Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 63 Complete Novel

*ASM Bk2063*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
………..Bayan shigarta tsayawa tayi daga gaban gado tana tunanin abunda zatai ma d’akin don fes yake, can dai ta fara gyaran gadon ta kakka6e abunda zata kakka6e bayan ta gama da gadon laundry ta nufa ta d’aukko floor wiper ta dawo ta fara gyara tsakar d’akin, bata d’au wani dogon lokaci ba ta gama ta maida ta ta dawo da d’an towel mai taushi ta goge furniture d’in, bayan duk ta gama ta kunna burner dake jone jikin socket ta zuba turaren wuta nan da nan daddad’an k’amshi ya fara karad’e d’akin, bayan d’akin ya turaru ta cire burner d’in ta nufi Parlor don shima ta turara shi, yana zaune a inda ya saba zama ya d’an kishingid’a Tv nata aiki wayar shi ruk’e a hannun shi yana lallatsawa, tana fitowa ya d’aga ido ya d’an kalle ta kafin ya maida su kan wayar, anan wurin kayan kallon ta jona ta tsaya tana jira ya gama turaruwa, tana cikin tsayuwar aka k’wank’wasa kopar parlon Haisam ya bada izinin a shigo, Saude ce ta shigo hannun ta ruk’e da d’an babban basket mai d’auke da kayan Breakfast ta tsaya daga bakin kujerun tana gaishe da shi ya amsa tare da d’an kallon ta ta nufi c-table zata d’aura yace ta kai dining area ta amsa da to ta wuce, Fatuu na tsaye tana kallon ta da murmushi tun da ta shigo itama murmushin take mata ta nufo in da take, tana zuwa Fatuu ta amshi basket d’in tana gaishe da ita ta fad’ad’a murmushin ta tana amsawa, godiya Fatun tayi mata k’asa k’asa da murya tace “Yayi kyau Amaryar mu, naji dad’in ganin ki haka sosae” yar kunya ce ta kama Fatun tana ta murmushi ta d’an sadda kan ta, tambayar ta tay mi take so a dafa masu da rana ta d’ago tace mata ko mi ta dafa tana ta murmushi tace in dai akwae abunda take so ta fad’i kar ta ji nauyi Fatun tace mata da gaske duk abunda ta dafa yayi tace to shikenan sukai sallama ta juya, kan Dining table ta kai basket d’in ta d’aura sama, juyowa tay ta nufi Kitchen plates da cups da sauran abun da zata buk’ata ta d’aukko saida ta d’auraye su tare da hannuwan ta da tay aikin sa turaren wuta sannan ta fito ta koma dining d’in, wata babbar Warmer a cikin kayan ta fiddo ta bud’e nan take wani irin k’amshi ya bugi hancin ta, Kaza ce guda d’aya babba ta gasu tasha kayan yaji da spices sun manne a jikinta daga k’asanta kuma a tsage yake tasa spoon ta juyata ta bud’e wurin nan take taga ashe Chicken and Chips ne ta ta6a gani Sauden tayi ba dai dad’i ba soyayyen dankalin turawa da dafaffen kwai ake cusawa a cikin Kazar bayan an tafasa ta sai a d’inketa a shafe ta da butter a bad’a kayan yaji da spices sai a gasa su tare a Oven, gani tay in ta yaga zata 6ata ta hakan yasa ta k’yale ta fiddo ledan sliced bread dake ciki ta aje kan table d’in sannan ta fiddo kayan tea da Flask mai d’auke da ruwan Lipton da ya sha kayan k’amshi sai wani bowl mai murfi ta bud’e shi nan kuma wainar k’wai ce murtuka murtuka, tunanin ta fara mashi magana kafin ta had’a tay hakan yasa ta nufi cikin parlon tana tafiya a hankali kai kace yanga take saidai kamata da kayan sukai ne yasa hakan, tana zuwa bakin kujeru kafin ta k’arasa taga ya mik’e ya tunkaro inda take yana zuwa saitin ta yay mata wani kallo ya wuce abun shi ta juya ta bi bayan shi, bayan ya zauna ta fara had’a mashi tea d’in