAH”.
(Dan ALLAH) data ambata yasa ban iya sake cemata komai ba. Daga haka ma na sulale ban sake fahimtar komai ba.

    ★

    Hankali tashe maigadi ya nufi cikin gidan. A dai-dai ƙofar shiga falo ya samu Maash tsaye. Rikicewa yay, musamman da yay ma fuskarsa kallo ɗaya ya ganta a tsuke kamar hadarin gabas. Cike da tashin hankali ya zube ƙasa saman gwiyawunsa yana kwaso rantsuwa. “Wlhy tallahi ranka ya daɗe ba laifina bane ba. Tace idan ban buɗe mata ba zata fasamin kai ne.”
Shiru baice masa komai ba. Maigadi ya sake rikicewa yana jera rantsuwa da magiya duk a gurbi ɗaya. Sai da ya mula dan kansa a hankali ya furta, “Jeka kan aikinka”.
Duk da a sauƙaƙe yay furucin hankalin maigadi bai kwanta ba sam. Dan gani yake akwai abinda zai iya biyo baya. So yake ya cigaba da bada haƙuri har sai yasan ainahin gaskiyar abinda ke zuciyar mai-gidan nasa, sai dai kuma baiga muhallin yin hakan ba. Dan haka sum-sum ya juya bakin gate zuciyarsa na rawa matuƙa. Cikin taraddadi da ƙaulani ya koma, kusan mintuna goma da komawarsa yana zaune ya zabga tagumi akai horn. Firgigit ya tashi domin dubawa. Sai da ya buɗe ƙaramar ƙofa yaga mai horn ɗin sannan ya buɗe gate ɗin gaba ɗaya. Cikin girmamawa ya gaisar da Hayatu dake shigowa. Shi kuma ya ɗaga masa hannu yana ƙarasa shigewa cikin gidan. Yana fitowa a motar Laalah ya zaburo, inda yake yazo shi adole ya sanshi, hakan ya sakashi sakin murmushi da kai hannu ya shafa kansa yana faɗin, “Laalah how are you?”. Daga haka ya wuce zuwa cikin gidan.
Koda yay sallama a ƙofar sai da aka kwashe kusan minti ɗaya kafin a amsa masa, tare da bashi izinin shiga.  Sarakin na zaune tamkar babu abinda ke damunsa. Hasalima dukan hankalinsa naga wayar hannunsa ne. Koda Hayatun ya shigo ma bai ɗago ba. A haka ya amsa masa gaisuwar da yay masa. Sanin hali yasa Hayatu bai damu ba ya cigaba da maganarsa. “Sir Alhamdullah yanzu haka tana tare da ita. Sai dai tace akwai matsala. Dan tana shiga motar ta sume mata, a yanzu haka ma suna clinic, sun kuma tabbatar da jininta yayi matsanancin hawa da take buƙatar taimakon gaggawa saboda gudun samun matsala a zuciyarta. Amma nadai basu damar yimata dukan abinda ya dace”.
Karan farko ya ɗan ɗago ya kalla Hayatun, sai kuma ya maida kansa ga wayar batare da yace komai ba. Tsahon mintuna biyu kamar yama manta da shi sai kuma ya ajiye wayar a gefensa. Hannunsa ya ɗan matsa tare da ɗagowa ya zubama Hayatun idanunsa. Dole Hayatu yay ƙasa da nasa kan dan baya iya jure irin kallon nan na ogansa mai kama da na abokin yaƙi a filin daga..
Cikin silent voice ɗin nan nasa da janye idanunsa daga kansa ya furta, “A sanarma Hameed ya shirya zuwa 9 zamu wuce Abuja. Sai kai magana da Faisal zamu iso masa da mara lafiya ya taremu a airport”.
Sosai Hayatu ya zaro idanu waje. Duk yanda yaso haɗiye abinda ke masa kai kawo ya kasa hakan. Bai ma san sanda ya furta, “Amma Sir baka ganin tafiya da ita zai iya ɗarsama family ɗinta wani abu a rai kuwa? Jiya ne fa suka kawota nan a matsayin amarya. Kasan fa sunan arewa komai nasu na tafiya da addini da al’ada”.
Ko motsi Maash daya kwantar da kansa jikin kujera ya lumshe idanu baiyi ba balle Hayatu yay tunanin samun amsa. Ya kuma san shirun nasa na nufin bazai tanka ɗin ba, ya kuma gama zartar da hukunci kenan. Jiki a sanyaye Hayatu ya juya zai fita. Yayinda yake ta sake-saƙen mai fishshesa a zuciya. Dan dolene fa suyi wani abu da zai gamsar da family ɗin ta. In ba hakaba akwai babbar damuwa fa, kwaɓarsu zata iya yin ruwa batare da sun farga ba, shi komai ma sake ruɗar da shi yake. Dan yarasa dalilin ogan nasa na ƙulla igiyar aure tsakaninsa da ƴar bala’in yarinyar nan. Tunda yasan idan amsar video ɗin nan yay niyya da tuni ya amsa tako wace hanya ai, duk da dai ya fahimci itama yarinyar akwai taurin kai, sannan tana da power a cikin al’umma game da aikinta, maybe shiyyasa ogan nasa yaƙi yin komai kai tsaye a kanta ya biyo ta wannan sigar.
Gashi bai sanar masa komai akan shirin nasa ba. Hasalima sai a jiya shima ya san da batun auren bayan sun baro Lagos a jirgi yake sanar masa. Ya shiga shock matuƙa, sai dai bashi da hurumin iya cewa komai tunda ya riga ya zartar da hukunci, amma ya yini ya kwana al’amarin nan na juya masa a rai. Dan duk duniya shine kaɗai kuma yasan Maash ɗin yayi wannan auren, ko su dangin yarinyar basu san shine ba, saboda baije musu a Maash ɗin ba. To koma dai miye, shi kam zaiga yaya wasan zai kaya, dan shi ɗin shaida ne, ogansa mutum ne mai tsananin taurin kai da aljananci na gaske. Ga hatsabibancin masifa da dagiya akan abu, ya tabbatar ba son yarinyar nan yake ba, dan inda hakane kai tsaye zaije yace yana sontan saboda shi bai iya ɓoye-boye ba tamkar bature yake komai nasa kai tsaye yake yinsa. Ko minene a ransa kai tsaye yake fiddashi koda bazai ma kowa daɗi ba shi babu ruwansa idan yayi dai-dai da ra’ayinsa kansa kawai yake kallo..
Kai tsaye anguwar su Samraah ya nufa, dan dolene yaje ya tsara abinda ya dace gudun samun akasi..

