Uncategorized

Shakuwa Ce Hausa Novel Complete

Bismillahi Rrahmani Rraheem

Gudu take kan faman sherawa cikin k’ungurumin dajin da baka jin komai sai kukan tsuntsaye. Haki ta tsaya tana yi sabida tsananin gajjiya da tayi,  sunkuyawar da zatayi sai ji tayi an d’auke ta da mari had’i da fizgo ta….  

Ja da baya ta soma hawaye masu zafi suna ci gaba da bin k’uncin ta kafin ta soma fad’in “Shema’u don Allah kar ki kashe ni,  kiji tausayi na, ki tuna I’m your only sister pls kar ki rabani da iyalai na… ” Ta k’arashe tana tsananin kuka. Wacce ta kira da Shema’u dariya ta tuntsire mata dashi kaman tab’ebb’iya kafin ta soma girgiza kai tana fad’in ” Aysha dole ki mutu,  and your family kar ki damu they’re in good hand,  nayi alk’awari babu abinda zai same su zan kula maki dasu fiye da yanda zakiyi,  kinyi kuskure Aysha tunda kika amince kika auri Man of my dream,  Aysha kin tab’a tambayar kanki me ya hanani aure all this while,  nasan baki damu kiyi ma kanki wann tambayar ba tunda burin ki ya cika kin auri mijin da kike so,  and you even gave him children bayan kinsan cewa ni na soma had’uwa dashi ni na fara sanin shi,  I should be the one in your place, ni ce ya kamata na kasance da AT not you Aysha…” Ta k’arashe tana mai fitar da hawaye tana murmushi tana girgiza kai tamkar tab’ebb’iya…. 

Aysha taci gaba da girgiza kai kurum hawaye na bin k’uncin ta don kuwa wannan wani Al’amari ne da bata tab’a zaton zai iya faruwa a gaske ba,  kai ko a film bata tab’a ji ba,  sai gashi yana faruwa akanta,  ‘yar uwa ke farautar rayuwar ‘yar uwa sabida namiji… Cikin rashin yarda da tunanin da zuciyar ta ke karanto mata ta shiga goge hawayen ta kafin ta soma fad’in ” Shema’u kar ki kashe ni pls you can have AT,  zan bar maki shi but pls don’t hurt me and my children..” Cikin tsananin kuka tana mai had’e hannayen ta waje guda alamun rok’o take maganar amma kaman cewa take Shema’u ta k’ara sautin dariyar ta… 

Ganin Shema’u tayi nisa cikin dariyar ta yasa Aysha soma ja da baya a hankali,  jini na ci gaba da bin k’afarta sakamakon k’aramin cikin dake jikin ta…. 

Kan tayi wani katab’us sai ji tayi Shema’u ta kuma finciko ta had’i da watsa mata mari mai ji da lafiya har guda biyu ta shak’e wuyar ta hawayen taurin rai na bin k’uncin ta take fad’in “You are so delusional Aysha da kikayi tunanin zan barki da rai, kin sace soyayyar kowa nawa daga gare ni,  Aysha you always stealing from me,  kowa ke yake so,  Aysha tun muna makaranta k’awaye sunfi sonki,  sanda Abbah yake da rai yafi sonki snn Momma tafi sonki,  you are always the good one, ni kuma ni ce maras jin magana ni ce wacce ba’a so, Koda Abbah ya zo da AT kai tsaye ke akace ya Aura despite the fact nice gaba dake,  nice ya kamata na soma aure ba ke ba Aysha… Why why Aysha meyasa kika sace komai daga gare ni.. “

Girgiza kai Aysha keyi hawaye na bin k’uncin ta,  ga azaban da marar ta ke mata tamkar zata mutu,  fuskar ta tayi jajazir sabida azaba. Cikin wani irin murya mai cike da azaba take fad’in ” Shema’u have mercy pls,  ki tausaya min ko don alhakin dake ciki na,  Shema’u kar ki hukunta wanda baida laifi….”

Dutsen gefen ta Shema’u ta jawo tayi saitin goshin Aysha dashi tana kuka shar shar da hawaye tana girgiza kai take kallon ‘yar uwan nata take fad’in..” Aysha ina sonki ina sonki sister but bani da zab’in da ya wuce na kashe ki, hakan ne kawai zai sa na mallaki duk abinda na rasa ta dalilin ki…”  ta k’arashe maganar had’i da kwad’a mata k’aton dutsen dake hannun ta akan ta… Wani k’ara Aysha ta saki lokaci guda Shema’u taci gaba da kwad’a mata dutsen nan jini na bin goshin Aysha,  babu d’and’anin imani haka Shema’u take hura hanci tana mai ci gaba da rabza wa Aysha dutsen nan da iyaka k’arfin ta…. 

