Halysaah Page 193 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 193…Bayan an kai Aunty Farida bangaren Hajja su Kilishi suka fito ana guɗa aka ci gaba da shagali a farfajiyar gidan sarauta, Khaleesat dai na zaune parlon Hajja sai kallon Small Mom din nata take ganin yanda tayi wani kyau na musamman, you just can’t stop staring at her beauty even though kanta na sunkuye, everyone’s attention was on her, wani rantsattsen Alkyabba ne akan tsadadden kayan jikinta, sai kirari ake jero mata a parlon. Bayan isha’i sai ga motoci uku da suka je dauko Aunty daga airport sun iso gidan su ma, wani dogari ya bude back seat din motar Aunty ta sakko tare da autar ta Baby dogarai dake wajen sai kirari suke mata, ta jira har aka sauko da Walid daga other car din aka zaunar da shi kan Wheel chair dinsa da aka dauko a booth, Jakadiyarta ma ta sauko daga motar karshe, Dogarai suna ta gaida Walid suna masa barka da dawowa amma ya sha kunu yaki amsa ma kowa yana hura hanci, turasa aka yi a keken zuwa cikin gidan yana bin kowa da harara, Aunty ta sauke ajiyar zuciya cike da takaici tana rike da hannun Baby ta bi bayansu, a ranta ta fara mamakin me kuma ake yi a gidan taji kidan kwarya na tashi da daddaren nan ga kuma hayaniyar mata da shewansu, sosai Aunty ta rame tayi baƙi ta fita hayyacinta, don babu kwanciyar hankalin shafa mai duk watannin nan da tayi tana jinyar Walid, wannan ne ma yasa ta saka Nose mask kar a lura da baƙin da tayi tunda dama hasken nata na Mai ne, don ma dai dare ne, suna shiga farfajiyar gidan wanda ko ina hasken fitilu ya haska tarrr, duk aka waigo ana kallonta da mamaki barin wanda basu san tana hanya ba, su Kilishi da wasu matan dake wajen suka nufota da fara’a suna mata sannu da zuwa, Kilishi har da rungumeta gam, sai kuma suka maida hankali kan Walid da alhini a fuskokinsu suna masa sannu da jiki, babu wanda Walid ya kalla cikinsu balle ya tanka har aka gungurasa a keke zuwa cikin gida, Hajiya Nafisah sai kauda kai take tana bobboye fuska tunda ta ga shigowar Aunty compound din, bata san ma tana hanya yau ba da tuni ta tafi ai, Aunty na kallon Kilishi da ta amshi jakarta ta nufi cikin gida tace “Me ake a gidan yau ne haka Kilishi?” Tuni Kilishi tayi gaba kamar bata ji ta ba, Aunty dai na biye da ita a baya tana amsa gaisuwan mutanen compound din gidan, ga wasu sun taso za su mata rakiya zuwa ciki, Aunty na shiga second parlor sai ga Khadijah, da gudu ta taho ta rungumeta tace “Momy me yasa kika kashe wayarki for days? Ina Ya Walid din? Ina Baby fa?” Aunty ta sauke ajiyar zuciya tace “Me ake yi a gidan naga mutane? ko Walimar dawowar Junaid?” Khadijah ta kasa cewa Aunty komai tana kallon mutanen da suka tsaya cirko cirko a bayan Aunty sun rakota tun daga waje, for the past 5 days da suka ji Mai martaba ya kara aure suke ta neman Aunty a waya su sanar mata amma wayarta a kashe yake, dama yawanci idan suna son magana da ita ta wayar Mukhtar suke kira sai ya bata waya, to tunda ya dawo suka dena samun ta a waya, ita kuwa Aunty baƙin cikin Sarki bai sanar mata dawowar Ajay ba yasa ta kashe wayarta kawai, don bayan tayi magana da Kilishi washegarin ranan da kanta ta kira Mai martaba amma har su ka gama magana sama sama bai sanar mata da dawowar Ajay ba, wannan