Uncategorized

Rayuwata ta gyaru bayan Adam Zango ya kore ni daga gidansa – Ummi Rahab

 A baya-bayan nan ne Ummi Rahab ta haifar da tashin hankali a Kannywood yayin da ta yi artabu da tsohon ubangidanta Adamu A. Zango a shafukan sada zumunta, inda har ta zarge shi da neman lahanta mata rayuwa.  A cewar Ummi Rahab, a lokacin da ta gano haka, Zango ya zo da wata shawara cewa yana son ya aure ta.  Ta bayyana hakan ne ga Jaridar Blue print a wannan hirar.

 To, me kika yi sa’ad da ya nemi aurenki?

 Na ƙi saboda na dade da sanin halinsa na auri saki.  Tun ina ƙarama, ya yi aure har sau shida, ni ma ina son in sami ‘yanci, in auri wanda nake so, kuma in yi rayuwa ta yadda nake so.  Ya zo da tsattsauran ra’ayi akan rayuwata da sanin cewa a matsayina na yar sa wadda ya raina dole na amince da kudirin sa. Ko da naƙi amincewa shi ne sai ya kore ni daga gidansa Sannana ya cireni daga cikin fim ɗinsa na Farin Wata Shakallo, amma zan iya gaya muku yau abin ya zama alheri a gare ni.

 To Ummi meye sirrin kyawunki?

 A lokacin da Adam Zango ya kore ni daga gidansa ya fitar da ni daga fim dinsa na Farin Wata Shakallo, mutane sun yi tunanin rayuwata za ta yi baƙi, amma na ci gaba da rayuwa ta yadda nake so, hakan ya zame min alheri. Yanzu haka Ina samun ƙarin gwiwa a kullum;  Ina shiga shirin mai suna WUFF, shirin talabijin wanda FKD, kamfani mallakin Ali Nuhu ke shiryawa.  Don haka, ina cikin babban fim.

         KARANTA WASU LABARAN

  Wasu hotunan Jaruma Rahama Sadau da suka bayyana Shatin farjinta

 Scholarship Ƙarƙashin Ma’aikatar Ilimi Ta Ƙasa Da Kuma Hukumar Samar Da Lamunin Karatu Ta Ƙasa. 

   Da Dumi-Dumi: Masu kutse sun sace NIN din yan Nigeria sama da miliyan Uku

 Yan Kannywood Sun fara yin Blue Fim

 Kwanan nan, an gan ki a shafukan sada zumunta da wayar salula da kudinta ya kai Naira miliyan 1.6 zuwa Naira miliyan uku.  Kuna da wadata sosai ne da har kika mallaki waya mai wannan tsadar haka?

 To, na ji abubuwa da yawa game da waccan wayar, amma ina alfahari da cewa, nan da nan aka ga irin wayar a hannun mutanen da suka zo auren Yusuf Buhari, ni ma na samu daga wajen wani abokina.

 Watakila da na fara wannan hira da tambayar in san wacece Ummi Rahab?

 To, an haife ni a Kaduna, daga baya muka koma Saudiyya tare da iyayena, amma na dawo Najeriya na kammala karatuna, duk da cewa ina shirin zuwa jami’a.  Lokacin da na zo Najeriya, ba da farko nake zama da Zango ba, amma ya dage cewa in zo in zauna tare da shi, saboda dan farin sa wato Haidar yana sona.  Na yarda da haka ya dauke ni kamar diya, har sai da ya samu ne da cewar yana so ya aure ni. Na ce masa ba zan iya aurensa ba saboda ina da saurayi kuma muna son juna sosai.  Mutumin mawaki ne, furodusa kuma daraktan fim;  Laƙabin sa shine Lilin Baba, amma ainihin sunansa Shu’iabu Ahmed Abbas.

 Zango ya fusata da haka sai ya yanke shawarar ya cire ni daga fim dinsa, ya ce ni ma in kwashe kaya a gidansa, na yi.  Amma ya zame min alheri domin a yau, na riga na shahara kuma ina da ayyuka da yawa suna tafe.  Ina fatan in auri Lilin Baba idan al’amura sun daidaita, amma gaba daya, ina yin babban aiki kuma ni har yanzu yarinya ce ban wani girma ba, badakalar kafofin watsa labarun kuwa wannan mun riga mun saba da ita a rayuwarmu ta yau da kullum.

Back to top button