Hisham dake tsaye gefe ya kafe su da idanu dariya ya fashe dashi kafin ya shiga tafe hannayen sa yana fad’in” What an interesting show,  you really are something Shemah,  gaskiya na jinjina maki yanzu kin nuna min zaki iya komai domin ki mallaki that damn Dr..  Wannan ya nuna min you don’t feel anything for me..” Ya k’arashe yana matso wa daf da ita…

Shema’u kuwa cike da firgici take duban Aysha tana kallon aika aikan da tayi,  ganin bata mosti bata numfashi yasata saurin sakin ta tana wani irin b’ari tamkar mazari. Cikin wani irin murya mai cike da firgici take duban Hisham tana zazzare idanu take fad’in ” Oh no no no,  na kashe ta,  I killed my sister,  Hisham na kashe ‘yar uwa ta…” Ta k’arashe tana waige waige tamkar wacce take tsoron kar a kama ta… 

Ganin she’s going out of control yasa Hisham saurin rik’o kafad’un ta kafin yace ” Kee.! Put yourself together,  don’t be such a daft,  ashe baki shirya ma aikin da kika yin ba,  barin fad’a maki,  what’s done has already been done,  gwara ma kisan yanda zakiyi ki k’arasa abinda kika riga kika soma.. ” Ya k’arashe yana wata kafiran dariya… 

Fincikewa Shemah tayi tana girgiza kai tana waige waige tana karkad’a masa yatsar ta manuniya take fad’in “Kar kayi tunanin tsame kan ka cikin mess d’in nan Hisham,  we are into this together,  wllhi if you dare think of betraying me,  I have my ways to get rid of you…. “

Dariya Hisham ya fashe dashi yana mai jinjina taurin zuciya irin na Shema’u kafin ya matso daf da ita ya rungumo ta cikin jikin sa duk da rawa da jikin ta keyi don har lokacin tsoro da firgicin abinda tayi basu bar jikin ta ba…  Saitin kunnen ta yake rad’a mata ” Idan kika taimake ni na mallaki abinda na jima ina farauta daga wajen AT kin gama min komai,  ina mai tabbatar maki your secret is safe with Dr Hisham….” Ya k’arashe yana wata irin dariya… 

Gyad’a masa kai Shema’u ta shiga yi, cikin rawar murya take fad’in  “You can count on me , wllhi wllhi zanyi komai ganin ka Mallaki _Sajmal Clinic_.”

Hisham ya kuma murmusawa kafin yace “Deal? ” da sauri ta gyad’a masa kai tace “Yeah deal”.

A rud’e ta kuma fad’in “Dr ka taimaka min yaya zanyi da ita?..” 

“Aw dama baki shirya ma abin ba kika soma yi?? Yaya kike aiki da ka ne babu lissafi Shema’u??. “

Gajeren tsaki ta d’an yi tana duban Aysha dake kwance lifeless a k’asa jini na faman kwarara a goshin ta da k’afafun ta kafin tace “Ko hak’a rami zamuyi mu tura ta ciki..? “

Hisham ya kuma tuntsurewa  da dariya kafin yace “Daga gani you’re very poor when it comes to mathematics,  anyway leave this to me,  I’ll take care of it,  yanzu abinda nake so dake tayani mu janyo ta zuwa cikin motar naku. “

Babu musu Shema’u ta shiga yin yanda ya umarce ta. “

*********

_Sajmal Clinic Kano_

Zaune yake saman kujeran sa na duba marassa lafiya,  lokaci zuwa lokaci yake jin k’irjin sa na wani irin yankewa yana fad’uwa.  Kasa ci gaba da ganin marassa lafiya yayi dole yayi excusing kansa ba don yaso ba…  Wayar sa naga ya d’auka dake saman table d’insa gefen wasu files wanda ba sai ance maka na majinyata bane kafin ya kafe wayar da idanun sa yana shafa saman screen d’in da d’an yatsar sa… 