tana yi tana tambayar yadda zata saka mashi komai har ta gama ta tura gaban shi ta fiddo kazar ta d’aura akan plate itama ta tura mashi ta curo waina d’aya daga cikin bowl d’in tasa a wani plate ta tura mashi sauran dake a cikin bowl d’in duka sannan ta d’aukko ledan biredi ta bud’e ta curo yanka biyar ta d’aura a gefen wainar k’wan da ta d’auka ta tura mashi ledan itama yana dai ta kallon ikon Allah, har ta gama had’a tea d’in ta ta zauna bai ta6a komae ba, hannu ya kai ya ciro slice na bread ya yagi wainar kwai ya had’e sannan ya d’auki cup d’in tea ya fara sha a nutse, kallon shi tay bayan wani lokaci ganin bai ta6a kazar ba yasa a hankali tace “gashi nan ka ci while it’s still hot kar ta huce” shiru bai ce Komai ba bai kuma kalleta ba saida ya k’ara sipping tea kaman sau biyu sannan ya d’aga ido suka sauka cikin nata, da hannu tay mashi nuni da kazar ya kai idon shi kan ta kafin ya sake maido su a kanta “miye wannan d’in?” d’an waro ido tay jin wata tambaya kenan ma bai gane shi ta aje mawa ba, cikin yar inda inda tace “C… chicken and Chips ne” hannu ya kai ya d’an ruk’e ha6ar shi taji yace “mi za’ai dashi?”
“Kai na aje mawa ka ci” tay Maganar tana d’an kikkafta idanu,
“Na zama ke kenan?” ya tambaya had’i da d’an d’age mata gira ta d’an zaro ido sai kuma ta d’an tura baki “ai ba ina nufin ka cinye shi ba duka kawae naga in na 6ara ta zan 6ata ne shiyasa na bar maka in ka ci ka rage sai in ci, kuma ma ai nima ba iya cinye ta zan yi ba ko” yadda tay Maganar cike da shagwa6a saidae ita matsayin lafiya lou take Maganar ta, d’an guntun murmushi taga yayi gashi ya kafeta da ido ita kuma sai faman kikkafta nata take tana d’an juyar da fuskar, wani plate ya d’auka ya rufe kazar ya kai hannu ya d’auki cup d’in shayin ya cigaba da sha, bayan ya cinye waina d’aya ya tura mata bowl d’in ta d’an kalle shi, saida ya k’arasa shanye tea d’in ya bud’e kazar ya d’aukko fork ya fara k’ok’arin 6alla sai dai kuma tak’i 6alluwa ta dad’i, aje fork d’in yayi ya kai hannu wurin cutlery set d’in dake a tsakiyar table d’in ya curo yar wuk’a, d’an jim yay bai sata jikin Kazar ba ganin tana buk’atar a wanke ta tunda anan suke aje lokaci guda Fatuu ta fahimci dalilin dakatawar tashi ta mik’e ta mik’a hannu alamar ya bata ya d’aga ido ya kalleta kafin ya bata, bayan ya mik’a mata ta fita daga cikin kujerar ta nufi hanyar kitchen ya bi bayan ta da kallo har ta shige Corridor sannan ya juya da wani irin yanayi akan Face d’in shi, had’e hannuwan shi yay ya d’aura ha6ar shi a ranshi ya raya yakamata a sa washbasin a wurin Saboda zaryar da yaga tana yi, bada jimawa ba ta dawo ta wanko wuk’ar ta mik’a mashi amman sai bai amsa ba yay mata alamar ta zuba mashi, ganin kazar ta d’an mata nisa yasa ta zagaya daga gefen shi ta jawo plate d’in ta fara yankar mashi, gaba d’aya sun cika juna da fitinannan k’amshin jikin su Haisam har d’an lumshe ido yay slowly ya bud’e ba tare da ta gani ba, tana yanko wurin cinye ta d’aura mashi a plate zata k’ara ya d’aga mata hannu alamar ya isa ta kai idon ta kan shi suka had’a ido, d’an tura baki tay ta marairaice fuska a hankali ta furta mashi gaskiya bai isa ba yayi kad’an, ido ya bita dashi da alama ya kasa ce mata komai ta k’ara yanko wani ta d’aura, kallon shi tay ta d’an bud’a ido ta tambayi ta k’ara ya d’an wurga mata harara ta