Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 4 Complete Hausa Nove

 

Ina yinku AbdulJalal novel fans irin💯💯💯 da duk sauran masoya wannan novel ina jin dadin comments dinku love u all ❤❤❤

I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢

Your comments give me courage

Haka suka cigaba da tafiya sunayi suna hira jefi² har suka shiga garin Kaduna 

Karfe 4 dai² suka iso kofar gidan su Jalila, suna parking Jalila ta fito bata tsaya bi takan JAWWAD ba balle trolley dinta, ta sakko ta ruga da gudu cikin Gida,

Ummi tana tsakar gida ta idar da salla Jalila ta shigo da gudu ta fada jikinta tana murna 

“I really miss you ummina”

“To karyani ki huta sarkin fitina ga yanda kika shigo da gudu kaman an koroki,”

“Bikiyi missing dina ba ko ni duk na damu saboda rashinki a kusa dani amma daga zuwana kin faramin fada”

Ana haka  JAWWAD ya shigo da trolley din Jalila,

“Au shi kikabari da dakon kayannaki? Kekam se a hankali”

Ummi tafada tana ture Jalila daga Jikinta

“Ba komai Ummi naga ta kagu ta ganki ne yasa ta manta da trolley”

Yafada yana murmushi

Murmushi Ummi tayi

Har kasa ya tsuguna ya gaida Ummi ya zauna

Ta amsa fuskata cike da fara’a haka ya zauna sukayi ta hira da ummi,

Ummi tana kaunar Jalal kodan yadda yake son diyarta dakuma yadda mahaifinsa yake tsaye akan lamuransu ita da yarta

Bayan haka kuma JAWWAD yarone me matukar biyayya da hakuri

Sallar la’asar yayi, be wani dade ba yace tafiya zeyi, 

“Jawwad tun yanzu”

“Ummi bana son tafiyar dare ne”

“Hakane kam bata da dadi”

To Dan jirani ina zuwa daki ta shiga ta dakko wani turare me kyau tabawa JAWWAD yayi godiya sosai

Yayiwa Jalila alama da ido ta tashi tarakoshi waje

“Sisyna zanyi missing dinki zuwan nan naki yayi min dadi gashi kin dawo kin barmu”

“Allah sarki yayana nima banji dadin rabuwa daku ba “

“Sisyna kiyi karatu kinji nasan ke mutuniyar kirki ce, banda kula kawayen dabasu zuwa makaranta

Banda tsokana da shagwaba”

Ya karasa maganar da sigar tsokana

“Insha Allah yayana”

“Good very good sister, insha Allah very soon zan dawo mukoma”

Dan turo baki tayi batace komai ba

Mortar ya bude ya dakko wani jaka yabawa Jalila

“Thank u very much my brother”

“Shhhhh don’t mentioned dear”

“Wish u safe trip brother thank u very much ka gaida min da Nana ta”

“Zan gayamata and karki manta dayiwa yayanki addu a”

“Addu a mekakeso in maka”?

“No bani ba Jalila yayanki Jalal”

“Yaya kaikam narasa wanan kaunar da kakewa Jalal”

“Hmm sisy na kenan zakiji komai insha Allah in kinkuma zuwa kano zakiji dalili”

Yabude mota ya shige yatada mota yana daga mata hannu

Seda ya bace ma ganin Jalila sannan ta koma cikin Gida 

“Ummina gayamin me yafaru bayan tafiyata ?”

“Ke dai bari Babyna gidan ba dadi daba kya nan, kawayenki na islamiyya se sintiri suke min, nayi missing dinki sosai daughter na”

Ummi tafada tana shafo fuskan Jalila

Jalila ta riko hannun ummi

“Allah sarki ummina haka kike sona dama?”

“Hmm Jalilana a duniyar nan a yanzu wanake dashi bayan ke kin ko son soyayyar dake tsakani da da uwa, da baki tambayi haka nakesonki ba”

To amma ya akai tsakanin Jalal da mummyn Sa basa jituwa shi bayajin wannan soyayyar ta mahaifiyarsa a ransa, Jalila tai maganar a zuciyarta

Da daddare bayan Ummi da Jalila sunci Abinci

Ta je ta dakko trolley din ta, ta dakko  kyautukan da ta zo dasu ta nunawa Ummi sannan ta dakko Wanda ,Jawwad yabata 

Katuwar teddy ne Ja da kuma manyan kwalin chocolate kusan guda biyar

“Allah sarki yayana Allah ya karemin Yaya Jawwad har yanzu be manta abinda nake so ba “

Ummi kallonta ta tayi tai murmushi

“Hmm Jalila kenan, Jawwad ya biyewa shirmenki hada siyamiki teddy da girmanki”

“To ni ummi har wani girma nayi

Yawwa Ummina tambayarki zanyi”

“Allah yasa nasani”

” Naga nabaki abunda akabani a gidansu Jalal baki tambayeni waye Jalal ba ko kinsanshi ne?”

“Eh nasan yaron koba makotan su Jawwad ba”?

” Ummi shine, amma kinsan yazama dan shaye² bashi da tarbiyya Sam bakiga yadda yakewa mamansa ba ya akayi kika sanshi?”

“Allah sarki Jalal da ba haka yake ba daga baya yazama haka abokin Jawwad ne tun suna yara kanana

Daga baya yakoma haka saboda wani abokinsa ko wayake oho?

Amma naji ance hada laifin mahaifiyarsa amma bansan ya akayi ba nikam”

“To Ummi ya akayi mahaifiyarsa tabari yazama haka”

“Ke rabu dani nima ban saniba sarkin tambaya meyasa baki tambayesu a can ba ni rabu dani bacci nakeji”

“To shikenan Ummi “

Har sun kwanta bayan wasu mintuna da kwanciyarsu,

Jalila ta nisa 

“Ummina”

“Na’am Jalilana”

“Yaushe zaki kaini garinku inga yan uwanki?”

“Jalila meyasa kikayi min wannan maganar,  so kike ki hanani bacci ko rigimar zakimin daga dawowarki ko baby, bana so yi baccin ki kawai nasan kingaji”

“Ummi bazan iya bacci ba sekin Sa ranar dazaki kaini garinku ni wallahi ko wasu irine ina so inje in gansu Dan Allah Ummi koba Sa sanmu ni inasonsu a haka Ummi kitemaka”

Jilila ta karashe magNar tare da rike hannun Ummi tana hawaye”

Fizge hannunta Ummi tayi

“Nemi gurin kwanciya kafin in wanka miki mari”

Ummi ta daka mata tsawa haka Jalila ta kwanta ta juya wa Ummi baya tana kuka

Har cikin zuciyarta Ummi takejin kukan Jalila tareda tausayinta.