yasa abun duniya ya taru ya mata yawa ta rasa tudun dafawa, ko ta ina babu dadi, ga Walid rashin kafafuwa sun sa ya dawo kamar mahaukaci ba dama tayi masa magana ko tayi masa gyara zai mata rashin kunya yayi mata kaca kaca, abinda yake mata yanxu ba shi da banbanci da zagi duk ya koma kamar ya haukace, Aunty kawai ta bada bikin dawowar Ajay ake yi a gidan taga mutane cike ta ko ina, tana kallon Khadijah da ta kasa ce mata komai tace “Ina Maryam fa?” Khadijah tace “Ta tafi gidan kawarta she said she can’t stand all this” Aunty tace “She can’t stand what? Me yake faruwa” Khadijah ta dake tace “Mu je ciki ki huta Momy, naga you look tired” ba komai yasa ta fadi haka ba sai saboda jama’an dake tsaye bayansu an zura masu ido da kunne, Hajiya A’isha ta shigo parlon da fara’a baki har kunne ta tafi ta rungume Aunty tana cewa “Lale lale, sannu da zuwa Fulani, ashe kuna hanya yau, maa sha Allah sannunku da zuwa sanyin idaniyan Sarki, Ina Walid din?” Khadijah ta kama hannun Baby ta juya ta bar parlon saboda wani takaici da ya rufeta, har sannan ita da yayarta Maryam basu dena mamakin yan gidan ba da yanda lokaci daya suka juya ma uwarsu baya suna murnan auren da Sarki yayi har da fiddo anko da gayyato manyan mutane, Hajiya A’isha tace “Hajja ma na gidan mu je ki gaisheta, gaskiya mun sha kewa Fulani, ni da nake cewa zan shirya zuwa dubiya ashe kuna hanya yau, shigowar ma ta dare kuka yi, Alhamdulillah sannun ku da dawowa” Aunty dai bata ce komai ba saboda bakin ciki, duk a kullace take da kowa a masarautar har Hajja da taki zuwa kasar da suke ta dubasu, sai ma ta ɓige da rashin lafiya, wanda ba komai yasa take rashin lafiyar ba sai don abinda ya samu Junaid, wato kiri kiri ta nuna tafi son Junaid akan Walid, yanxu kam tasan zamanta da kowa a duniya, hatta Jakadiyarta a yau zata sallameta ba sai gobe ba don bata bukatar ta kuma, ashe dama haka rayuwar take sai iftila’i ya sameka duk a juya maka baya, har suka isa sashin Hajja Aunty bata sauke Nose mask dinta ba ga masu mata rakiya na biye da ita a baya, nan taga jama’a zazzaune a parlon, har da dattijan aminan Hajja, ga kayan marmari iri iri a parlon, a wannan lokacin kuma su Aunty Farida suna daya daga babban dakunan dake part din Hajja ita da su Hajiya Zaliha, Aunty ta zauna kan Carpet ta sauke Nose mask dinta amma ba duka ba tana gaida Hajja, Hajja tace “Hafsat, kun dawo lafiya” Aunty tace “Alhamdulillah Hajja, ya muka same ku?” Hajja tace “Alhamdulillah, shigowan dare ku ka yi?” Aunty tace “Eh mun huta a Abuja har zuwa lokacin tashin Flight din mu zuwa garin nan” Hajja tace “Me yake samun wayarki ba a samun ki kusan sati daya kenan” Aunty tace “Wallahi na kan kashe wayar ne Hajja” Aunty ta juya ta gaida dattijan dake parlon kowannen su na tambayarta jikin Walid, Hajja tace “Ina Walid din?” Aunty tace “An tafi da shi sashinsa, Hajja barkanmu kuma da arziki na samu labarin dawowar Junaid cikin koshin lafiya, nayi farin ciki sosai, Allah Ubangiji ya tsare gaba, Allah kar ya maimaita mana wannan abun tashin hankalin” Hajja tace “Ai tun a can da kika samu labarin za ki kira kiyi wannan magana ba yanxu da kika dawo ba Hafsat…” Aunty tace “Wallahi babu wanda ya sanar min Hajja, da yake kinga ina kashe wayata ne, ko Mai martaba