WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)
Unique Barakancy
TWENTY-NINE📍
“Wayyo Allah billy my husband to be is back, shirya ki rakani dan Allah”…..
Eesha ta fada cike da murna….
“Iyee na tayaki murna, Dr dinne ya dawo?”….
Dayake eesha na yawan basu labarinsa, su sun dauka soyayya suke sosai dan har waya take nuna musu tanayi dashi….
“Eh wallahi shine, ke tashi mu fara shiri zuwa anjima zamu tafi, kunyar zuwa gidan surikai nake ni kadai”…….
Karab Umaima tace;
“Dan Allah nima zani, in shirya muje?”…..
“A’a wallahi yi zamanki kafin muje kimin wuff da saurayi, waye baisan halinki na snatching ba? Gwara billy nasan maza basa gabanta so hankali kwance zanje da ita”……..
“Mtssss sai kije ki cinyeshi ai, in snatching din zanyi sai in miki? Kila ma be hadu ba mtsssss”….
“Karki kuskura ki gayamin maganar banza, nasan har ki mutu bazaki taba haduwa da kamarsa ba wallahi, ke tsayawa miki describing dinsa bata lokaci ne shiyasa zan tafi da billy atleast zata baki testimony mtsssss”……
“Rabu da ita eesha, waye besan halinta ba? Niko dama anything that has to do with man kinsan I’m out so baki da case, dama dai wata fine babe dince ehnn, anyway mu fara shiri toh”….
Billy ta fada tana dariya…..
“Karki batamin rai kema, da anfara maganar arziki dake saikin nuna hali ko kunya bakyaji”….
“Sorry ma’am, zo in fara miki kwalliya yanda zaki rudasa ya kasa ganin kowa saike kawata”….
Cikin farin ciki eesha tace;
“Yauwa shiyasa nake sonki wallahi, zoki tayani zaban kayan daya kamata nasa”….
“Bakida case kawata”….
Tinda suka gama waya da eesha take zaune tana tinanin yanda zata billowa al’amarin, damuwarta daya yanda Deen ze karbi lamarin amma abu daya ta sani ko yanaso ko bayaso dole ya amince, ta dade da sanin eesha nasan Deen dan aminiyarta wato mahaifiyar eesha tasha nuna mata su hada ya’yansu aure kuma ta amince da hakan dari bisa dari dan ta yarda da tarbiyyar eesha sosai….
Tana cikin wannan hali Umm tashigo ta sameta..
Dafa kafadarta tayi tace;
“Meyafaru? Why are you looking disturbed?”….
“It’s Saif’s dad!”….
“Shi yazo?, meyace miki toh?”…..
“Wai aure zeyiwa Saifuddeen, kuma yana san dansa ya dawo kusa dashi, kinji wata maganar banza?”….
“Toh menene dan ya masa aure? Inace ya isa auren? Yanada aikinshi da arzikinshi da komansa so why bothering?”…….
Cikin bacin rai mami tace;
“Kinji wai auren mafa he has someone for him, bansan wacce ze hadashi da ita bama”…..
“Bangane someone for him ba? Ina lefin abar yaro ya zabo abarsa da kansa”……
“Nima dai shi nagani, nasan bazai wuce fitsararrun ya’yan abokansa ba shiyasa nace masa be isaba nima inada wacce zan hadasa da ita kuma saidai ya hakura ya bari ya auri zabina dan bazan yarda ya auro wacce ban yarda da tarbiyarta ba”…..
Tinda ta fara magana Umm ta sake baki tana kallonta kamar hoto, saida ta dire sannan tace;
“So what do you guys mean by trying to make your son’s life a game, so kuke kuyita playing dinshi kamar wani toy? Bazaku bari fadanku ya tsaya iya ku kadai ba sai kun sashi? Haba yaya!”……
“Huh idan baki fahimce niba wazai fahimceni Jamila, why are you always like this in my hard time?”…..
“Ni bawai ban fahimceki bane the thing is that he has his right to choose a wife bawai kuyi masa auren dole ba kamar a kauye?”……
“Nidai tinda kika koma UK you start thinking like foreigners! Da anyi magana kice right right!, shikenan yaro bazeyiwa iyayensa biyayya ba?, just tell me you’re not ready to support me kawai, dama kinsaba bin bayansa ba yau kika fara ba”……
Murmushi Umm tayi tana girgiza kai tace;
“No pls karkice haka yaya, you know I got your back anyday anytime, idan banyi supporting dinki ba wa zanyi supporting? Yanzu ya kikeso ayi toh?”….
Wani ajiyar zuciya Mami ta sauke tana dan murmushi, dama tasan inba haka tayiwa Umm ba tsap sai tace ba ruwanta kuma Deen sai yafi saurin amincewa idan Umm tasa baki dan Umm akwai dabara…..
