Uncategorized

Abban Sojoji Chapter 28 Book 2 Complete Novel

 

“`The father Of Soldiers“`

 

Story &  Written 

       By 

      Hafsat Bature

          (Boss Lady)

                                               Ita kan ta Hafsat ba ƙaramin tashin hankali tashi ga ba ganin halin da yarinyar ta shiga, da alama ma raunukan nata sun ɗuri ruwa dole sai an fitar da ruwan Ya Salam, Yarfa hannu kawai take yi tana zabga uban kuka,  hankali atashe JAHAD ta kalli hafsat tare da cewa “Aunty dan Allah ki taimaka mu mayar da ita asibiti aduba ta…..’ ta ƙare maganar tana faman zubda hawaye,

  Ita kanta hafsat tunanin da take yi kenan can ne kawai mafi ta, ta shi tayi jiki na rawa ta ɗauko hijab ta zura sannan ta ɗauki mukullin motarta da ta bari a saman mirror,

 da kanta ta cuccu6i hosana daker ta ɗauko ta a kafaɗarta, ta fuce da ita cikin sauri itama jahad tabi bayanta a babban falon suka samu aunty babba saman Sofa hannunta ɗauke da plate ta dafa taliya sai faman ci take a tsiya ce saboda yunwar da ta taso ta, duk ihun da hosana take yi a kunnanta amma batayi yunƙurin tashi ba, balle taje ta dubo meke faruwa,

  Ganinsu afujajen yasa ta miƙewa tana cewa “Hafsat ina zuwa cikin daren nan? Ina zaki kai ta?

   Batare da hafsat ta kalle ta ba tace “Zan mayar da ita asibiti ne,” hankali atashe aunty babba tace “Saboda me !! Acikin daren nan ! Ki barta kawai inyaso gobe dr yazo ya duba ta har gida,” 

   tsoki hafsat taja dama a ƙule take da Mommyn nata saboda duk ita taja mata halin da suke ciki,.  

  Wuce ta tayi tana cewa “da yake ba jikin ki bane ae dole ki ce haka,’ 

Bin su kawai aunty babba tayi da kallo har suka fuce, abayan mota hafsat ta kwantar da hosana, sannan suka shiga gaba ita da jahad, taja motar da gudu ta fuce da ita a wani privet hospital takai ta, cikin sa’a suka karbi hosana kuma nan take suka shiga bata taimakon gaggawa, 

Yayin da hafsat da jahad suka samu wuri suka zauna nan waje suna jira saman waiting chairs, runtse ido kawai jahad ke yi tana faman karanto addu’a, tsigar jikinta har tashi take yi saboda jin yarda ihun hosana ya cika asibitin gaba ɗaya baiwar Allah, ita kaɗai tasan azabar da take sha,

Ita kanta hafsat dake gefenta jikinta duk ya gama mutuwa haƙiƙa taji tausayin Yarinyar fiye da tunanin mai tunani,

Jim kaɗan suka ji tsit babu kukan hosana babu alamar shi, jin hakan yasa jahad yin zumbur ta miƙe ta tunkari ƙopan ɗakin da suka kwantar da ita, tsoranta kar ace hosana ta mutu ne shiyasa suka ji shiru,

   turo ƙopar Nurse tayi ta fito cikin sauri jahad ta tare ta tana cewa”dan Allah sister ya jikin nata yake? ta tambaya a ɗan ruɗe

  Nurse ɗin tace “Alhamdulillah, kada ki sa damuwa aranki, jikinta da sauƙi sosae anyi mata dressing na raunukan nata sannan Mun taimaka mata da pain relievers yanzu haka allurar bacci mu kayi mata, addu’a kawai zaku ci gaba da yi mata,’ tana faɗin hakan ta wuce gaba,

   Ajiyar zuciya jahad tasaki har hankalin ta ya kwanta sosai, komawa tayi ta zauna gefen hafsat wadda ke ta faman yin gyangyaɗin bacci, 

