Halysaah Page 215 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 215…Khaleesat na zaune kan darduma da daddare bayan ta idar da sallan isha’i Noor ta shigo dakin rike da wayar Umma a hannunta ta duka tana mika ma Khaleesat wayar tace “Wai Aunty tace a kawo maki waya” Khaleesat ta amshi wayar tana duba screen din ta ga Aunty Faridah ce a kan layin, ta kai wayar kunne a hankali tace “Aunty” Aunty Farida tace “Na’am, ya kike Khaleesat” Khaleesat tace “Lafiya lau, ina yini?” Aunty Farida ta amsa sannan tace “Ya jikin naki?” Khaleesat tace “Na ji sauki Aunty” Aunty Faridah tace “Maa sha Allah, Allah ya kara lafiya” Khaleesat tace “Ameen” Aunty Farida tayi shiru at first, sai kuma tace “Yauwa kina ji na?” Khaleesat ta gyada mata kai kamar tana ganinta tace “Ina ji Aunty” Aunty Faridah tace “Ai zaki iya zaman mota zuwa Bauchi gobe ko?” Khaleesat tayi shiru, haka nan kawai taji gabanta ya fadi sosai, da kyar tace “Aunty me ya faru?” Aunty farida tace “A’a ba wani abu bane, Junaid ne bashi da lafiya amma da sauki sosai, but since you are much better now ya kamata ki zo ki dubasa” Khaleesat bata san sanda ta mike daga kan darduman da take zaune ba bayan taji abinda Aunty Farida tace, da kyar ta zauna gefen gado cikin wani yanayi tace “Aunty ba shi da lafiya kuma? Me ya same shi?” Aunty Farida tace “Ke bana son hauka baki ji na ce maki da sauki ba” Khaleesat ta girgiza mata kai hawaye suka kawo idonta tace “Aunty ai yana nan kano fa” Tana fadin haka ta mike ta nufi handbag dinta ta bude tana dubawa nawa ne a ciki, Aunty tace tace “Baki san ya dawo Bauchi ba kenan” Khaleesat ta sake kudin hannunta ko kifta idonta bata yi jin abinda Aunty Faridah tace, da kyar ta koma ta sake zama edge din gado cike da karfin hali tace “Aunty yana Bauchi kuma? Yaushe ya je?” Aunty Farida tace “Na fa ce maki bana son hauka ko” Khaleesat ta goge hawayen da ya gangaro idonta muryarta na rawa tace “Bazan yi ba” Aunty Faridah tace “Ki ma yi tunda baki da hankali da nutsuwa, gobe za a zo daukar ki daga Bauchi ki kasance cikin shiri” Hawaye kawai ke zuba idon Khaleesat ta kasa cewa komai, Aunty Farida tace “Kin ji abinda na ce maki?” Khaleesat tayi karfin hali tace “Na ji” Aunty Farida tace “Sai da safe, he is much better now kawai ya kamata ki zo Bauchin ne ki dubasa” Sallama Aunty Farida tayi mata ta katse wayar, Khaleesat ta dora kanta saman pillow tana jin hawaye na gangaro mata a ido, wayar ne ya fara vibrate sai da ta firgita, ta dago kanta da sauri, taga Aunty Farida ce ke kira still, ɗagawa tayi ta kai kunne amma ta kasa cewa komai har sannan hawaye bai daina zuba idonta ba, Aunty Farida tace “Kin san Allah idan kika ce zaki kamo hanya kamar wata gantalalliya a motar haya sai nayi mugun saɓa maki, na ce maki gobe za a zo daukar ki, idan haukan ki ya kuskura ya kai ki tasha da sunan zaki biyo motar haya za ki ga abinda zan maki” Cikin rawan murya Khaleesat tace “To Aunty” Aunty Farida ta katse wayarta, a hankali ta fashe da kuka don da Aunty Faridah bata sake kira ba intention din dake ranta kenan dama, daren ranan bacci kaurace ma Khaleesat yayi gaba daya, yanda taga rana haka taga daren, ita da har cikin dare sai ta ci abinci yau ko yunwan bata ji tana ji ba, har sallahn asuba bata runtsa ba, karfe bakwai na safe na yi ta kira Aunty Farida da wayarta, har ya katse Aunty Farida bata ɗaga ba, tayi mata kira ya kusa hudu babu answer, kwanciya tayi kan darduman da take zaune tana goge hawayen idonta, tayi lamo tana sauraran kiran Aunty Faridah amma shiru, a haka bacci barawo ya saceta a wajen…. Wajen karfe sha daya Khaleesat ta farka a firgice daga baccin da take, waige waige ta fara yi tana neman wayarta zata duba agogo taga babu wayar a kusa da ita, ta mike tsaye da sauri taga an saka mata wayar a caji, dauko wayar tayi, sosai gabanta ya fadi ganin miss calls din Jay biyu, bata san sanda ta duka kasa ba cause sai da taji maranta ya kulle, tafi minti biyar a duke har sai da taji ciwon da take ji ya ɗan ragu sannan da kyar tayi dialing number Jay, har ya katse bai daga ba, sai da tayi masa kira biyar bai yi picking ba, ta kira Aunty Farida ita ma har ya katse bata daga ba, sosai taji ta fara loosing mind dinta, a haka Umma ta shigo dakin ta sameta, Umma na kallonta ta