Uncategorized

Maciji Ne Page 93-94 The End Hausa Novel

Elegant online writers📚📚

Free book

Page 93/94

_______________Ko a cikin jirgi fattu na kusa da baffanta,wanda yayi tsuru cike da tsoron jirgin,dan kuwa wannan shine karon farko daya hau jirgi.amma haka fattu ke kwantar masa da hankali har suka ƙarasa Ghana.

Part guda aka warewa baffa wanda ke dauke da duk wani kayan more rayuwa.baffa ya cika da farin cikin ganin irin rayuwar jin dadin da fattunsa keyi.abinci kala kala aka ajiye masa,har yama rasa wanda zaici.haka fattu keta zuba masa abincin tana tura masa.

Saida ya huta sosai nutsuwarta ta dawo jikinsa, sannan aka taru apart din da aka saukeshi, har Sultan Habib.godiya suka farayiwa baffa,bisa irin taimakon da yayiwa rayuwar yarsu,sannan suka ce suna bukatar yayi zamansa anan gurinsu,tunda bashi da kowa acan Nigeria.

Kuka kawai baffa keyi na gani yadda bayin Allah nan ke karramashi, suna son ya kasance tare dasu,amma wadanda ya taso cikinsu,haka suka koreshi korar kare bayan sun karbe masa dukiya.

Fattu ce ta dan turo baki tana kallon innarta da mahaifinta,kafin tace “Ni gaskiya ban yarda baffana ya zauna anan ba,tare zamu tafi dashi can gida,bana son yayi nesa dani,kuma shima yafi son zama kusa da fattunsa ko baffa”fattu ta faɗa cikin salon shagwabarta.

Murmushi baffa yayi,yace kwarai kuwa fattun baffa,duk inda kike to Nima Ina can koda kuwa cikin dokar dajine”baffa ya faɗa cikin murmushi.

Dariya sukayi suma,kafin mahaifin fattu yace “wato dai zara kin kwace mana baffanki ko?”ya faɗa da murmushi akan fuskarsa.

Dariya fattu tayi kafin tace “Allah ba haka bane daddy nayi kewar baffana,kuma nima inason in kula dashi,kamar yadda ya kula da rayuwata abaya”

Jinjina kai sukayi gaba ɗaya,suna ayyana irin kaunar dake tsakanin fattu da baffanta.

Kafin su bar kasar Ghana saida mahaifin fattu ya mallaka wa baffa kanfaninsa na ƙera takalma da jakunkuna,ya maida sunan sa akan  takardun kamfanin,sannan ya bashi gida,wanda idan yazo zai rinka sauka aciki sannan ya damkawa fattu takardun gida dana kamfanin,harda mukullin sabuwar mota yar yayi.

Kuka sosai baffa yayi yana godiya,fattu ma tayi matukar murna sosai.adeeb kam godiya yayiwa Sultan habeeb,haka innar fattuma ba’a barta abaya ba,dinkuna ta sanya aka yiwa baffa,na gani na faɗa, masu kyau da tsada.sosai baffa ke yaba karamcin iyayen fattu,ba abinda zaice saidai Allah ya saka musu da aljanna.

Washe gari kuwa jirginsu ya daga zuwa Misra,fattu harda kukan rabuwa da yan uwanta,haka innarta ta cika ta da kayan gyara kala kala.

Wani ƙayataccen bangare su fattu suka sauka,wanda bayan tafiyarta Ghana ,Adeeb sanya aka kera musu.tsyawa fadar irin tsaruwar da bangaren yayi abune mai matukar wahala.kallo daya zakayiwa gurin kasan an kashe kudade makudai.

Baffama bangare guda aka ware masa inda zai zauna.haka yasha kyaututtukan gurin iyalan Adeeb,sannan shima Adeeb ya ba baffa kanfaninsa na motoci,baffa neman zaucewa yayi da irin wannan kyautukan da ake ta bashi.

Sosai ake girmama baffa cikin fadar,dan kowa yasan shidin waye.

