Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 25 Complete Novel

*ASM Bk2025*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

…….Parlor Gwaggo tace su shiga, a saman 2 seater Hajiya ta zauna gwaggo ta zauna kan one seater tana fuskantar ta ta shiga gaida ta rai a 6ace Hajiya tace “bazan amsa gaisawar ki ba Dije don kin ban mamaki wllh” waro ido gwaggon tayi a d’an rude tace “Hajiya mi kuma ya faru?” a d’an harzuk’e tace “haba Dije ace da girman ki ki tasa yarinya gaba kina gaba da ita sai kace wata kishiyarki to da me kike so ta ji ne? Baki tunanin hakan na iya jefata cikin wata matsalar kuma sakamakon damuwa da tayi mata yawa! Haba Dije in ran ki ya 6aci ai ba Kya bari hankalin ki ya gushe ba komae a hankali ya kamata a bi shi, nasani abun Sam ba dad’i to amman wannan abun da kike ba shine zai samar da mafita ba sai ma ya jaza wata matsalar” tana yin shiru cikin karewar murya gwaggo tace “amman hajiya mafitar nike son samo wa amman Fatuu ta watsa man k’asa a ido ta nuna man iyakata ta goyi bayan Mahaifinta….” Katseta Hajiya tayi a fad’ace tace “ta k’i bin bayan mahaifinta Dije duk D’iya ta gari kina tunanin zata ga mahaifinta a cikin matsala ne alhali tana da hanyar da zata taimaka mashi kuma ta k’i, ko kece Fateema na tabbatar hakan za ki yi kada ki zama mai son kan ki mana, sannan Maganar nuna iyaka ba wata iyaka da Fateema ta nuna maki kema kina da naki muhimmancin kamar yadda mahaifinta keda nashi” dakatawa tay tana maida numfashi yayin da gwaggo ta sadda kanta tana matsar k’walla Hajiya ta koma lallashinta tana bata baki akan a bi komae a hankali itama Fateemar ta san ba son Al’amarin take ba kawae bata da yadda zatayi ne don haka sai ayi Addu’a Allah ya za6a abunda yafi zama Alkhairi kawae amman ta daina abunda take Matan don zai iya jawo wata matsalar, sosae ta lallasheta har saida ta ga gwaggon ta saukko sosae sannan ta mik’e don tafiya bayan sun fito tsakar gida tace ma gwaggo taje ta d’aukko mata kayan baccin Fateema bama zata dawo gidan ba tunda dama kora da hali ake mata, d’an guntun murmushin yak’e gwaggon tayi kafin taje ta d’aukko mata saida ta sawo hijab ta rakata har wurin gidanta tana ta ta koma kafin suka yi sallama hajiyar na jaddada mata kan aci gaba da Addu’ar Allah ya za6a abunda yafi zama Alkhairi, lokacin da ta koma gidan a d’akin Saude ta iske Fatun kwance ta bata kayan baccin tace mata ta sa tay kwanciyarta har zata fita kuma sai ta dakata ta tambayi Saude Fatun ta ci Abinci tace mata a’a wai ta k’oshi hajiyar tace ta tashi taci ba yadda ta iya dole ta tashi Saude taje ta zubo mata Abincin, bayan ta gama komae tasa kayan baccin ta kwanta tunanin yadda Hajiya tayi da gwaggo ta shiga yi, Hajiya na komawa bedroom d’in ta toilet ta shiga tayo wanka bayan ta fito tayi shirin kwanciya ta kwanta, tunanin Maganar auren Fatun ta shiga yi ita kanta bata farinciki da Al’amarin sai dae tana fatan Allah ya za6a mata abunda yafi zama Alkhairi. Washe gari bayan sun yi breakfast Fatuu na zaune a d’akin Saude tunanin gwaggo ya dameta hakanan take jin son ganinta lokacin Hajiya ta koma bacci Saude ta shigo bayan ta gama gyara gidan da murmushi ganin Fatun ba bacci take ba tace mata ko ta tashi tay wanka tafi jin dad’in jikinta tace to, bayan ta fito ne ta maida kayan jiya data zo da su gidan tace ma Saude zata je gida ta canza kaya tace to, lokacin da ta isa a zaure ta tsaya tana ta wasi wasi can dae ta shiga ciki ba kowa a tsakar gidan hakan yasa bata yi sallama ba daga yanayin kopar d’akin gwaggon ta gane tana nan a ciki d’an jimm tayi kafin tay shahada cike da fargaba tay yar sallama ba tare da ta shiga ba shiru ba’a amsa mata ba hakan yasa ta k’ara yi sai lokacin ta jiyo muryar gwaggon ciki ciki ta amsa mata a hankali ta d’aga labulan ta shiga gwaggon na kwance saman gado tana huta gajiyar aiki da ta gama, ta ji shigowarta saidae bata bud’e idanunta dake a rufe ba balle ta kalleta, saman kujera ta kai ta zauna a d’arare idonta akan gwaggon, har bayan wani lokaci bata kalleta ba hakan yasa Fatuu shan jinin jikinta ta ji kamar ta tashi ta fita don ta lura kaman