“Yauwa ko kefah yar’uwa, yanzu so nake ki tayani shawo kan dan naki ya amince”……
“It’s ok yanda kikace haka zaayi, amma wa zaki aura masa?”………
“Eesha! Yar gidan Hajiya Saratu”…..
Dan jimm Umm tayi sannan tace;
“Toh shi Saif din yana sonta ne?”…..
“Gsky rabonsa da ita tun tana karama, I just want them to bond now, I believe it’ll work out!”….
“Toh Allah yasa, niko sai naga kamar yana san yarinyar nan daya kawo fah, ko zamu kara tambayarsa ne?”……
“Wlh be isaba I’ve given him enough chance and you were the witness! And I’m sure zeso eesha dan tanada kyawawan hali”…….
“I am not against eesha din tinda nasan mahaifiyarta mutuniyar kirkice same with itama but I want you to give him one last chance about this girl, nida kaina zan masa maganar eesha zan kuma nuna masa ya fadamin gsky idan har yana san ita fatima zainab din I’ll help him ayi canceling maganar eesha, anything he says will be the final say I promise you!”..
“Shikenan! Anjima eesha zata zo”….
“Allah ya kawota lafiya”……
“How do I look?”….
Ta fada tana jujjuyawa……
“Perfect! Kinyi kyau kamar wacce zataje gasar kyau, I don’t think Doctor can withstand this beauty! Ke dole ma ki rudashi kawata, badan karki zageni ba dana kara da wani abu”………
Billy ta fada tana kallon eesha tindaga sama har kasa kamar ……
“Gsky karki kara toh, iya hakama ji nake kamar kaina ze fado, dadina dake iya hyping wallahi”….
“Hmmm su iya hyping manya, kar aje dai ana rawar kai”….
Cewar Umaima tana harararsu….
“Badai ruwanki yar bakin ciki, munsan haushi kikeji dan bazaki samu irin saurayinta ba”…,
“Kece abun tausayi da baki da aikinyi sai bin jin a sinki mata, gwara ni inada mashinshini arrijalu”…
“Kehhh ya isheki haka! Saurayi banga damaryi bane ke kanki kinsani, dan babu kalan da basa zuwa dm dina kullum not to talk of masu bina akan hanya, lesbian nina zabarwa kaina and it doesn’t mean you talk to me anyhow, wanda ya fika ya fika just accept bitch!!”…..
“Mtssssss bani da lokacinki yar iska kawai”….
“Gwara kar kiyi lokacina inba hakaba yanzu sai in miki cin mutunci irin namu na yan iska, eesha zo mu wuce dan Allah”….
“Yauwa billy muje, kinga mami ma tamin text, the driver is out”…..
“Awwwwn, gsky inlaw dinki naji dake”…
“Kedai bari shiyasa nake sonta wallahi”….
“Hakan nada kyau muje ko”…
“Yes”……
“Ni dama nasan zaka nemeni! Ba ka dauka karya nakeyi ba?, ka dauki yarda ka dora masa bakasan macuci bane”……
“Kayi hakuri, ni kadai nasan irin dana sanin da nakeyi dana barsa yayi fooling dina ban shiga gidannan ba, harda min wayo wai nabar kasar it isn’t safe here”…
Sameer ya fada yana jin daci a ransa…..
“Karka damu zan taimaka maka, kaine zaka sameta”…..
“Toh amma bacewa kayi matarka bace?”….
“Wasa nake, haushi kabani na kin yarda dani shiyasa na fadi hakan”…..
“Kai har naji hankalina ya kwanta wallahi, yanzu kasan inda yake tinda kace baya cikin prison din sanda abun ya faru?”…..
“A’a bansani ba amma nemo inda yake abu ne me sauki sosai, kawai ka kwantar da hankalinka”….
Ya fada yana smiling ganin komai zezo masa da sauki, zeyi amfani da sameer ya dawo da masoyiyyarsa…….
“Toh nagode, amma Deen yacemin I should stay away from you, wai kai mugune is that true?”…..
“Inda mugune ni bazanzo inyi kokarin taimaka maka ba ko ka taba ganin inda mugu ke taimako? Kawai yazo ya shirya maka karyane dan yana son yarinyar”….
Ya fada yana bata rai alamun beji dadin abinda sameer ya fada ba……
“Yi hakuri abokina, na yarda kai ba mugu bane dari bisa dari, yanzu meye abunyi, ko zaka bani phone number ka?”……
“Karka damu mu hadu anan gobe by 2pm, so nake ka nuna masa bakasan komai ba, you’ll play him smart as he did to you, sai goben”…..
Yana fadin hakan ya juya ya fara tafiya…..