Tayi rigingine tana tuna abubuwa da dama dasuka shude

*********

Aliyu Imam Habib shine cikakken sunan mahaifin Jalila su biyune kawai a gurin iyayensu shida  yayansa Usman Imam Habib (babansu Jawwad)

Mahaifansu sun haifi yara dayawa sun rasu su biyune suka rage asalin iyayensu Fulanin Adamawa ne ne akayi wata rigima yan fashi suka je rigar fulanin  aka karkashe wasu, yawan hare² da ake kaiwa fulanin ya tilasta wasu suka watsu a Sassan Nigeria an kashe musu yan uwa da dama malam imam da shi da me dakinsa mairo sukayo hijira zuwa kano.

  an kashe musu yan uwa dayawa, wasu daga cikin yan uwan Nasu kuma basu San inda suke ba abinda suka tsira dashi bashi da wani yawa, duk da kasan cewar su masu arziki a rugarsu amma haka suka siyar da abinda ya rage musu suka taho kano (ta dabo jalla babbar Hausa kodame kazo an fika)

Zuwansu kano a lokacin duniya tana kwance , a lokacin in akayi baki masarautar kano zamanin sarki Ado bayero ke bawa baki masauki Dan haka masarautar kano su sukabawa su malam imam masauki, inda akabasu katon Gida a unguwar mandawari

Gidansa ya kasance kusa da gidan wani alaramma malam shehu, malam shehu yanada Tarin almajirai dan haka zuwan malam imam kano basu San kowa ba wannan makocinasu shiya zama kamar Dan uwansu

Shi ya kai Imam kasuwa ya hadashi da wani almajiransa ya koya masa san’ar takalma a kofar wambai

Sannan in ya dawo sukan zauna da malam shehu ya koyamasa karatun addini

Imam yasamu Ilimi me tarin yawa a gurin malam shehu wanda ya kaishi ga zama mahadddacin qurani, sannan yana samun alheri a kasuwancinsa yA tsaya akan gaskiyarsa dai² gwargwado,

yana samun rufin asiri a sana’arsa

    Haka bangaren matan malam uwar gidansa ta dauki mairo kaman Yar data Haifa yayinda amaryarsa takasance masifaffiya Dan bata shiga shirgin mairo tunda taga uwargidamta ta dauketa kaman ya, uwargidan malam shehu ta iya saka Dan haka ta dinga koyamata sakar kayan sanyi

A zamansu a kano  mairo ta haifi yaronta na farko ya rasu a ranar da ta haifeshi yarasu bayan wani Dan lokaci ta Haifi na biyu 

Suka masa sunan Usman wato sunan malam shehu, yatashi da ilimin addini da soyayyar iyayensa gashi malam shehu ya daukeshi kaman jikansa yana matukar kaunarsa da ya isa sakawa a makaranta akakai usman makarantar boko

Seda mairo ta kuma haifan yara biyu suna mutuwa sannan ta haifi Yaronta namiji akasamasa Aliyu 

Addu’a Imam yayi tayi Allah ya bar masa Aliyu Usman ya samu Dan uwa,

Usman ya tashi da matukar kaunar Dan uwansa kullum yana tare dashi har Goya masa shi mairo takeyi,

Ba ‘a Dade ba

Ta kuma haifar mace itama ta rasu daga nan bata sake haihuwa ba,

Haka suka rungumi yaransu suna kula dasu malam imam be sakasu a harkar kasuwanci ba se dai ya tsaya musu akan Neman Ilimin su, na islama Dana zamani,

A kwana a tashi malam shehu Allah yayi masa rasuwa, sun shiga matukar damuwa da tashin hankali haka akayi zaman makoki kowa ya watse.

Rayuwa tacigaba a haka malam imam be taba tunanin sunemi wani daga danginsu ba, yana ta kula da yaransa , yakuma siyan gidajen kusa dasu ya hade a cikin gidansu.

Usaman da Aliyu suka girma da matukar kaunar junansu, gasu masu matukar biyayya duk da kasancewar su maza amma daga kan shara gyaran gado wanke² bawanda basu iyabaan Usman yafi Aliyu hakuri, shi

    Aliyu akwai kafiya da taurin kai sannan yana da zafi, halin babansu ya dakko, gashi shine karami amma in ya dau zafi sedai Usman ya kyaleshi amma duk da wannan halin nasa kaf kayan gidan nan shi yake wankewa ya goge sannan yana matukar son yayannasa amma wataran in kaga yasa Usman a gaba yana masa fada seka dauka shine babba

(Ashe JALILA ba a banza ta dakko ba) 

shidai malam imam kullum zancensa be wuce

” Ku rike junanku Ku rike zumunci, kunga bayan imu IMU bamu da wasu dangi duk sun watse wasu sun mutu Ku rike junanku Ku nemi ilimi ko bayan ba raina karku yada zumunci”

Kwanci tashi asarar rai Usman yagama makarantar secondary ya shiga Jami’a yake karantar engineering, 

Bayan ya kammalla jami’a ne aiki be samuba ya dawo Gida ya zauna yake dan bin babansa kasuwa, ana haka ya hadu da wata yarinya Zainab da farko dai suna mutuncine kawai kafin daga baya abin yakoma soyayya,

Lokacin daa malam Imam yasamu labarin Usman yana zuwa tadi gurin yarinyar ya kirashi yayi masa nasiha yace tun wuri in yasan ba aurenta zeyi ba ya dena zuwa gurinta

Shidama Aliyu be tsaya iya karatu ba yana taba kasuwanci 

In yafita abinda yasamo se yabawa Dan uwansa yace yafara Tara kayan aure tunda ya fuskanci yana matukar son zainab, 

Duk randa Aliyu beje makaranta ba haka zewuni Neman kudi ba abunda zeci a ciki haka ze dauka ya bashi, 

   Sannan dayake  mutane dayawa sun San Aliyu saboda yana da baki ba kaman Usman ba salihi ne kaman mairo, Aliyu ya dinga shiga yana fita domin yaga danuwansa yasamu aiki amma abu yafaskara kai kace shine yake nemawa kansa aikin

  Shekarar da Aliyu yasamu admission, babansu ya dauki kudin 

Registration ya bashi amma daya tashi se ya hada kudin da Wanda ya dinga Tarawa ya tafi yaje kasuwa Yakama shago aka zuba takalma ya dankawa Dan uwansa yace gashi nan ya dinga juyawa yasamu yayi aure

Dafarko Usman kin amincewa yayi seda yaga Aliyu yadena kulashi, yadena cin abinci tare dashi yayi fushi sosai sannan ya yadda ya karba

Malam imam yace aikuwa badi se dai kanemi naka kudin kashiga makaranta, we da Aliyu yabata shekara biyu be fara makaranta ba saboda yaga kasuwancin da ya kafawa yayansa ya bunkasa

Duk wannan abun baya hana in Usman yayi masa laifi ya zauna ya kare masa masifa, amma beta ba yimasa gori ba.

  Shekara ta zagayo Aliyu sannan ya Shiga Jami’a

Usman ya cigaba da kula da shago yasamu Sana’a yafara core ransa saga batun samun aiki

Ahaka har Allah yasa Usman ya auri Zainab aka ware masa bangarensa a cikin gidan yasata a ciki, tana zaune da mairo lafiya saboda ita Sam bata da hayaniya Dan haka Zainab bama Shiga harkarta take ba balle kyautatawa ko akasin haka ya Shiga tsakaninsu.

