Hausa novels

Halysaah Page 55 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 55…Wajen karfe uku na yamma Khaleesat na zaune bakin kofar dakin Umma Aunty Farida na combing din mata dogon gashinta bayan ta wanke mata shi da Shampoo da Conditioner, har wani sheki baƙin gashin nata yake yi bayan Aunty Farida ta shafa mata man gashi, tun daga wajen wanke gashin Aunty Farida ke ta mata fadan ta bar gashinta ya kakkarye saboda banzan da tayi da shi ta dena kula da shi, ita dai Khaleesat bata ce mata komai ba don har sannan basu san irin zaman da tayi a gidan Abdul ba, don ma abun ya tsaya iya kakkaryewan gashi, har bata son tuna experience dinta a gidan Abdul hakan yana traumatizing dinta, su Mama Zubaida da Mama Shatu dai na bakin murhu suna girka abincin siyarwansu na yamma, suna yi suna kuskus a bakin murhun, lkci lkci sai su kalli direction din su Khaleesat, ita dai Aunty Farida dama ko kallo basa isanta a gidan, a da dai ta biye su har dambe sun sha yi amma yanxu bata da wannan time din, kallon stark illiterates kawai take masu, wasu mata biyu ne suka shigo gidan babu ko sallama, sun yi shiga ta alfarma sun sha gwala-gwalai suna taku cikin isa, at the same time suna bin ko ina na gidan da kallo cike da kyama gashi dama su Mama Zubaida sun yi gaje gaje da ruwa a tsakar gidan ranan, Khaleesat ta dinga kallonsu haka Aunty Farida da ta ajiye comb din hannunta, Mama Zubaida ta mike tace “Sannun ku da zuwa ko dai batan hanya ku ka yi ne, in gidan Hajiya Samira matar Alhaji Bala ku ke nema can karshen layi za ku karasa sai ku yi tambaya a nuna maku gidan, amma ba nan bane” Momy ce ta shigo gidan tana tafiya gansan gansan da Drebanta a bayanta yana biye da ita, mayafin nata ma ko yafa shi bata yi ba, gashi ta sha wani tsadadden baƙin glass no respect, Khaleesat ta dinga kallonta babu ko kiftawa, lkci daya taji gabanta ya fadi sosai, ta juya ta kalli Aunty Farida, sai ga Meemah ita ma ta shigo gidan tana yatsine fuska, ita ko mayafin ma babu a hannunta, Aunty Farida ta dake tace “Bayin Allah lafiya? Daga ina haka, babu ko sallama” Daya daga matan da suka shigo da farko tana ma Aunty Farida wani matsiyacin kallo tace “Ba shi ya kawo mu ba, a irin wannan bolan za ayi maku sallama?” Umma ta fito daga dakinta don tana jin duk abinda ake cewa, tsaye tayi bakin kofa tana kallonsu, Mama Shatu da Mama Zubaida dai sai zazzare ido suke kamar wa enda suka yi ma sarki karya, Momy ta karaso har tsakiyar compound din tana tafiya cikin isa da gadara, fuskar nan nata babu ko digon mutunci tace “Zuwa nayi in ji ko shegiyar er ku tana da gadon Abdul ne, Ko kuma shi ma satan da ku ka yi ma ubansa kuke da niyyar za ku yi masa, in kuwa babu gado to yanxun nan ba sai anjima ba a maido mana kudadensa dake account din er ku…” Umma ta kalli Khaleesat nan da nan hankalin Umma ya tashi sosai, Aunty Farida tace “Ikon Allah, shi ne sai anyi wannan zuga haka kamar za ayi yaki?” Meemah ta matso har gaban Aunty Farida tana mata matsiyacin kallo tace “Yakin ne ai, ko kin ga alamar da sassauci muka zo? sanin halin familyn na ku na sata wanda ku ka gado a gun Malam me dattin hula ya sa mu ka yo tattaki a mayar mana da kudaden mu tun wuri, ai kowa yasan sata da cin amana shi ne tambarin gidan nan, don haka tun wuri ba a jiyo kan mu ba a maido mana Miliyan