💧💧SIRRIN ZUCI……..
💞
Na Feedohm💞
1 to 2
البسم الله الرحمن الر حپم
================= Gidan Novels =====================
Lumshe Ido yayi sannan ya budesu tar bisa kan wata karamar yarinya dake zanen yar galala ….
Fito yayi da bakinsa a hankali ….da sauri yarinyar ta kallo sama tana murmushi tare tsalle tana daga mashi hannu …
Iska ya huro mata …sannan ya daga mata hannu ….itama hannun ta daga mashi ….
Wata tsohuwa ta fito daga wani karamin gida wanda duk unguwar babu talaka sama dasu ….
Meenalle …Meenalle. ..ta fara kwada kira ….
Yar karamar yarinyar ta juyo da sauri tana bata fuska …cikin shagwaba tace …..Kai kaka ke kullun sae ki batawa mutun suna …nasha fada maki Meenal fa ake cewa? …
tsohuwar tace …to naji sarkin hakuri zo muje ki sayo mana kwaki ko bakijin yunwa?
Saman benen ta kalla. ..har yanzu yana tsaye ita yake kallo …daga mashi hannu tayi tare da langwashe kai …sannan taja hannu tsohuwar suka koma gida ….
Kudin ta karbo sannan ta sako hijab ta fito …tana zuwa bakin kofa taja birki tare da dafe kirji ….hal ka ban tsoro …ta fada hakoranta waje …
Hararanta yayi…ke kuma sarkin tsoro ko …ya fada yana gyara mata hijab dinta …
Kai …aikena fa akayi …ta fada tana neman cire agogon dake makale a hannunsa …
Hannunsa ya janye don karta bata mashi…sannan yace …Me zaki sawo?
Baki ta tabe tana kokarin wucewa sannan tace …kaini Kaka tace kabar sawo man komae ..wae ku yan yankar kaine …kuma tace wae kaina zayayi tsada …
Dariya ya sake a hankali kafin yace mata. ..ni kuma kakata tace man indae mace na yawo to kasa ake rufeta …ya fada idonsa na kallonta …
Ido ta waro cike da tsoro …da gaske Mai kamshi?
Ganin ta tsorota ya saka yace ..eh mana ai bana so a rufeki shiyasa ma nace ki fada man in sawo maki …
Kamar jira take ya rufe baki tayi saurin mika mashi naira hamsin din da ta gama nannadewa …
Amsa yayi ..yace me zaa sawo. ..
Kwaki na talatin sae sukari na ashirin …ta fada a hankali ..
kai ya girgiza kana ya tafi. ..har yayi nisa ta kwala mashi kira…ya juyo. .tace …Dan Allah kace a maka arha ..kuma kayi sauri kar kaka tace na dade …
Kai ya daga mata sannan ya tafi ..
Baifi minti goma ba ya dawo rike da manyan ledoji. ..tana hangoshi ta tareshi tana dariya …
Duka ledojin ya mika mata ya juya …tayi saurin janyo hannunsa ..to ka tsaya mana na duba inda canji ba sae ka bani ba …ta fada tana bata rai ..
Dariya ta bashi sossae ..ya dawo suka shiga zauren gidan …
Zama tayi kasa ta zazzage kayan tsaf …ido ta waro lokacin da ta daga katon gwangwanin madara ..tace …Nawa ka sayo wannan …ta fada tana kallonsa ..
Naira biyar …ya ce idonsa yana kallon karamin bakinta …
Uhmm saura arba’in da biyar kenan ta fada …biscuit ta cigaba da fitowa da chocolate sae ledar cos cos da sugar sae lemuka kala kala …duk wanda ta daga sae ta tambayeshu kudinsa …daga wanda zayace biyu biyar sae na biyar ….har ta fito da tiyar garin kwaki …
Wannan nawa yake? …
Kura mata ido yayi ..sannan yace …wannan a shagon wani abokina ya bani su …
Dariya tayi kana ta maida kayan tana kallonsa …to bani canjina …ta fada lokacin da ta gama maida kayan …
Ido ya waro …wane irin canji kuma?
Harara ta balla mashi …sha biyar mana. .ba yanzu mukayi lissafi ba naira Talatin da biyar ka kashe …
Murmushi yayi ..ya lalubi ajihunsa …babu ko naira 500 bare kananan canji. ..
dubu daya ya mika mata …ta make kafada …ni canjina zaka bani ….ta fada a shagwabe
Dukawa yayi dae dae tsawonta ….kiyi hakuri Meenatou …banda canji…kinji. ki bari anjima zanyi canji sae na baki ….
aa Ni dae ban yarda ba ….muje a canzo su …ta fada. .
To naji shiga da kayan sae ki fito muje. …ya fada idonshi a lumshe …
Ka gudar man da canji …tace
Hannunta ya kamo …baran gudu ba ….ya fada har lokacib idonshi a rufe …
Shiga gidan tayi tana waigenshi …aje kayan tayi ta fito da gudu …kaka nata kiranta. ..amma ce mata tayi ….Kaka Kawata ta mutu ake kiranmu muyi mata addua ….
Feedohm💞
.
💧💧 SIRRIN ZUCI……
💞
Na Feedohm💞
3 to 4
Suna fitowa daga zauren Gidan …dae dae lokacin mota ke horn kofar gidansu ….da sauri ya kalli motar sannan ya kalli kofar get din …babu alamun mai gadi zaya bude ….hannunsa ya zame ya nufi kofar zaya bude …
Ka tsaya wallahi duk wayonka bara ka gudar man da canji ba …ta fada lokacin da ta bishi da gudu …
Murmushi yayi a ranshi yace …Meenatou kenan ….
Gate din ya bude sannan ya matsa jiki. motar …na ciki ya rage glass din dauke da faraa …yace
Ma’aruf …ina mai gadin ne …
Lumshe ido yayi wanda ya zame mashi dabi’a sannan yace …wallahi ban san inda ya tafi ba …amma ko ma meye na tabbata baya kusa. …ya saka hannun ya bude motar ….
Dae dae lokacin Meena ta iso gurin tana sheshsheka ….
Hararanshi tayi …sannan tace ..wallahi yau ko’ina zaka shiga sae ka bani canjina dan ba asi ta yayeni ba …na gaji mutun sae wayau ..dama ranar nan na biyoka canjin Biyar baka bani ba to yau sae ka hada man da ita …don na gaji da wahala. ..ta karasa maganar kamar zatayi kuka
Mutumin yafito cikon motar dauke da murmushi …ya dafa kanta yace …Mamata canjin nawa zaa baki ?
Dariya tayi kana tace …Abba canjin sha biyar ne biyar din wancen satin dana biyoshi amma ya gudu wae bayya da canji …..Au na manta Abba Ina wuni…
Dariya yayi yace …dama mamana ina zaki tuna idonki ya rufe da kudi …Ma’aruf bawa mamana canjinta….
Murmushi ..yayi yace ..Wallahi Abba banda canji kuma kasan halin Meenatou …
Shima dariyar yayi yace …Mamana bata da wani hali mara kyau …mu shiga gida sae yasamo Maki Canjinki ko mama..nima na gaji da cinye maki kudi kullun ….
Dariya ta sake tana kallon Ma’aruf din …hannunta Abba ya kama suka shige ciki…
Da Sauri ta karbe kayan da wata kyakykyawar mata ta fito dashi daga kitchen …sake mata tayi tana murmushi …
Yau Mamanmu ce a gidan mu …Ta fada tana dauke da murmushi. ..
Meena tayi dariya sannan tace …Eh man ae mai kamshine ya cinye man kudi naira ashirin har da ta rannan …
Dafe kanshi ma’aruf yayi …sannan yayi sama da sauri yana fadar ..Wayyo Meenatou kamar na cinye maki Million bara dole na samo maki canjin ki yanzu. .
Matar tayi dariya tace …Sae kuwa ka biya mamanmu canjinta yau ….zo kici abinci kafin. ya samo maki ….
Girgiza kai tayi tana murmushi…na koshi..
Abba ne yace. .. ai kuwa na kusa batawa da ke mamana
Da Sauri ta matsa kusa dashi …Abba me nayi …
Matar ta tareta tace …da bakicin abinci kullun a gidansu Mai kamshi ..
Ido ta waro …In ci abinci ku sayar dani ?
waye zaya sayar dake …inji Abba ..
Ni dae ba ruwana …ta fada sannan ta fara kwalawa Ma’aruf kira …Matar ta nuna mata inda yake …
Ta kuwa shige dakin da sauri …lokacin da kyar ya samo naira sha biyar …ya mika mata …sae da kyar ya samu ta karba shima da kashedin da ta gansho sae ya biyata ko kuma ta cire mashi agogo …
To kawae yace mata don so yake ta barshi da wannan masifar canji ….sae da ya hada mata da sweet sannan ta tafi tana mita..
Bayan ta fita ya dafe kai. ..sannan ya kwanta saman gado…shi kanshi yasan yau duk inda ta ganshi sae ta nunashi tana binshi canji …iska ya huro …sannan yace …yau ba abunda zaya saka na fita indae ban samo naira biyar ba ….idonshi na lumshe fuskar dauke da murmushi …bacci ya daukeshi ..
••°°
Kunnenta Kaka ta rike …wane shegene ya kiraku kuyiwa gawa addua …
Ido ta waro …wallahi Allah kaka wa …
Bakinta ta buge….rufe man baki ke yanzu ko dabbobin gidannan ai sun bar kama rantsuwarki ..
Baki ta turo waje …tana kefta idanuwa …
Ma’aruf kika bawa kudin ya sawo maki ko? ….ta tambayeta tana kallonta
*Feedohm*💞.
💧💧SIRRIN ZUCI……
💞
Na Feedohm💞
4 to 6
Ido ta waro waje …Hauka nake da zan bashi…ae in fada maki kaka wani shago naje mai saukin tsiya komae naso naira biyar suke sayowa ..su fa ko daga kasar Dandiyana suke siyo kayansu …ta karashe maganar hakora bude ..
Gwagwanin madara ta dago tace ..naira nawa kika sayo wannan ? …
Shiru tayi tana tunanin nawa ma Ma’aruf yace mata …da sauri tace Naira biyar …ta fada tare da nunota da hannu …
Kwafa tayi sannan ta fito da wata naira biyar din ta miko mata …kije ki sayo man irinta karba. ..
Babu tantama ta karba ta fice da gudu …daga zaure ta tsaya tana hangen saman benen gidansu Maaruf …ganin baya nan ya saka ta sake murmushin jin dadi tare da fadar …Allah ya soni da yanzuma sae yaci zalina. ..ta nufi babban shagon dake unguwar …
Cikin saa tana zuwa taga gwangwan madarar jere …ta washe baki sannan tace a miko mata …aka saka mata a leda …ta fito da naira biyar ta mika mashi ..
Mai shagon ya karba yace mai zaa baki da wannan …
Rufe ido tayi sannan tace a hankali ..Mai kamshi Ma ya iya cuwa cuwa ashema har da canjina yace naira biyar to bara na koma ya jama kanshi sae ya fito man da kudina …?
Sanna ta nuna wani karamin sweet aka miko mata …ta juya …mai shagon yace ke kawo kudin madarar mana ..
Wani kallo ta mashi sannan tace ..wanda na baka fa ..
Yaushe kika bayar …ya tambayeta …
Malan Dallah biyar din da nabaka fa ka miko man canjin alawa ko bashi kake bina ..
Tsaki yaja ya fizge ledar sannan ya nuna mata hanyar fita ..fice ki bawa mutane guri ..sakaran banza ..Ubanwa ke sayar da katon Gwangwanin peak naira biyar ..fice dallah …
Kuka ta sake gurin …wallahi ba inda zanje sai kun biyani kudina ai bani nace ka tambayeni me zaa bani da biyar din ba …gashi ka saka na kashewa kaka kudi kuma ka hanani abunda na saya .kuma dazu anan aka sayeta naira biyar din …ni sae ka bani kudina kuma wallahi baran sake siyan komae ba anan …
Cikin tsawa yace …zaki fice ko sae naci ubanki anan …kaga marar kunyar yarinya
Tsaye tayi gurin taki wucewa sae da ya dauko bulala ya biyota a guje sannan ta wuce tana kuka …..
Tana shiga dakin ta fada saman cinyar kaka tare da sake kukan da babu digon hawaye ko kadan a idonta ….
Cikin kula tsohuwar tace….Me kuma ya faru Meenalle. ..
Kafa ta fara haurawa tana fadin …ba kudin da kika aikeni bane naje shagon da zan saya babu sae na fito wata akuya ta fizgesu daga hannuna …
Murmushi tsohuwar tayi ..duk da tasan karya take….kuma ta tabbata bara ta kashe kudin ba ..sae dae ko faduwa sukayi …
Ta shafi kanta …to yi shiru mana Aminatuta …dan akuya ta fizge biyar ba sae kiyi hakuri tunda kin san dae baran maki fada ba …banda abunki nima na wuce irin akuyar data fizge naki ta fizge hannuna …yi shiru Meenalle share hawayen mana …
Kin shirun tayi sae ma sabon salon turje turje da ta sake ta hambare duk inda taso ido rufe kuma ko hawaye babu ….
Saukar tsintsiyar kwakwar da taji a kafarta ya saka ta bude idonta da sauri tare da kallon kafarta. ..ganin ledar garin kwakin Da Ma’aruf ya sayo mata ta fashe gashi duk ya zube a kasa ya saka ta gane bannar da tayi ….
Lokaci guda ta tuno da zafin tsintsiyar kwakwar kaka ta zuba da gudu ta fice daga gidan …
Tana jin Kaka na kiranta amma bata tsaya ba ta fice daga gidan …
°°••
Tulin kayan wankine jibge gaban Yar mashiyar budurwar da bata wuce shekara 17 ba ….ta saka hannu tana daga kayan a yatsine tana kauda fuska gefe …
.
Wata mata ta fito daga wani karamin daki …tace Haba luba kiyi sauri ki wanke mashi mana su zaya saka …
Yatsina fuska tayi tace …ni gaskia innarmu baran iya wankewa baba wannan kayan ba …kaya sae wari suke …ga kudi a kai mashi wanki ….ta mike tsam ta shige daki …
Ficiciyar Sallamar Meena ne ya katse mata hanzari …
Matar ta kalleta da faraa ….Su Aminatu ne a gidanmu …
washe baki tayi tana fadin ….Eh Man inna ..fada mukayi da Kaka na taho nan …Mamata tana ciki? .ta tambayeta.
Tana ciki Aminatu…..
Da gudu ta fada dakin tana kwalawa Mamanta kira ….ta zaune saman darduma tana addua ….ta juyo tana kallonta har ta karaso …bata tsaya gurin mamar ba ta wuce gurin wani dan karamin tebur ta dauki ayaba ta saka baki tare da lumshe ido ….da sauri ta budesu tace ..mama karki ga na rufe ido ba fa ki dauka wani abu ..ni ba Mai kamshin unguwar mu ba.. nake kwaikwayo kawae nayine naga ko zai man kyau …kinsan dazu sae da yaci man zalin biyar muka rabu …shi wannan shegen taurin bashine dashi kamar babansu Luba .. ….
*Feedohm💞*.
💧💧 SIRRIN ZUCI….
💞
Na Feedohm💞
7 to 8
Sallamar babansu luba ce ta katse mata sauran maganarta …..da sauri ta koma bayan mamarta….
Ya shigo fuska daure …Idonshi na kan Meena …ya Nuna Nuna mamar da Hannu cikin daga murya yace …Banda iskanci Rabi kina ji ina kwala maki kira kikayi shiru …
Dukar da kai tayi …tace wallahi Malan banji ba kayi hakuri …
Yace …baki ji gidan ubanwa ba …sau nawa ina kiranki dan rashin mutunci har muryata ta dashe ..
Meena tace. . .to tunda bata ji ba kuma ba shikenan ba . kai babansu Lubar nan ka cika masifa …ko dan baka da ko sisine ? ….
Mamar tayi saurin zaunar da ita tare da buge mata baki ….
Girgiza kai yayi yana fadin …owo Rabi har kin haifi diyar da zata fadawa mijinki magana ..to nima ina da yaron da zai mata dan banzan duka ….ya fice daga dakin
….Dafe kai tayi idonta cike da hawaye tace …Nashiga Uku Aminatu waya ce ki zo gidannan …ba na hanaki zuwa ba …kinga yi maza ki fice ki koma gidan Kaka yanzun nan ….
Ai kuwa da gudu ta fice dae dae zaune Musa( _babban dan Malan_)Ya shigo rike da wata doguwar bulala ..tayi saurin boyewa bayan kaure. ..yana shigewa gidan ta fice da gudu ta koma gidan Kaka …..
••°°°••
Wallahi Malan Kaka ce ta aikeni shi yasa na makara …tafada tana daga hannu …
Babu Abunda Ya dameni da wadda ta aikeki ita bata san lokacin Islamiyya ba …?
Tace .. Lah Malan ai lokacinsu babu islamiyya ta tsofa ba ..
Yace Aminatu Abubakar ki matso ba bugeki ki shiga aji …don yau ba wani da uzurinki da zan karba ….
Matsowa tayi …yana daga bulalar ta matsa da sauri..hannu ya saka ya fizgota tare da zuba mata bulala a baya. ….wani tsalle tayi ta shiga cikin babbar rigarshi ta aza mashi cizo a kirji …..
kokarin fiddota yake amma taki sakinshi …da kyar ya samu ta fito lokacin ta sake mashi cizo yafi 5 .. shi kadae yasan azabar da yake ji …idanuwansa sunyi jawur. ..yana ganin ta fito ya shige toilet din makarantar da sauri ya cire rigar …duk inda ta cijeshi ta fasa shi …wani karamin kwalla ya goge tare da yi mata Allah ya isa …duk islamiyyar babu mai son dukan Meena saboda irin wannan abun shima yau tsautsayi yasa Headmaster yace yayi taren yan makara …
Sae da ya gama kananan kwallan shi sannan ya fito daga toilet …Headmaster ya ganshi yace …Ustaz Har ka gama dukan yan makaran ..
Harara ya balla mashi ya wuce office abunshi ….daga cikin office din yana hango Meena nata wasanta …Allah kadae yasan iya Allah ya isar da ya ja mata …bai kuma fita ba har aka tashi …
••°°°••
Ganin motar gidansu Ma’aruf ta fito ya saka ta karasa gurin da sauri tana washe baki. ..
Abba ta gani ciki …yana ganinta ya sauke glass din …ta gaidashi …ya amsa mata cikin Faraa .
Abba kaga Mai Kamshi har yau bai biyani bashina ba …ta fada tana bata fuska ..
Dariya yayi yace …to ae mamana Mai kamshi baya lafiya. ..
Ido ta waro …me ya sami Maikamshina ? ta kareshe maganar kamar zatayi kuka. ..
Murmushi yayi ya fito daga motar tare da jan hannunta suka shiga gidan …Mamanshi bata falo suka wuce dakinshi ….yana kwance yana bacci …tana hangoshi ta janye hannunta daga Hannun Abba ta duka kusa da gadon da yake …tana kallon fuskarshi …fita Abbah yayi …
Hannunsa ta damke tana kallon fuskarshi .sajen dake kwance a fuskar ta taba …..Mai kamshi …ta fada a hankali …
Idonsa yana rufe amma ba bacci yake ba ….ta kara kiran sunanshi. ..ganin bai amsa ba ya saka ta sake mashi kara dae dae kunnenshi …
Da sauri ya bude idon yaji karar har cikin kanshi …dariya ta sake …sannan ta shafi wuyanshi …saurin dauke hannunta tayi tana kallonshi shima ita yake kallo ..
Mai kamshi jikinka Zafi ..ta fada kamar zatayi kuka ..
Daga mata kai yayi tare da lumshe ido …itama idon ta lumshe sannan tace. ..Amma mai kamshi wannan ciwon naka har da taurin bashi ke kara mashi yawa …
Dariya ta bashi yayi saurin janyo drawer dake jikin gadon ya fito da sabuwar naira biyar ya daura mata a hannu …
Baki ta washe tace. ..ka gani ko Mai kamshi yanzu ko mutuwa kayi babu bashin kowa akanka …lokacin guda idanunta suka ciko da kwalla tace …kuma ko bana so ka mutu Mai kamshina …ta fada lokacin kwallar ya gangaro kumatunta …
*Feedohm*💞
💧💧SIRRIN ZUCI…..
💞
Na Feedohm💞
================= Gidan Novels =====================
9 to 10
Zaune ya tashi tare da janyota ya zaunar da ita bisa cinyarshi ya share mata hawayen
Yace …ai mutuwa dole ce Meenatou ..
Girgiza mashi kai tayi ..aa ni bana so ka mutu …
Shafa kanta yayi yace …to kiyi addua meenatou Allah ya bamu tsawon kwana kinji ko …Na furta maki Sirrin Zuci …mai dadin saurare…
Film din dake kunne a dakin ta maida hankali gareshi …..zuwa can ta mike tana washe baki …tace Mai kamshi kaci abinci …
Film din ya kalla shima ciki wata budurwace take bawa saurayinta abinci abaki …murmushi ya sake ya girgiza mata kai alamar aa …
Ta fice …zuwa can sae gata da abinci cikin Plate ya kalleta da mamaki yace …ina kika samo …
Baki ta washe gurin Mamanku naje nace zaka ci abinci ta bani …
Zama tayi saman cinyarshi …tare da debo abincin a spoon ta mika mashi …ahankali yace ..bana cin abinci da spoon sae da hannu Meenatou
Ido ta waro ..Kai mai kamshi dazu dana zo cizon malan na taba hammatarshi kuma wari take ….
Lumshe ido yayi ya bude …wani abu ya tokare mashi makoshi baya kaunar Meenatou ta taba wani namiji duk da tana karama ….
Shiga toilet ki wanke hannun ki fito …ya fada a hankali …
Sae da ta bashi abinci sannan ta fice …ya bita da kallon ….gida ta koma ta sakewa Kaka kusa sae tazo ta gaido mai kamshinta baya da lafiya …
Da farko kaka cewa tayi bara tazo ba amma da taga masifar ba mai karewa bace ta ziro Hijab ta biyota …
Mamar Ma’aruf taji dadi sossae sanna ta kara son Meena a ranta …haka shima Ma’aruf murmushi kadae yake yi tare da lumshr ido har suka tafi ….
Kasancewar an koma Boko kullun kafin ta tafi makaranta sae ta shiga ta ganshi …ta bashi abinci .. sannan take wucewa haka idan ta dawo sae ta shiga ta bashi abinci ko da kuwa zata dade bata dawo ba to zaya jirata ….Abincin Rana tare suke ci …tana bashi tana ci …amma da anzo gurin nama nanne zancen zai canza salo …don sae taci Yanka 4 kafin ta bashi guda …idan kuma kazane to sae ta cinye tsokar sannan tace ya gashi ya cinye …sae dae kawae yayi murmushi. yace ya koshi. ..haka zata sake mashi kuka sae yaci …hakanan zaya danci abinda zai iya ya bar sauran kashin …Har Allah ya bashi lafiya ….
••°°
Kaka nidae wallahi wannan wanke wanke wanken yayi man yawa …ta fada cike da shagwaba …
harara ta dalla mata …sae ki nemi wanda zaya tayaki …
Sallamar Ma’aruf ce ..yasa ta sake Murmushi tana cewa …Yauwa Maikamshi zoka tayani mu gama na fada maka wata magana
Kaka tace ..bara ya tayaki ba dan kaniyarki ….Ma’aruf ko za zauna ka kyaleta …ta shimfida mashi tabarma ..
Murmushi yayi yace …barta na tayata Kaka naga kayan sun mata yawa ita kadae. ..
baki ta washe …Yauwa mai kamshina ..kayi wanke wanke sae in maka dauraya nafi iya dauraya kai kuma kafi iya wanke wanke …
Yana wankewa tana daurayewa har suka gama ..kaka na kallonsu cike da fata kala kala aranta ….
Bisa tabarmar ya koma ya zauna …zonan Meenatou …ya fada a hankali. ..
Kusa dashi ta koma ta zauna ta harde kafa tana kallonshi ….
Wani karamin zobe na gold ya fito daga cikin jikkanshi …ya zura mata a hannu …
Kallon zoben take ..tana kallonshi ..ni ka sawo mawa ?
Daga mata kai yayi …ta kare washe baki tace …. don kar na fadawa kaka kace idan aikeni na dinga karbowa kyauta a shago …
Ido ya lumshe sannan yace aa …kinsan Zuciya ?
Lallae ma Mai Kamshi tun muna primary one muka ganin zuciya ….
Yace Good …to ki aje wannan itace zuciyata …
Dariya take har da kwalla …kai kuma wannan itace zuciyarka …to nima bara na baka taea zuciyar …ta kwance dankwalinta ta zare ribbon din dake kanta ta mika mashi …
Amsa yayi yana daga shi …sannan yace na meye wannan …
Hararanshi tayi sannan ta saka hannu zata fizge ….to bani abuna tunda baka so …
Aa sorry Meenatou ina so mana …wannan shine zuciyarki ?
Eh man mamana ta bani shi da sallah …ina sonshi …
cikin jikkarshi ya saka sannan ya mike ya ma kaka bankwana ya wuce ..
*Feedohm💞*
💧💧 SIRRIN ZUCI…..
💞
Na Feedohm💞
11 to 12
Wani karamin yarone ya shigo office din headmaster yana kuka rike da ya gaggen littafi …
Ustaz ya kalleshi Yace..me ya faru kake wa mutane kuka…
Yaron yace .Meena ce ta yaga man littafi …
Wani wahallalen miyau ya hade tare da shafa kirjinsa …sannan yace …Jeka Allah ya saka maka …ya juya yaci gaba da duba lttafin dake gabanshi …
Wani sabon malamin da bai dade da zuwa ba ya kalli Ustaz yace ..Haba ustaz wane irin Allah ya saka mashi …ya nuna yaron tare da fadin ..jeka kirata. .
Bai fi minti biyu ba ta shigo da uwar sallama. …Sabon malamin ya ce ta rage tsawonta …
Zama tayi tsakar office din ta mike kafa ….tsawa ya daka mata. ..babu shiri ta yi kneeldown din …Kallon Ustaz tayi tace …Ustaz Dan Allah kayi hakuri shi ya fara daukar man goriba ya cinye ..
Da sauri Ustaz ya juyo yace. .Meena Abubakar bani na kiraki ….ya kakkabe riga ya fice daga office din …
Sabon malamin ya bata punishment din wanki toilet din makarantar duka tare da share ko wane glass. …tana kuka ta gama ko aji bata koma ba ta wuce gida …
Sae da ta bari lokacin tashin malamae yayi saboda suna tsayawa meeting kullun …lokacin mangrib tayi kowa na sauri yaje masallaci sannan ta nufi hanyar islamiyya. ….tun kafin ta isa ta cika jikkarta da duwatsu …
Wani lungu mai duhu ta samu ta shige wanda ta san dole tanan sabon malamin zaya wuce …Cikin saa sae gashi ya taho kanshi na kasa yana tafiya ….katon dutse ta samu ta saita keyarshi ta jefa mashi ….dafe gurin yayi ya juyo yace …Uban waye ke yo jifa …bai rufe baki ba ya kara jin wata a goshinsa har sae da jini ya zubo ….
Tana ganin ya dafe gurin da sauri ta fito daga maboyarta ta kukan kura tayi ta shige cikin rigarshi …rudashi tayi ta dinga sake mashi cizo tare da yakushi ta ko ina …
Da kyar ya samu ya babbareta …tare da zubawa da gudu …don duk tunaninshi aljanace ….
••°°°
Ustaz ya kalleshi cike da tausayi yace …Malan isiya sae naji headmaster yace ka samu hadari jiya a hanyarka ta komawa …
Sosa kai yayi yace …wallahi kuwa Ustaz ina saman mashin wani mai mota ya bangajemu …
Meena dake tsaye ta kalli ustaz tace. .Malan meye hukuncin mai karya…
Dan wuta …ya bata amsa don yanzu tsoronta yake ji …
to Malan isiya ma dan wutane …jiya gabana akayi …wata aljanace ta rotsa mashi cizo sannan ta shige a rigarshi ta yakusheshe ta ruga …
Wata dariya Ustaz yake har da dafe cikin sannan ya kalli malan isiya da sae yanzu ya gane wannan shegiyar yarinyar ce ta masa rashin mutunci …
Ustaz yace. …Malan da mai motar ya bugeku sae ka fada kan aljanar ?
Shiru yayi …yana nan tsaye kuma duk yaron da yazo wucewa to Meena zata tareshi ta bashi labarin malan yayi karya yace hadari yayi alhalin aljana ce ta shige rigarshi ta yakusheshi …wani ma har yadda aljanar tayi masa take nuna masu da bango …. yana tsaye da uwar palasta a goshi …cikin dubara ya sulale ya fice daga islamiyya….Tun daga lokacin malan isiya bai kuma dawowa ba …
••°°°••
Mai kamshi ina irin wannan alawar daka sawo man jiya …ka tunata …ta fada rike da hannunshi tana murmushi …
Daga mata kai yayi …na tunata ..
Yauwa to ita zaka kara sawo man …ta mika mashi wata rabin naira biyar …
Dan Hararanta yayi …waye zaya amshi wannan rabin kudin ?
*Feedohm💞*.
💧💧 SIRRIN ZUCI……
💞
Na Feedohm💞
13 to 14
Hararansa tayi …Kai baka san yarda ake cuwa ba …ai murdeta zakayi ka mika masu da sun baka sae ka rugo da gudu. ..
Murmushi yayi yace. ..Idan Allah ya kamani fa ..
Washe baki tayi tace …ai zan maka addua ya yafe maka tunda yana saurin amsar adduar mu …
To kawae yace mata ya juya ya koma cikin motarshi ya fice daga unguwar …har ta bar ganinshi tana daga mashi hannu …nan ta zauna tana zanenta a kasa. …sae da tayi budu budu da kasa sannan ta koma gida ….
Tana shiga kaka tace sae tayi wanka….rantsuwa ta hauyi wae mamarsu Ma’aruf ta mata wanka daga gidansu take ….kaka tace bata yarda ba. ….
Turo baki tayi tace …ni wallahi na gaji da wannan cacar kullun wanka …
Kaka ta rike baki tace. ..yanzu dan kaniyarki Meenalle wankan ne wahala ….to ai kuwa indae kina nan gidan ki dinga irin wannan wahalar ..tashi tun kafin na taso …
Mikewa tayi ta nufi hanyar zaure tana amsa sallamar karya …Girgiza kai kakar tayi tare da fadin Allah ya shiryaki Meenalle ….Zaure ta ci zamanta har sae da kaka ta fara gyangyadi sannan ta dawo ta kwanta kusa da ita …
••°°°••
Kai ta daga tana kallon benen gidansu Ma’aruf sannan ta fito tana tafiya tana kallon gidan ko zaya fito ya bata sakonta ….har ta bar unguwar bata ga kowa ba …..Ledar dake hannunta ta saka hannu ta fito da biscuit daya ta fasa ta ci rabi ta maida rabi ta kulle …
A bakin kofa ta tarad da Malan Musa mijin mamarta zaune ya kallon masu wucewa ….gaidashi tayi yaki amsawa. ..har ta shiga zauren ta dawo baya ta tsaya gabanshi …
Angon mamarmu ina wuni _Kamar yadda taji wasu mutane na kiranshi da can baya_…ta sake gaidashi ..