nufeta tace “Lafiya me ya same ki?” Khaleesat ta kasa daurewa ta fashe da kuka sosai tace “Umma ina ta kiran su basa ɗagawa kuma” Umma tace “Su wa kike kira?” Cikin kuka tace “Su Aunty Farida” Umma tace “Ke bana son shashanci, ko daxun nan mun yi magana da Faridah” Khaleesat tace “To Umma ya jikinsa ta ce?” Umma ta juya tace “Ban sani ba, tunda ke baki da nutsuwa a rayuwar ki, ki dinga yin abu kamar ba er musulmai ba, daga mutum bai da lafiya sai kuma ki fara abubuwa kamar warce bata san Allah ba” Khaleesat dai hawaye kawai ke zuba idonta, Umma ta fita ta bar mata dakin. Sai da Khaleesat ta kusa samun heart attack a wannan rana don har azahar ba a zo daukanta daga Bauchi ba, ga bugun zuciyarta yaki dawowa dai dai tun daxu, duk kiran da tayi ma Aunty Farida taki daga mata waya, Jay ma har ta gaji da kiransa he is not picking, gashi wayar Hadiyah a kulle yake, Mami kuma bata da layin da ake samunta da shi, tana ganin karfe biyu da yan mintuna taji bazata iya daurewa ba patient dinta ya kare gaba daya, ta tashi tana tafiya a hankali ta tafi parlor ta leka taga babu kowa a parlon, taga alamar Umma na cikin dakin Nenne, ta juya ta koma daki da sauri ta dau hijab dinta har kasa ta saka tana share hawayen idonta da bayan hannunta, ta dau handbag dinta me dauke da kudade zata fita kenan sai ga yaron Mama Shatu ya shigo dakin ya tsaya a bakin kofa yace “Aunty ga mota babba ya zo za a tafi da ke” Khaleesat ta dinga kallon yaron. Tun da Khaleesat suka kama hanyar Bauchi ta zama restless, duk sitting position din da tayi a motar sai taji she is not comfortable, ta rasa zaman da zata yi ta samu sukuni, a haka suka iso Bauchi wajen karfe shidda da rabi. Khaleesat wasn’t even after the warm welcome da aka yi mata a cikin masarauta, inda hankalinta gaba daya yake daban, bayan ta idar da sallah ta daga kai ta kalli Mami a hankali tace “Mami Hadiyah fa?” Mami tace “Tana can ɓangaren su, bata san kin dawo ba ne da ta zo” Halysaah ta sauke kanta tace “To bari in je can din” Mami tace “Baza ki fara cin abinci ba?” Khaleesat tace “Anjiima zan ci Mami” Mikewa tayi ta nufi kofa ta fita, walking slowly ta tafi part din Jay, tana shiga ta tarar da Hadiyah tana sallah a parlor, ta nemi waje ta zauna da tunani iri iri a ranta ta jira har Hadiyah ta idar da sallahn, Hadiyah na kallonta tana murmushi ta mike ta koma kusa da ita ta zauna tace “Welcome Halysaah, ya hanya? Ya kuma kika baro su Umma?” A hankali Khaleesat tace “Ya Jawwad fa?” Hadiyah tace “Ai suna asibiti basu dawo ba….” Khaleesat ta dinga kallon Hadiyah tana jin bugun zuciyarta na tsananta tace “Pls tell me, is he critically ill Hadiyah?” Hadiyah ta sauke ajiyar zuciya tace “Da sauki ai, da muka je daxu dai bamu samu ganinsa ba i think he is sleeping” Khaleesat ta marairaice lokaci daya hawaye suka cika idonta tace “Don girman Allah ki gaya min gaskiya Hadiyah” kawai sai ta fashe da kuka, Hadiyah ta zaro ido tace “Meye haka kuma Halysaah, na ce maki da sauki fa, ni dai ya kika baro su Umma tunda ke abun kuka baya maki wahala” dai dai nan Jay ya shigo parlon, Khaleesat ta daga kai tana kallonsa yace “Halysaah” Mikewa tayi tana kallonsa a sanyaye, yace “I am just seeing ur calls now Halysaah, ya hanya?” Ta nufesa tace “Don Allah zaka kai ni asibitin Ya Jawwad” Jay yace “To bari in yi sallah, kema ki je kiyi sallah…” Tace “Ai nayi” Yace “To zauna ki jira ni” komawa tayi ta zauna kan kujera ya wuce Bedroom dinsa, 30 mins ago suka dawo daga asibiti kuma tare da Ajay suka dawo yana can part dinsa yana bacci amma saboda baya son ayi interrupting masa baccin yasa bai ce mata tare suka dawo daga asibitin ba, Mami da Aunty Farida ce kadai suka san sun dawo asibiti amma har Hadiyah ma bata sani ba. Jay na fitowa daga dakinsa Khaleesat ta mike, Jay ya ɗan kalleta yace “Mami ma sun ce a kai su asibitin amma sai karfe takwas da rabi ake bari a shiga wajensa don haka kiyi hakuri har zuwa sannan, yanxun nan zaki ga karfe takwas din yayi, so be patient kin ji” Kasa ce masa komai tayi but she look restless, Hadiyah ta karaso parlon da tray din abinci da taje dauko mata ta ajiye kan table, Jay yace “Yauwa ga abinci an kawo maki ki zauna ki ci kafin mu je asibitin, nasan yunwa kike ji” Kamar zata yi kuka tace “Wallahi bana jin yunwa”

