Hausa novels

Kanwar Maza Page 54 Complete Novel By Ayshercool

Page 54

 

Dafe ƙirji mama ta yi tana salati, ta ce “Ɗan nan, da gaske kake wannan maganar?”

 

Abubakar ya ce “Wallahi da gaske nake, kuma ba a bakin mutum ɗaya ba, ni da wani abokina Abdurrahman muka je, abun da na jiyo kenan”.

 

Mama ta ce “Ya salam! Yanzu menene abun yi?”

 

“Ba wata maita a musulunci, haka malaminmu ya gaya mana, to so suke a fasa shikenan a fasa bani Sabir ɗin, ko kuma kuɗin da aka kawo ɗin suke so a mayar, ƴan baƙin ciki ne kawai”.

 

Mama ta kalleta ta ce “Ke! Waye ya saka da ke? Da ke ake ke zaki yanke wa kanki hukunci?”

 

“Mama ba haka bane ba, to kuɗin za a mayar, idan aka mayar kuma an fasa ba za a bani Sabir ba fa kenan”

 

Aliyu ya shigo yana tambayar meyafaru?.

 

Mama ta gaya masa abun da ya faru, Aliyu ya kalli ruma da ta kumbura baki ya ce “Ke ki na son sa a haka?”

 

“Ba fa maye bane ba, ƙarya suke yi. Ni fa bana son shi, amma idan aka fasa ba fa zasu bani Sabir ɗin ba, kuma mama ba kwanan nan aka ce shi ya kashe Anty Aisha ba, kuma ƙarya ake yi masa ba? To wannan ma ina ga ƙarya ake yi masa, ni dai ko za a fasa, kar a mayar da kuɗin nan, kuma a bani Sabir”.

 

“Ke ki ka nema musu kuɗin, ido a kwabo” Yaya Abubakar yayi maganar yana dungure mata kai.

 

Aliyu ya ce “Mama, bana tunanin wannan abun ya kai a fasa aure saboda shi, dama rumaisa na buƙatar tsayayyen namiji jajirtacce, saboda halinta, sannan shi mutum ne fitacce, irin wannan sharrin ba abun mamaki bane ba, ban ƙaryata b kai tsaye, amma ke ki ka gaya mini addu’a da ki ka din ga yi, kina jin son abun a ranki, lamarin ya kwanta miki a ranki, da bai kwanta miki ba sai mu ce babu alkhairi, dan babu hijjabi tsakanin addu’arki gareta da Allah, a ganina mu cigaba da addu’a babu ma’ana a kawo wannan zancen ma, tun da ai ita ma rumaisan tana son sa ko?”

 

“A’a nifa ba son shi nake yi ba, kawai saboda a bani Sabir ne”.

 

“To amma ai ke ki ka ce mai kuɗi ki ke so, kuma mai kyau wanne ne bashi da shi a ciki?”

 

“Wannan har wani kyakykyawa ne? Kullum yana wani zazzare ido”

 

Mama ta ce “Tashi ki bar wurin nan, mara kunya, ana maganar aurenki kina tsoma baki”

 

Aliyu ya ce “To sanin ma’anar auren ma ta yi? Amma mama ya kike gani? A kan wannan dalilin zaki saka a ɗauki kuɗin da aka kawo shekaranjiya a mayar musu ne?”

 

Abubakar ya ce “A’a ba ayi haka ba, na gamsu da maganganunka nima, mu cigaba da addu’a dai, Allah ya zaɓa abun da ya fi alkhairi”

 

Mama ta amsa da Amin, sannan ta tashi ta saka Yasir a gaba suka tafi kasuwa.

 

Likitoci suka karɓi iman, kasancewar asibitin sun san matsalar Iman, nan da nan suka karɓeta.

A duk lokacin da ciwon ya tashi, Asibitin ake kawota, tun tana yarinya abu kaɗan sai ta yanke jiki ta faɗi ta suma. Aka din ga binciken abun da yake damunta har ƙasar waje, ƙarshe dai aka ce zuciyarta ce ke kumbura wasu lokutan.

Ammi ta alaƙanta hakan, da yawan damuwa da take yi, mussaman a lokacin yadda ake tsangwamarta, hakan ya sanya hankalin ammi ya tashi sosai.

