Fentin Zina Page 39 Hausa Novel
PAGE 39.* Nuna shi tayi da yatsa tace bana fada maka abunda ke raina ba? Bana fada maka ka nisance ni ba? Meyasa ka nemi aure na ba tare da amincewata ba? Meyasa? A tsammaninka banida gata ne komai zaka mun, toh lallai kayi kuskure na fada cewar bana bukar sake ganin ka a rayuwata amma ka ki me kake bukata daga gareni ne?.Tana kokarin sake magana ta hadiye sakamakon ganin shi data yi duke kan gwiwowinsa idanunsa cike da hawaye baki na rawa ya soma magana.Ki gafarce ni kada ki yanke mun wannan hukuncin ina sonki! Ina matukar kaunar ki idan kika ki amince mun ban san wani hali zan fada ba,,,, ya karashe da hade hannayensa duka biyu alamar roko ya lumshe idon shi wanda hakan ya baiwa hawayen dake makale damar sauka har zuwa saman kumatun shi.Takawa tayi zuwa inda kujerar kekenta yake ta zauna cike da tarin tunanuka cikin ranta, tabbas tana son shi amma a halin yanzu bazata iya mika yardarta fgare shi ba don tabon da maza sukayi mata a rayuwa ba mai saurin goguwa bane.Ajiyar zuciya ta sauke mai karfi wanda sautinsa ya bayyana ta dago idonta ta sanya a cikin nashi daya kure ta dasu kamar zai hadiyeta tace cikin sanyin murya.Hakika ka kai na mijin da ko wacce zata yi fatan samu duba da irin kyawawan dabi’un ka, bazan kasance mai butulci wa ni’imar ubangiji ba ta hanyar kin amincewa da auren ka, don ban san kuma wani tanadi ya mun ba, saboda haka nike so in sanar da kai na amince ka zama mijina.Kafin ta kaiga karasawa ya daga hannayen sama yana godiya ga Allah.Kada kayi gaggawar godiya domin auren ne kadai na amince dashi amma bazan iya mika maka linzamin rayuwata ba, ba kuma na so ka tambayeni dalili ina dai fatan zaka yi mun wannan alfarmar.Mikewa yayi tsaye daga tsugunen da yake ya tako har zuwa gabanta ya harde hannu wanda yake dabi’ar shi yace,.Ni Ammar nayi alkawarin kulawa dake tamkar sarauniya a fadarta, na kuma yi alkawarin mantar dake dafin da aka shayar dake ta hanyar tarairaya da rarrashi, zan kuma kasance mai faranta miki har zuwa inda Allah ya nufi karshen numfashi na, bance ki yarda dani yanzu ba amma nasan lokaci ne zaiyi aiki akan komai, iya aurena da kika amincewa ni wannan kadai ma ya isheni farin ciki.Murmushin gefen baki tayi tace Allah ya zaba mana abunda yafi zama alkhairi.Ameen yace ya shiga karanto mata kalaman soyayya daga karshe da yaga magrib ta kusa sai ya mata sallama cike da kewarta bayan ya karbi numberta ya wuce gida kai tsaye.Dakinshi ya wuce ya dauro alwala ya fito ya nufi masallaci.Bayan isha ya dawo gida a falo ya tadda ammy zaune tana kallon tashar sunnah TV yaje ya zauna kusa da ita yace ammy barka da gida.Dan kallon shi tayi ta fahimci fuskar shi cike take da annuri ta gyada kai gami da cewa yawwa sannu dai, na dawo na tarar baka nan ina kaje? Ta jefa mai tambaya.Sosa keya yayi: uhm ammy naje unguwa ne, ya fada yana sunne kai kamar mara gaskiya.Bata ja zancen ba ta kamo wata gabar tana kallon shi tace, yanzu da hutunka ya kare zaman me zakayi a gida ya kamata ka koma wajen aikin ka kasan bana son wasa a harkar nema kada ya zama don kaine mai kamfanin kaci karenka babu babbaka hakan zai baiwa ma’aikatanka damar yin yadda suke so.Ai dayake nayi magana dasu dazun kuma na gamsar dasu da bayanai na dora manaja na ya kula da komai kafin in koma nasa kuma insha Allahu komai zai gudana tamkar ina nan.Tabe baki Dr. Amina tayi tace Allah yasa.Ameen ya amsa da.****Shirye-shiryen biki ake tayi ta ko wani bangare, ango Ammar farin ciki fal a zuciyar shi idan ya tuna gobe ne fa! gobe ne daurin auren shi da sahibar sa, cikin ‘yan kwanakin nan ba karamin shakuwa bace da soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsu, gefe daya yana son shureim kamar dai shi ya haife shi hakan yasa yace lallai da zarar sun gama cin amarcin su shureim ya dawo hannun su,, bata tsammata ba ai kuwa tayi matukar jin dadi sosai ta shiga mishi godiya har saida yanuna mata fushin sa a cewar sa ai shima ubane a wurin shureim. Sai dai abu daya daure masa kai na yadda yake ganin kamannin