Ko inda take bai kalla ba …ta sake cewa ..kodae mamansu Luba ta ci maka Uwa shi yasa ka dawo nan ka zauna …ta kefta ido daya …
Cakumota yayi ya hade da dakalin da yake zaune …Uban me kikace ….ya fada da karfi. .
Wani mutumin dake zaune nesa dashi ya taso ya amsheta tare da bashi hakuri sannan ya jashi suka tafi kasuwa dan gudun abunda zaya je ya dawo …
Miyan wahala ta hade sannan ta ida shiga cikin gidan ….
Musa Ustaz ….ta fada lokacin da taga musan zaune tsakar gida daga shi sae gajeren wando ..kusa da Luba
Harara ya banka mata tare da yin kwafa ….
Kara cewa tayi …su musa da luba ba magana. ..kunyi zaune kamar turmi …
Zanci Ubanki Meena …Luba ta fada tare da tasowa …dakin mamarta ta fada da gudu …amma bata tsira ba sae da ta biyota ta mata zagin uwa da uba sannan ta fice …
••°°••
Meena dan Allah ki rufa man asiri kizo ki koma gidan kaka wallahi bazan iya da masifarki ba …ke kamar jaka kowa ya bugeki amma bara ki natsu ba …dan Allah ki zo ki shirya ki tafi ….Mamarta ta fada idonta taf da hawaye ..
Ni Ba inda zan koma wallahi ..ai gidan ma bana baban Luba bane ashe na bakine …ta turo baki ..
Waya fada maki nawane Meena ki rufa man asiri. ….
Shiru tayi taci gaba da baccin karya. .. .
Can kuma ta mike kamar an tsikareta tare da kallon mamarta sannan tace ….ni mama waye babana ? …..
Kallonta take sannan ta dauke kanta gefe guda tace …tashi kije kiyi wanka kizo ki koma gidan kaka ….
••°°•••
Tsaye yake ya harde hannuwanshi kofa gidansu Meena ya kurawa ido kamar yana kirga kasar gurin …
wayarshi tayi kara ya duba message ne ya shigo …da sauri ya buda sannan ya sauko tare da daukar keys din motar ya fice daga gidan ….
*Feedohm💞*
💧💧 SIRRIN ZUCI……
💞
Na Feedohm💞
15 to 16
Office dinsu ya nufa …yana zuwa aka bashi takardar tafiya karo karatu kasar indiya nan da wata biyu ake so ya tafi …Course din na shekara 5 ne suna so ya zama cikkaken Pilot ….Karba yayi yakoma gida …dama Abba ya dade yana nemar mashi sae akace sae gurin aikinshi sun saka mashi hannu …sae yau ya takardar ta fito suka saka hannu ….Mamarsa ya bawa takardar sannan ya kara fita da sauri ….
Meenatou. ..ya kirata ahankali …
Ta juyo cike da masifa tace …kai me yasa ka cika cin zali na …tun yaushe nake nemanka ka bani kudina shine ka boye dan kasan ka kashe man kudi ko
Dafe kanshi yayi tare da lumshe ido sannan yace …Meenatou na nemeki bakyanan ..
Baki ta bude tana kallonshi sannan tace ..ni dae bani kudina ..ta mika mashi hannu ..
shiru yayi yasan ko ya bata kudin dake jikinshi bara ta amsa ba …dan naira dari biyarce karama ciki …a hankali yace …banda canji bara na shiga gida na dauko maki …
Gefen rigarshi ta tace …sae dae mu tafi a haka karka kuma guduwa ….
Meenatou haka zaki rikeni kamar kin kamo barawo ..please ki sakeni kinji ..
ta daure Fuska Allah mai kamshi idan kaga na sakeka to ka bani kudina …
Kaka ta leko tana mata dakuwa. ..Meenalle uwaki nace …zaki sakeshi ko sae na fito …
kafa ta fara bugawa tana fadin …kaka kudina fa ya cinye kusan sati guda …ganin tsohuwar ta fito ya saka ta sake mashi riga tare da fashe da kuka ta zauna gurin …
Daukarta yayi da hannu yana bawa kaka hakuri …ce mashi tayi ya sauketa kasa amma yayi murmushi ya shige da ita gida
Falo ya zaunar da ita yana lallashi sannan ya dauko mata rabin biyar dinta ..dama tana aje saman mirrow ..ya bata tare da sweet din ….Haka Mamanshi ta shigo ta isketa tayi bacci saman kirjinsa ta wuce tana kallonsu ….
ko motsin kirki kasa yi yayi gudun kar ya tayar da ita …sae da ta dade tana bacci shi kuma yana kallonta sannan ta tashi …..gida ya rakata sannan ya bawa Kaka hakurin karta dake ta sannan ya fice …
*Meena*
Diyace tilo ga alhaji Abubakar mai zinari
..wani hamshakin mai kudine a cikin garin kaduna …Sunyi aure da Rabi’at..Auren soyayya …ko shekara basu datse ba Allah ya albarkacesu da Meenatou …Mahaifinta yana mutuwar sonta amma matsakar uwar Alhaji Abubakar bata san danta ya haifi diya mace don tace dawainiyace da wahala haihuwar mace …Tunda Rabi ta haifi Meena zaman gidan Alhaji Abubakar ya zame mata zaman makoki …kullun mahaifiyarshi tana gidan …wulakancin yau daban na jibi daban …har Meena takai wata Takwas. ..sae Uwar Alhaji Abubakar ta kawo wata diyar kawarta tace sae ya aureta ….sannan ya saki mahaifiyar meena ko ta tsine mashi …suna kuka suka rabu …Sannan mahafiyarshi tace ko bayan ranta kar ya neme su idan kuma ya nemesu bata yafe mashi ba …..
Da dan kudin da ta samu ta gina gida ta ginawa mahaifiyarta kaka itama karamin gida …gida daya suka fara zama da kaka tana rainon diyarta …
Meena nada shekara 5 Malan Sani ya fito yace zaya aureta ….lokacin yanada rufin asiri dae dae gwargwado ..sannan yana da mata daya mai suna Saratu ..itace mahaifiyar su Luba da Musa ….
Ta aureshi ashe bata sani ba dan cacane …dan haka duk abunda ya mallaka sae da ya kare gurin caca …harta gidan da suke zaune sae da ya sayar ..sannan ya roketa suka dawo karamin gidan da ta mallaka …ita da mamansu luba kuwa …kowane yana daraja dan uwanshi …matsalar tana gurinsu luba da Musa …ko kadan basu da tarbiyya wanda sak halin Malan Sani ya biyo …da yake rabi macace mai hakuri bata taba gayawa wani mutun cewa ga zaman da take gidan mijinta sannan bata nunawa kowa gidanta suke zaune ba ..da farko auren ya yarda Meenalle ta zauna gidanshi amma daga baya sae yace sae dae ta koma gidan ubanta ..haka ta mayar da Meenalle gidan kaka….lokacin da Meenalle tace mata gidantane tayi mamaki sossae dan bata san wanda ya fada mata ba ..
*Feedohm*💞
💧💧 SIRRIN ZUCI …..
💞
Na Feedohm💞
17 to 18
Mai kamshi wae ina kake samun kudin da kake rabawa mutane ….
Lumshe ido yayi yace …Allah ke bani meenatou
Dariya ta sake tare da tarba hannu sama tace. ..Allah ka bani kudi irin na Uncle Ma’aruf nima na dinga bawa mutane …
Kallonta yayi tare da fadin Uncle Ma’aruf a hankali …
Da Sauri ta kalleshi tace ..Mai kamshi kaji nace maka Uncle Ma’aruf ko ..haba nima yanzu na zama baby …ina Musan gidansu Luba ..ka ganeshi?
Uhm yace mata duk da bai sanshi ba …
Ta wash baki tace …to shi naji yana cewa I love dinshi ta gaida mashi Uncle ..kila ko babanta yake nufi ko kuma i love you dinta itama …uhm ohon mashi dae shima dae ya sani …kuma yake ce mata I Kiss me wallahi …in gaya maka Mai kamshi kamar a film dinnan daka kunna man rannan ….Ni kuma naga duniya ba kullun ake kwana gado ba. …kasan ko jiya kaka kasa ta saukeni na kwana
Lumshe ido yayi tare da mikewa tsaye yace. . Meenatou tashi kije kiyi sallah …
Miyau ta hade sannan tace ..ni bana Sallah yau ..
Ido ya waro gwanin shaawa yace ..Me yasa bara kiyi sallah ba Meenatou …
Sae da tayi dariya sannan tace …yo malamarmu ta boko naji rannan tace wa kawarta wae bata yin Sallah nima kuma naga da kadan ta fini tsawo …shi yasa nima nace banayi ..
Tunda Take magana yake kallonta har sae da diga aya sannan yaja numfashi a hankali ..ya wuceta …
Hannunsa ta kama tare da rike kunne…Mai kamshi zanje nayi kaji? ..
Murmushi yayi tare da shafar gefen fuskarta yace …Yauwa Meenatou ta ..kije kiyi zanzo na tambayi kaka ki rakani unguwa …
Wani uban tsalle da daka tare da rungumeshi cikin sabo ta dankara mashi cizo a hannu …
Da Sauri ta janye bakinta lokacin da ta lura da cizon da ta sake mashi
Idanuwanta suka kawo ruwa ta duka gabanshi tare da kallon kasa ….
Meenatou …ya kira sunanta a hankali …ganin bata dago ba ya saka ya duka shima tare da dago kanta da hannunsa ..hawaye ya gani bisa fuskarta …murmushi yayi sannan ya share mata hawayen …
Hannunta ta daura saman lebenshi tana kallon fuskarshi …lumshe ido yayi tare da zura hannun cikin bakinshi …kadan ya hade hakoranshi da hannunta ….ga mamakinshi sai ji yayi ta sake mashi ihu tare da murginawa kasa tana fadi ..
Wallahi sae na rama ai ni ba da karfi na cijeka ba ….
Dariya yake sossae sannan ya mika mata hannu yace …Rama Meenatou …babu kunya ta murje idonta ta dana mashi cizo sannan ta mike tana dariya ta shige gida …..
Dariya yayi ya shige masallacin kofar gidansu ….daya fito sae da ya shiga gida yayi wanka ya saka blue din shirt data fito da zaharin kyanshi tare da bakin jeans …ya fito sae kamshi yake …
Daga zauren gidansu taji kamshinshi ta sake ihu tana kewaye zatayi wanka tana fadi …naji kamshin mai kamshi bara na fito …
Ruwa ta shafawa kafafuwanta tare da wuyanta da hannunta sannan ta zubar da ruwan ta dauro zani ta fito …
Tsakar gida ta tarad dashi suna zaune da kaka suna fira. ..
Kaka ta bita da kallon tuhuma. .nan da nan ta hau rawar sanyin karya tana fadin. ..kaka ruwan sanyi….dakyar na watsawa bayana don hannuna rawa yayi tayi. ..
Aa Meenalle. …kya ma fadi gaskia dan kaniyarki ..muje dakin ki gwada man bayan naki …
Bata fuska tayi tace ..na fara nonuwa fa …
tashi tayi ta bita da fada daki da gudu ….
Ma’aruf da kusan suman zaune yayi …bashi yayi magana ba amma kunya ta rufeshi ….da kyar ya iya tambayar kaka meena zata rakashi gidan mamarta ya gaida ta …
Taji dadi sossae tace ..ba komae Ma’aruf ko da duniyar zaka bari da Meenalle wallahi na yarje maka bara ka taba cutar da Meenalle ba …ina fatan Allah ya nuna man girman Meenalle na nuna mata mijin da babu kamarshi a duniyarnan Ma’aruf…
Dukar da kai yayi cike da kunya ….Meena ta fito taci uban jan janbaki duk fuskarnan duk tasha digon baki sae washe baki tayi ….
suna hada ido suka lumshe ido tare …tayi saurin bude idon tare da warosu …Mai Kamshi ? …ta fada da karfi …bafa kai nake kwaikwayo ba hakanan nayi abuna ….
*Feedohm💞*
💧💧SIRRIN ZUCI……
💞
Na Feedohm💞
19 to 20
A mota ta isheshi da surutu duk surutun akan babansu luba ya kare tana fada mashi shima babansu luba taurin bashine dashi ..wae idan ya karbi kudin mutane dakin mamarta yake boyewa. da anzo kiranshi sae dae yayi karya yace baya nan …
Har sae da taga an tsaya kusa da wata katuwar plaza a jiki an rubuta MIMA Plaza …parking yayi ya fita ya zagayo ya bude mata. …murmushi yayi tare da jan hannunta ….
Kaya sossae taga ya jida sannan aka biyoshi dasu a baya …sannan tun da suka shiga taga kowa yana bashi girma kuma bai biya kudi ba …kasa hakuri tayi ta kalleshi tace …
amma Mai kamshi kai babban barawone..
….
Kallonta yayi ya tada mota sannan yace ..da nayi me kenan Meenatou …
Uhmm banda sata zaka shiga shago ka debo kaya ka fito bakq basu kudi ba …ko bashi suka ba …
Murmushi yayi yace …eh bashi suka bani …
Uhmm Allah to ya fito masu da kudinsu …nima da kyar kake biyana bare wasu ..uhmm .. ta tabe baki …
Idan ban biyasu ba ai sun zo su kamaki don dake nayi kwatance …..ya fada hankalinshi naga titi ..
Dadinta ma nasan gidanku sae in kaisu ka biyasu ….
Dae dae gidansu Mamarta taga ya tsaya ta budeshi. …mai kamshi ba dae labarin da na baka na babansu luba ba kazo zaka fada mashi ..
Hararanta yayi …yace …kinsan baki so a fada mashi kuma kike fadawa mutane ..
Dan Allah kayi hakuri mai kamshi wallahi rannan ma da kyar wani ya kwaceni gurinki. .kuma ma kai kadae na fada mawa da yan ajinmu …
Ki fito muje mana …ya fice daga motar …da sauri ta biyoshi tana rantsuwar bara ta kara bawa wani labari ba ….data isheshi yace mata ba za gaya mashi ba …sannan ta kyaleshi …sun gaida sossae da Mamarta sannan ya aje masu kayan da ya siyo masu ya tashi …taji dadi sossae tare da godiya don dama tuni ta san shi …
°°••°°
Kaka jiya kinsan me ya faru
….
ya zaayi na sani Meenalle ….
Uhm kema fa kar na baki labari kizo kici amanata yarda mai kamshi yaman gidansu mama ….ta fada a hankali …
Dariya tayi tace …indae kinsan gulmar mutanece karki fada man nima amanarki zanci …
Shiru tayi …zuwa can ta kasa hakuri tace …Kaka babansu Luba fa dan iskane ! ..
Meenalle kaniyarki nace ..tashi ki wuce ki bani guri ….sae ki saka a daure mutun yana gani ….
••°°••
*Two month*
Shiru tayi tana kallonshi …a hankali tace Maikamshi …
Yaakae Meenatou …ya fada idonshi na kallonta ..
Zaka manta dani? …
Murmushi yayi tare da dawo kusa da ita…Zuciyarshi ya nuna da hannu …tare da lumshe Ido…kina nan ciki Meenatou ….ya furta a hankali
Zuciyarshi ta dafa tare da daura kanta a bisa tafi minti goma Sannan ta janye tana kallonshi …idanuwanta suka ciko da kwalla …tace ..Mai kamshi Ka dawo da wuri na dinga ganinka.. …
Lumshe ido yayi …zan dawo Meenatou amma kiyi alkawarin nima zaki sakani a taki zuciyar …
Da sauri ta janyo hannushi ta tura a rigarta ..tana fadin. ..taba kaji Mai kamshi akwaeka ciki Allah. ..da karfi zuciyarta ke bugawa ….janye hannushi yayi daga jikinta ya mike tsaye ….Tashi muje Abba na jirana a mota …
Hannunshi ta rike yana janye da ita ….har harabar gidan …nan ne ta sake sabon kuka sae ya tafi da ita …da kyar kaka ta cireta daga jikinshi …shima idonshi ya kada yayi jawur …..
Mamarshi ta dauketa ta dinga lallashinta ranar nan gidan ta kwana …sae da daddare Tayi shiru lokacin Ma’aruf ya kira waya …kuka ta sake mashi sae ya dawo …lallashinta yayi sossae …wayar na kunnenta tana kwance jikin Mamarshi bacci ya dauketa …daga cikin wayar yake jiyo saukar numfashinta lumshe ido yayi …sannan yaki kashe wayar ya daurata a kirjinsa..yana sauke numfashi …ganin tayi bacci ya saka mamarshi ta zare wayar …gani tayi har lokacin wayar na kunne .. wayar ta kanga a kunnenta tana jiyo bugun zuciyarshi …Shafa kanta tayi tare da sumbatar kanta sanna ta maida mata wayar a kirjinta …
💧💧SIRRIN ZUCI……
💞
Na Feedohm💞
21 to 22
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya kullun da safe Ma’aruf zaya kira Mama AWaya …haka itama Meena tana gama shirin makaranta zata shiga gidan …bara ta fito ba har sae ya kira sunyi magana …kullun idan suna wayar tambaya dayace yaushe zaya dawo ….sae dae yace maka nan ba da dadewa ….wata irin shakuwa ta kara shiga tsakaninsu ….haka Mama na kokarin ganin ta taimakawa da kaka da komae na bukata …
wani lokacin idan ya kira da daddare anan gidan take kwana rungume da wayar…
••°°••
Gab da zasu gama primary lokacin Meena ta gama fadawa kaf yan makarantarsu cewa gidan mamanta babansu luba ke zaune …duk inda ta zauna bata da labari sae na babansu luba….sannu sannu magana ta koma kunnenshi ….ranar sae da yayiwa Rabi wulakanci sossae dan har cewa yayi zaya daketa …da kyar maman su luba ta shiga tsakani ..
Abokan cacarshi ya fadawa mawa wasu suka bashi shawarar indae yana so ya zauna cikin gidan dole ya dauki mataki …in kuma ba haka ba to yana ji yana gani Meena zata girma ta fitar dashi cikin gidan …hankalinshi yayi mummunan tashi domin wannan gidan shine rufin asirinshi …
A rude ya sami wani babban abokinshi wanda tare suke komae nasu …shine ya bashi shawarar indae yana so ya gaje gidan to dole yasan yadda zai hada auren da Musa da Meena ….
Shawarar ya dauka …ya kuwa samu rabi da maganar …daga farko taki amincewa …amma daga baya daya sameta akan cewa ta nuna mashi bashi ya haifi Meena ba …hakuri ta bashi amma ya tashi ya fice daga dakin …tun daga ranar yake fushi da ita …
Rabi tana da ilimin addini kuma tasan darajar miji ga matarshi don haka har daki ta sameshi ta bashi hakuri sannan ta nuna ta yarda … Da yake munafukine ranar soyayya kala kala ya nuna mata …tunda ga ranar yakoma yana lallabata …
Ita da kanta ya tura ta sami kaka da maganar amma fifir taki yarda …wasu malaman unguwarsu ya turo mata suka dinga mata sharhi akan Meena tare da bata baki ….da kyar suka shawo kanta ta yarda ….
Bayan sun tafine Meena ta dawo daga islamiyya sanye da uniform …tun daga zaure ta fara kwalawa kaka kira …
Kaka tace ..Meenalle ta yau kuma me aka samo …
dariya tayi ta zube bisa kafarta …sannan ta kalleta tace …Kaka Maikamshi yace ya kusa dawowa …kinsan idan ya dawo ko ..uhmm kaka kenan ..ranar zan kwashi adashena na hada mashi abinci mai dadi kuma ba bashi zan mashi ba kyauta …kinga ko ranar zan saka wadannan kayan Sallan da Mamana ta dinka man …inyi kyau sossae wallahi ko ke bara ki ganeni ba ……Yana zuwa zance I Love you Uncle Ma’aruf..I Kiss Me Mo Uncle …kinsan waya koyaman wannan turancin ? Girgiza kai ..kaka tayi a hankali ….tana kallonta …
Zama ta gyara sannan tace …wani littafine na samu na kaiwa Mamansu kausar kawata ta koya man …Allah ko Kaka Ina son Mai kamshi … …tashi tayi ta shige daki ta cire Unifoam dinta sannan ta dawo ta zauna tare da sake sabon surutu kuma duk kan Ma’aruf …wanda kullun dama firanshi take ..
••°°••
Rabi na zaune daki babansu Luba ya shigo rike da goro a hannu …gabanta ya zube mata sannan ya zauna yana washe baki … Ga goron auren danki….ya fada yana dariya …
Zumbur ta mike ..tana fadin na shiga uku ni Rabi …Aminatu Malan shekararta 12 kenan ..haba Malan …wani kuka ta fashe dashi tare da dukewa gurin …..
Mikewa yayi ya fice daga dakin tare da barin goran a kasa ….Musa ya shigo cikin babbar riga yana washe baki … Dukawa yayi ya gaisheta yana washe baki …kasa amsawa tayi har ya mike ya fice daga dakin yana tattare riga …dakin uwarshi ya shiga ..Wanda itama sae yanzu take jin labarin ..kallonshi tayi sama da kasa ta wuce su tare da tur da halinsu …
Feedohm💞
💧💧SIRRIN ZUCI …
💞
Na Feedohm💞
23. to 24
Cikin sauri Rabi ta fito daga cikin gidan Malan …yana shingide bisa dakalin kofar gidan …mutane ke zuwa tare da mashi murna …bata kalli kowa ba ta tsayar da mai adaidaidata …tasha tace ya kaita cikin saa ta samu motar kaduna mutun daya ake jira …..ta hau suka tafi …
°°••°°
Kofar gidan Alhaji Abubakar ta sauka …bakin gate taga motarshi da alama yanzu ya Dawo …
Yana hangota yayi saurin fitowa ya tareta …Rabi dama kina raye ? ….ya tambayeta a rude ..
tambayar ta sosa mata rai …saurin daga mashi hannu tayi sannan tace ..Muna Raye ko muna Mace abubakar wannan ba damuwarka bane …nazone na tuna maka da amanar Da Allah ya baka tana bukatar taimakon Ubanta Abubakar ..Idan har kabar Ameenatu ta wahala a duniya daga ni har ita sae Allah ya tsayar damu ya mana hisabi ….Wata takarda ta fito da ita daga jikkarta ta daura mashi saman motar ta juya sannan tace ….Duk lokacin daka shirya daukarta ka nememu ta nan Abubakar ….Bata jira cewarsa ba ta haye adaidaitar da ta kawota ….
bata isa gida ba sae wajen sha biyu na dare ….gidan kaka ta wuce ta buga masu gidac…cikin bacci Meena taji bugun gidan da yake bata da tsoro ta fito ta tsaya jikin kofar tace ..
waye ke bugawa kamar barawo …baka ga gidanmu bane …to mugu idan ma kudin adashe na kazo nema to ban amso ba …
Ki bude Ameenatou ….
Mama kene …hala wani abu mugun babansu Luba ya maki ..kema dae Mama kawae kice ya fitar maki daga gida …
Ameenatou nace ki bude ko ….ta fada da karfi ..
Da sauri ta bude tare da tsayawa tana kallonta …amma mama banga wani ciwo a jikinki ba ….
Shiru tayi ta shigo tare da rufe gidan da sauri …kaka ta tada …ta kalleta a dan tsorace tace …Rabi lafiya da wannan daren hakan ? …
Da Sauki dae …daga kaduna nake …ta fada tana kallon meena dake zaune ta kura mata ido. .
Gurin wa kika je kaduna yanzu rabi …
Gidan Abubakar Gwaggo can naje ..na tuna mashi da amanarshi …na kasa Hakura gwaggo ko taimakeni …idonta ya kawo ruwa. .
Da sauri meena ta matsa tare da dafa mamanta tace …Mama Shi Abubakar din zai taimaki babansu luba ya sakeki ne ? …
A a Ameenatu babanki ne ..shine mahaifinki …ta fada da sauri ..
taba baki tayi ..su babana manya ni bana sonshi ..mai kamshine komae nawa…babana baya sona bai taba zuwa ya dubani ba ..amma mai kamshi yana sona ..ni bani da wani baba …
Kina da Ameenatu babanki yana sonki karfinshi aka fi ….ta fada hade da dafa …
Ba wani Mama …baya sona …nima bana sonshi …ya taba zuwa ya kaini makaranta kamar yarda babansu sauran kawayena yake kaisu …ko ya taba man kayan sallah …Duka ba Ma’aruf yake man ba …shike kaini makaranta idan an koroni ya har goyani yake idan ina kuka ya man komae …shi kadae na sani arayuwata cikin maza …sae ke da kakata …kawae ki bar maganar babana ….kwanciya tayi bata sake cewa komae ba …
°°••°°
Meenatou …ya Fada Ahankali …
Rufe idonta tayi sannan ta bude …
Bara ki amsa ki …ko bakya jina …ya kara fada ahankali ..
Yaushe ka dawo …ina son na ganka Mai kamshi ..dan Allah ka dawo …ta fada cikin kuka ….
duk ya rude bai taba jinta ahaka ba koda take mashi kukan ya dawo kullun ba irin wannan kukan bane …na yau yasha banban dana kullun …asalin kuka take mashi mai shiga zuci ….
Zan dawo Meenatou …zan dawo gobe kinji ko …kiyi shiru please Meenatou nima na so nazo na kara ganin inga ya kika zama Meenatou ….Kiyi Hakuri gobe zan dawo …ya fada cikin lallashi …
Da gaske Mai kamshi …ta fada cike da doki …
Da gaske Meenatou..kin tuna Ranar da zamuje gidan Mama dake …ya fada cikin wasa …
Uhm na tuna Mai kamshi ..ina lissafawa shekara 3 da sati 5 yau …ta fada tana murmushi kamar yana ganinta …
sae da yayi dariya sannan yace …kin tuna abunda kika fadawa kaka. ..
Aa ban tuna ba …ta fada a hankali. ..
ya shafi sajensa yace …a wancan ranar Meenatouta ta fadawa kaka cewa ta fira kirgar dangi ..to na tabbata …
da sauri ta kashe wayar tare da rufe fuska …Mamansa na ganinta tayi murmushi tace …aa su mamana an fara kunya kenan .
Wayar ta kara ringing amma har ta tsinke bata dauka ba ….text ya turo …dan lokacin Meenatou na js one. .kuma babu abunda ba zata iya karantawa ba …
_Please Meenatou ki daga wayan baran sake cewa komae ba_
reply ta mashi tace … _Uhm Uhm sae da safe Maikamshi_
Yana ganin text din yayi murmushi sannan ya tura mata
_Wow Meenatou ta fara hankali …am Very Happy na kusa Furtawa Meenatou Sirrin Zuci …_
tana karantawa ta yi murmushi tare da mikawa Mamanshi wayan …kin karba tayi tace mata. …
Jeki da Ita mamana taki ce ..dama bari mukayi ki gama primary sannan ….
tsaye tayi rike da wayar ta kasa koda motsin kirki ….
°°••°°
Babansu Luba ya shigo cikin dakin tare da nunata da hannu ….Dan Iskanci Rabi shine kika wucemu shekaranjiya ko gaisuwa babu …sannan ma da zaki fita ubanwa kika tambaya …..
Ganin bata kulashi ba ya saka yace …kuma ki shirya Musa yace yana bukatar matarshi nan da wata biyu ..kije ki sanar da innarki ku shirya duk abunda ake bukata na samo masu gida a kauye …acan zasu zauna don bazan cuci yaro ba ace sae nan da wasu shekaru zai tare da matarshi …tunda har ya nuna yana bukatarka …don haka kuje ku shirya ni na gama koma ….
bata ce mashi komai ba har ya karaci fadanshi ya tafi don kanshi ….
*Feedohm💞*..
💧💧SIRRIN ZUCI …..
💞
Na Feedohm 💞
25 to 26
Tun da asuba Meena ta bar gida …inda take adashen kudin taranta ta nufa ..tana zuwa ta karbo kudinta sannan ta shige wani shago ….shinkafa ta sawo dan kwati ….Tare da gwangwani biyu na wake…Cefane tayo tare da namanta na dari biyu …
Wani karamin littafi ta dauko tana karantawa …alalan shinkafa tayi kokarin yi tare da miyar wake. ..ba laifi tayi kokari don duk inda bata ganeba zata ruga da gudu gidansu Ma’aruf ta tambayo mamanshi. …ta dawo …nan da nan gida ya fara kamshi …bayan ta gama ta dauko wasu kwanukan kaka sababbi ta zuba ….sannan ta kai markaden kunnun aya ta hada mashi …kaka ta gwada mata yarda zatayi har ta gama ..duk kwadayi irin na Meena bata ci ko yankar nama ba …..
Wanka ta shiga tayi …wannan karon wankan gaskia da gaskia tayi …tana shafa vasline Ma’aruf yayi Sallama ….wata kara tayi tare da fitowa da gudu ta makalleshi ….
tsigar jikinshi ta tashi yar. …don daga ita sae zani …..kokarin zameta yayi cikin wayau don gani yake yanzu yana iya daukar zunubi indae zaya yarda ta dinga hade jikinsu. …
Galala ta tsaya tana kallonshi …lumshe ido yayi a hankali…hakan ya kara mata damar kare mashi kallon …
a hankali tace …Mai kamshi ya zama ba indiye …..
Uhmm Meenatou fa ? …ya tambayeta ….tare da kura mata ido …
murmushi tayi sannan ta dauko tabarma ta shinfida mashi …tana fadin ..
Mai kamshi Allah yasa dae yadda na bar surutu kaima kabar cin zalin …..
Ya zauna yana fadin …ayya Meenatou har yanzu baki bar surutu ba …..
Da gaske na daina …yanzu Allah idan na rantse har kaka na yarda ….ta fada tare da shigewa daki ..
Kaya ta sanyo sannan ta fito. ..lokacin har ya mike zaya tafi ….
Bata fuska tayi tana kallonshi ….murmushi yayi yace …zan koma gida Meenatou ko tsayawa banyi na gaisa da mama na fito ….
Cikin shagwaba tace …uhm uhm ni dae ban yarda ba …
Ido ya lumshe. .Meenatou kin canja komae ya canza daga gareki Sossae …kyanki ya fito kamar bake ba Ameenatu ….
Nidae ka zauna dan Allah ….ta fada a hankali …
yanzu zan dawo …..mamaki sai ganin hawaye yayi a idonta. ..
Ya Salam ….ya fada a hankali …Meenatou wallahi yanzu zan dawo ..
To ka cire takalminka kaje kadаwo …
Na tafi ba takalmi Meenatou …ya fada a hankali..