saki murmushi tace to bari a zuba mashi mahad’in kazar ta d’ebo dankalin ta zuba tana shirin sake d’ebowa ya kai hannu ya ja plate d’in ba tare da ya ce komae ba ta k’ara yin murmushi, tana shirin komawa wurinta taga ya kai hannu ya tura plate d’in kazar wurin da ta zauna, bayan ta koma ta zauna a nutse suka cigaba da yin Breakfast d’in tana yi tana d’an satar kallon shi, saida ya cinye wanda ta zuba mashin ya yago tissue ya goge bakin shi, mik’ewa yay zai bar wurin ya juya suka had’a ido taji yace ya bata space ta cinye komai ta d’an bud’a ido ya juya ya tafi tay d’an murmushi had’i da d’an girgiza kai, ba laifi ta d’an ci sosae bayan ta gama ta mik’e ta fara kwashe kayan tana kaiwa kitchen, saida ta wanke abubuwan da suka 6ata kazar da ta rage ta saka ta fridge wainar k’wan kuma da ledan biredin ta ajiye su saman counter, bayan ta gama fitowa tay ta wuce Bedroom saida ta d’aukko wayar ta daga cikin purse ta koma gefen gado ta zauna, bayan ta bud’eta tunanin wa zata kira ta shiga yi can ta kira Fauzy tana fara ringing ta d’aga,
yar shewar farinciki tay tace “K’awata Amarya ai ban tsammaci ganin kiran ki ba don banyi tunanin zaki tuna da wata Fauzy ba da wuri haka” d’an murmushi mai sauti Fatun tay ta tambayi ya suke da Aunty Mareeya tace mata duk suna lafiya ta k’ara ce mata ya gajiya had’i da yi mata godiya, tana dariya tace ai ita ke tattare da gajiya su tasu tabi jiki tuni har saida Fatun ta d’an girgiza kai, tambayar ta Ya Haisam Ango tayi tace mata yana parlor, hiran School suka shiga yi ta tambayi yaushe zata dawo Fatun tace mata jibi in Allah ya kaimu,
“ah haba dae jibi, ki bari sai kin gama cin Amarci kaman after a week sai ki dawo” tana murmushi tace mata so take ta samu matsala kenan Fauzyn tace to ta bari sai kaman Wednesday tazo amman ba jibi ba, tuna mata tay tace kar Amarci yasa ta manta da Assignment d’in da aka basu ran Friday dai, Fatun tace to zata yi jakarta ma na gida amman yanzu zata kira Kawu Amadu ya kawo mata, daga baya sukai sallama tana ce mata ta gaishe mata da Ango tana murmushi tace zai ji,
Bayan sun gama wayar Kawu Amadu ta kira har saida ta kusa yankewa sannan ya d’aga ta gaishe dashi yana yar dariya yace “Amaryar mu kun tashi lafiya” amsa mashi tay da lafiya lou suma ta tambayi ya suka tashi yace mata lafiya, jin ta d’an yi shiru yasa shi tambayar ta lafiya dai ko cikin yar in ina tace mashi dama don Allah so take ta rok’e shi ya kawo mata jakarta ta makaranta, farko cewa yay shi ba zai kawo ba ta marairaice tana rok’on shi k’arshe sai cewa tay shikenan bari tazo ta d’auka da kanta yana dariya yace ai dama yana cikin shago ya sake ya ganta sai ya zane ta kuma da tsallan kwad’o zai maida ta, itama dariyar take a hankali tace mashi ai yanzu ta wuce wannan a wurin shi yace eh lalle ta isa shi take gaya ma haka ko to ta gwada fitowar zata sha mamaki, rok’on shi ta k’ara yi yace bari ya kawo mata tay mashi godiya ta tambayi gwaggo yace ta na cikin gida, bayan sun gama wayar d’an jimm tay tana son kiran gwaggo amman kunya take ji, can dai tay dialing lambar ta ta fara ringing, bayan ta d’aga a kunyace ta gaishe da ita tana murmushi ta amsa tay mata sun tashi lafiya da tambayar d’anta Haisam Fatun tace mata yana parlor tace to ta gaishe mata da shi tace to, d’an shiru sukai can gwaggon ta ce badai wata