goman Abdul, kun zata bulus za ku ci ga banza ta fadi ko? To Sponsoring din matsiyaciyar er ku da ya dinga yi da kudinsa ma ai ba yafewa yayi ba sai kun biyasa a lahira wallahi, kawai babban farin cikin dake saka ni nishadi idan na tuno shi ne karewar da zata yi as dropout din John Hopkins university, don ko kaf zuri’arku za ku siyar baza ku samu kudin biya mata ta ci gaba da karatun a kasar Amurka ba, da yau ta gama John Hopkins sai bakin ciki ya kasheni, amma Alhamdulillah a dropout zata kare, Abdul kuma ya yar da kwallon mangwaro ya huta” A fusace Momy tace “Ke Meemah tsayuwa cikin kangon bolan nan ne ke burge ki da baza kiyi abinda ya kawo mu mu fita ba, ko so kike Cholera ya kama mu? Ina ke ina cacar baki a irin wannan gida” Aunty Farida tayi wani murmushi tana kallon Meemah tace “Sai dai kuwa bakin cikin nan ya kashe ki don kina ji kina gani Khaleesat zata gama karatu a makarantar da kike fada, Allah ya ji ƙan ki in Advance” Cikin tsawa Meemah tace “Keee, ki iya bakin ki, kar ki gan ni tsaye a wannan bolan gidan a gabanki kiyi zata ni sa’ar yin ki ce, don wallahi inda na bi da kafata ma baki isa ki bi ba har duniya ta nade, ni ba sa’ar ki bace ta ko wani angle, banda Abdul yayi downgrading dinmu ya kaskantar da darajan da Allah yayi mana ina mu ina hada hanya da matsiyata talakawa irin ku balle har aje ga auratayya? Ke ki duba irin wajen da ku ke rayuwa wanda ko karen gidanmu baza mu bari yayi rayuwa a cikin wannan hali ba, To wallahi ki iya bakin ki ni ba sa’ar yin ki bace, ba karamin aikina bane in sa a shafe babin ki a duniya” Tun kan Aunty Farida ta mayar ma da Meemah amsa Umma ta hanata, cikin fushi Aunty Farida tace “Kamar yaya in yi shiru Umma, gidanmu fa suka zo suka same mu kuma ki ce inyi shiru? ashe ma karyar arziki suke in don saboda miliyan goma za su yi wannan uban zugan kamar masu bibiyan miliyan 50 har su tsaya suna kumfar baki suna tada jijiyoyin wuya akan 10M, uban wani ya saka ya tura mata kudin a account dinta da har za su zo nan suna gaya ma mutane maganar banza, ko kuma rokonsa tayi ya saka mata kudin, su arzikin ma wallahi da gani taka haye suka yi, da can su ma matsiyata ne” Meemah ta mika ma Momy handbag dinta tana huci zata cakumo Aunty Farida, Momy ta dakatar da ita tace “Ke me ya kai ki, ki taɓa ta ki ce kin taɓa wa? Salon ta goga maki ƙashin tsiyarsu kike kokarin dambe da ita? Yanzu wannan har Class din damben ki ce in ba rashin wayo irin naki ba Meemah? Ai ba a dambe da talaka matsiyaci” Umma ta kalli Khaleesat tace “Ta yaya za ki fiddo kudaden a account din ki Khaleesat?” Khaleesat ta sauke idonta tace “Sai naje banki, bani da Atm card, kuma kudin bazai fita lokaci daya ba….” Momy na mata matsiyacin kallo tace “Sai ki tashi ki tafi bankin ai don wallahi kudaden nan baza su kwana a account din ki ba yau, da niyyar ki kin ci bulus tunda ubanki ne ya nema masa kudin ba” Khaleesat ta daga kai ta kalleta, ita har sannan ta kasa daina mamakin matar nan, kai tunda aka haifeta ma ita ba a taɓa shayar da ita ruwan mamaki yanda mahaifiyar Abdul ta shayar da ita ba, yau sati daya da sakin da Abdul yayi mata amma kullum in ta tashi sai ta zauna tayi mamakin uwarsa ganin abun take kamar Drama, ba ayi ranan da zai zo ya wuce da Momy bazata fado mata ba, bata taɓa san akwai mutane irin Momy