Kalaman Soyayya

Sakonnin Soyayya Na Mata Na Barka Da Shan Ruwa Ga Samarinsu 2023

SAKONNIN SOYAYYA NA BARKA DA SHAN RUWA

NA MATA

1} Zuwa ga zaɓin zuciyata, ina fatan ka
sha ruwa lafiya? Ina fatan izuwa yanzu
nutsuwa ta game jikinka, ishiruwa ta
gushe daga makoshinka? Ina kuma fatan lada ya tabbata a gare ka. Fatan ka sha ruwa lafiya? Ka Huta Lafiya.

2} A dukkan lokacin da na ga daren
Lailatilkadari, zan kasance mai rokon
Ubangiji Ya mallaka min kai a matsayin
mijina uban ‘ya’yana, ina fatan kai ma
zaka kasance mai tsawaita tsayuwa cikin kowane dare domin ganin cikar
burinmu? Ina Son Ka.

3} A lokuta da wurare daban-daban ina
ganin ka kana yi min gizo, ina ganin ka a lokacin da idanuwana ke a rufe ko a
buɗe. Ba na iya yin komai ba tare da
tinaninka ba. Fatan Ka Sha-ruwa Lafiya.

4} Jin muryarka na sakwan guda, na jefa ni cikin kogin tinaninka, na tsawan
lokacin da idanuwana ke kasancewa a
buɗe. Barka Da Shan-ruwa.

Karanta>>> Maganin Toilet Infection Da Kuma Rashin Sha’awa Ga Mata

5} Irin kulawar da kake nuna min a
kullum na saka ni tinanin irin yadda
rayuwarmu za ta kasance a nan gaba. Zanbzamo tamkar sarauniya a gidanka, kai kuma zaka zamo sarkin da babu wani mai irin masarautarsa a duniya ta kowace fuska. Ina Son Ka.

Karanta>>> Ga Masu Neman Karin Kiba Ga Hanyar Da Zaku Bi

6} Zuciyata ba za ta taɓa canja matsayin
da kake da shi ba a cikinta. Murmushina gare ka ba zai taɓa yankewa ba. Son ka a cikin zuciyata ya yi kafuwar da ba zai taɓa goguwa ba a cikinta na har abada. Barka Da Hutawa.

Karanta>>> Ina Mata Masu Fama Da Rikecewar Al’ada Ga Magani Da Izinin Allah

7} Da a ce zan iya zama komai, da na
zama ruwan hawaye a gare ka, a haife ni a cikin idanuwanka, na rayu a saman
kumatunka, na mace a saman laɓɓanka. Ina son ka so mara misaltuwa. Barka Da
Shan-ruwa.

Karanta>>> Amfanin  Zobo Ga Lafiyar Jiki Da Kuma Illolinsa

8} A dukkan lokacin da kake bukatar
wani ya taya ka hira, karda ka manta
kana da ni, ka nemo ni domin ɗebe maka kewa a cikin kowane irin yanayi da lokaci. Fatan Ka Wuni Lafiya? Yaya
Ibada?

Karanta>>> Amfanin Dabino Da Kuma Magungunan Da Yake Yi Guda 50

9} A lokacin da na tino irin rayuwar da
na yi a baya, na kan hango irin asarar da na yi, na kasancewa ta ni kaɗai ba tare da kai ba, yanzu na same ka, ina ji na a matsayin wata wadda ta fi kowace mace sa’a a rayuwa. Ina fatan na kasance a tare da kai na har abada. Barka Da Shan-ruwa.

Karanta>>> Amfanin Kubewa Musamman Ga Ma’aurata

10} Ba zan taɓa mantawa da ranar cikar burina ba, ranar da wanda nake so ya nuna min soyayyarsa a fili, ba kowa bane face kai hasken idaniyata. Ina son ka. Barka Da Hutawa. Fatan Ka Sha-ruwa Lafiya?

Karanta>>> Fassarar Mafarkin Ruwan Sama 

Back to top button