gwaggo bata huce ba can dae tayi k’arfin halin kiran sunan gwaggon murya na rawa shiru bata amsa ba bata kuma bud’e ido ta kalletan ba don sama fuskarta ke facing ta tada kai da Pillow, murya na rawa Fatuu ta ci gaba da cewa “Gwaggo don Allah ki yi hakuri ki yafe man ki daina fushi da ni wllh ban jin dad’i don ke matsayin Mahaifiya ta ce bazan so in ga kina fushi da ni ba, kuma ba iyakar ki nike son nuna maki ba kawae ina tausayin Baffa na ne don ban son Ard’o ya tsine mashi hakan matsala ne a gareshi kuma kinsan Ard’on zai iya kema nasan bazaki so hakan ta faru ba” ta k’arasa cikin karewar murya tana share hawayenta duk Maganganun da take gwaggon na jinta har can k’asan ranta wani iri take ji, mik’ewa Fatuu tay ta nufi gaban gadon ta duk’a akan gwuiwowinta ta dafa bakin gadon da hannu cikin muryar kuka tace “gwaggo don girman Allah ki yi hakuri ban son ganin ki a cikin damuwa…” sai lokacin ta bud’e idanun jin Maganar a kusa a hankali ta sauke su kan fuskar Fatun dake share share da hawaye sai kuma ta yunk’ura ta tashi zaune ta jingina bayanta da kan gadon shiru kaman bazata yi magana ba fatuu nata kallonta can ta sauke ajiyar zuciya murya ciki tace “Shikenan Allah ya za6a abunda yafi zama Alkhairi” a hankali Fatuu ta amsa da Amin kafin ta sadda kai tana kallon saman gadon can taji gwaggon tace ta tashi taje tay abunda zatayi ta d’ago suka had’a ido tana son ta k’ara bata Hak’uri amman ta kasa ganin yanayin fuskar tata, mik’ewa tay jiki a mace ta nufi hanyar fita gwaggon ta bita da ido har ta fice, d’akinta ta nufa tana shiga ta zauna a gefen gado tay zugudum hakanan hankalinta ya k’i kwanciya da yanayin gwaggon tana ta zaune can ta mik’e ta nufi wardrobe don ta canja kaya tana k’ok’arin fiddo kayan kud’in da baffanta ya aiko mata suka fad’o k’asa d’aukko su tay har zata maida su ciki sai kuma tay wani d’an tunani ta fasa maidawar ta aje su a gefen gado, bayan ta gama shiryawa d’aukar kud’in tayi ta fita ta sake komawa d’akin gwaggon k’irjinta na bugawa, lokacin da ta shiga har sannan gwaggon na zaune yadda ta barta, a bakin gadon ta tsaya da kermar murya tace “gwaggo gashi” kallon kud’in da take mik’a Matan tay kafin ta d’aga ido ta kalleta without saying anything ganin haka yasa Fatun cewa “d..da…dama Baffa ne ya turo ma Kawu Amadu wai ya bani in Siya k… kayan kitchen” da k’yar ta kai Maganar gwaggo na jin hakan nan da nan yanayinta ya canza sosae ta juyar da fuskarta gefe kaman bazata ce komae ba ita kanta Fatuu k’irjinta bugawa yake sosae bayan d’an wani lokaci ta ji gwaggon tace “sai ki je ki siyan ko” da sauri tace “ai ni bansan ma ina ake saida su ba kuma bansan mi zan siya ba” nan ma shiru gwaggo tay sai daga baya tace “sai kije in Saude bata komae ta raka ki tunda ita tasan inda ake saidawar zata taimaka maki da abunda ya dace” shiru Fatun tay ganin tak’i tafiya yasa gwaggon juyowa ta kalleta sai lokacin ta juya jikinta sukuku ta nufi hanyar fita gwaggon na bin ta da kallon takaici, d’akinta ta koma ta zauna a gefen gado tana tunanin ko ta kai ma Saude ko kuwa kar ta kai can ta mik’e ta yafa gyalen ta ta fita saida ta tsaya bakin kopar d’akin gwaggo tace mata ta tafi gidan Hajiyar shiru tay mata da farko saida ta k’ara maimaitawa sannan ta jiyo muryar ta ba yabo ba fallasa tana fad’in a dawo lafiya, Lokacin da ta isa Hajiya na zaune a parlon saman 2 seater tayi wanka ta shirya tana kallo bayan tayi sallama hajiyar ta amsa mata da d’an murmushi ta nufeta, gefenta ta nuna mata taje ta zauna tun kafin tayi Magana Hajiyar tace “ai d’azun nike tambayar Saude ke tace man kin je canza kaya nace ko dae kin kasa jurewa kinje ganin masoyiyar taki” ta k’arasa tana yar dariya itama Fatun murmushi take yi Hajiya tace “in ce dae ta sake maki yanzu?” Kai Fatuu ta d’aga kafin tace “eh” jinjina kai Hajiyar tayi tace “komae d’an hakuri ne kuma duk abunda Allah ya kaddara sai ya faru to kuwa ba makawa sai ya farun shiyasa ake son komae a rink’a bin shi a hankali ba a dau zafi ba” shiru Fatun tay kan ta a k’asa can Hajiyar tace mata ko taje d’akin Saude ta k’ara hutawa sai lokacin ta d’ago ta kalleta a