To muje tare sae mu dawo ….ta langwabe kai …sallama yayi da kaka sannan suka tafi …
••°°••
Wallahi Abubakar koda rana daya ka sake man maganar Rabi ..to zan daga maka nono …Ta fada a fusace …
Kuka ya fashe dashi tare da dafa guiwarta ta yarje mashi yaje ya dauko Meena amma fir ta kiya daga karshe tashi tayi ta bar mashi Falon …..yafi Awa zaune gurin …duk lokacin daya bude ido Rabi yake hangowa tare da jinjirar diyarta lokacin da take kuka zasu rabu …hannu ya saka ya share hawayen tare da fadi. …Allah sarki diyata ina sonki …Hannu ya daga Sama yace …Ya Ubangiji Allah ka saukar da zuciyar Mahaifiyata na karbo diyata na nuna mata gatan da baa taba gwadawa wani shi ba Allah ka kare man Aminatu Ya Allah …..hawayen dake idonshi suka idasa fitowa …ko yaya Aminatu ta koma. …ya fada tare da mikewa shima. …..
••°°••
Baki ta turo tana fadin …wae mai kamshi babansu kausar ya bani dog (kare) amma kaka tace bara na karbo ba …wae mala’inkun rahama basa shiga gidan dake da kare ….
Lumshe ido yayi yace …to kiyi hakuri mana Meenatou …
Kafada ta make sannan tace …To Dan Allah mai kamshi ba idan na tara karnukan da yawa ba sae ka dauko man mota ba na kaisu lagos a saya a bani kudin ….kuma banda bakin ciki irin na kaka ba sae na ajeshi a zaure ba ….idan mala’ikun sunyi niyar zuwa ko ta katanga ba sae su diro ba…tunda katangar gidan mu ba irin taku bace …ko na baka ka aje man ? ….
Dariya ya sake sossae tare da mikewa ya dauki hanky dinshi ….gam ta rike hanky din tana kallonshi …
Ki saki Mana Meenatou ….ya fada a hankali ..
Uhm uhm. ..ka bari na wanke maka wallahi na iya ..kuma da kyau zan wanke maka ….ta karbe hanky din daga hannunsa ….
girgiza kai yayi tare da sanya takalmi yana fadin ….Idan kaka ta gama baccin kice mata nazo muyi bankwana amma zan dawo …
Da gaske dae komawar zakayi Maikamshi …ta fada kamar zatayi kuka …
Meenatou ba mungama wannan maganar ba tun dazu …nace maki saura 1yr na gama na dawo baki daya ..mu zauna tare mu rayu a tare ko Meenatou …karkiyi kuka kinji ko …..ya rike hannunta yana kallon cikin idonta …
kanta ta sadda kasa tana kokarin hade hawayen dake neman zubo mata ….kwantar da kanta tayi bisa cikinsa tana shakar kamshinsa ….
Ji yayi wani sabon lamari na neman hargitsa mashi tunani …yayi saurin janyeta tare da ficewa daga gidan
*Feedohm*💞
.
💧💧SIRRIN ZUCI ……
💞
Na Feedohm💞
27 to 28
Zaman dirshan tayi gurin tare da hade kai da guiwa tana kuka …..
Haka shima tunda ya koma gida kasa samun natsuwa yayi …wani zafi zuciyarsa ke masa ..har Mamanshi sae da ta mashi magana amma yace mata bakomae ….
Kwanciya yayi …yaki hada komai …sae da Mamansa ta shigo dakin da kanta ta hada mashi jikkanshi …lokacin Abba na cikin mota yana jiranshi …..
Bayan sun gama bankwana da Mamanshi sannan ya shiga gidan kaka da sauri. …
kaka na tsaye tana kwashe shanya …tace ..Ma’aruf ba dae Tafiyar bace ko …
Murmushin yake yayi yana raba ido cikin gidan tare da fadin …Har ma mun fito Kaka …ina Meenatou ? ..
Meenalle …ta kwala mata kira ….amma shiru bata amsa ba …aje kayan dake hannunta tayi ta leka daki amma bata ciki ….dawowa tayi tana kwala mata kira shiru duk gidan ba inda bata leka ba amma Ba Meenalle. ..tayi mamaki sossae don tasan bata aiketa ko ina ba …sannan lokacin data fito ta ganta tsugunne tana kuka ….
dawowa tayi inda ta barshi tana taba hannu …tace…kaga Ma’aruf wallahi bata gidan bansan inda ta tafi ba ….
Wani abu ya tokare mashi kirji …duk irin daurayi irinta Ma’aruf sae da yaji hawaye na neman zubo mashi …
Lumshe ido yayi tare da ciro wani karamin abu mai shape din heart da envelope daga cikin jikkarshi ya daurawa Kaka bisa hannu tare da fadin …Na Meenatou ne Kaka….ya fice kamar kwae ya fashe mashi a ciki…..
Yana fita aka bude mashi mota ya shige ba tare da ya juyo ba ko sau daya …daga karshe ma kanshi ya daura saman cinyar Abba …
Tana daga bayan gidansu tun da taga ya Shiga gidan kaka tasan tafiya zayayi dole …ta rabe jikin bango tana kuka ita kadae. ..har fito ya shiga mota tana kukan …tana ganin an tada motar ta fito da gudu tana kuka da karfi …motar tabi da gudu …..tana daga hannu. …
Karo tayi da mutun da yasaka dole ta tsaya daga bin motar ……
Tsinka mata mari yayi tare da fizgarta yayi gidan kaka da ita ….bata dago bare tasan wanda ya mareta …kuka take har idonta ya bushe ….
Suna shiga gidan kakar mutumin yayi wurgi da ita tsakar gida …da sauri kaka ta fito daga daki tana kiran lafiya kuwa …
Turus tayi ganin musa cikin gidanta ….Meenalle ta kalla gefe guda kwance a kasa idanuwannan sunyi jawur da fuskar …..da sauri ta matsa tare da dagota
Meenalle ina kika je. .me ya sameki Meenalle ….ta fada duk ta rude …
Ma’aruf dina ya tafi kaka. ..ya kuma tafiya ya barni …kaka kice mashi ya dawo dan Allah ….ina Sonshi Kaka ….ina so ya zauna tare dani …ta rungumeta tare da fashewa da wani sabon kukan
Kiyi Hakuri Meenalle zaya dawo kinji ko …dan Allah ki bar kukan karki karya man zuciya nima …ta fada lokacin da itama idonta ya kawo ruwa. ..
Kutmar uban can …kina matana kina son wani don Uwarki. …musa ya fada da karfi …
Ba Meenalle ba har kaka sae da ta firgita suka dago suna kallonshi …..ya nuna Meenalle da hannu yace. ….Ki tashi muje dan Uwarki tun kafin na maku shegen duka ku duka biyu. ….
Meenalle ta kalli kaka tace …da gaske yake kaka ….
Rashin amsar data bata yasa ta dan fahimci wani abu …don tasha ganin ana yiwa kananan yara aure a kauyensu Kaka lokacin da sukaje wani biki tun ma kafin ta kai haka
Kaka ta nunashi da hannu …Kai Musa ko ubanka bai isa ya nuna man hannu ba bare kai …
Gurin Meenalle ya nufo da sauri kaka ta tareshi …hannu ya saka cikin rashin imani ya buge tsohuwar tare da jan Meenalle kamar kayan wanki ya fice daga gidan ….
Duk mai adaidatar daya tsayar baya tsayawa sae da kyar ya wani ya tsaya ya shigar da ita sannan ya shiga ….
Kuka kawae take …amma ba kukan abunda ya mata ba …aa kukan dukan da yama kaka da kuma kukan rashin Ma’aruf. ….
Ba gidan Malan sani ya wuce da ita ba aa tasha suka nufa …
Duk abunda yake kallonshi kawae take ita kadae tasan abunda ke ranta ….yana cewa ta shiga mota ta shige babu matsala ….
wani gari aka ajesu …sae da suka hau mashin sannan suka shiga kauyen …..wani karamin gida mai cike da jamaa yan tarar amarya suka nufa ….tun daga kofar gidan ta gane danginsu Babansu Luba ne don daga ganin hancinsu zaka gane …
Ji tayi ana ga amaryar musa ….ta kuwa kalli gefenta taga sae washe baki yake. .
*Feedohm💞*
SIRRIN ZUCI…..
💞
Na Feedohm💞
29. to 30
Duk abunda suke kallonsu kawae take har kowa ya watse ya barta ita kadae ….
Dakine da tabarma shinfide sae tukunyar ruwa …zoben dake hannunta take murzawa ta kurawa kofar ido …zuwa can ya shigo sae uban wari yake …tayi saurin goge hawayenta tare da maida hannunta baya ….
Gefe ya zauna ya kura mata ido yana washe baki yace …Meena an kawo maki tuwo ko …
Harara ta balla balla mashi tace aa …Babansu Luba aka kawo man …
da yake sakarae ne bai san darajar iyayenshi ba sae washe baki yayi yace …Danshi dai yanzu yazo …ya matso kusa da ita …
Matsawa tayi tana hararanshi tace …bansan iskanci wallahi.. kai musan nan dama dan iskane …ta murguda baki. …
Tashi yayi ya cire riga …ta kalli kirjinsa duk da yanzu ta bar cizo amma ba abinda zai hana ta cije wannan shegen ba ….ta fada a ranta. ..
kafin ya ankara tayi kukan kura ta fada saman jikinshi ai kuwa ya fada kasa ya bugu ….ta dankara mashi cizo ta saka hannu ta murde abun fitsarinshi da karfi …..wani kara ya sake don tabbas yaji azaba sossae …
Tana ganin ya fita hankalinshi ta mike da gudu ta fice daga dakin …
Lokacin da ya dawo hankalinshi ya fara nemanta yana sabbatun Sae yaci Uwarta …babu inda bai duba amma bai ganta ba. …
Meenalle tana cikin gidan kuma duk neman da yake tana kallonshi bayan wani rumbu. …..har ya gaji da neman ya koma daki ….
Nan gurin tayi baccinta ….tun da asuba kuwa ta farka ….ta leka dakin yana kwance kamar gawa…. alwala tayi tayi sallah …sannan ta fita ta debo kaikayin gero ta zo ta zuba mashi ruwa ta koma ta sheka mashi ….kamar aljana kafin ya gama hauka kaikayin ta koma inda ta kwana ta lafe …..
Sae da safe sannan suka hadu. … ya bita zaya daka yana zagi …ta kuwa fice daga gidan da gudu …..shima binta yayi amma ya kasa kamota dole ya kyaleta amma ya dauki aniyar duk lokacin daya kamata sae ya mata dan uban duka. …
Bata dawo ba sae dare …lokacin tayi kawaye yara da yawa kamarta ….tare sukayi wasa sannan tabi wata gidansu taci abinci ….kasancewar kauyen scattered ne shi yasa ba kowa ya san kowa ba …wani gidan ma bara kayi tunanin akwaeshi cikin garin ba …don tafiyace ba karama tsakanin gidajen ….
Tana dawo …ta leka dakin ta make murya tace …Kai Shege Musa …..
ya taso kamar mahaukaci amma kafin ya fito har ta boye inda ta kwana ….bai ganta ba …haka ya karade gidan har ya hakura. ….
••°°••
Bayan kaka ta mike gidansu Musa ta nufa tarad da Malan Sani kofar gida ….duk abunda ya faru ta fada mashi amma sae ce mata yayi ai matar musa ..kuma yana da ikon ya kaita duk inda yaso …
Tana jin abinda ya fada ta shige cikin gidan ta sami Rabi zaune bama tasan abunda ke faruwa ba ….ta hauta da fada ta inda ta shiga ba tanan ta fita ba …sannan ta fada mata har da dukan da musa ya mata ….
Ran Rabi idan yayi dubu ya baci …fita tayi ta samu Malan sani a zaune …
Ina kuka kaiman diyata Sani …ta fada cikin tsawa …
Mijinta ya dauke abunshi ..ko bada saninki akayi auren ba ne ? ….shima ya fada cikin harguwa. .
A ranan dai anyi ba dadi tsakaninsu …sae ranar ya fahimci wacece Rabi sannan zata iya komae akan diyarta …dan cewa tayi ma sae ya saketa amma fur yaki sakinta ….
Bata koma gidan ba taja hannun kata suka bar unguwar …babu irin neman da basuyi wa Meenalle ba amma babu labarinta …hakanan suka hakura suka dawo ….
••°°••
Ma’aruf duk wani kuzarinsa ya tafi kullun ka ganshi cikin damuwa yake …duk yan matan dake juyi gabanshi yanzu sun shiga taitayinsu don sun gane jiran kowa yake yaci mashi mutunci. ….
Abokanshi kuwa sunyi tambayar duniya kullun amsa dayace ….karsu dameshi …..mutun daya kawae yasan labarin Meenalle …..
Yau ma kamar kullun ya kira Mama ..yace ta bada wayar akaiwa Meenalle ….
Cikin lallashi tace mashi ..An kai Meenalle boarding school …..
Tunda ya yanke wayar ya fitar da sim din bai kuma kiran wani ba a nigeria. …Su Abba sunyi neman duniya amma wayar bata shiga ….
*Feedohm*💞.
💧💧 SIRRIN ZUCI …..
💞
Na Feedohm💞
31 to 32
Watansu Biyu da aure amma Musa duk ya kare yayi baki dama abunka ga bakin ….fitinar meenalle ta bi ta dameshi kullun da irin muguntar da zata mashi sannan sau daya ya taba kamata ya daketa …shima ya wahala gurin dukan don duk sae da ta yakuceshi ta cijeshi …..shi bai ma daketa ba kamar yadda ta wahalar dashi …..
Sannan ma duk ta gama zubar mashi da mutunci ga mutanen kauyen …duk gidan da ta zauna bata da labari sae nashi dana ubanshi ….daga inda zata ce Babansu Musa dan iskane yara yake wa iskanci a garinsu sannan kuma dan cacane …alhalin bata taba ganin yana iskanci ba ..gara ma cacar ta fadi gaskia ….
Idan kuma ta shiga wani gidan sae tace Babansu Musa barawo …don tsabar karya irinta meenalle har cewa take ya taba dirawa gidansu Maikamshinta ya sace masu jarkar mai ja….
Haka idan ta kuma shiga wani gidan su kuma tana iya ce masu …Musa Mijinta dan iskane su yi kaffa kaffa da yaransu ….
Mutanen kauyen duk sun yarda don sun tabbata meenalle bara tayi masu karya ba a tunaninsu. …
Idan kuma Labarin kirki ya tashi …to labarin mai kamshine …wani sa’in ta fadi gaskia wani sa’in kuma har da karya. ..duk kauyen ba wanda baisan Maikamshin Meenalle ba …haka ba wanda baisan yana da taurin bashi ba
Har labarin irin ciwon da taurin bashi ya sake mashi ba sae da taba yan kauyen …
Lokaci guda tayi farin jini a kauyen kowa sonta yake …duk inda ta gifta sae kaji ana Meenallen Maikamshi …sae ta washe baki….haka mamanta da kakarta kowa ya sha labarinsu ….har fada masu take …kakarta da tana da wani buje duk ya yage …ita ta sace bujen ta yarda don ta gaji dashi …..
Musa kuwa duk wanda ya ganshi da yaronshi to zaiyi kokarin ganin ya raba su
Don kar ya bata masu yara …kauyen ya isheshi …. yaje har gida ya fadawa Malan sani halin da yake ciki …
Rufeshi yayi da fada akan shine ya kyale Meenalle …amma amsar da ya bashi ita tayi matukar girgizashi …don ce masa yayi …yana matukar son Meenalle ….
Yafi Minti ashirin kafin yayi magana.. . yace mashi to yayi hakuri zaya sake nema mashi wani gida acan kauyen dangin uwarshi ….haka ya koma gida jiki a salube. ….
Amma yana zuwa kofar gida yaja burki don ganin Meenalle ta tara mashi yara sun cika gidan wae yan kwana ta debo yara sunfi Ashirin …dole ya zauna kofar gida anan yayi bacci ….
Da Allah ya taimakeshi yaran duk suka koma gidajensu zasuyi kalaci ….ya shiga gidan jiki a sabule ya sameta sae wanka take tsakar gida ta saka karamin siket duk ya jike ya bi mata jiki …ta dan fara kirgan dangi ga kuma hips da take dasu dama can …..tayi jawur kamar baa kauye take zaune ba …..
Kamar sakarae haka ya zauna yana kallonta har sae da ta gama sannan ta juyo tana kallonshi tare da watsa mashi harara. …tace ..
Kai Musa lafiya kake kallona kai dai mayena ne wallahi …..
Bakomae Meenalle …ya fada da sauri. ..don bala’in tsoronta yake tare da sonta yanzu ..
Tabe baki tayi ta shige daki ….ta sanyo kaya sannan ta fito ta zauna kusa dashi tana washe baki ….
Tace …Musa bani hamsin …
haka ya ciro yana kyarma ya mika mata …ta fice tana mashi ….awara ta saya taci sannan ta shige gidan kawayenta suka fito wasa …..
••°°••
Kaka da kanta ta koma gidan Alhaji Abubakar amma sae aka ce mata an kwantar dashi asibi …haka ta dawo bata samu ganinshi ba …don ta tabbata shi kadae zaya iya kwatarma Meenalle Yan’cinta ……
Abban Ma’aruf ma da kaka ta fada masu da cewa yayi zaya shigar da kara …amma wani amininshi ya bashi hakuri tare da lallabarshi …indae ya shigar da kara to duniya zata dauka yana son kashe auren ne don Ma’aruf ya aureta ….haka ya suka hakura amma basu yarda Ma’aruf ya sani ba …kawae sun barta a cewa Meenalle ta tafi boarding school …
*Feedohm💞*
💧💧 SIRRIN ZUCI ….
💞
Na Feedohm💞
*Ban ma san me zan fada ba …am speechless wallahi …duk irin godiyar da zan maku bara ta gamsar dani ba na fahimci kun yarda da ina tare daku ….Nagode sossae Allah ya bani ikon faranta maku …ina yinku sossae …Thanks For your support and cares …..08066598868 Shine real number na ta yanzu wadanda ke fadar bana masu magana wancan number da suke messages na bar amfani da ita ..*
💞
33 to 34
Haka Musa ya tattara kayanshi da Meenalle suka koma kauyen Ruhogi can cikin zariya …..acan ma Meenalle cikin Kwana kadan ta zama yar gari ….kasancewar gida daya suka zauna da dangin Uwarsu musa ….
Cikin wata biyu zaman ruhogi ya fi karfin Musa ..ga kuma wani bala’in son meenalle da yake …ko mi tayi mashi baya iya ko da mata maganar banza ne ….abunda ta fada a wancen garin sae ma ya zama wancen garin da suka baro yafi mashi dadin zama …dan a ruhogi cewa ta dinga yi ko rosu akayi saboda Musa dirawa yake gidan matan aure yana kwartanci …sanna ga muguwar satar awaki da yake masu …har cewa take wae ya dira gidan maigari ya shiga dakin amaryarshi mai garin ya saka aka mashi mugun duka …sannan abincin mutane yake sacewa idan sun aje a waje kafin su shigar dashi gida ….
Fitinar Meenalle ta isheshi dole ya tattarota ya maidota gidan malan sani ……
Ranar da suka dawo garin kuwa. ..kafib keftawar ido suka nemi Meenalle suka rasa ….gidan kaka ta koma …acan ta iske Mamanta da kaka zugum …
Ranar sunyi murna sossae da ganinta …rabi ta rungumeta tana tambayarta rayuwarta …bata boye masu komae ba ta basu labari ..sunsha dariya sossae sannan duk wani takaici dake zuciyarsu sae da ya fita …don ko ba komae sun tabbata Meenalle ba inda zata shiga a cuceta ….
Daga nan gidansu mai kamshi ta shiga …ta tarad da ba kowa gidan sun tafi Umara su duka …sannan Ma’aruf kuma bai dawo ba …haka ta dawo tana share hawaye …anan gidan kaka ta kwana …
Tun da Safe sukaji sallamar mutane …Kaka ta fita tana binsu da Kallo …ko baa fada mata ba tasan Malan Sani da dansa ne suka dauko masu yan Sanda …
Ta kallesu tace …Bayin Allah Lafiya kuma …
Wani daga cikinsu yace …idan munje office kunyi bayani ….
tace to Allah ya kaimu lafiya …ta shiga ta dauko hijabi …tare suka fito da Rabi da Meenalle ……
a Police Station akace wae ana tuhumarsu da sacewa musa mata. ….daga kaka har rabi kasa rufe baki sukayi saboda maki …
Meenalle ce ta kwashe da dariya tace …ni ba wanda ya saceni …Musane yace na je gurin kaka wae zai sa babanshi ya rude saboda a yana binshi bashi. ….
Dan Sanda ya kalli dayan yace mata. ..Kece Meenalle …
Ta daga mashi kai tana washe baki. …yace. .kece matar tasa. ….nan ma daga mashi …
Tace. ..haka nima naji ana fada. ..amma kasan ko ..ina kazar nan da ake sawowa amare to ni ko ita baa bani ba …kai ko kumshi ma baa man ba. .ina dae jin wannan auren na irin su shegu Musa ne. ….
ya Kalli Rabi yace zasu iya ganin Uban Meenalle ….
aa tace mashi. …..sae gasu musa sun shigo …..nan dae aka bawa musa matarshi sannan aka ce su kaka su koma gida. …..
••°°••
Alhaji Abubakar na zaune a office dinshi …babban amininshi Alhaji Sadee ya shigo ….ya dade tsaye yana kallonshi kafin ya dafa kafadarshi….
Alhaji Abubakar wae lafiya kake kuwa. ….
Gumi ya goge sannan ya dago idanuwanshi sunyi jawur yace …ba komae Sadee ..
Zama yayi saman kujera yace …A tunani Abubakar yanzu mun zama daya ….duk wata damuwarka ni ya dace na santa. ..ka dubi girman Allah ka fada man meye Matsalar. …Sirrin zuci …baya da wani amfani har sae an fito dashi an warwareshi …..
Lumshe ido yayi …nan take ya fada mashi duk abunda yake faruwa dangane da diyarshi tilo da mahaifiyarshi ta hanashi dauka ..sannan yanzu yarinyar na bukatar taimakon Mahaifinta. ….
Ajiyar zuciya yayi sannan yace. ..lallae Abubakar kana cikin damuwa. ..amma me yasaka tun farko baka fada. man ba ?
*Feedohm*💞
💧💧 SIRRIN ZUCI …..
💞
Na Feedohm💞
35 to 36
Shin Abubakar Aminatu ba jininka bace ? …ya tambayeshi cikin natsuwa
Tabbas Jininace Sadee kana sane ko da hajiya ta sakani auren Lami bamu taba samun haihuwa ba sannan ba kwanciyar hankali nake samu ba …babu kwanciyar Hankali ina kake tunanin samun zuri’a …
In Kuwa Aminatu jininka ce to tabbas itama tana da hakki akanka ba mahaifiyarka kadae ba. . Abubakar dole mubi umarnin Mahaifanmu indae bai sabawa Musulunci ba ….shin barin diyarka kana tunani baka sabawa Allah ba …tunda aka haifeta ka taba zuwa ka ganta. ..kana sane da cinta shanta tufafinta yana wuyanka ….
Shiru Abubakar yayi sae uban gumi dake kyeto mashi ….
Sadee ya cigaba da cewa …Aminatu Diyata kamar yarda take diyarka …bani address din Aminatu zanje ni na daukota na riketa kamar yarda na rike Ahmed da Mus’ab ….zan daga darajarta har sae mahaifiyarka ta hankalta ….
Sannan ba zan baka Aminatu ba har sae mahaifiyarka ta rokeni akan hakan …inaso wannan ya zama sirrin zuci …daga ni sae kae sae matata …..
Tabbas duk abunda Sadee ya fada gaskia …Aminatu nada Hakki mai girma gareshi ….Takardar da Rabi ta bashi ya laluba ya mikawa Sadee …..bai ce mashi komae ba ya fice daga office din ….
kasancewar dare ya kusa ya saka ya koma gida …acan ya sami matarshi Mai suna Saadiya ya fada mata komae dangane da matsalar Amininshi …
Mace ta gari. …nan take ta goya mashi baya tare da bashi karfin guiwar abunda yake shirin aikatawa …..
Tun da Safe suka shirya tare da Babban danshi Mus’ab suka nufi garin su Meenalle ….basu sha wahala ba suka gane gidan Malan Sani ….nan sukayi parki g Mus’ab ya fita daga cikin motar …..
Meenalle na tsakar gida tana ta uban bala’in Malan Sani yacewa Mamanta yar iska …..malan na duke bai ce mata komae ba har sae da ya gama alwala sannan ya nade babbar riga ya biyota da gudu …ta kuwa kwaso a guje. ..a bakin kofa tayi karo da Mus’ab dake ta faman sallama …..tureshi tayi ta wuce da gudu …ya bita da kallon ….
…
Gidan kaka ta nufa ….a hanya ta tsaya ta gama wasanta sannan ta wuce …tana shiga gidan taja birki tana fadi …
Kai Aljani bakae ne na baro gidansu Luba ba ….
Mus’ab da tunda yaga yarinyar ta kwanta mashi a rai …yace ..bayan wasa kika tsaya a hanya …
Kilbibi …ta fada kafin ta gaida Alhaji Sadee dake ta faman kallonta ….
sannan ta kalli Mus’ab tace …to mujiya sae a daina kallona kuma ko ….ta murguda baki …
Murmushi ya sake mata yace ….Meenalle da alama kina da dadin zama
Ta shige daki abunta …Alhaji Sadee bai boye komae ba ya fada masu komae dangane da yadda sukayi da Alhaji abubakar……nan da nan ya kirashi a waya sukayi magana da kaka …dan. Rabi cewa tayi bara ta amshi wayar ba …
Kaka ta kira Meenalle ta fada mata zaa tafi da ita …amma kememe taki yarda sae tayi bankwana da Ma’aruf idan ya dawo sannan suzo zata bisu ….da lallashi sannan ta bisu ….
Suna tafiya Musa na zuwa yazo daukar matarshi …kallon banza suka mashi sannan sukace ya duba inda ya ganta ya dauka …daga karshe ma kaka bori tayi tace sae ya fito mata da Meenalle …haka ya tafi jiki ba dadi ….
*Feedohm*💞
SIRRIN ZUCI……
💞
Na Feedohm💞
37 to. 38
Ina Labarin Ma’aruf ….Bai kuma kiran iyayenshi ba har sae da ana saura kwana biyu ya dawo …shima magana dayace ..shin Meenatou sunyi hutu ta dawo gida ….
Abba yace. ..aa Ma’aruf Mamana bata dawo ….
Abba ka fada man gaskia. ..kodae Meenatou ta rasune kuke boye man …idonshi ya ciko da kwallah ..
Calm down Ma’Aruf Meenatou bata rasu ba kaji ko …yaushe zaka dawo …
Jibi Abbah …ya fada tare da kashe wayar ….
Raliya ta dafa mashi kafada tare da tausasa murya …What wrong Ma’aruf …..ta langwabe kai
Fuskarta ya kalla sannan ya kalli kafadarshi ..da sauri ta janye hannunta daga jikinshi tare da zama bisa kujeran dake facinng dinshi…
Ta kura mashi ido har tsawon mintina sannan ta sauke ajiyar zuciya ..tace. ..Ma’aruf please meke damunka …
ya juyar da kai gefe guda tare da fadin …Tashi kije Raliya ….
Haba Ma’aruf tafiya fa zamuyi atleast ka tsaya muyi magana da. girman Allah …
Ido ya lumshe tare da mika mata wayarshi ….drop your number zan nemeki ….
Wani dadi taji don ta dade tana jiran wannan rana sae yau Allah ya bata …jikin kyarma ta karba tare da saka mashi number. ….
Thank you Ma’aruf you completed my life….am very happy ….ta fada dauke da murmushi …
Idonshi ya lumshe ya nuna mata hanya …amma ta tsaya tana fadin …please Ma’aruf muyi pictures mana …
To the hell of you and ur bullshit pic ….ya fada cikin tsawa tare da nuna mata hanya …
Haka ta wuce tana waigenshi …
_Raliya Saad yar nigeria ce cikin garin kaduna tazo karatu india itama tunda ta kyalla ido taga Maaruf take binsa bai taba tsayawa ya mata magana in ba yau ba Raliya irin matannan ne Yan bariki duk abunda take so sae tayi yarda tayi ta sameshi …Yar guntuwa ce ..sae dae tana da hips amma ba irin cikkakar matan nan bane ..haka tana da gashi dae dae gwargwado amma duk da haka tana karawa dana doki ..sannan farace tas da ita …tana dauke da kananan ido kamar yar china_..
================= Gidan Novels =====================
°°••°°
Su Meenalle tun da aka sauka gidan Alhaji Sadee take washe baki ganin gidan mai kyau … Hajiya Saadiya ta mata tarba mai kyau ..kamar ita ta haifeta …
Suna zaune bayan mangrib Alhaji Abubakar yayi sallama ya shigo …tunda ya shigo yake kallon Meenalle. ..har dae ta kasa hakuri ta matsa kusa da Hajiya Saadiya tare da zungurinta ….
Lafiya Meenalle …ta fada tana kallonta
Bata fuska tayi tace ..to tunda na zama yar gayu ba sae adaina ceman Meenalle ba ….ta kifta ido ..
Tayi murmushi tace to yaakae Aminatu. …
Baki ta washe tare da nuna mata Alhaji Abubakar tace …Kinga wancan sae kallona yake da idanuwanshi kamar na magen gidansu kausar… oh na manta ban baki labarin kausar ba ko …Haba Itama kawata ce in gaya maki kullun mamarsu Idan tana girki sae ta barbada wani abu a ciki …ai ko nace zan fada wa babansu kausar sae ta bani naira hamsin tace kar na fada ..in gaya maki da kaka ta aikeni na yarda kudin sae naje gidansu kausar din nace zan fada tana barbada magana….rannan da naje ta bani kwakwa da dabino tace dan Allah kar na kuma zuwa gidansu …sae nace mata to na tafi ….
Hajiya tayi dariya tana kallon Alhaji Abubakar ..sannan tace mata …Ni kam naga kamar kuna ma kama Meenalle …
Kai ta juyar tana fadin …ki nemi Meenalle. …..Sanna ta kurawa Alhaji Abubakar ido tace …Kuma kamar da gaske dan dae shi kamar yana shafa jan baki ..shi yasa lebenshi yayi ja ….ni kuma nawa hink ne ….kinga na fishi haske ..wae bashine yazo nema gurin Wancen ta nuna Alhaji Sadee .
tace …tashi ki matsa ki gaidashi ….
Ta mike ba gardama ta isa gurinshi
*Feedohm💞*
💧💧 SIRRIN ZUCI ……
💞
Na Feedohm💞
39 to 40
Maimakon ta gaisheshi …sae lekewa tayi gefen fuskarshi tace mashi ….Ka daina kallona ni matar musan gidansu Luba ce …kasan waye Musa ? ..