Ta din ga faɗi tashi, domin ganin iman ta samu lafiya, tayi iya ƙoƙari iman ta samu sauƙi, sai dai lokaci zuwa lokaci jikin ya kan motsa.

 

Yanzu haka ammi hankalinta ya tashi, ba ta ƙaunar ganin wani abu ya sami iman, shiyasa kullum cikin addu’a take yi mata, Allah ya sanya iman ta samu miji nagari, wanda zai iya haƙuri da ita ya jurewa larurarta.

 

Sai dai a wannan karon, su kansu likitocin lalube suke yi a cikin duhu, ake ta bankawa Iman ruwa da allurai, aka yi hoton zuciya, amma zuciyarta lafiya ƙalau.

 

Hajiya Sauda ce zaune a turakar turaki, ta dube shi ta ce “Ranka ya daɗe, ni baka gaya mini ina ku ka je ba ranar juma’a, ka zo mana da abubuwa na ciye-ciye, haryanzu baka ce mini komai ba”

 

Turaki da yake cin ayaba, ya ce “Dama dole ne duk in mu ka je sai an gaya miki?”

 

“A’a tambaya dai kawai na yi, na zaci wani abun alkhairin ne ya samu ai”

 

Ya ce “Eh, kusan haka, abun farincikin ne”

 

“Kamar me fa?”

 

“Aure muka je nemawa takawa, na gidan galadima”

 

“A’a, neman aure kuma, yaushe Aishan ta rasu, da har za a nema masa wani auren?”

 

Turaki ya ce “Addini ya bashi dama, Aisha ta kai watanni huɗu da rasuwa babu laifi a ciki dan yayi wani auren”.

 

Danne fushinta ta yi, ta ce “Amma wa zai aura haka da na ji ka ce, kun je nema masa aure”.

 

“Eh, wata yarinya ce, ƴar mutunci iyayenta masu dattaku sosai, su suka bamu wannan kayan duk da na zo da su”.

 

Cikin son bugun ciki ta ce “Kuma ƴar waye? Ai na zata iman zaku aura masa, ta maye gurbin aisha”

 

“To, idan lokaci yayi zaku ga koma wacece, koma itan ce, ko ba ita bace ba”

 

“Amma dai Allah ya baka yawan rai, ni na rasa dalilin da ya sanya, ka fi fifita ƴaƴan wasu a kan naka, na rasa me muka yi maka da ni da yarana. Tsakani da Allah duk yadda Samha take ƙaunar yaron nan a wannan karon ba zaku yi mata adalci ta maye gurbin aisha ba, taƙi auren kowa ta dage sai shi, amma ka yi burus, ku ke je waje nema masa auren wata?”

 

Turaki ya ce “Ban fifita kowa a kan ƴaƴana ba, sai dai son da nake yi wa ƴaƴana, ba zai sanya na zaɓi son zuciya ba. Ba zai yiwu sun kawo wadda suke so ya aura na wuce masa gaba a matsayina na ubansa, na yi amfani da ƙarfin ikona, na ce sai ya auri ƴa ta ba, ki sani zan iya tursasa shi ya auri ƴa ta, amma ba zan iya tursasa shi ya so ta ya kyautata mata ba, na yi mata nasiha tun ba yau ba, a kan ta haƙura da shi, ta yi addu’a ta nemi wani ta aura, har haɗata da na yi da ɗan gidan madaki, Muhammad Sani, ya ce ya na sonta ta watsa mini ƙasa a ido, sai yanzu kuma ku ce ga abun da ku ke so sai na yi, ba zai yiwu ba, kuma ku yi haƙuri, da Samha da takawa duk ƴaƴana ne, ba wanda zan yi wa dole a kan wani abu da yake son zuciya”

Ba ƙaramin ƙuluwa ta yi ba, da jin maganganun turaki, ba ta sake cewa komai ba, ta tashi ta bar ɗakin.

 

Zainab ce ta shiga falon mama, in da Samha ke zaune tana kallon tv, hannunta riƙe da wayarta, ta zauna tana faɗin “Ohh God, ita wannan yarinyar ita kenan kullum cikin ciwo?”

 

Samha ta kalleta ta ce “Wacece?”

