Haihuwa Da Hanji Page 38 Hausa Novel
“Dakata!!”Wata murya mai amo tayi maganan.Chakk suka tsaya daga ɗora wukan a maƙogoron kawun.”Mecece alaƙarshi da ƙungiya?”Yayi tambayar a kausashe.”Babu mai girma shugaba””Ku kyaleshi jinin shi bai halalta mana ba”Suman daaɗi ne ya tafi da kawu Dukda azabar da yake ciki, dunkule shi suka yi suka tura cikin buhu aka saɓe shi kaman kayan wanki aka fitar sai haushi suke ji bai musu amfani ba tsabar lalacewarshi, a booth na mota aka saka shi sai da suka yi tafiya mai uban nisa kan suka buɗe booth ɗin suka cilla shi ƙasa suka yi tafiyarsu.Ya fi awa nawa yana mutsu-mutsu ga zafin rana Allah ya kawo wani mai ruwa ya taimake shi ya buɗe buhun sai ya fara tari da mayar da numfashi sama sama, da kyar yake ambatar “Ruwa! Ruwa!!”Mai ruwan ya bashi ruwa a gora ya sha sossai yana sauke numfashi kan ya fara kalle kallen wurin da yake, wani kauye ne na daban “Me ya saka ka cikin buhu bawan Allah?””Sace ni aka yi ‘yan yankan kai ne suka sace ni Allah ya kubutar da ni”Abin mamaki ya ɗauke shi har gidan mai garin garin suna da karamci aka bashi wuri yayi wanka ya wanke najasar jikinshi ya rama sallaolin da suka hau kanshi, har abinci ya ci aka ba shi kuɗin mota ya nufi Dutsen-wai cikin zuciyarshi saƙe-saƙe ne mai yawan gaske ga bakin cikin abin da su larai suka yi mishi ga yadda ya sha jinin jikinshi da abin da ya riska a kwanakin wanda har abada ba zai taɓa mantawa ba, yana isa Dutsen-wai gidan mai gari ya nufa yana neman iso aka mishi iso ya ce “Toh dama na zo ne in sanar kuma in nemi a gargaɗi duk jama’ar garin nan cewa duk wanda ya sake cewa Ɗiyata Afeefah Mayya sai mun yi shari’a har kotun koli don Afeefah ba Mayya ba ce, ita kuma ba Annoba ba ce””Toh fa da kanka Malam Labaran? Kana lafiya kuwa?””Lafiyata ƙalau kawai dai na san Afeefah ba Mayya ba ce kuma kar a sake ce mata haka don abin da Mayu suke yi ko a mafarki ba zata iya ba wannan abu ne da ya shallake dukkan tunanin mai tunani.”Ya ƙarasa cikin tabbatarwa da jimami.”Dama tun farko tsantsar jahilci da son zuciya ya sa kuka lakaba mata abinda ba shine ba, ashe kenan mutum ba zai taɓa mutuwa haka siddan ba? Har fa tambari kuka buga na cewar tun tana ciki ta cinye ɗan uwanka amma Alhamdulillah tunda ka gane gaskiya kuma kana shirin tsayawa a kanta sai ka yi wa kanka faɗa ka nemi tsari da jahilci don wallahi mugun ciwo ne kuma shi ke ɗawainiya da mafi yawanku cikin wannan ƙauye”.Malam liman ne ya jero wannan jawabin, kawu ya gamsu har ya ji jikinshi na ɗan sanyi barin ma da malam liman ya sake nusar dashi akan Allah shi ba ruwanshi, da ya turo mu duniya yayi mana umarnin mu nemi sani a kanshi kafin mu bauta mishi, ba ka da hujjar kare kanka da rashin sani a wurin Ubangiji matukar baka tashi ka nema ba.kan ya dawo gida labarin dawowarshi ya riske su bai damu da zancen mutane ba da wasu ke cewa kila ta cika shi da kuɗi ne wasu na zaton ko don ta auri mai kuɗi yanzu ai dole ya ja ta jiki. Shi kuwa hankalinshi ya fi tafiya ga jan hankalin da