hankali ta mik’a mata kud’in hannunta hajiyar ta kalli kud’in kafin ta kalleta kafin tayi Magana Fatun tace “dama Baffana ne ya turo man su wai in sayi kayan kitchen to lokacin gwaggo tana fushi ban bata ba sai yanzu shine tace in je in sayi kayan nace mata ban san inda ake saidawar ba sai tace in zo in Aunty Saude bata komae ta raka ni” ta kai Maganar kamar zata sa kuka, yar ajiyar zuciya hajiyar ta sauke kafin ta amshi kud’in tace taje d’akin Sauden ta amsa da to ta mik’e jiki a sa6ule ta wuce, shiru Hajiya tay tana bin kud’in da kallo cikin ran ta tana ayyana da gaske dae Auren zasu yi mata Sam itama bata son hakan saidae ta san in Allah ya kaddaro hakan to fa ba makawa sai ya faru, ajiye kud’in tay a saman hannun sofa taci gaba da kallon can kuma Haisam ya fad’o mata a rai ta san ba lalle in yasan da Maganar ba hakan yasa ta kai hannu gefenta ta d’auki wayarta ta fara kokarin kiran shi, Lokacin da kiran ya shiga Haisam d’in na zaune kan kujera 3 seater a Parlor yana operating laptop dake ajiye a saman table d’in gaban shi Fanan kuma na kwance kan ta na a saman cinyoyin shi tana bacci daga ita sai wasu matsiyatan lingerie da suka bayyana kaf surar ta sunan dae tasa ne kawae, hannu ya kai ya d’auko wayar da ke ajiye a gefen laptop d’in yana ganin sunan da yay appearing saman screen d’in yay d’an guntun murmushi had’i da maida bayanshi jikin kujera ya jingina sosae kafin yay picking tun kafin tay magana cikin cool voice d’inshi yace “Sweetheart how a’r u” daga can d’ayan bangaren ta amsa mashi da tana lafiya kafin ta tambayi ya suke yace mata lpy,