bamu samu min yi wannan magana da shi ba…” Hajja tace “Ikon Allah, amma kina da labarin an maki abokiyar zama ai” Aunty ta daga kai da sauri tana kallon Hajja babu ko kiftawa, lokaci daya taji bugun zuciyarta ya tsaya cak, ta sauke Nose mask dinta a hankali don har wani dishi dishi ta fara ganin Hajja da mutanen dake parlon, nan da nan wani azababben zufa ya fara keto mata a goshi, Hajiya Habibah dake zaune parlon ta gyara zama tace “Sai dai fatan Allah ya hada kanku ya kauda duk wata fitina da rigima….” Duk mutanen parlon suka amsa da Ameen ya Allah, Aunty ta kasa dena kallon Hajja kamar idanuwanta za su fito, zuwa yanxu zuciyarta ya ci gaba da bugawa amma da sauri da sauri, Gimbiya Firdausi ce ta shigo parlon da wasu manyan mata uku suna guda, tana kallon su Hajiya Habibah tace “Ina Amaryar za a mata rakiya zuwa sashin sarki” Hajiya Ladidi aminiyar Hajja tace “Tana daki, ki karasa ciki….” Gimbiya Firdausi ko lura da Aunty bata yi ba ta karasa dakin zata fito da Aunty Farida, Aunty dai na zaune ta koma kamar statue din da aka dasa a wajen don ko motsi bata yi, lokaci daya kanta yayi mata wani irin nauyi, kawai ta mike bata ko ganin gabanta ta fita daga parlon Hajja, direct bangaren Mami ta nufa, Mami na shirin zata tafi bangaren Mai martaba ita da Hajiya Shafa’atu don rakiyar Aunty Faridah sai ga Aunty, Aunty na huci tace “Da ke za a ci amanata Aseeyah?? In kowa zai min haka ban tsammaci haka daga gare ki ba wallahi, kuma dama da dadewa an gaya min kullin da kike shirya min don a min kishiya… Allah ya isa tsakanina dake da duk mutan gidan nan, kuma duk sai naga karshen ku wallahi” Tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka tana girgiza kai cike da bakin ciki tace “Allah ya isa, Allah ya isa tsakanina da ku, ni za a munafurta don bana nan ku zuga Sarki ya kara aure, don nasan wannan ba ra’ayinsa bane ra’ayinku ne, sarki bazai taɓa tunanin yi min kishiya ba, kuma wallahil Azeem duk sai na ga bayan ku ko zan yi yawo tsirara, ita kuma tsinanniyar amaryar zan ga ko zata iya zaman gidan sarauta har ma ta yi kishi da ni, koma wacece ita da ƙafafuwanta zata gudu wallahi” Hajiya Shafa’atu tace “Wa iyyazubillah, Fulani kan ki daya kuwa, ko kin fara hauka ne kike gaggaya ma mutane magana haka?” A mugun fusace Aunty na huci tace “Dalla rufe min baki munafukar banza kawai kema, yan iska gayyar tsiya, za ku san da Hafsat ku ke yi, ita tsinanniyar amarya bari mu ga ko zata iya zaman gidan nan” Mami uffan bata ce ba banda murmushin da take tana girgiza kai kawai, don sam ita bata iya cacan baki ba a gidan, Aunty na wani huci ta juya ta bar wajen xuciyarta na mata zafi, kai ko shirka aka ce tayi a wannan lokacin domin taga bayan yan gidan nan gaba daya da ita kanta shegiyar Amaryar da aka auro tana ji a ranta zata iya yi, har zata tafi bangarenta taga kawai gwara ta tafi bangaren Mai martaba idonta ya gane mata wacece wannan Amaryar da tayi gigin auran mata miji ta shigo gidan nan, shekara da shekaru tana kashe makuden kudi wajen hana Sarki kallon wata mace da sunan zai aureta, kuma kwalliya na biyan kudin sabulu, amma daga taje tayi jinyar ɗan ta a kasar waje, shi ne har abubuwan da take yi ya lalace tunda har Sarki ya iya auren wata mace, lallai ta cuci kanta Walid