liman yayi mishi na neman ilimi Dukda a yanzu wani tataburzun ne gabanshi don saurin da yake zabgawa yana so ya tabbatar babu kowa ne a gidanshi kafin faɗuwar rana.Kaman daga sama suka ganshi ya faɗo Asabe murfin tukunya ce a hannunta sai da ya subuce ya faɗi ƙasa ya tsaya kyamm yana kallonsu “Toh ban mutu ba! Kuma dama an ce sai abu ya same ka kake sanin masu sonka ashe dukkanku maƙiyana ne na tara? Ashe za ku iya bari na in mutu? Toh an gama wallahi gwara in zauna ni kaɗai na da in cigaba da zama da ku don haka kowaccenku ta tattara ya nata ya nata ta bar min gida na sake ku saki ɗaiɗai…””Innalillahi wainna ilaihi rajiun Malam ka tsaya ka saura…”Ya katse ta da masifa “Babu abin da zan saurara Asabe! dole ku bar min gida a yau ba sai anjima ba kuma ku tattaro yaranku kaf ku fice min daga gida a tabbatar kuma an dawo min da kudade na mugayen banza mugayen wofi”Sai masifa yake ko ya tsaya ya saurare su abin ya mishi zafi rigima fa sossai ya kachame don suma sun ce in zasu tafi ba zasu tafi da yara ba tunda ba da su suka zo a kullin gararsu ba ko hutawa bai yi ba aka sake komawa gaban manya ya rantse shi ya sake su su tafi kuma baya bukatar ko wani ɗa don za su iya saka wuyanshi gabas su yanka tunda suka iya watsar da rayuwarshi alhali yana chan cikin tsaka mai wuya.”Labaran!”Malam liman ya kira shi ya amsa”ka san ko ma menene suka yi laifinka ne?””Ta yaya? Ina fa chan gaban azzalumai mutanen nan don basu da imani suka ƙi daukar waya alhali ga abin da nace su yi da kuɗina ba nasu ba su kubutar da ni, ba don Allah na so na da sauran numfashi ba da na jima da mutuwa yanzu zaman makoki ake””Labaran ka yarda kaso mai girma na abin da ya faru laifinka ne””shiyasa na ce ina so in ji ta yaya?”*****A ɓangaren Rayyan ba zai ce ga yadda yinin ya kasance mishi ba don baya gane komai, kawai yana so ya ji an daina ko magana a gangarshi ya ji shiru na ratsawa don ya samu damar gamsar da kanshi cewa da gaske ya rasa mace ɗaya jal mafi muhimmanci a rayuwarshi, wacce ta cire shi daga wahala ta bashi so da kauna ta raine shi fiye da yadda ta raini ‘ya’yan da ta haifa da cikinta, ko gaisuwa aka mishi sai dai ya gyaɗa kai don baya magana, idanunshi har tsoro yake ba wa wasu idan ya buɗe, An yi an yi ya ci wani abu tun safen har dare ko ruwa bai yarda ya sha ba don raɗaɗin da yake ji daga zuciyarshi har akan harshen shi baya tunanin zai iya cin wani abin don cikin nashi ma jinshi yake a cushe, ganin yana shirin yi wa kanshi illa ya sa Sulaiman yi mishi allurar bacci don daga ƙarshe numfashi wahalar fita ya fara mishi.Su basa yarda da wani zaman makoki daga yinin da aka binnetan duk na waje suka watse, Afeefah tsabar yadda ta kasa yarda cewa Mammi ta tafi a ɗaki ta cigaba da zama hakan ya mata hijabi da haduwa da mutane dayawa ciki har da su mommy da Saleem, don Saleem yayi niyyan kwana a tare da Rayyan mommy ta sanar dashi yayi aure ai, ya shiga tsantsar mamaki ya kuma ji babu daaɗi a lokaci guda, yana mamakin yadda Rayyan yayi aure cikin