 

“A status ɗin Nusaiba na gani, wai iman babu lafiya, ba ta san waye a kanta ba ma, shikenan ita giwa kullum tana hanyar asibiti saboda ƴar tsintuwa, dama ta mutu ko sa huta gaba ɗaya”

 

Samha ta yi ajiyar zuciya, tare da ji a Jikinta, aikin ta ya fara aiki kenan.

 

Fuuu mama ta shigo falon,. Kamar mai tafiya a kan iska.

Duk suka bita da kallo, suna tambayar ko lafiya?.

 

“Hmm, ni da turaki mana, ya gaggaya mini magana a kan kawai na ce, meyasa bai saka adam ya auri Samha ba, wai nema masa aure suka je yi ranar juma’a.

 

Ƙuuuu Cikin Samha ya bayar, wani irin fargaba da faɗuwar gaba ya kamata, neman aure aka je yi wa Adam?.

 

“To kin ji, a wannan karon dai kya haƙura ko?” Zee ta yi maganar tana kallon Samha.

 

“Mama, neman aure kuma? Ba iman za su bashi ba?”.

 

“Bana tunanin ita ce, wata ce daban gaskiya, tun da ya ce sun je nema masa ne, da ita ce ai ba sai sun yi haka ba”

 

Wani irin gumi ne ya shiga ratsowa daga cinyar Samha, gaba ɗaya kanta ya toshe, saboda jin abun a bazata an shammaceta da yawa.

 

“Amma mama wacece haka?”

 

“Oho ina na sani, bai gaya mini ba, ni takaici ma bai barni na san wacece ɗin ba”.

 

Cikin hanzari, ta tashi tafi ɗakinta zuciyarta na yi mata zafi, tsabar wulaƙanci a waje ma ake je aka nema masa wata bayan ita gata a zaune an san tana san shi

 

Zama ta yi daɓas a gefen gado, zuciyarta na ƙuna, wannan shine baba na ɗaka gemu na waje, amma mayar da ita wata sako tumaki ɓallo jakai.

 

“Tun da naga aikin malamin nan yana aiki, Adam da ni ka ke zancen, wallahi kana ji kana gani sai an mayar da kai mace, ba zaka amfani kowacce mace a rayuwar aure ba, sai dai ta kalleka ka kalleta, amma kai da sake kwamciya da wata matar, har abada sai dai idan ni ka aura, zaka gane baka da wayo”.

 

***

Mai sunan baba yana tsaye a kitchen, yana kwashe abinci, kasancewar mama bata nan, babu kowa a gidan, mama tana kasuwa, sai shi da ya dawo gidan yanzu, yayi saurin ɗora girki, dan ya san tsaf rumaisa zata dawo a kowane lokaci idan ba a gama abinci ba, idan ta din ga kwanciya tana kuka, sai ta saka ya daketa. Ga lokaci ya riga ya ja.

 

Mama ce ta kira shi a waya, ya ɗaga yayi sallama.

 

Ta amsa sannan ta ce “Babana kana ina ne?”.

 

“Na dawo gida, na ɗora girki ne”.

Kanwar Maza Complete Novel Document Txt

“Yauwwa, dan Allah idan rumaisa ta dawo, ka saka ta yi wanka ta yi salla, ka tafi da ita asibitin da ta kwanta, an kwantar da iman ku wakilceni ku dubata, yanzu muka yi waya da hajiyar, wai an kaita asibiti ba ta san waye a kanta ba, ni kuma bana tunanin zan dawo da wuri”.

 

“Tom” ya faɗa a taƙaice ya ajiye wayar, ya cigaba da aikinsa.

 

“Assalamu alaikum” rumaisa ta yi sallama, sai dai kan ya amsa ta fara cewa “Wani gardin ne yake yi mana abinci yau, Allah ya sa yayi daɗi, na ji ƙamshin miyar har tsakiyar kaina, Allah yasa ko shinkafa an gama, in fara rage hanya, dan yunwar da nake ji ba a cewa komai” ta ji shiru ba a amsa ba, ta nufi kitchen ɗin tana cewa “Baƙon aljani muka yi ko kurma, da nake magana aka shareni”.

 

Tozali da tayi da shi ne, ya sa ta ci wani wawan burki, rabon da yayi girki har ta manta, dan haka ba ta kawo shi ne ba.