matsala ko da sauri tace mata eh ba komai, tambayar ta tay wai ta fad’a ma baffanta zancen gwaggon tay yar dariya tace ta fad’a mashi mana yayi farinciki sosae ma, cikin yar shagwa6a tace amman shine bai kirata ba tace k’ilan ya bari sai an samu natsuwa ne, bayan sun gama ta shiga kiran Baffan nata cikin sa’a ta shiga ya d’aga ta gaishe da shi yana murmushi ya amsa ya tambayi ya take ita da maigidan nata, cike da shagwa6a tace “Baffa shine kasani amman baka kira ni ba gaba d’aya ma ka manta dani” yar dariya yayi “haba ni na isa in manta da inna wuro gaba d’aya, dama zan kira na bari a nutsu tukun, na matuk’ar yin farin ciki da jin abun Alkhairi wllh har bazan iya kwatanta maki ba ashe dai rabon shine mijin naki yasa komae ya faru, kinga sakamakon yi ma iyaye biyayya Allah ya juya komai, Nagode inna wuro ina matuk’ar Alfahari dake matsayin jinina, ina rok’on Allah ya k’ara ma rayuwar ku Albarka ya jikan Mahaifiyar ku” har k’walla sun taru a idanun ta ta amsa mashi da Amin, tambayar ya karatun ta yay tace mashi Alhamdulillah yace Allah ya bada sa’a, bayan ta amsa ta tambaye shi Yadikko yace tana d’aki bari ya mik’a mata tace to, bayan ya kai ma Yadikkon cike da Farinciki tana washe baki suka gaisa tana fad’in Amaryar su, tambayar ya gida da Angon ta tay Fatun ta amsa mata ta shiga yi mata Allah yasa Alkhairi da nuna yadda tay murna da Al’amarin tace Addu’ar da suke tayi ce Allah ya amsa taji mata dad’i sosae wllh da Al’amarin ya juye haka dama haka take ta fata, daga jin yadda take Maganar Fatuu ta fahimci ba k’aramin farinciki take ba, tambayar ta su Mino tay tace basu kaiga dawowa daga islamiyya ba tace to in sun dawo zata kira ta tambayi yaushe zasu zo tace suna nan zuwa in ta Haihu, a shagwa6e tace a’a ita dae bata yarda ba wllh tana dariya tace suna nan zuwa bada dad’ewa ba, bayan sun gama Magana da Yadikkon ta ba Baffan wayan suka cigaba nan yake tambayar ta Haisam yace bai da Lambar shi yana son yi mashi godiya tace ai yana nan ko a kai mashi yace to, mik’ewa tay da sauri ta nufi hanyar fita, Yana kishingid’e kan kujera ta tunkaro shi Wayar kare a kunnanta, tana zuwa daga gefe ta tsaya ta cire wayar daga kunnan ta a hankali tace mashi Baffan ta ne yake son Magana da shi ya d’an d’aga mata kai ta mik’a mashi wayar ya amsa, gyara zama yay a nutse ya gaisa da shi nan ya hau yi mashi godiya sosae da Addu’oi, k’asa k’asa yake amsa wasu wasu kuma yay shiru daga baya sukai sallama ya mik’a mata phone d’in idon shi cikin nata da d’an murmushi ta amsa ta maida ta kunnan ta, har ta juya kaman zata tafi sai kuma ta dakata tana tambayar Baffan yaushe zasu zo to jin yana mata sallama yace mata ba yanzu ba sai an d’an jima, aikuwa cike da shagwa6a ta hau Jujjuya jiki tana ita dae bata yarda ba don Allah su zo kwanan nan kai kace da gayya take juya jikin saidae ita bata ma san tana yi ba kuma da alama ma ta manta da a gaban Haisam d’in take, shi kuwa kafe bayan nata yay da ido da wani kalan expression mai wuyar fassaruwa yake kallon nata, bayan sun yi sallama ta juyo suka had’a ido ta sakar mashi d’an murmushi shima ya d’an yi mata, juyawa tay zata tafi taji yace in ta gama abunda take zasu gaishe da Hajiya ta juyo tace mashi to sannan ta tafi, tana komawa Bedroom d’in bada jimawa ba akai knocking kopar ya bada izinin shigowa, Amadu ne ya shigo