kankanin lokaci alhali shi bai taɓa ji Rayyan ya furta sunan wata macen a matsayin buduruwa ba, ya kuma ji ba daaɗi yadda bai kasance tare dashi a bikin ba amma ya mishi Fatan alkhairi ya ɗauki su mommy suka koma gida don har yanzu a tsohon gidansu suke har shi, ya ce ba zasu koma chan inda ya zauna da Sabrina ba wani zai saya musu don bai san me suka binne ciki ba.sai dare ta fito ta nufi ɗakin Abeeha dake kwance rib da zazzabi, a gangarta ta zauna tare da rike hannunta “Afeefah da gaske Mammi ta tafi ko? Idan na je ɗakinta ba zan ganta ba ko? Yanzu shikenan ba mu da uwa ba mu da uba?”Ta danne hawayen da ke shirin ziraro mata tace “Haka Allah yake lamarinshi Adda Abeeha, dukkan mu da muke rayuwa a yanzu kwananmu ne bai kare ba idan ya ƙare dole za mu tafi””ba za ki gane raɗadin da nake ji ba Afeefah”Ta girgiza kai “Duk wanda za ki ji Adda Abeeha na ji shi, kar ki manta ko da aka haifeni ba ni da uba, ban kuma buɗi ido na tarar da mahaifiyata ba sai a hoto kin ga ko zafi da raɗaɗin maraici na fara dandana, shi ne tun a cikin cikin mahaifiyata har zuwa zanin goyona. Adda Abeeha ku gode Allah kun rayu da iyayenku har girman ku…”Kuka ne ke shirin kwace mata amma ta dake ta danne.”Don Allah ki daure ki daina yi wa Mammi kuka haka! Mu bita da Adu’a shi ta fi buƙata a halin yanzu”Matar uncle Sanusi dake ɗakin tace “maganar Afeefah gaskiya ce Mahaifiyarku Adu’a take buƙata Abeeha ba kuka ba ita ai tata ta yi kyau! Allah ya sa jinyar da ta sha ya zama kankarar zunubanta ne”Suka amsa da Ameen.”Mommy ya Adda Jannah?”Afeefah tayi tambayar a sanyaye.Matar uncle sanusi tace “Ta farka amma tana under kulawar likitoci don ɓarin ya zo ne bagatatan ga cikin ya fara girma, ta dai ji jiki kam sai dai Allah ya kawo na moro suna chan tare da su mamanku”Ta fahimci da su matar uncle Mansur take nufi don haka Adu’a suka mata na samun ingantacciyar lafiya.Abeeha ta dubi Afeefah “Yaya fa?”Shiru Afeefah tayi don bata san me zata ce ba, a lokacin mommyn ta fita daga ɗakin “Yana ɗakinshi Adda Abeeha”Miƙewa zaune Abeeha tayi ta riƙo hannunta.”Afeefah na san zaman ku da yaya babu daaɗi, na kuma san kina tsoron shi da kuma tsoron kasancewa inuwa ɗaya da shi amma wallahi a yanzu babu wanda Yaya zai fi buƙata kaman ke! Mammi za ta yi farin ciki idan kika kular mata da shi at his worst moment irin wannan…””Ta yaya Adda Abeeha? Mutumin da bai taɓa min kallon matsayin abu mai muhimmanci ba, wanda bai taɓa ɗaukata da kima ko daraja ta mace ba macen ma matarshi?”Tayi maganan cikin sanyi, tun ɗazu yaƙi take da zuciyarta akan Rayyan, tana so ta je inda yake amma tana tsoro ta san yana buƙatar wani amma bata san ta yadda za ta rarrashi mutum irin shi mai dakakkiyar zuciyar da baya bayyana rauninshi a fili ba.”Trust me Afeefah za ki iya, na san kema kin san me ya fi buƙata a yanzu tunda duk waennan abu kin yi going through a rayuwarki… A lokacin da muka rasa Abbu akwai Mammi Dukda bata da lafiya ta tsaya mana dukkanmu har saida muka zama daidai muka amshi