 

“Ina rigimammar matarka?” Ta tambaya da yar dariya still da murmushi akan fuskarshi ya d’an kai idon shi ya kalli Fanan d’in, kamar kuwa tasan rigimar ta gama yi mashi kafin tay bacci ita ala dole suje a duba lafiyar su ganin har yanzu bata samu juna biyu ba dama tun suna wata guda da auren take Maganar samun cikin shi kuma yace is too early a fara wannan kuma yasan lafiyar su lau kawae time ne bai yi ba, amsa mata yay da tana bacci tace su fa dare ne ko ya amsa mata da yea,

 

“Yar gidanka dae Aure za’ai mata nace bari in sanar maka nasan ba lalle in ka sani ba” Hajiya ta fad’a bayan sun gama gaisawar, shiru ya d’an yi lokaci guda yanayin fuskar shi ya d’an canja don ya fahimci wadda take Magana akai slowly ya yace “waye zai mata aure?” Hajiya tace “wllh can garin su wai kakan ne ya bayar da ita sai dae kawae Mahaifinta ya kira ya sanar zai zo d’aukar ta……” Nan ta kwashe komae ta fad’i mashi har da halin da Fatun ke ciki ita da Dijen, sosae ya 6ata fuska ya ma kasa cewa komae har saida Hajiyar tace “Haisam are u there?” Sigh yay yace “yea” taci gaba “abun ba dad’i wllh yarinyar na son yin karatu to kuma ga Maganar aure” Haisam d’in yace “but this’s a forced marriage I think zaki iya yin wani abu bai kamata ayi mata aure ba” sauke ajiyar zuciya Hajiya tay tace “kagane su a wurinsu hakan daidai ne don haka suka saba za6a ma yara miji ….” Katseta yay “amman ita ba a wurin su take ba ai why za’a mata haka? U ave to do something sweetheart I think is part of ur work right?” D’an guntun murmushi mai sauti Hajiya tay tace “abunda nike son ka gane wannan family issue ne kaman yadda na fad’i maka haka suke ma yaran su yanzu inna ce in shiga Maganar ba lalle in yi nasarar hana yi mata auren ba in kuma aka yi nasarar to kuwa mahaifin nata ne a matsala kamar yadda na fad’i maka d’azun hakan ne ma yasa ita Fateema ta nuna ta Amince don fitar da mahaifinta daga halin da yake ciki” fuska a kwa6e yake saurararta bayan ta gama yace “so now u mean there’s no way out dole ayi mata auren?” Hajiya tace “to ya za’ai in haka Allah ya kaddaro dole sai anyi mata auren sai dae ai fatan Allah ya zaba abunda yafi zama Alkhairi, ita kanta Fateemar ta ban mamaki wllh ban yi tunanin zata yi k’arfin hali har haka ba to amman nasan ba yadda zata yi ne bata son mahaifinta ya shiga matsala ne Saboda ita, yanzu tace sati mai zuwa mahaifin nata zai zo d’aukar ta yanzun nan ma ta kawo man kud’i da ya turo mata don ta sayi kayan kitchen” shiru bai ce komae ba har saida hajiyar tace ko shima ya fara baccin ne sannan ya yi magana yace Allah yasa hakan yafi zama Alkhairi ta amsa da Amin daga haka su kae sallama tace ya gaishe da Fanan, tun bayan da suka gama wayar still yay hannunshi dake ruk’e da wayar ya d’an dafa ha6arshi da shi kwata kwata bai ji dad’in Maganar auren ba sosae ran shi ya 6aci don har fuskar shi ta bayyana hakan, ya dau lokaci a hakan mutsu mutsun da Fanan ta fara yi ne yasa