★★★

   A gidan Abba kam sai a safiyar yau ƙananun magana suka fito sosai. Dan kuwa Mom ta titsiye Abba taji komai daya faru a wajen ɗaurin aure dama kafin ɗaurin auren. Dan haka ta shiga bazama na kusa da ita su kuma suka ɗauki zance ƙus-ƙus. Tun anayin abin a gwargwaɗe har dai komai ya fito cewar bada Mansoor aka ɗaurama Samraah aure ba da wani ne daban. Dan mahaifiyarsa ta shata layi akan auren nasu, duk da dai shi Mansoor ɗin yaso bijirewa amma su Kawu Musa suka ce bazasu bashi ba saboda abinda mahaifiyar tasa tazo tayi a jiyan har gida batare da matan cikin gida sun sani ba sai su Gwaggo Gudidi kawai. Tun dai zance na iya cikin gida har maƙwafta suka fara shigowa jin gulma da kawo wadda suka jiyo a waje. Yanda Mom ta nuna farin cikinta a fili akan abinda ya farun ya ƙona zukatan su Gwaggo Gudidi da ƴan Gwarzo. Sai ga faɗa ya kaure tsakaninta da Aunty Jimmai babbar ɗiyar Kawu Musa. Kafin kace mi gida hargitse. Suka haɗu sukama Mom tatas, dan babu abinda suka manta basu faɗa mata ba har sai da tai kuka. Kuma Gwaggo Gudidi ta tabbatar mata indai tana raye sai Abba ya ƙara aure. Da ƙyar da ƙyar dai Musaddiq ya kwantar da wannan tarzoma. A kusan kuma dai-dai lokacin Hayatu ya iso gidan. Inda ma ALLAH ya taimaka Musaddiq da Abba da su Kawu Musa na ƙofar gida a lokacin da ya iso ɗin, dan haka ya samu tarba ta mutunci. Cikin ɗar-ɗar da addu’a a ƙasan ransa bayan sun gaisa ya sanar da su abinda ke tafe da shi kamar yanda ya tsara domin bama ogansa kariya. Hankalinsu ya tashi da jin Samraah babu lafiya. A take babu ɓata lokaci suka muƙe domin binsa asibiti dubata. Bai hanasu ba, dan bashi da wani zaɓi, sannan hakanne ma zai taimaka masa tsarin nasa ya tafi dai-dai yanda yake buƙata batare da Maash ya rufta ba ko shi dake ɗan kore ba………✍️

Hummmm🥱

 

File Name   Tsutsar Nama… Hausa Novel Doc.
Title   Tsutsar Nama Book 2
Author    Billyn Abdull
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    19/06/2024
File Size    650Kb
Format Size    TXT
Phone No
Download Tsantsar Nama Book 2 Complete Novel Document By Billyn Abdull

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button