🐅 MATAR DAMISA🐅
(The Wife Of Tiger)
*ASMEETAH* *NOVEL* ✍️✍️✍️
*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________
https://ww.facebook.com/103637491942644/
💫💫 *{{N W A}}* 💫💫
بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم
*BOOK* *ONE*
P➡️59 & 60 ⬅️
Bayan kuliyar ta gama ci da wuta, juyawa Ayush tayi ta rungumi Junaid tana jijjiga shi “Yaya Junaid! Yaya Junaid ka motsa manaa, dan Allah” tana kuka tana ambatan sunansa,
Tasan wannan aikin Mahaifinta ne,
Shi kuwa yana nan a qafe ko motsi babu,
Rungumarsa tayi sosai, hawayen ta ne suka sauƙa akan wuyan Junaid!
Cikin ikon Allah kuwa yayi firgitt yana sauke numfashi sama-sama, idonsa ne suka sauƙa akan fuskar Ayush wanda yayi jawur tsabar kuka, hannu yasa yana goge mata hawaye cikin sassanyar murya yace “meya farune my Yushert, fatan ba abunda ya sameki ko? Ina kuliyar?”
Waige-² ya tsaya yi amma baiga komai ba, hakan ya yi matukar ɗaure masa kai.
Ita kuwa gaba ɗaya ta ruɗe sai faɗin “Yayana! Yayana babu abunda ya sameka Allah yana tare da kai, bazan taɓa barin wani abun cutarwa ya cutar mun da kai ba….”
“Yushert tambayarki nake ina kuliyar? Yau saina kasheta, bazan bari tabar gidan nan ba saina sheƙeta”
Wuce wa yayi zai tafi
Ayush tayi saurin riƙo hannunsa “a’ah Yayana kuliyar ta tafi, karkasa kanka cikin matsala please”
“Zan tinkari wannan matsalar kuwa, zanga ta yanda kuliyar ta fito kuma meyake kawota, gurin wa take zuwa, wa yake turota duk zan bincika…” a cewar Junaiddd.
Suna cikin wannan halin sai suka jiyo sallamar Mommy ta shugo hannunta riƙe da key din motor,
“Lafiya kuwa, meyake faruwa ne naga kunyi cirko-²
Ayush meyake faruwa ne”
Ayush ce ta nufo gurin Mommy tana zuwa ta rungumeta tana kuka,
Itama kanta batasan kukan mai take yi ba…
“Sorry Ayusher, ke da Junaid ne koh?
Meya miki ne..”
Girgiza kai tayi tana faɗin “Yaya Junaid bai mun komai ba Mommy kawai nayi kewarki ne”
Mommy itama rarrashinta ta shiga yi tana faɗin “kiyi hakuri ai gani nam ko, kin tabbata ba Junaid bane ya sanya ki kuka ba?”
Ɗaga kai kawai Ayush tayi ba tare da tace komai ba,
Shi kuwa Junaid tsayawa yayi yana kallonsu yayi wani tur6une fuska cikin 6acin rai yace “wai mommy meyasa kike son ɗora mun laifi ne, komai akayi sai kice ni komai ni, haka a hospital kika hau kaina da masifa wai ni nayi wa Doctor Hasheem dukan mutuwa alhalin ni bansan komai ba haba haba….”
Yana kaiwa karshe ya haura upstairs….
Mommy kuwa kallo kawai ta bishi da shi daga karshe kuwa ta jinjina kanta tace “Allah ya shirya mun kai Junaid…”
Ayush itama jin Abunda Junaid ya gaya yasa zuciyarta bugawa
“Wai daman Yaya Junaid ya yiwa Dr Hasheem duka?? Innalillahi zan so naga Dr Hasheem”
Maganar zuci take har kwalla yaso ya ku6uce mata,
Sai ji tayi Mommy ta dafa kafad’arsa tana tace “My Doughter tunanin mai kike yi?”
Murmushin yaƙe kawai tayi, tace “babu komai”
“Ok karki damu kinji komai zai dawo normal, bari na shiga kitchen nasan yarana suna jin yunwa ko?”