Cikin lokaci kalilan baffa ya wanke yayi fes dashi,masha Allah kyakykyawan bafillatani,yayi kiba ya koma Alhaji sosai.ba jimawa suka shirya shida Adeeb da fattu dasu nanny sukaje suka sauke farali.

Sun dawo da kwana uku aka shirya gagarumin taron nadin Adeeb matsayin sarki.sannan ranar za’a gudanar da bikinsu shida fattu.

Anyi taro na ban mamaki wanda saida ya girgiza duniya,taron daya hada sarakunan hasashe daban daban,daga turawa,larabawa zuwa hausawa,ba kalar mutanen da babu agurin.

Taro yayi taro,an nada Adeeb matsayin sarkin misra,SULTAN ADEEB MUHAMMAD ASHRAF.

haka aka kammala taro ya tashi lafiya,kuma ranar Adeeb ya mallaka fattu dankareriyar mota mai shegen tsada da kyau,sannan ya mallaka mata kamfaninsa wanda ake hada mayukan shafawa na mata da kayan kwalliya.

Murna dai agurin fattu ba’a cewa komai.

Sati biyu da nada Adeeb matsayin Sarki,fattu ta kama laulayi, wayyo kuzo kuga murna gurin bayin Allah nan,haka nanny ta zage tana kula da fattu,ita da amma,suna bata gata da kulawa sosai,haka uban gayya,dan har kuka yayi lokacin da labarin cikin fattu ya sameshi.kuma yayi mata alƙawarin idan ta haihu ta zabi inda take son zuwa yin karatu.

Cikin fattu nada wata biyar aka yi auren tareeƙ da wata yar uwarsa,rana daya aka daura auren dana Rashad,anyi biki na kece raini,su fattu sune akan komai na biki, zakuyi mamaki yadda fattu ta zama babbar mace,tayi mugun kyau har ta gaji,suna nunawa juna soyayya mai tsafta ita da Adeeb,yayin da suke rainon cikinsu cike da so da kauna.saidai fattu tana da girman ciki,dan yanzu haka inka ganta zaki tunanin cikin yakai wajen watanni bakwai, dan girmansa. 

Komai yana tafiya daidai arayuwarsu fattu,basu da wata matsala yanzu,domin suna cikin aminci da kulawar yan uwa,sarauniya suhaimat da Sultan habeeb,sunyi matukar murna da samun cikin fattu,addu’oi kuwa,ba  irin wanda fattu bata samu,domin takanas ake biyawamutane makka,dan suke suyi mata addu’a.

Lokacin da cikin fattu ya cika wata tara,ko tashi bata iyayi da kanta,saidai idan Adeeb ya tasheta idan tana zaune ko kwance,amma kasancewarta mai hakuri da kawaici,haka take daurewa tana nuna bata jin wahalar ciki,shikuwa Adeeb tausaya mata yake sosai.

Wata rana da safe suna barci nakuda ta kama fattu,aikuwa,nan da nan likitoci kwarraru,wadanda ke mata awo suka rufu akanta,cikin hikimar ubangiji,fattu ta haifi yaranta takwaye, mace dana miji masu matuƙar kama da Adeeb, kyakykyawa na ban mamaki.

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Ki

Irin murnar da ahalin nan suka nuna abin ba’a cewa komai,ta ko ina zuwa ake ganin jarirai,ranar suna aka sanya musu  sunan baffa dana Nazli,Abubakar,amma ana kiransu da Ameer da ameera.

Fattu ta sami alkairi sosai haihuwar yaran nan.dan motoci ma sun sami sama da guda sha biyar,banda gidaje da tsabar kudi.sai muce Allah ya  raya twince.

Bayan suna da sati biyu aka daura auren baffa da nanny,bisa ga amincewarsu,bayan fattu tayi shawara dasu,ba nuna ja suka amince,dan dama sun kamu  da son juna.