Girgiza mata kai yayi …tace ..Kai yanzu duk girmanka baka san Musa ? ..Uhmm to Dan Mijin Mamata ne. ..In Gaya maka Sunan babanshi Sani wae sae ace in dinga jin kunyarshi ni kuma nace bazan ji kunyar ba ..kasan me yasa?…
Nan ma girgiza kai yayi tare da kamo hannunta …tayi saurin janyewa tana hararanshi …sannan tace …
Ranar jumaa mamansu Luba tayi alala …kasan Mayen alala ne ..aiko ya ci sossae ya dinga banka mana tusa mai shegen wari ..nima kasan cikina ya kumbura naje zanyi kashi haba can naji babansu Luba yana zawo da karfi …aiko tunda lokacin na daina jin kunyarshi
Dariya ta bashi sossae …gata kyakyawa da ita sannan ga surutu da saurin shiga rai ….ya dade tana bashi labarin musa. ..amma sam ya kasa yarda da zancen wae an mata aure …haba ubanwa ya isa ya aurar man diya tana karama …ya fada a ranshi …..sannan ta zuba mashi labarin mai kamshi sossae …ayadda take bashi labarin yaji yana son ganin yaron …don har zoben da ya bata sae da ta nuna mashi ….
Dan zaman da yayi da ita ta shiga ranshi sossae sae wajen karfe Sha daya na dare sannan ya tafi …shima sae da Sadee ya mashi da kyar sannan ya tafi ….cike da kewarta ….
••°°••
Mus’ab ya shigo rike da ledar chocolate ..Meenalle na zaune saman carpet da duwatsunta tana yar carabke …
Ya samu guri ya zauna yana kallonta tare da mika mata ledar ta amsa tana kallonshi tace …Kai dae Mayenane Allah …dan kawae kana samo man chocolate da yanzu na maka rashin kirki ….
Murmushi yayi mata yace ..har kin iya wani rashin kirki ….
Harara ta balla mashi tace. ..kai Malan ni mai kamshi kawae nake kyalewa a garinmu. ..
Wae waye wannan mai kamshin Meenalle …
Baki ta washe ..ta fito da zoben dake hannunta tace …Shi wata irin zuciya gareshi ..ka ganta nan shi ya cirota tana ta jini shaaa…ya saka man a hannu sannan ya saka wani abu ya kulle hanjinshi dashi don kar ya fado kasa …abun gwanin ban tausayi ……
ta mayar da zobenta a hannu….
Ni kuma kasan me na bashi ? …
Ya girgiza mata kai yana murmushi ….
Nima zuciyata na bashi amma ni da reza na cirota tana ta jini sae da aka kaini asibiti fa …..nasha wahala sossae kamar zan mace …ranar da ya tafi ko ..ranar Shege Musa ya daukeni …..
Tayi dan karamin tsaki ta mike tsaye. …nina yi tafiyata tunda ko sannu bara kace man ba …ta shige dakin hajiya saadiya. …..
Kwanciya yayi saman carpet din tare da rufe idonshi yana murmushi
••°°••
Ranar da Ma’aruf ya dawo kamar zayayi hauka daya samu labarin wae an wa Meenalle Aure ?,…Abunda ya dinga maimatawa kenan ….Shin waye Meenalle ta aura ….Bata san yana mutuwar sonta ba ….kuka ya dinga yi ..kamar karamin yaro …a ranar ya tsani duk wata mace …..
Abba da ya fada mashi sae da yayi dana sanin fada mashi da yayi …..
Tun safe ya bar nigeria ….Ya koma india …don bara ya iya cigaba da rayuwa a gurin ba
*Feedohm💞*
💧💧SIRRIN ZUCI ……
💞
Na Feedohm💞
41. to. 42
Meenalle zo ki mikawa Mus’ab Wannan jug din….Momma ta fada ..
Da gudu ta amsa ta shige part dinshi ….yana ta game abinshi ta dire mashi saman cinyarshi …sannan ta bi falon da kallon ….
Hannunta ya janyo ya zaunar da ita barinshi ….Me kike kallo …..
Tabe baki tayi tace …wani gulma na gani …
falon ya bi da kallo sannan yace …ina kika gani ..
wani frame ta nuna tare da fadin …in ba gulma ba komae na dakin maikamshi sae ace sae an kwaikwaya ….
fuska ya bata don ya gaji da labarin Ma’aruf Yace …Karki kuma man maganar maikamshi anan …
Harara ta balla mashi tace ..don kasan ya fika kyau? ..
Cikin tsawa yace …zan bata maki rai wallahi kika kuma fadin sunanshi anan
Baka sonshi ne don ya fika tsada? ..ta fada a hankali. .
Eh bana sonshi ….shima ya fada …
Idonta ya ciko da kwallah ..sannan ta fara tafiya da baya da baya zata bar dakin ….har ta kai kofa ta tsaya tare da fadin …Karka kuma man magana ba ruwana da kai …nima bana sonka ..Bana Sonka tunda baka son Maikamshi .. ….ta fice da gudu tana kuka …..
Da sauri ya bi bayanta ….a corridor ya tarad da ita ta hade kai da guiwa tana kuka …tsugunnawa yayi …
Meena ….ya kira sunanta a hankali …
Banza tayi dashi ….lallashinta ya cigaba dayi amma bata kulashi ba …so take yace yana son mai kamshinta amma shi ya kasa …..
••°°••
School bag din dake hannunta ta yarda a kasa tare da dukewa tana kallon Momma …..
Mus’ab ya shigo falon yana ganinta duke yayi sauri zubewa gabanta …Meena me ya faru …..
Momma na zauna tana kallonsu bata ce masu ķomae ba don tasan Halin Meenalle. ..
Duk ya rude yana tambayarta amma taki bashi amma ….kamar ya mata kuka ganin yanayinta ya canza ..Please Meena Meke damunki …
Sae da taga dama sannan ta dago tana hararanshi tare da fadin …Kaini karka dameni …
Ya kwantar da murya . .ba damunki zanyi ba Meena kinji …fada man zakiyi abunda ke damunki …
Kaini ciwon ice Cream ke damuna …..ta fada tana turo baki …
Mtss ya saki tsaki tare da mikewa. ….takaicin tsakin ya sakata ta fashe da kuka. …..yayi sauri dawowa yana fadin …tashi ki cire unifoam dib kizo muje
Bai rufe baki ba ta mike da gudu ta fada daki ….bata fi minti Goma ba ta fito sanye da doguwar riga da karamar hijab ….
Hannunsa ta rike …Suka fice …
Ice cream ta kwasa a gurin tare da chocolate kala kala …sannan suka dawo gida …bakin gate din gidan tace ya tsaya ….ta fice ta shige wani gida dake facing dinsu …binta kawae yayi da kallo har ta rufe kofar sannan ya shiga gida …
Tayi Sallama yafi biyar amma ba wanda ya amsa mata… dage labulen falon tayi ta shiga …mutane zaune a falon da alama magana suke ….
ta tsaya tsakiyarsu tana kare masu kallo…wata yar budurwa da ta kasa daurewa tace mata …Ke lafiya …
Harara ta watsa mata tare da kara yin sallama da karfi ….
Wae lafiya ko bakya da hankali ne …..budurwar ta sake fada tare da tasowa …
Bata kulata ba ta sake yin Sallama ….wata daga cikinsu ta amsa sallamar …sannan Meenalle tace …Ni makarantarmu an hanani kula wanda bai amsa sallama ba ..
*Feedohm💞*
💧💧SIRRIN ZUCI…..
💞
Na Feedohm💞
43. to 44
wata tace amma bai hanaki shiga gidan mutane ba ..? ..
Kallonta tayi ..itama budurwace tana kwance jikin wata daga ita sae bra da pant. …
Ido ta waro sannan ta sake kallon wadda ke tsayen itama duk uwar darin ce…. duka yan matane gidan su kusan 8 amma babu mai kayan kirki. .
Miyau ta hade ta samu guri ta zauna tsakiyar tafalon sannan tace …Ina Mamanku …
Wata daga cikin yan matan ta taso ta zauna kusa da ita tare da dafa ta tana kallonta …..sannan tace …Ya sunanki …
Keni sunana Meenalle a garinmu anan kuma Meena …Maikamshi kuma yace man Meenatou …kinsan duk yafi iya fadin sunana …shi kuma wancen kilbabben yace man wae Sweet Meenah. ..kinsan ai kilbabben da nake nufi ko?
Hannunta ta kama tace .. meenah …
Harara ta balla mata …tace wancen Mayen nawa fa ..ai mayena ne Allah …ke ni dae bara na tafi …dama zuwa nayi naga ko zan samu kawa ..sae na ga kuma duk baku sa kaya yan iskane ….ta mike …
Da Sauri ta janyota ta fado jikinta …tare da matseta a kirjinta…nan da nan idonta ya canza kala ta saka hannunta cikin pant din Meena tana shafata. .
Hannun Meenah ta buge tana kokarin kwace kanta. …amma ta kasa …..kuka ta sake mata tana zaginta tare da kai mata duka amma duk abanza ….
Wata ta taso tace. …Ruky meye haka ki kyaleta bana so …
harara ta sake mata …ina sonta ne …
Nifa. …ta tambayeta a fusace …
Idan na gama da ita zanji dake …ta fada ta shiga ba da shafa. …
Duk falon ba wanda ya kulata kowa harkar gabanshi yake ….daga karshema budurwar daukar meenalle tayi ta shigar da ita daki ta rufe dakin ta cire mata kaya tsaf …ta dura mata wani abu a baki ….tun daga lokacin Meenalle bata kuma sanin inda take ba …har sae da ta gama Shafeta tsaf tare da daukarta pic sossae sannan ta fito dakin ta rufota …
°°••°°
Mus ‘ab kuma tunda ya shiga gida hankalinshi ya ki kwanciya don basu harka da mutanen wancen gidan …bama su san juna ba…amma wani sashen na zuciyarshi ya tuna mashi Meenalle face ..kila ma ta dade da sanin mutanen gidan sae kawae ya aje mata kayan da suka sawo a dakinta ya shige dakinshi ya kwanta. …
Bata Farka ba sae kusan Laasar …jikinta ta duba babu kaya wani miyan wahala ta hade tare da share hawayen da suka zubo mata …ita dae taji seniors na fadin lesbian …amma bata taba ganin anyi ba ..
To ko shine wannan …ta tambayi kanta …aiko baza manta ba Ustaz ya taba fada masu duk wanda ke lesbian baya shiga aljanna
Hawayen ta share ta saka kayanta sannan ta fito har lokacin suna zaune ….tana fitowa budurwar ta taso tana fadin
Baby har kin tashi …..
Bata ce mata komae ba ta rabe ta fice daga falon ….kwado ta gani sagale jikin kofar ta janyo kofar da sauri tare da rufesu ta baya …..ta tafi da keys din ..
Bata fadawa kowa ba abunda ya faru …haka bata kuma bin ko ta kofar gidan ba ….tun daga lokacin ta hankalta da shiga duk gidajen unguwar …..
••°°••
Dafe kanshi yayi tare da lumshe ido …Again Raliya ForGod sake me ya kawoki gidan infact me ma ya maidoki nan kasar bayan kin tafi..
zama Tayi tare da goge hawayenta ….Ma’aruf Kaine ka maidoni …bazan iya rayuwa babu kai ba ..Ma’aruf dad dina baya lafiya…amma na baroshi nazo gunka please ka amsheni
Tausayi ta bashi don yana ganin yarda take son dade dinta kuma ita kadae ce dashi ….ya lumshe ido tare da zama a kujeran dake facing dinshi ..Me ya sameshi …ya fada a hankali ….
Paralysis ya kamashi ….
Ya Salam Raliya ..Allah ya bashi lafiya …amma raliya ki fahimceni bawae nayi rejecting naki ba san raina ..wallahi Zuciyata tuni tana gurin Meenatou ..ko da na aureki bazan baki farinciki ba …
Na yarda Ma’aruf indae zan zauna dakai. …please wacece Meenatou zan zauna da ita ka hada mu …
Kinga Meenatou can …ya nuna mata wani frame dake makale jikin bangoshi ….
Sauri tashi tsaye tayi tana nuna Photon. ..Waccen Yarinyar ce Meenatou da kake fada ….waccen yar iskar yarinya …
Tsawa ya daka mata ….Tare da nuna mata hanya …fice man daga gida ..
Indae akan waccen yarinyar ce wallahi sae ka rabu da ita …komae nake so duniya sae waccen shegiyar yarinyar ta kwace man …bazata yiyu ba wallahi …wannan karon bazan bar maki ba ….
Ta fice daga gidan da sauri ..mota ta shige ta fizgeta da karfi ta bar unguwar ….
*Feedohm💞
💧💧SIRRIN ZUCI …..
💞
Na Feedohm💞
45 to 46
Dome Hotel din da suke zaune ta nufa. ..Ruky na kwance bisa gado tare da Precious. ..tajanye mayafin da suka rufa dashi ..
…Ruky muga phone dinki please ….ta fada da karfi
Idonta na rufe ta lalubi Phone din ta mika mata …
amsa tayi ta koma falo tana bincikar wayar ….Gallery ta shiga ta fara scrolling pictures din dake cikin ….
Murmushi tayi tare da marking din pictures din da take bukata ta tura a tata phone din sannan ta mayar mata …ta sake fitowa ..
Gidan Ma’aruf ta koma …falo ta iskeshi …yana ganinta ya mike kamar zaki yayo kanta
Uban me kika zo nema Kuma. ..ya fada lokacin daya shakare mata wuya ….
Da kyar ta mayar da numfashi tare da mika mAta mashi wayarta …..da kyar ta buda baki tace ka duba ciki zaka Meenatou ..
Sakinta yayi ya amshi wayar …jikinshi ya fara kyarma ganin photon Meenalle tare da wata babu kaya jikinsu …..
Karya kike raliya …Ba Meenatou bace forcing dinta akayi ….Why …ya fada da karfi …
Wayar ya tandara da kasa tare da sulalewa gurin …ko’ina jikinshi kyarma yake …da hannu yake nuna mata kofa amma taki fita …kasa controlling kanshi yayi ya mike tare da shakaranta ….sae da kyar ta samu ta kwaci kanta ta fice da gudu …
.kamar mahaukaci ya fara wurgi da kayan dake tsakiyar falon yana kuka ….
Why Meenatou …. ..Me yasa haka . …rayuwar da nafi tsana fiye da komae. …Rayuwar da karuwa mai bin maza ta fiku daraja ….shin bara ki barni da bakin ciki daya ba Meenatou…sae kin hada man da wannan mummunan rayuwa ba kyasona Meenatou ….Me yasa kika bari na tsaneki Meenatou? ….na tsaneki Meenatou ..na tsani duk wata mace yanzu. ….haka ya dinga sabbatu shi kadae. …..
••°°••
Alhaji Sadee ya dauki Meenalle kasancewar Weekend ne ..gidan Mahaifiyar Abubakar ya nufa da ita. .kasancewar ta sanshi sossae ya saka ta amsheshi hannu biyu ….
Ina ka samo wannan kyakykyawar yarinya haka tubarkallah ….ta fada tare da janyo Meenalle ta zaunar da ita gefenta …
Alhaji Sadee yayi murmushi yace. ..Diyar Kanwata ce Hajiya shine na daukota …
Meenalle ta kalleta …gata dae tsohuwa amma taci kwalliyarta. tace …tsufa dae yayi shawagi …ni Kakata bata abun yara amma ke tsohuwa dake kin shafa jan baki ….
Sadee ya tashi yace bara yaje ya dawo zaya bar Meenalle anan ….tace mashi to …
Tunda ya tafi take ta mata uban surutu kamar dama sun saba ….nan da nan tashiga ranta …sae bayan isha’i ya dawo ya dauketa kamar karta tafi haka hajiya taji …don cewa tayi ya bar Meenalle amma yace tayi hakuri zaya dinga kawota suna gaisawa ….
Ranar koda Alhaji Abubakar ya shigo gaidata …sae da ta mashi firar Yarinyar da Sadee ya zo da ita ….uhm kawae yace mata. ….
Duk bayan kwana biyu Sadee zaya sauki Meenalle ya kaita gidan Hajiyar Abubakar. …
Sannu sannu shakuwa ta shiga tsakaninsu sossae wanda in har aka dade Meenalle bata je gidan Hajiya ba to da kanta zata taso tazo ta ganta ta koma ….
A lokacinne Hajiya ke fadawa Abubakar tana Shaawar yarinya kamar Meenalle …har take fada mashi ..da yanzu Aminatunshi tana nan da takae kamar Meenalle ko ta fita …
Cewa yayi shima bai sani ba …..
Akwae lokacin da tace mashi ko dae zaya nemi Rabi ya karbo diyarshi don tana bukatar ganin jinin danta ..tunda har yanzu bai kuma samun Haihuwa ba …
Nan ma ce mata yayi bai san inda suke ba ….
*Feedohm💞*
💧💧SIRRIN ZUCI …..
💞
Na Feedohm💞
47 to 48
°°••°°
Kwanci tashi ba wuya har Meenalle ta gama Secondary school …
Alokacin ne Mus’ab ya fara nuna mata abunda ke ranshi …amma fur taki yarda …har ta manta da wani aure a rayuwarta …duk wata zaa kaita garinsu gurin su kaka da mamanta har lokacin mamanta bata koma gidansu Musa ba ….haka Musa ya kasa Hakura da Meenalle kullun cikin bala’i yakewa ubanshi ya nemo mashi matarshi …su duka hankalinsu ba kwance ba …
Wani zuwa da tayi har bangazar musa tayi amma sam bai ganeta ba …don kwata kwata ta canza hutu da jin dadi sun canzata. ..bara ka taba cewa diyar hausawa bace
Duk zuwan da zatayi sae ta shiga gidansu Ma’aruf haka zaa ce mata baya nan sannan babu mai numbershi tunda ya tafi bai nemi kowa ba …haka zata ci uban kukanta har ta taho …
Shima mus’ab kokarin cusa kanshi yake amma hakan bai samu ba ……
Lokacin da waec and neco. ta fito a lokacin Alhaji Abubakar ya ce zaya fitar da ita kasar india karatun lawyer ….Alhaji Sadee ya yarda don har lokacin bata san waye ubanta ba ….
Cikin saa ta samu Visa cikin sauri …Su biyun suka kaita indiya tare da mika amanarta gurin wani lecturer amininsu dake can ….
°°••°°
Batayi wata uku ba ta goge wata wayewa tazo mata ta kara kyau da diri duk wanda ya kallu meenalle alokacin sae ya kuma kallonta
Kyakykyawa first class …duk fadin makarantar ba wanda bai san MMA _Meenat Ma’aruf Abubakar_ …
Sun fito daga lecture su kusan Uku a jere …Shamy ta dauki ihu tare da fadin ….Wow *Mr M*…da sauri suka kalli wani ginin dake kallon makarantar …..
Yana rike da glass cup hannushi guda dauke da magzine sannan idonshi sanye da farin siririn glass ….
Feena ta daka uban tsalle tana fadin Yaushe ya dawo …
Shamy tace jiya sajan Sadam ke fada man …Kai *Mr M* ji yanda ya kara uban kyau ….Wallahi Ina mutuwar kaunar …nayi missing dinshi wallahi…..kissing hannunta tayi tare da Nunashi
Sae lokacin Meenalle ta da ido ta kalli wanda suke maganar akae ….
Tafi minti ashirin tana kallonshi har sae da soofy ta buga mata littafi a kai sannan ta sauke ajiyar azuciya
Soofy please meye real name dinshi ….ta fada a hankali …
Tsayawa sukayi suna kallonta cike da mamaki. …..karo na farko kenan da suga Meenalle a wannan yanayin ….kamar tayi kuka tace….Please i need to know ….
Shamy tace …lallae MMA har kin kamu da sauri haka …ina cika bakin ?…injin yau kin yarda akwae mutumin da yafi Maikamshin kyau ….
Please ku fada man dan Allah …ta kwantar sa murya …
Soofy tace …kyaji da gulmarki yadda kike da class wancen babanki ne a wannan fannin …sunanshi *Mr Ma’aruf* …..
Ihu ta kurma ta ruga da gudu dakinsu ……..
Feedohm💞
💧💧SIRRIN ZUCI……
💞
Na Feedohm💞
49 to 50
Wae Meena me ya sameki kike ta murna ko dae Dady zaya zo …..Shamy ta tambayeta. ..
Ido ta waro tare da lumshe ido. . Sirrin Zuci ne ..ba bukatar ku sani …..tana gama fada ta shige toilet …wanka tayi sannan ta fito …ta dade tana shafe shafe …sannan ta dauko wani sabon turare cikin jikkanta ta fesa ta dauko kayan fulani ta saka tare da takalmi mai tsinin …babu abunda bata saka ba cikin kayan fulani har abunda suke daurawa a kai sae da ta daura ….ta fito ….su shamy suka bita da kallon mamaki har ta fice daga makarantar …
Ba tare da shakkar komae ba ta shige gidan Mr Ma’aruf ….
.
Da Sallama ta shige falonshi ….ba kowa ciki sae kamshi dake tashi …..bisa kujera ta samu ta zauna ….ga wani tafkeken hotonshi manna jikin bango a gefen dama. …tana kara juyawa ta hango abunda ya saka dole fararan hakoranta suka fito …photon Meenalle ne kafe a gefen haggu anyi rubutu da gold a jiki …Meenatou …amma duk ya farfashe..
Bata fuska yayi lokacin daya shigo falon ….
Me kike bukata …ya fada lokacin da ya dauki remote …
Shiru tayi tare da kura mashi ido …jin shirun yayi yawa ya saka ya dago da kanshi .
Suna hada ido yayi saurin janyewa ….
Hanya ya nuna mata tare da fadin …idan kallo ya kawoki ga kofar da kika shigo a bude …..
zuwa nayi mu gaisa dakai …kullun Sae na ganka amma baka taba ko da kulani ba irin dan kallon ma da akeyi a kauda fuska idan an kamaku baka yi man …ko baka kula mata ?..
Ido ya dago yana kallonta sannan ya maida kallonshi ga tv ….
Allah sarki ashe magana kadan kake kayi shiru ….ta sake fada a hankali …..wae ma dan rowa ko ruwa bara ka bani ba nazo gidanka…ko ka bani baran karba ba….Mai rowa dae dan wuta
Da sauri ya kalli photon Meenalle ..ya tuna lokacin da tazo gidansu ta zauna tana zuba mashi surutunta .. yana rike da ice cream take ce mashi…Gidanku fa nazo Mai kamshi dan rowa bara ka bani ko ruwa ba ..ni bana ma shan abunda kake sha..ko ka bani so daya kawae zan sha ..shima sae kace man please sannan. …Maikamshi me rowa fa dan wuta …
itama photon ta kalla tare da kallon fuskarshi …ga mamakinta sae taga hawaye na zuba ….
Da sauri ta dawo kujeran dake kusa dashi tana kallonshi cikin rawar murya tace. ..nayi wani abu daya bata maka raine Mr Ma’aruf?..please ka yafe man …
wannan karan ma da sauri ya kalleta …kije please ..ki tafi …ya fada a hankali …
A hankali ta mike ta juya tana tafiya kallo ya bita dashi …yana ganin zata juyo yayi saurin dauke kanshi ….
••°°••
Har kusan sati daya bata kuma ganin Mr Ma’aruf ba inda yake zama .suna fitowa daga lecture ta …ta bar su Shamy ta shige gidanshi …
Falo ta zauna tana jiranshi …amma har kusan minti 39 bai fito ba …sae dae tana jin nishi sama sama yana fitowa daga dakin dake facing dinta …..tun yana fitowa a hankali har ya fara fitowa da karfi ….zaune tayi tana son taje ta duba kuma tana tsoron …
Jiki ba karfi ta mike tana Sanda ta tura dakin …Ganinshi tayi kwance kasan tiles …hannunshi rike da kirjinshi ….da sauri ta ida bude dakin ta dago kanshi tare da daurawa saman kafarta tana girgiza shi …
*Feedohm💞*
💧💧SIRRIN ZUCI…..
💞
Na Feedohm💞
51 to 52
Mr Ma’aruf me damunka …ta fada a rude …
Lunshe ido kawae yake …ya kasa budesu gaba daya….sannan bakinshi ya kasa furta wata kalma
Kuka take iya ranta ..tare da girgiza shi tana kiran sunanshi ….
Jin kukan yake cikin ranshi ..sannan so yake ya bude idon yaga wacece amma sam ya kasa ……
Ma’aruf ka tashi dan Allah ….
Please Ma’aruf ka bude idonka don Allah ka kalleni …nice Meenallen Maikamshi ..ka tashi bana so na rasa ka wannan karan ….
Yana jin Lokacin data fadi Meenalle kokari yake ya bude idonshi …amma ya kasa ..bakinshi kawae yake motsawa. ..ita kadae ke iya jiyo sautin ..Meenatou …da yake fada ….
Rungumeshi tayi tana kuka …sannan ta fice daga dakin ganin baya numfashi ta kira security dinshi suka sakashi mota aka wuce dashi asibiti …..
Emergency aka shiga dashi …abu na farko da aka fara bukata shine jini …..Har lokacin Meenalle kuka take …..
Amma tana jin ance zaa kara mashi jini ta mike tace a debi nata …
Doctor yace ..Madam baa Fiye dibar jinin mace ba …amma akwae jinin fresh anan sae a sanya mashi …
Aa Ku debi nawa ku saka mashi na yadda …ta fada tana kuka. ..
Kiyi hakuri ..wanda muke dashi normal yake …
Bana so a gauraya mana jini da na wani …koda jinina idan kuka diba zaya kare na yarda ki dauka indae Ma’aruf zaya tashi ….
Ganin ba yarda zaayi da ita ya saka aka auna nata cikin saa tana da isasshen jinin da zata bashi …nan da nan aka kwantar da ita gadon da yake kusa da nashi aka diba …..
Kafin a saka mashine suka dibi nashi jinin jikinshi aka auna sannan aka kara mashi da na Meenalle …
Har 10 dare bai farka ba …secutity din yace ta tafi zaya kula dashi …amma hararan data zabga mashi itace amsarshi ….
Anan ta kwana …ganin har da asuba shiru ya saka taje ta samu nurse din tana kuka ta fada masu …ce mata sukayi karta damu zaya iya tashi ko da yaushe tayi hakuri ….
°°••°°
Duk wani test da zaa mashi an gama …doctor ya kira Meenalle kamar yarda tace mashi ita matarshi ce …
Bayani ya mata mijinta nada Kidney problem ( _Nephropathy_) kuma yayi attacking dinshi sossae dole a saka shi adjoining room zuwa wani lokacin kuma baa bukatar kowa yaje inda yake akwae nurse. din da zasu dinga kula dashi …idan kuma har lokacin da suka yankar mashi baiyi ba to gaskia sae dae ayi mashi transplant na kidney …
Yarda ta dinga kuka …shi kanshi likitan sae da yayi nadamar fada mata …
Wata nurse ta tambayi doctor din ko mai ke saurin kawo ciwon …
Rashin bacci na saurin haifawa da mutun ciwon koda …ke har ciwon sugar da ciwon zuciya duk rashi isasshen bacci na kawosu …..amma indae mutun zaya samu isasshen bacci to lalurar zata iya gushewa …idan kuma har tayi illar da sae an mata aiki to bayan anyi insha Allah zata gushe …
Harta ta ruwa gurbatattu zaka iya daukar ciwon koda …don haka ya kamata mu dinga kula da rayuwarmun ….
Sannan rashin shan isasshen ruwa ..mussaman lokacin zafi. …sannan rike fitsari. ..shima yana nakasa koda …sannan yawan cin gishiri…sannan yawan cin nama shima yana kawo matsalar koda ….haka kuma yawan amfani da magungunan saukaka zafi ko antibiotics ..sanna yawaita shan lemuka masu gas …kamar coca cola …lacasera da ire irensu ..
••°°••
Kwananshi 5 A gurin amma ko fardadowa baiyi ba …duk da an hana kowa zuwa gurinshi amma Meenalle na makale ta glass kullun …abinci ma sae da likitan yayi mata da gaske take ci …
Maganar makaranta kuwa ta manta da labarinta …..sae a kwana na 6 ne Ma’aruf ya fara bude idonshi ….lokacin tana tsaye inda take zama ta hango yana motsa bakinshi …..
Da sauri ta matsa gurin .tare da dafa glass din gurin tana hawaye mai dauke da murmushi ….
..Meenatou ..yake fada a hankali …. Why Meenatou ? Me ya maidoki rayuwa. .ko kinzo kiyi proving abunda kike aikatawa …Karki kuma zuwa inda nake …i hate you Meenatou …Bana son ganinki …kin cutar da zuciyata da yawa…idan ina ganinki baran iya rayuwa ko kinzo ki kasheni ne Meenatou ..na rokeki karki bari idona yayi tozali dake in dae har soyayyar yarintarki gaskiyane ….hawaye ke bi ta gefen idonshi kamar an bude fanfo …yayinda da kirjinshi ke sama da karfi
Baya tayi da sauri ta jingina da bango …kanta ya fara juya mata ….
*Feedohm*💞
💧💧SIRRIN ZUCI…..
💞
Na Feedohm💞
53 to 54
Da Gudu ta fice daga asibitin …dakinsu ta koma ta fada saman carpet tana kuka ….su shamy dake nemanta sukayo kanta suna tambayar inda taje ..ganin ba magana zata masu ba ya saka suka kyaleta sae ta koma ….
Bata koma Asibitin ba sae da ta tabbatar ya koma bacci ..sanna taje tana lekenshi tana hawaye …ji tayi an dafa kafadarta ta juyo da sauri.
Ganin Nurse din dake taimaka mashine ya saka ta goge hawayen …
Kiyi hakuri Mrs Ma’aruf ..mijinki zai samu sauki Soon ….
daga mata kai tayi tare da share hawayen …taji dadi sossae ko ba komae yau an kirata da Mrs Ma’aruf …..
Murmushi tayi mata sannan tace ..doctor yana bukatar magana dake ….
Binta tayi suka shiga office dinshi …ya zaune da uwayen takaddu gabanshi ….yace ta zauna ….
Mrs Ma’aruf nasan dae ke musulmace ..kuma zaki yarda da kaddara mai kyau ko mara kyau. ….
Kallonshi kawae take tana hawaye …so take ya fada mata kai tsaye abunda yake son fada …amma sae da ya mata waazi da yake balarabene sannan ya fada mata gaskia sae sun wa Ma’aruf dashen koda ..don duk yarda suke tunanin abun ya wuce nan …..
Tun da yake maganar take kuka har ya gama sannan yace dole ta kira yan uwanshi domin ciki wani zaya bashi kidney daya …
Meye amfani doctor?
.komae zaa bukata na yarje a cire nawa indae Ma’aruf zaya tashi …ko da zuciyata a cire a saka mashi ..Doctor nafi sonshi da kaina a duniya …ku shirya duk abunda zaa kashe zanje na kawo …ina so ayi mashi aiki ya samu sauki da wuri ….tana gama fadar haka ta mike tana kuka …
Dady ta kira tace tana bukatar kudi masu yawa …babu musu ya turo mata 10 million. ..da ta ga kamar bara su isheta ba ta fitar da sarkar gold dinta da Alhaji Abubakar ya sawo mata da wata sallah …ta sayar naira million 5.5
Wanshekare da safe ta hada kudin ta kai masu …naira million 9 kadae suka amsa suka bata sauran. ..ko a ranar sae da doctor yayi encouraging nata aka ta kira wani ko mahaifiyarshi ta bashi wanda baya da wata damuwa a tare dashi …amma ta saka mashi kuka …dole suka fara preparing cire tata daya a saka mashi …duk wani aune aune da yakama suyi sae da sukayi …suka tabbatar idan an cire tata daya wadda aka barta zata iya fuctioning sossae a jikinta …sannan aka shiga dasu dakin tiyata …..