a rayuwar nan ba, muryar Mama Zubaida taji tace “Ai ba zama zaki yi kina zazzare ido ba kamar barauniya, tashi za ki yi ki kama hanya ki tafi banki ki fiddo masu da kudadensu tunda ba gadon Abdul din gare ki ba kuma ba kudin tsohon ki bane, duk wani abu na rashin gaskiya dake da uwarki da kanwarta gaba ku ka basa ba baya ba, banda haka ta yaya za kuyi shiru da makuden kudadensa har Miliyan goma a account dinki? So ku ka yi ku danne kudin ko yaya? Don ma kun samu masu hakuri da kawaici da wasu ne idan ba a zo da motar yan sanda an tafi da ku ba ku ce bani ba, wannan ai rashin gaskiya ne da rashin tsoron Allah kiri kiri, duk kun yi mukus da bakin ku za ku cinye miliyan goma ga banza ta samu” Aunty Farida ta juya tana kallon Mama Zubaida, sai kuma ta nufeta tana cewa “Zubaida idan ban zubar maki da hakora a gidan nan yau ba ki ce bani ba, don kaza kazan ki akwai tsinannen da ya sako bakin ki? Uwarki muka yi ma rashin gaskiya ko ubanki?” Mama Zubaida tayi wani shewa tana tafe hannu tace “To yau kika saba Farida? Ai ke fitsararriya ce dama mara mutunci mara kunya shi yasa ga ki har yau duk kyan ki kin rasa mashinshini sai dai kiyi tuwo tuwo a garin legas kina hadawa da karuwanci, waye bai san wannan ba?” Aunty Farida zata cakumo Mama Zubaida Mama Shatu ta shige tsakaninsu tace “Ke yanxu Farida Zubaida sa’arki ce zaki dinga zaginta haka ta uwa ta uba don kawai tana kishiyar yayarki? Daga dai ta fadi gaskiya banda ɗan Adam baya son gaskiya?” Aunty Farida tayi wani wurgi da Mama Shatu sai ga ta a kasa timmm, tuni Mama Zubaida ta shige dakinta ta kulle kofarta da sakata tana cewa “Haka kawai ki shafa min bakin jini irin na ku? Allah ya sauwake in yi dambe dake Farida, ku je can ku ji da rashin sa’ar ku a rayuwa, ku kenan daga wannan iftila’in sai wannan bala’in, ko wani fitinar duniya a kan ku ya kare, daga wannan sai wannan, Allah kadai yasan laifin da ku ka tafka a kasar ku, kilan ma ta zina aka sami ke da yayar taki, ga bakin jini da rashin sa’ar ku ya shafi Malam ya talauce” Da kafa Aunty Farida ta hambare uban miyan da Mama Zubaida ke yi na abincin siyarwanta, miyar duk suka malale kasa, shinkafar ma dake cikin kwando ta kifar da shi a kasa tana zagin Mama Zubaida ta uwa ta uba, Mama Shatu ganin yanda aka yi watsi da kayan sana’an Mama Zubaida ya sa ta ja bakinta tayi shiru ta tafi gun nata miyan ta zauna tana cewa “Hakuri kawai za kiyi Farida, hakan ba dadi kam” Momy ta rike haɓa tace “Alhamdulillahi da na yi iya bakin kokarina na ganin ban hada iri da gayyar tsiya ba, ku kuga wannan tsiya haka kamar ‘yar tasha, ga talauci ga tashanci, Abdul ya so ja mana abun fade a dangi Allah ya takaita min abun, kuma ba dai kun ce kudade na banki ba, to zuwa yau da daddare in ga alert din Miliyan goma, in kuwa ba haka ba gobe da sassafe za ku gan ni a gidan nan ba kuma zuwan lumana zan yi ba, ai shi ramin karya kurarre ne, kuma ko kwabo daya yayi ciwon kai a kudaden nan wallahi sai an daure er ku…” Momy na kai wa nan ta bude handbag dinta ta ciro takarda dauke da account details dinta ta jefa ma Khaleesat sannan ja tawagarta suka yi waje tana cewa “Haka kawai Meemah zata ja min bala’i ta hada ƙashi da wannan iri na fitina, irin tsiya, to kiyi dambe da ita ki ce kin yi dambe da wa? Kina ganin yarinya kamar mahaukaciya, A’a wallahi