 

“Yi haƙuri, ban san kai ne ba, dan Allah ka yi haƙuri”

 

Kifi yake sakawa a miyar, ba tare da ya kalleta ba, sum-sum ta bar wurin ta koma ɗaki ta kwanta.

 

Mai sunan baba bai tashi gaya mata saƙon mama ba, sai da ta fara shirin islamiyya, ya ce “Na gaya wa shugaban makarantarku ba zaki shiga ba yau, zamu je dubiya”

 

“Ina?” Ta tambayeshi tana kallonsa, sai dai ta manta shi mai sunan baba, idan ya ce ayi kawai ayi, ba tare da tambayoyi ba.

 

Har suka tafi dubiyar, mamaki take yi, waye babu lafiya, ta lissafa wannan ta hango wancan, amma ta kasa gano waye babu lafiya.

Sai dai ba ta ƙara sarewa da al’amarin ba, sai da ta gansu a asibitin da aka kwnatar da ita.

 

Lambar mama ya kira, ya tambayeta wani ɗakin ne, ta sanar masa, yayi gaba rumaisa ta bishi a baya.

Sai da suka je ƙofar ɗakin sannan ya tsaya, ya kalleta ya ce “Ƙwanƙwasa ki fara shiga”

 

Ta matsa gaban ƙofar, ta ƙwanƙwasa sannan ta buɗe ta shiga da sallama babu kowa a ɗakin, sai iman da ke kwance, hannunta ɗauke da cannula, an rataye robar ruwan da aka gama saka mata a drip stand.

 

Shiga ya yi shima, sai dai babu kowa a ɗakin sai ita kaɗai.

 

Da sauri rumaisa ta ƙarasa gaban gadon tan faɗin “Subhanallah, Anty Iman, baki da lafiya ne?” Sai dai ta tarar bacci take yi.

 

Ta kalli mai sunan baba ta ce “Amma ya naga babu kowa a wurinta” shirun da yayi mata ya sanya, ta tuna ta yi tambaya ba a gurbinta ba.

 

Da sauri ta ce “Bari na duba waje, ko zan ga wanda yake zaune tare da ita”. Ta juya ta fita da sauri, shi kuma ya tsaya a tsaye, ya sake kallonta tana kwance cikin doguwar rigar material, dogon gashin nan ya sha ribbon, duk da ya ɗan hargitse, ga farar fatarta gwanin sha’awa, babban abun burgewa da jikinta, bai wuce wuyanta ba, duk da ba ta da ƙiba, amma tana da irin wuyan nan, mai guru-guru.

 

Da sauri ya sunkuyar da kansa yana a’uzubil’ahi.

 

Zagayawa rumaisa ta shiga yi a cikin asibitin, tana mamakin waye yake zaune da iman a asibiti, ya bar ta ita kaɗai babu kowa?

 

A hankali Iman take furta “Ammi, Ammi ruwa, ƙishirwa nake ji” yana jin ta, yayi shiru, kamar babu kowa a ɗakin.

 

Tun bayan farfaɗowarta, kasancewar ciwon kan baya sauka, ya sanya likitocin, suka yi ta yi mata allurar barci, da sai yanzu ta saketa ta tashi.

 

Duk da tana cikin ciwo, sai da ta razana da ta ganshi, a tsaye yana danna wayarsa.

 

Tunani take yi ko a mafarki take, ta miƙa hannu jikinta yana rawa, tana ƙoƙarin ɗaukko robar ruwan da ke kan side bed.

 

Sai a lokacin ya motsa, ya ƙarsa, ya ɗau kofi, ya zuba ruwan ba tare da ya kalleta ba ya ce “Tashi ki sha”

 

Cikin tsananin tsoro ta ce “Bani in sha a kwance, ba zan iya tashi ba”

 

Miƙa mata ruwan yayi, ya ga iya gudun ruwan ta, ta fara ƙoƙarin sha a kwance, ya karɓa kofin ya ce “Tashi!”

 

Kamar zata fashe da kuka ta ce “Dan Allah ka yi haƙuri kaina ciwo yake yi”

 

Haushi ne ya kama shi, gani yake kawai tsabar langwai ne, da iskanci. Ya saka hannu ya ɗagota gaba ɗaya, hakan yayi dai-dai da shigowar nusaiba.

