Uncategorized

Yan Mata Masu ziyartan dakin samari bayan Sallah ga darasi Mai tsoratarwa

kwanaki 2 bayan sallah wata yarinya ta kirani tana kuka take sanar dani cewa akwai wani abokin saurayinta ya dauki hotunansu ita da saurayinta acikin wani irin yanayi na soyayya ba tare da sun sani ba.

Yana yi mata barazana dashi sabida haka tana bukatar taimako na.

Da naji batun babba ne,  kuma ni ban gane da waye nake waya ba sai na ce mata wannan ba batun da za’ayi a waya bane.

Tana kuka tace na fada mata inda nake kawai ita zatazo, na sanar da ita, Jim kadan sai gata nan tazo acikin adaidai ta sahu,  abin mamaki yarinya ce karama wacce duk bata wuce 20 years ba,  ganin tazo na tashi a inda nake muka ja gefe tana kuka yayin da take bani labari.

Wai tayi ma saurayinta abincin sallah ne, sai yace takai musu dakin abokinsa acan ne zasuci abincin.

Bayan taje daukan kwanukanta nanne saurayin nata ya rinjayeta har shedan ya shiga tsakaninsu.  sai da dare abokin saurayin ta din ya kira ta yace taje ta sameshi a dakinsa, da taki zuwa sai yace ta duba watsapp dinta tana shiga taga  bidiyonsu da hotuna ita da saurayinta acikin yanayi da bai dace ayi hoto ba.

Cikin takaici na kalleta na rasa ma ni ta ina zan fara, ina shi saurayin ki din? 

Na tambayeta ta ce min shi ta fara gayawa da farko ya nuna kamar ya damu daga baya kuma kota kira wayansa ma baya dauka, daga karshe ma wayar ya kashe.

Na danyi shiru sannan nace toh ni tayaya zan iya taimaka miki acikin wannan lamarin,  kema ba wani sabawa mukayi dake ba balle samarin ki, taya zan iya hanasu sake wannan bidiyon domin na tabbatar da hadin bakin shi saurayin ki din aciki.

Tace wai taji ance ana iya goge abinda yake cikin wayar mutum ba tare da yasani ba kuma ance mata nine kawai zan iya wai dan Allah in taimaketa, aurenta ya kusa kuma idan suka sake bidiyon  zai iya lalata komai.

Sai na kara fahimtar cewa akwai laifinta kaso 70% aciki, wanda take soyayya dashi daban wanda kuma zata aura daban.

Related Articles

Saura kadan na koreta wlh sabida haushin da ta bani, da na tuna zasu iya amfani da hoton su rinka juyata sai ta bani tausayi.

Na karbi lambarsu, sannan nace taje.

Bayan ta tafi na dauki lambar abokin saurayin ta din na kira shi,  yana shiga kai tsaye ya kama sunana, bansani ba ashe yana da lamba na yana kawomin aiki wani lokaci,  muna gaisawa yace min yaje wajen aiki na akace na tafi makaranta, nace masa eh ya fadamin inda yake inason yin magana dashi, yasanar dani naje na sameshi.

Bayan mun gaisa nace masa akwai wani abinda ake cikawa ya bani wayarsa bari na saka mishi aciki,  babu musu yabani sabida alokacin suna tare da wasu suna hira.

Na karba nakoma gefe na bude gallery na bincika banga komai ba, sai nakoma duba irin apps din da yake aiki dasu,  sai naga akwai Vaults apps, wato app din da zaka iya 6oye abu batare da wani ya gani ba acikin wayarka,  nayi yunkurin budewa sai naga akwai security,  hakan ya tabbatarmin da cewa acikin nan hotunan suke, nan take natura app din awaya na,  sannan nagoge na cikin wayarsa,  nasake turawa acikin wayarsa dana budeta kai tsaye saita koma sabo nashiga ciki, nan naci karo da hotuna da video daban-daban ba ma iya na wannan yarinyar ne kadai ba, akwai na ‘yan mata dayawa wanda dashi kanshi acikin hotunan ya dauka, nan take na duba nashi akalla guda 5 nayi marking nasu na turasu a waya na.

Sai na mika masa wayarsa, yacemin menene kasaka min sai na rasa amsar da zan bashi,  nan take wani tunani yazomin zai iya kasancewa akwai wani wajen adana abu bayan app din dana goge.

Sai nace bani na nuna ma daya bani kai tsaye nashiga email nashi na bincika banga komai ba,  sai na kara shiga Drive,  abin da ya rikitar dani hotunan da Bidiyon da na samu a drive ya ninka wadanda na goge, suma kab na gogesu. Sai na mika masa wayar nace masa ina zuwa yana kirana, kawai nayi banza dashi na tare adaidaita sahu nashiga na tafi.

Bayan na sauka na kira yarinyar nan na huce haushin da ta bani; ya za’ayi kina mace wacce aurenki ya kusa har ki yadda kiyi ma wani banza can abinci wanda bashi zaki aura ba harma ki kaimasa dakin abokinsa, wannan wanne irin rashin hankali ne?

Tacemin wai kuskure ne,  nace mata wannan yazama darasi awajenki, 90% na samari idan suka kai ‘yan mata dakinsu 6oye camera sukeyi su dauki duk abinda ya faru.

na sanar da ita naje na gogesu duka sai ta kiyaye gaba.

Tayi ta godiya.

shi kuma wancan gayen daga baya ya kirani yacemin yaga abinda nayi masa amma duk nayi abanza, kuma yanzu ne zai tabbatar mana da cewa zai sake bidiyonta.

Nace mai toh muje zuwa yanzu dani yake abin, ba ita ba.

Akwai hotunansa guda 5 dana tura awayana nan take na tura masa su ta whatsapp nace masa nima yanzu inada nashi, ko barazana ya kara yi mata nima sakesu zanyi,  kuma idan ya kara kirana da maganar banza nanma zaiga abinda zanyi.

Da haka fa mu ka samu wannan case din ya mutu ko yayi sauki zance.

Nayi wannan rubutun ne sabida ya zama darasi a wajen ‘yan mata masu karamin tunani da ake rudan da wasu ‘yan kalamai ayi wasa da mutuncinsu, idan kika tsare kanki ko kallon banza babu wanda zaiyi miki amma idan kika saki jikinki kowa kallon araha zai rika yi miki.

Allah ya tsaremu da alaka da mugayen mutane

Back to top button