*4 Hours*
Aka fito gangaro su sannan aka kaisu adjoining room su biyu aka jerasu ……
Ta fishi jin jiki sossae don har sae da ta kwana biyu bata farfado ba …shi kuwa kwana daya ya farka. ..tana kwance kusa da gadonshi …ya kura mata ido. …har doctor ya shigo. ….
Ya mashi alluran da ya kamata sannan ya fice don baa cika son a takura masu da magana ba ….
Ranar da ta farka tana bude ido suka hada ido …murmushi ya sake mata tare da lumshe ido …ita murmushin ta maida mashi ..sannan ta kawar da kanta gefe guda ta goge hawayen dake neman zubo mata …..
Lokacin da likitan ya shigo ..ya sameta ta farka shi kuma yana bacci ….
Murmushi yayi mata yace …Congrat Mrs Ma’aruf …yanzu hankali ya kwanta ya samu sauki ko …
Murmushi tayi ta lumshe ido….a haka ya mata allura ya fice …
••°°••
Satinsu biyu acikin asibitin suka samu sauki …sae dae har lokacin suna daure da belt don sae yayi wata shidda zaa cire ….
Haka har lokacin Ma’aruf bai san taka maimai wanda ya bashi kidney ba. ..don tun kafin ayi aikin ta roki Doctor din da kar ya fada mashi ita ta bashi ….
Meenalle na kwance bisa gado Ma’aruf ya fito daga toilet dinshi sanye da jallabiya …kallonta yayi dauke da murmushi yace …
Fateema ya jikin … _kamar yarda ta fada mashi sunanta_
Murmushi tayi tace Alhamdulillah….
Good …ga abinci nan an kawo ki tashi kinji ko …
Tashi tazo yi amma ta kasa …ya matso tare da dagota ta ya jingina ta da kirjinshi kafin ya dauko filo ya saka mata abayanta ya janye jikinshi …yana fadin Sorry Sister kinji
Zama yayi yana bata abincin har sae da ta dauke kai sannan ya tashi yayi sallah ….
Da yake ya fita lafiya kuma doctor yace mashi tare akayi masu aiki. ..shi yasa yake tausayinta da yaga shi har ya samu sauki amma ita ba wani sauki sossae ….
A wani bangaren na zuciyarshi …yana jinta sossae matsalar ya riga ya saka mata tsanar soyayya ….
Idan tana bacci bashi iya dauke idonshi a kanta …haka idan yana bacci bata iya dauke idonta daga kallonshi …
Ana Gobe zaa sallamesu …doctor ya shigo ….Ma’aruf yayi ta rokanshi akan kar ya bar asibitin sae ya fada mashi wanda ya bashi koda …
Doctor ya saci kallon Meenalle yaga idonta na kanshi …sannan ya mai da kallonshi ga Ma’aruf ….yace …gobe zan fada maka …ya fice …
Yana fita ta bi yanshi ta sameshi da kuka kar ya fada mashi ….
Yace Mrs Ma’aruf mai yasaka baki san yasan ke kika ceceshi?
Bakomae doctor dan Allah karka fada mashi ..
wannan ba hujja bace Aminatu …dole a nuna mashi wanda ya bashi …
Zaa nuna mashi amma bani ce zaa nuna mashi ba doctor
*Feedohm💞*
💧💧 SIRRIN ZUCI….
💞
Na Feedohm💞
55 to 56
Me yasa bake ba Aminatu Abubakar? …sannan wacce kike so a nuna mashi …
Doctor ni zan kawota ..kawata shamsiyya ita nake so ka nuna mashi ..ka taimakeni …ta fada cikin kuka. .
Me yasa to Mrs Ma’aruf?..
Wannan Sirrin zuci ne ….
Wayarta ta fito ta kira Shamy tace ta zo ta yanzu ta mata kwatancen asibitin da suke …..
bata fi 10 mints ba sae gata …tana zuwa doctor ya mata bayanin abunda suke so tayi …
Dadi kamar ya kasheta don dama tana mutuwar son Mr Ma’aruf ..kuma ta tabbata idan aka ce ita ta bashi to babu abunda bara ya iya yi mata ba ….don doki kasa barin asibitin tayi sae da wata nurse tace mata baa kwana ba wani dalili sannan ta tafi …
°°••°°
Murmushi ya sake yana kallon Meenalle sannan yace ….yau zan huta da tashin dare da kukanki ..
Hararansh tayi lokacin da take neman maida hawayen da suka zobo mata tace …ni kuma zanyi kewarka ..
Nima ai zanyi kewarki Fateema wasa nake maki kinji ko …karki bari hawaye ya kara fitowa daga kyawawan idanuwannan ..
Lumshe ido tayi tace …Da Zan iya da tuni na tsaidasu Ma’aruf ……
Yauwa ga doctor nan …ya fada lokacin da ya mika mashi hannu …lokaci guda kuma ya bata rai yana cewa …ya na ganka kai daya ..tana ina ?
Doctor yayi murmushi tare da daga murya yace …Mrs Ma’aruf …
Da sauri Meenalle ta kalleshi lokacin da gabanta ya yanke ya fadi …ganin ya kira wata da sunan da ta dade tana mafarki…Sunan da tun tana karama ta so ta amsa sunan …hawaye suka zo mata. ..tayi saurin Mikewa daga kujeran da take ta juya da niyar ta bar dakin…
Hannunta taji an rike da sauri. ..ta juyo tana kallon Wanda ya rike mata hannu ….
Kanta ta sadda ta kasa cigaba da tafiyar ganin Ma’aruf rike da hannunta. …
Ina zaki Fateema bara ki tsaya kiga wadda ta taimakeni ba …lokacin da lumfashina ya nemi ya bar jikina dalilin wata?….ya fada yana kallonta
Shamy ta shigo taci uwar kwalliya …
Meenalle ta girgiza kai tana toshe bakinta …
Ma’aruf yace ..Doctor baka ga wata yarinya ba Wadda ta kawoni Sunanta Meenatou ..ko ba ita ta kawoni ba …
Doctor ya nuna Shamy yace ..Shamsiyya ce ta kawoka kuma ita ta baka kidney dinta daya …bansan wata mai suna Meenatou ba anan …
Da sauri Meenalle ta kwace hannunta ta fice daga dakin tana kuka. …Ma’aruf duk dokin ganin wadda ta taimaka mashi da yake ..sae da ya yunkura zaya bita amma doctor ya tareshi ….lumshe ido yayi duk da ba karan kukan yake ji ba amma yana jin zafin kukanta a ranshi ….
Gurin Shamy ya juyo yana mata godiya sae washe baki take
Yace …kin taimaki Rayuwata Shamsiyya ..banda bakin da zan gode maki …amma ina neman Alfarmar ki aureni a lokacin ne zan nuna maki tsantsar godiyar da nake maki ….
Mr Ma’aruf. ..ta fada lokacin da take washe baki …da gaske zaka aureni …
daga mata kai yayi yana kallon gadon Meenalle …
Shi daya kamata ya nuna zakewa amma itace ta nuna zakewa a gurin …
Tare suka koma gidanshi…sae rawar kai take mashi …kokari yake ya sakata zuciyarshi amma ina ..babu wani babi face na Meenalle ….
Sae dare ta tafi shima sae da ya lallabata sannan …
Da safe ya yanki ticket ….sannan ya kira Shamy sukayi bankwana ta bashi address din iyayenta ya tafi akan bara ya dawo ba sae angama maganar komae akansu …
*Feedohm💞*
💧💧 SIRRIN ZUCI ….
💞
Na Feedohm💞
_Godiya ba adadi gareku …..💞_
57 to 58
Ina labarin Musa?
Da musa ya matsawa Malan sani lamba sae an nemo mashi matarshi …
Malan sani ya rasa yarda zayayi …gashi abokanshi na bashi shawarar ya shigar da kara don Uwar Meenalle da kakarta su suka boyeta ….
Alokacin baida ko sisi ga musa ya addabeshi …dole ya sayar da gidan da suke ciki _Gidan Rabi_…ya shigar da karar …
Su kaka na zaune tsakar gida aka kawo masu sammaci daga kotu ….
Wae ana tunanin sun sace matar Musa ….ana nemansu ranar litinin akotu …
Haka suka shirya suka tafi kotu da safe …aka karanto masu da karar da akayi akansu ..tare da tambayarsu sun san da zance …
Kakata ta murje ido tace bata san da zancen ba kuma sae an fito mata da diya ….
Da Alkali yaga kamar zaa rainawa kuto hankaline sae ya kori karar .
Da yake akwae kudin gidan sae Malan sani ya daukaka kara tare da daukar lauya ….
Lokacin da suka shiga kotun …anan ne aka rufe kaka don ana tunanin ita ta sace kaka …aka rufeta sati biyu a sail ….
Ran Rabi in yayi dubu ya tashi …taje har kano tasami Alhaji Sadee ta fada mashi
••°°••
Meenalle tun da ta koma hostel ba abunda take sae kuka ….Friends dinsu sunyi lallashin duniya amma taki kulasu
Kwata kwata rayuwar garin ta fita ranta. …haka shamy bata da Labari sae na Ma’aruf …wata sa’in idan suna waya sae dae Meenalle ta bar gurin tana kuka …..Sannan taki fadawa Shamy din dalilin da ya saka take hakan …
Sae a hankali sannan ta fara komawa dae dae har ma ta fita lecture …
Da marece ta fito daga lecture ta daga idonta ta kalli benen Ma’aruf kamar yadda take kullun …suka hada ido ….alama ya mata da ta jirashi yana saukowa …..gurin tayi tsaye kanta na kasa har ya karaso …
Dariya ya sake bayan ya leka fuskarta tare da lakutar Hawayen yakae baki ….Bara naji ko hawayen nada zakine shi yasa basu wahalar fitar ….
Murmushi tayi ta saka hannu zata share …yayi saurin saka hanky dinshi ya share mata yana girgiza kai ……
Guri ya samu ya zauna …yana tambayarta …Meke faruwa Fateema …ko har yanzu baki warke ba ….
Girgiza mashi kai tayi tare da juyawa bangare guda ….
To me yasaka kike kuka ? …Wani ne ya sakaki kukan? ..ya sake fada a hankali yana leken fuskarta ..
Kamar tace Kaine Ma’aruf …amma ba dama …sae dae girgiza mashi kai tayi …
To kiyi hakuri kinji Fateema …bana son ganin hawayenshi ko kadan …kin koma gida bayan kin warke? …
Nan ma girgiza mashi kai tayi tare da share hawayen dake binta …..
Kinci abinci ? ….ya tambayeta lokacin da yake kallon bakinta …
Uhm …tace mashi ..
Lumshe ido yayi yace ban yarda ba. ..tashi muje kinji ko …kamar kin taba zuwa gidana can baya …kece ?
Daga kai tayi tana murmushi ….
Hararan wasa ya sake mata yana fadin. ..lokacin kinje kallona ne ko kinje ki saka man ciwon da zamu hadu asibiti …..
bata ce komae ba sae murmushin da tayi..wanda har hakoranta suka bayyana
*Feedohm💞*
💧💧 SIRRIN ZUCI ….
💞
Na Feedohm💞
_Godiya ba adadi gareku ….. Wadanda suka man magana ban mayar masu ba …su gafarceni ba yarda na iya ne ….💞_
*Wannan page din kyautane ga Masu Yara kanana Allah ya raya Mana ku bisa turbar addinin musulunci ya saka masu tausayi da imani🙏🏻*
57 to 58
Ina labarin Musa?
Da musa ya matsawa Malan sani lamba sae an nemo mashi matarshi …
Malan sani ya rasa yarda zayayi …gashi abokanshi na bashi shawarar ya shigar da kara don Uwar Meenalle da kakarta su suka boyeta ….
Alokacin baida ko sisi ga musa ya addabeshi …dole ya sayar da gidan da suke ciki _Gidan Rabi_…ya shigar da karar …
Su kaka na zaune tsakar gida aka kawo masu sammaci daga kotu ….
Wae ana tunanin sun sace matar Musa ….ana nemansu ranar litinin akotu …
Haka suka shirya suka tafi kotu da safe …aka karanto masu da karar da akayi akansu ..tare da tambayarsu sun san da zance …
Kakata ta murje ido tace bata san da zancen ba kuma sae an fito mata da diya ….
Da Alkali yaga kamar zaa rainawa kuto hankaline sae ya kori karar .
Da yake akwae kudin gidan sae Malan sani ya daukaka kara tare da daukar lauya ….
Lokacin da suka shiga kotun …anan ne aka rufe kaka don ana tunanin ita ta sace kaka …aka rufeta sati biyu a sail ….
Ran Rabi in yayi dubu ya tashi …taje har kano tasami Alhaji Sadee ta fada mashi
••°°••
Meenalle tun da ta koma hostel ba abunda take sae kuka ….Friends dinsu sunyi lallashin duniya amma taki kulasu
Kwata kwata rayuwar garin ta fita ranta. …haka shamy bata da Labari sae na Ma’aruf …wata sa’in idan suna waya sae dae Meenalle ta bar gurin tana kuka …..Sannan taki fadawa Shamy din dalilin da ya saka take hakan …
Sae a hankali sannan ta fara komawa dae dae har ma ta fita lecture …
Da marece ta fito daga lecture ta daga idonta ta kalli benen Ma’aruf kamar yadda take kullun …suka hada ido ….alama ya mata da ta jirashi yana saukowa …..gurin tayi tsaye kanta na kasa har ya karaso …
Dariya ya sake bayan ya leka fuskarta tare da lakutar Hawayen yakae baki ….Bara naji ko hawayen nada zakine shi yasa basu wahalar fitar ….
Murmushi tayi ta saka hannu zata share …yayi saurin saka hanky dinshi ya share mata yana girgiza kai ……
Guri ya samu ya zauna …yana tambayarta …Meke faruwa Fateema …ko har yanzu baki warke ba ….
Girgiza mashi kai tayi tare da juyawa bangare guda ….
To me yasaka kike kuka ? …Wani ne ya sakaki kukan? ..ya sake fada a hankali yana leken fuskarta ..
Kamar tace Kaine Ma’aruf …amma ba dama …sae dae girgiza mashi kai tayi …
To kiyi hakuri kinji Fateema …bana son ganin hawayenshi ko kadan …kin koma gida bayan kin warke? …
Nan ma girgiza mashi kai tayi tare da share hawayen dake binta …..
Kinci abinci ? ….ya tambayeta lokacin da yake kallon bakinta …
Uhm …tace mashi ..
Lumshe ido yayi yace ban yarda ba. ..tashi muje kinji ko …kamar kin taba zuwa gidana can baya …kece ?
Daga kai tayi tana murmushi ….
Hararan wasa ya sake mata yana fadin. ..lokacin kinje kallona ne ko kinje ki saka man ciwon da zamu hadu asibiti …..
bata ce komae ba sae murmushin da tayi..wanda har hakoranta suka bayyana
*Feedohm💞*
💧💧SIRRIN ZUCI….
💞
Na Feedohm💞
59 to 60
Haka kawae yake jin farinciki idan yana tare da ita …tare suka jera har cikin gidanshi …ya dauko mata abinci ..tare da lemon ..sannan ya zauna yana tsokanarta har ta koshi ….
Komae nata na burgeshi …bata tafi ba sae da ta gyara mashi gidan sae kamshi yake sannan ta tafi …
Bayan ta tafi ya kira Shamy ya mata bayanin komae …yace mata duk wata magana an riga an gamata …iyayenshi sunje gidansu an kuma bashi ita …..
Haka ta koma hostel Meenalle na kwance ta fada kanta sae hauka take ..ta kusa zama matar Mr Ma’aruf ….
Kamar saukar aradu Meenalle ke jinta …har ta gama ta haukanta bata motsa ba …sae da ta leko fuskarta tace mata …You’re not happy MMA
Am very happy Shamy …Allah ya sanya albarka …tana gama fadar haka ta fice …..
Ma’aruf dinne yazo ya kira Shamy …tana zaune bisa wani dutsi tana hango su….sae wannan iyayi yi Shamy take …..
Dukar da kanta tayi daga barin kallonsu …motsi taji a bayanta …ta dago a tsorace ….Ma’aruf ta gani ya harde hannuwa ya zuba mata ido ….
Saurin juyar da fuskarta tayi tana kakaro murmushi …
Fateema. ..ya kira sunan a hankali …akwae abunda ke damunki kawae baki so na sani ….
Allah ba komae Mr Ma’aruf kawae kaina ke ciwo na fito na sha iska. ..ta fada tana murmushin yake ..
A nan zaki huta …? ..ta so muje na kaiki inda ciwon kan zaya tafi kinji ko ..? ..
Shamy ta iso gurin tare da dafa Meenalle tana fadin …Hubby wallahi mu kanmu bamu san Meke damun MMA ba …
Ido ya waro ..dama kin santa ne ..
Yeah friend dinta ce… Shamy ta fada tana murmushi .
Tashi muje to kinji ko …ki bar nan gurin akwae sanyi da yawa kinji ko …rigar sanyin dake jikinshi ya ciro tare da rufa mata …sannan Shamy ta dagata suka jero tare ..
Ma’aruf ..yace su shiga mota bara su tafi a haka ba …Shamy mai miji aka shige gaba ….ta glass din yake kallon meenalle …duk wani motsi da zatayi a idonshi take …yaso ace itace ta bashi kidney don ya masifar tausayin yarinyar …sannan kallonta yake Meenalle komae tayi burgeshi take ….
Wani guri ya kaisu …ya masu shopping sossae …aka saka a bayan mota …sanna ya dauko wasu kananan ledoji guda biyu …ya mikawa Shamy daya ..ta karba tana godiya ….
Sannan ya mikawa Meenalle guda …ta saka hannun dama zata karba …ya kurawa zoben dake hannunta ido sannan yaki sakin ledar ….
Da Sauri ta janye hannun ta maidasho baya …
Yaso ya ce ta fito da zoben ya gani amma sae wata zuciya tace mashi ba abunda yake tunani bane …don yanzu tuni zoben yamata Meenalle kadan …haka ya kauda tunanin zoben a ranshi ..
°°••°°
Lokacin Alhaji Sadee na tunanin case din karamine …ko Alhaji Abubakar bai fada mawa ba …ya shirya ya tafi …
Ranar da sukaje kotun ..Alkali ya tambayi Rabi shin da saninta aka aurar da Meenalle …..
Rabi tace eh da saninta aka aurar da Meenalle ..
Alkali ya tambaya ..shin ko ubanta ya san da auren ? ..
Tace. ..aa ubanta baisan da auran ba domin ba gurinshi ta tashi ba. …
Alkali yace a kira mashi Wadanda aka daura auren gabansu ….babu shamaki malan sani ya kirawo har wanda ya daura auran …Alkali yace aure ya dauro kuma ba wanda zaya warware auren ba tare da wata kwakwkwaran hujja ba ..
Alkali ya nemi a kira Meenalle …Alhaji Sadee yace sam bata kasar …
Alkali yace to nan da sati biyu a kawo Meenallen …sannan aka sake kaka suka tafi da ita ..
••°°••
Hajiyar Abubakar ta tasa Abubakar dole sae ya karbo diyarshi don tana bukatar ganin jikarta …
Murmushi yayi yace shi yanzu baisan inda zai ga su Rabi ba ….sae dae tayi hakuri …
Kuka ta saka mashi amma ya tashi ya fice daga gidan …
Lokacin tayi nadama sossae …kuma Meenalle ta bar mata son diya mace …don ta gane Rahamace …itama so take ta ga jikkarta ko da ace musakace bama mai lafiya ba …
*Feedohm💞*
SIRRIN ZUCI……
💞
💦Talented writers forum💦
Na Feedohm💞
61 to 62
Alhaji Sadee ya kira Meenalle yace ta taho gida nan da sati biyu …
Taji dadi sossae ko ba komae dama garin ta isheta …
Ranar ta fito zata tafi asibiti …taga motae Ma’aruf inda yake ajeta idan yazo gun Shamy ….
Hanya ta canza tayi uban zagaye …ta fice daga School din …Taxi ta tara ta kaita asibitin ..
Tana zaune doctor na mata bayanin yarda zata kula da lafiyarta idan ta koka gida …kanta na bisa table din doctor din .
Magunguna ya rubuta mata …wanda zatayi amfani kafin ta dawo …mika hannu tayi zata karba taga an karba ….
Lumshe ido tayi ba tare da ta dago ba ….kujera yaja ya zauna kallon doctor din …
Ya jikinta …ya fada tare da kallonta …
Alhamdulillah …bata da matsala …doctor ya fada ..
Lafiya lau kuma ta zo asibiti …Ya kalleta. ..Fateema ki fadawa doctor abunda ke damunki …
Babu komae …ta fada ahankali …
Doctor yace …Tazo ne tana so ta koma gida shine na rubuta mata maganin da zatayi amfani dashi …sannan bara tasha wani ruwa ba sae swan har tsawon wata shidda ….
Ido ya lumshe sannan ya mike. . tashi muje Fateema. ..
Ba musu ta mike suka fice tare da yi ma doctor din godiya. …
Gaban mota ya bude mata sannan ya zagaya ya shiga …..kura mata ido yayi yana karantarta …
Fateema. …..
Kamar tace mashi Meenatou dae ..amma babu dama …sae dae ta juyo da fuskarta gefenshi idonta na rufe. ..
Ba da wata manufa ba ya kamo hannunta ya rike. ..Fada man meke damunki …
Girgiza kai tayi idanuwanta suka ciko da kwalla …
Babban yatsanshi ya saka ya share kwallan …sannan ya tada motar hannunta na rike cikin nashi suka fice daga asibitin …..
Kafin ya maida ta makaranta jikinta ya hau rawar sanyi …
Ya shafi wuyanta …ya dauki zafi kamar wuta …kwantar mata da sit din yayi baya ta kwanta …sannan ya wuce da ita gidanshi …tun kafin su isa ya kira Shamy yace ta tarad dashi gidanshi …..
Suna isa ya yi Parking ya fita ba tare da ya mata magana ba ya dauketa ya shigar da ita gidan …dakin shi ya kaita ya kwantar da ita saman gadon …
Sannan ya fita ya shiga kitchen ya hado mata coffee ….lokacin da ya dawo idonta a. rufe …sae yayi zaton ko bacci take …ja aje coffe din ya gyara mata kwanciya sannan ya rufe ta da bargo ya fita daga dakin ya koma falo ..
Yana fita ta bude idonta tare da tashi zaune ..tana kallon dakin …duk kusurwar dakin hoton Meenalle ne …wani photon ma bata san inda ya dauketa ba ….
Kanta ta daura saman cinyarta tana kuka ….hannu ta saka ta janyo pillown dake gefenta ….
Ribbon din da ta bashi tun tana yar yarinya ta gani cikin wani glass cover an Rubuta _*My Heartcherry*_.. _*They say you only fall in love once, but that can’t be true… Every time I look at your Pictures, I fall in love all over again Meenatou*_
Glass din ta dinga shafa tana hawaye …ita kadae …..Motsin magana ta taji ya saka ta yi saurin komawa ta kwanta ..
Tana jin lokacin da yake cewa Shamy ta shiga dakinshi friend dinta na ciki …..
Ta turo dakin ta shigo tana fadin ..Meena meke damunki . .ta zauna bakin gadon tare da dago kanta. …
Ayya …me kike wa kuka kuma …dan Allah ki daina Meena …tashi ki sha magani zaki samu sauki ….ta fada kamar zatayi kuka ..
Ma’aruf ya shigo yana tambayar ta farka …amma sae ganinta yayi jikin Shamy tana kuka. …
Bara ya iya jin kukan ba shi yasa ya juya da sauri ya fice daga gidan ….
Da kyar Shamy ta samu tayi shiru ta hada mata ta hada mata Coffee sannan ta bata maganin da Ma’aruf din ya bata …ta koma tayi bacci …
Shamy ta kira Ma’aruf din tace yana ina. ..
Ce mata yayi …Ina Fateema …
Da yake ta san Fateema yake cema mata …sae tace mashi tayi bacci ..
Ya sake ajiyar zuciya yace gashinan zuwa. ……
ko da ya dawo ce mata yayi ta tsaya su kwana anan ta kula da ita ….
Murna tayi don ko ba komai yau zasuyi fira sossae da shi …
Amma sae taga hankalinshi sam ba gareta yake ba. …duk minti biyu ..zaya leka dakin yaga ko ta tashi …
Meenalle kuwa ta dade da tashi amma taki bude idonta …tana jin lokacin da suka shigo da shamy ya daga bargon tare da shafar wuyanta yaji ko zazzabin ya sauka …
Shamy ta wani hade rai tana fadin Meye zaka wani tabata bayan ba aurenta zakayi ba …ni bana son wannan wulakanci ..
Shima daure fuska yayi yace. ..bakya ganin bata lafiyane. .
Don bata lafiya sae ka tabata har da wani lumshe ido ..me kake nufi …
Bai ce mata komae ba don baya son ganin fushinta …sae towel daya mika mata tare da fadin …please ki jikashi ki dinga goga mata a jikinta ..
Hararanshi tayi tace..tunda har ka iya taba wuyanta wannan ma bara ya maka wuya ba…
Kwantar da murya yayi yace. . Please Shamy kiyi mata mana. .friend dinki ce fa …
Bafa zanyi ba ..ta fada kai tsaye ..
Ok …to fita …ya nuna mata kofa …
*Feedohm💞*
?
💧💧 SIRRIN ZUCI ……
💞
💦Talented Writers Forum💦
Na Feedohm💞
63. to. 64
Tsaye tayi tana kallonshi cike da mamaki …tunda take bata taba ganin ya daure mata fuska ba sae yau …kullun cikin lallashinta yake …
Tsawa ya daka mata lokacin da ya fito daga toilet rike da bucket a hannu …
Baki ji abunda nace maki ….Get out …ya nuna mata kofa …
Fita tayi a fusace tare da banko masu kofar …shima karamin tsaki yaja …sannan zauna gefen gadon tare da cire bargon …..
har ya kai hannu zaya daga mata riga ya tsaya cak yana kallon fuskarta …mikewa yayi …ya rasa ta yaya ma zai mata …tana jinshi sae dukan hannunshi yake …sannan ya mike ya fita daga dakin …he decide yaje asibiti ya kira wata nurse tazo ta mata ya bata kudi
A falo ya wuce Shamy zaune ta kasa fita daga gidan ….tana ganin ta fito ta tareshi …
am sorry Habibi …
Lumshe ido yayi tare da kallonta bai ce mata komae ba …
Kayi hakuri Please bara naje na mata kaji dan Allah…Please Hubby …
Kofar dakin ya nuna mata tare da zama kujeran falon ….
Da Sauri ta shiga dakin. ..ta tarad da Meenalle zaune tana goga towel din a jikinta a hankali. ..
Tayi saurin amsa tana fadin ..Sorry MMA kawo na maki …
A hankali tace. ..barshi ma nayi. …
Sorry please ta fada tare da rike mata hannu …
Komawa tayi ta kwanta ….rigarta ta cire sae dae ta kasa kwance belt din dake kirjinta na aikin da aka mata …
Ma’aruf ta kira ya kwance sannan ya fita ya basu guri …
Sae da tayi sati daya a gidan tare da shamy …kula yake bata sossae idan ya shigo ya ga tana kuka …ya dinga tambayarta meke damunta sae dae tace ba komae ….
Ranar da zasu koma ..ya shigo dauke da iv card na bikinsu ya mikawa Shamy ta gani ….
Wani Tsalle ta buga ganin designing din da aka masu da ratsin gold …ta makale Meenalle tana nuna mata …
murmushi tayi ta kallah tana karantawa
*Conjugal Bless* 💖
_MR MA’ARUF IBRAHIM_
*weds*
_SHAMSIYYA A MAMMAN_
_on 21 July 2017_
sae decoration din da aka bishi dashi da gold ana rubuta meenatou …idan ba sani kayi ba bara kace mae aka rubuta ba …zaka dauka kwarewace gurin wanda ya buga IV din …
Wow yayi kyau …ta fada tana waro ido …
Murmushi yayi ya wucesu …sae uban murna Shamy take. …sae da ya canzo kaya sannan ya fito rike da ticket guda uku ya mika masu ….
Da nashi dana Meenalle Sae na amarya Shamsiyya ….
Meenalle ta kalleshi ido a waje tace Mr Ma’aruf ..ni ba gobe zan tafi gida ba …
Gobe zaki tafi Fateema ..ya fada a hankali tare da bude coca cola ya zuba a cup …
Da Sauri ta tashi ta je ta dauke cup din da sauran lemun tana kallonshi …doctor yace ka daena shan lemun dake da gas a ciki …
Lumshe ido yayi sannan ya bude su yana mata wani irin fitinanne kallo …
Da sauri ta juya ta koma kusa da shamy ta zauna tare da daura kanta saman bayanta ….
Zo nan Fateema ….ya fada tare da mika mata hannu …
Makale kafada tayi tana kallon shamy …wacce ita hankalinta ma naga wayarta sae daukar photon IV din take tana turawa a social media ….
Ido ya lumshe yace …me zaki bani tunda kin dauke nawa …
Mikewa tayi ta je ta bude fridge ta dauko mashi lemun kankana da abarba da ta hada dazu ta tsiyaya mashi a cup ta mika mashi …
Hannunta da cup din duka ya hade ya rike yana kallonta …
Bata fuska tayi ya saketa da sauri tana yarfe hannu. ..
*Feedohm💞*
💧💧 SIRRIN ZUCI ……..
💞
💦Talented Writers Forum💦
Na Feedohm💞
65. to. 66
Tun da safe suka tafi Airport …shi da Shamy suka zauna side daya sae Meenalle na gabansu ita da wata mata …..
Ko da suka sauka Meenalle har ta kira su Alhaji Sadee tace sun iso ..don haka tare motocinsu Ma’aruf suka iso da wadanda aka zo sauka Meenalle dasu ….
haka ta shige mota ba tare da ta kallesu ba …har suka fice daga airport din …sae lokacin ta sake kuka tare da fadawa jikin Mus’ab don tare suka zo …
Bawan Allah duk ya rude ..duk da yayi aure
har da yaro daya baya. tafiyarta ……
Haka suka isa gida …
Sae da ta huta sannan Alhaji Abubakar da Sadee suka kirata Falo ..
Alhaji. Abubakar yace …da gaske Aminatu an maki aure …
Gabanta ya fadi don tama manta da wani aure a rayuwarta …daga masu kai a hankali …
Alhaji Abubakar yace …da yardarki aka maki auren ? ..
Nan ne tace aa …bata san anyi auren ba sae dae kawae musa ya zo ya dauketa ..