Allah ya Albarkaci kasuwancin usman, aciki ya dinga tallafawa karatun Aliyu dakuma iyayensu da girma ya cinmmusu,

   A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah, matar Usman ta haihu ta haifi da namiji, aka sakamasa sunan Aliyu suke cemasa Jawwad, Zainab taji haushi ga mahaifinta memakon ayi mata kara a saka sunanshi se a wani saka sunan Aliyu

Aliyu yayi murna da haihuwar JAWWAD dakuma karar da dan uwansa yayi masa kullum yana tare da Jawwad, yaronma yana matukar kaunar Aliyu Jawwad, soyayyar da Aliyu yakema Usman Yakoma kan Jawwad,

Jawwad yana da shekaru biyar cif, Aka tura Aliyu bautar kasa kwara state yaji babu dadi sakamakon rabuwar dazeyi da gida gakuma dansa JAWWAD dayake matukar kauna

Haka Aliyu yayi shirin tafiya yayi sallama da mutan gida iyayensa sun masa nasiha sosai akan ya kula da Kansa da addininsa, Usman beji dadi ba ya Shiga damuwa sosai, saboda shi lokacin da yayi NASA bautar kasar a kano yayi beyi nisa da Gida ba.

Haka Aliyu ya shirya ya tafi kwara, wani babban kamfani aka turashi kamfanin yakasance mallakin masarautar garin Wanda ya kasance na construction ne na gine² dakuma tituna

Aliyu yaga mutane daban² wanda suke da banbancin addini da al’adu da zaman takewa na rayuwa

Aliyu ya hadu da wani bayerabe a kamfanin me suna Abiola Wanda ya kasance kuma hadimi ne a cikin masarautar garin dukda banbancin addininsu amma tasu tazo daya shiyake zagawa da shi gurare a cikin garin

In Baku manta ba kusan halin Aliyu da shige²

Dan haka yace yana so abiyola ya Shiga dashi gidan sarautar yaga  yanda take, haka akayi ya dauke shi ya Shiga da shi cikin masarautar ya dinga nuna masa abubuwa, haka ya dinga kallonsu wasu iri saboda yanayin saraautarsu  yayi daban da masarautar kano

Wasu abubuwan sun kayatar dashi wasu kuma sun bashi haushi haka abiola ya dinga bashi labarin

masarautar da abubuwan data kunsa  ciki kuwa hada labarin shalelen masarautar wadda akan a batamata rai gara abatawa sarkin saboda tsananin kaunar da sarkin yake mata

Sarki yana matukar kaunar yarinya nan, shikam Aliyu duk surutun nan da abiola yake besan me yake cewa ba saboda ya shagala da kallon abubuwan kayatarwa da suke a masarautar,

Wani part suka karaso kai bakace a Nigeria ne ba ya hadu karshen haduwa an kawata shi da abubuwan zamani da kawatuwa

“Nan kuma inane?”

“Ai nan shine bangaren yarinyar danake gaya maka jikar sarki ce, bangaren shalelen gidan ne”

“Ehenn mushiga inga mene a ciki mana”

Zaro ido abiola yayi “sokake in kwana a kurkuku baza ja min wahala ba iyakacin mu nan”

“To meye a ciki gani fa kawai zanyi”

“Dan Allah kabari ka zo mutafi kaga akwai masu tsaronta Dan haka kazo mu tafi”

Da kyar abiola ya shawo kan Aliyu ya yadda suka tafi.

Abiola ne durkushe a gabanta, ta hakimce tana cin kayan marmari

Tayiwa hadimanta umarnin sutafi subata guri

Sannan ta mike zaune sosai

“Abiola”

Takira sunan shi

Ya Dan kalleta ya maida kansa kasa

“Waye wannan Wanda kuka shigo da shi dazu?”

Gabansa ne yayi mummunar faduwa ya tsorata, nan da nan gumi ya rufe shi ya kama in’ina 

“Abiola bafa abu me wahala na tambayeka ba kawai na tambayeka waye shine

Ina kallonku dazu ta saman bene kuna jayayya waye shi? Daga ina yake? Mekuma ya zo yi nan”?

Da kyar abiola ya hadiye wani yawu ya daidaita nutsuwarsa Ya dan suka da Kansa yace

” your royal Highness Dan bautar kasane an turoshi kamfani domin yayi aiki sunanshi Aliyu daga kano state yazo nan”

 A kidime ta kalleshi kana nufin musulmine

“Eh bahaushe ne kuma musulmi”

Gigicewa ta danyi tare da bashi umarnin ya tafi seta nemeshi

 Nan ta Shiga sintiri a gurin

Da karfi tai shouting

“Impossible!!!!!!”

Wanda ya janyo hankalin masu yi mata hidima ,kafin  su an kara……..

Kafin su Ankara takuma yi musu wani shouting din

“Ku tafi kubani guri” 

Sun² suka fice su ka bar gurin dakinta ta koma ta cigaba da sintiri to yanzu ya zatayi meye mafita washe gari takuma sawa aka nemo mata 

Abiola da yarabanci sukayi magana wannan karon 

(kunsan dai ni ba yarabanci nake ji ba Dan haka bansan me suka ce ba)

Naga Abiola ya daga kai ya kalleta a razane

“Ko bazakayi ba”

ta tambayeshi

“Zanyi yanda kikece”

Ya fada Kansa a kasa

“Mark u idan maganar nan ta fita wani yajita hukuncinka shine..

Tai taku biyu

” life imprisoned!!! “

Ya dago da sauri ya kalleta

“Yes ” tafada tana kallonsa “you can leave”

Da la’asar har camp Abiola yaje ya lallabo Aliyu ya fito da shi kan cewar za suje yawon shakatawa ne,

Wani hadadden lambu ya kai Aliyu, an kawata lambun da kayan itatuwa masu matukar kyau gurin yayiwa Aliyu kyau matuka,

“Gaskiya gurin nan yayi kyau so cool”

Aliyu yayi maganar yana murmushi tare da shafa Kansa

“Dagaske gurin yayi maka kyau”

Sukaji muryar mace a bayansu

Abiola yasan muryar wace dan haka yakara nutsuwa tare da sunkuyar da kai

Aliyu ne ya waigo yaga me maganar sanye take da riga da skirts na atamfa kanta ba Dan kwali

matashiyar budurwace bazata fi shekara goma sha takwas ba ba dai fara ce ba amma tana da kyau black beauty ce

Takuma maimaita abinda tace

   “dagaske gurin nan yai maka kyau”

Tafada tana murmushi, Wanda seda dimples dinta ya lotsa ta kara kyau

Shima Aliyu murmushi yayi mata

“Sosai makuwa gurin yayi matukar kyau kuma da kikazo seyakara haskawa kyansa ya kara fitowa”

Murmushi ta kuma yi 

“That’s good”

Tafada tana kallonsa

“Akwai gurare masu kyau a garin nan gurare masu saka nishadi, Wanda nasan babu su a garinku”

Tafada tana Dan kashe masa Ido 

“Kinsan garin namune kika fadi haka”

“No ba kayi kama da yan garin nan ba shiyasa nasan ba Dan garin nan bane kuma bana tunanin kanajin yarenmu”

Shikam abiola gefe yakoma ya nutsu kaman bashiba

“Hmm to garinmu yafi naku kyau”

“Wane gari kenan?”