Sai sannan na samu na k’are masa kallo,  sanye yake cikin faran yadi k’al mai laushin gaske,  wuyan rigar da d’an gaban rigar sun sha sirirn aiki da zare golden colour,  haka nan hannun rigar an zagaye ta da irin aikin wuyar rigar.  Fari ne amma ba can ba, dukda idanun sa naga kan screen d’in wayar sa zaka gane yanada yalwan idanu,  dogon fuskar sa ya dace da siririn hancin sa wanda yake zat kaman an zana,  haka nan d’an k’aramin labb’an sa tamkar ya shafa Jan baki… Duk yanda kyakkyawan mutum ya kai toh fah wannan mutumin ya kai,  gashin kansa a kwance suke luf bak’ik’irin sai ka lura ka hangi d’an furfura da suka soma fitowa daga wasu sassa na sumar nasa,  a ido zaka iya bashi shekaru 36 zuwa 39, amma a zahiri Dr AT is at his late 40s, magidanci ne d’an shekaru 48 a duniya….  Mik’ewa naga yayi yana mai ci gaba da shafa wayar sa,  sosai fuskar sa ta cika da damuwa…  Sai snn nayi nazarin k’irar jikin sa,  tabbas shekarun sa sunfi jikin sa tsufa,  ko kusa idan baka sani ba,  bazaka zaci yakai shekarun da yake a yanzu ba,  ko da shike abinka da likita sun iya kula da motsa jiki da yanayin abincin da suke ci…

D’an tsaki naga yayi had’i da shafe goshin sa,  ga dukkan alamu bai samu wanda yake nema a wayan bane,  ko kuma wayar bata shiga ba.. 

*********

“MARYAMA don Allah muje mu tari a daidai ta mu tafi gida,  k’ila dai yau Daddy Ya mance ne damu.” Cewar wata yarinya da bazata wuce shekaru 16 zuwa 17 .

Wacce ta kira da Maryama ta juyo tana duban wacce ta ida magana kafin tace ” Haba Sajida bafah lallai bane Uncle yazo d’aukar mu,  k’ila Aunty ce zata zo mu d’an k’ara hak’uri kin san Aunty tanada uzurin gida a gaban ta. “

Sajida ta d’an turo baki had’i da yin still kafin tace “Wllhi na k’osa muyi SSCE d’in nan mu huta, kawai ma bin su Momma da Aunty Shema’u zanyi mu tafi Jalingo tare. ” Ta k’arashe tana mai dariya had’i da d’an tafe hannaye. 

Maryama ta murmusa kafin tace ” Ashe su Momma sun zo.? “

Sajida ta gyad’a kai kafin tace ” Ehen shiyasa nake fad’a maki Momy yau dole ta mance damu koda Daddy zaice ta d’auko mu tunda yau Aunty Shemah da Momma sun zo, ba lallai ta tuna da mu ba.. ” Ta k’arashe tana sab’a jakar makarantar ta a kafad’. 

Mik’ewa Maryama tayi ta kakkab’e rigar uniform d’inta kafin tace ” Shikenan muje, Allah sa mu sami a daidaitan don kin san idan yamma tayi layin nan ba’a faye samu ba.”

Suka jera suna tafiya yayinda Sajida taci gaba da fad’in “Wllhi har wani dad’i nake ji gobe babu wann shegen lesson d’in mutum zai koma gida da wuri. “

Murmushi kawai Maryama tayi sanda suka k’arasa bakin titi don neman abin hawa.”

********

A razane ya mik’e had’i da damk’e wayar jikin kunnen sa cikin hannayen sa yana fad’in “Hisham me kake cewa,  Innalillahi wa inna ilaihirraj’un,.” Bai gama jin abinda Hisham ke fad’i ba yayi jifa da wayar ya fito a guje cikin tsananin birkicewa,  gaba d’aya duk yanda ya wuce cikin asibitin kallon sa suke cike da firgici,  basu tab’a ganin sa cikin irin yanayin ba…  Wasu nurses maza guda biyu suka biyo bayan sa suna masa magana, inaa ko kulasu baiyi ba,  bai ma san me suke cewa ba,  motar sa dake ma’ajiyan ta kurum ya k’arasa,  ya mata key kafin ya fice a guje cikin tsananin tashin hankali…

WRITTEN BY:   SAMEENA ALEEYU

NOVEL NAME:   SHAKUWA CE

UPLOADER:     AIHAUSANOVELS 

  DOCUMENT SIZE:         450KB

DOCUMENT TYPE:              TXT

MODIFIED DATE:    19- NOVEMBER -2022

CATEGORY:               LOVE   STORY

PRICE:                            FREE

Proceed To Download Shakuwa Ce Hausa Novel Document.

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Domin Karanta Littafin Sai ku Danna Inda Aka Saka Read More

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

Copyright 

If you are the right owner of this novel and you want us to remove it from our site please mail Us at aihausanovels@gmail.com

Back to top button