Ɗalibar mai suna Binta Isa, tana matakin aji na 400 a Tsangayar Ilimi ta Jami’ar Bayero Kano, Allah ya yi mata rasuwa a dakin kwanan ta da ke jami’ar.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, daga mataimakin magatakardar hulda da jama’a na Jami’ar, Lamara Garba, ya tabbatar da cewa dalibar wanda ta fito daga jihar Kogi, ta gamu da ajalinsa ne da misalin karfe 7 na daren ranar Juma’a bayan ta yi korafin ciwon kirji.
Sanarwar ta ce, “Daraktan kula da lafiya na Jami’ar, ta ce marigayiya Binta Isa ta taba ziyartar asibitin New Campus a ranar Laraba, 24 ga watan Nuwamba, 2021 kuma ta koka da ciwon kirji inda aka gano ta tare da bata wasu magunguna.
“Daraktan ya kuma bayyana cewa marigayiyar ta samu sauƙi inda ta ci gaba da halartar laccocinta a ranakun Alhamis da Juma’a, da kuma sauran ayyukan da ta saba yi.
Read Also: Jarumar Shirin Labarina Ta Auri Tsohon dan wasan ƙwallon ƙafar Nigeriya.
Wata budurwa ta haihuwa a sansanin horar da yan bautar ƙasa.
“A ranar Juma’a, 26 ga Nuwamba, 2021 da yamma wajen sallar magriba, alamunta sun sake dawowa, kuma ta yi korafin ciwon kirji ga abokan zamanta, amma ta samu ta yi alwala ta yi sallar magriba a daki.”
“Duk da haka, abokan zamanta sun yi mamaki da suka dawo suka tarar da ita a kwance babu rai a tare da ita. Nan take suka buga kararrawa wadda nan take aka garzaya da ita asibitin koyarwa na Aminu Kano inda likitoci suka tabbatar da rasuwarta.
“Mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Sagir Adamu Abbas, tare da magatakardar jami’ar, Malam Jamil Ahmad Salim, daraktan kula da lafiya na jami’ar, Dakta Gezawa, da kuma daraktan tsaro, Abdulkadir Ibrahim duk sun halarci wurin domin tabbatar da faruwar lamarin.
“Kamar yadda al’adar ta ke, hukumar jami’ar ta tuntubi dan uwan marigayin wanda ke zaune a Kano halin da ake ciki.”
Wato Farfesa Abbas ya kuma nuna alhininsa game da rasuwarta tun ta, ya kuma mika sakon ta’aziyya ga iyayenta da ‘yan uwa da abokan aikinta. Ya roki Allah ya gafarta mata kurakuranta, ya kuma sa Aljannar Firdausi ce makomarta.