Ammi kullum abu sai kara lalacewa yake,hauka take tun ƙarfi,gaba ɗaya ta gama kwarzane jikinta,tananan kamar wata horuwa, tayi ta ihu tana yakushun jikinta.(ai dama ammi hausawa sunce idan zaka gina ramin mugunta ka gina daidai da kai,hakkin rayukan da kika kashema kadai sun isheki)

Waziri ma yana gidan yari,saidai shikam yayi ladama,ya koma ga Allah,kullum yana istugfari.

Yaran fattu sun taso cikin kulawa da soyayya,idan kun gansu gurin fattu,to nono kawai zata basu,dan tuni ta fara karatunta ,tace anan gida zatayi karatu,bazata je ko ina ta bar mijinta ba.

Abin sai son barka,rayuwa tayi musu daɗi,suna zaune cikin kwanciyar hankali,fattu ta buɗe gidajen marayu ajahohin Nigeria sosai,ta taimakawa yan kauyen su,tayi musu makaranta, ga ruwa ya wadata,ta tallafawa mabukata, gaba ɗaya sunyi nadama abinda suka yiwa fattu da baffanta,dan lokacin da baffa yaje basu ganeshi ba,haka gwogwgo hansai tayi ta kuwa wai ya maidata  dakinta,dariya kawai yayi tare da bata makudan kudade kafin ya bar kasar.

Amare da angwanye ma suna zaune cikin aminck da soyayya,yayinda ko waccensu ke dauke da yaron ciki,saidai muce Allah ya raba lafiya.

Fattu ce zaune akan kujera tana bawa ameer nono,yayinda Adeeb ke gefenta riƙe da ameera,kallonta yeke cike da ƙauna da sha’awa,yadda take shayar da yaron cikin nutsuwa.

Ajiyar zuciya yayi tare da faɗin “Alhamdullah ,Allah na gode maka kacikani da ni’imarka ta ko ina ,ka bani mace mai hankali da nutsuwa,sannan ka hadamin kan ahalina,ka bani yara kyakykyawa har biyu a lokaci daya,Allah Nagode maka”Adeeb ya faɗa cike da kushu’i yana  mai jin dadi cikin ransa.

Murmushi fattu tayi tare da kamo hannunsa tayi kissing, sannan ta Dora kanta akan kafadunsa, tace “Ina sonka mijina kaine farin cikina,kuma rayuwata,Allah ya raya mana yaranmu bisa hanya madaidaiciya”

“Ameen Hulwa ana ahubbikteeer Hulwa anti sururi”ya faɗa yana mai kara rungumeta ita da yaran ajikinsa.

Tammat bi hamdillah.anan na kawo karshen wanna littafi Mai suna MACIJI NE.

 

Jinjina gareka mijina,na gode da gudunmawarka gareni,Allah ya bamu zaman lafiya,ya raya mana zuri’a.

Much love.

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Godiya ta musamman gareki,maman nafi,na gode sosai da gudun mawarki akan wannan littafi.

Gaisuwa gareku macijine fans inq kaunarku.

Jinjina ga elegant online writers,Allah ya hade kanmu.

Ina godiya gareku yan uwana,da addu’ar ku gareni 🫠🫠🫠

Allah ya sa mu amfana da darasin dake cikinsa,muyi watsi da sharrin dake cikinsa.

Allah ka yafe mana kuraruranmu,kasanya imaninmu ya nunku fiye da nada.

Godiya agareku masoyansa ,da kukayi ta bibiyar wannan littafi,tun daga farko har karshe,Allah ya hadamu gidan aljanna.

Sai mun haɗe daku cikin sabon littafina

RAINON DAWA.

Ga mai bukata,zai fita kudinsa kamar haka.

Normal group 300₦

Special group 500₦

Manyan mata masu bukata ta private,kuma ga naku1000₦

Zaku biya ta wannan acc. Din.

Saratu Kabir

U.b.a

2215749011.

Evidence of payment

08148360851

Saina jiku masoya.

Show me You love,

Kuyi payment na wannan littafin.💘💘💘

Kada kusake baku labari.

Saina jikiku.

Takuce har kullum anty mammy.

Mrs babi💘💘

Back to top button