Ta tambaya 

“Se dai ki canka”

Ta Dan kalleshi 

“Kana kama da hausawa”

“Yes ni bahaushene”

Jikinta ne ya danyi sanyi ta dan tafi tunani

“Akwai matsalane?”

Girgiza kai tayi

“A’a babu”

“Bari in tafi kar mamana tai min fada na Dade”

Ta juya tafara tafiya

“To ai baki gayamin sunanki ba”

“Marry”

Tabashi amsa a takaice

“Maryam, a nice name”

“Ki ban lambarki mu dinga gaisawa mana kinga semuje ki nunamin inda yafi garinmu kyau”

Murmushi tayi masa ta bashi lambarta sannan ta tafi

“Abiola naga tunda yarinyar nan tazo kawani kame a gefe ko kasanta ne kokuma akwai matsalane baka gayamin ba?”

MatsalaBabba ma kuwa

Amma a fili se yace 

“A’a bawani matsala kawai dai na Baku gurine”

Tun daga nan Aliyu ya jone da marry kullum cikin waya suke in tanaso ta ganshi se tace su hadu a lambu

Yayi² ta nuna masa gidansu amma se tace in mamanta ta ganta da wani zatayi mata fada ne 

Sunyi matukar shakuwa soyayya suke sosai mussaman tayi masa girki sufita guraren bude ido 

Dukda kasan cewarta kirista bata shigar banza sedai yawo ba dan kwali shima Aliyu ya hanata

In lokacin salla yayi zata jirashi yayi salla koma ta tuna masa, suka shaku matuka amma besan wacece ita ba,  tanayin abubuwan dasu kan bashi mamaki, indai zasu hadu ko Suyi waya setayi masa sallama, gashi lokaci zuwa lokaci yakan ji tace masha Allah, subhanallah da maka mantansu

Se yayi zaton kawai saboda yana yawan fada ne itama takeyi

A kwana a tashi gidansu marry aka fuskanci sauyi a tare da ita sakamakon yawan fita datakeyi,

Kuma fitar ma ita kadai dan haka aka tsaurara mata tsaro ta shiga damuwa sosai rashin ganin Aliyu da batayi sedai suyi waya abun ya dameta matuka,

Aliyu yace tabarshi yazo shi Inda take amma tace masa baze yiwu ba,

Wasa² suka shiga matukar damuwa saboda rashin ganin juna

Abiola yake gayawa abinda yake faruwa 

Abiola ya tausayawa Aliyu ganin yadda marry ta jashi fage me matukar wahala dakuma hatsari

(Wato soyayya)

Gakuma banbancin addini da kabila ga kuma uwa uba dokar masarautarsu 

Aliyu yasaka ranar zuwa kano domin yaga gida don kusan watansa hudu a kogi state haduwarsa da marry ne ya mantar dashi kewar Gida datake damunsa da farko,

     Wata rana Suna waya da daddare shida marry yake gayamata yanaso yaje kano domin ganin Gida 

Kuka sosai ta kama yi masa ya shiga damuwa 

“Haba maryam ya haka zaki tayarmin da hankali kin hanani zuwa inda kike kinki bari mu hadu, 

   bakisan yadda nakeji ba ne naga kaman baki damu ba ko baki yadda dani bane bansani ba”

“Noo bahaka bane nima ina cikin damuwa an samun tsaro sosai, am sorry Aliyu akwai abunda na boye maka amma inaso mu hadu kafin ka tafi”

“A ina zamu hadu ?”

Yai mata tambayar cike zakuwa

“Inda muka saba haduwa a garden”

“To shikenan kaman karfe Nawa?”

“Da yamma by God will”

“Allah ya kaimu da rai da lafiya”

“I love u Aliyu”

“Love u more my dear”

“Kamin wani Alkawari”

“Wane Alkawari ?”

“Will u marry me?”

“I will me sunan mum insha Allah in dai family dinku zasu yarda dani su bani auren ki, bantaba soyayya ba se akanki, akanki nafara kuma daga kanki nagama insha Allah”

Ajiyar zuciya tayi

“Aliyu ka kwanta karka makara sallar Asuba kaimin addu a lamuran suzo da sauki”

“Kullum inayimana kiyi bacci me dadi zanzo a mafarkinki muje yawo”

Dariya sukayi suka kashe wayar

Kaman yadda tayi masa Alkawari haka tayi kokari seda ta fito daga Gida bawanda yasani

Inda suka saba haduwa yauma anan suka hadu

Se dai sabanin sauran kwanaki dasuka saba haduwa yau fuskarta dauke take damuwa 

Kusa dashi ta zauna shiru ya Dan ratsa 

Sannan ya kalleta

“Baki da lafiyane?”

Ta girgiza masa kai 

  “Ya akai kikayi wannan ramar haka meyake damunki, tell me, meyake faruwa”

Idonta taf hawaye ta kalleshi 

“In ka tafi yaushe zaka dawo?”

“Bazan Dade ba insha Allah”

“Dagaske kake zaka aureni?”

  “Am serious ina sonki son da bantaba zaton zanyiwa wani makamancinsa ba bayan Dan uwana I love u with all my heart”

“Aliyu ina sonka Dan Allah in kagama service ka tafi dani garinku ka aureni musulunta zanyi”

Mamakine yacika Aliyu ba maganar da tayine ya bashi mamaki ba illa magana da tayi da harshen Hausa Wanda be taba zaton ko zo tasani da hausaba

” Noor (sunan da yake kiranta dashi kenan)

Dama kin iya Hausa?”