  Rufe idonta kawai tayi tana faman ci gaba da yiwa hosana addu’a, bata jin zata iya runtsawa a daren nan,

tsawon awanni suna anan jugum time ɗin hafsat ta jima da yin nisa a baccin ta, jahad kuwa na nan ido buɗe, kamar daga sama taji hosana na kiran sunan ta ƙasa ƙasa da farko tayi tunanin gizau muryarta keyi mata amma daga baya ta tabbatar da cewa ita ɗin ce ke kiranta,

  Cikin hanzari ta miƙe ta shiga ɗakin samun ta tayi ta tashi zaune saman gadon,  ba ƙaramin farin ciki bane ya cika jahad, ganin yadda fuskar hosana ta sa6e an matse mata ruwan anyi dressing ɗin wurin ga bandage nan a forehead ɗinta da saman hancinta, duk da fuskar ta canza sosai kamar ba ita ba,  idanuwanta sun buɗe sosai tana ganin jahad takama Murmurshi 😥

Faɗawa saman gadon jahad tayi ta rungumo ta sosai ajikinta tana faɗin “Allah sarki hosana ashe kin farka ban sani ba kina ta kiran suna na, ya jikin naki? Akwai inda ke miki ciwo yanzu”?   Tayi tambayar tana janye jikinta daga na hosanar,

   Daker ta iya cewa “Naji sauƙi sosai jahad ba inda ke mun ciwo yanzu, amma magana tana mun wahala,Kuma ina jin jikina kamar ba nawa ba”

   hannu jahad tasa tana shafa gefen fuskarta tace “Insha Alah zaki dawo dai-dai hosana, yanzu hankali na ya kwanta tun da naga kina murmushi nasan cewa sauƙi ya samu, yanzu ki faɗamun wanene yayi maki wannan bugun mutuwar?’ 

   turo baki hosana tayi tana cewa “Wannan mara imanin, saboda nazo na same ta, ta shaƙe maki wuya kamar zata kashe ki, na bata haƙuri ta ƙyale ki ta ƙiya shine na gartsa mata Cizo a hannun, wannan ne fa kawai yasa ta kamani ta jibga ta faffasa mun fuska……….,” shessheƙar kukan da take yi ne ya hana ta cigaba da maganar

   Cikin sanyin Murya jahad tace “ashe duk don saboda ni ne tayi maki wannan bugun, babu komai akwai ALLAH ! , Zai bi mana haƙƙin mu duk wanda ya zalunce mu Allah zai saka mana insha Allah!

 Jinjina kai hosana tayi tana share hawayen ta tace “Yaya Omar bazai ƙyale su ba, duk sai sun gane kurensu…..

  ta faɗi wit angry face can kuma ta sake cewa “Jahad komai yasa yaya Omar har yau baizo ya duba mu ba”?

   Jahad tace “muyi mashi Uziri hosana, ni nasan cewa yana sane damu kuma zaizo nan very soon,’

 Sun jima suna yin fira atsakanin su, ita kanta jahad tasan cewa hosana juriya kawai take yi tana yin surutu, daker tasamu hosana ta koma ta kwanta, itama a gefenta ta ra6a ta kwanta, lokaci guda bacci ya kwashe su su duka,

Ba ƙaramin bacci suka sha ba, don kuwa har sai da gari ya waye rana ta fito sannan jahad tafarka, hosana kuwa nata faman sharar baccin ta, ganin yadda hosana ke bacci anatse ya ƙara tabbatarwa da jahad cewa tasamu sauƙi sosai, tashi tayi ta cire hijab ɗin dake jikinta, ta shige toilet ɗin dakin Alwala tayi sannan ta fito ta ɗauki hajiabin ta zura, tana faman tunanin in da zata samu tayi sallah don babu carpet, 

  Fitowa tayi don ta duba hafsat samu tayi bata anan inda tabar ta jiya babu ita ba alamarta a wurin, sai taji hankalin ta ya ɗan tashi tsoranta kar ace guduwa tayi tabarsu a asibitin,