Alhamdulillah …Ya fada tare da tashi ya fita …
Sadee ne ya. bude mata komae a ranar har da ba shine ubanta na Asali ba sae da ya fada mata …sannan ta fada mahaifinta na sonta don ba yarda zayayi ne shi yasa har ya barta hannu. mamanta ..
Tabbas bata mu sa mahaifinta na sonta ba .don zaman da tayi tare dashi ya nuna mata so ..sae dae bashi da dalilin da zai banzatar da ita don Mahaifiyarshi ta umurceshi don Haka tace Ma Sadee ..yayi hakuri tacigaba da kallonshi a matsayin ubanta ..
Nan ya nuna mata matsayin da uwa ke da shi ga yayanta tare da mata waazi sossae har jikinta yayi sanyi ta cire kalmar da take fada cewa bata daukeshi uba na kirki ba ..
A Ranar ta dauke Abubakar a matsayin Ubanta amma ta kasa yarda da hajiyarshi a matsayin kakarta
Basu bar falon ba sae ga hajiyar ta shigo tana murna an fada mata Meenalle ta dawo
ta janyota jikinta tana fadin …yaushe kika dawo yata ..
zare jikinta tayi ta fita daga falon ta barta zaune tana kallon Ikon Allah
Sadee lafiyar Aminatu kuwa ? ..ko wani abu kukayi mata
Murmushi yayi yace …babu abunda ya sameta Hajiya …
Anya kuwa Sadee …ta fada tana taba hannu ..
Me kika gani ne Hajiya ..ya fada yana murmushi ..
Ahto ..naga yarda Meenalle ke nan nan dani amma yau ta nuna kamar bata sanni ba …kasan Allah Sadee ..ina kaunar Aminatu ..da iyayenta zasu. bar man ita da ta zauna hannuna har na aurar da ita ..shin ni kau sadee baka san inda Rabi da diyarta suke ba ..idan nama abubakar maganar baya saurarena ..
Hajiya kenan . yanzu kuma jikkar har mace kina so ..?
jikinta yayi sanyi tace ..to tunda ita Allah Ya bani ba dole na rungumeta ba ?
Hmm Aa Hajiya ki tsaya ki gani ko Allah dae zai baki namijin ….yana gama fadar haka. ya tashi ya shiga ya kira mata matarshi ta fito …
Sama Sama suka gaisa ta tashi ta tafi cike da tunani
*Feedohm💞*
💧💧 SIRRIN ZUCI. ….
💞
💦Talented Writers Forum💦
🔝
Na Feedohm💞
69. to. 70
Tun da safe Meenalle ta shirya tace wa Sadee zata je ta Gida gurin Mamanta …
Direba ya saka ya kaita har zarian sannan ya bata kudi masu yawa …
A Zaure ta tarad da Mamanta na waina …ta rungumeta cike da murna ..suka shiga cikin gidan …ta sake maman ta fada cinyar Kaka tana kuka ….
Yaro ya shigo wae ana kiran Meenalle ….
Kamar tace bata zuwa sae kuma taga kara taje kila drivern da ya kawota ne zaya juya …dan haka ta dauki gyalenta ta fice …
Sae da ta daga kai ta kalli Benen gidansu Ma’aruf kafin ta fita …
Tsaye ta ganshi rike da robar swan yana waya …sae murmushi yake da alama da shamy yake …
Ajiyar zuciya ta sake ba tare da ta fita ba …sae aikawa tayi tace wanda ke kiranta ya shigo tana zaure …
Kamar mahaukaci ya shigo duk ya rame yayi baki …sa sauri taja baya tana bata fuska ta nuna shi …Kai ke nemana? ..
Washe baki yayi yana fadin …kece Meenalle …Meenalle ke kika koma haka …Allahu Akbar …kin ganeni …nine Musa ..
Musa ta fada tana kallonshi sama da kasa ..sannan tace …daga ina. ..
Baki ya washe yace…Musa dae Mijinki har kin manta ni ..gaskia an cuceni …
Ido ta waro. …oh wae Musa dan Sani na gidansu Luba? ..
Shi ma Meenalle ….bara naje na fadawa Baba kin dawo sae a janye karar sae mu koma ko ? ..
Dariya tayi tare da nuna shi da hannu. . ina jin har yanzu baka manta da ko wacece Meenalle ba ko …..
Bata jira amsarshi ba ta koma gida ta barshi tsaye …
••°°••
Mamanta ta kalleta tace …wa nene ya aiko kiranki ..
Mama wae Musa ne ..ta fada a hankali…sannan ta kalli kaka. tana goge hawayen da suke neman zubo mata tace ..
Kaka Maikamshi ya shigo ….
Daga mata kai tayi tace ..yazo Meenalle ..Kullun sae ya tambayi shin kin dawo Meenalle ..ko dazu da safe ya shigo ya gaidamu ….jiya ya dawo ma ..
Lumshe ido tayi a hankali tana kallon wainar da suketa lodawa a Coler ..wannan fa ta mecece..
Tsohuwar ta kaudar da kai tace …gudunmuwa nakewa Maikamshi ta bikinshi …aure zayayi ..jibi ake daura auren ma Meenalle ….
Kaka ta goge hawayen da suka zubo mata tace …naso Meenalle …naso ki zama matar Ma’aruf …amma aka cucemu …Yana sonki sossae. .
Tashi tayi tana fadin …zan koma kaka…….
Da sauri ta fice daga gidan ta shige mota tace su koma kawae …..haka driver ya jata suka koma gida ba tare da tayi kwanakin da ta zo yi ba. …
••°°••
Tana shiga gidan ta tarad da Shamy tazo ….suka rungume juna suna ihu …
Shamy tace tazo daukarta ne …ana ta hidimar biki amma babu ita ….sannan Mr Ma’aruf duk yabi ya damu baki zo ba …gaskia ki shirya ..don ni na riga na tambayi dady da mommy ashe ba wanda kika fada mawa …da banzo ba da bara ki zo ba kenan. ..
Murmushi tayi tace ..Shamy ai kinsan dole nazo bikinki ..
Harara ta sake mata tace ..Banga alama …ni dae yanzu ki shirya muje …
Duk wani abunda zata bukata sae da ta dauka …sannan ta shiga tayi wa Mom bankwana suka shiga mota da yake shamy tare da driver suka zo …suka koma zaria ….
••°°••
Tun a mota Shamy ta kira Mr Ma’aruf tace tare suka taho da Fateema …
Yana tsaye ta bene ya kurawa gidan kaka ido ya waro ido yana murmushi ..yace da kun shigo gari ki kirani ..
Ok hubby ..ta fada tare da kissing din wayar sannan ta kalli Meenalle tace ..
Gaskia dole ki saki jikinki wannan bikin ..in ba so kike ki dagawa hubby hankali ba. .ni na rasa wane irin mutuncine tsakaninku ..karfa kiyi man snatching. ..
Murmushi Meenalle tayi tace …kisha kurumin Shamy sanin kanki ne banda niyar maki snatching karki manta kidney dina daya tana jikinshi ..kuma silar hakan ne na hadaku ..kinga kuwa fadin kalmar snatching kamar butulci ne kika mani …..
Zatayi magana ta dakatar da ita .. please mu bar wannan maganar Shamy. ..
Shamy ta kwantar da kanta a bayanta tare da fadin …Am so sorry Meena. ..
Lumshe ido meenalle tayi ..itama ta daura kanta saman cinyarta ..a haka har suka isa …
Suna shiga garin ta kira Ma’aruf ta fada mashi sun iso ..yace su jirashi bakin gari ..zaya zo yanzu ..
*Feedohm💞*
💧💧 SIRRIN ZUCI …..
💞
💦Talanted Writers Forum💦
🔝
Na Feedohm💞
71. to 72
Ko 15 Mints basuyi ba ya iso tare da kwankwasa masu glass din motar ..da yake side din Meenalle yayi knocking sae ta sauke glass din …
Kamshinshi ya bugeta bata san lokacin da ta furta ..Maikamshina….
Saurin kallon bakinta yayi tare da fadin Me kika fada fateema ..
Lumshe ido tayi tare da bude kofar ta fito ..sannan tace ..Ango ina wuni ..
No ba haka kika fada ba …abunda kika ce shi zaki maimata ..
Dan hararanshi tayi tace …Cewa nayi ..sae Kamshi kake …
A hankali ya lumshe ido tare da dubar Shamy yana fadin muje na kaiku …shi ya tafi
Motarshi suka shiga …Har gida ya kaisu …Meenalle ta shiga ciki ta barsu a mota …..gidan ya cika da kawayensu ..har da soofy. ..sae murna suke ana labarai …..
Da daddare kowa yayi bacci aka bar Meenalle sae juyi take …Soofy ta farka ta dade tana lura da ita …sannan ta gangaro kusa da ita ta kira sunanta a hankali …
Meenalle ta bude ido tana kallonta tace …Bakiyi bacci ba …
Soofy ta mike tare da jan hannunta suka koma falo …zama sukayi sannan ta kalli Meenalle tace …Meena meke damunki ..
Me kika gani Soofy …ta fada tana kallonta …
Meena komae ma na gani …Mr Ma’aruf shine Ma’aruf dinki ko? ..
Da sauri ta rufe mata baki …tace …waya fada maki Soofy ..dan Allah ki bar wannan maganar …bashi bane .
am not kid …Meena…me yasa zakiyi haka …kuma ba Shamy ce ta bashi kidney ba kice Meena …duk wannan sirrin na meye ….Shin baki sonshi ne yanzu ….Dole zan fada mashi gaskia gobe ..
kuka ta sake tana fadin ..
aa Soofy. ..karki fada mashi dan Allah …wallahi baya sona yanzu …
Karya kike Meena ..har yanzu akwae kaunarki ..duk da bai san ke bace Meenalle amma ki kalli idonshi kaunarki ce ke cike dashi …kuma sae na fada mashi …
Cikin kuka …wallahi Soofy baya kaunata naji yana fada ne ..ya tsaneni ..bansan me na mashi ba. ….
Ke dae kika sani ..ni zan fada mashi idan kinso idan zai aureki sae ki ki aurenshi
Soofy ni matar aurece …ta fada a hankali
A masifance ta juyo tana fadin karya ne wallahi …
Hannunta ta ruko tana kuka …ki yarda dani Soofy ina da aure ..da banda aure da babu abunda zai hani bude *SIRRIN ZUCI* …sun aurar dani ga wani …wani wawa Soofy Wawa irin Musa …Tabbas ina son Ma’aruf ..amma katanga babba ke tsakanina dashi …sun dasa mashi tsanata ta yarda har yake furtawa ….ya zanyi Soofy ….ta kara fashewa da kuka. .
Tausayinta yayi balain kamata …dukawa tayi tare da rungumeta a jikinta …kiyi hakuri Meena…in sha Allahu dole musa ya sakeki …kin sani mahaifina Justice ne …zan mashi magana dole a bi maki hakkinki …kiyi hakuri dan Allah
°°••°°
Karfe biyu dae dae aka daura Auren Ma’aruf da Shamy gaban dunbin mutane. …Amarya baki yaki rufuwa haka ango …Sae shirye shirye ake ..don bayan biki da kwana uku zasu bar kasar saboda karatunta da kuma aikinshi …
Wajen karfe 9 ne akace a fito da amarya zaa tafi dinner ..
Amarya ta shigo hall tare da manyan kawayenta guda biyu ….
Chanchadi Mazakwae …uhmm abun baa magana ..idan kaji ana Carai ..to wannan amaryar ta wuce anan …Sky blue din gown ne a jikinta …fuskarta na rufe da wani golding din net daga samanshi ya fitar da wani shape kamar an daura crown ……
Ango na zaune suka shigo ….lumshe ido yayi tare da jingina da kujeran da yake kai ..sannan ya bude su a hankali tare da sakin wani fitinannen kallo yana kallon right side din amarya ….
Sae lokacin na kalli inda yake kallo ….
Ido na waro sannan na lumshesu nima kamar yarda yayi …Phone dina ta sulale ta fadi kasa …duka glass din ya dargaje😒😥😥…bansan lokacin da nayi zaman dirshan ba …ina kallo.. .sae da na lalubi wayar da niyar na fada maku me na gano …sae lokacin na lura ashe ta dargaje 😒😒😒
*Feedohm*💞
💧💧 SIRRI ZUCI ….
💞
💦Talented Writers Forum💦
🔝
Na Feedohm💞
================= Gidan Novels =====================
73. to 74
Meenalle nagani tsaye rightside din amarya …sanye da gown itama amma Pinch colour ….sae head maroon …ta gaji da haduwa ..fatar har wani kyalli take. ….
Ma’aruf ya taso a hankali har ya iso kusa da amaryarsa …hannnuta ya kama tare da matsawa kusa da Meenalle …
Natural beauty …ya fada mata dae dae kunnenta ….phone dinta tayi kara ….
Ta dan saci kallonsu ta dauke kai ..tare da ficewa daga hall din ….ta dauki sayar. ..
Aminatu …gamu a bakin gate amma kamar baku ciki ko ? …aka fada daga dayan bangaren …
Muna ciki. mana ku shigo har zaa fara dinner ….
ki fito. ki shiga damu please …ko mun shigo bamu san inda zamuyi ba …don gurin da alama yana da girma. ….
Okey ..gani nan fitowa ta fada …tare da juyawa ta kalli su Shamy …Ma’aruf rike da hannunta …wani abu ya tokare mata kirji ta fita da sauri ….
Daga can side din ta hango wata bakar jeep ….ta fito da wayarta ta kira number. ..kuna ina …
Ki tsallako muna cikin jeep din dake tsaye gefe guda ….kafin tayi magana an kashe wayar ..
Tabe baki tayi ta tsallaka tare da knocking din glass din motar na gaba ….
Kofar baya aka bude …wani kato ya fito ya toshe mata baki ya jata cikin motar suka hau titi da gudu …
Hannun ta cire daga bakinta tare da jan uban tsaki ta gyara zama cikin motar tana watsa masu wani uban kallo ..
Da cewa kuka yi na fito kunzo sace ni ne da baku wahalar da kanku ba ….ta fada tana kallonsu ..
Torch light din wayarta ta kunna ta haska su daya bayan daya. ..sannan ta maida hasken ga na kusa da ita ..
Musa Sani ..ta fada tana kallonshi ….matsalata dakae wawa ne …bakka ganewa ..dan zaka dauki yarinyar da kake tunanin matarka ce sae ka hado da wadannan jakunan ….? ..
Ke…..wani ya daka mata tsawa …tare da nunata da hannu.
Hannun yaji an murde da karfi har sae da yayi kara alamun karewa .tare da angazashi baya ….daga lokacin bai kuma cewa komae ba ..
Meenalle ba tsoro …haka ta dinga wankesu ..har suka shiga wani tsohon daji …sae lokacin ta lura sun bar titi ….
Bata kuma cewa komae ba sae kallon ikon Allah da ta tsaya tana yi ….har suka isa wani dogon gini ..baraka iya cewa ga karshensa ba . ..
Daya ya sauka ya bude masu gate din suka shigar da motar ciki. …
Ba wani babban gida bane …duka kofarshi daya ta shiga ciki sae ta gate ..duka gidan arufe yake …suka faka motar suka fito …
da yake akwae hasken wuta …ta bisu da kallo ..kamar mahaukata haka suke ko wane bakikkirin dashi sae mazurai suke …
Ta hadiyi wahalallen miyau sai lokacin gabanta ke faduwa ….amma ta dake ta na hararansu ….
Mu shiga ciki Meenalleta …Musa ya fada yana dariya …
Murmushin ta sake mai cike da takaici …tace ..ai ko bakace ba Musa kasan zan shiga sannan na zauna daku har sae kun gaji dan kanku ku mayar dani kuma na kwanta idan kai dan iskane kayi gigin zuwa kusa dani …
Girgiza kai yayi yana wata dariya ..Meenalleta kenan ..kiyi hakuri ki soni muyi rayuwa a duniyata ..ki haifa man ya’ya kyawawa irinki …
Wace duniyace gareka Musa…duniyar karnuka ..Sannan ba Ya’ya zan haifa maka ba …Uwaye zan haifa maka. …
Gaba yayi yana dariya ta bi bayanshi …sauran suka take masu baya. ..har wani karamin daki ya kaita mai dauke da karamin gado sae wasu akwatuna guda uku …
Meenalle ga lefenki nan …wanda da ban baki ba ….akwae english wears a ciki kinsan ni mayan sune ….ya fada yana washe baki ..
Dariya ya bata sossae har tana rike ciki …sannan ta nufi gurin gadon ta cire pillow ta aje a kasa ta kwanta ..tunda dama tayi isha’i ..
Tana kwance ya shigo tayi saurin tashi zaune tana kallonshi…kazar amaryace na kowa ..ya fada yana kallon kirjinta …
Babu tsoro taja ledar …tana dubawa ….je ka dauko plate ..ta fada ba tare da ta kalleshi ba …
Da sauri ya mike yana fadin Meenalle har kin sauko zaki ci kazar amare ..kila dama dan ban nuna maki ita ba shi yasa kike zagina dazu ..
Musa baka gane …ko dae Mamansu luba hada maka da nonon awakai lokacin da take shayar da kai….ta fada tana murmushi
Da kuwa ta cuceni yasin …ya fada sannan ya fice daga dakin …
Da Sauri ta mike ta rufe dakin da keys din dake jikin kofar ta koma ta harde kafa ta fara cin kazarta …
*Feedohm💞*
💧💧SIRRIN ZUCI …..
💞
💦Talented Writers Forum💦
🔝
Na Feedohm💞
75. to 76
Meenalle bude ga parantin ….ya fada yana buga kofar …
Musa Aje akwanta sae Allah ya hada mu gobe ….ta fada daga cikin dakin ..
Haba Meenalle ke fa kikace na dauko ..ki bude dan Allah …wallahi ni bama kazar zanci ba ..ke nake so…
ashe ma kai sakaraine …..ta nannade ledar tare da gyara kwanciya ..
Yayi lallashin duniyar nan ..amma taki ko kulashi ..daga karshe yace …Meenalle ke yar iskace ko…kinsan ba tare zamu kwana ba kika cinye man kaza ko…to wallahi da safe sae na maki shegen duka ….ya bugi kofar da karfi ya wuce ….
Tana kwance taji alamar mota ta fita daga gidan …ta mike ta leka ta taga …taga sun fice sae mutun daya zaune bakin kofar an barshi gadi …..
Ta bude kofar ahankali tare da lekawa …babu kowa sae falon dake gauraye da hasken wuta …ta fito tana sanda ta rufe kofar shigowa ciki sannan ta shiga wani karamin daki mai shegen duhu. …da wayarta ta haska taga duk kayan fadane aciki ..sae bindiga da bata wuce 5 ba kirar AK ….sae uwayen akwatuna da da buhu cike da kudade ….
Sae lokacin ta tabbatar yan fashine .. ..dakin da aka bata ta koma da kwanta ..
Su Musa suka dawo babu irin bugun duniyar da basuyi ba amma Meenalle bama ta sani ba tana baccinta …
Da Asuba ta farka ta iske missed call kusan 76 …50% duk na Ma’aruf ne …sae Soofy itama ta kirata …sae Mamanta ….
Mamanta ta kira ..tace fada mata duk abunda ke faruwa …sannan tace mata ta kwantar da hankalinta …ta dinga mata addu’a in Allah ya yarda zata dawo ….
Sannan ta kira Soofy ..itama addu’arta ta roka ta kashe wayar …
Text ya shigo mata na Ma’aruf ne … _Fateema ina kika shiga ne ? kina dae lafiya ko ,? …._
Reply ta mashi _Na koma gida fatan Alkhairi kai da amarya_
Ta kashe wayar gaba daya …cikin saa taga toilet acikin dakin …ta shiga tayo alwala ..cikin akwatin da Musa ya nuna mata ta duba ko zata ga hijab …amma babu …sae Zanin atamfa ta dauko ta lulluba tayi sallah …..
Sae da gari ya waye sannan ta fita daga dakinta …lekensu tayi babu wanda ya farka ..kamar matattu …tsaki tayi ta bude kofar …
Firgigi suka farka …ko wane sae ya taso da zuciyarshi …da sun hada ido da musa sae ya koma ya kalli kasa …
Musa kuwa duk bala’in da yayi niyar ya mata sae ya kasa …ya matsa yana washe mata baki…..ba kuma wani abu ya hana ya mata ba .aa tunowa yake da lokacin da suna kauye ..idan zai bugeta azabar da take mashi …
••°°••
Tun kafin a shiga court Alhaji Abubakar ya sami Alkali ya mashi bayanin Musa ya sace Yarinyar …Haka aka nemi Malan Sani shima bai zo kotun ba …..
Alkali ya aika a daukoshi …yana zaune bisa dankali aka daukoshi sae masifa yake
Aka zo dashi office din Alkali …aka tambayeshi ina Musa ….kada kai yayi yace bai sani ba ..
Juyin duniyar nan Amma Malan sani ya yace bai san inda musa yake ba ….
Nan take Alkali ya raba auren tare da tsare Malan Sani har sae Musa ya dawo da Meenalle lafiya ..idan kuma wani abu ya sameta to hukunci mai tsanani zai hau kanshi …
Lokacin da labari ya isa gurin musa sae cewa yayi …indae sae ya dawo da Meenalle zaa saki Malan sani sae dae ya mutu a daure …
Ran Malan sani yayi bala’in baci …ranar ya tsinewa musa yafi a kirga. .sannan yayi nadamar abunda ya dinga yi akan musa gashi yanzu ance ya maido Yarinyar a kwanceshi yace sae dae ya mutu a daure …..
••°°••
Ma’aruf da amarya aka koma india …rayuwa suka bude mai kyau …matsalar daya ce Shamy bata san yarda zata kula da mijinta ba ….illa iyaka ta dafa break ta ta fi school …amma abincin rana dana dare sae dae ya sawo masu …
Lokacin suna gab da fara exam amma babu Meenalle ..hankalin Ma’aruf yayi bala’in tashi ..har rigima sukayi da Shamy lokacin …wae sae ya fada mata dalilin da yasa ya damu ….
Bai ce mata komae ba …yaja har school din ya saki iyayen kudi sannan ya samu wata wadda ta riga ta gama school din aka sakata ta zaunawa Meenalle …
Shamy ta shiga dakin Ma’aruf rike da cup din coffee …bai san ta shigo ba yana rike da photon Meenalle ….ji yayi an fuzge photon tare da fasashi kasa …
Lumshe ido yayi ba tare da yace mata komae ba ya duka yana tattara photon ..
kafa ta saka tayi wurgi da wanda ya tattara ….
Azuciye ya mike ya wanka mata mari …tare da jan hannunta ya fitar da ita daga dakin ya saka key …
Bugun kofar ta dinga yi kamar mahaukaciya tana bala’i ….har sae da ta gaji sannan ta yi shiru …sae da tayi Wata ba tazo shinfidarshi ba …haka bata mashi magana ba …
Ma’aruf ba mai son hayaniya bane ganin abun nata bana karewa bane ya saka ya kirata da kanshi ya lallasheta ganin lokacin tana dauke da ciki …..
*Feedohm💞*
💧💧SIRRIN ZUCI ……
💞
💦 Talented Writers Forum💦
🔝
Na Feedohm💞
77 to 78
An baza ko ‘ina ana neman Meenalle amma ko labarinta baa samu …an kirata a waya an tambayeta ina take amma sae dae tace wallahi bata sani ba ….
Haka musa ma nemanshi ake ruwa jallo ..amma da yake munafukine ..suna da wani tsari indae ana neman su to basu taba haduwa da masu neman nasu ….
Kuma bai fasa shigowa zaria ba ….duk lokacin da yaso zaya shigo kuma ya fita ba tare da wadanda ke neman nashi ba sun ganshi …ko da kuwa zaya wuce ta gabansu to shi kadae zai gansu ….
Meenalle kuwa tana can zaune …duk tabi ta ishesu ….akwae ranar da suka bata girki …Shinkafa da miya …sae da ta juye masu quatern gishiri cikin miyar ….ranar Musa kamar yayi hauka don baya cin gishiri …..
Sannan babu shegen da ya isa ya nuna mata hannu ….komae tayi masu kuwa …Musa ma ya taba gigin dukanta ranar da suka dawo daga fashinsu sa daddare suka iske kofar bude …sukayi ta murna don sun saba kwana a waje …ga sauro ..ga kunamu ….Suka shiga falon babu wuta su duka sukayi mamaki don babu inda zaka tarad ba da wuta a gidan …
Gashi babu mai ko waya …haka suka shiga cikin …ko wane da ya shiga sae ya fito da gudu yana ihu rike da kafa ….
Zuwa can wuta ta kawo …sae lokacin suka lura da cewa kwalbace farfashe a kasan gurin ….kuma sun tabbata Meenalle ta sakata ….
Musa ya shiga dakinta a fusace tana kwance ya fizgota tare da daura mata mari ….bai sauke hannu ba yaji kalan nata a fuskarshi. ..afusace ya cire belt ya zura mata…
Zafi da azaba bata san lokacin da ta murde mashi abun fitsari ba tare da aza mashi cizo a idon dama …..
A rude ya fito yana ihu rike da wando ….suka tareshi suna rikeshi …wasu na Allah ya kara wasu na tausayinshi ….kafin safe ido ya kumbura ….
Sae da yayi sati baya fita …don daga karshe ma zazzabi ya rufeshi …tunda lokacin bai kuma gigin dukanta ba …
kowa ta isheshi a gidan …bayan ya warkene. ..yayi alkawarin ko zata mutu sae ya kwanta da ita ranar ..don haka suna gama fashinsu ya sawo mata kaza …har wani karamin gidansu ya tsaya yayi wanka sannan suka taho …
Da yake generator dinsu ya lallace …babu wani shamaki suka kutsa kai cikin falon ….
Meenalle na tsaye bayan kaure rike da tabaryarta …Musa ya kutso kai rike fa ledarshi .
.
ta daga tabaryarta iya karfinta ta buga mashi a goshi …ya dafe gurin tare da sakin ledar ya koma baya da gudu …
Lafiya oga …wani ya tambaya …
Saboda azaba da hannu ya nuna mashi cikin gidan …ya daga labubalai ya shiga yana lafiya ….dukan da yajine ya bashi amsa ya yo baya dafe da goshi ga jini na zuba …
Cikinsu babu wanda bai yi kokarin shigowa ba haka babu wanda baiji ciwo ba …da Meenalle ta tabbata kowa ya samu rabonshi ta dauke ledar ta shige dakinta da gudu ta saka makulli .
Safe suna zaune kowane fuska a kumbure ta fito ta saka su gaba tana ta dariya ..
wani Sale cikinsu sae da yayi kuka ranar saboda takaici …gashi sun san ita tayi masu wannan rashin kirkin amma babu halin magana …
Bayan sati daya ne suka dawo suka iske ta kona masu duk abunda aka tara a gidan …
Ranar sukayi Meeting musa baya nan suka sami Meenalle suka roketa tazo su fitar da ita cikin gari …
Cewa tayi bata so bara ta tafi ba …don bata gaji da zaman ba ..
Suka dinga hada ta da Allah ..Da kyar ta yarda ta shiga motar suka taho ….Har kofar gidan Kaka suka ajeta sannan suka juya da sauri …
*Feedohm*💞
💧💧SIRRIN ZUCI ….
💞
💦Talented Writers Forum💦
🔝
Na Feedohm💞
79. to 80
Lokacin da musa ya dawo ya iskesu tsaye bakin gate ….ya taresu yana tambayar lafiya…sae suka ce masu police ne suka zo suka tafi da Meenalle basu nan …
Kamar mahaukaci ya juya ya tafi police station din rike da bindiga …da yake shashasha ne yama manta da nemanshi ake soyayya ta rufe mashi ido …
Yana zuwa ya fara harbe harbe yana zage zage …nan da nan suka kamashi suka daure …
••°°••
Ina Raliya ..
Da Raliya ta tabbatar Mr Ma’aruf ya rigaya ya mata nisa …don ko tana tsafi da bakar jaba bara ta sameshi ba …har office dinshi taje messenger shi ke fada mata yayi aure …sae ta tattara kayanta ta koma nigeria …ta sayi gida ta bude wani bariki na yan lesbian …da yake dama maza ba damunta sukayi …ba …dama Mr Ma’aruf ne take bala’in so kuma bata samu ba …
Haka ta lallashi partner ta Ruky da ta rude tana son Meenalle tun tana yarinya don tun lokacin da Meenalle ta shigo gidansu har ta dauketa bata kuma kara kula Raliya ba …suka shirya suka koma kamar da ..
°°••°°.
Bayan an rufe musa ne aka sake Malan Sani ….Lokacin Ya koma yana so rabi ta koma gidanshi …amma fur kaka tace bara ta koma ba ….
Sannanne kaka ta murje ido tace Malan Sani sae ya tashi daga gidan …
Malan sani ya tsorata ganin Kaka zata maidashi kotu …gashi ya sayar da gida kuma ba kudi. …yayi nadama sossae Rabi tace a kyaleshi amma ya saketa dan bara ta koma gidanshi ba …
Jiki na kyarma ya bata takardar saki … .
••°°••
Meenalle kuwa tana dawowa kaka ta mayar da ita gidan ubanta …ko sati bata kara ba ta koma makaranta …
Ranar da ta isa kasar bata san wanda ya fadawa Ma’aruf ba sae ganin kiranshi tayi ..bata dauki kiran ba sae da suka hadu School da Shamy take mata tsegumi ….. .
Duk yarda Shamy taso Meenalle taje gidanta amma taki yarda taje …haka ta hakura ta kyaleta …Shima Ma’aruf yayi kokarin su hadu ya ganta amma duk ta toshe hanyar da zasu hadun ….
••°°••
da Hajiya ta ishi Abubakar maganar diyarshi …sae ya dauko mata Sadee ..ya gaya mata gaskia ….
Su hajiya har da kuka tana neman gafararsu. ..sannan tace akaita gurin Rabi ta roki gafara …haka suka shirya suka tafi ….
Lokacin da Abubakar yaji auren Rabi ya mutu ..ba karamin farinciki yayi ba. …ya fadawa Hajiya yana so ya maido rabi …da yake hajiyar tasha wahala gurin matar da ta sakq ya aura ..sae ta amince dan da nan …
••°°••.
Cikin wata hudu akayi komae aka gama ..rabi ta koma gidan tsohon Mijinta …wancan matan kuwa tana jin zayayi aure tace bara ta zauna da kishiya ba ..ta tattara komatsunta ta yi tafiyarta ….
Da Hajiya kuwa ta gyara halinta suka zauna lafiya da Rabi. …da labari ya sami Meenalle har kukan murna sae da tayi …
*Feedohm💞*
💧💧SIRRIN ZUCI ….
💞
💦Talented Writers Forum💦
🔝
Na Feedohm💞
81 to 82
*Nine Month*
Tun da Safe Ma’aruf ya kira Meenalle …yace tazo Shamy na kiranta bata lafiya ….
Taxi ta hau …kasan cewar tsakanin makarantar da gidansu Shamy din akwae nisa …minti biyar tayi ta isa gidan …
Lokacin har an fito da Shamy din daga cikin gida zaa kaita asibiti …
Da Sauri ta isa gurin Ma’aruf tana tambayarshi lafiya ….