Tayi tambayar tana kallon Ayush
Wacce kanta ke ƙasi tana wasa da yatsun hannunta,
Ajiye mayafin ta tayi sannan ta nufi kitchen, itama Ayush bin bayanta tayi tana faɗin nima zan taya ki girkin,
Juyowa Mommy tayi da murmushi a fuskar ta tace “to shikenam zo mu fara nasan baki iya girkin ba”
Rufe fuskarta tayi tana dariya, tana so ta koyi girki sosai….
******
Junaid kuwa bayan shigarsa room
Kai tsaye ɗakin sirrin sa ya nufa,
Zama yayi akan sofa da ƙaramin glass table a gabansa sai faman daddanna laptop yake,
Duk bincikensa baya wuce akan *SARKI* *RAAMUD* wanda mutane suka fi saninsa da sarki zalimun wanda ba kowa ne yake iya ganinsa ba sai a wanda ya bama ikon ya kalle shi,
Wadanda suka sanshi sun sanshi wanda basu san shi ba sune suketa wahalar da kansu kamar dai Junaid…
Ga dai drowing dinsa a jikin poster amma an rasa a yanda za’a ganshi,
Haka ya rinƙa faman bincike amma ya kasa gano a yanda yake,
Har bacci ya yi awun gaba dashi akan sofa..
Around 4pm Ayush ta shugo ɗakin Junaid da sallama a bakinta, jin shuru ba’a amsa mata ba yasa tayi tunanin yana toilet,
Tsayawa tayi tana ƙarewa ɗakin kallo!
Taci kwalliya ba ƙaramin kyau tayi ba
Tasha doguwar riga na atampa mai launin black and red ga tayi ɗaurin ɗan kwali mai tuta a gaba, tasau gashin nan ya baje har saman qugunta, ga wani irin makeup da bata taɓa yin irinsa ba sai kamshin turare take ta fitarwa……
Karo na biyu kenam tana zuwa ɗakin Junaid akan yazo suci abinci amma bata samun sa
Har ta gyara masa room ta sauya bedsheet, ta feffeshe ɗakin da air-fresh mai shegen kamshi…
Sannan ta fice a ɗakin a tunanin ta yana toilet!
Sai wannan zuwa karo na biyu still bata same shi ba,
Hakan yasa tayi knoking door ɗin toilet shuru ko motsin ruwa bata jiyo ba
Ta tura kofar ta leƙa cikin toilet babu kowa
“To kodai ya fice a gidan ne babu wanda ya sani”
Fuskar ta ne ya nuna damuwa kamar zatayi kuka,
Saitin wadrobe ɗinsa ta tsaya
Zata jingina bayanta a jikin bango, ƙofar ɗakin sirrin ne ya buɗe bata ankara ba sai ji tayi ta tafi luuuuuu yaraff ta faɗi ƙasi tayi matukar tsorita tasau ihuuu,
Bata ta6a tsammanin akwai ɗaki a gurin nan ba..
Jin ƙarar ihun ne yasa Junaid ya razana daga baccin ya tashi yana “waye ne”
A gigice Ayush ta tashi tana waigawa bayanta, ba karamin tsorita tayi ba
Jikinta yana 6ari “wayyo Allah na nashiga uku ina ne nam..”
ƙarasa shugowa cikin ɗakin tayi tana kalle-²
Har Junaid yazo gabanta bata ganshi ba,
Kafin ta ankara dashi ya janyo hannunta sunyi wajen asalin room ɗinsa
Ya rufe wannan ɗakin yasa mata key!
Yayo kanta yana faɗin “meya shigar dake cikin ɗakin can? Na baki damar ki shugo nan ɗakin amma banda can…..” ya nuna secret room da yatsar sa idonsa kuwa akanta.
“To t t too ni bansan akwai ɗakin a cikin ɗaki ba, ban ban saniba wallahi, wayyo Allah na zuciyata zata fashe! Tsoro nake ji..”