Dakatar dashi sameer yayi da sauri yana fadin;
“Baka fadamin sunanka ba pls”…..
“Yusuf!”….
Ya fada yana karawa gaba da sauri…..
“Alhaji Ibrahim kana gani shadaya ta wuce amma yarinyar nan shiru batazo ba ka tabbata kayi yadda akace kayi kuwa?”……
Dan jimm daddy yayi sannan yace;
“Nayi wallahi! Kuma munyi da ita zatazo da sassafe ma, I don’t know what is happening yanzu”…
“In banda abinka ai kayi ganganci ya zaayi tazo ka bari ta fita daga gidan, ai cewa zakayi ta kwana anan gidan naka tinda tanada guri anan amma sai ka barta ta fita?”…..
Cewar Alhaji habibu rai a bace, bama shi kadai ba kusan duk wanda suke parlourn hankalinsu a tashe yake……
“Gaskiya nayi mistake, wallahi saida ta tafi nima nayi tinanin hakan, yanzu meye abinyi toh?”…..
Alhaji lawal ne ya karba da fadin;
“Hmmm kallonku kawai nakeyi, bari in fada muku gaskiya wannan abu ya lalace dan bazaisa tazo ba, saidai abi ta wata hanyar a mata kiranye ta tawo ko a ina take!”……
“Ka kawo shawara me kyau, asan yanda zaayi a mata kiranye instantly, kayiwa boss text message”…
“On it”
Daddy ya fada yana daukan wayarsa…..
“Done! nasan yanzu komai ze kammalu, mu jira zuwanta any moment from now kawai”…..
Tanadai zaune a parlourn amma ita kadai tasan meyake damunta, jinta take kamar akan kaya burinta kawai tabar gidan gashi ta rasa yanda zatayi ta fita, kamar ana janta haka takeji har wani gumi ta fara tsabar yanda zaman gidan ya isheta, damuwarta daya ta bar gidan ta tafi gidan daddy a samu a daura auren, gashi shikuma ya kasa ya tsare a parlourn ko nan da chan yaki motsawa ita kuma haka kawai taji tana shakkar tashi ta fita a gabansa, abun duniya ne ya ishe ta cire meyafin abayar data yafa, hakan be ishe taba ta sake zare ribbon din kanta, haka gashin ya biyo hannunta ya zubo a gadon bayanta wani ya zubo ta gaba kamar mahaukaciya sabon kamun hauka…….
Deen na kallon duk abinda takeyi amma be tanka mata ba, so yake yaga gudun ruwanta dan sarai ya kula zaman gidan ne ya isheta shiyasa ya kasa ya tsare dan beyarda da fitar da takeso tayi ba, gashi tin dazu yake tambayarta ta fadamasa WACECE ITA’ amma taki cewa komai har yayi zuciya ya kyaleta, wai shi zaa nunawa miskilanci? Sai suka cigaba da zaman kurame yayi kamar baya kallonta nan ko duk abinda take yana kallo ta kasan ido”…….
“Hmmm abun ya motsa kenan”…
Yafada kasa kasa yana kallon dogon gashinta daya rufe har fuskarta……
Wani ajiyar zuciya ya sauke tuno da laushi tsantsi da irin kamshi da gashin yakeyi a lokacin daya taba har ya kusasa suyi accident, a take yaji yana san kara tabawa dan be gaji da tabawa ba, daurewa yayi ya dauke kansa yana kokarin korar abinda shedan yake raya masa….
Kasa hakuri yayi ya sake dagowa ya kalleta, cikin basarwa yace;
“Ke nemi dankwali ki daura”…….
Shiru bata amsa shiba kuma sarai ta jisa!
“Ke ba magana nake miki ba! Ba dole aljanu suyita bin mutum ba tinda shi besan ya rufe kansa ba, ni banga abin nunawa a gashin doki bama”…..
Still bata kulashi ba kuma tanada answer daidai dashi, kawai ke din da yake cemata ne yake bata mata rai…..
Kamar yasan abinda take tinani yace;
“Zainab magana nake miki fah”…..
Dan haka kawai yaji beyarda sunanta fatima ba, akanme zatasa sunan mami a sunanta so gwara yace mata zainab kawai…..
“Zaka gayamin inda kaga zainab a gurinnan”
Ta fada a ranta still bata dago ba….
“Ko ba sunanki zainab ba?”….
Sai a lokacin ta dago fuska a hade tace;
“Kaga mallam ka rabu dani inji da abinda yake damuna!!”……
“Meyake damunki? Fadamin”….
“Kayi kadan in fadamaka damuwata, just mind your business!!”…….
Zeyi magana kenan sukaji sallama a bakin kofar, Deen ne ya amsa ciki ciki ko sunji ko basuji ba shidai yaga sun shigo…..