shureim da Ahmad saidai bai kawo komai a rai ba kuma bai tambaya ba yabarshi a matsayin kamace kawai da ake iya samunta a ko ina..Zaune suke a cikin shagonta da aka shigar da keken dinkin cikin gida saboda mazan da zasu zo daurin aure su samu su zauna.Ji nake kamar na matso da gobe tayi gaggawar riskata domin na kosa ki zamto matata.Cewar Ammar yana kallon cikin idanunta cike da shauki.Kashe masa ido daya tayi shi kuwa ya lumshe ido ya bude su a kanta yana sakin ajiyar zuciya ya kuma cewa, anya soyayyarki bazata iya ajalina ba kuwa? Lallai ina sonki da yawa Ameenerh ina matukar kaunar ki, dan Allah ki daure ki mun koda rabin son da nike miki ne wallahi baza kiyi nadama ba.Hawaye ne suka soma sintiri a kumatunta, hankalinshi ya tashi ainun ya tashi daga zaunen ya durkusa kan kafafun sa yana cewa cikin tashin hankali mai girma,Ki gafarceni idan na fadi ba daidai ba wallahi banyi nufin in bata miki rai ba ina mai rokon afuwar ki.Ganin yadda hankalin shi ya tashine yasa tasa gefen hijabin ta ta goge fuskar ta kana ta dago ta dubeshi tace.Baka mun komai ba Abu-shureim sunan data rada masa kenan.Hankalina ne ya kasa kwanciya da son kasantuwar mu ma’aurata, sai nake ganin kamar ban maka adalci ba, kyauwun halayen ka baka cancanci auren mace kamata ba da har kake furta irin kalaman nan a gareni, hakika nayi nadamar abubuwan dana aikata abaya nasan su suke bibiyata, ta karasa tare da kuma fashewa da wani sabon kukan.Baice mata komai ba bai rarrashe taba yasan abun akwai ciwo dole ya dinga sosa mata rai dukda baiji ainahin labarin daga bakinta ba amma ‘yan gulma da tsegumi na unguwar su sun sanar masa komai harma da karin gishiri.Don kanta ta gaji tayi shiru ya mika mata handky wannan karon mai launin shudi bata musa ba ta karba ta hau share hawayen ta.Ki daina saka wani damuwa cikin rayuwar ki game da ni, idan kikayi hakan nema zai zama baki mun adalcin ba, Allah ne shaidata akan soyayyar da nake miki sannan nayi alkawarin sanya ki farin cikin da bashi da misali a gidana, bawai ina yabon kaina bane don kiji dadi a’a kawai ina fada miki asalina domin hankalin ki ya kwanta dan Allah ki mun wata alfarma. Ya fada yana kallonta, itama dagowa tayi tana kallon shi, yacigaba da cewa, ki mun alfarma kada ki sake saka damuwa a ranki domin hakan na kuntata ni kuma zai illata zuciyata kinjiii ya langwabe kai irin na sangaltattun yaran nan yana kashe mata ido.Dariyace ta subuce mata harda kyakyatawa, shiko ya samu abun kallo sai yaga ta fi yi masa kyau fiyeda ko wace rana daya ganta.Tayata yayi da dariyar ba tare da sanin mema take wa dariyar ba.Ita ma ganin yana dariyar ta dakata da nata tace ya naga kana dariya kasan me nakewa dariyar ne? Ta tambaya fuska a sake.Girgiza kai yayi yace bazan tambaya ba kuma bance ki fada mun ba ni dai idan zaki cigaba da dariya ahaka ina so.Allah Ko? Ta tambaya.Kwarai kuwa zan zauna inyi ta kallon ki bazan gaji ba.Kace lallai dai kana da aiki.Babba ma kuwa, shima ya bata amsa.****Rana bata karya saidai uwar diya taji kunya, a yau aka daura auren Ameena Ibraheem tare da angonta Ammar Abdulkadeer sai kuma fateema Ibraheem tare da angonta Anas Adam.Daurin auren daya samu halarta daga mabambamta mutane daga wurare dabam dabam.Abdul ma dakyar ya lallashi zuciyar shi ya halarci daurin auren nata dukda zafin da zuciyar tashi take masa kamar bazai kai labari ba, sai kuma ya sake tarar da wani sabon abu dangane da auren aminin shi da kanwar tsohuwar matar shi, hakan ya matukar jijjigashi sai ciwon kirji ya soma taso masa kadan kadan Allah ya taimake shi ya taho ne tare da abokin shi sai ya kamashi yasa shi a mota ya tuka suka soma tafiya.Kaini asibiti ina da bukatar inga likita. Ya fadi hakan ne cikin nishi saboda ciwon dake nukurkusar shi.Abokin nashi ya kalle shi cike da tausayin shi ya karya kan motar ya dauki hanyar zuwa asibiti, ko kafin su isa harya galabaita sosai don haka emergency aka kaishi aka soma bashi taimakon gaggawa don son dawo da numfashin sa daidai.An dan dau dogon lokaci a cikin dakin emergency