“Na iya Hausa”

Tabashi amsa

“How comes ban taba ji kinyiba”

Wata nannauyar ajiya zuciya ta sauke 

“Mamana kiristace babana kuma musulmi ne kuma ba haushe ne family din babana dukansu musulmai ne kuma musulmi suke aure

Baba nane kadai ya auri kirista wadda ta kasance ya mace tilo a masarautarmu yan uwanta duk mazane dan haka ake matukar sonta a cikin masarautar da ta ISA aure ta dage akan wannan musulmi take so akayi² ta hakura taki Dan haka aka kyaleta ta aureshi

  Tunda ta aureshi ya tafi da ita take samun cusgunawa daga dangin mahaifina suka takura mata da kyama da tsangwama a daddafe ta haifeni ta yayeni babanta yece sedai ta dawo Gida a hakura da auren ba za adinga wulakanta masa ya ba a matsayinsa na sarki me fada a aji amma ace ana wulakanta yarsa a gidan aure

Dangin mahaifina suka kwaceni shekarata takwas a hannunsu babana ya rasu a gurin kakata na zauna ita ke koyamin karatun addini shekarata takwas amma na haddace izu ashirin na Qur’ani

Da  mamana taji rasuwar mahaifina ta daga hankalinta akan se an batani ,

An kai ruwa rana seda kakana ya hada da karfin mulkinsa sannan aka karbeni daga dangin mahaifina

A gurin kakannina ni musulma ce na iya abubuwa dayawa kuma na tashi da Hausa a bakina dana dawo nan mamana ta maidani addinin ta sannan tayi Alkawari bazata bari inyi gangancin datayi ba, family dinmu ba a auren Wanda ba yarenmu ba ko kuma ba addinin mu ba  tun daga kan mamana akasaka wannan dokar”

Tana kaiwa nan ta sauke ajiyar zuciya

  “Meyasa tun farko kika boyemin hakan, why”?

Idonta taf da hawaye ta kalleshi

” please Aliyu don’t leave me tun randa kukazo da abiola na ganka naji ina sonka kate makamin Aliyu, in kai haka zaka ceceni daga halaka danakee ciki zan samu damar komawa addnina na musulinci”

“Lallai abiola munafiki ne shine ya kyaleni nake ta fama ko Ashe yasan komai”

“Ni nahana shi yagaya maka Dan Allah Aliyu kar kaarabu dani kayi Alkawari zaka aureni”

  Kuka take sosai

“Is OK ai bance miki nafasa ba Dan haka kiyi shiru zansan yadda za ayi zanzo innemi aurenki a gidanku”

Zaro ido tayi tace baze yiwu ba ita dai kawai ya tafi da ita basu saniba

    “Idan nayi haka banyiwa iyayenki adalci ba kibari inje kano in dawo zamuyi abinda yakamata”

Haka sukayi sallama kaman bazasu rabu ba

   Aliyu ya dawo kano cike da tunanin noor (marry) sunyi farinciki da ganinsa, dayake da weekends ya dawo yaita zuba ido yaga Jawwad amma be Ganshi ba

  “Wai INA Dana ne” ya tambayi Usman 

“Hmm wallahi wani yaro ya hadu dashi a kusa da makarantarsu, sun likewa juna yaita kuka se an kaishi gurin yaron, shima yaron in aka tashi daga tasu makarantar seyabiyo shi gida direbansa da malaman makarantarsu suyita nemanshi se mun maida shi makarantarsu yayita kuka,

To shine babansa yace Dan Allah da weekends  akai Jawwad kokuma shi akawo shi akawo shi nan”

“wannan wane irin shirmen banza ne kawai Ku dauki da Ku kaiwa mutanen da Baku Sani ba to ni ban yaddaba, akan me kawai ni gayamin inane inje in dakko shi”

“Sannu sarkin azarbabi kai ko kara babu, gidan mutanen kirki ne har nan mahaifin yaron yazo ya roki alfarma yanzu yasakasu a islamiyya daya”

Inna mairo ce take wannan jawabin

“Au saboda wulakanci had da canza masa makaranta haka akeyi kaikuma kana zaune”

  Seda aka gaya masa gidansu yaron yana gadon kaya Yakama hanya ya tafi dakko JAWWAD,

yana zuwa ya tarar an shiryasu me gidan ze fita da su Jawwad da wani yaro da befi sa’an jawwad ba 

  Da gudu Jawwad ya tafi ya rungume Aliyu ganin haka yasa shima Yaron ya tafi ya rungume Aliyu, ya rungume su gaba daya

Suka gaisa da mutumin 

Aliyu Yace masa

“Dana Nazo dauka”

“Wanne kenan?”

Mutumin ya tambayeshi

  “Jawwad mana”

“To ai har gida na tura aka dakko shi da izinin mahaifinsa”

“To ai nine babansa tafiya nayi ne kuma na dawo abani Dana ban yadda ya dinga zuwa wani guri yana zama ba”

Yayi maganar yana janyo hannun Jawwad aikuwa Jalal ya fashe da kuka ya bisu yana “daddy kace ya dawo min da shi”

Aliyu ba yadda beyi ba adena kai Jawwad gidansu jalal amma abu yaki,

Inma ba akai Jawwad ba za akawo JALAL sekace tagwaye

A yan kwanakin da Aliyu yayi a kano Dan uwansa ya fuskanci akwai abunda yake damunsa saboda Sam baya walwala sosai  

Usman ne yaje ya sameshi adaki yana waya da marry ya jirashi ya gama sannan ya mai tambayar

“Dan uwana me yake damunka ne naga Sam Baka da walwala ko akwai wata damuwa ne”?

” akwai kam yayana”

“Me yafaru?”

Usman ya fada yana kallonsa

Be boye masa komai ba ya gaya masa halin dayake ciki

Jinjina kai yayi

“Gaskiya Dan uwa ka debo da zafi shawarar da zan Baka ka hakura bana tunanin abin nan ze yiwu kasamu wata anaan ka aura”

” a lokacin da ka dakko naka Auren waya hanaka, kamin addu a kawai bana son wanna shawarar taka , tashi kabani guri'”

Aliyu ya fada yana nuna masa hanyar fita

Satinsa daya a kano ya koma kogi state an kai ruwa rana sosai a gidansu marry da aka gano tana soyayya da musulmi kuma bahaushe

Kwanci tashi Aliyu ya kammala service dinsa 

Dayazo da maganar auren marry Gida malam yace be yadda ba, ga yayan musulmi nan a garin nan dan haka ya hakura da maganar yarinyar nan.

Marry kuwa taita rashin lafiya saboda Aliyu ya tafi ga kuma anki yadda da ya aureta, mamanta ta dena kulata sarki yayi fushi da ita duk da soyayar da yake mata, ita kuma ta kafe tace ita se Aliyu

  Shima nan haka Aliyu yake ta fama da malam amma yaki yadda, inna mairo CE kawai ta goyi bayansa amma malam ya kafe yace be yadda ba sedai ya auri musulma

Da wannan rikicin seda aka shafe shekara biyu ana fafa tawa da wannan rikicin 

Marry taje ta samu maman ta tace itafa gaskiya zata tafi kano gurin Aliyu shi takeso bazata iya zama a garin nan ba

A gigice Maman ta taje tasamu sarki ta gaya masa, juyin duniya marry ta kafe tace itafa gaskiya tunda bazasu yadda ba tafiya zatayi, 

Dan haka sarki yace to ya sallameta basu ba ita har abada karta kara dawowa, marry tace ta yadda,

Tana kuka mamanta na kuka haka ta hada kayanta ta nufo kano………

Bayan la’asar marry ta sauka a kano layin Aliyu ta shiga kira bugu biyu ya dauka

“Aliyu kana ina ne?”

ta tambayeshi

“Ina gida”

Yabata amsa

“Kazo ka tafi dani Dan Allah”

“Ahh wai kina ina ne?”