Akanta eesha da billy suka fara sauke ido, zaro ido sukayi a tare suna karasowa inda take, itako fatima zainab yi tayi kamar bataji alamun mutane sun shigo ba……
Da sauri billy ta rungumeta tana fadin;
“Wow kece or am dreaming? Eesha dama kinsanta shiyasa kikemin wulakanci ko? Wayyo Allah naji dadi dana biyoki eesha, ashe alkhairi ke kirana inzo inga pretty girl dinnan”…. Sai kuma tashiga taba gashinta tana fadin;
“Wayyooo Allah kinada gashi sosai gashi da laushi wallahi, kai I’m already obsessed with you! Ina sonki wallahi, nima…”….
Wani tsawa Deen ya daka mata tsabar yanda ransa ya baci, ya taso kamar ze mareta yace;
“Saketa!!!!”…….
Sosai tsawar ya shiga billy saboda daga sama tajita dan batasan da wani a parlourn ba, ta saketa da sauri jiki na rawa……
“Out!!!!”….
Ya fada yana nuna musu kofa…..
Tinda suka karaso eesha tayi sumar tsaye saboda tozali da Deen da tayi, ashe pictures basa masa Justice? Dama haka ya hadu sosai? Wannan ai saidai tadinga boye kayanta dan wallahi ko irinsu billy ba zata bari su gane matashi ba, ta dade bataga captivating namiji irinsa ba dan ko ita da takejin tanada kyau sannan kuma gata mace tasan sai a daukeshi sau hamsin baa dauketa ba, ashe akwai maza masu kyau irin haka? A take taji zata iya mutuwa akansa, ga wani kishinsa da yazo mata lokaci daya ta kumaji babu abinda bazata iyayi ba akansa, ta kuma tabbatarwa zuciyarta Deen nata ne ita kadai…….
“Ke mahaukaciyar inace ina magana zaki tsaya kina kallo na, oya bita ku bace daga gurinnan! Kananun yan iska kawai!!!”…….
“Saifff menene haka? Wani irin rashin hankali ne wannan, daga ganin mutane sai ka fara zaginsu?”…..
Umm ta katseshi tana shigowa parlourn mami biye da ita a baya…..
Bece komai ba ya juya ya haura sama rai a bace….
“Karku kulashi dawo ku zauna kunji?”….
Zama sukayi a daddare dan harga Allah tsawar daya musu ta tsoratasu kadama billy taji labari….
“Ku saki jikinku mana, me kuka masa haka?”…
Umm ta tambaya dan tasan haka kawai daga ganinsu bazai musu wannan zagin ba…..
“Babu abinda muka masa, kawai billy ce taga roommate dinmu shine take mata magana”….
“Wacece roommate din taku?”……
Basu bawa Umm ansa ba Deen ya sauko da sauri cikin tashin hankali yace;
“Ina take?”…..
Mikewa Umm tayi ganin yanda ya sauko hankali tashe, cikin rashin fahimta tace;
“Wa kenan?”…
“Fatima or zainab, I left her in this parlor”…
Sai a lokacin su eesha suka kula ashe tabar parlor”..
“Probably in the bedroom”…..
Cewar Mami tana typing message akan a kawowa su eesha refreshments…..
Komawa ciki yayi da sauri yashiga nemanta baji ba gani, cikin toilet ne store ne babu inda be duba ba, haka kawai yaji hankalinsa be kwanta ba tinda ya hau samannan shiyasa ya dawo ya dubata sai prediction dinsa ya zama daidai ya rasata…..
Dawowa parlourn yayi cikin tashin hankali yace
“Mami banganta ba fah!”…
Hankali tashe suka mike suma suka shiga nemanta a ko ina na gidan, su kansu su eesha sunyi mamakin batanta dan basuga sanda tabar parlorn ba…..
Babu inda basu duba a cikin gidan ba, har securities da mai gadi sun tabbatar da bata fita ba amma sama da kasa sun nemeta sun rasa……
Deen da yazama so frustrated yanaji kamar ya shake su eesha da suka zake ana nemanta dasu yace;
“Ni nasan so take ta fita shiyasa na tsareta, wayennan idiots din sukazo suka sani tashi gashi yanzu she’s no where to be found! Allah idan banganta in the next 30mins I’ll hold you guys responsible!, waya sani ko turoku akayi! Musamman ke! you’ll tell me why you hug her!!!”…….
Domin samun cikakken Littafin sai ku dannan Bulun Rubutun dake kasa ko kuma hoton 👇👇
https://www.aihausanovels.com.ng/2023/01/wace-ce-ita-chapter-23-complete-novel.html
~Uniquebarakancy~