room din, zuwa lokacin kuma ya kira gidan su Abdul din ya fada musu.A gigice babu bata lokaci mama da kannen Abdul din guda biyu suka karaso asibitin daidai ana fito da Abdul daga emergency za’a kaishi male ward amenity.Bin nurses din sukeyi har zuwa cikin dakin.Nurse Daya ce ta juyo bayan sun gama gyara shi tace kada ku yawaita surutu saboda yanayin jikin nashi.Mama ce ta amsa mata da cewar kada ki damu baza mu dame shiba don muma mun fi damuwa da halin da yake ciki.Nurse din tace Allah ya bashi lafiya.Ameen dukka suka amsa nurses din suka yi waje su kuma kowa ya samu guri ya zauna sai abokin Abdul din ne yace mama ni barin je gida in dawo Allah ya sawwaka masa.Ameen Allah ya maka albarka.Ameen yace tare da barin cikin dakin.Nan suka ci gaba da zama shuru har yamma ya farka da salati yana fadin Ameena ki yafe mun na tuba Anas dan Allah ka yafe mun wallahi sharrin shaidan ne, haka yayi ta maimaitawa kafin zuwa can ya fahimci a inda yake sai yayi shiru.Mamace ta matso kusa dashi tana kallon yadda fuskar shi ta rame kamar ya dade yana ciwo, idanunsa dake lumshe ya bude ya sauke su akan ta.Sannu Abdul meke damun ka yanzu?Dan yamutsa fuska yayi yace kaina ne ya danyi nauyi kadan sai kuma kirjina nike ji kamar an daura mun dutse.Sannu kaji, Allah ya baka lafiya.Kannen shi suka gaishe shi ya amsa, likita ya shigo ya duba shi ya masa abubuwan da suka kamata sannan yayi masa tambayoyi yana amsawa daya gama yayi rubutu a dan karamin paper ya mikawa mama yace a siyo wannan maganin yasha zai dan samu saukin abunda yake ji, amma fa ya kula Kada a rika bari yana shiga halin bacin rai ko tunani.Toh likita mun gode Allah ya saka da alkhairi zamu yi kokarin kiyayewa sai dai ina son sanin meke damun shi.Kallon ‘yan dakiku likitan ya mata kafin yace ke waye a gurin shi?Likita ni mahaifiyar sa ce.Jinjina kai yayi yace ok fine danki yana fama da ciwon zuciya da alama bai jima sosai a jikin shi ba a halin yanzu dai zuciyarsa ta kumbura sakamakon sanya damuwa da tunani a ranshi.Innalillahi wa inna ilahi raji’un, na shiga uku nikam.Am mama Ko kwantar da hankalinki zai samu lafiya da izinin ubangiji kedai ki tabbatar ya dinga shan magungunan shi akan lokaci sannan ya kula da bin dokar da duk za’a saka masa.Zaiyi likita nidai fatana Allah ya baiwa dana lafiya.”””***”””Bangaren amare kuwa a daki aka kaisu domin yin sallama da iyayen su, sai kuka suke rizga tunba ma Ameena ba kamar wannan shine karonta na farko da zatayi aure.Haka aka gama musu nasihar su aka dauke su aka mika ko wacce gadakin mijin ta.Ammar washe baki kawai yake yi yayinda yake kokarin danna hancin motarsa zuwa cikin gida yasan yanzu amaryar shi tana nan tana jiran shi, rurin wayar shi ce tasa ya taka birki ya daga yana fadin.Ai ka bani mamaki ace auren babban abokin ka guda baka halarci daurin aure ba? Koma menene uzurinka ya kamata ka dakatar dashi na dan lokaci koda baza ka iya yin absent na yin Daya ba.Ta Cikin wayar yake cewa maida wukar ka mun afuwa tafiyar gaggawa ce ta kamani yasa ban samu daurin aure ba amma ai gani na dawo tare ma zamuyi siyan bakin amarya ka ganni nan a harabar gidan ku kai dai nike jira.Ammar tsabar haushin abokin shi ma kashe wayar yayi kawai ya tuka motar zuwa cikin gidan yayi parking a parking lot ya fito daidai Ahmad na karasowa inda yake.Sanin halin shi yasa Ahmad din ya soma cewa yi hakuri mana mutumin, nine naka fa kasan bazan yi hakan dagangan ba am very sorry kaga yau ba ranar bacin rai bane a garage ka kada amarya taga kamar ina yi mata bakin cikine yasa nasa ka fushi.Murmushi ne da yayita kokarin dannewa ya subuce masa yace shiyasa ka iya yaudaran ‘yan mata da wannan dadin bakin naka ai ko ‘yar gidan waye sai ta zurma.Um nidai muje in maka rakiya inzo in tafi gida akwai appointment.Girgiza kai Ammar yayi yace Allah ubangiji ya shiryar dakai.Ameen yace suka shiga falon dake ta wake banda na Cikin main falon mama, suna dariya…………. *TOH FA! GA AHMAD GA AMEENA KOYA ZATA KASANCE IDAN SUNGA JUNA???* *EESHERT ADAMU* *MATAR MAJEEDADI✍️*