“Aliyu kazo ka daukeni ina kano fa yanzu na karaso”

Zaro ido yayi

“Are u serious?”

“Dagaske nake”

A kidime ya tashi ze fita sukayi karo da Usman 

“Dan uwa ina zaka, naganka a kidime haka”

  “Dan uwa marry ce ta biyoni kano”

“What are u serious”

” yanzu mukayi waya da ita ta fadamin”

“Muje tare” 

Usman ya fada yana Jan hannunsa suka fice

Kaman yadda ta fadamasa a tasha sukaje suka sameta rungume da akwatinta

Haka suka Dakkota suka taho gida 

Suna zuwa Zainab ta karewa marry kallo

“Wannan fa daga ina”?

Tafada a yatsine saboda ta ganta tare da Usman ga kuma uban akwati

” bakuwace”

Shine kawai abinda Usman yace mata suka wuce bangaren inna mairo 

Lokacin ana ta kiraye² sallar magariba dan haka suka kaita dakin inna mairo suka tafi masallaci

Bayan inna ta idar da salla ne tare da lazimi

Ta kalli marry tace mata 

“Sannu da zuwa”

  “Yawwa mama ina wuni”

Tafada da hausa amma a hausan tata zaka fuskanci ba cikkakiyar ba haushiya ce ba 

“Lafiya kalau, amma banganeki ba “

Dan sunkuyar da kai tayi

“Tare muke da Aliyu”

Nan inna mairo ta gane wace ce

Tabata Abinci da ruwa tabata guri ta huta

Se bayan sallar isha’i sannan su Aliyu suka dawo gidan a dakin inna mairo suka hadu suna jiran zuwan malam Imam suji me ze yanke,

Zainab se sintiri take so take taji wace wannan bakuwar dasuka zo da Usman da Aliyu harda su trolley ita dai bata san taba

Akajima se ga malam imam ya dawo yazo ya samesu a zaune jungun² a dakin inna mairo

“Ya akayine na ganku a zaune kunyi shiru, bakuwa mukayine”

Inna mairo ce ta shiga korawa mamalam imam bayani

Ransa ne yayi matukar baci da jin inda jawabin NATA ya dosa, ya tashi ya bar gidan gaba daya

Seda yayi kwana biyu baya shiga harkarsu

Zainab kam ta uzzurawa Usman setaji wace ce yarinyar nan amma yaki gaya mata

A kwana na uku

Aliyu ne yasamu malam a tsakar gida yaje gabansa ya durkusa

“Baba na dama akwai lokacin da zezo kayi fushi dani haka kadena kulani Aliyun ka nefa dan autanka 

Kasan bantaba dakko maka magana ba meyasa bazaka yadda da niba”

“Ya raina baze baci ba, seda na jamaka kunne akan yarinyar nan, amma saboda baka jin maganata kaje ka ja jubota ka kawomin ita gida haba Aliyu yaushe kafara dena jin maganata”?

   Marry tanajin abinda ya faru a hankali ta tako ta karaso gaban malam imam ta zube

“Baba ba laifin Aliyu bane ni na kawo kaina dan girman Allah karka koreni, kafison in koma inda na baro kan addinina na baya?

Baba kaifa malamine kuma ubane dan Allah baba musulunta zanyi, ka auramin Aliyu idan na bar nan bazan koma gida ba wani gurin zanyi in ka koreni bansan inda zani ba,”

Duk wannan maganar da take cikin kuka takeyi 

Aliyu ma gaban malam ya durkusa ya rike hannunsa 

“dan Allah baba na ka amsa mana ka yadda in auri maryam dan Allah baba inba ita na aura ba wallahi bazan iya auren wata mace ba”

Usman ma gaban malam yaje

” baban mu tun tasowarmu kake sonmu kake kula damu, kake son abinda mukeso, baba ka amince da bukatar dan uwana,

Baba ka girmama son da maryam da Dan uwana kema junansu Wanda yasa ta baro daular da take ciki ta taho gurin mu, inka yadda da auren nan kaman kayi jihadi ne”

Inna mairo ma cewa take

“Malam a duba lamarin nan d’a na kowa ne mukanmu misaline munzo garin nan. Bamu da kowa”

Ajiyar zuciya yayi ya nisa sannan yace……

Numfasawa yayi ganin yadda yaran gaba daya suke durkushe a gabansa ga maryam da take ta kuka

Ko ba komai Aliyu yaron kirki ne tun tasowarsa ba taba dakko masa magana ba dukda fadansa da shige shigensa baya dakko magana

Kuma ya duba misalin da inna mairo tai masa Suma yadda sukazo basu San kowa ba malam shehu ya daukesu kaman yayansa Dan haka ya numfasa

“To shikenan na amince Allah ya tabbatar mana da Alkhairi yayi muku albarka gaba daya”

Marry ta dago da sauri

“Baba dagaske ka yadda in auri Aliyu”

Ya gyada mata kai 

Da gudu marry ta tafi gurin Inna mairo ta rungume ta

“Mama bani da bakin godiya mama kiyimin godiaya gurin baba, kun gama min komai a rayuwa da kuka karbeni nagode sosai.

” ba komai maryam nima nayi diya dama bani da ya mace”

Inna mairo tayi maganar tana sharewa marry hawaye

Aliyu da Dan uwansa haka suka dinga yiwa mahaifinsu godiya tare da adduo’i

Usman yaji dadin yadda baba ya amince ko ba komai shima Dan uwansa ya samu farin ciki

Bayan malam imam ya koma daki ya kira Aliyu yayi masa nasiha  ya ja kunnensa game da rike amana da yi masa gargadin zama jakada nagari na addinin musulinci da kuma kabilar hausawa

   Haka marry ta karbi musulinci  ta koma maryam Amma aliyu yake kiranta da noorat saboda sunan mahaifiyarsa ne

Abubuwa sunzo mata da sauki saboda tasan addinnin musulinci se Dan abinda ba a rasa ba.

Itakuwa Maman Jawwad tunda taga abunda yafaru gashi kuma mutanen gidan sun karbi maryam.ta fara jin haushi, yadda inna mairo take kula da maryam kamar yarta amma ita dasukayi kusan shekara shida da ita bata wani shiga sabgarta,

Dan haka ta shiga yayatawa a anguwa kanin mijinta Aliyu ze auri kirista dukda tasan ta musulinta, hakanan se yan unguwa su shigo dan aga matar da Aliyu ze aura.