ruk’e da jakar Fatun da d’an murmushi ya nufi cikin parlon ya tsaya daga gefe yana gaishe da Haisam d’in, bayan ya amsa ya nuna mashi armchair yace ya zauna mana, mik’ewa yay ya nufi hanyar Bedroom d’in da alama kiran ta zai yi, yana tura kopar daidai ta kawo bakin kopar zata bud’e ta yafo mayafi golden da ta sa jiya da yake a atamfar akwae golden brown harda takalman da ta saka jiyan mahad’in gyalen half cover masu tsini sun k’ara mata tsawo ta tattara gashin ta a baya ta sa red ribbom sai yayi kaman ta saka hular gashi don ya rufe gefe da gefen fuskar, tura kopar da yay ta buge mata goshi da sauri taja baya had’i da sa hannu guda ta dafe wurin da ta bugen, bai yi zaton tana a bakin kopar ba yay moving zuwa inda take tsaye ya kai hannu ya cire hannun ta da ta dafe goshin wurin har ya d’an canza kala, bin wurin yay da kallo ya kasa furta komae don gaba d’aya wata irin kasala yaji ta fara saukar mashi sakamakon K’amshin ta da ya cika mashi hanci, jin yayi shiru yasa ta d’aga ido ta kalle shi suka sauka cikin nashi nan take gabanta ya fad’i ganin irin kallon da yake mata da sauri ta sauke idon ta k’asa, d’ayan hannun nashi slowly ya zagaya dashi bayan ta ya matso da ita suka had’e da juna nan take wutar Fatuu ta d’auke ta fara shiga wani irin yanayi dama kuma a tsume take har saida ta d’an runtse ido, jikinta ne ya canza wata irin kasala ta baibaiye ta wani abu ya fara mata yawo a jiki ga k’afafuwan ta na neman kasa d’aukarta, sauke gudan hannun shi da ke ruk’e da natan yay k’asa ya d’an sunkuyar da face d’in shi Slowly ya d’an fara matsawa da ita saitin tata, jin saukar breathing d’in shi a gab da Fuskar ta yasata d’agowa da sauri har saida gabanta yay wani irin bugu ganin fuskar shi kusan saura kad’an ta had’e da tata, wani irin kallo mai wuyar fassarawa suka shiga bin juna da shi, da k’yar Fatuu ke daurewa gudun kada ta zaqe don ta kai wata ga6a da take neman rasa control idanun ta har sun fara lumshewa sai k’ok’arin daidaita su take amman abun yaci tura kawae sai ta rufe su gaba d’aya, bin dogayen eye lashes d’in ta yay da kallo sai d’an far far suke sakamakon idanun nata dake motsi, numfashin ta ne ya nemi tsayawa jin ya had’e faces d’in su nan take jikinta ya fara d’an rawa ta koma yin numfashi da sauri da sauri shima nashi da d’an k’arfi yake fita yana had’uwa da nata, sun d’an d’auki lokaci a haka suna ta shak’ar scent d’in juna, can ya janye fuskar ta shi a hankali ya maidata gefen tata ta yadda kwantaccen sajen shi ya had’e da gefen tata fuskar cikin wata irin murya mai fuzgar mai sauraro ya furta “am sorry, bansan kina a wurin ba….” Kasa ko d’aga mashi kai Fatuu tay idonta still na a rufe taji ya k’ara furta “Uncle d’in ki na jiran ki a parlor” yana yin Maganar ya d’ago ya cire hannun shi dake tallabe da ita ya juya ya nufi hanyar Laundry ba tare da ya ko kalleta ba, da k’yar ta d’an bud’e idanun ta da suka gama canza kala tabi bayan shi da kallo kar ya shige ya rufe kopar, kasa cigaba da tsayuwar tay don gaba d’aya jikinta ya gama mutuwa da k’yar ta ja jiki zuwa bakin gado ta zauna dabas still breathing heavily, hannu tasa ta dafe goshin ta ta d’an sadda kai, ita kad’ai tasan mi take ji a jikinta, da k’yar ta fara k’ok’arin daidaita kanta tunowa da yace Kawu Amadu na a parlor, mik’ewa tay jiki a mace ta nufi kopar ta