  Hankali atashe ta fito harabar asibitin ga mutane nan nata wuce wa wasu na shigowa wasu na fuce wa, sai faman waige waige take yi tana neman hafsat, har wurin ajiye motoci taje taga ko zata ga motarta amma babu ita, hakan na nufin tabar asibitin kenan, da alama ma tun asubahi tabar asibitin, tuni jikin JAHAD yayi mugun sanyi, 

  Koma wa tayi tasamu wurin inda taga wasu mata zazzaune suna fira, tayi musu sallama suka amsa mata da fara’a 

   Tambayarsu tashiga yi idan suna da abun sallah su ara mata, nan wata daga cikin su ta miƙa mata sallaya ɗinsu da suka zo da ita, anan harabar jahad tayi sallah bayan ta kammala ta mayar masu da dardumar sannan ta koma ciki a kasalance, bakowa tafi ji ba face HOSANNA, yanzu in da gaske hafsat tafiya tayi tabarsu yaya zasu yi? Ina zasu dosa? bakomai ma yafi damunta ba face Hosana in tafarka ta son dole akwai yunwa atattare da ita, gashi ita ba ta da ko sisi balle ta siya musu abunda zasu samu su Ci, 

   Gefen hosana tasamu ta zauna wadda ke kwance tana faman sharar bacci, tagumi ta zabga tare da zuba mata Ido tana kallonta, in taƙaice muku tsawon lokaci ba hafsat ba alamarta 😧😳 Gashi in sunce zasu kai kansu gidan duka ba wanda yasan hanyar da zai bi, saboda da daddare ne kawai suka fito daga gidan baza su iya shaida kwatancen gidan ba, gashi ko Sunan unguwar basu Sani ba, ajiyar zuciya jahad tasaki aranta tana jin cewa hutu ne yazo musu, zasu ci gaba da rayuwarsu ne kawai akan titi,

__________________SEHRISH__________________

Around 8 Ta farka kai tsaye kitchen ta wuce har time ɗin rigar jiya ce ajikinta da rolling ɗinta, a kitchen ta samu Azmee harta kusan kammala breakfast din gaba ɗaya, bayan tayi sallama ta shiga suka gaisa da junan su, Daga bisa ni azmee tace “Ina fata jiya kin kai ma SGR dinner ɗinsa ko? don na shigo na taras da kayan abinci a warmers ko ta6a su ba ayi ba,’ 

   Sehrish tace “Na babban yaya ne, Jiya bai samu yaci ba dana kai masa, Tea kawai yasha daga baya yace mun yana buƙatar fruits, shine kafin naje na kawo masa har bacci ya ɗauke sa,’

  Jinjina kai azmee tayi tare da cewa “Allah sarki da alama jiya sun sha aiki ne that’s why harya gaza cin abinci, Yanzu bari na shirya miki breakfast ɗinsa ki kai masa da sauri saboda nasan dole ya tashi da yunwa,’

   Sehrish ta amsa mata da Toh, ta tsaya tana jiran ta shirya mata kayan breakfast ɗin nasa,

Shiru tayi tana tunano maganar da HAROON ya faɗa mata jiya, akwai abunda ya tsaya mata arai take son fitar dashi

“Aunty azmee dan Allah me ake nufi da ZAREN BA KALAR YADIN bane? ta tambaya tana kallom azmee  dake shirya abinci cikin warmers asaman kitchen drawers din dake jere,

  Ba tare da ta juyo ta kalle ta ba tace “idan aka ce Zaren ba kalar yadin bane, a tunani na ana nufin kamar abunda bai dace da wani ba, a misali kamar ace kina son wani wanda yafi ƙarfin ki nesa ba kusa ba, bari na baki wani misali ma kamar yanzu ace mace tana Son Namiji wanda ya kasance hamshaƙin mai kuɗi ne ko mai mulki ga ilmi ga kyau gashi prominent dae, ke kuma ace kin kasance ƴar talakawa ce koma kina aiki a ƙasan shi baki da duk wani abu daya mallaka da zaku zo ɗaya dashi kin ga kuwa ba sa’an yin ki bane,wannan shi ake nufi da Zaren ba kalar yadin bane……’

   Jinjina kai sehrish tayi aranta tana cewa “Wato abunda haroon yake nufi kenan hmmm,”

Sannan a fili tace “To Aunty azmee me ake nufi da cewa ISKA NA WAHALAR DA MAI KAYAN KARA,!”?