 

Wani irin ihu ta saki, ta riƙe hannunsa, hawaye na bin fuskarta, sabodaa ji ta yi, kamar kanta ya rabe biyu.

 

Da gudu Nusaiba ta ƙaraso tana faɗin, “Wanene wannan, bawan Allah lafiya?” Tayi maganar tana yi masa kallon sani, amma ta manta a ina ta san shi.

 

Wani mugun kallo ya yi mata ya ce “Wane irin shirme ne zaki tafi ki bar mara lafiya ita kaɗai, wace irin jinya ce haka?”

 

Gaba ɗaya ruɗewa nusaiba ta yi, ba ta san waye ba, amma kwarjinin sa ya razanata, ta ce “Likita ne ya ce a bani jininta na kai gwaji yana buƙatar result yanzu, ammi kuma ta riga ta tafi gida ta je ta huta, shine na je lap ɗin asibiti, suka ce ba sa yi, shi ne na fita waje, da takawa nake jira ya zo ya kai, likita ya ce lallai yanzu yake so”

 

Tsaki yayi, ya kalli iman ya ce “Ke kuma cikani” wata irin kunya ce ta kamata, dan ba ta san ta riƙe shi haka ba.

Ta sakar masa riga, ta karɓi ruwan ta fara sha.

 

“Ita kuma wannan ma shiririciyar ko ina ta tafi oho mata”.

 

Rumaisa kuwa lungu da saƙo na asibitin take ta bi, har ta gaji ta kama hanyar komawa ɗakin, kawai ta hango motar takawa, yayi parking ya fito daga motar, hannunsa riƙe da leda.

 

Aikuwa ta nufe shi, babu tsammani ya ganta a gabansa.

 

“Dama kai ne a wurin Anty Iman? Haka ake jinyar mutum dama, ka yi tafiyarka ka barta? Kai idan aka yi maka haka zaka ji daɗi ne?”

 

Sororo yake bin ta da kallo, yadda take yi masa haƙilon masifa kamar babarsa.

 

“Ya ina magana kana kallona, sai wani abun ya sameta? Kawai ka ɗau mota ka tafi yawonka, ka bar mara lafiya ita kaɗai? To wallahi sai na gaya wa ammi” banza yayi mata, ya nufi cikin asibitin, rumaisa kuma ta bishi tana cigaba da mita.

 

Cike da shiga taitayi, Nusaiba ta bawa mai sunan baba haƙuri, ita dai ba ta san waye ba, amma ta tsinci kanta da shakkarsa.

 

Ta kalli iman ta ce “Iman, me zan baki ki ci to, tun jiya baki ci komai ba, an ce lallai ki samu ki ci wani abun, ga abinci ga fruit wanne zaki ci?”

 

Iman ta girgiza kai ta ce “Na ƙoshi, bana son cin komai” mai sunan baba a ransa yake jinjina halin mata, su a rayuwarsu ta duniya komai sai an lallaɓasu? Abincin ne ba zata ci ba, sai an yi ta rarrashinta, alhalin ta san kanta zata cuta idan ba ta ci ba.

 

Takawa ne yayi sallama, ya shigo hankalinsa a kan iman, ya ƙarasa gaban gadon ta.

 

Nusaiba ta ce “Maman sabir, yaushe ki ka zo?”

 

“Tun ɗazu muka zo ni da mai sunan baba, ashe wannan ne yake jinyarta, ya tafi ya barta ita kaɗai” tayi maganar tana nuna Adam.

 

Nusaiba ta ce “Eyya, ni ce tare da ita, jininta na tafi kai wa a gwada, ba yadda zan yi ne shiyasa na tafi na bar ta”.

 

Rumaisa ta ce “Au na zata shi ne ai”.

 

Ta ƙarasa ta leƙa fuskar iman ta ce “Anty Iman ya jiki?”.

 

Cikin ƙarfin hali ta ce “Da sauƙi Alhamdilillah “.

 

Adam ma lallaɓata yake yi, ko za ta ci wani abun, amma ta ce ita ba ta cin komai, ya din ga rarrashin ta, ta ce tuffa take so, takawa ya tashi ya ce bari ya je ya duba, ya sayo mata.