bud’e, bayan ta fito saida ta k’ara tsayawa a cikin Corridor ta k’ara daidaita natsuwar ta sannan ta nufo cikin parlon, tana shiga suka had’a ido ta fara mashi murmushi wanda yafi kama dana yak’e shima d’an murmushin yake mata ta nufi inda yake, a d’ayar armchair d’in ta zauna ta gaishe da shi ya amsa shiru ta biyo baya don sai taji kaman muryar ta ba a daidai take ba, hannu ya kai ya d’aukko bag pack d’in daga k’asa ya d’auro ta kan hannun kujera yace mata ga ta nan da k’yar tace mashi ta gode, ganin ya mik’e alamar tafiya zai yi yasa cikin yar rawar murya tace don Allah ya tsaya yay breakfast yay mata wani kallo mai kaman harara ya juya ya tafi ta k’ara ce mashi ta gode ya d’aga mata kai kawae lokacin ya bud’e kopar ya fita, zaune tay turus tama rasa mi yake mata dad’i a hankali ta d’aga ido ta kallo kopar Bedroom d’in ta shiga tunanin zuwa zatai tay mashi magana su tafi ko kuwa, ji tay bazata iya zuwan ba tay zaune zuciyar ta na tariyo mata abunda ya faru a tsakanin su, tana haka bayan wani lokaci taji k’arar bud’e kopar Bedroom d’in aikuwa da sauri ta sunkuyar da kanta k’asa, nufo cikin parlon yay idon shi akanta ya tsaya daga gefen ta taji yace zasu iya tafiya sai lokacin ta d’ago ta kalle shi ta d’an d’aga mashi kai, mik’ewa tay har zai juya sai kuma ya dakata ya juyo yana kallon ta ta d’an kawar da fuskar ta, “How are feeling, ko wurin na ciwo muje Hospital?” D’an kallon shi tay had’i da girgiza kai a hankali tace a’a yama daina zafin ya jinjina kai yay gaba ta bi bayan shi a ranta ta shiga raya kenan duk abunda yay mata d’azun ban hak’uri ne Saboda ya buge ta, yana gaba tana biye dashi suka shigo harabar gidan, suna cikin tafiyar ta kai idon ta can gefe wurin parking space ta hangi d’awisu ya bud’e jikin shi yana kuka gwanin burgewa, murmushi Fatuu ta saki tunowa da can baya lokacin da ta kawo ma shi Fruit na karin ciwo ta iske zashi Masallaci har suka fito tare ta tsaya a harabar tana ma d’awisun wasa shi kuma ya nufi hanyar Masallacin yana d’an d’angyasa k’afa Saboda raunin da yaji da kwalba, gab da zai shiga ta kware murya tace Ya Handsome kayi man Addu’a Allah yasa in zama likita ya d’aga mata kai ba tare da ya juyowa ba, fad’ad’a murmushi tay bata ta6a kawo wa a ranta wai zasu yi aure ba don ita auren ma bai gabanta a lokacin duk da kuruciya, ko ba aure a tsakanin su Haisam nada daraja a wurinta ta silar shi ne ta san kanta ko lokacin da ta kasa mashi uzuri da abu ya Faru tsakanin su harda girman da yake da shi yasa duk da tana tunanin laifi yayi mata amman bata son girman shi ya fad’i ne gashi hakan ba K’aramin karya mata zuciya yay ba don tana ganin ita tana k’aunar shi shi kuma sha’awar ta yake ashe duk ba haka bane, Kallon bayan shi taci gaba da yi wata irin k’aunar shi na ratsa mata zuciya har tana d’an yin murmushi a haka har suka k’araso part d’in suka shiga,
lokacin da suka shiga basu samu kowa a cikin parlon ba an dai gyara shi fess sai k’amshi ke tashi, Hanyar Bedroom d’in ta ya nufa ta bi bayan shi, knocking kopar ya d’an yi daga ciki ta bada izinin a shiga ya tura da yar sallama ya shiga, tana zaune a bakin gado idanunta sanye cikin glasses hannunta ruk’e da Littafin Addini tana dubawa bata dad’e da komawa cikin d’akin ba bayan ta yi Breakfast, d’ago ido tay ta kalle shi tana niyyar yin Magana Fatuu ma ta shigo da sallama Hajiya ta saki murmushi tana amsa mata kafin tace “Maraba da Amaryar mu” d’an sadda kai tay Hajiyar ta nuna mata gefen ta da hannu alamar tazo ta zauna, tsaye Haisam yay daga gaban gadon bai zauna ba ya gaishe da ita ta amsa tay mashi an tashi lafiya, kai idon ta tay kan Fatuu da ta d’an sunnar da kai da murmushi tace “Amarya an tashi lafiya ya bak’unta kuma?” a hankali tace Lafiya lou,