Lumshe ido yayi yace tana labour ne wallahi …tun jiya …
Bayan sun je asibitin ne akace. ..sae an mata CS saboda haihuwar tazo amma kuma Mahaifar ta rufe. …
Canza mata asibiti yayi ya maidata asibitin da aka masu aiki …yana tunanin ko zasu iya mata wani abu …don baya kaunar CS …Cikin Saa ya tarad da doctor din da ya mashi aikin Kidney …
Thesame nan ma cewa akayi sae anyi aikin don barata taba iyawa ba …
Haka aka shigar da ita dakin tiyata …Meenalle duk ra rude. ..bayan minti 45 ..wata nurse ta fito da baby boy …
Ta nufi wani room dashi da sauri …Meenalle ta bita tana tambayarta lafiya. …
bayan ta fito daga dakin ta zo tana masu bayanin …boy dinne yasha ruwan mahaifa kuma akwae matsala. …
Abunka da ruwa ruwa nan da nan idon Meenalle ya ciko da kwalla …don tasha jin inda yaro ya samu irin wannan matsalar da wuya ya tashi …..
Minti Talatin da shigar nurse din ta fito ta fada masu cewa baby boy din ya koma ga Allah ….
Meenalle ke ta hawaye …amma Ma’aruf lumshe ido yayi kawae yana kallon dakin da Shamy ke ciki ….
Zuwa can aka gangarota ….aka shigar da ita wani dakin ….lokacin idonta biyu tana kallonsu …ta yafito Meenalle da Hannu ….
Doctor din ya girgiza mata kai …yace tana bukatar hutu ….
Bayan an shiga da itane ..ta dinga rokan doctor din akan ya barta tayi magana da Meenalle minti 30 kawae ….daga farko cewa yayi tayi hakuri …amma daya fahimce ta sossae sae yaga bai dace ya hanata ba ….
Shi da kanshi ya kira Meenalle yace ta shiga patient din nason magana da ita ….
ta shiga da gudunta …Ma’aruf ya bita da kallo ….
Shamy ta rike mata hannu suna kuka …Ma’aruf dake kallonsu ta cikin glass ya kura masu ido …ya rasa wace irin shakuwace tsakaninsu ..wadda har daga fitowarta da operation take son magana da ita bayan gashi …
Meena …Shamy ta kira sunanta ahankali …
Meena ya maimata a ranshi tare da matsawa saitinsu yana kallonta ..
Ki fadawa Ma’aruf gaskia…Dan Allah Meena ko bayan na mutu ki fada mashi ki gaya mashi bani na bashi kidney ba Meena. . ki fada mashi ke ki bashi ..kece masoyiyarshi ta gaskia bani Meena ..ki fada mashi kece Meenallen shi ….
Girgiza mata kai tayi tana kuka …aa Shamy zaki warke dan Allah ki bar wannan maganar …zaki warke insha Allah ..
Hannuta ta kawo …bazan tashi ba Meenalle ..baby din na haifa ki rikeshi Meenalle ke na bawa amanarshi ..ki auri Ma’aruf dan Allah …idanuwanta suka fara rufewa
Kuka ta saki da karfi tare da ficewa da gudu …a kofa ta bangaji mutun tsaye amma ta wuceshi …ta fita tana kiran doctor …
Ma’aruf na tsaye idonshi a lumshe doctor yazo ya jashi yana fada mashi matarshi ta rasu ….
Meenalle kuwa gurin ta suma ….ko bude ido Ma’aruf baiyi ba bare yaga yarda akayi da ita …
Bayan sun shiga office da doctor din ..Ma’aruf ya tambayeshi …wacece cikin su ta bashi Kidney …
Ganin babu bukatar boyewa yanzu doctor din yace …Meena Abubakar ….
Idonshi ya lumshe hawayen dake makale suka gangaro …
Waya ya fito ya kira wani friend dinshi dake aiki airport yace yana son helicopter yanzu ….
bai kuma cewa komae ba ya nemi a bashi gawar Shamy ..
Cikin wani box aka sakata sannan aka nufi airport da ita …suka koma nigeria ……
*Feedohm*💞
💧💧SIRRIN ZUCI …..
💞
💦Talented Writers Forum💦
*Godiya mai tarin yawa ga talented writer Allah ya hada kanku tare da hakuri da juna*
_Islah tee_
_Zahra_
_Smart_
_Halieymerh_
_Mufeedah_
_da sauran mu gurin bara ya isa ba na rubutu ku duka💞_
*Thank you so much for your well nd eniest wishes*
*Mum twins*
*Aunty Sis*
*Khadija Candy*
*Bilkisu bilyaminu*
*Namesy Classic*
*Aunty Maijidda*
*Salamatun Inna*
*nd Ladies Novel world members*💞
Na Feedohm💞
83 to 84
A gidan Iyayenta aka mata sutura …bayan sati biyu …ya taka har gidan Kaka …ya fada mata komae sannan ya nemi yaje gurin iyayen Meenalle …
Kaka baki yaki rufuwa …ita da kanta ta kaishi har gidan Alhaji Abubakar ..lokacin su Rabi an murje ..ni kaina kasa ganeta nayi …
Maganar da Ma’aruf ya gayawa kaka ita ya maimatawa Rabi da Alhaji Abubakar ….sannan ya nuna yana bukatar aurenta kafin ya koma ..
Alhaji Abubakar yace sae an nemi Meenalle anji ta bakinta ….
Haka aka kira Meenalle a waya aka tambayeta …
Kasa cewa komae tayi ..sae kaka ta ce …ta yarda …
••°°••
Biki ake amma bada sanin amarya ba …komae an mata cikin gata da aminci ….
Kaka kuwa baki yaki rufuwa …..haka hajiyar Abubakar sae nan da nan ake da dangin rabi …
Kudi kawae Abubakar ya tura aka sayar mata komae acan…..aka hada mata komae na jin dadi ….
°°••°°
Ma’aruf kuwa sae da aka gama komae sannan yama iyayen Shamy bayanin duk abunda ya faru sannan ya taho …
Meenalle kuwa tunda Kaka ta kirata ta fada mata an daura mata aure gabanta keta faduwa …haka Ma”aruf bai kirata ba ko sau daya …
Karfe 8 din dare Ma’aruf ya dawo …direct makarantar su ya nufa …Soofy ya kira yace ta kira mashi Meenalle din …
Yana cikin mota ta iso sanye da maroon din hijab mai hannu …cikin sanyin murya ta mashi sallama ..
Ya amsa kasa kasa tare da dagowa ya kalleta ..wani abu ya tokare mashi kirji ….ya lumshe idonshi ….
Shiga tayi ta zauna …tana zama ya rufe kofar yaja motar …..
bata ce mashi komae ba ..har suka isa wani katon gida ..ba wanda aka aje Shamy a ciki ba ….
Ya fito ya yi gaba abinshi …haka itama ta biyoshi cikin sanyi jiki har ta iskeshi falon tsaye ….
Bayanshi ta tsaya kanta na kasa tana wasa da yatsunta da suka sha jan lalle ….
Juyowa yayi idonshi a lumshe ya kira sunanta …a hankali …
Bata dago ba …amma ta amsa a hankali …
Na dawo dake rayuwata Meenatou ba wae don ina son haka ba…..
Idonta ya ciko da kwallah …bata yi tunanin gogesu ba …
Ya cigaba ….Meenatou duk da irin son da nake maki kina yarinya lokaci guda kin gogeshi …zan maki adalcine saboda abunda kika man …amma maganar so ..babu sam …bazan so yarinyar da ta yada darajarta ba. …..
Da sauri ta kalleshi ….tana nuna kanta da hannu …..daraja Ma’aruf ….
Yes Meenatou …ya fada idonshi na kanta …
Girgiza kai tayi …tana fadin …Nagode sossae ..Meenalle Maikamshi …na fita fitina Allah ..ko ka manta
Murmushi yayi kasa kasa yace …Ta ya zan manta ….wucewa yayi ya shige wani daki ya barta tsaye ….bayanshi ta bi itama ta shiga ….
Bai kalleta ba….ya cire suit din dake jikinshi ya fada toilet …hijab dinta ta cire …ta haye saman gado ta kwanta …..
Tana kwance ya fito daure da towel ya tsaya gaban mirrow daga ya shafa wannan sae ya shafa wannan …kamar mace …nan da nan dakin ya dauki kamshi …..
Da gefen ido ya kallota tana kwance ta rufe ido ….takowa yayi a hankali ya sauko pillow a kasa tare da shimfida bargo …ya dawo ya sabeta ya dire ta saman shimfidar ya koma ya kwanta saman gado ….
Wallahi Ma’aruf baran kwana a kasa ba duk abunka ..ta fada tana kallonshi …
Hararanta yayi yace …idan bara ki kwanta anan ba ki koma dakinki ..
Itama hararan ta sake mashi tana fadin ..haka kuma baran kwana ni kadae ba …Na rantse maka da Allah baran kwana ko ina ba…
Juya baya yayi ya kyaleta …yana jin lokacin da tazo ta kwanta gabanshi …don neman magana ma daura kanta tayi a hannunshi tayi pillow …
Baice mata komae har tayi bacci a haka ..gangarowa tayi ta shige kirjinshi …ajiyar zuciya ya sake tare da gyara mata kwanciya …sannan shima baccin ya daukeshi …..
Ya rigata tashi da asuba …yayi wanka tare da alwala …ya dawo ya tadata yaga har ta tashi …jallabiya ya saka ya tada sallah …sae da yayi nafila sannan ya jirata ta fito ya ja masu jam’i ……
Yana kwance wajen 9 ta fito cikin shirin makaranta …tun daga sama har kasa ya bita da kallo …sannan ya kau da kai. …
Ki sako Hijab ..sannan …ya fada ahankali …
Bata ce komae ba ta sako hijab din ta fito tana tura baki …mikewa yayi ya dauki keys yayi gaba ..Kamar kurame suke tafiya…
Restaurant ya biya da ita sae tayi breakfast sannan ya wuce da ita makaranta …
*Feedohm💞*
💧💧SIRRIN ZUCI ……
💞
💦Talented Writers Forum💦
Na Feedohm💞
85 to 86
kasuwa ya wuce ya sawo masu duk abunda zasu bukata sannan ya dawo gida ya aje kayan ya wuce office …
lokacin da Meenalle ta dawo …sannan ta samu damar zagaye gidan …ba karamar dukiya aka kashe mata ba …dakin da take tunanin nata ne ta shiga …..buda baki tayi tana kallon ikon Allah ….drawer ta bude akwatuna ta gani set Hudu masu shegen kyau …da kyar ta saukosu duka ta zazzagesu kaf kasa tana dagawa ….
Dae dae lokacin Ma’aruf ya shigo dakin …jingina yayi da kofar ya kallonta …sae da ta gama daga komae …sannan ta dauko wata sarka da yan kunne ta aje gefe guda ….tana fadin ….Duk da bana magana da maikamshi bara ya dawo ya fada man yarda ya sawota …
Lumshe ido yayi tare da barin dakin ba tare da ta sani ba ….
da kyar ta mayar da kayan cikin akwatunan ..amma ta kasa maida akwatunan inda suke …..
Cikin lefen ta fito da Riga da siket na material milk colour ta aje bisa gado …..wanka tayi sannan ta saka kayan tare da sarkan da ta fito ….
Yana kwance falo daga shi sae farar singlet da boxer ja idonshi a rufe ……
Ta dade tsaye tana kallonshi ….sannan ta matso kusa dashi ta dafa kujeran …Uncle Ma’aruf ta fada a hankali…
Banza yayi da ita kamar bacci yake. …sajenshi ta shafa…shiru ya mata …amma wani zafi yake ji a ranshi
..
Ma’aruf dan Allah ka tashi kayi hakuri …wallahi bansan me na maka ba ka yafe man ….ta fada kamar zatayi kuka …
shiru ya mata …..tasake cewa …kaji to Dan Allah idan bara ka bude idon ba ka fada man nawa ka sayi wannan sarkan mai stone a ja ta cikin wadannan akwatinan …
Dariya sossae ta bashi …amma ya danne ya bude idoshi …ya murde hannun da ta shafi sajenshi dashi …ta sake kara tana kokarin janyewa ….
Tashi yayi zaune …sannan ya sake mata hannun yana hararanta ….duk lokacin da kika kuma tabani sae na karya hannu ….yana gama fada ya shige daki …
Zama tayi gurin ta sake kuka tana rike da hannun….
Jin kukan yake har cikin ranshi …keys ya dauka ya fice daga gidan kwata kwata
Lokacin da ya dawo da daddare har tayi bacci a inda ya barta …wuceta yayi ya shige daki yayi wanka sannan yayi kwanciyarshi …..juyi kawae yake amma babu alamun bacci a idonshi ….ganin kwanciyar ba zata fishsheshi ba ya saka ya fito falon …..
Kanta na bisa hannun kujera …ya dauketa ya daura saman doguwar kujera ….
Cikinta ya shafa yaji kamar bata ci komae ba …ledan da ya shigo dashi ya dauko …kazane da fresh milk sae dugheese ya zazzage cikin plate tare da knife …
Kumatunta ya dinga shafawa tare da hura mata iska …tayi saurin mikewa tare da sakin sabon kuka …
Shiiiiiitttt ya daura hannunshi saman lebenta …sannan ya tura mata plate din ….
Mikewa yayi ya koma saman kujera ya kunna TV …hararanshi kawae take …suka hada ido …jira take yace.. taci ..amma ya shareta …
Hawayen takaici suka gangaro mata …ya dan saci kallonta …ta bashi tausayi …
Kici mana Meenatou ….ya fada a hankali don ya gane abunda take so taji kenan ..
Hawayen ta saka bayan hannu ta share tana fadin …dama ko baka ce na ci ba yanzu nayi niyyar ci ….
Murmushi yayi kasa kasa ….baice mata komae ba …
Har ta koshi sannan ta dawo kusa dashi ta zauna kasan carpet .
..
Plate din ta mika mashi …tana kallonshi ..
Harara ya banka mata ….tayi saurin dauke kai tana fadin ..
dan Allah kaci kaima …
Murmushi ya sake kasa kasa yace ..ba bukata …
Please ….ta fada ..
Girgiza kai yayi yace …A da Meenatouta tayi forcing dina naci irin haka .. yanzu ke ba tawa bace …kuma baran ci ba ….ya mike ya shige daki ….
Ni din taka ce …ta fada a hankali sannan ta mike ta shiga dakin
Kayanta ta cire daga ita sae inners…sannan ta daura towel ta shige toilet ….akan idonshi tayi komae har ta fito ….duk abunda yake shafawa sae da ta shafa ….sannan ta leka fuskarshi taga idon a rufe …murmushi ta sake tana murza hannu..
..
*Feedohm💞*
💧💧SIRRIN ZUCI …..
💞
Na Feedohm💞
87 to 88
Pillow ta sauke kasa tare da shinfida bargo ….sannan ta hawo gadon ta koma gabanshi ta dinga murginoshi kasa ….
Yana jinta yayi banza da ita yasan dai barata iya daukarshi ta maidashi kasa ba. ..sae uban nishi take …sae da ta gaji dan kanta taga bara ta iya maidashi kasa ba ….sannan ta janyo hannunshi ta daura kanta ….bata fi minti 10 ba ya gane bacci ya dauketa ta gangaro jikinshi …ya saka hannun ya gyara mata kwanciyar sannan shima baccin ya daukeshi ….
••°°••
Ganin bata fito ba har karfe 9 ya saka ya leka dakinta ….tana kwance saman gado ido a rufe ….
Meenatou …ya kirata a hankali ….
Shiru ta masa ….Ki fito ina jiranki falo ….ya wuce abunsa …
Yayi minti 20 yana jiranta amma shiru bata fito ba ……
Dan karamin tsaki ya sake lokacin da ya duba agogon dake makale a hannunshi ….
Ya koma dakin a fusace ya tsaya bakin gadon tare da dago kanta ….
Da sauri ya taro kan …ganin ya koma da kanshi ….jijjiga yayi …yana kiranta ….sae lokacin ya lura da ba lumfashi a jikinta …..
Daukarta yayi ya sakata mota ya ja motar da gudu …tun yana tafiya ya kira doctor
Yana zuwa suka amsheta emergency ….kusan 1hours sannan aka samu numfashinta ya dawo normal shima da taimakon oxygen …
Ma’aruf na wajen dakin sae..kae da kawowa yake …doctor na fitowa ya tareshi yana tambayar lafiya …
ce mashi yayi ..zafin masassara ne ke damunta … da marece aka sallamesu suka koma gida ….
A gate din gidan ta saka mashi kuka wae barata iya takawa ba ….jikinta ya taba yaji da zafi …sannan ya dauketa suka shiga …
Dakinshi ya direta …ya shiga kitchen ya dafa mata ruwan zafi ..sannan ya dafa mata kwae guda biyu ya kawo mata ….Ya aje saman stool din dake gefen gadon ya fita …
Sae da yayi kusan Awa daya sannan ya dawo …yarda ya aje haka ya tarad da abunshi …ya kalleta ta gefen ido …ta maida hankalinta kan wani dan karamin littafi dake aje gefen gadonshi …
Bakya jin yunwa ne Meenatou …ya fada tare da zama gefen gadon …
Bakya jin yunwa ne Meenatou …ta maimaita abunda ya fada tare da sake mashi harara ..sannan tace ….ko wannan abun zaya shekara anan baran ci ba duk da ina jin yunwan ..tunda nima lokacin da baka lafiya idan naje gidanku ai a baki nake ba …nima din sae ka rama man ..har dukana ake a makaranta idan na makara ..to wallahi sae ka rama man ..
Murmushi yayi kаsa kasa tare da fadin …Dama Halinki ne Meenatou …gori ba …
Sannan ya janyo flask din ya hada mata tea din tare da dauko sandwitch ya mika mata ….
Ka Wanko hannunka ta fada tana hararanshi …
Ni ai ban taba hamatar ko wane kato ba …ya bata amsa ba tare da ya kalleta …
Nima da nake tabawa ai yanzu na daina ….
Sae ta mata? …ya tambayeta tare da kura mata ido …
Bata ce komae ba ta koma ta kwanta tare da rufe idonta …..
Ki tashi kici ….ina da aikin yi da yawa …ya fada tare da kallonta …
Bata motsa ba tace …Alhamdulillah …
Kafada ya dage tare da ficewa daga dakin …..
Bai kuma dawowa ba sae bayan isha’i ….
lokacin ta dan tashi tayi wanka tare da sallah sannan ta koma ta kwanta amma jikinta kamar wuta ga Uwar yunwar dake damunta. ..kuka take a hankali …
Ya shigo da sauri ya shige toilet yayo alwala tare da kabbara sallah .. ..
Sannan ya janyo ledar daya shigo da ita ya fito da abunda ke ciki …
Ya zauna yaci ya koshi sannan ya yo wanka…sae lokacin ya leka fuskarta …tare da duba duba abunda ya bar mata …
Da Sauri ya kira sunanta ….Meenatou …
Tana ji tayi banza dashi …hannu ya sanya ya cire hannunta dake saman goshinta …
Zafi sossae yaji jikinta …nan da nan ya rude ..ya janyo kayan da ya. shigo dasu ..ya fito da Fresh milk ya bata …da yake yunwa take ji ..batayi gardama ba ta amsa. …
*Feedohm💞*
💧💧SIRRIN ZUCI …..
💞
Na Feedohm💞
89 to 90
Towel ya jiko da ruwa sannan ya dawo zaya jika mata jiki ….
Bargon data nannade jikinta dashi ya cire tare da tadata zaune zaya cire man shirt din dake jikinta ….
Hannunshi ta rike …duk da zafin masassaran dake damunta bai hana ta sake mashi harara ba tare da fadin. …Meye zaka cire man riga …
Karamin tsoki yaja ..yace …cire hannunki daga jikina Meenatou …
Allah Ma’aruf bara ka ga jikina ba ….ta fada kamar zatayi kuka ..
Hararanta yayi tare da fadin..Meye a jikin naki da zan kalla Meenatou …jikin da kowace kazama ta gama kallo ..mtsee ..
Hannunta duka biyu ya hade ya rike da hannu guda tare da cire mata rigar …ya barta daga ita dae bra …..haka ya zare Siket din ya bar mata Pant …sae uban ihu take mashi amma ko kulata bai yi ba ….
Har sae da zafin jikinta ya ragu sannan ya sake hannun sae lokacin ya lura da tayi bacci ….
Har ya dauko rigar zaya maida mata ya tsaya tare da kurawa surarta ido …tabbas Meenalle ta hadu ta ko ina ….
Sauke ajiyar zuciya yayi tare da jefar da rigar gefe guda …ya mike yayo wanka ya kashe haske sannan ya dawo ya kwanta ….janyota yayi ya rungume yana maida numfashi a hankali ….
Da asuba ta rigashi tashi ….ta kwace kanta daga rikon da ya mata …tare da sake ihu ganin yarda take …lokacin jikinya ya koma lafiya lau …
Jikinshi ta haye tare da dukanshi da pillow tana fadin Allah ya isa ka gani Maikamshi …ganin hakan bai mata ba ya saka ta daga jallabiyarshi ta zare hannuwan ta cireta …ta barshi daga shi sae boxer dake jikinshi tare da sake mashi cizo a kumatu tana fadin …Nima na rama …kuma baran kara kwana da kai da mugu ….ta dauki rigarta ta fice daga dakin ….
Tana fita ya mike tare da girgiza kai ..don duk abunda take yana jinta shareta kawae yayi …
••°°••
Lokacin sun gama Exam ba makaranta ..da safe ta hada masu Break su zauna su ci tare sae dae babu magana sae harare harare …
Ranar da daddare taki zuwa dakinshi …duk da take …haka shima ya kwanta sae juyi yake …kusan Karfe biyu yaji ta bude kofa a hankali tare da kwanciya kusa dashi …..bai yi motsi ba sae da ya tabbatar bacci ya dauketa sannan ya janyota jikinshi …a haka bacci ya daukeshi ……
tunda Asuba ta sulale ta koma dakinta a tunaninta bai sani ba …
Da Safe da ya fito ..kamar abun arziki ta tareshi tace ..
Good Morning …
Ya dan kalleta kafin yace ….Morning …sannan ya ja kujera ya zauna …
Ta hada mashi komae sannan ta tura mashi gabanshi tana fadin …kasan me yasaka na gaidaka ?,..
Girgiza mata kai yayi yana kallonta …
Ta washe baki tana fadin …so nake bakin ciki ya dameka na kwana ni kadae ban mutu ba …ta watsa mashi harara …
Dariya ya sake har da rike ciki …..
Me kakewa dariya ..? ta tambayeshi tana hararanshi. ..
Hararan ya maida mata ba tare da yace mata komae …har ya gama breakfast dinshi ya mike ya tafi office ..
Haka da daddare ranar yana jin lokacin da ta dawo jikinshi yayi murmushi ya janyota ya rungume …da asuba yana jin tana kokarin kwace kanta amma yaki sakinta ….
Tayi kwance sae Mazurai take …ya bude ido tare da zuba mata harara …
Ta hadiyi yawu tare da zuba mashi harara itama sannan tace ….
Daga zuwa tayar dakai Sallah sae ka rikeni ….
Harara ya zuba mata yace …ta ina kika shigo …
Ta kalli kofar tare da fadin …ta kofa mana …
Keys din kofar ya fito daga kasan filon daya daura kanshi …
*Feedohm💞*
💧💧SIRRIN ZUCI …..
================= Gidan Novels =====================
💞
Na Feedohm💞
91 to 92
Turo baki tayi tare da fadin …To Maikamshi na dawo din dakinka sae akayi me ..dadin abun ma ba cire maka kaya nayi ba nace zan gasa maka jiki don na kalleka ..kuma anan din ma zan dinga kwana kullun duk tsiyarka….tana gama fadar haka ta mike tare da fadawa toilet ..
dariya ya dinga yi sossae yana jinjina baki irin na Meenalle ..gashi dae ya nuna mata ya san nan take kwana maimakon ta nuna taji kunya sae ma ta nuna ta fishi baki ….
°°••°°
Zamansu haka ya fara damunta ..har lokacin bai fada mata asalin laifinta ba ..sae dae ya dinga jifarta da maganganu ……
Soofy ta kira a waya ta fada mata matsalarta ….
Shawarwari ta bata sossae tace ta dameshi ya fada mata laifin da tamashi ..sannan kar tayi zuciya baa banza yake mata haka ba ….
yana zaune falo …rike da wani novel .. tayi sallama ba tare da ya kalleta ba ya amsa mata …
Hannushi ta bude tashige jikinshi tare da maidawa ta rufe ….
Ya dan Saci kallonta …tana sanye da karamar riga pink sae three quater baki ….manyan kalaba ne akanta ….ya saki ajiyar zuciya tare da maida kallonshi ga littafin ….
Ta rasa yarda zata mashi magana …shimq ma ya gaji da zaman da take a jikinshi Allah kadae yasan me yake ji ….
Ya rufe littafin tare da zareta ya maidata saman kujera yana fadin .
Menene Meenatou ..
Bakomae …Dama magana nake son muyi …ta fada a hankali …
Ina saurarenki ….ya fada tare da lumshe ido..
Dan Allah ina so ka fada man abunda na maka ….
Banda lokacin wannan maganar Meenatou …tashi ki fitar man daga falo indae wannan ya kawoki .
Kayi hakuri dan Allah …..Da Kana sona Ma’aruf …amma yanzu me yasa kake man haka …ta fada a hankali ..
Saboda bana sonki yanzu …ya fada kai tsaye …
Kana sona mana …ta fada tare da sakin kuka ..
Idanuwanshi sukayi jawur ..cikin tsawa yace ..karya kike bana sonki Meenatou …ya karashe maganar tare da fadawa saman kujera ya dafe kanshi
Kai ta girgiza tare da fadawa dakinshi da gudu …
Drawer dinshi ta dinga janyowa tana kuka har ta fito da glass din da ribbon din da ta bashi yake …sannan ta fito dakin …
Yana ganin ta fito ya mike da sauri tare da nunata yana fadin …ki mayar dashi Meenatou .
Cikin kuka tace.. idan baka sona me kake da wannan …
Ki maidashi nace Meenatou ..ya fada tare da nufota …
Kasa ta jefar dashi da karfi glass din ya fashe …
Daga hannu yayi da niyar marinta yayi saurin rufe ido ….ta cikin fasasshen glass din ta bi zata wuce ….
Da sauri ya duka tare da saka hannunshi inda zata taka saman kwalaban …
Rufe ido tayi zata daura kafar a hannunshi Ta taka ta wuce ….amma ta kasa …kuka ta sake da karfi tare da juyawa ta canza hanya da gudu …..
Binta yayi da kallo …hawayen dake makale a idonshi suka sauko …ya dauke ribbon din ..sannan ya kwashe kwalbar ya koma daki ….
°°••°°
Kusan satinsi biyu a haka …gurin bacci kawae ke hadasu
Duk rintsi basu raba makwanci duk da ba wani abu ke shiga tsakaninsu ba …sae dae ta daura kanta a hannunshi …idan tayi bacci ya maidota jikinshi …
Soofy ta sake kira tagaya mata yarda sukayi …
Cewa tayi Meenalle kiyi hakuri ki sake jaraba tambayarsa karkiyi zuciya …indae kinyi imani da soyayyar da yake maki tun ta yarinta to har yanzu akwaeta ….
To kawae tace …zata je amma wannan shine na karshe …idan ya fada mata to ..idan kuma bai fada mata ba. ..sae dae su cigaba da zama haka …
*Feedohm💞*
💧💧SIRRIN ZUCI ….
💞
Na Feedohm💞
93 to 94
Shigowa Meenalle tayi yana zaune yana kallo ….ta samu guri ta zauna ..tana kallonshi …
Mr Ma’aruf ….ta fada a hankali ….
Ido ya dago a lumshe …yace . Meenatou Wani abu kike bukata ….
Girgiza kai tayi a hankali tana wasa da zoben dake hannunta. …
Ok. .ya fada tare da cigaba da kallonshi …
Ganin baida niyar kulata ya saka ta mike ta koma kusa da kujeran da yake zaune. ..
Ta kwantar da murya tace …Kayi hakuri Ma’aruf …wallahi bansan laifin da na maka ba …Dan Allah ka yafe man …
Ya danyi murmushi ciki ciki yace …Meenatou kenan na rasa kalmar zan bi wajen fada maki ki daina zuwa inda nake amma kin kasa ….please ki fice daga falon nan ….
Daga kai tayi tana kallonshi idonta cike da hawaye tace ..Dan Allah Ma’aruf ka fada man laifin da na maka …wallahi bansan nayi maka shi …tun ina karama muka rabu ..yaushe har mukayi haduwar da ka tsaneni kuma wane kalar laifi na maka …
Kayi hakuri dan Allah nice fa Meenalle Ma’aruf ka tausaya man mana. …
sossae yaji tausayinta …sae dae yana tunano pictures din da Raliya ta nuna mashi …tsawon shekaru masu yawa da suka wuce ….lumshe ido yayi …yace …Idan har Meenatou zaki iya bawa wata wace jikinki shekaru da suka wuce tun kina yarinya to yanzu fa ….
Kuka ta fashe dashi tace …ban fahimceka ba Ma’aruf …wallahi ban gane me kake nufi ba …..
Mikewa yayi ya daga hannunta sama tare da janta har zuwa kofar falonshi…ya bude tare da turata waje. …karki kuma zuwa falona …
Kuka ya kwace mata ta toshe bakinta ta juya da gudu …sae ji tayi ya kamo hannuta tare da sakata a jikinshi ya rungumeta ….
Daga kai tayi sossae tana kallonshi …sannan ta maida kanta a kirjinshi …tana jin lokacin da ya sake ajiyar zuciya …a haka ya zauna saman kujera tana kirjinshi …sun dade a haka sannan ya dago kanta yana kallonta …
Meenatou …yaja sunan…
Bata amsa ba sae da ta kalleshi …kin san Raliya …ya tambayeta ..
Girgiza kai tayi a hankali tana share hawaye ……
Mikar da ita yayi ya zaunar da ita sannan ya shiga dakinshi .
ya fito dauke da wata waya ya kunna tare da mika mata a hannu …
Da sauri ta yardar da wayar tare da sakin kuka ….take ta tuno da abunda ya faru lokacin da ta shiga gidan wadannan yan iskan …
Wallahi dole suka man Ma’aruf …ta fada tare da buga kanta jikin hannun kujera …
Fuskarta ya kamo ya saka hannunsa cikin gashinta …yana kallonta …
Kwantar da kanta yayi bisa kirjinsa …Sorry Meenatou …i trust you yanzu kinji ko …kiyi hakuri ..na yarda baki aikata ba …
Kuka take sossae bata ga laifinshi ba abunda ya mata …don ta tabbata kara karuwa mai bin maza da yar lesbian ….
Cikin kuka take fadin wallahi banyi ba Ma’aruf …me yasa ka yarda …
Lallashinta ya dinga yi har ya samu tayi shiru. ..shima yayi nadamar abunda ya dinga mata …ashe bada hakkinta ba …..
a haka bacci ya dauketa sae ajiyar zuciya take ….Allah kadae yasan iya kissing din da ya mata …kafin ya dauketa ya kaita dakinshi ya kwantar da ita saman gado ya fita ….