shi kai idanun shi kanta slowly ta fara bud’e nata idanun kafin ta ware su a kan fuskar shi tana ganin yanayin fuskar tashi ta yunk’ura ta tashi zaune shi kuma ya d’age kan nashi yana facing sama duk a tunanin ta Saboda rigimar zuwa Asibitin da ta gama yi mashi ne hakan yasa ta kai hannu ta kamo hannun shi guda a sanyaye tace “babe are u angry with me?” Shiru bai ce komae ba bai kuma d’ago ba cikin breaking voice ta kuma cewa “am sorry for dat son da nike maka ne yasa am eager to ave child wit u…” Kwalla ne suka taru a idonta tay shiru sai lokacin ya d’ago ya bita da ido kawae, shi kan shi bai san miya sa Maganar auren Fatun ta dame shi ba, sosae yake jin ba dad’i a ran shi da k’yar ya d’an yi mata guntun murmushi yace kar ta damu ba wannan ke damun shi ba, cike da kulawa ta tambayi abunda ke damun shi kawae sai ce mata yay bai jin dad’in jikin shi ne da sauri ta matsa ta fara tatta6a jikin nashi wai ko fever ce shi dae bai ce mata komae ba can ya fara k’ok’arin tashi yace zai je ya kwanta itama mik’ewa tay ya kai hannu zai d’auki laptop d’in ta rigashi d’auka bayan ta rufeta suka nufi bedroom d’in shi yana shiga ya kwanta dama shima sleeping dress ne a jikinshi, Fanan duk ta damu don tunda suka yi aure bata ta6a ganinshi a cikin irin yanayi haka ba yawanci in taga canji tattare da shi ta tambaye shi zai ce ya gaji ne ko kan shi na mashi ciwo yanzu kuma ta fahimci kamar yana cikin damuwa ne, cike da kulawa ta zauna a gefenshi ya kalleta tace mashi ko ta had’o mashi coffee ko tea ya d’an girgiza mata kai alamar a’a tace to miya ke damun shi ta d’aukko mashi magani tun da taji ba fever a jikin shi d’an murmushi yay mata ya kai hannu ya jawo ta ta hawo gadon sosae a hankali ya furta “am Ok” da yar damuwa tace “are u sure?” Lumshe mata ido kawae yay ta kwantar da kan ta a chest d’in shi tana shafa lallausar sumar dake kwance a wurin da hannunta guda akai akai take d’aga ido ta kalli fuskar shi ya rufe idonun shi hakan yasa tay tunanin yay bacci a wani bangare na zuciyarta kuma she’s thinking what makes him so worried sanin shi ba abu kadan ke sa a ga damuwar shi ba, jin saukar numfashin ta a saman chest d’in shi yasa shi gane tayi bacci slowly ya ware idanunshi dama yayi hakan ne don bai son taci gaba da tambayan shi abun da ke damun shi gashi ya kasa sanar da ita zancen Auren da za’a yi ma Fatun don baison ma yin maganar, a nutse ya kai hannu ya janyeta daga jikinshi ya tashi zaune ya had’e hannuwan shi ya d’aura habar shi sam ya rasa ma tunanin da zai yi ba kamar da Hajiya ta nuna ba abunda za’a iya yi a hana su yi mata auren can ya sauke hannuwan ya kai hannu kan side drawer ya d’auki wayar shi saida ya gyara ma Fanan kwanciya ya lullu6e mata rabin jikinta da duvet ya rage hasken d’akin sannan ya juya ya fita, Parlor ya nufa ya zauna kan kujerar da ya tashi ya fara kokarin kiran layin Fatuu……..

.

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button