“Ba dai yar kunya muka fara dake ba” Hajiya ta tambaya tana murmushi hakan yasa Fatun d’agowa itama murmushin ne akan fuskar ta a hankali tace mata a’a, “Yauwa to, ni ba surukar ki bace Kakar kice a hakan zaki cigaba da kallo na muci gaba da wasa da dariya kaman da, don ma yanzu anyi hankali natsuwa tazo an rage sani nishad’i” yar dariya Fatuu tay ba tace komai ba, kallon Haisam tay “Kai kayi tsaye kaman wani Security ka samu wuri mana ka zauna, ko gadin Matar taka kake?” Fuskar shi a sake kaman zai murmushi ya kalleta ta nuna mashi Stool a gaban mirror tace ya d’aukko shi sai ya zauna, yin yadda tace yayi suka d’an yi shiru kafin ta fara magana,
“Alhamdulillah, duk abunda Allah yayi mai kyau ne, a koda yaushe muna rok’on Alkhairi so duk abunda muka ga ya faru damu in ma mai kyau ko akasin hakan Alkhairi ne, Fateema ina maki barka da shigowa wannan Family don a yanzu kin zamo wani 6angare nashi, ina fata zaki d’auke mu a matsayin dangin ki, ki rungumi kowa matsayin dan’uwan ki duk da bani da shakku akan ki nasan ki farin sani nasan baki da matsala to sai kinyi hak’uri don shi mataki ne nasara ba kamar a yadda Auren naku ya kasance, dole daga baya za’a iya fuskantan yan matsaloli bama fata in sha Allahu muna fatan Allah zai shige mana gaba, sannan ina son ki saki jikin ki kada wai ko don kiga ga yadda akai auren naki ki takura kanki Ki k’i yin walwala, duk aure aure ne duk kuwa yadda aka yi shi ki walwala ki farinciki ki Alfahari da Auren, gidan mijin ki naki ne so ba buk’atar takura kai, duk yadda bani da haufi akan mijin ki ance wai zo mu zauna zo mu sa6a, so a duk lokacin da yay maki wani abu da baki ji dad’in shi ba ki k’ok’arin yi mashi Magana kada kice zaki bar abun a ranki duk d’an Adam ajizi ne zai iya yi maki laifi ba tare da ya ankare ba, ta hanyar yi mashi magana ne zai gane har ya gyara laifin shi, in kuma bai gyaran ba wanda bana tunanin hakan ni kizo ki sanar dani kar kiji wani abu, duk yay maki wani abun da kike tunanin fad’i ma wani don neman mafita ko shawara kizo wuri na kar kice zaki kai k’ara gidan ku hakan ba komai yake jazawa ba face matsala, zai iya maki abu kije ki fad’a daga baya ku shirya ki manta ma amman su kuma abun na nan a ran su watak’il su k’ullace shi ko makamancin hakan, don haka k’opa ta a bud’e take duk in kina da wata matsala kizo gun Hajiyar Sanata ki fad’a mata ni kuma in sha Allahu zanyi k’ok’arin ganin na daidaita komai, ina Fatan zaki cigaba da yi mashi biyayyar dana san kina mashi kada don ya zama mijin ki kice zaki rage kan hakan a’a a yanzu k’arawa ya kamata kiyi don muhimmancin shi a yanzu yafi na da ya tashi daga Yayan ki Handsome ya koma Mijin ki wanda Aljannar ki ke a tafin kafar shi” d’an dakatawa tay kan Fatuu a k’asa haka Haisam d’in Fuskar shi na a gefe,