ƙaddararmu amma a yanzu bata nan ita da ta fi kowa sanin Ya Rayyan a duniya, na sani a kwanakin nan bacci sai dai idan da allura ko magani hakanan zai yi ta ciwo amma ba zai nuna ba, ba zai yi magana ba ba zai ci abinci ba don Allah ki taimakemu ki kula dashi matsayin ki na matarshi”Kai Afeefah ta gyaɗa ganin Abeehar ta fara hawaye, tun dazu take so taje gareshi har cikin zuciyarta amma bata san me zata yi ba in taje ɗin, Miƙewa tayi tana kallon Abeeha”Ki yi bacci zan kula da komai in shaa Allah”Godiya Abeeha zata yi mata amma tayi saurin ficewa Abeeha ta mayar da idanun ta rufe hawayenta na gangara.Afeefah na barin sashen tayi ɗakin ta wanka tayi saboda yanayin zafi da ake dan yi tayi Sallar isha ta jima tana yiwa Mammi Adu’a tana hawaye kan ta yi shafa’i da wutiri ta nemi riga da wando na bacci jajaye ta saka ta ɗora hijab har ƙasa a kai sai ta fito ta nufi ɗakinshi, sai da tayi knocking ta buɗe ta shiga hasken a kunne don haka ta hange shi kwance kan gadon ɗakin idanunshi a rufe ya ɗan dukunkune kaman mai jin sanyi amma kuma bai rufa ba, kamshin shi da ya kama ɗakin na nan yadda yake ta nufi gaban gadon ta ɗan tsaya a kanshi kaɗan tana kallonshi.Allah sarki mutuwa, in ba mutuwa ba mai ya isa ya jijjiga Rayyan har haka a yini guda har ya rame, fuskarshi dake fari tass yayi wani irin ja musamman kan hancinshi, daga yanayin baccin da yake zaka san ba na farin ciki bane don a baccin ma sai yamutsa fuska yake, a hankali ta ja bargon ta lulluɓa mishi har kafada, sai ta isa wardrobe dinshi ta dubi wani bargo ta zo ta shimfida a ƙasa ta zagaya ɗaya ɓangaren ta ɗauki pillow daya dake cike da kamshinshi zuciyarta na bugawa sossai ta kwanta a ƙasan bayan ta kashe wutan ɗakin, ko motsi tayi sai taji kaman yana nan a kusa da ita saboda yadda daga bargon har pillown ke fidda azabbaen kamshin shi ga kasancewar ta under roof ɗaya da namiji abin da bata taɓa ba sai take jin ta wani iri da kyar bacci ya ɗauketa. Chan cikin dare sai ta fara jin kaman numfarfashi a ɗan tsorace ta farka ta miƙe zaune sai ta ji kaman daga kan gadon da yake kwance ne da sauri ta miƙe tsaye ta tafi ta kunna hasken ɗakin ta nufi gangar shi.Ya haɗa zufa yayi sharkaf sai juye juye yake kaman mai mummunan mafarki, numfashinshi na seizing kaman mai ciwon asthma hankalinta ne ya tashi bata san ta riƙe hannunshi ba tana jijjigawa”Ya Saraki! Ya Saraki ka tashi..!”Duk ta ruɗe saboda yadda yake yin kaman zai mutu, da karfin gaske ta jijjigashi hakan ya sa ya buɗe rinannun idanunsa ya zuba mata yana sauke numfashi a hankali hankali, hawaye ne ke bin idanunta suna diga a duk inda suka samu zarafi kama daga gaban hijabinta har kan hannunshi dake cikin nata.”Mummunan mafarki kake? Sannu ka ji? Bari na kawo maka ruwa”Duk ta rikice tsabar yadda ta ganshin ya dameta, da sauri ta nufi frigde ta kawo mishi ruwa da kyar ya miƙe zaune ya ɗan yi tapping wayanshi ya kalli time karfe biyu, lumshe ido yayi ya buɗe a kanta tana miƙa mishi ruwan, bai san me yasa ya karɓa ba ya dai tsinci kanshi yana shan ruwan yana jin wani abu dake tsaye mishi a makoshi na sauƙa a hankali, sai kuma ya ji cikinshi na murdawa yana jin amai na taso mishi rabon shi da abinci tun jiya da daddare don ko karyawa bai yi ba rashin lafiyar mami ya riskeshi, ruwan ya miƙa mata tana daga tsaye tana kallonshi har lokacin idanunta na cike da kwalla.