Duk surutun da ake a gari Aliyu da yan gidansu suka toshe kunnensu, dama ba a tunkarar Aliyu da maganar Dan ansan masifaffe ne 

Sedai ayiwa Usman ko magulmata in sun shigo suyiwa inna mairo

Aka ware musu bangarensu a cikin gidan, dukda kasancewar maryam kabila kuma wadda tayi girma a gidan sarauta amma tana da matukar biyayya da girmama manya ba ruwanta da hayaniya, mamansu Aliyu ana kiranta inna mairo amma ita se dai tace mata mama

Malam ya tsaida ranar daurin auren maryam da Aliyu sati biyu

Usman shi ya hadawa Aliyu lefen da aka bawa maryam itakuma tace ai tana da kayan sawa

Inna mairo tace mata wannan itace Al’adarmu ana hadawa mace kayan lafe abata

A lokaci kankani mutan gidan nan suka saki jiki da maryam ta shiga ransu saboda tsabar nutsuwa da biyayya gashi kullum tana tare da Jawwad yaron yana sonta wataran hada JALAL in an kawo shi,

amma banda Zainab wadda ba ruwanta da ita

yan gidansu Zainab musamman sukazo don ganin maryam suka dinga Yar mata da bakaken magana yayarta wadda suke cewa Yaya mairo ta dinga ziga Zainab,

“Ba ruwanki da ita kuma karki kara yadda danki yaje inda take don arna mugayen kazamai ne gasu da asiri na bala’i dan haka ki rike kanki karki bari a mayar miki d’a da irinta dan wannan tuban nata be kai zuci ba mumafuka CE yaudararku kawai takeyi”

Haka sukayi ta zigata sannan da yamma suka fito zasu tafi suka tarar maryam tana wanke² a tsakar Gida

Se Yaya mairo ta waigo ta kalli Zainab

“wai ya sunan ta ne”

Ta tabe baki

“Wai maryam” Zainab ta fada a wilakance

“Kutt dan wulakanci sunana aka samata”

Itakam maryam tana ganinsu ta fara murmushi 

“Sister zaki tafi ki gaida gida Allah ya kiyaye hanya mungode”

Tai maganar tana dan durkusawa

“Au dama ta iya hausa, tab wai Allah ya kiyaye Ashe tasan Allah”

Yaya mairo tafada tana wani kebe baki

Da maryam ta fuskanci wulakanci zasuyi mata seta cigaba da aikinta

“Tab an baro iyaye an fake da za a musulinta an ta ho bariki,

Allah dai ya kiyayemun kanwata”

Ido taf hawaye maryam ta dago tana kallonsu

“Meye kuma na kura mana ido to indai kurwarmu ce kwalelenki dangin maita, banda jaraba wannan kanin mijin naki yarasa wadda ze aura se tubabbiya tir”

   “Nawa ubanki yabani gudunmuwar auren da zanyi?”

Sukaji yo muryar Aliyu dama shi ba sabgar matar wansa yake shiga ba saboda ya fuskanci bata da mutunci ita da yan gidansu

   “Zainab bari in gaya miki wani abu guda daya tunda iyayena suka karbi maryam banga matar da ta isa tazo tana zaganmin mata ba muddin kika kuma kuskuren zaginta zan baki mamaki munafukan banza kawai marasa tarbiyya”

“Noorat aje wanke² kikoma daki rabu da su jahilai kawai”

Lokaci² maryam kanyi kuka inta tuna da iyayenta tana kewarsu

   

   Yayinda ya kasance bangaren iyayen maryam ma haka mamanta kullum setayi kukan bakin cikin rabuwa da yarta kullum cikin tunanin Allah yasa kar yarta ta fuskanci kalubalen da ta fuskanta a gurin al ummar hausawa ubangiji yasa tana hannu nagari.

Ranar wata juma’a bayan sallar juma’a aka daura auren Aliyu da kuma maryam

Malam imam shi yayiwa maryam kayan daki yayinda Usman shi yabiya kudin sadakin maryam

Suma aka basu guri a cikin gidan ranar maryam bakinta kasa rufuwa yayi ji take kaman mafarki waita mallaki Aliyunta 

    Haka rayuwa tacigaba da gudana yayinda maryam ke fuskantar wulakanci daban² daga bangaren Zainab, danginta, kawayenta da kuma  sauran yan unguwa

Ko ruwa maryam ta sha da Kofi Zainab bazata kara taba kofin ba datayi abu zata fara cemata tubabbiya ta baro danginta ta taho yawon ta zubar indai Jawwad yaje inda take har dukansa takeyi amma kullum shida Jalal suna manne da maryam

Maryam bata taba kulata ba, ita soyayyar da Aliyu da iyayensa suke mata yafiye mata komai dayake Allah besa ta samu haihuwa da wuri ba 

Aliyu ya maida ita makaranta takuma yin waec bata samu admission ba dan haka se ta shiga poly ta karanta catering

  Rashin haihuwar da batayiba ya dameta matuka Aliyu ke kwantar mata da hankali, yana cemata gasu da Jawwad ga Jalal suma yayan sine

   yayinda Zainab take cewa tunda an saba zubar da ciki sannan akai aure ya za ayi yanzu asamu haihuwa tunda angama barar da kwayayen a titi sannan aka tsallako aka taho wai an tuba,

Itakam maryam bata tanka mata, se dai in Aliyu yaji yazo ya kare mata tas, 

malam imam ya sha Jan kunnen Zainab akan wannan abubuwan data ke wa maryam amma bata fasa ba dan ba kunyace da ita ba.

   Katsam maryam tasamu ciki ta fara laulayi tayi farinciki sosai da wannan cikin dukda kasancewar cikin na wahalda ita Aliyu shiyake mata komai har cikinta ya fara girma sannan tasamu sassauci

Amma bangaren cin mutinci daga yan uwan Zainab da sauran yan unguwa se abinda yayi gaba yayinda

Zainab ta dinga cewa watakila ma cikin bana Aliyu bane cin zarafi daban²

Babban bakin cikin Zainab maryam bata kulata kome zatayi

Wata tara cif Allah y sauki maryam lafiya ta haifi ya mace me matukar kyau kamanta daya da Yaya mairo kalar Fulani sosai

Tunda aka haifi yarinyar nan JAWWAD da JALAL suka zama yan raino JALAL baya tafiya Gida kullum yana manne da jaririyar nan, 

JALAL Ya dinga bin Aliyu yana cewa Abee (yanda JAWWAD take kiransa) yana cewa dan Allah Asama jaririyar JALAL dariya Aliyu ya dinga yi yana cewa JALAL kataba ganin ansawa mece sunan maza

Shidai ya dage asawa babyn sunansa 

“Kar ka damu yarona ko dan kaunar da kakewa dana Jawwad zanyima yanda kakeso”

Ranar suna ta zagayo akasawa jaririya suna Jalila

   Watan Jalila 3 Zainab ta haihu itama ta haifi ya mace lokacin Jawwad yana da shekaru Tara

Ranar suna akasama yarinya Nana Fiddausi sunan Jakarta

  Nana da JALILA suka tashi kamar yan biyu 

Jalila ba abinda ta bari bangaren halin mahaifinta na fada da Neman magana in tafita bata da aiki se Neman magana da cin zalin yayan mutane, sukuma iyayensu su kamata su daka  tare da yimata gorin Yar tubabbiya jikar arena

Abin yana bakantawa maryam da shikansa Aliyu maryam ta dauki son duniya ta dorawa Jalila in dai aka taba Jalila ji take har cikin zuciyarta amma se ta kauda kai,