“Na dawo gare ka Zakee manyan dawa, ga Fateema nan Amana ce a wurin ka duk da nasan kasan da hakan amman ina fad’a maka ne don kada ya zama ba wanda ya fad’a maka hakan, ka ruk’e ta Amana dama can kai kamar guardian ne a gare ta to yanzu matsayin ka ya koma biyu don haka sai ka linka komae, kuma don ta zama taka ba yana nufin ta zama baiwar ka ba duk kyautatawar da zaka yi mata lada zaka samu haka in har kaci zarafin ta ka munana mata tabbas zaka samu zunubi don haka ta zama taka ne don ka kyautata rayuwar ta, sannan ina son jan hankalin ka kayi k’ok’arin zama adali ga matan ka nasan ba sai nayi maka bayanin yadda zaka zama adali ba kasan miye yin Adalci tsakanin mutane, idan har ka za6i yin rashin Adalci to ka bud’e ma kanka da kanka kopar matsalolin da zasu hana maka kwanciyar hankali ga kuma zunubi a wurin ubangiji, a k’arshe ina Addu’ar Allah yasa Albarka a Auren ku ya kauda duk wata fitina, yasa ya zame maku silar shiga Aljanna gaba d’ayan ku, Amin ya Rabbi” a hankali Haisam ya amsa da Amin Fatuu kuma a cikin rai ta amsa Hajiya ta kai hannu ta d’an bugi shoulder d’in ta tace ita bazata amsa ba ta d’ago tana yar dariya tace ai ta amsa,
“Oh Fateema ni wannan in nayi sakaci ban yi da gaske ba yar gaisuwar da nike samu yana zuwa ma ai sai ki hana shi ya tattara ni ya zuba a dustbin” cikin rashin Fahimta Fatun ta d’an waro ido Hajiya taci gaba “eh mana, kina irin wannan kwalliyar ina zai rink’a tunawa da wata tsohuwar matar shi…” Tun kan ta rufe baki Fatun tasa tafukan hannuwan ta ta rufe fuska Hajiyar nata dariya, a hankali Haisam ya d’ago ya kalli Fatun suka had’a ido da Hajiya ta d’an harare shi cikin wasa yay d’an guntun murmushi ya juyar da fuskar shi gefe,
“Yanzu dae ki bani cin hanci sai in yafe maki shi in kuma fad’a maki abubuwan da zasu sa ki kama shi a hannu” cire tafukan hannuwan tay tana murmushi bata ce komai ba, mik’ewa yay yace ma Hajiyar zai d’an je G.r.a tace a dawo lafiya ya nufi hanyar fita, kallon Fatuu Hajiya tay ta d’an kai mata bugu tace bazaki tashi ki raka shi ba yaran zamani duk baku san abunda ke sa ana kama miji ba, mik’ewa tay a kunyace ta nufi hanyar fita Hajiya ta bita da ido tana murmushi a ranta ta ayyana Allah kenan gwanin hikima, wasu mutanen na shigowa rayuwar mu ne in ma su amfane mu ko mu mu amfane su, wasu su tsaya wasu kuma su tafi bayan sun taka rawar da zasu taka, a fili ta furta “Allah kasa Mudace”, tana fitowa har ya kusan fita daga parlon taja ta tsaya a bakin corridor, kamar yaji a jikin shi ya juyo suka had’a ido, dakatawa yay ganin haka yasa ta nufe shi walking slowly, a d’an gaban shi ta tsaya tana bin shi da kallo ganin ya kafeta da ido yasa cikin yar inda inda tace “D…dama Hajiya ce tace in rako ka” da k’yar ta kai Maganar Saboda kallon da yake bin ta dashi ba Arzik’i ta sunkuyar da kanta,
“Ok thanks, ki koma” taji yace ta d’ago, kai ta d’an d’aga mashi yana shirin juyawa tace “Sai ka dawo Allah ya tsare” dakatawa ya sake yi ganin yanayin fuskar shi kaman zai murmushi yasa itama ta d’an yi mashi, “Do you need something?” da sauri ta girgiza mashi kai alamar a’a ya d’aga kai ya wuce, saida taga fitar shi sannan ta juyo tana d’an sakin Murmushi ta nufi komawa Bedroom d’in Hajiya…………..
…
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page :Â Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page :Â @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel:Â Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.