Ƙoƙarin sauƙa yake daga gadon ba tare da ya ce uffan ba sai jiri ya kwashe shi ya tafi zai faɗi da wani irin hanzari ta riƙe shi”Ya Saraki baka da lafiya…! Jikinka zafi sossai me kake so in kawo maka?”A karye take maganan, kaman ba zai yi magana ba yana tsaye tana dafe dashi Dukda ya tabbatar in faɗuwar ne ɗan tiny body ɗintan nan bai isa riƙe shi ba a hankali yace “Amai…!”Kalma na farko da ya furta kenan tun bayan Ameen da yake ta cewa in an yiwa Mammi Adu’a.”Amai za ka yi? Sannu mu je bayin ko in kawo maka abu ka yi daga nan?”Shiru ya mata sai ya yunkura zai cigaba da tafiya nan ta gane bayin yake son zuwa da taimakonta ana tafiya ana hutawa suka shiga bayin, sai da ya dafe jikin sink ya kalleta ya kalli kofa.”In fita? Za ka iya?”In ba don halin da yake ciki ba za ta iya rantsewa ya Harare ta, bata ƙara magana ba ganin ya zuba mata idon da suke sake firgitata da bata tsoro ta fice da sauri sai da ta rufe kofa ya lumshe ido.Kai tsaye kitchen nasu taje ta haɗo tea mai kauri ta dawo ɗakin gadon da ya jajjanye bedsheets ɗin ta gyara ta tsaya daga gefe kaman security, ganin ya jima bai fito ba ta yunkura ta nufi bayin tana shirin yin knocking yana buɗe kofan da sauri ta matsa baya, ya kalleta ya dauke kai ganin bashi da ƙarfin jiki ta matso ta kama hannunshi bai hanata ba har suka isa kan couch ya zauna yana jinguwa tare da riƙe kanshi da kaman zai fashe yana cewa “Asshhhh!”Kaman zata yi kuka take jera mishi sannu.Tea din ta ɗauko “Ya… Saraki!”Ta faɗa a rarrabe, ya ɗan buɗe ido ya kalleta yana jin sunan na mishi wani iri har a cikin jikinshi “ka sha tea ka ga cikin ka babu komai sai ka sha magani Don Allah…”Ya lumshe ido kawai fuskar nan tamau, hawaye ne ya zuba mata ta ɗan ja Shesheka sai ya bude idanun yana kallonta ya zubawa hawayen idanu haushi yake ji, takaici yake ji Meyasa shi ba zai yi kukan kaman kowa ba? Meyasa take da arhar hawaye a sadda shi yake nema? Zuciyarshi zafi yake mishi raɗaɗi da kuna yake mishi.Hannu ya miƙa mata don yana da buƙatar yin Sallar isha don bai yi ba kuma ba zai iya samun karfi ba matukar ba abu bane ya shiga cikinshi, da sauri ta miƙa mishi ta koma gefe tana share fuskanta wanda ta rasa me yasa hawayen nata suka ki tsayuwa muddin ta kalleshi sai ta ji suna zubowa tsabar tausayinshi.Kurba bai fi hudu yayi ba ya ajiye, ta dubo magungunanshi ta ajiye mishi ya kalleta tace “Don Allah Ya Saraki ka sha ko zaka samu sassauci…!”A karye tayi maganan yayi shiru “Wanne ne zan cire maka?”Ya sake yin shiru “Ya Saraki…!””Get out of this room..!”Yayi maganan a kausashe ta girgiza kai za tayi magana ya ce”Nowww!”Da ƙarfi yayi magana yana zaro mata idanu…