ya ja mata jaraba da masifa a rayuwarta, inda bata je jinyarsa ba da duk haka bazai faru ba, kamar mahaukaciya haka ta nufi babban parlon sarki, Su Kilishi ne da Hajiya A’isha, Hajiya Sumayya, Ummi duk a zaune parlon don tarban Aunty Farida a parlon sarki, ko wanne baki har kunne barin Kilishi dake guɗa bayan su Gimbiya Firdausi sun shiga da Aunty Farida zuwa Parlon sarki dake ciki, Gimbiya Firdausi ta fito daga second parlor din bayan ta kai Aunty Faridah, dai dai nan Aunty ta shigo parlon, duk ta dinga bin su da kallo ganin yanda suka cakare cikin ankon leshi tana huci cike da bakin ciki tace “Munafukan banza Munafukan hofi yan iska, har ni za ku ci amana ku munafurce ni? Allah ya isa tsakanina da ku wallahi” Mikewa Kilishi tayi tace “Hattara Fulani a bangaren Sarki fa kike gashi an shigo masa da sabuwar amaryar sa, kar ki ce za ki kawo mana hayaniya muna cikin farin ciki don Allah….” Aunty na jijjiga kai tace “Duk sai kun yi da kun sanin abin nan da ku ka aikata min, wallahi sai kun yi da kun sani” Tana kai wa nan ta nufi second parlor din Mai martaba kamar zata tashi sama, Mai martaba na ta kallon Aunty Farida dake zaune kan kujera kanta a kasa taki dago kai duk da kiran sunanta da yayi bayan fitar Gimbiya Firdausi, kamar ya samu TV haka ya dinga kallonta, sai ga Aunty ta shigo parlon kamar an hankadota, cikin rawan murya tana kallon Mai martaba tace “Ranka shi dade me na maka zaka saka min da wannan mummunan abu? dama sakayyar da zaka min kenan ina can ina jinyar ɗan ka kayi min kishiya? Idan baka gode min ba hidimar da nayi ma Walid na jinya ai baza ka saka min da kishiya ba, yanxu adalci kenan kayi min?” Sai a sannan Aunty Faridah ta daga kanta a hankali ta kalli Aunty, Aunty taji sauran maganganun bakinta sun makale a throat dinta ganin warce ke zaune parlon a matsayin kishiyar ta, babu ko kiftawa take kallon Aunty Faridah with shock written all over her face, Mai martaba bai ce mata komai ba instead ya nuna mata kujera alamar ta zauna, Aunty tayi wani murmushin takaici heartbeat rate dinta na rising ta juya ta fice daga parlon ko ganin gabanta bata yi sosai ta wuce su Kilishi. Daren ranan Aunty bata yi bacci ba saboda bakin ciki da takaici, wanda da yana kissa da ya kasheta kawai tsabar yanda yayi mata yawa, barin ma da su Khadijah suka bata labarin duk abubuwan da su Kilishi suka dinga yi, sannan suka gaya mata har Hajiya Nafisah sai da ta zo tarban amarya jiya da ita da kawarta, Aunty ta ci kuka ta gode Allah tana tunanin mafita, kawai ta yanke shawaran kama hanyar Nijar gobe da safe ta tafi nema ma kanta mafita ko nawa zata kashe, da tayi kishi da Faridah gwara koma wani sabon Allah ne aka ce tayi kawai tayi, in dai tana numfashi sai ta fitar da Faridah daga gidan nan bazata taɓa kishi da buzuwa ba, taji ta wani kara tsanar Khaleesat da duk danginta, yanxu kam bazata nuna komai ba, zuwa jibi kawai zata gaya ma sarki za ta garinsu don ta haka ne kawai zata shiga Nijar ba tare da an san ta shiga ba, ko tsirara zata yi yawo sai ta fitar da Faridah har ma da Khaleesat daga gidan…. Su Kilishi na zaune kan Carpet a babban parlon sarki da safe wajen karfe goma sha daya, kowa ya nutsu sosai saboda sarki dake Parlon da alama magana zai masu gaba daya, kana kallonsa