Cikin wayar ya duba …number raliya ya gani …yayi hamdala Allah yasa bai gogeta ba …tunda dama tunda abun ya faru da ya dauki wayar bai kuma kunnata ba ….
Ringing daya ta dauka …ya tambayeta inda take …da yake bata ganeshi ba tunda ba da numbershi ya kirata ba. . ta mashi kwatancen gidan da suke …da yake ta dawo da taga nigerian ba harka
Direct can ya nufa ….yana zuwa yacewa mai gadin ya kira mashi ita ….
Ta fito rike da sandar guragu tana tafiya …..lumshe ido yayi lokacin da ta iso …
Mr Ma’aruf …ta fada tana washe baki …
Alhamdulillah Raliya …yaushe kika zama haka ….
Tabe baki tayi tace …accident muka samu wallahi ..amma dad yace zaa gyara man kafar ta koma kamar yarda take da …idan aurena kazo karka damu da wannan …
Dariya ya sake …yace ai ta riga ta zama haka Raliya ..wannan shine makomar munafiki…kin rabani da Meenatou kike tunani …well da zuwa nayi ki fada man wace shegiyace tayi forcing din Meenatou …amma yanzu yarda na ganshi ma naji dadi ..dan nasan soon itama waccen zata hadu da tata kalar masifar ….
Yana gama fadar haka ya shige mota ya barta tsaye …..
*Feedohm💞*
💧💧SIRRIN ZUCI …..
💞
Na Feedohm💞
95. to. 96
Kwafa tayi ta shige cikin gidan tana dogara sandarta ….
Yan matane birjit sunata shashansu ….kusa da wata taje ta zauna …tana rada mata magana a kunne …murmushi sukayi tare da tabawa …
••°°••
Zaune ya isketa tana cin Apple …kusa da ita ya zauna yana murmushi …
Har kin tashi ….ya fada tare da kanne mata ido …
Da kai ta bashi amsa sannan ta mika mashi wanda ke hannunta …
Bai amsa ba sae dae ya bita da ido tare da janyota jikinshi ….
Am sorry Meenatou ….ya fada a hankali …
Batace komae ba ta saka mashi apple din a baki tare da mikewa ta dauko mashi dinner ….
A plate ta zuba mashi ta tura mashi gabanshi kamar yarda ta saba …sannan taja nata …
Kujeran da take zaune ya dawo ya dagata sama ya zauna sannan ya daurata saman cinyarshi ….ya karbi plate din ya debi tare da bata a baki ….
aa Maikamshi ….ta fada tare da kau da kai gefe guda ….
Why Meenatou ….? .
Ka manta abunda kace …ta fada tare da kura mashi ido …
Lumshe ido yayi tare da girgiza kai …Me na fada Meenatou …
Hararanshi tayi tare da fadin …ka manta kace bara ka taba bani abinci da hannunka ba …
Dafe kanshi yayi …dama yasan zaa rina. yanzu komae ya mata baya yasan sae ta dinga tunawa tana fada mashi …
Cikin lallashi ya shafi wuyanta ….tare da langwabar da kai yace …To ai lokacin Meenatou kin bata man raine …
Harara ta banka mashi tace …yanzu fa. …
to yi hakuri na tuba kinji ko …ya fada tare da mika mata abinci ..
Karba tayi tare da kwafa ….
Shi ya rigata fitowa daga wanka …ya shinfida tarduma yana jiranta ….
Sanye da kayan bacci ta fito daga toilet din….
Sabon salo …ya fada a ranshi …bai san taji shi ba …sae da ta banka mashi harara tare da hayewa gado abinta ..
Meenatou …ki sauko muyi sallah ko …? .
Nayi a toilet …ta fada tare da gyara kwanciya …
Girgiza kai yayi ya tada sallah shi ya gama sannan ya hawo gadon tare da janyota …
Kin tuna?,…ya fada cikin kunnenta ..
Girgiza kai tayi tana kallonshi…
Lumshe ido yayi ..yace …lokacin da kika ceman malamarku bata sallah ..yanzu ai kin gane dalilin rashin yinta …
Duka ta kai mashi a kirji tare da lafewa tana dariya …
Shima dariyar yayi yana fadin …I love you Meenatou you’re my everything …
••°°••
Tana zaune taji Sallama …ta mike tare da daukar hijab ..
Tana bude kofar ta sake uban Tsalle tare da rungume kaka …
Imagine kakata …ta fada tana dariya …
Hajiya tayi zuru tana kallonta …sae da kaka ta buge mata hannu tana fadin …baki ga hajiya bane ..
Turo. baki tayi tace. ..na ganta ..ai bata sona …
naki kaniyarki Meenalle ..bata sonki ta hawo jirgi kamar zamu fado tazo inda kike ….
Ma’aruf dake tsaye jingine da kofa tunda suka shigo ..sam bata lura dashi ba …
Ya ja hannu hajiya yana murmushi yace …Taho hajiya rabu da ita zata neme mu ne da kanta …
Sae lokacin tasan tare suke …ba kunya ta nufeshi tare da rungumeshi ta mashi kiss a kumatu …
Oyoyo ……
Hancinta yaja a hankali har ta saki kara …yace …baran amsa ba ..
Ta dan ja baya kadan tare da waro idanu tana kallonshi …acikin shagwaba tace …Why ..
Hannu ya mika mata ta matso kusa dashi sannan ya kalli hajiya ya kalleta …
Murmushi tayi taje ta rungumi hajiyar tana mata sannu da zuwa …
*Feedohm💞*
💧💧SIRRIN ZUCI ….
💞
Na Feedohm💞
97 to 98
Bayan sun hutane Kaka ta kurawa Meenalle ido tace ..
Meenalle banga alamar samun da ba da wuri ….
Kaka a Ina …ta tambayeta cikin rashin fahimta ..
to ba hausa ina nufin banga ciki ya fito ba …
Ta sake dariya tare da kwalawa Ma’aruf kira ….yana tsaye yana shan ruwa gaban fridge ya iso yana tambayarta lafiya da ido ..
Hannunshi ta janyo tare da zaunar dashi kusa da kaka tace ….Fadawa kaka me kace ..
Me nace kuwa Meenatou ….ya tambayeta a hankali ..
Harara ta sake mashi …ya saurin dafe kai …yasan Meenalle da naci ta yiyu wata magana ya mata shine bata hakura ba zata tada ta yanzu …
Lokacin da kace bana da ko. …
bata karasa ba ya tashi tare da jan hannuta da karfi ya shige da ita kitchen …
Am sorry Meenatou …baran sake fadar komae ba …
Harara ta sake mashi tana fadar …naji to ka sake man hannu ko ….
Zan sake amma karki sake fadar komar kinji ko …ki manta …
In manta me ..har cewa da kayi karuwa ta …
bakin ya murde ta sake kara …ya daure fuska sossae …yace …
Kar na kuma jin wannan kalmar a bakinki ….me kika hadawa su kaka .
Yanzu dae zaka tayani mu hada masu ..ta fada tare da kwantowa jikinshi ….
Murmushi yayi suka fara aikin tare sae da suka gama girkin suka gyara kitchen din tare
Kwanansu goma cif …tun Meenalle bata sakin jiki da Hajiya har ta koma tana sakin jikinta kamar yarda take da kaka …
Ranar da suka tafi kuwa kuka ta yini mashi …sae da kyar ya samu ya lallasheta tayi shiru ….
Da yake rigima take ji …ko abinci bata masu ba …fita yayi ya sawo masu abinci …inda yake sawo wa ya samu sun rufe …sae ya sawo mata kaza da ice cream ya dawo ….
Tana kwance bisa kujera ya dawo ko dan oyoyon da ta saba mashi batayi ba …ya wuceta ya shiga kitchen ya dauko plate ya juye da knife sannan ya dawo falon …
Ya leka fuskarta tare da kiran sunanta a hankali …Meenatou …
Zaune ta tashi tana sharar kwalla …da sauri ya rungumota ..
Ya Salam Meenatou …kukan ne har yanzu …Sorry yi shiru kinji ko …Muna next month zamu je ….
Da sauri ta washe baki …tana fadin da Gaske …
Daga mata kai yayi alamar eh …tare da janyo plate din
sauko kici …
Saukowa tayi tana cin abunta ba tare da ta sake cewa komae ba …sae da ta koshi sannan ta kalleshi tana murmushi tace …
Kasan dama ina son kazar amare ..amma wadda na taba ci bata kai dadin ta nan ba …
Hararanta yayi yana fadin ..waya baki wata kazar amare …
Musa ya sawo man ita …amma karamace bata isheni ba …
Baki ya tabe yace. ..Bata amaren bace shi yasa kika cinye…
Allah itace….kuma ban rage ko kadan ba ….
Dawowa yayi kusa da ita tare da janyo hannunta yana murzawa ….
Idan na sawo maki ta amaren zaki cinye …ya fada dae dae kunnenta
Harara ta sake mashi tana fadi …dukanta kuwa .. .
Girgiza kai yayi tare da jan hancinta …..
Idan na sawo maki ta amaren ma Meenatou bara ki ci ba ….
Giranta ta hade tana fadin Kana wasa da ni …
Ko ? .. ya tambayeta …..
Eh …..
Zakiyi bayani da kyau …ya fada tare da mikewa tsaye …
Kaima din zakayi bayani …..ta fada tana hararanshi …
Hannunta ya janyo ta mike tsaye yana kokarin zura hannunshi cikin rigarta
*Feedohm💞*
💧💧SIRRIN ZUCI …..
💞
Na Feedohm💞
99 to 100
Saurin rike hannunshi tayi ..Meye haka …ta fada kamar zatayi kuka …
Bayanin nake so ki sakani nayi da kyau …
Bafa irinshi nake nufi ba ….ta fada tare da dukar da kanta kasa ….
Hmm ….kawae yace ..ya saketa ya shige daki …bayanshi ta bi ….tana murmushi ita kadae …ya dan juyo ya kalleta tayi saurin juya baya itama ….murmushi ya sake sannan ya juya ….
°°••°°
Kayan Sport ya aza mata saman jiki ….
Ta waro ido tare da kallonshi ..har ya sako nashi …riga da wando sae hula tare da safar hannu da takalmi …da yake kayan yellow ne …sae sukayi bala’in mashi kyau …abunka da fari ….
Ki tashi kin canza kayan ..ko sae na canza maki da kaina …ya fada tare da kamo hannunta ….
Harara ta sake mashi tare da cire siket din dake jikinta ta saka wandon …sannan ta juya mashi baya
Bude man zip din …ta fada a hankali ….
Zip din rigar ya zage mata …ya kai hannu ya shafi wani digon baki dake tsakiyar bayanta …sannan ya saka hannu ta baya ya karbi rigar daga hannunta …
Hannunta ta daga sama ya zura mata rigar …sannan ya duka ya dago kafarta ya daura saman cinyarshi ya saka mata takalmin …tare sa safar hannu sa hula …ya ja hannunta …
Wani labule ya daga …wanda ke facing din side dinta ….ta bishi da kallon mamaki ganin koface a gurin …don duk zamanta bata san meye a gurin ba …
Wani abu ya danna a jikin kofar …glass din ya bude suka wuce ….sae da suka wuce wani dan corridor sannan suka isa wani katon fili ….
Ido ta bude tana kallon gurin …kamar baa gidan ba …
Gurin yayi masifar kyau …har da filin football gefe guda an zagayeshi da net …sannan swimming pool shima zagaye da net din…
Sae gurin table tennis da volley ball hade …
Gefe daya kuma flowers ne masu shege kyau ….ganin ta sake baki tana kalle kalle ya saka ya kwanto bayanta …
Me kike so muyi aciki …
Ido ta waro tare da nuna mashi Volley ball din …
Oya let start ….ya dauko kwallon tare da wullo mata …
Ka fara buguwa …ta fada ban mata iya komae ba …..
Sae ya bugo mata Ball biyar bata maido mashi ko daya ba …amma da ta samu ta bugo mashi sae ta hau tsalle tana mashi gwalo ..
Bata iya komae ba Sae masifar rintu ….har sae da aka fara kiran magrib sannan ya ce ta taho su koma ciki …
Zubewa tayi gurin ta mike kafa tana nishi …
Mene Meenatou …kin gaji ko …ya fada tare da dagata sama …
kafana baran iya tafiya ba ….ta fada kamar zatayi kuka ..
Da sauri ya duba kafar baiga abunda ya sameta ba …
haka ya sabeta a kafada …ya direta gaban fanfon dake gurin sukayi alwala ..sannan ya sake daukarta ya kaita dakinshi ya shinfida mata darduma …
Ya fice masallaci ..
Ya saba dawowa da anga Sallah …amma ranar sae da ya tsaya aka yi Isha’i sannan …ya dawo …
Tana tsaye bakin kofa kamar zatayi kuka …ya shigo …da sauri ta juya mashi baya …
Rungumota ta baya yayi tare da daura kanshi saman wuyanta yana shakar kamshinta
Nayi laifi …tuba nake ….ya fada cikin kunnenta …..
Make kafada tayi tana murza idonta ….
am sorry Meenatou …ya fada a hankali ..
juyowa tayi tana kallonshi tace ..To ina ka tsaya …
juyota yayi tana facing dinshi yace ….Kazar amare naje sawo maki…sae da na nemo wadda zata maki wuyar cinyewa….
*Feedohm💞*
💧💧SIRRIN ZUCI ..
================= Gidan Novels =====================
💞
Na Feedohm💞
Nagode sossae da sakonninku …wanda ban bawa amsa ba dan Allah suyi hakuri wallahi yayi man wuya nabi kowa na bashi amsa …Kuyi Hakuri🙏🏻
101 to 102
Gabanta yayi mummunar faduwa tayi tsuru tsuru tana kallon carpet ..
Tsaf ya gama karantarta ….lebenta na kasa yaja ..tare da jan hannunta …bai tsaya falo ba …ya wuce bedroom dinshi da ita …
Tana zaune kamar mutun mutimi ya fito wanka …sannan ya mika mata towel …
Sae da ta dauki kayan baccin da zata saka ta shiga toilet din dasu …gudun kar ta fito yace ta saka gabanshi ….
Yana zaune bisa abun sallah ta fito ..ya mika mata hijab …
Raka’a biyu sukayi …ya dafa kanta ..ya dinga kwararo mata addu’a ….tana zaune kamar gawa …sae binshi take da ido ….
Ledar ya janyo ya juye cikin plate ..
Gata nan kici Meenatou idan ma bata isheki ba akwae wata a leda don bana so kice nima na kawo maki karama bata isheki ba …
Harara ta banka mashi tare da fadin …ni na koshi …
Dariya ya sake Kasa kasa yace …da sauri haka Meenatou…ko dai na matso na baki da kaina …
Saurin ja da baya tayi ganin ya matsota .
Dariya ma abun ya baci …kamar ba Meenatou dake bala’in sae ta kwana kusa dashi ba …amma yau tana gudunshi …
Yau naga abunda ya daure man kai …Meenatou ni kike jiwa tsoro …
Bawae shi takewa tsoro ba …aa abunda zaya mata shi takewa tsoro. ….
Sae da kyar ya samu ta karba sau daya ta kau da kai …duk cika bakin Meenatou yau ga kazar amaren a gabanta amma ta kasa ci …ko ta manta da Musa ya kawo mata ..ba sonshi take ba kuma tana da yakinin da bara ya mata komae ba shi yasa ta sake jiki ta cinye ….
Amma Yau ta Ma’aruf mai dadin ma ta kasa ci ….
Da kanshi yaja hannuta ya kaita toilet sukayi brush sannan suka fito ….
Can karshen gado ta koma ta makure ….
Murmushi yayi ya fita ya rufo kofar falon sannan ya dawo ya hawo gadon tare da kashe fitila …
janyota yayi tayi saurin mikewa zaune tana fadin …Yau zan iya kwana a dakina ni kadae …
Ko ..ya tambayeta yana kokarin rabata da rigarta …
Wallahi kuwa …ko gidan musa na taba kwana ni kadae. ..ta bashi amsa da sauri ..
Gidan Ma’aruf fa …ya tambayeta ….
Shima zan iya kwana …please ka sakeni …ta rike hannunshi …
Maidata yayi ya kwantar da ita tare da hade bakinsu guri daya ……
*
*
••°°••
Ba karamar jarumta Meenalle tayi ba …duk ihun da zakaji ana cewa amare nayi ko daya batayi ba ….sae dae hawayen da suka dinga fita daga idonta ..haka wani Allah ya isa da zakaji amare nayi duk batayi ba …kuma hakan yayi bala’in kara mata value a gurinshi …ba kamar shamy ba da yasha cizo da zagi a first night dinsu wanda ko kwatar matsewar Meenalle batayi bare ashe ta fita shan wuya
Ma’aruf baiyi tunanin zai sameta virgin ba ..don duk tunaninshi Musa ya riga ya warga mashi farinciki ..amma sae ya sameta budurwa mai tarin Ni’ima …albarka tashata kala kala …don har cewa ya dinga yi …
Meenatou indae ni zan daga kafa ki shiga Aljannah ..to na daga maki ita ki wuce Meenatou ….
Da asuba ya shiga toilet sae sauri yake ya fito ya taimaka mata . .
Dama already ya daura ruwan zafi ya zuba kanunfari aciki …
Yana fitowa ya ganta bakin kofa tana dafa bango zata fita …
Yayi saurin isa gurinta ya riketa yana tambayarta. ..
Meenatou ina zaki …
Bata ce mashi komae ba sae hawayen da ke fito mata ….lips dinsa ya kai gurin idonta …ya tsotse idon tas …sannan ya dauketa ya shige da ira toilet …
Cikin zuwan zafin ya sakata …bai saka detol ba sae kanunfarin da ya dafa ruwan dashi …don ya riga yasan detol na bata gaban mace sossae saboda chemicals din daka hadashi dashi …
Kara ta sake tare da rikeshi gam..
Sorry kawae yake ce mata …don ya san tayi bala’in shan wahala …
Sae da ya tabbatar ta gasu sannan ya canza mata wani ruwan zafin da babu komae a ciki yace tayi wankan tsarki ya fita ….
Suna azkar bacci ya dauketa …ya kwantar da ita saman jikinshi sae da ya gama sannan ya maidata saman gado ya rungumeta kamar zaa kwace mashi ita. …
*Feedohm💞*
💧💧SIRRIN ZUCI ….
💞
Na Feedohm💞
103 to 104
Shi da kanshi ya shiga kitchen ya soya masu bread da kwai da kifi …sae ya dafa masu tea ….
Kafin ya dawo har ta fito daga wanka tana sha mai ajikinta …
Da Sauri ya karba ya shafa mata sannan ya taimaka mata ta saka kaya …riga da siket na atamfa ….
Hannunta ya kamo yana kare mata kallo sannan yace …
Kinyi kyau Meenatou ..duk da ma ke din mai kyauce…ina matukar kaunarki kinji ko. ..Allah ya maki albarka ..ban san wace irin godiya zan maki ba …kin adana man jikinki duk da kin auri wani kafin ni …naji dadi sossae …
••°°••
Da Daddare kuka ta saka mashi bara ta kwana a dakin ba …sae da ya mata alkwarin bara ya mata komae ba sannan ta yarda ta kwanta shima karshen gado ….sae da tayi bacci ya maidota jikinshi …
Tun daga ranar bai kuma neman wani abu ba ..ta koma ta saki jikinta dashi kamar da …soyayya suke zubawa kamar ba gobe …idan yana office waya ba makale a kunneshi …idan kuma yana gida gwanin ban shaawa …
Yana kwance ya saka eyepiece a kunneshi yana sauraren wani waazi ..ta shigo falon …sanye da kayan sport don yanzu ta kware sossae da wasanni ….
Ta dade tsaye tana jiran ya tashi suje …sae ya ware mata hannunshi ta shiga ciki tare da kwanciya saman kirjinshi …ya maida hannun ya rufe.
Eyepiece daya ya cire daga kunnenshi ya makala mata akunne …suka cigaba da jin wa’azin tare …wasan da baayi ba kenan ranar ….
••°°••
Da daddare suna zaune ta kalleshi tana bata rai …tace
Ina kazata ta rannan …ta tambayeshi tana hararanshi …
Wace ciki Meenatou …..
Ka manta …ba fa ta jiya …bana sonta don bata kai ta ranan nan dadi ba …wacce ka sayo man nace bana ci …ka tunata ? to ita zaka biyani …..ta fito da ido waje ..
Dariya ya sake yace …Kazar amarya zaki ce man …ita kike son kici yanzu …
Bata kawo komae ba tace …eh Please …
Cak ya dauketa ya direta saman gado ..yana fadar bara yanzu zan baki …
Hadashi ta fara yi da Allah ganin abunda yake shirin yi mata …amma ko saurarenta baiyi …ba ..ranar ma tarihi ya maimaita kanshi …tayi nadamar tambayar kazar da tayi …
Meenalle irin matannane wanda ko yaushe zaka jisu kamar ranar aka fara saninsu ….
Tun daga ranar bata kuma mashi maganar kaza ba …ko kawo mata yayi …sae an zauna anyi alkawarin bara ya mata komae ba …sannan take yarda taci ….
••°°••
Safiyar wata litinin suka dira A nigeria …gidanshi dake kaduna GRA Unguwar sarki suka sauka …tun kafin su iso dama ya saka an gyara ko ina tsaf …
Kwanansu biyu suna hutawa sannan ta je gidansu ….
Hajiya sae nan nan take da ita …taga gata sossae …kuma ta iske mamanta cikinshi ……
daga can gidan Sadee ya kaita …sae da tayi kwana biyu sannan ta dawo gida …
Da ta dawo Ko kulata baiyi ba ..don fushi yake da ita …wae ta tafi ta barshi …da ta fara rikitashi nan da nan ya huce yana dariya …
*Feedohm*💞
💧💧SIRRIN ZUCI…
💞
Na Feedohm💞
105 to 106
Satin daya a garin suka je zaria …a gidansu Ma’aruf din ta sauka ..sae dae ta kwana gidan kaka ….
Suna zaune tace mashi tana so suje islamiyyarsu ta gaida malaman …
Ya harareta yace. . ki dai nemo gafara. ..
Zagayo wa tayi bayan kujeran da yake …ta sagalo hannunta bisa wuyanshi ….kanshi ya dago yana kallonta …ta dauro fuskarta saman tashi ….suna fitar da numfashi tare ….
Baka so Ustaz ya yafe man ..? ta fada dae dae bakinshi ….
Nan da idanuwanshi suka canza ..ya zagayo da ita ya daura saman cinyarshi ….tare da kwantar da kanshi a kirjinta ……..
••°°••
Wani dan karamin gida ya fara biyawa da ita …ya fito da key ya bude gidan tare da jan hannunta cikin …
Cherii …ina ne nan ..ta fada tare da kallonshi …
Daki dayane cikin gidan babba …yana bude kofar …ya duka yana fadin ….Teeta ……
Wata kare ta fito ta tsaya gabanshi tana sinsinanshi tare da haushi …sannan ta duka gabanshi …
Ya kalli Meenalle …yace ..kin tunata ? ..
Girgiza kai tayi a hankali cike da mamaki
Hannunta ya janyo ta duka kusa dashi …sannan ya juya yana kallonta yace ….
Kin tuna ranar da na fito gida na ganki kina kuka …na tambayeki me aka maki …sae kika ceman …wae mamansu kausarce tace idan karensu ya haihu zasu baki guda ….Sae kikace kaka tace bara ta aje kare a gidanta ba …saboda mala’ikun rahama basa shiga gidan …..Sae kika ce ko zan aje maki shi a gidanmu bakin gate ..idan mala’ikun sun zo sae su shigo ta katanga …to shine na karbo maki anan….ya kara maganar tare da dago habarta …
Rungumeshi tayi tana murmushi ….
Sannan suka tashi sukaje islamiyyar…
Ustaz na ganinta ya ganeta ….Aminatu abubakar ..
Ta amsa da fara ‘a….duka malaman islamiyyar suka taso suka gaisa da Ma’aruf …
Ustaz ya kalli gefen fuskarshi ya shafi wani tabo yace ..Aminatu gaskia ba karamar cuta kika mani ba …
Tayi murmushi tace …Ustaz sae dae a yafe dan Allah …..
Yace ..ai an yafe Aminatu…
Tace Ustaz ina wata shaddarka da ka taba zuwa da ita sabuwa ..daka koma gida kaga an yageta ta baya ….
Da Sauri yace Kece ko aminatu …..
Eh Ustaz sae dae a yafe …Wallahi lokacin banda abun goge majina ..sae na Yaga da reza …
Basu bar gurin ba sae da Ma’aruf ya masu alkhairi mai yawa sannan suka tafi ….
°°••°°
A gurin kaka take samun labarin Musa ya kara guduwa daga prison sannan har yau baa kara ganinshi ba …..
•°°••
Ma’aruf bai san Meenalle na da ciki ba sae da yakai wata shidda sannan ya fito ….wata sabuwar soyayya da kulawa yake bata ….Ko karatu zayayi in yana gida sae dae ya zauna tana jikinshi ta karanta mashi ….
Karyar Rashin lafiya kuwa ya sha yayita gurin aiki sae yayi sati bai je ba ….
Ranar wata litinin ta tashi da mugun ciwon mara …Ma’aruf na kwance gefenta …yana bacci ..ta mintsineshi da karfi …
Ya mike yana kallonta ….cikin kuka tace …sae aja wa mutun ciwo sannan a kwanta ayi bacci …
Me ya faru kuma Meenatou …..
Maimakon ta bashi amsa sae ta fashe da kuka …..da farko ya dauka rashin jin Meenalle ne ..
sae daga baya ya fahimci da gaske take ……
Feedohm💞
💧💧SIRRIN ZUCI …..
💞
Na Feedohm💞
107 to 108
Da sukaje asibiti cewa akayi sae an mata CS itama …
Please doctor kuyi wani abu mana …bana son CS dinnan wallahi …ya fada tare da rike hannun doctor din ya rufe idonshi gam ….
Calmdown mana …in Allah ya yarda ba wata matsala Mr Ma’aruf …
taya zan kwantar da hankalina bayan Meenatouta tana can tana labour …ni dae kawae ayi mata komae amma banda CS ….ya karashe maganar da karfi ….
Nurse ta shigo tana fadin Sir zata iya haihuwa da kanta mahaifar ta bude da kanta …
Daga doctor din har Ma’aruf din rigen shiga ake dakin duk da mutane basu shiga amma haka suka kyaleshi ….
Yana Zuwa ya zauna tare da tallabo kanta ya daura saman cinyarsa ….
A wahale ta bude ido tare da rike hannunsa tana kallonshi da i
Cheri…ta fada tare da lumshe idanu …
Iska ya hura mata yana shafar kanta ganin yarda take zufa duk da sayin AC dake dakin …
Hannunta ya damke sossae tare da daura gudan hannun a goshinta
Sorry ..Meenatou …ki daure please kinji ko …ya fada dae dae kunnenta ..
Girgiza mashi kai tayi ..aa Cheri mutuwa zanyi kamar yarda shamy tayi ..ka yafe man kaji ka sakawa babyn mu sunana …
Bazaki mutu ba Meenatou ki barni …da rayuwarki nake rayuwa ..idan babu ke Meenatou Zan kasance kamar gawa da raice ..kin manta alkawarin da kika man ..kince Tare zamu rayu sannan mu mutu a tare ..ko kin karya alkwarin ne Meenatou?,……
Zafin ciwo bai hanata girgiza mashi kai ba ….
Yauwa Meenatou …zaki daure ko?..ki daure ki haifa mana baby ki bashi tarbiyar ..Ina Matukar sonki da kaunar ko da can da kika ga na shareki Meenatou dan ba yarda zanyi ..amma soyayyarki tana cikin Zuci …ta zama Sirrin Zuci …zan iya rayuwa babu abinci Meenatou ..indae kina tare dani …Dukiya da duk jin dadin duniya yana tare dake Meenatou ..kece hasken dake haskaka rayuwata …idan babu ke zan dawwama cikin duhun da bazaya taba gushewa ba …
Kin kasance wani bango Wanda akayi shi da azurfa a gareni …ki daure Meenatou …Ke din kamar Hurul ‘ain ce wadda Allah ya sauko man domin cikar rayuwata ….
Idonshi ya lumshe tare da daura lebenshi saman nata yana tsotsa ya mata katanga da faffadan kirjinsa …yana jin lokacin da taja numfashi da karfi tare da kara rikeshi. …hawayen dake zuba a idanunta. …suke gangarowa saman lebenshi ….
Doctor dake tsaye da baby a hannunshi ya dafa bayan Ma’aruf tare da daura babyn a bayanshi …
Ya dago da sauri yana kallon Dr din …
Murmushi yayi mashi yana fadin ..Congrat Mr Love ..ya mika mashi baby din. .
Yaron ya kallah dauke da murmushi a fuskarshi sannan ya kalli Meenalle wadda har lokacin Idonta a lumshe yake
Dukawa yayi Dae dae kunnenta …ya kira sunanta a hankali …
Meenatou…
Bude idonta tayi tare da kallonshi …Deep kiss ya manna mata a goshi…sannan ya dago da idanuwanshi da suka rike zalla soyayya ya na kallonta …
Barata iya jure irin kallon ba ta juyar da kai gefe guda tana murmushi ….
Tsam ya mike tare da komawa inda ta juya …zata sake juyar da kanta ..ya saka hannu daya ya rikota …
Me kike so a rayuwarki Meenatou …fadan me nene gurin ..ko da lumfashina zaya kare zan cika maki shi ..
Hannunshi ta rike tare da daurawa saman kirjinta …Kai nake so Ma’aruf .kai kadaene gurina …daga kai bana son komae …
Babyn ya daura mata a kirjinta ya duko da kanshi ya sumbaci lebenta …kin Samu Meenatou dama can ni naki ne …kin saka man farinciki mara misaltuwa a rayuwa. .dame zan saka maki ..?..
Ka barshi a sirrin zuci …ni kadae zan fahimci haka …
°°••°°
Dama Already ya fadawa dangi tana labour ….tun da safe jirgin su Hajiya da kaka da mahaifiyar Maaruf ya dira …farinciki kamar baa taba haihuwa ba a dangin ….
Hajiya tace. zaa koma da Meenalle nigeria …amma Ma’aruf yayi kememe yace ba inda matarshi zata tafi …
*Feedohm💞*
💧💧SIRRIN ZUCI …
💞
Na Feedohm💞
109 to 110
Juyin duniyar nan amma ya kiya …da daddare ya samu Meenalle zaune daki …yaron na hannu kaka zaa mashi wanka …
Hawa yayi saman gadon tare da kwanciya ya daura kanshii saman cinyarta ..yana kallonta …
Murmushi tayi tare da shafar sumarshi …
Bara ka bari a tafi dani ba Cheri….ta fada tare da juyar da kai ga barin kallonshi …
Kina so ki bisu ne. .? ..ya jeho mata tambayar..