Allah ya maki tsari” A haka duk suka fita daga compound din, Khaleesat taji hawaye ya cika idonta, Umma komawa dakinta tayi tayi tagumi ranta ba dadi, ita kam ta gode Allah da jarabawa iri iri, daga wannan sai wannan, Khaleesat ta dau takardan da Momy ta jefa mata ta juya ta shiga dakin Umma hawaye na zuba idonta, Aunty Farida kuwa bata fasa zage su Mama Zubaida da Mama Shatu a tsakar gida ba, Mama Zubaida taki fitowa kuma taki tanka Aunty Farida, Mama Shatu kuwa tayi tsit kamar bata san da wa Aunty Farida take ba, daga karshe bayan Aunty Farida tayi masu wankin babban bargo ta shige dakin Umma tana huci, Umma ta daga kai tana kallonta tace “Yanxu ban isa ince ki bari ki bari ba Farida?” Aunty Farida ko tanka Umma bata yi ba ta dau Hijab dinta ta saka tana kallon Khaleesat tace “Ki tashi ki shirya mu tafi bankin” Mikewa Khaleesat tayi tana goge idonta ta dau hijab dinta ta saka, a haka suka kama hanyar banki da Aunty Farida, amma suna isa bankin suka tarar an tashi aiki sai ran Monday don karfe hudu har da rabi a lokacin, Aunty Farida na kallon Khaleesat bayan sun fito bankin tace “Goben karfe nawa ne tafiyar naku?” A hankali Khaleesat tace “Flight din karfe daya zuwa Abuja, daga Abuja kuma jirgin yamma ne” Aunty Farida tace “Kuma bazai yiwu a daga tafiyar ba Khaleesat? Kinga banki dole fa sai Monday idan Allah ya kai mu” Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba, ita kanta she is just confuse bata san yanda zata yi ba. A haka suka koma gida kusan karfe biyar da rabi, Umma na kallonsu tace “An tashi a banki ko?” Aunty Farida bata ce komai ba ta cire hijab dinta ta nemi waje ta zauna, Khaleesat ta zauna tana kallon Umma tace “Banki sai ranan litinin, sun tashi yau” Umma tayi shiru bata ce komai ba, can tace “Kema kin san bai amshi kudinsa ba me yasa zaki yi shiru har na sati daya Khaleesat? Yanxu da kinyi magana tun yaushe za a san yanda za ayi a cire kudin a mayar masa kayansa, yanxu rashin mutuncin da suka zo suka mana makota na ji ina amfanin sa?” Aunty Farida tace “A’a ta min maganan kudin fa ranan Alhamis, a lkcn ma tayi zaton yau ne tafiyar ashe gobe ne, kuma kema kinsan Khaleesat bazata taɓa ko biyar a kudin nan ba tunda ba nata bane, kawai dai dama matsiyata ne yan iska daga Abdul din har iyayensa” A hankali Khaleesat tace “In ma an cire kudin an basu bazan iya tafiya babu kudi a account din ba, don baza a bari in shiga kasar ba, they wilk see i am not financially capable idan babu kudi a account dina, shi yasa ma ya bar kudin a account din all this years” Aunty Farida tayi shiru don bata ma san me zata ce ba, haka ma Umma da ta rafka tagumi tun shigowarsu, after a while a hankali Umma tace “Ni tsorona kar su dawo goben da suka ce bamu san kuma da me za su zo mana ba” Aunty Farida ta mike tace “Sai su zo su amshi babu tunda su yan iska ne” Daga haka ta fice daga dakin, Khaleesat taji hawaye ya cika idonta, Umma na kallonta a hankali tace “Kiyi hakuri Jiddah, wataran duk hakan zai zama labari, Allah ya bamu ikon cin jarabawan mu, in ma kin koma makarantar in ma baki koma ba duk yanda Allah yayi dai dai ne” Kai kawai Khaleesat ta gyada mata ta mike ta dau tsintsiya zata yi gyaran dakin Umma tana goge hawayen dake sauka idonta….*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

Back to top button