zaka ga fara’ar dake tattare da shi a fuskarsa, babu wanda baya cikin parlon daga su Kilishi har ‘ya yansu, Mami ma na zaune da Khaleesat a kusa da ita, Hadiyah kuma tana kusa da Hajiya A’isha, Ummi ma na parlon ko ina yayi tsit, har Aunty ma na zaune parlon kamar dai babu komai ta ci kwalliyarta amma kana ganin idonta kasan bata yi bacci ba, ga wani shegen duhu da fuskarta yayi, Aunty Faridah ma na zaune kan kujeran dake opposite din wanda Aunty ke zaune looking Gorgeous and breathtaking, lokaci lokaci Sarki ke satan kallonta, ita dai kanta na kasa tana wasa da zobunan yatsun ta, wani sai ya zata Aunty Jakadiyar Aunty Farida ce, daga kusa da kujeran Sarki Walid ne zaune kan Wheel chair dinsa fuskar nan tasa babu walwala kamar ko da yaushe, kowa ya shigo da ƙafarsa amma shi sai dai a turasa yanxu kafafuwansa basu da amfani ji yake kamar ya hadiye zuciya ya huta, Mukhtar ma na parlon don shi ya gungura Walid zuwa parlon, su Kilishi dai duk sun san calmness din nan na Aunty ba na Allah da annabi bane sai satan kallonta suke, Khaleesat ta ɗaga kai for the third time ta kalli Aunty Faridah da bata son daga kai a Parlon, har sannan bata samu sun yi magana da ita ba gashi yau za su dau hanyar Amurka da Ajay for his treatment, Sun fi minti goma parlon sarki bai ce komai ba nan kuma jiran shigowar Ajay da Jay yake, Jay ne ya fara shigowa parlon da sallama Ajay na biye da shi a baya, Hajja kuma na bayansu tana biye da su, duk aka daga kai ana kallonsu, Walid ya wani zaro ido a tsorace yana kallon Ajay kamar yaga fatalwa ya fara tura Wheel chair dinsa da kansa yana komawa baya a mugun tsorace, Ajay dai kallonsa kawai yake yana tafiya a hankali, Hajja ma ta saki baki tana kallon Walid kamar yanda kowa na parlon ke kallonsa da mamaki, Mai martaba dake kallonsa shi ma yace “Are you okay Walid?” Walid na zare ido yace “Ba ya mutu ba, me ya zo yi nan? Ba ya mutu ba, kuna ganinsa kuwa ko ni kadai nake ganinsa” Gaba daya a birkice yake har sai da Mukhtar ya mike ya rike Wheel chair din nasa yace “Walid Junaid ne, shi din ne, he is not dead, he is alive” Walid ya dinga kallon Ajay daga sama har kasa babu ko kiftawa kamar idonsa za su zazzago waje, Su Kilishi suka ce “Allah sarki, kana can kana jinya baka san abinda ke faruwa ba ashe Walid, ai Junaid ya dawo cikin koshin lafiya bai mutu ba…..” Wani irin kara Walid yayi da karfi yana kallon Aunty cikin rawan murya yace “Wallahi Momy kin cuceni, kin cuce rayuwata, kina gani dai Junaid bai mutu ba ashe, Momy kin cuceni gashi nan bai mutu ba ni kuma na zama gurgu har karshen duniya….” Jiki na rawa Aunty ta mike ta nufesa da sauri zata rufe bakinsa ya wani hankadata har sai da ta fada kan Hajiya Sumayyah, Walid ya kara rushewa da kuka yace “Wallahi ke ce kika sa ni inyi wannan abun Momy, ke kika kawo shawaran kissa, ke kika sani in kashe Jawwad saboda title din Yarima da aka naɗa sa, duk ke kika goyi bayan plan dina har na sa aka harbe Junaid aka jefa sa cikin ruwa a Lokoja, to gashi nan kin ga bai mutu ba kuma da kafafuwansa biyu ni kuma kin cuceni na zama gurgu har karshen rayuwata, wallahi kashe kaina zan yi bazan ci gaba da zama a duniyar nan ana tura ni akan keke ba, Momy kin cuce rayuwata, ga Junaid nan da lafiyarsa bai mutu ba”