  Har sai da azmee ta ɗanyi dariya jin wannan, ɗan gyaran murya tayi kafin tace “Kamar mutun ya yi ta wahalar da kansa akan abunda bazai ta6a samu ba, yanzu in mutun ya sanya kayan kara ana iska shin kayan zasu zauna ne batare da sun tarwatse ba? 

  Sehrish tace “Eh hakane kuwa,” 

  “Yawwa ma’anar kenan, mutun yasanya wa ransa abunda bazai ta6a samu ba, kin ga zai tashan wahala ne,” 

  ta ƙarasa maganar tare da cewa “Zo ki ɗauki breakfast ɗin ki kai masa na kammala,”

ƙarasawa sehrish tayi ta ɗauki tray ɗin duk jikinta yayi sanyi ga me da abunda Azmee ta fassara mata yanzu, amma taci alwashin duk runtsi duk wuya zata jaraba Soyayyarta Agare shi ba fashi 💔

    Fuce wa tayi ta miƙi hanya kamar daga sama taji muryar haroon a kunnanta yana cewa “ƴar Shila barka da safiya fatan kin kwana cikin ƙoshin lpy, 

   Shiru tayi bata bashi amsa ba, yana tsaye ruƙe da ƙugu daga shi sai gajeran wando ajikinsa, 

Ci gaba da magana yayi “Dole kisha ƙamshi baby, an fa samu Freedom dole a hura hanci, hallau dae bari na ƙara tunasar miki, shisshigi da kutsi ba zai kai ki ga cin nasara ba akan wancan Babban kayan da ki ke hari, ke bama shi ba ko junaid dana ga kina shisshige mawa wlh yafi ƙarfin ajin ki, kwara ma ni zan iya yin maneji na lalla6a ki mu rufa wa juna asiri, ke ƴar aiki ni kuma ɗan masu gida Fantsararre,,,

  takaici ya hana ta cewa komai wuce wa kawai tayi upstairs, 

   Tun da ta nufi part ɗinsa take jin tashin ƙamshi ya gauraye ko’ina Har cikin hancin ta direct masu daɗin ƙamshi,

   Bayan tayi sallama tashi ga, babu kowa a palor ɗinsa ƙarasawa tayi ta ajiye masa tray ɗin asaman table ɗinsa, tsayawa ta ɗanyi don ta jira fitowarsa,

  Tana cikin tsayuwar nan wayarsa da ya bari asaman hannun Sofa ta soma ringing da ƙarfi har sai da sehrish ta ɗan yi firgit da ido, kai idonta tayi a inda wayar take hada sa hannu tana dafe kirjinta, matsawa tayi a ƙoƙarinta na ta ɗauki wayar takai masa,

  Adai-dai time ɗin yafito cikin sauri Don ya ɗauki wayar saboda Kira ne mai mahimmanci agare Sa yasan dashi

   Jin motsin mutun yasa sehrish ɗagowa takai ido a kansa, aikuwa a tsananin firgice ta ɗanyi wani sauti tare da yin Hanzarin juyawa cikin tsananin farga ba,

   Sam baisan da mutun ba, fitowa yayi daga shi sai ɗan pant a jikinsa gaba ɗaya halittar jikinsa ta bayyana,

   bin bayan ta yayi da kallo mamakin sa ganin yarda ta razana kamar taga wani dodo, wuce wa yayi yasa hannu ya ɗauki wayarsa sannan ya shige ciki yana amsa kiran a kunnansa,

  Juyo wa sehrish Tayi jin alamar ya koma ciki sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, gaba ɗaya duk ta firgice ta gigice ta tsorata da yanayin da tagansa…

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Back to top button