Daga mai sunan baba har Adam babu wanda ya kula wani, takawa na tafiya, iman ta fara ƙoƙarin kwanciya, mai sunan baba ya kalli Nusaiba ya ce “Ke, zuba mata abincin nan” gaba ɗaya suka tsaya suna kallonsa.

 

Rumaisa ta jinjinawa Nusaiba kai, dan ba ruwansa da baƙunta yanzu sai ya balebalesu da masifa.

 

Romon kifi ne da dankalin turawa, sai ƙamshi yake yi, idon iman ya cika da hawaye, dan ko ƙamshin abinci ba ta so, ya karɓa ya je gaban iman ya ajiye shi, ya tsaya mata ƙiƙam a ka, ba tare da ya furta komai ba, ta kama cokali, ta fara cin abincin nan, jikinta yana rawa, saboda tsoro da fargaba, ga wata irin Muguwar kunya, dan ba ta saba cin abinci a gaban maza ba, ko a taron mata ba iya ci take ba.

 

Sai da ta ci sosai sannan cikin faɗa  ya ce “Kuna sane kuke wahalar da iyayenku, dan kun ga suna ta taku. Ke kuma tashi mu tafi” yayi maganar yana kallon rumaisa.

 

Ta tashi, kamar ta tuntsire da dariya, daga Nusaiban har iman ɗin kamar ka ce kyet su zura da gudu, saboda tsoro.

 

Ruma ta ce “Anty iman, Allah ya ƙara afuwa”.

 

Cikin sanyin jiki ta ce “Amin maman sabir na gode”.

 

Bayan tafiyarsu Nusaiba ta ce “Ke iman, wannan jarabbaben mutumin fa?”

 

“Yayan rumaisa ne” ta bata amsa.

 

“Kam bala’i, yau na ga wanda ya taka takawa iya tsare gida, daga zuwa ya hau ni da masifa”

 

Iman ta sunkuyar da kai ta ce “Mhmm, baki ga komai ba”

 

Babu daɗewa takawa ya dawo da tuffa, Nusaiba ta bashi labarin abun da ya faru, bai ce komai ba yayi shiru, dan shi kansa jin kan mai sunan baba yana bashi mamaki.

 

***

Iman jikinta yayi sauƙi, mama ma ta je asibitin ta dubata, ta warware, sai dai lokaci lokaci, kan ya kan matsa mata da ciwo, aka sallameta daga asibiti. Sai dai tun da ta koma gida, washegari ta sake tashi da ciwon kan, sai dai ta yi ƙoƙari ta jure, saboda ba ta san sanya ammi a damuwa.

A ranar da aka sallameta daga asibiti ranar Jabir ya dira Nigeria, daga wurin duba mahaifinsa.

Hajiya Lubabatu ta yi mamakin ganinsa ya dawo, dan sun yi da shi zai yi sati uku a can kan ya dawo.

 

“Wai kai Jabir, menene ya dawo da kai tun a yanzu?”

 

“Bakomai, ji na yi an ce iman babu lafiya, shiyasa na dawo ita ma na dubata”.

 

Cikin rashin fahimta ta ce “Wace Iman ɗin, kai a wa? Meye haɗinka da ita?”

 

“Bakomai zumunci kawai”.

 

“Ban gane zumunci ba? Jabir kar na zo na ji wata magana saɓanin wadda nake son ji, ka san halina dai ban da kyau”

 

“Babu wata magana da zaki ji, kawai dai ina yi ne saboda Adam” tsaki tayi, ta shiga wata sabgar daban ta ƙyaleshi.

 

***

Yau tun da safe ammi ta kira mama, ta sanar mata da Adam zai zo wurin rumaisa, domin idan da wani abu da take buƙata ta gaya masa na game da shirin biki.

Amma mama ta ce “A’a hajiya, a ƙyaleta kawai, duk abun da aka yi Allah ya amfana”

Ammi ta ce “Ai da ni da ke, babu ruwanmu, namu ido abu ne na ma’aurata, dan haka yakamata su din ga tattaunawa domin su fahimci junansu!.

 

READ ƘANWAR MAZA PAGE 55 HERE


Proceed with your download by clicking the below button

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button