Gaba ɗaya ta kiɗime ta ruɗe.
Shi kuwa sai binta yake da kallo
Shima yasan a cikin tsoro take
Ganin yanda take ta magana a har harɗe yasa ya jawota ya haɗe bakinsa da nata
Ji kake tsitt kamar wanda aka ɗauke wuta..
A tunanin sa yin hakan zaisa hankalinta ya dawo jikin ta!
Hot kiss yake bata kamar zai cinye bakin ta
Ita kuwa tinin ta fita hayyacin ta
Kwakwalwarta bazasu iya ɗaukar irin wannan bada saƙon ba
Ta ƙankame shi sosai, jikinta ne yahau ɓari sai kakkarwa take tayi
Nan take numfashin ta ya ɗage cakk
Ta tafi duniyar suma!
Shi kuma bai san ta suma ba haka ya riƙeta yanata faman tsotse mata baki,
Shi jin bakinta yake kamar zuma,
Zaƙin masifa ne da yawunta shiyasa idan ya kama baya yi da wasa…..
Ita ta ɗanɗana masa shiyasa 😅😅
( to fah idan yawun kamar zuma yake 🤔 shi kuma cann ƙasan ya za’a ji shi kuma 🙈🙈🙈😜😜😜🤣🤣🤣))…
Jin bata motsi yasa ya ɗan dakata, tayi baya zata faɗi da sauri ya riƙota ya karata a saman faffaɗar kirjinsa! kwantar da ita yayi akan gado yana furta sunanta cool “Yushert! Yushert!! wakeup please,
kinga banason irin wannan wasan ki tashi mana…”
Dubata yayi yaga bata numfashi!
Hankalin sa ba ƙaramin tashi yayi ba,
jijjigata yake sosai amma ba alamar motsi, bakinta ya buɗe ya ɗora nasa yana hura mata iskar bakinsa tare da daddanne mata kirji, ganin har wannan lokacin bata farfaɗo ba yayi toilet da gudu ya ɗebo ruwa yana kwara mata
a gigice ta tashi tana jan numfashi sama-2
wani irin dogon ajiyar numfashi yaja ganin ta farfaɗo,
“Sorry Yushert, sorry you not feelling well?”
Ita kuwa wani irin kallo take wurga masa da shanyayyun eyes ɗinta,
kafin ya ƙara furta wani abu ta jawo kwalar rigar sa ya rufu akanta ta zagaya hannayenta ta bayansa ta ƙanƙameshi,
“ina sonka Yayana! ina matuƙar ƙaunarka!! kada ka ce oh’ohhh Yayanah,
jikinka laushi, surarka gwanin burgewa ina so ka kasance dani Yayaa naah……”
toshe mata baki yayi da hannunsa
“Shiuuuuuu🤫🤫🤫 ya isa haka, kiyi shuru”
“Oh’ooh! kace kana sona toh”
tana kallon cikin idanunsa kamar mai jin bacci.
“kinga banson yarinta fa tashi mu sauƙa falo yunwa nake ji …”
yanaso ya tashi daga samanta amma taƙi barinsa ta rungume shi sosai,
“Uhm uhmm ni saika furta mun idan ba haka ba mutuwa zanyi…”
murmusawa yayi sannan ya manna mata kiss akan goshi
yace “I love you my Yushert….”
dai den lokacin da Mommy ta shugo da kulolin food a hannun ta,
ganinsu a haka yasa tasau baki tana kallon su cike da mamaki tace “mezan gani haka JUNAID?????
TOHH MY FANS KUYI HAKURI DA QARANCIN TYPING YANAYIN NE SAI A SLOW,
SANNAN NAYI TAFIYA NE SAKAMAKON RASHIN WAYA, AMMA YANZU NA DAWO……
Domin sauke CikakkenLittafin Sai Ku Danna bulun Rubutun dake kasa
Matar Damisa Book 1 Complete Novel Document
*COMMENTS* *AND* *SHARE* *PLEASE* 👏👏👏