A cikin Gida ma Maman jawwad yimata take ko Yaya Jalila ta kwace Abu a hannun Nana, in dai Nana tayi kuka Zainab ta dinga zage² kenan tana cin mutuncin maryam

  Wata rana hakan ya kuma kasancewa inna mairo bata nan, Jalila tasaka Nana kuka Zainab kuwa  ta wankawa Jalila mari sekace sa’arta, Jalila seda ta fadi tana kuka, sannan Zainab ta dinga zaginta tana cemata Yar gaba da al fatiha jikar arna

  “In kika kuma sheganta min yarinya zan baki mamaki dukanta ne kiyi tayi kezaki ji kunya dan anjima tare zasu cigaba da wasa kuma ko kinki yan uwanta ne”

Maryam ta fada tanaama Zainab kashedi

  “Na fada Yar gaba da alfatiha Yar arna ai ba karya nayiba, kuma Ya”ya na daban ita daban su duk danginmu musulmine tun daga farkonmu har karshe”

  Murmushi maryam tayi

  

“Kina bakanuwa kike cewa kaf zuri’arku musulmine watakila ma hada kakanki ake zagaye Dala tsirara kinga watakila garani damuke kiristoci akan Wanda suke bautawa tsunburbura

Jahilar banza se fadan musulinci abaki amma ke babbar Jahila ce manyan sahabban manzon Allah salallahu alaihi wassalam a cikinsu wasunsu bautar gunki sukayi amma daga baya suka zama manyan hadiman musulinci babu banbanci a musulinci annabi be taba kyamatarsu ba”

(Kunsan me hakuri be iya fushi ba)

“Nice kakana ya zagaye Dala tsirara” 

Zainab tafda tana nunkanta da yatsa

  “Au tambayata kike kina bakanuwa wata kilama shine barbushe”

Maryam tabata amsa

Ana haka Sega Yaya mairo sunzo ta Tarar ana wannan rigimar 

Sukazo suyiwa maryam taron dangi Sega Aliyu ya dawo ba shiri suka watse don suna tsoronsa yanayin fuskar maryam ya nuna masa akwai Matsala dan haka da suka shiga daki

Ya kalleta “noorat meyake damunki ne, gayamin me ya faru”

Batai aune ba se taji hawaye

“Habiby bana jindadin yadda ake treating baby(JALILA) ana mata gorin wai ita Yar arna CE ga baby da Neman magana aita zaginta nafara gajiya nafara rama mata am tired suma dasukazo a musulmi ai ba dabarar su bace”

Ta karasa maganar cikin kuka

Ajiyar zuciya yayi

  Ya janyo ta jikinsa yana share mata hawaye

“Tunda naga wannan matar tazo nasan a Rina maybe itace ta taba minke, kiyi hakuri Nima abun yana damuna amma kibani dan lokaci wani mataki nake shirin dauka”

“My love wani matakin zaka Dauaka AbU ya Riga yazaga gari”

  “don’t mind u will see”

“To shikenan bari naje na wanke mana kaya”

“Just relax baby zanyi mana, yanzu ki huta kawai”

Bayan wani dan lokaci Aliyu ya nemi aiki a Kaduna ya kuma samu aikin sannan ya nemawa maryam admission a ABU Zaria 

Malam yayita fada dan meyasa ze bar Gida ya koma wani gari da bashi da kowa

Yaiwa malam bayanin yana tsoron abunda ya faru da mahaifiyar maryam itama ya faru da ita a dalilin cin zarafin da ake mata kar itama ta karaya ta koma cikin ahalinta ta koma addininta na baya, haka malam ya yadda badan yaso ba

Usman ma da inna mairo sunyi bakin ciki nesa  da Aliyu ze yi  dasu tun tasowarsu suna tare amma yanzu ze tsallake ya barsu

shima Aliyu ba a son ransa ba sedan samun nutsuwar matarsa da kuma kare mutuncin iyalansa daga wannan kyama da cin zarafi da ake musu ze bar gidansu da yan uwansa

 Haka ya tattara matarsa da yarsa suka koma Kaduna inda ba Wanda yasansu

Su Jawwad ma har kuka sukayi dukda sun fara girma lokacin baban Jalal yana ta shirin kaisu boarding school Jawwad da Jalal in zasu shiga Jss 1

Akasaka Jalila a makarantar Islamiyya da zamani halin Jalila na Neman magana yana nan bata denaba

 yayinda maryam ke zuwa makaranta kuma take taba kasuwanci

Aliyu ma aikinsa yake yana samun rufin asiri dai² gwargwado har ya mallaki gidan kansa

Hankalin maryam ya kwanta sosai yanzu ba Wanda yasan asalinta balle yayi mata gori

Lokaci² suna zuwa kano su gaishesu Usman ma yana zuwa ya dakko Jawwad Jalal da nana yazo dasu amma koda wasa Zainab bata taba zuwa inda suke ba

  Bayan shekaru biyu da dawowar Aliyu Kaduna Allah yayiwa malam imam rasuwa 

Sunyi bakin ciki sun shiga tashin hankali ba kadan ba sunyi kuka har suka hakura

   Bayan rasuwar ne Zainab ta hurawa Usman wuta cewar tunda yana samun kudi sosai tun da har kasashen waje yafara fita kan harkar 

Kasuwanci, dan haka dole Suma subar gidan nan dan be kamata ace kamarta tana zaune a wannan Gida ba Usman yayita nuna mata saboda inna mairo karsu barta ita kadai gashi ta Riga ta saba da unguwar, amma Zainab ta rufe ido taitamasa fitina

  Haka yaje yasamu inna mairo da zancen ta shi daga Gida tace ba komai ita subarta anan su su tashi,

  Amma yaki yadda, wataran inna mairo ta ta shi da amai da gudawa aka kaita Asibiti ta galabaita matuka dan haka Usman ya kira Aliyu ya sanar masa da safe

Be dau wani lokaci ba Aliyu yayo kano dan maryam bata San ya tafi ba 

Se bayan la’asar kawai setaga Usman yazo yace mata su shirya kano zasu tafi,

“Me zamuyi a kano INA abu Jalila”?

” shima yana can”

“Dan Allah abban Jawwad in wani abu ne yake faruwa ka gayamin”

 “Babu komai inna CE ba lafiya”

A kidime ta shirya ita da Jalila suka yo kano

Kai tsaye Asibiti suka nufa inda ya kaisu wani daki

Tana shiga Aliyu ta gani a kwance akan gado rai a hannun Allah jini na fita ta hanci ta bakinsa gashi ko kwarzane babu a jikinsa amma da yayi numfashi ze gudan jini ta hanci ta bakin……

Share please

More comments more typing

Ina amfani da wannan dama domin mika barka da sallaha layya ga al ummar musulmi a duk fadin duniya sekuma Allah ya kaimu bayan salla 

Saura aki bani naman salla

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Love u all

Abduljalal novel fans

Back to top button